Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

★DAKAKKIYAR ZUCIYA★!!!
Abdul'aziz sani mad akin giñi
Littafi Na Daya (1)
Part A.
A WANI ZAMANI CAN BAYA MAI TSAWO DAYA
SHUDE,A BIRNIN KISRA ANYI WANI SAURAYI
MAI
SUNA SHUBAIRU IBINI HAURAS.Shubairu ya
kasance dan kimanin shekaru talatin da uku
kuma
Allah yayi masa baiwa da yawa.Abu na farko ya
kasance kyakkyawa na gaban kwatance domin a
gaba daya birnin Kisra babu wani 'da namiji mai
irin kyawunsa.Abu na biyu shine yana da tarin
ilmi na addinai kala kala har guda tamanin da
uku.Abu
na uku yana da wata irin baiwa wacce mutane
suka kasa gane asalinta domin tana kama da
tsafi
wasu kuma su kirata da suna TSATSUBA.Ita dai
wannan baiwa yanayinta shine ko da Shubairu
baisan mutum ba bai taba ma ganinsa ba da
zarar ya kalli fuskarsa zai iya ganin duk abinda
ya faru
ga mutum a rayuwarsa tun daga kuruciyarsa
kawo
izuwa girmansa har abinda ya aikata a wannan
rana.Idan kuwa ya dafa kan mutum da hannunsa
na hagu zai iya ganin irin daukakar da mutum zai
samu ko kaskanta nan gaba a rayuwarsa.Wani
abin mamaki shine duk da yana da wannan baiwa
bazai iya gayawa mutum abinda zaiyi ya kare
kansa ba daga abubuwan sharrin da zasu same
shi.Shidai Shubairu bai kasance dan kowa ba a
cikin birnin Kisra,ma'ana shi ba dan sarakai bane
ko attajirai ya kasance maraya don tun yana yaro
dan shekara shida iyayensa suka mutu a lokacin
da suka fita bayan gari kiwon dabbobinsu yan
fashi
suka kawo musu samame.Bayan yan fashin sun
kashe iyayeyn Shubairu sai suka fara kokarin
sace
dabbobin nasu su gudu dasu.Bisa sa'a saiga
dakarun sarki Kuzzaru sun fito kewaye.Koda
sukayi
arba da yan fashin sai suka fatattake su suka
gudu.Dama a wannan lokaci iyayen Shubairu sun
fito kiwo ne tare da Shubairu kuma wani iko na
Allah yan fashi basu kashe shi ba.Shidai
Shubairu
tunda yaga an kashe iyayensa saiya fado kasa
daga kan rakumi ya rinka tsala kuka.Bayan
dakarun sarki Kuzzaru sun kori wadannan yan
fashi sai sukaga kyakkyawan yaro na gaban
kwatance zaune a kas bisa ciyawa yana ta
kuka.Shugaban dakarun wanda ake kira da
Huzaika
ya tunkaro Shubairu yana mai kura masa idanu
cikin alamun tausayawa.Koda Shubairu yaga su
Huzaika sun durfafo shi saiya tsorata ainun ya
yunkura zai ruga da gudu.Cikin hanzari Huzaika
yace dashi tsaya yakai wannan yaro kada ka guje
mu domin mu ba masu cutarwa bane a gareka
mun kasance dakarun sarki Kuzzaru mai mulkin
wannan birni na kisra.Koda jin wannan batu sai
Shubairu ya koma ya zauna ya cigaba da yin
kukansa.Da isowarsu Huzaika daf da gawar
iyayen
Shubairu sai suka cika da mamaki domin
dukkansu sun gane Mahaifin Shubairu wanda ke
kwance a mace.Domin shine yake kai madarar
shanu a gidan sarki kullum da sassafe ana
biyansa
bayan kowane kwana talatin.Cikin matukar
mamaki
Huzaika ya sake duban Shubairu yace yakai
wannan yaro ma'abocin kyawun fuska mene ne
dangantakarka da wadannan mamata? Cikin
shesshekar kuka Shubairu yace IYAYE
NANE.Koda
jin haka sai Huzaika yaji ya kamu da tsananin
tausayin Shubairu don haka saiya durkusa a
gabansa ya share masa hawaye sannan ya rike
kafadunsa yace mene ne sunanka?Shubairu ya
fada
masa sunansa.Huzaika yace daina kuka yakai
Shubairu ka sani cewa yanzu zan dauke ka tare
da
wannan dukiya ta iyayenka na kai ku wajen
sarki.Tabbas sarkina mutum ne mai tausayi dajin
kai don haka nasan cewa bazai bari ka wulakanta
ba.Koda gama fadin haka sai Huzaika ya mike
tsaye ya dauki Shubairu ya dora shi akan dokinsa
shima ya hau kan dokin ya zauna sannan ya
umarci dakarunsa dasu kada wadannan dabbobi
izuwa gidan sarki.Dabbobin dai adadinsu bai
wuce guda ashirin ba.Guda goma sha biyu shanu
ne
kosassu ragowar guda takwas kuwa rakuma ne
manya lafiyayyu.Nan take dakarun suka cika
aikinsu aka nufi cikin gari.Fadar a cike take
makil
da jama'a ana tafiyar da harkokin mulki kamar
yadda aka saba.Sarki Kuzzaru na zaune bisa
karagar mulki fadawa sun kewaye shi a gefen
damansa kuwa matarsa ce gimbiya Lamrisa a
zauna ta caba ado na gaban kwatance kuma
gashi
ta kasance mai tsananin kyawu tamkar ita tayi
kanta.A wannan lokaci gaba dayan mutanen
dake
cikin fadar satar kallonta sukeyi kuma kullum
haka abin ke faruwa domin kowa ji yake kamar
ya
sureta ya gudu da ita.A wannan lokaci sarki da
fadawansa na cikin raha sai hira suke da dariya
cikin nishadi.Ita kuwa gimbiya Lamrisa fuskarta a
murtuke take.Fiye da shekaru goma sha daya
baya
babu wani mahaluki daya taba ganin murmushin
gimbiya Lamrisa.Shi kansa sarki Kuzzaru rabo da
yaga murmushin Lamrisa da dariyarta tun
shekarar
farko da sukayi aure saadda take amarya.Bayan
cikar shekara guda ne da taga bata sami haihuwa
ba ta matsawa sarki Kuzzaru akan shiga neman
magani da bincike wajen bokaye.Abinda binciken
ya tabbatar shine matsalar rashin haihuwa daga
gareta ne kuma har abada ba zata iya haihuwa
ba.A kalla an ziyarci bokaye dari ba daya duk
bayani iri daya sukeyi.Tun daga wannan lokaci ne
gimbiya Lamrisa ta kamu da tsananin bakin ciki
ya
zamana cewa kullim bata da aiki DARE DA RANA
face kuka.Saida ta kwana arba'in a cikin wannan
hali sannan sarki ya samo kanta da kyar da
taimakon bokansa har ta saki jiki ta cigaba da
rayuwa amma fa tun daga wannan lokaci ne aka
daina ganin murmushinta da dariyarta.Babu irin
kokarin da sarki Kuzzaru baiyi ba akan yaga
Lamrisa ta manta da batun matsalar rashin
haihuwarta amma abu ya gagara don haka saiya
hakura ya zuba mata idanu kawai.Ana cikin
wannan zaman fada ne aka ga sarkin yaki
Huzaika
ya shigo dauke da kyakkyawan yaro dan shekaru
shida a hannu.Nanfa kowa da kowa ya kurawa
yaron idanu cikin tsananin mamaki,ba wani abu
bane ya haddasa hakan ba face ganin yadda
kamannin wannan bakon kyakkyawan
yaro sukà zama iri daya dana gimbiya Lamrisa
tamkar itace ta haifeshi alhalin kowa yasan cewa
bata taba haihuwa ba.Sa'adda Gimbiya Lamrisa
tayi arba da yaro Shuhairu sai ta cika da
tsananin
mamaki kuma nan take taji ta kamu da tsananin
son sa a cikin zuciyarta.Lamrisa dai bata san
sa'adda ta mike tsaye ba ta taryi Huzaika ta
mike
hannu zata karbi Shubairu tana murmushi.Al'ama
rin dayai matukar baiwa kowa
mamaki kenan a cikin fadar aka bude baki ana
kallonta.Kawai sai akaji sarki ya daka mata
tsawa.Cikin razana ta tsaya cak ta kame kamar
gunki.Sarki Kuzzaru ya mike tsaye ya tako
kafafunsa yazo har gaban sarkin yaki Huzaika
fuskarsa a murtuke ba sassauci.Gaba daya
mutanen fadar saida suka tsorata domin kowa
yasan cewa idan ran sarki ya baci kowa sai yaji
ba
dadi.Duk da cewa ya kasance mutum ne mai
saukin kai,hakuri,tausayi da jin kai.Kai wasu ma
daga cikin jama'ar dake fadar tuni jikinsu ya
kama karkarwa saboda tsoron kada sarki ya
fusata ya
doka dirkar gini da hannunsa fadar ta rushe gaba
daya kowa ya hallaka tunda ya kasance
gagarumin
Sadauki mai karfin Allah ya isa.Sarki Kuzzaru ya
dubi sarkin yaki Huzaika a fusace yace yakai
dirkar
birnin Kisra a ina ka samo wannan kyakkyawan
yaro kuma mene ne dalilin da yasa ka shigo
dashi
nan fadata?Koda jin wannan tambaya sai sarkin
yaki Huzaika ya risina cikin biyayya yayi gyaran
murya sannan yace ya shugabana dazu bayan na
fita zagaye da safe tare da dakaru don tabbatar
da
tsaron gari kamar yadda ka umarcemu dayi
kullum sai kawai muka hango wadansu yan fashi
suna
kokarin kada wadansu dabbobi izuwa cikin
daji.Nan take muka sukwani dawakanmu izuwa
kansu ai kuwa suna hango mu sai suka tarwatse
suka ruga izuwa cikin jeji.Muna isa inda
dabbobin
suke mukayi arba da gawar mutane biyu,mace da
namiji.Namijin dai ba wani bane face Lunzaru
mai
kawo madarar shanu nan fada kullum da
safe,macen kuwa matarsa ce mahaifiyar wannan
yaro wanda muka tsinta zauna a kas kusa da
gawar tasu yana ta sheka kuka.Ya shugabana na
sani cewa kai mai adalci da jin kai ne bisa haka
ne na dauko wannan yaro tare da dabbobinsa na
kawo su gareka domin yaron yana bukatar
taimako
tunda yanzu ya zamana maraya.Sa'adda Huzaika
yazo nan a labarinsa sai kawai yaga hawaye ya
zubo daga idanun sarki cikin sanyin jiki sarki ya
sumbaci goshin Shubairu sannan ya karbeshi
daga
hannun sarki yaki ya mikawa Gimbiya Lamrisa ya
dubeta cikin murmushi yace karbi wannan yaro
yake matata yau kin sami mai kore miki bakin
cikin daya addabi zuciyarki tsawon shekaru goma
sha daya.Koda jin wannan batu sai fadar gaba
daya ta rude da shewa masu kade kade da bushe
bushe suka kama aikinsu.Ita kuwa gimbiya
Lamrisa saita rungume yaro Shubairu ta fashe da
kukan farin ciki ta ruga izuwa cikin gidan
sarautar.Sarki Kuzzaru ya koma kan KARAGAR
MULKI ya zauna sannan ya share hawayen dake
bisa kumatunsa ya dubi jama'ar dake cikin fadar
gaba daya yace yaku jama'ata kuyi sani cewa a
yau ina cikin tsananin farin ciki haka kuma ina
cikin matukar bakin ciki.Ba komai ne yasa nake
wannan farin ciki ba sai domin a yau ne matata
gimbiya Lamrisa ta fita daga cikin kuncin bakin
ciki na tsawon shekaru goma sha daya.Tabbas
wannan yaro da aka kawo zai kawar mata da
kewar
rashin haihuwa domin nasan cewa zata reneshi
kamar yadda zata reni dan cikinta.Dangane da
bakin cikin da nakeyi kuwa shine wannan talaka
nawa da yan fashi suka kashe wato mahaifin
Shubairu ya kasance masoyina na kwarai,a
duniya
ban taba samun mutum MAI KAUNATA ba
kamarsa.Tabbas akwai sirri mai karfi a tsakanina
dashi amma kuma ban isa na jawo shi jikina ba
shi yasa bakusan alakar dake tsakanina dashi
ba.Jin ya mutu ne na zubar da hawayena domin
nasan cewa na rasa masoyi wanda bazan taba
samun kamarsa ba.A iya sanina da Lumzaru ban
taba sani cewa yana da aure ba bare ma nasan
cewa yana da 'da.Ko shakka banayi yana boye
wannan kyakkyawan da nasa ne domin inda wani
ya taba ganinsa da tuni labarinsa ya cika
gari.Bisa
dalilin faruwar wannan al'amari daya faru a yau
na
tsintar wannan yaro na bayar da hutun kwana
bakwai a kasata kowa ya zauna a gida ya
huta,sannan kuma na bayar da umarni a sallami
dukkan tsofaffun fursunoni a dukkan kurkukun
kasar nan wadanda sukayi shekaru uku da
tsarewa.Haka kuma na shirya walima ta kwana
bakwai kullum dare da rana anan fadata domin
taya farin ciki bisa samun wannan yaro kuma ina
gaiyatar kowa da kowa,talaka da mai kudi,bawa
da basarake ban bambance ba.Koda jin wannan
batu
sai fadar ta sake rudewa da shewa mutane suka
kama farin ciki.Kamar yadda sarki Kuzzaru yayi
alkawari haka al'amura suka kasance wato saida
aka shafe kwanaki bakwai ana shagalin walima
dare da rana a cikin birnin kisra a gidan
sarauta.Talakawa,attajirai,sarakai da sauran
jama'a
kuwa suka rinka cincirindo a cikin gidan sarki
saboda yawan jama'a idan mutum ya dubesu sai
yayi zaton cewa mutanen duniyar ne kaf suka
taru
amma duk da wannan yawa na jama'a saida
abinci
da abin sha ya wadace su kai almajirai ma saida
suka daina barar abinci a tsawon wadannan
kwanaki bakwai.Daga wannan rana gimbiya
Lamrisa ta cigaba da renon yaro Shubairu ta
kaunace shi ainun tamkar itace ta haifeshi,dare
da
rana tana tare dashi babu abinda ke raba su.Duk
wani gata na duniya babu irin wanda Lamrisa
bata nunawa Shubairu ba,kullum idan tayi masa
wanka
sai ta caba masa ado irin na yayan sarakai.Kai
saboda tsananin son da Lamrisa ke yiwa
Shubairu
saida tasa wani gwani masassaki ya sassaka
gunkinta dana Shubairu wanda yayi matukar
kama
dasu aka ajiye gumakan biyu a tsakiyar katon
falon dake bangaren turakarta.Babu abinda zai
dada
baiwa
★littattafañ hausa
mutum mamaki face yadda gaba dayan mutanen
gari ke girmama Yaro Shubairu ya zamana cewa
ana kiransa da suna YARIMA.Shi kansa sarki
Kuzzaru nan da nan ya shaku da Shubairu yaji
kamar dan cikinsa ne amma duk sa'adda ya tuno
da cewar Shubairu bazai taba gadonsa ba sai ya
cika da tsananin bakin ciki ya kulle kansa a cikin
turakarsa yayi kuka ya more.Kullum idan sarki
zai
tafi fada tare da Shubairu yake tafiya,kuma wabi
abin sha'awa shine shiga iri daya sukeyi kuma ko
yaushe Shubairu na zaune daf dashi bisa karagar
mulki.Shi kansa Shubairu ya tsinci kansa a cikin
sabuwar rayuwa ta daula har ya rinka jin kamar
bai
taba rasa iyayensa ba saboda sa'adda iyayen
nasa
ma ke raye bai taba samun irin wannan daula ba.
WATA RANA da hantsi fada ta cika makil da
jama'a Shubairu na zaune daf da sarki saiga wani
mutum mai siffar attajirai ya shigo cikin fadar.Da
zuwan mutumin saiya fadi gaban sarki ya kwashi
gaisuwa sannan ya dago kai ya dubi sarki yace
ya
shugabana ni sunana Ubairu ibini Lauras kuma
na fito ne daga birnin Mirsa.Na kasance bafatake
mai
tarin dukiya don haka duk sa'adda zan fito
fataucina nakan fito da rakuma dubu dari gami
da
dakaruna mutum dubu hamsin masu tsaron
lafiyata
da dukiyata.Yanzu da hanya ta biyo ni ta kofar
birninka saina yanke shawarar na shigo cikin
birninka na yada zango kuma na baje kolina a
ranar da kasuwarku ke ci.A halin yanzu masu
gadin kofar birninka sun hanani shigowa da
rakuma na da kuma dakaruna,ni kadai suka bari
na shigo shine nazo neman alfarma a wajenka
domin
ka bani izini na shigo da hajata da
dakaruna.Yanzu
haka daya daga cikin masu gadin kofar garin ne
ya
rako ni izuwa nan fadarka domin yaji da bakinka
idan ka amince.Lokacin da attajiri Ubairu yake ta
wannan bayani Shubairu ya kura masa idanu.Nan
take idanun Shubairu sukayi jawur kuma fuskarsa
ta sauya yanayi daga annuri izuwa fushi.Har
sarki
Kuzzaru ya budi baki zaiyi bayanin amincewarsa
akan Ubairu ya shigo da dakarunsa da dukiyarsa
sai Shubairu ya tari numfashinsa yace Ya Abbana
inason na gana dakai a sirrance.Koda jin wannan
batu sai mamaki ya kama kowa a cikin fadar
domin Shubairu bai taba tsoma bakinsa ba a
cikin
harkokin mulki sai yau.
da fatan xaku gafarcemu na dan rashin postin da
bamayi wannan ya damo Asaline saka makon
rasa wasu littattafan da mukayi da kuma
lalacewar computer mu.
★DAKAKKIYAR ZUCIYA★!!!

Littafi Na Daya (1)
Part B.
BAI TABA TSOMA BAKINSA BA A CIKIN
HARKOKIN
MULKI SAI A YAU.BA TARE DA GARDAMAR
KOMAI
BA SARKI YA MIKE TSAYE YA KAMA HANNUN
Shubairu suka koma can gefe daya inda babu
wanda zaiji abinda zasu tattauna sannan ya
dubeshi yace yakai dana me kake son zaka gaya
mini ne har da ka katse mini hanzari bisa
alfarmar
da wannan bakon attajiri yazo mini da ita?
Sa'adda
Shubairu yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar
zuciya cikin takaici yace yakai abbana ai wannan
attajiri wakili ne na babban makiyinka sarki
Farhama na birnin Kairufa.Ina tabbatar maka da
cewa hajar da yazo da ita bisa rakuma dari ba
komai bace face wadansu mugayen aljanu guda
dubu dari biyar wadanda idan har ka bari aka
shigo dasu cikin birninka sai sun hallaka gaba
dayan jama'armu.Sannan ayi maka juyin mulki
ayi
maka kisan gilla a kone dukkan wadannan
kyawawan gine ginenmu.Ya Abbana duk wannan
bayani danayi maka yanzu na ganshi ne akan
fuskar attajiri Ubairu a lokacin da yake gabatar
da
kansa.Ina so ka sani cewa a zahiri idan ka tura
aka duba wannan haja wacce attajiri Ubairu yazo
da ita babu abinda za'a gani face kayayyakin
karafa na dangin zinare da lu'u lu'u amma idan
mai karfin sihiri zai dubesu zai ga cewa wasu
muggun bakaken aljanu neLallai kasan matakin
da
zaka dauka akan wannan al'amari idan kuwa kayi
sakaci lallai karshen mulkinka yazo.Sa'adda yaro
Shubairu yazo nan a zancensa sai hankalin sarki
Kuzzaru ya dugunzuma ainun ya kurawa Shubairu
idanu cikin tsananin al'ajabi.Abu na farko shine
tabbas ya san cewa fiye da shekaru ashirin baya
sarki Farhama nata shirya masa mugun tanadi
don
ganin bayansa amma yana tsallakewa bisa
taimakon bokansa mai suna Zuraita Ibini
Laufur.Abin mamakin shine tunda aka tsinto yaro
Shubairu boka Zuraita bai sake zuwa fada
ba.Alhakin a da can duk bayan kwana uku sai
yazo
ya yiwa sarki bayani bisa abubuwan da yake
hangen zasu iya faruwa nan gaba a cikin
binciken
da yayi.To waishin menene ya hana Boka Zuraita
zuwa fadar a tsawon kwanaki arba'in da
bayyanar
Shubairu?Sarki Kuzzaru ya tambayi kansa a cikin
zuciya kuma ya kasa baiwa kansa amsa.Sarki
Kuzzaru ya sake tambayar kansa yace to wai
shin
shi wannan yaro Shubairu yaya akayi yasan
al'amarin Ubairu?Ni dai a sanina da mahaifin
wannan yaro bai kasance boka ba.A ina Shubairu
ya sami ilmin tsafi?Bayan sarki Kuzzaru ya gama
yiwa kansa wadannan tsauraran tambayoyi a
cikin
zuciyarsa saiya kawo gwauron numfashi ya ajiye
sannan ya dubi Shubairu cikin murmushi yace
yakai dana tabbas na yarda da duk wannan
jawabi
da kayi mini,dalili kuwa shine nasan mahaifinka
mutum ne mai gaskiya da amana kuma nayi
imani
cewa ka gaji halayensa don haka zanyi amfani da
wannan shawara daka bani lallai zan san matakin
dazan dauka a kai.Koda gama fadin haka sai
sarki
ya kama hannun Shubairu yaja shi suka koma
izuwa kan karagar mulki suka zauna.A wannan
lokaci gaba dayan fadar tayi tsit kowa ya
zubaido
kuma ya kasa kunne yaji abinda sarki zai fadawa
attajiri Ubairu tunda ba'a san shawarar da yayi da
yarima Shubairu ba.Bayan sarki Kuzzaru da
Shubairu sun zauna akan karagar mulki sai sarki
ya dubi attajiri Ubairu yace yakai wannan babban
bako ka koma can wajen gari wajen dukiyarka da
jama'arka ku kafa tantuna ku kwana acan lallai
kafin safiya zan yanke hukunci bisa
bukatarka.Koda jin wannan batu sai attajiri
Ubairu
yayi murmushi gami da godiya sannan ya mike
tsaye dan ya juya ya fice daga cikin fadar.Koda
ya
hada idanu da yaro Shubairu sai akaga ya fadi
kasa yana tari da kyar ya mike tsaye ya fice
daga
fadar ba tare daya yarda ya sake hada ido da
shubairu ba.Al'amarin dayai matukar baiwa kowa
mamaki kenan har shi kansa sarki
Kuzzarun.Bayan
tafiyar attajiri Ubairu sai sarki ya sallami
fadawansa
da sauran mutanen gari amma banda sarkin yaki
Huzaika bayan jama'a sun watse sai sarki ya dubi
Huzaika yace yakai dirkar birnin kisra kayi sani
cewa Shubairu yazo mini da shawara bisa
wannan
bakon attajiri akan kada na kuskura na bashi
izinin
shigowa cikin birnina tare da hajarsa da
dakarunsa
domin wakili ne na babban makiyinmu sarki
Farhama.Hakika nayi matukar mamaki bisa
wannan
al'amari wani abu daya sake daure min kai shine
tunda ka kawo Shubairu gareni boka Zuraita bai
sake kawo mini ziyara ba.Abinda nake so da kai
shine yanzu ka tafi izuwa gidan boka Zuraita
kace
dashi menene dalilin da yasa ya daina ziyarta ta
har tsawon kwanaki arba'in,sannan kuma ka gaya
masa cewa ina neman shawararsa bisa wannan
bakon attajiri dayazo mini.Koda jin wannan
umarni
sai shi ma sarkin yaki Huzaika ya cika da
mamaki
amma sai yayi shiru baice komai ba.kawai saiya
risina yace an gama ya shugabana.Nan yake
Huzaika ya juya ya fice daga cikin fadar ya tafi
izuwa gidan boka Zuraita wanda ke can kusa da
karshen gari.Sarki kuwa sai ya kama hannun
Shubairu yajashi suka shige izuwa cikin gidan
sarautar suka nufi bangaren turakar gimbiya
Lamrisa.
*Al'amarin Attajiri Ubairu kuwa tunda ya baro
fadar
sarki Kuzzaru ya kasance a cikin matukar tashin
hankali da matukar damuwa ya cigaba da tafiya
cikin sauri da waige waige kamar ace kyat ya
fita
da gudu.Kallo daya mutum zaiyi masa ya fahimci
cewa lallai babu alamar gaskiya a tare dashi.Da
isar Ubairu bayan gari inda yabar rakumansa da
dakarunsa saiya umarci dakarun nasa dasu kafa
tantuna.Cikin mamaki dakarun suka mike suka
kama bin umarnin domin su a zatonsu yana zuwa
zaice su kada rakumansu a shiga cikin birnin
kisra.Bayan an kafa tantunan sai Ubairu ya shiga
cikin nasa tantin ya zauna yayi tagumi yana
tunanin abinda zai fissheshi.Yana cikin wannan
hali
Wani Jibegegn aljani baki sidik ya bayyana a
gabansa.Girman Aljanin yakai na wani katon
tsauni
saboda tsananin munin aljanin kuwa idan mutum
ya dubeshi sai zuciyarsa ta tashi yaji kamar zaiyi
kumallo.Babu abinda zaifi firgita mutum a tare da
wannan aljani face kwala kwalan jajayen
idanunsa.Cikin fushi aljanin ya dakawa Ubairu
tsawa yace yakai wakilin sarki Farhama saboda
me
zaka shanya mu a rana tamkar mun kasance
bayinka?Shin ka manta ne cewa sarki Farhama
ya
turo mu ne domin mu baje wannan birni na Kisra
a cikin abinda bai wuce yini daya ba?Sa'adda
Ubairu yaji wannan batu sai ya dubi aljanin yace
haba Darkusa kaima kasan cewa in babu matsala
babu yadda za'ayi a sami wani jinkiri a cikin
wannan aiki.Tabbas akwai gagarumar matsala
domin ina ganin cewa asirinmu ya tonu,sarki
Kuzzaru bazai taba bari mu shiga cikin wannan
birni nasa ba har mu sami damar cika
aikinmu.Koda jin haka sai aljani Darkusa ya cika
da tsananin mamaki yace yaya akayi asirinmu ya
tonu alhalin karfin sihirinmu yafi nasa kuma yafi
na
bokansa?Dajin haka sai Ubairu yayi ajiyar zuciya
yace ai lokacin dana isa fadar sarki Kuzzaru sai
nayi arba da wani shu'umin yaro a tare dashi
wanda bzai fi shekaru shida ba a duniya.Muna
hada idanu dashi naji zazzabi ya shigeni kuma
naji
gaba dayan sirrikan tsafina sun daina aiki.Nikam
bana raba daya biyu akwai TSATSUBA a tare da
wannan yaro.Tabbas idan har muna son mu cika
umarnin sarki Farhama dole ne sai mun fara
kawar
da wannan yaro saboda sun tattauna kuma babu
wanda yaji abinda suka zanta a tsakaninsu.Yayin
da aljani Darkusa yaji haka saiya tuntsire da
dariyar mugunta lokaci guda kuma ya turbune
fuska yace.Haba yakai Ubairu yanzu kai kankanin
yaro ne zai firgitaka haka amma dai ka bani
kunya..To tsaya kaji ni kam bazan yarda ni da
jama'ata mu shiga cikin fushin sarki Farhama ba
saboda haka daga nan zuwa wayewar gari lallai
kasan hanyar da zakabi ka shigar damu cikin
wannan birni ko ta halin kaka koda karfin tsiya
kuwa.Idan kuwa kaki ni da kaina zan kashe ka in
yaso na koma na gayawa sarki Farhama cewa ka
kasa gabatar da aikinsa na kashe ka.Lokacin da
Aljani Darkusa yazo nan a zancensa sai hankalin
Ubairu ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe
domin ya fuskanci cewa yana cikin GABA TSINI
BAYA SIYAKI domin ya tabbatar da cewa idan
har
ya kasa shigar da rakumansa cikin birnin kisra
lallai koda ya koma birnin Kairufa sunansa GAWA
domin akan wannan sharadi sarki Farhama ya
bashi jagorancin wannan tafiya.Sarki Farhama ya
kasance takadirin matsafi kuma GWARZON
MAYAKI
mai tsananin KARFIN DAMTSE da jarumtaka
amma
kuma ya shakkar sarki Kuzzaru a bangaren
sadaukantaka domin sau bakwai suna
kwamarzuwa a FILIN YAKI sunayin KARE JINI
BIRI
JINI.Wato duk sa'adda sukayi yakin kowannensu
yana matukar shan wahala tamkar zasuyi
RAGAS!
Ba komai ne ya haddasa hakan ba face karfin
damtsensu da iya yakinsu yazo daya inda ka
sami
bambanci shine Sarki Farhama yafi sarki Kuzzaru
karfin sihiri.To amma sai boka Zuraita ya rinka
baiwa sarki Kuzzaru kariya bisa dukkan sharrin
sarki Farhama na tsafi.Gabar dake tsakanin sarki
Farhama da sarki Kuzzaru ta samo asali ne tun
daga iyayensu akan wani abu daya faru kimanin
shekaru talatin baya.Al'amarin ya faru ne a wata
safiya sa'adda wadansu fatake daga birnin
Kairufa
suka shigo cin kasuwa a cikin birnin Kisra ashe
ba
fatake bane barayi ne wadanda suka kware a iya
sata.Musamman sarki Farhama ya dauko hayar
barayin daga can wata nahiya daban ya biya su
dukiy mai yawan gaske akan su sato masa wata
kanwar sarkin birnin Misra wacce ta kasance
TAURARUWAR TAURARI a cikin 'YANMATA na
wannan zamani ana kiranta da suna
SIYAMAT.Saboda tsananin kyawun Siyamat saida
labarinta ya bazu a ko ina a duniya a wannan
lokaci ya zamana cewa yayan sarakai,attajirai da
bokaye suka rinka zuwa neman aurenta daga
kowanne bangare na duniya.Mahaifin sarki
Farhama kuwa sau tara yana aiko da dumbin
dukiya wacce ta shallake hankali a matsayin
toshi
domin a bashi auren gimbiya Siyamat ga dansa
Yarima Farhama.Duk sa'adda aka kawo dukiyar
sai
sarkin Kisra ya karba ya adanata yace a koma a
gayawa mahaifin sarki Farhama cewa ya cigaba
da
sauraronsa.Lokacin da Masoyan Gimbiya Siyamat
sukayi yawa kimanin mutum dari bakwai kuma
dukkaninsu masu arziki ne sai hankalin mahaifin
sarki Kuzzaru ya DUGUNZUMA ainun ya rasa
abinda ke masa dadi domin ya rasa wanda zai
baiwa auren Siyamat a cikinsu.Bisa wannan dalili
ne ya kira mahaifin Boka Zuraita suka kebe
domin
yin shawara.Mahaifin Zuraita yayi shiru yana
tunani
daga bisani ya dago kai ya dubi sarkin Kisra yace
ya shugabana kayi sani cewa a halin yanzu a
cikin
masoya yar uwarka gimbiya Siyamat babu mai
matsayi da daraja kamar Yarima Farhama dan
sarkin birnin Kairufa to amma fa ka sani cewa
idan
Yarima Farhama ya auri gimbiya Siyamat har
abada ba zaka sake ganin Siyamat ba har izuwa
lokacin da ajalinka zai cika.Abinda na gani kenan
a
cikin bincikena na tsafi.Ka sani cewa idan ka fito
fili karara kace ba zaka aurar da ita ga Yarima
Farhama ba to fa sai sarkin Kairufa ya nemi yaki
da kai.Domin dansa Farhama ya haukace a cikin
son Gimbiya Siyamat idan har bai aureta ba zai
iya
kashe kansa ko kuma hankalinsa ya tabu.A
duniya
babu abinda sarkin Kairufa ke so sama da dansa
Yarima Farhama don haka zai iya sallama komai
nasa domin biyan bukatar dansa.Shawarar da zan
baka itace kasa a shirya gasa mai matukar
wahalar
gaske ta neman auren gimbiya Siyamat wacce
babu wanda zai iya samun nasara kaga shike
nan
dole ne Yarima Farhama ya hakura da auren
Siyamat in yaso kai kuma sai ka aurar da ita ga
dan sarkin da hankalin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment