Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A
FADAR BOKA JABARUL SIHIR.?
Marubucin littafin yace mu hadu a KOGON ANNOBA na
biyu don jin cigaban wannan kasaitaccen labari.
Zan Cigaba insha Allah.
Admin Dr. Goni S Abubakar.

KOGON ANNOBA
Littafi na biyu 2
Na Mansur Usman Sufi
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
Kogon Annoba Part A
Littafi Na Biyu 2
Marubucin Littafin
Mansur Usman sufi
Kamar yanda boka Zulwal ya fada haka al amarin ya
kasance wato tun da dukun dukun safiya sarki Siyamul
ansar da su yarima Yarima Nazmar sukayi shiri bayan sun
rabu da mahaifiyarsu suna masu zubar da hawayen
rabuwa da juna suka dauki hanyar tafiya tare da dakaru
masu yi musu rakiya mutum dubu biyu tafiyar sa'a uku
sukayi suka iso wani daji mai tattareda kayan ni'ima nau'i
nau'i daban daban koramai na gudana acikinsa atsakiyar
dajin akwai wani dan madaidaicin gida shi dai wannan
gida da zallan duwatsun wuta masu kwarin gaske da
isowarsu bakin kofar gidan sai sarki Siyamul ansar ya
sauka daga kan dokinsa yaje ya kwankwasa kofar gidan
wanda ta kasance mai tsananin tsawo da kaurin gaske
saida ya kwankwasa sau uku ba tare da yaji motsin
alamun za a bude taba koda ganin haka sai su yarima da
boka Zulwal suka sauko daga kan dawakansu suka tako
har izuwa kofar gidan suna masu yin cirko cirko domin
suga an bude kofar tsawon dakika dari biyu shiru ba aji
sautin bude kofar ba al amarin da yayi matukar
dugunzuma hankalin sarki Siyamul ansar ya dubi boka
Zulwal yace ya sarkin bokaye shin yanzu me nene abinyi?
har boka Zulwal ya budi baki da nufin yace wani abu sai
kawai aka hango wani kyakkyawan saurayi mai cikar
kamala da annurin fuska ya tunkaro kofar gidan kallo
daya zakayiwa saurayin ka fahimci ya kasance gwarzon
mayaki mai karfi na Allah ya isa saurayin yana sanye da
kayan fata riga da wando takalmin dake kafarsa anyi
shine da patar damisa akafadarsa yana dauke da wata
qatuwar zakanya.
Koda isowarsa inda su sarki Siyamul ansar ke tsaye sai ya
bisu da kallo cike da mamaki ba tare da yace da dayansu
uffan ba yasa hannu daya ya tura gofar gidan ta bude ya
kunna kai izuwa ciki yayin da sarki Siyamul ansar da
tawagarsa sukayi arba da qatuwar zakanyar dake dauke
akafadar saurayin kuma sukaga yadda ya bude kofar
gidan da hannu daya wanda sai karti majiya karfi mutum
ashirin sun taru sannan zasu iya bude kofar sai suka cika
da tsananin mamaki domin basu taba gani ko jin jarumin
da yayi wannan jarumtaka ba suna nan atsaye a kofar
gidan sai sukaga saurayin ya fito daga cikin gidan ya tako
da kafafunsa har izuwa inda suke ya dubesu cikin
nutsuwa yace aminci ya tabbata agareku yaku wadannan
baki shin menene ke tafe daku izuwa gareni koda jin
wannan tambaya sai sarki Siyamul ansar yayi gyaran
murya yace yakai jarumi Huzaifal bin masnur kayi sani
cewa ba komai ne ke tafe dani izuwa gareka ba face wata
muhimmiyar bukata bukatar kuwa itace inaso kayi mana
jagora izuwa gidan boka Jabarul sihir domin nemowa
wadannan 'ya'yan nawa maganin da zai warkadda su
larurar dake damunsu ta rashin jin magana kuma har su
mayar da abinda suka daukowa wadansu tsuntsaye
wadansu tsutsaye inason ka fadi dukkan abinda kake
bukata da ya danganci dukiya da mulki ni kuwa zan baka
shi.
Koda jin wannan jawabi daga bakin sarki Siyamul ansar
sai.jarumi huzaifal yayi shiru yana mai sunkui da kansa
kas ya shiga dogon nazari daga can sai ya dago kai ya
dubi su Yarima Nazmar gimbiya Hulaisa sannan ya dubi
sarki Siyamul ansar yace yakai wannan sarki mai daraja
kayi sani cewa fiye da shekaru goma ubangijina ya
baiyana mini cewa zakazo gareni da wata bukata na
amince zanyi maka wannan aiki amma sai dai bisa
sharadi guda daya jal wanda sai ka amince dashi zanyi
wannan gagarumar tafiya da jin haka sai sarki Siyamul
ansar yace fadi sharadinka ya jarumin kwarai Huzaifal
yayi gyaran murya a karo na biyu sannan yace sharadina
shine bayan na samu nasarar debo ruwan ma'ul diya'u
wanda shine zai warkar da su Yarima zaka yarda kayi
imani da ubangiji kai da jama'arka baki daya idan ka
daukar mini wannan alkawari shikenan ka biyani
dukkanin aikina ba tare da ka bani dinare da ko wani
yanki na masarautarka ba koda jin wannan batu sai sarki
Siyamul ansar yayi shiru duk tattaunawar da akeyi
tsakanin Jarumi Huzaifal da sarki Siyamul ansar boka
Zulwal da su Yarima Nazmar suna sauraro koda Boka
Zulwal yaji sharadin da jarumi Huzaifal ya gindayawo
sarki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun domin ya
tabbatar idan sarki Siyamul ansar yayi imani cewa zai
karbi addinin musulunci duk shirinsa zai tarwatse na son
mallakar birnin SARIRUL AIWAN da ya dade yana muradi
yana cikin wannan hali ne wani tunani ya fado masa
tunanin kuwa shine tunda sarki Siyamul ansar umarninsa
yakebi bana jarumi Huzaifal ba lallai akwai tabbacin
burinsa zai iya cika sa'adda yazo nan a tunaninsa sai ya
cika da farin ciki a ransa sarki Siyamul ansar ya kada
shirun da ya wanzu a tsakaninsu ta hanyar bude baki
yace yakai jarumi Huzaifal hakika na amince da wannan
sharadin naka matukar 'ya'yana zasu daidaita yanda nake
bukata amma kuma wani hanzari ba guduba menene
batu a gameda cewa su yarima sune zasu zamo ajalina da
jin wannan tambaya sai murmushi ya subucewa jarumi
Hullzaifal har fararan hakoransa suka baiyana farare qal
ya dubi sarki Siyamul ansar cikin annurin fuska yace kada
ka damu ya shugabana kasani cewa matukar kana tare
dani kuma kayi imani da ubangijin musulunci mahaliccin
sammai da kassai da abin dake cikinsu babu yanda za ayi
'ya'yanka su zamo ajalinka yanzu dai abinda za ayi shine
ku biyoni izuwa cikin gidana kudan shakata kafin abinda
ya kamata ayi tunda na lura cewa kun gaji ainun kuma a
tsarin addininmu ubangiji ya umarce mu da mu
girmama ma'abota mulki matukar basu hana mu bauta
masa ba.
Koda gama fadin haka sai jarumi Huzaifal ya juya ya shige
gaba yana mai.kunna kai izuwa cikin gidan yana mai
yafito su sarki Siyamul ansar na hannunsa ba tare da bata
lokaci ba sarki Siyamul ansar Yarima Nazmar gimbiya
Hulaisa boka Zulwal ne a karshe suka suka biyo bayan
Huzaifal yayi musu jagora har izuwa cikin gidan da
shigarsu izuwa cikin gidan sai suka cika da tsananin
mamaki abinda ya basu mamaki shine yadda aka tsara
gidan bisa tsari da kayatarwa gidan yana dauke da
manyan dakuna guda uku masu girma da fadi suna da
kofa ɗai ɗai da tagogi guda biyu a wani daki ne dake
kallon yamma cikin gidan jarumi Huzaifal ya sauki su
sarki Siyamul ansar aciki dakin cike yake da kayatattun
kujeru kuma an shimfide kasansa da kilisai masu taushi
wani daddadan kamshi ya mamaye turakar bayan jarumi
Huzaifal ya sauke su acikin turakar sai ya fice daga cikin
dakin jim kadan sai gashi ya dawo dauke da wani dogon
paranti cike da nau'in kayan marmari da gasasshen
naman zakanya gamida tatacciyar madarar shanu ya
ajiye agaban su sarki Siyamul ansar a bisa wani dan
madaidaicin tebur na katako a tsakiyar turakar yana ajiye
abincin ya dubesu yace ai sai ku dan kimtsa cikinku ko
yana gama fadin hakan ya fice daga dakin sarki Siyamul
ansar da boka Zulwal suka bishi da kallo cike da matukar
mamaki tayaya akayi har ya sarrafa naman zakanyar da
ya farauto acikin kankanin lokaci haka kuma a inama ya
samu wannan tatacciyaro madarar shanun al halin babu
wata dabba dake rayuwa acikin dajin saida suka kammala
kimtsa cikinsu suka huta sannan aka dunguma gaba daya
suka fice daga gidan har jarumi Huzaifal suna ficewa ya
mayarda kofar gidan ya rufe ta ruf kawai sai suka ga ya
kusanci wani bangare adajin mai tattare da sarkakiya sai
gashi ya janyo wani ingarman doki fari sol mai kyawun
launi bayan ya hau dokin ne kowa ya hau abin hawarsa
sai aka nausa cikin daji aka fara tafiya dakaru masu rakiya
na biye dasu ana fara wannan tafiya ne jarumi Huzaifal
yaki yarda ya jera da kowa face Yarima Nazmar da
gimbiya Hulaisa yana mai satar kallonsu fuskarsa cikeda
annuri ana cikin hakan ne Yarima Nazmar ya dube shi
yace yakai wannan jarumi a dazu da kuna magana da
abbana naji kace akwai wani ubangiji da kake bautawa
wanda ya halicci sama da kasa bayan abin bautarmu.
Koda jin wannan tambaya sai Huzaifal yayi murmushi ya
dubi Yarima Nazmar yace tabbas akwai ubangijin da ya
halicci duniya da abinda yake cikinta kuma yake aiwatar
da duk abinda yaso da ace zaku gwada neman taimakon
ubangijin nawa da kun kasance jarumai kamar yanda har
kullum kuke muradi sa'adda Yarima Nazmar yaji amsar
wannan tambaya sai ya cika da mamaki yace wacce
hanya zanbi in samu taimakon ubangijinka Huzaifal yace
ai abune mai sauki kawai duk sa'adda wani abu ta taso
maka kace kana neman taimakon ubangijin gaskiya
ubangijin da yayi rana da wata yayi mutum da aljan
dabba da tsuntsaye ruwa da iska ubangijin da babu wani
ubangiji bayan shi a ranka ba tareda ka furta wani yaji ba
lallai kai da yar uwarka inason ku boye mini wannan sirri
dake tsakanin mu Yarima Nazmar da yar uwarsa sukace
ai kuwa babu wanda zaisan da wannan sirri har sai
gaskiyar abinda kake gaya mana ya baiyana daga wannan
kuma Huzaifal ya shiga basu daddadan labarai masu
sanyaya nishadi da annashuwa haka dai aka cigaba da
wannan tafiya babu sassauci ana cikin tafiyar ne kwatsam
ba zato babu tsammani sai aka hango jibga jibgan
mutane masu tsawo da kauri qirar mutanen farko
yawansu yakai dubu biyar suna da miyagun makamai
masu baraza ga rayuwar mutane da aljan nan fa gaba
daya dakarun sarki Siyamul ansar suka firgice sukaji
tamkar su cika wandunansu da iska amma sai sukaga
mutanen sunyi musu kawanya suna masu fitowa daga
kusurwar dajin.
Lokacin da mutanen suka kammala yi musu kawanya sai
aka fara kallon kallo daga can sai akaga mutanen sun
ɗane sun sake bayar da wata yar siririyar hanya a
tsakiyarsu da mutum zai iya wucewa sai ga wani garjejen
qato ma'abocin kwarjini da ban tsoro ya ratso hanyar ya
fito izuwa gaban mutanen ya dubi su sarki Siyamul ansar
a wulakance sannan ya bushe da mahaukaciyar dariya
mai kama da haniniyar doki sannan daga bisani ya
turbune fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya
bude wawakeken bakinsa mai dauke da wadansu
wargatsattsun hakora cikinsa marasa kyan gani cikin
kakkausar murya yace yaku wadannan kwari maza ku
sallama kanku izuwa gareni kafin in zare muku ruhinku
daga gangar jikinku kafin garjejen qaton ya gama rufe
bakinsa jarumi Huzaifal ya tari numfashinsa yana mai
maida masa da cewa shin wanene kai kuma menene
nufin ka agaremu garjejen qaton ya bushe da dariya a
karo na biyu sannan ya kurawo Huzaifal idanu masu
kama da garwashin wuta yace eh lallai da kyau yan
samari shin har kanason kasan wanene ni to inaso kai da
abokan tafiyarka kusani cewa nine sadauki RAUZAM
shugaban yan ta'addar wannan nahiyar baki daya amma
fa na yaba da jarumatarka matuka ganin yanda ka iya yin
magana baki da baki dani amma lallai bazan bar dayanku
a raye ba jarumi Huzaifal ya katse shi da cewa amma idan
har ka cika namijin duniya muyi fada da juna kuma kada
dayanmu ya rike makami a gwada yar qashi idan nayi
nasara akanka na cinye ka da yaki idan kaine kayi nasara
ka kashe ni sai ka kashe abokan tafiyata. Koda jin abinda
Huzaifal yace sadauki Rauzam ya takarkare ya kwarara
uban ehu da ya firgita gaba daya jama'ar dake wajen
sannan yace da kyau jarumin kwarai haka akeson namiji
da zuciya irin ta manya yana gama fadin hakan sai kawai
ya daga annayensa sama ya falfala da gudu izuwa inda
Huzaifal ke tsaye duk sa'adda ya ajiye kafarsa daya sai dai
kaji kasa na amsa kuwwa tamkar zata rufta.............
Zan Cigaba insha Allah
Admin Dr. Goni S Abubakar
Kogon Annoba Part B
Littafi Na Biyu 2
Marubucin Littafin
Mansur Usman sufi
Yana gama fadin haka kawai sai ya daga hannayensa
sama ya falfala da gudu izuwa inda Huzaifal ke tsaye duk
Sa'adda ya ajiye kafarsa daya sai sai dai kaji kasa ta amsa
tamkar zata rufta koda ganin haka sai Huzaifal ya sauko
daga kan dokinsa yana mai gyara tsayiwarsa gamida
dunkule hannayensa biyu da isowar sadauki Rauzam
yakai masa wani wawan naushi a fuska ya sunkuya
hannun Rauzam ya naushi iska sannan duka kacame da
azababben yaki mai matukar ban al'ajabi da ban mamaki
ana fara wannan gumurzu nefa Huzaifal ya fahimci cewa
Rauzum ya fishi tsagwaron karfin damtse domin idan ya
naushe shi a fuska ko a jiki inda ya nausa din sai jini ya
taru Huzaifal ya daka tsalle tamkar an harbo shi daga
cikin baka ya daki kirjin Rauzum da kafafunsa biyu
saboda karfin dukan sai da Rauzum yayi sama tamkar an
janye shi daga qugiya yayi katantanwa a sama sau uku
cikin gwaninta jarumi Huzaifal ya daka tsalle sama yayiwa
Rauzum luguden naushi sau goma sannan suka sauko
kasa a tare yana mai dora kafarsa a wuyan Rauzum
alokacin da jini ke juba a hannayensa a hancinsa da
bakinsa kuma numfashinsa ya fara sargewa Huzaifal ya
dube shi yace yakai wannan dan ta'adda kayi sani cewa
matukar zaka bayarda gaskiya ga ubangijina kuma ka
daina wannan haramtacciyar sana'a taka zan kyaleka ka
cigaba da rayuwa koda jin haka sai Rauzum yayi
murmushin karfin hali ya furzadda gudan jini a bakinsa
cikin kakkausar murya yace ai da inyi mubaya a agareka
gwara ka kashe ni domin za a shaida cewa ni jarumi ne
kafin Rauzum ya gama rufe bakinsa Huzaifal ya zare
takobinsa ya datse masa wuya.
Koda sauran yaransa sukaga abinda ya faru ga
shugabansu sai sukayi kururuwa suka afkawo su jarumi
Huzaifal aka kacame da azababben yaki sai da aka shafe
tsawon sa'a biyu ana wannan yaki sannan Huzaifal suka
samu nasarar hallaka gaba daya yaran Rauzum a inda
kowanne daga cikinsu Rauzum a kashe dakarun rakiya
mutum saba'in dayake duhun dare ya fara kawo kai sai
kowa ya sanyawo kansa magani kuma aka kafa tantuna
sannan akayi kalaci saida aka shafe tsawon kwanaki biyu
a wannan daji a iya wannan kwanaki jarumi Huzaifal ya
koyawo su yarima yadda ake yaki kuma bisa mamaki sai
gashi suna rike duk abinda aka koya musu al'amarin da
yayi matukar bawo sarki Siyamul ansar mamaki kenan
domin sau tari yana koya musu yaki amma basa rikewa
da hantsi aka sake yin shiri aka cigaba da tafiya saida suka
shafe kwanaki hudu ana keta miyagun dazuzzuka amma
bisa taimakon ubangiji basu sake haduwa da wani abin
cutarwa ba sau tari idan miyagun dabbobi suka hango su
sai kaga sun tarwatse sun bazama izuwa cikin daji
al'amarin da yayi matukar bawa sarki Siyamul ansar da
boka Zulwal mamaki kenan abinda basu sani ba shine
kawai tsananin addu o in da jarumi Huzaifal ke karantawa
ne suka tsare su daga sharrin dabbobin a iya tsawon
wannan kwanaki babu abinda ke tsaida su face idan
lokacin bacci yayi ko lokacin gabatar da sallan jarumi
Huzaifal a ranar kwana na biyar ne da yamma sakaliya
suka hango gidan boka Jabarul sihir akan tsakiyar wani
qaton dutse da ba a ganin karshensa.
Lokacin da ya zamana saura taku ashirin atsakaninsu sai
kowannensu yaja linzamin dokinsa ya tsaya suka sauko
sannan suka raka da kafafunsu suka durfafi gidan suna
masu zare makamansu da isarsu izuwa bakin kofar gidan
suka tarar kofar ta kasance doguwa mai tsawo da fadi
kuma anyi tane da zallar mulmulallen karfe Huzaifal ya
matsa kusa da kofar ya karanta ayatul kursiyyu da
tsarkakakken sunaye yana mai tofawa ajikin kofar sai
gashi ya tura kofar da hannu daya tamkar ya yaye labule
kawai sai ya kunna kai izuwa cikin gidan sarki Siyamul
ansar boka Zulwal yarima Nazmar gimbiya Hulaisa
dakarun rakiya ne a karshe suka bi bayansu da sauri da
shigarsu suka tarar da wata hangamemiyar fada ta gaban
kwatance gaba daya fadar gidan anyi shine da zallar farin
gilashi idan mutum ya kalli ko ina a fadar sai yaga hoton
surar jikin gilashin aqalla girman fadar yakai gari guda kai
tsayawa misalta tsaruwa da kawaitar fadar yakan iya
zamowa kauyanci sai dai abinda ido ya gani wani abin ma
idan mutum ya gani bai taba gani ko jin sunansa ba
abangaren yamma afadar bisa wata matattakala mai
hawa shida aka ajiye wata qasaitacciyar karagar mulki ta
gaban kwatance boka Jabarul sihir ne zaune bisa karagar
fuskarsa cike da annuri tamkar wanda aka bawo mulkin
duniya boka Jabarul sihir ya kasance garjejen qato mai
tsawo da kauri tamkar toron giwa duk da kasancewar
shekarunsa sun dan ja kallo daya zakayi masa ka fahimci
cewa ya kasance gwarzon mayaki mai tarwatsa maza
afilin daga a wannan lokaci boka Jabarul sihir na tsaye ne
cikin doguwar alkyabba da akayi mata cin baki da zaren
lu'ulu'u akansa yana sanye da kambun mulki da akayi shi
da zallar zinare yana walwali da daukar idanun mai
kallonsa duk inda mutum ya kalla ajikinsa guraye ne da
layun tsafi zaune bisa wadansu qayatattun kujeru afadar
yan majalisansa ne na jinsin mutum da aljan kuma gaba
daya fadar kewaye take da wadansu irin zaratan dakaru
masu matukar muni da ban tsoro suna dauke da makami
masu barazana da rayuwar bil adama lokacin da boka
Jabarul sihir yayi arba da su sarki Siyamul ansar sai ya
mike tsaye zumbur daga kan karagarsa ya tako
matattakalar fadar ya sauko kasa yana mai takowa da
kafafunsa yana kusantar inda suke fuskar cike da annuri
tamkar zai sadu da yan uwansa na jini.
Koda ganin hakan sai su jarumi Huzaifal suka dafe
takubbansu lokacin da ya zamana saura taku goma
tsakaninsu sai boka Jabarul sihir yaja ya tsaya ya dubi su
jarumi Huzaifal ya bushe da dariyar farin ciki sannan ya
budi baki cikin kakkausar murya yace lale marhabun da
manyan baki masu daraja na dade ina jiran zuwa wannan
rana mai cike da farin ciki agareni yanzu sai ku miko min
kwan sihirin da su yarima suka dauke mini akogon
Annoba koda jin wannan batu sai sarki Siyamul ansar ya
daka masa tsawa yace kai tsohon la'ananne kai sani cewa
baka isa mu damka maka kwan sihiri ba face ka amince
zaka debo mana ruwan koramarka wanda dashi ne zan
warkar da 'ya'yana koda gama fadin haka sai sarki
Siyamul ansar ya zura hannunsa a aljihu sai gashi ya fito
da wani kwai mai girma tamkar gwanda yayin da boka
Jabarul sihir yayi arba da kwan sihiri sai ya takarkare ya
kwarara uban ihu paruwar hakan keda wuya sai gaba
daya duhun ya yaye sai ga boka Jabarul sihir cikin
gagarumar shigar yaki a hannunsa yana rike da wata
zabgegiyar adda mai tsawo da tsinin tsiya koda ganin
hakan sai sarki Siyamul ansar ya zare takobinsa boka
Zulwal yayi koyi dashi suka ruga izuwa kan dakarun fadar
jarumi Huzaifal kuwa ya zare takobinsa ya ruga kan boka
Jabarul sihir aka kacame da azababben yaki ana cikin
hakan ne sai su yarima Nazmar sukaga wadannan
miyagun tsuntsaye na ratsowa ta saman fadar tamkar
yadda danshi ke ratsa kasa suna dura a gabansu daya
bayan daya koda ganin hakan sai yarima Nazmar da
gimbiya Hulaisa suka falfala da azababben gudu izuwa
kan tsuntsayen suna masu rayawa azuciyoyinsu cewa
muna neman taimakon ubangijin musulunci ba tare da
sun riki wani makami ba suka afkawa tsuntsayen da yaki
su kuwa dakarun rakiya sai suka zare makamansu suka
tari wadansu dakaru afadar dake bangaren yamma aka
yamutse da fada abu kamar wasa sai gashi jarumi
Huzaifal da boka Jabarul sihir sun shafe tsawon sa'a biyar
suna yaki ta hanyar kaiwa juna miyagun hare hare.
Lokacin da boka Jabarul sihir ya fahimci cewa ya kasa
samun nasara akan Huzaifal da karfin damtse sai ya fara
amfani da karfin sihirin tsafi har ya zamana yana yin
amfani da dukkanin sirrikan tsafinsa tabbas boka Jabarul
sihir ya hadu da gamonsa dakyar da siɗin goshi ya samu
nasarar zabgawo Huzaifal daushi aciki ya bazadda shi kas
koda Huzaifal ya fahimci halinda yake ciki sai ya kira
sunan ubangiji karfi yana mai neman taimakonsa take ya
samu wani gagarumin karfi kawai sai ya mike tsaye
zumbur yayi tsalle sama tamkar an harbashi daga cikin
baka ya dira akan boka Jabarul sihir yana mai rarraba
kafadunsa cikin zafin nama ya sanya hannayensa biyu ya
murde masa wuya sannan ya dako tsalle ya dira bisa
kafafunsa cikin gwaninta adaidai wannan lokaci ne gawar
boka Jabarul sihir ta fadi kasa racaca jini ya kwaranya
nan take dakarun gaba daya da suke yaki da su sarki
Siyamul ansar suka qame suka zama gumaka kuma
komai na fadar ya sandare ya zamana saura tsuntsaye
dasu yarima suke cikin yaki nan fa jarumi Huzaifal boka
Zulwal da sarki Siyamul ansar suka zuba idanu suna
kallon fafatawar da akeyi babu abinda yafi basu mamaki
sama da yadda su yarima Nazmar ke ragargazar
tsuntsayen babu sassautawa a inda za kaga sun kirbawa
tsuntsu naushi sun karya kafa ko fukafuki nan fa ya
zamana ihu da kururwar tsuntsaye ya mamaye fadar jini
kuwa ya dinga kwaranya yana malala tamkar an balla
teku su kansu su yarima sunyi matukar mamakin irin
wannan gagarumin karfi da suka samu sai da dakika dari
da sittin ta shude sannan yarima Nazmar da gimbiya
Hulaisa suka samu nasarar kashe gaba daya tsuntsayen
amma gaba daya jikinsu ya rine da jini tamkar an
tsomasu cikin tekun jini cikin matukar farin ciki sarki
Siyamul ansar ya ruga inda 'ya'yansa suke ya rungumesu
a kirjinsa cikin tsananin farin ciki daga can su yarima
suka janye jikinsu daga na mahaifinsu suka dube shi
sukace ya abbanmu kayi sani cewa dukkanin wannan
nasara da kaga mun samu akan wadannan tsuntsaye
mun samu taimako ne daga ubangijin jarumi Huzaifal
saboda haka munyi imani da ubangijin musulunci koda
jin haka sai sarki Siyamul ansar boka Zulwal da dakarun
tsakiya sukace muma munyi imani da ubangiji mahalicci
cikin matukar farin ciki jarumi Huzaifal ya karanta musu
kalmar shahada suka maimaita.
Faruwar hakan keda wuya sai sukaji gaba daya fadar ta
kama girgiza koda ganin hakan sai jarumi Huzaifal ya
falfala da gudu izuwa kofar fita dake fadar yana mai yiwa
su sarki nuni da su biyo bayansa ai kuwa suna kammala
fita daga fadar sai gaba daya ginin fadar ya dinga rushewa
kuma gaba daya ya nutse cikin karkashin kasa Huzaifal ya
dubi su duka su hudun yace bamuda bukatar nemo
ruwan ma"ul diya'u dan warkar da su yarima imani kadai
da sukayi da ubangijin musulunci ya warkar dasu daga
lalurar dake damunsu ta rashin jin magana koda gama
fadin haka sai jarumi Huzaifal yaje ya kama dokinsa ya
hau sannan kowa ya hau nasa aka cigaba da tafiya
sa'adda lokacin sallah yayi sai jarumi Huzaifal yayi
umarni aka tsaya da tafiya bayan an samu ruwa a wata
korama anyi alwala su yarima sun sauya tufafin dake
jikinsu sai Huzaifal ya shige gaba yayi musu limanci
sa'adda su sarki sukaga yana yin ibadar bisa tsari mai ban
sha'awa sai sukaji kaunar addini ta kara shiga ransu
bayan an kammalane aka dauki hanya yayin da aka isa
birnin sarirul aiwan sai aka kafa tutar musulunci jarumi
Huzaifal ya auri wata baiwar sarki Siyamul ansar mai suna
ZARIMAT BINTU FANNAS daga wannan rana jama'ar
birnin suka kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali
ya zamana babu manyan jarumai kamar su yarima
Nazmar da sanin ilimin addinin musulunci.
ALHAMDULILLAH
THE END
Anan wannan littafi yazo karshe wato mai suna KOGON
ANNOBA da fatan littafin kunji dadin shi kuma ya qayatar
daku daga ni naku mai debe muku kewa gOnI S
AbUbAkAr ke cewa sai mun hadu a wani sabon littafin
KOGON ANNOBA
Littafi na Daya 1
Na Mansur Usman Sufi
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment