Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

a tsatsaye har sai da ya kaita da kwanciya kullum cikin tunanin Fateema take mik'ewa tayi da sauri da taji Muryar Fateema kamar a mafarki

Abakin k'ofa suka had'u da Fateema Fateema kuwa ta rungumeta ta fashe da kuka inna wuro itama kukan ta Fashe dashi ta d'ago Fateema tana k'are mata kallo Gani tayi Fateema tayi wani mugun b'aki ta rame kasusuwa a k'irjinta kamar sarka wuyanta ya wani k'ara tsayi Inna wuro cewa tayi

"Subhanallahi Fateema cuta kika yi? Mai ya sameki haka?

Fateema kuka ta k'ara fashewa dashi tace "inna babu abinda banyi ba babu abinda bai sameni ba Inna naga rayuwa nashiga taskun rayuwa wlh nasha wuya a gidan Lado"

Inna hawayen daya zubo mata ta share tana "naga alama Fateema ko baki fad'a ba kinsha wuya satinku d'aya da tafiya wani ya samu Baffa ya gaya mishi Wanda kika aura d'an karya ne Dan yaudara ina nan ina Murna Kin tafi saudiya wlh sai fad'awa mutane nake kuna can muma kwanan zamu biku Ashe ba saudiya kuka tafi ba wai K'auye ya kaiki"

Fateema ajiyar zuciya tayi ta samu guri ta zauna ta cire hijabin jikinta ta fara bawa Inna wuro labarin irin wuyan da ta sha a gidan Lado babu abinda ta b'oye mata har yanda yake gurzata kamar dabba sai da ta fad'a mata ta k'arasa maganar da kuka tana

"Inna nayi danasanin rabuwa da Bashir Inna baka sanin darajar Abu sai ya sub'uce ma Ashe Bashir mai kud'ine tunda nake a gidansa ban tab'a cin wake da gero ba ban tab'a cin rogo da kulli ba wlh Inna bana yiwa su Aliyu wanki Bashir ne yake musu amma sai gashi nayi wankin y'ay'an Lado Inna har dukana Lado yake yi matarsa maimuna ma ta dakeni tunda nake da Bashir sau d'aya ya tab'a dukana shima wlh nasan bango na kaishi shi yasa ya dakeni Dan na raina bashir bana bashi girma a matsayin mijina inta zaginsa Inna agaban su Nura na sha ganin Bashir na kuka a b'oye sabida rashin mutuncin da nake masa Inna bana bashi hakkinsa sai naga dama wlh nayi danasani Inna Ashe acikin rufin asiri nake agidan Bashir na tonawa kaina asiri bansan mai ya rufemin ido ba bansan mai ya toshemin kunne ba idan Bashir na fad'amin ahaka Dana raina arzikin da Allah yayi mishi wlh yafi dubu domin na duba Y🅰TSUNMU ba d'aya bane inwani yafika kafi wani a lokacin in yace min haka wani haushi ne yake k'ara rufeni Inna sabida idona ya rufe
Inna naga rayuwa duniya fad'i gareta idan baka godewa Allah da niimar da ya maka ba tabbas zaka godewa azabarsa Inna dubeni dan Allah kamar tsohuwa a lokacin da nake gidan Bashir haka
Nake"?

Fateema tace tana duba jikinta

Inna girgiza kai tayi tace "ina fa lokacin da kike gidan Bashir ba haka kike ba Allah sarki Bashir bawan Allah nima naji kunyar abinda muka masa ni hankalina ma bai dawo jikina na sai Dana ga yanda 'yanmata da zawarawa suke fafutaka Dan suga sun samu koma waye sun aura Dan mazan yanzu suna k'aranci kafin ka samu na aure ba k'aramar wahala kake sha ba kinsan Ashe Rabi kawarki Mijinta yafi Bashir mijinki talauci dan ke baki tab'a zuwa gida kince ataimaka miki da abincin da zaki ci ba amma ita kuwa kullum tana hanyar gidansu dan ataimaka mata da abinda zasu ci ke in tak'aita miki ma yanzu haka wankau take yi a gida nima bansan haka ba sai da naje gidansu muna hira da mamanta take bani labari wlh tun a lokacin jikina yayi sanyi nace lailai bamuda godiyar Allah Ashe duk matar da kika gani agidanta ki kalleta kawai ita tasan mai take fuskanta ta kuma San abinda take gani dan wata mijin nata ga kud'in amma bata da kwanciyar hankali kowace dai mace da iirin jarrabtar da Allah ke mata a gidan miji dan haka ayanzu lallab'awa zamuyi in kin gama idda Baffa ya nemi Bashir ya bashi hak'uri ki koma gidanki cikin rufin asiri kije ki rik'e y'ay'anki"

Fateema da sauri tace "inna ai bazan iya tsayawa nayi idda ba wlh na matsu na ga y'ay'a'na wata kusan takwas ko tara kenan rabona dasu Ina kuma so na nemi yafiyar Bashir dan nasan hakkinsa ne ya kamani"

"Lailai bakida hankali ke yanzu idan akace ki doshi gidan Bashir ahaka ke kya soma kinganki kuwa? Ai ba Bashir ba ko y'ay'anki bazasu ganeki ba dan babu Wanda zai yarda kin tab'a yin fari ga hak'oranki duk sun zama jajjaye fatana ma idan kin gama iddar Bashir ya yarda ya maidaki d'akinki dan kinyi muni da yawa ni in ba gizo idona ke min ba wlh har hak'ora kika yi"

Inna wuro tace tana lek'a bakin Fateema

Fateema Hannu ta kai ta tab'a hak'oranta ta fashe da kuka tana "Allah ya tsinewa Lado albarka duk shi ya janyo min yanzu inna haka zan hak'ura har sai na gama idda Kafin naga y'ay'ana"

Inna cewa tayi "ee haka zaki hak'ura mana watak'ila zuwa lokacin kya dan yi kyaun gani amma kuwa tsautsayi yasa ki kaje ahaka wlh bazasu gane ki ba kima dai yi addu'a Allah yasa bai yi aure ba"

Fateema dafe k'irji tayi tace "insha Allahu ma bai yi aure ba Inna ai nasan Bashir na sona bazai iya yin aure ba ko ma auren zai yi ina yaga kud'in"

Inna mik'ewa tayi tana "aiko bashi da kud'i tsaf zai samu wacce zai aura dan matan yanzu sunyi yawa ni ki tashi kije kiyi wanka sai wani bugawa kike kamar bakya wanka"

Fateema mik'ewa tayi da Sauri dan ita kanta tasan tana bugawar dan duk wankan da zatayi d'oyin baki da Hammatar Lado ya zauna ajikinta ruwa ta cika awani k'aton bokiti ta nufi band'aki dan tayi wanka

Ahaka ranaku suka ringa shud'ewa Fateema ba laifi ta dan ciko ba kamar sanda ta dawo ba amma har a lokacin bata washe ba tana nan bak'ik'irin kullum cikin k'irga kwanakin da zata gama idda take dan ta matsu taga yaranta ta kuma ga Bashir dan har mafarkinsu take yi,sawa tayi aranta idan Allah yasa ta koma gidanta rik'e Bashir zata yi da Hannu bibiyu ta kuma daina masa rashin kunya dan ta koyi hankali a gidan Lado ta kuma sanin darajar miji

Ana gobe zata gama idda matsuwa tayi gari ya waye dan ta rantsewa Inna babu abinda zai hana taje ta ga y'ay'anta

Tun k'arfe shidda ta tashi ta d'ebo kayan da zata sa dan sabon d'inki Inna tayi mata Inna ganin d'okin da take yayi yawa yasa tace babu inda zataje da sassafen nan ta bari wajen k'arfe goma sha d'aya sai ta tafi

Dak'yar Fateema ta kai goma da rabi inna ganin idan ba barinta tayi ta tafi ba hankalinta ba zai kwanta ba

Tundaga nesa Fateema ta fara k'arewa gidan Kallo mamaki Fal aranta gidan dake jikin gidansu Alhaji Ahmed ne ya tafi da imaninta had'ad'en gida ne na bugawa a jarida gashi upstairs tsayawa tayi ta saki baki tana kallon gidan dan gidan k'arshe ne a had'uwa sai da ta kai minti ashirin a tsaye tana kallon gidan dan gidan yama haska unguwar gabad'aya ko gidan Alhaji Ahmed bai kamo k'afar gidan ba girgiza kai Fateema tayi tace "ikon Allah yau naga gidan dayaci uban gidansu Khadija lailai na k'ara yarda Y🅰TSUN MU ba d'aya bane inka fi wani wani yafika yau naga wayanda suka fi su khadija nima naga wayanda Bashir ya fi" ahaka ta lalace tana kallon gidan tana surutai sai da ta gaji dan kanta ta nufi gidan Bashir da yanzu shima ya canza tunani ta fara yi ko dai su Alhaji Ahmed ne suka taimaka musu suka gyara musu gidan dan ta San kad'an da aikinsu dan suna da alheri da kyauta sai da ta gama k'arewa gidan kallo tana tunanin indai dagaske gyara musu su Alhaji Ahmed sukayi ba siyar da gidan Bashir yayi ba lailai ta more dan itama za'a sa gidanta asahun gidan masu kud'i dan gidan shima yanda aka canza shi kamar masu kud'i ahaka ta fara kwankwasa gate d'in gidan tana k'ara k'arewa gidan kallo

Wani dan saurayine yazo ya bud'e gidan "Fateema tayi Sauri ta gaishe shi ce mata yayi daga ina? Wa take nema?

Fateema ce mishi tayi dan Allah Wanda yake zaune
A gidan ada kafin su siyi gidan take nema

Saurayin yanajin abinda tace yagane Bashir take nema

Ce mata yayi "au kinga gidan da suka koma can sati biyu da suka wuce suka tashi daga nan suka koma sabon gida ni kuma na kama haya"

Fateema kanta ne ya d'aure da bayanin da ya mata ta kuma fahimci Bashir siyar da gidan yayi take gabanta ya fad'i tafara tunanin watak'ila talauci ne yasa ya siyar da gidan ya koma haya ganin saurayin na neman ya maida gate d'in ya rufene yasa tayi sauri tace "dan Allah bawan Allah kasan wani Bashir mai robobi daya tashi daga gidanan kafin shi Wanda ya koma can gidan ya siyi gidan"?

Saurayin girgiza kansa yace " gaskiya bansani ba amma zaki iya zuwa ki tambayi shi Alhaji
Da yabar gidan watak'ila zai iya sani" daga haka saurayin ya rufo gate d'in

Fateema hawaye ne ya hau zubo mata tana tunanin ta ina zata fara Neman Bashir da y'ay'anta wani dabara ne ya fad'o mata akan taje gidansu Alhaji Ahmed ta tambayesu tasan zasu iya sanin inda Bashir ya koma dasauri ta nufi gidansu Khadija tana zuwa tafara kwankwasa gate d'in gidan da Sauri

Mai gadine ya bud'e gate Fateema ganin bata San shi ba yasa tace "dan Allah Hajiya Khadija na ciki"?

Mai gadin girgiza mata kai yayi yace " ai sun Dade da komawa Lagos yanzu iyayen Alhaji Ahmed ne aciki"

Fateema gabanta ne ya yanke ya fad'i da taji mai yace kasa magana tayi maigadi kuwa ganin tana b'ata mishi lokaci ya mayar da k'ofar gate d'in ya rufe

Fateema kuka ta fashe dashi tana ta Shiga uku ta ina zata fara neman Bashir da y'ay'anta sabon gidan dake jikin gidan Alhaji Ahmed ta nufa tafara kwankwasawa dan so take idan suma basu San Bashir mai robobi ba daga nan sai ta nufi gidan kanensa dan tasan su bazasu kasa sanin inda bashir yake ba

Mai gadi ne ya bud'e k'ofar yace mata wa take nema

Fateema tunani ta fara yi na wa zata ce tana nema can dabara ta fad'o mata tace matar gidan take nema

Mai gadi har da zai fad'owa Haleema kafin ya barta ta shiga ciki amma da ya tuna gargadin da Bashir ya masa akan duk Wanda yazo Neman shi ko Matar gidan yabarsu su shigo dan bayasan wulak'anci arayuwarsa watak'ila ma masu neman taimako ne

Mai gadi bata hanya yayi yace bismillah amma suna can wajen lambu masu gidan tabi ta wancan flawowin suna can

Fateema shigewa tayi da sauri tana mishi godiya

Tana kaiwa tsakiyar gidan kafin tabi hanyar da mai gadi ya nuna mata tsayawa tayi ta saki baki tana kalle kalle in banda zikiri babu abinda take yi dan tunda take arayuwarta bata tab'a ganin had'add'en gida irin wanan ba hayaniyar da take jiyowa daga wajen lambu ne yasa ta dawo hankalinta ta nufi wajen tana cigaba da kalle kalle

A lokacin Bashir da Aliyu da Nura suna sanye da farin armless iri d'aya da dogon wando suna ta buga ball Bashir inka ganshi a lokacin da su Aliyu bazaka gane su ba dan wani irin kyau da k'iba Bashir yayi ya k'ara zama wani giant

Haleema tana zaune ita da Hameeda da Sumayya suna zaune akan wani had'ad'un kujeru dake wajen suna kallonsu Bashir Haleema tana sanye da wani doguwar Riga tayi parking gashinta tayi wani fresh itama kana kallonta zaka San tana d'auke da ciki ko wata biyu ko uku su Hameeda sun k'ara zama 'yan mata suma sunyi kyau masha Allah sai tafawa su Bashir suke suna a goal sumayya kuma tana kwance ajikin Haleema tana shan madara Haleema ita kuma tana wasa da gashinta

Fateema daga d'an nesa ta tsaya ta zuba musu ido gwanin ban sha'awa dan Sam babu Wanda ta gane a cikinsu duniyar tunani ta tafi na wataran Bashir ya zama mai kud'i suma sun Gina irin wanan gidan suna irin wanan wasanin

Ihun da su Hameeda sukayi na a goal ne ya dawo da ita hankalinta adai dai lokacin da Bashir yaje ya rungume Haleema yana murnar ya cinye su Aliyu ai kamar cewa akayi ya kallo corridor d'in sukayi ido hud'u da Fateema gabansa ne ya yanke ya fad'i yace "Fateema"!

Fateema wani irin da baya tayi data ga Bashir jikinta ne ya hau rawa ta nuna shi da yatsa tana "Bashir"!*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_

*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*

*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*

*A short and interesting story*

Page 75-80

Wajen k'arfe biyar suka iso kano Fateema wani irin farincikine ya ringa ratsata a lokacin da ta sauka daga motar ta lumshe ido ta k'ara shak'ar iskar kano gani take kamar daga kurkuku tafito

Adaidaita ta tara suka dau hanyar gidansu sai kalle kalle take kamar wata bak'auyiya

Tun kafin su k'arasa k'ofar gida tafara k'ok'arin sauka daga adaidaita sahun sabida murna gani take kamar ta shekara rabonta da gida

Mai adaidaita sahun
Bai gama tsayawa ba ta duro daga adaidaita sahun ta cilla mishi kud'insa ta shige gidansu da gudu tana kwad'awa Inna wuro kira

Inna wuro dake kwance ba lafiya sakamakon jininta da ya hau tun lokacin da su Fateema suka tafi da sati d'aya wani yasamu Baffa ya gaya mishi Lado d'an karya ne babu wani saudiya da ya kai Fateema k'auye ya kaita tun daga lokacin jinin Inna wuro ya hau sakamakon yawan tunani da take yi tun tana rashin Lafiya a tsaitsaye har sai da ya kaita ga kwanciya kullum cikin tunanin Fateema take mik'ewa tayi da sauri da taji Muryar Fateema kamar a mafarki

Abakin k'ofa suka had'u da Fateema Fateema kuwa ta rungumeta ta fashe da kuka inna wuro itama kukan ta Fashe dashi ta d'ago Fateema tana k'are mata kallo Gani tayi Fateema tayi wani mugun b'aki ta rame kasusuwa a k'irjinta kamar sarka wuyanta ya wani k'ara tsayi Inna wuro cewa tayi

"Subhanallahi Fateema cuta kika yi? Mai ya sameki haka?

Fateema kuka ta k'ara fashewa dashi tace "inna babu abinda banyi ba babu abinda bai sameni ba Inna naga rayuwa nashiga taskun rayuwa wlh nasha wuya a gidan Lado"

Inna hawayen daya zubo mata ta share tana "naga alama Fateema ko baki fad'a ba kinsha wuya satinku d'aya da tafiya wani ya samu Baffa ya gaya mishi Wanda kika aura d'an karya ne Dan yaudara ina nan ina Murna Kin tafi saudiya wlh sai fad'awa mutane nake kuna can muma kwanan zamu biku Ashe ba saudiya kuka tafi ba wai K'auye ya kaiki"

Fateema ajiyar zuciya tayi ta samu guri ta zauna ta cire hijabin jikinta ta fara bawa Inna wuro labarin irin wuyan da ta sha a gidan Lado babu abinda ta b'oye mata har yanda yake gurzata kamar dabba sai da ta fad'a mata ta k'arasa maganar da kuka tana

"Inna nayi danasanin rabuwa da Bashir Inna baka sanin darajar Abu sai ya sub'uce ma Ashe Bashir mai kud'ine tunda nake a gidansa ban tab'a cin wake da gero ba ban tab'a cin rogo da kulli ba wlh Inna bana yiwa su Aliyu wanki Bashir ne yake musu amma sai gashi nayi wankin y'ay'an Lado Inna har dukana Lado yake yi matarsa maimuna ma ta dakeni tunda nake da Bashir sau d'aya ya tab'a dukana shima wlh nasan bango na kaishi shi yasa ya dakeni Dan na raina bashir bana bashi girma a matsayin mijina inta zaginsa Inna agaban su Nura na sha ganin Bashir na kuka a b'oye sabida rashin mutuncin da nake masa Inna bana bashi hakkinsa sai naga dama wlh nayi danasani Inna Ashe acikin rufin asiri nake agidan Bashir na tonawa kaina asiri bansan mai ya rufemin ido ba bansan mai ya toshemin kunne ba idan Bashir na fad'amin ahaka Dana raina arzikin da Allah yayi mishi wlh yafi dubu domin na duba Y🅰TSUNMU ba d'aya bane inwani yafika kafi wani a lokacin in yace min haka wani haushi ne yake k'ara rufeni Inna sabida idona ya rufe
Inna naga rayuwa duniya fad'i gareta idan baka godewa Allah da niimar da ya maka ba tabbas zaka godewa azabarsa Inna dubeni dan Allah kamar tsohuwa a lokacin da nake gidan Bashir haka
Nake"?

Fateema tace tana duba jikinta

Inna girgiza kai tayi tace "ina fa lokacin da kike gidan Bashir ba haka kike ba Allah sarki Bashir bawan Allah nima naji kunyar abinda muka masa ni hankalina ma bai dawo jikina na sai Dana ga yanda 'yanmata da zawarawa suke fafutaka Dan suga sun samu koma waye sun aura Dan mazan yanzu suna k'aranci kafin ka samu na aure ba k'aramar wahala kake sha ba kinsan Ashe Rabi kawarki Mijinta yafi Bashir mijinki talauci dan ke baki tab'a zuwa gida kince ataimaka miki da abincin da zaki ci ba amma ita kuwa kullum tana hanyar gidansu dan ataimaka mata da abinda zasu ci ke in tak'aita miki ma yanzu haka wankau take yi a gida nima bansan haka ba sai da naje gidansu muna hira da mamanta take bani labari wlh tun a lokacin jikina yayi sanyi nace lailai bamuda godiyar Allah Ashe duk matar da kika gani agidanta ki kalleta kawai ita tasan mai take fuskanta ta kuma San abinda take gani dan wata mijin nata ga kud'in amma bata da kwanciyar hankali kowace dai mace da iirin jarrabtar da Allah ke mata a gidan miji dan haka ayanzu lallab'awa zamuyi in kin gama idda Baffa ya nemi Bashir ya bashi hak'uri ki koma gidanki cikin rufin asiri kije ki rik'e y'ay'anki"

Fateema da sauri tace "inna ai bazan iya tsayawa nayi idda ba wlh na matsu na ga y'ay'a'na wata kusan takwas ko tara kenan rabona dasu Ina kuma so na nemi yafiyar Bashir dan nasan hakkinsa ne ya kamani"

"Lailai bakida hankali ke yanzu idan akace ki doshi gidan Bashir ahaka ke kya soma kinganki kuwa? Ai ba Bashir ba ko y'ay'anki bazasu ganeki ba dan babu Wanda zai yarda kin tab'a yin fari ga hak'oranki duk sun zama jajjaye fatana ma idan kin gama iddar Bashir ya yarda ya maidaki d'akinki dan kinyi muni da yawa ni in ba gizo idona ke min ba wlh har hak'ora kika yi"

Inna wuro tace tana lek'a bakin Fateema

Fateema Hannu ta kai ta tab'a hak'oranta ta fashe da kuka tana "Allah ya tsinewa Lado albarka duk shi ya janyo min yanzu inna haka zan hak'ura har sai na gama idda Kafin naga y'ay'ana"

Inna cewa tayi "ee haka zaki hak'ura mana watak'ila zuwa lokacin kya dan yi kyaun gani amma kuwa tsautsayi yasa ki kaje ahaka wlh bazasu gane ki ba kima dai yi addu'a Allah yasa bai yi aure ba"

Fateema dafe k'irji tayi tace "insha Allahu ma bai yi aure ba Inna ai nasan Bashir na sona bazai iya yin aure ba ko ma auren zai yi ina yaga kud'in"

Inna mik'ewa tayi tana "aiko bashi da kud'i tsaf zai samu wacce zai aura dan matan yanzu sunyi yawa ni ki tashi kije kiyi wanka sai wani bugawa kike kamar bakya wanka"

Fateema mik'ewa tayi da Sauri dan ita kanta tasan tana bugawar dan duk wankan da zatayi d'oyin baki da Hammatar Lado ya zauna ajikinta ruwa ta cika awani k'aton bokiti ta nufi band'aki dan tayi wanka

Ahaka ranaku suka ringa shud'ewa Fateema ba laifi ta dan ciko ba kamar sanda ta dawo ba amma har a lokacin bata washe ba tana nan bak'ik'irin kullum cikin k'irga kwanakin da zata gama idda take dan ta matsu taga yaranta ta kuma ga Bashir dan har mafarkinsu take yi,sawa tayi aranta idan Allah yasa ta koma gidanta rik'e Bashir zata yi da Hannu bibiyu ta kuma daina masa rashin kunya dan ta koyi hankali a gidan Lado ta kuma sanin darajar miji

Ana gobe zata gama idda matsuwa tayi gari ya waye dan ta rantsewa Inna babu abinda zai hana taje ta ga y'ay'anta

Tun k'arfe shidda ta tashi ta d'ebo kayan da zata sa dan sabon d'inki Inna tayi mata Inna ganin d'okin da take yayi yawa yasa tace babu inda zataje da sassafen nan ta bari wajen k'arfe goma sha d'aya sai ta tafi

Dak'yar Fateema ta kai goma da rabi inna ganin idan ba barinta tayi ta tafi ba hankalinta ba zai kwanta ba

Tundaga nesa Fateema ta fara k'arewa gidan Kallo mamaki Fal aranta gidan dake jikin gidansu Alhaji Ahmed ne ya tafi da imaninta had'ad'en gida ne na bugawa a jarida gashi upstairs tsayawa tayi ta saki baki tana kallon gidan dan gidan k'arshe ne a had'uwa sai da ta kai minti ashirin a tsaye tana kallon gidan dan gidan yama haska unguwar gabad'aya ko gidan Alhaji Ahmed bai kamo k'afar gidan ba girgiza kai Fateema tayi tace "ikon Allah yau naga gidan dayaci uban gidansu Khadija lailai na k'ara yarda Y🅰TSUN MU ba d'aya bane inka fi wani wani yafika yau naga wayanda suka fi su khadija nima naga wayanda Bashir ya fi" ahaka ta lalace tana kallon gidan tana surutai sai da ta gaji dan kanta ta nufi gidan Bashir da yanzu shima ya canza tunani ta fara yi ko dai su Alhaji Ahmed ne suka taimaka musu suka gyara musu gidan dan ta San kad'an da aikinsu dan suna da alheri da kyauta sai da ta gama k'arewa gidan kallo tana tunanin indai dagaske gyara musu su Alhaji Ahmed sukayi ba siyar da gidan Bashir yayi ba lailai ta more dan itama za'a sa gidanta asahun gidan masu kud'i dan gidan shima yanda aka canza shi kamar masu kud'i ahaka ta fara kwankwasa gate d'in gidan tana k'ara k'arewa gidan kallo

Wani dan saurayine yazo ya bud'e gidan "Fateema tayi Sauri ta gaishe shi ce mata yayi daga ina? Wa take nema?

Fateema ce mishi tayi dan Allah Wanda yake zaune
A gidan ada kafin su siyi gidan take nema

Saurayin yanajin abinda tace yagane Bashir take nema

Ce mata yayi "au kinga gidan da suka koma can sati biyu da suka wuce suka tashi daga nan suka koma sabon gida ni kuma na kama haya"

Fateema kanta ne ya d'aure da bayanin da ya mata ta kuma fahimci Bashir siyar da gidan yayi take gabanta ya fad'i tafara tunanin watak'ila talauci ne yasa ya siyar da gidan ya koma haya ganin saurayin na neman ya maida gate d'in ya rufene yasa tayi sauri tace "dan Allah bawan Allah kasan wani Bashir mai robobi daya tashi daga gidanan kafin shi Wanda ya koma can gidan ya siyi gidan"?

Saurayin girgiza kansa yace " gaskiya bansani ba amma zaki iya zuwa ki tambayi shi Alhaji
Da yabar gidan watak'ila zai iya sani" daga haka saurayin ya rufo gate d'in

Fateema hawaye ne ya hau zubo mata tana tunanin ta ina zata fara Neman Bashir da y'ay'anta wani dabara ne ya fad'o mata akan taje gidansu Alhaji Ahmed ta tambayesu tasan zasu iya sanin inda Bashir ya koma dasauri ta nufi gidansu Khadija tana zuwa tafara kwankwasa gate d'in gidan da Sauri

Mai gadine ya bud'e gate Fateema ganin bata San shi ba yasa tace "dan Allah Hajiya Khadija na ciki"?

Mai gadin girgiza mata kai yayi yace " ai sun Dade da komawa Lagos yanzu iyayen Alhaji Ahmed ne aciki"

Fateema gabanta ne ya yanke ya fad'i da taji mai yace kasa magana tayi maigadi kuwa ganin tana b'ata mishi lokaci ya mayar da k'ofar gate d'in ya rufe

Fateema kuka ta fashe dashi tana ta Shiga uku ta ina zata fara neman Bashir da y'ay'anta sabon gidan dake jikin gidan Alhaji Ahmed ta nufa tafara kwankwasawa dan so take idan suma basu San Bashir mai robobi ba daga nan sai ta nufi gidan kanensa dan tasan su bazasu kasa sanin

Please Login or Register in order to submit comment