Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zasu yi ba zan iya ce miki yaudarar da mai gida ya min ya aureni wlh bai yi miki shi ba


Nifa ana dab da aurena da Wanda nakeso na had'u da Lado Wanda zan aura ina sanshi gashi da rufin asiri amma wlh sabida kwad'ayin abun duniya na bijire nace bana sanshi Dan Lado har mukullin mota ya kawo min wlh iyayena har fushi sukayi dani saurayina kuwa har kuka yaringa min amma na murzawa idona toka nace idan ba lado ba sai rijiya

Aranar da aka d'aura aurena da lado iyayena suka ce wlh duk abinda nagani kar na sake na doso inda suke Dan na watsa musu k'asa a ido babu irin shawarar da basu bani ba amma kinsan Wanda yayi nisa baya jin kira gani nake basu San mai suke cewa ba basu San arziki ke kirana ba Ashe rabon zan zauna a kauye ne yake kirana Lado ba iya karyar arziki ya min ba harda ta iyali Ashe nice ma matarsa ta uku to kingani dawane fuska zan Koma wajen iyayena su saurareni Dan haka kema kiyi hak'uri Dan mu muka janyowa kanmu"


Fateema hannu ta d'ora aka ta fashe da kuka tana "baiwar Allah nayi dana sanin abinda nayi arayuwata gwara ke buduruwa ce baki da cikakken hankalin daya kamata ace ina dashi lura da na tab'a aure har da yara hud'u domin ni kingani nan ba yarinya bace da yarana guda hud'u haka na tsallaka na barsu nabar mijina mai sona sabida kwad'ayin abun duniya da rashin godiyar Allah Wanda sabida rufewar da idona yayi ban dubi yarana ba
Ban dubi mijina ba
Ban dubi yatsar dake hanuna naga tsayinsu ba d'aya bane na tsallakasu nabi san zuciyata sabida rashin hankali irin nawa wlh gwara ke akaina nifa yanzu ki dubi halin Dana jefa kaina yanzu wanan uban aikin da ya zayyano ina zan iya
Nan hakkinsa sau uku yake k'arba arana baiwar Allah wanan wane irin masifa da balai ne dawane zanji wayyo Allahna kaicona nayi nadamar abinda nayi"


Fateema tace tana fashewa da kuka Ainau itama kukan ta fashe dashi Dan itama tana cikin tashin hankali har gobe.



Readers kuyi hakuri previous page d'in Dana yi nayi mistake instead of nasa lado Bashir nasa


Baiwar Allah maganarki bata min dadi ba ke kin tsani sadnaf dinan sabida ta fiye Jan aji Dan taga anasan novel dinta yau intayi typing gobe bazata yi ba

Haba baiwar Allah magana mai dadi ma ai sadaka ce idan baki godemin ba ai bazaki tsinemin ba domin kuwa ina iya bakin kokarina Dan nayi typing, ba biyana ake yi ba ra'ayin kai na ne nake typing bawani ne yasani ba,ko angaya miki duk Wanda yake rubuta novel bashida aikin yi ne,wlh nan da kika gani ina da aikin yi sa kaina kawai nayi,Dan bazan kashe kaina abanza ba,dasafe bakwai na tafi makaranta na dawo biyu nayi ayyukan gida,ina aiki ina typing banida hutu ko kad'an amma ahaka kika rainawa k'ok'arin danake,Dan Allah kiyi typing 10 lines kika if it is easy to type.
*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*





Page 65-70



Lado bashi ya tashi daga barci ba sai wajen k'arfe hud'u da rabi mik'ewa yayi yafita waje Dan yayi wanka


Ganin bai ga kowa a tsakar gida ba yasa ya nufi b'angarensu zainab dan yana kyautata zaton Fateema tana can


A bakin k'ofa ya tsaya ya d'aga labulen d'akin zainab da Maimuna ya hango suna ta hira k'asa k'asa da alama gulma suke yi


Lado girgiza kai yayi yace "aikin kenan gulma da munafirci ina Fateemar take"?

Zainab ce ta bashi amsa Dan yana d'aga labule maimuna ta kau da kanta Dan haushin Lado take ji Dan da bai yo amarya ba da itace da girki


"Gulmar me zamuyi mai gida inaga tana d'akin Ainau"

Lado bai ce komai ba ya saki labulen ya nufi b'angaren Ainau Har a lokacin kuka suke d'aga labulen d'akin da Lado yayi ne yasa Ainau tayi sauri ta share hawayen fuskarta Fateema kuwa ko gezau ba tayi ba ta cigaba da kukanta


Lado had'e rai yayi ya kalli Ainau yace "kukan mai kuke yi"?

Ainau shiru tayi ta kasa magana gabanta na fad'uwa Dan har gobe tana tsoron Lado


Wani mugun tsawa Lado ya daka mata yace "ba tambayarki nake ba kukan mai kuke yi"?


Cikin rawar jiki Ainau tace tace "ba kuka mukeyi ba wa"


Fateema katseta tayi da sauri tana "Lado kuka mukeyi Dan bak'incikin yaudarar da ka mana ka auremu ko tsoron Allah ba kaji Lado kayi mana irin wanan muguwar yaudara Lado kaji tsoron Allah ka sakemu Dan ni bazan iya rayuwa awanan k'auyen ba"


Lado dariya ya k'yalk'yale dashi yace "ai ni bani na yaudare kuba Ku kuka yaudari kanku dama ki Adana wanan hawayen naki Dan zai miki amfani nan gaba Dan ayanzu dai baki ga komai ba tukuna daga kawoki har kike wanan kukan ai babu saki atsakaninmu Fateema in kinga na sakeki to ki tabbata na samu wata sabuwar injin Dan duk matan Dana aura kece bazawara sauran kuwa duk ni na b'are su aleda shiyasa nake tunanin ke zan iya sakinki ina samu wacce zata maye gurbinki ba tare da b'ata lokaci ba yanzun nan ki tashi ki kaimin ruwan wanka kizo ki fara had'a had'ar d'ora abincin dare Dan bana so aringa kaiwa dare ana girki"


Fateema baki ta cuno zata luk'a mishi Ashar suka had'a ido da Ainau ta girgiza mata kai da sauri Fateema haka ta mik'e tafita waje ta kai mishi ruwan wanka tana hawaye.


Atak'aice bak'aramin wahala Fateema tasha wajen girkin dare ba dan Lado hana Ainau yayi ta tayata yace gwara tayi ita kad'ai ahaka zata
saba shi yama San da Fateemar ce bazata tab'a tayata ba in banda kuka babu abinda Fateema ta ringayi Ainau sai tausayinta take ji


Da ta gama girkin Daren ma sai da Lado yasa ta share gidan tas su zainab sai murna suke yi



Fateema daddare bayan angama cin abinci d'akin Ainau ta gudu ta kwanta Dan tana tsoron Lado ya k'ara damkarta aikuwa ko minti biyar batayi a d'akin ba Lado ya shigo d'akin yana hamma da mik'a Fateema hawaye ne ya hau zubo mata tana "Lado Dan girman Allah kayi min rai wlh banida Lafiya jikina duk ciwo yake min" Lado ko saurararta bai yi ba ya kamo hanunta sukayi waje Fateema sai magiya take mishi




Aranar Fateema tagane kuranta Dan babu sunan Wanda bata kira ba har Khadija ta kira mak'ociyarta Dan Lado bai raga mata ba ko k'adan Dan musamman ya nemo maganin k'arfi bawai Dan yaji dadi ba aa zalar mugunta ce kawai



Atak'aice Fateema kwananta biyar a gidan Lado ta canja kamanin inka ganta bazaka tab'a yarda ita bace dan tabi tayi bak'i ta rame bata da aikin da ya wuce kuka da nadama kullum Ainau ce kawai take tausayinta a gidan aranar da ta cika sati d'aya a gidan Lado yayi musu sallama zai koma bakin aikinshi banda uban dokokin daya k'afa a gidan yacewa su zainab su sawa Fateema ido sosai Dan karta yi yunkurin gudawa





B'angaren Bashir kuwa ayau aka d'aura aurensa da Haleema aranar kuma ta tare a gidansa da aka gyara sosai Dan Filin da Alhaji Ahmed ya bashi bai fara ginawa ba tukuna,Su Hameeda dai sunga ankawo amarya basu San Bashir aure yayi ba




Bayan sallar isha Bashir ya shigo gidan tundaga zauren gidan yaji kamshi turare ya doki hancinsa,Palonsu Hameeda yafara nufa Dan gidan part biyu aka maidashi part na farko shine b'angarensa Dana amarya,sai na ciki inda Su Hameeda suke


A Palo ya tarar dasu azaune Aliyu da Nura na buga game Hameeda da Sumayya na kallo aladabce suka ringa mishi sannu da zuwa yabisu da kallo d'aya bayan d'aya yana amsawa tare da ajiye ledojin hanunsa

Nura tashi yayi daga game d'in dayake ya koma kusa da Bashir yana "Abba dazu ankawo wata ta shiga d'akin Umma wacece ita"


Su Aliyu suma maida hankalinsu sukayi wajen Bashir gabad'aya suna jiran suji mai zaice

Bashir murmushi yayi yace "Auntynku ce aka kawo muku Dan ta ringa muku girki tana kula daku tana muku abinda ranku yakeso"

Sumayya mak'e kafad'a tayi tace "ni Umma ce zata ringa mana girki tana kula damu Abba Yaushe Umma zata dawo"?


Aikuwa Su Nura kamar jira suke Sumayya tayi tambayar dukansu suka hau cewa yaushe Fateema zata dawo


Bashir rasa amsar da zai basu yayi take tausayinsu ya rufeshi Dan yasan suna kewar Fateema

Bashir murmushi ya k'irk'iro yace "Ku kwantar da hankalinku Ummanku takusa dawowa dazu munyi waya da ita

Ai da sauri Su Aliyu suka matsa kusa dashi cikin tsananin farinciki suna "Dan Allah Abba ka kira mana Ummanmu awaya muji muryarta"

Bashir wani irin tausayinsu ne ya k'ara rufeshi dayaga yanda suke tsallen murna wata dabara ce ta fad'o mishi yace musu "Ina zuwa to bari na d'auko wayata"

To suka ce suka ringa murna Bashir ya mik'e yayi waje

D'akin Fateema ya nufa da yazama mallakin Haleema ayanzu ya d'aga labulen d'akin ahankali tare da sallama


Haleema na kan gado ta sunkuyar dakai ko ina na jikinta a lullub'e amsa sallamar tayi can k'asan murya

Bashir kuwa yaji tsigar jikinsa ta tashi wani iri yaringa ji aransa ya k'arasa kan gadon ya zauna agefenta

Magana ya farayi yana "ina dawowa yarana suka hau cewa ankawo wata tashiga d'akin Ummansu suka hau tambayata wacece to nayi musu bayani da Auntynsu ce amma sun samin rigima da alailai na kira musu ummansu awaya suji muryarta to shine nace bari na fad'a miki zan kiraki a waya na had'aku amatsayin Ummansu"


Tunda yafara magana kanta a sunkuye yake sai da ya gama ta d'ago cewa tayi "insuka ji muryata bazasu gane ba Ummansu bace"

Murmushi Bashir yayi yace "karki damu dak'yar in zasu gane Dan muryarku kusan iri d'ayace Dan itama Fateema k'aramar muryace da ita"

"To shikenan bari na d'auko wayata a jaka" Haleema tace tana nufar inda Jakarta ke ajiye Bashir da kallo ya bita har ta dawo

Murmushi yayi dayaga tayi Sauri ta sunkuyar dakai cewa yayi " amma fa kinyi kyau"

Haleema batace komai ba illa ma k'ara sunkuyar dakai da tayi Bashir mik'ewa yayi yace mata bari yaje ya dawo

Yana zama Su Aliyu suka zagayeshi suna murnar zasuji muryar Fateema

Bashir Number Haleema ya kira yasa a handsfree yana fara ringing Su Nura suka k'ara matsawa kusa da Bashir kamar zasu shige wayar


Haleema kuwa sai da ta daidaita muryarta ta d'aga wayar Su Aliyu had'a baki sukayi wajen cewa Umma

Haleema kuwa tuni ta rude ta kasa magana ganin sun cigaba da " Umma Umma bakya jin mu ne Aliyu ne Umma Sumayya ce Umma Hameeda ce Umma Nura ne yaushe zaki dawo Umma"


Bashir ji yayi hawaye na neman zubo mishi Haleema kuwa ta d'aure tace "Aliyu Hameeda Sumayya Nura kuna Lafiya ya makaranta kar ku damu ina nan zuwa na kusa dawowa"


Nura da sauri suka ce to "Umma kamar yaushe zaki dawo gobe"

Aliyu kuwa da Hameeda kallon juna suka yi Dan suna jin muryar sun San bana Fateema bane Bashir kuwa yana Lura dasu

Haleema cewa tayi "ba gobe zan dawo ba amma nakusa dawowa kunji zan taho muku da kayan dad'i inzan dawo kunji 'yan albarka"

Nura da sauri yace "to Umma sai kin dawo Abba ma ya kawo wata Aunty wai zata ringa kula damu kafin ki dawo"

Haleema rasa mai zata ce tayi Bashir kuwa ya kashe wayar yana "Ai kunji muryarta yanzu ko ta kusa dawowa Aliyu da Hameeda suna so suce kamar ba muryar Ummansu ba amma suna tsoro

Bashir yasan da magana abakinsu amma so yake ya k'aucewa tambayarsu mik'ewa yayi ya d'auki ledojin da ya shigo dasu ya ware nasu Hameeda ya mimik'a musu yana maza suje suci Su kwanta shima kwanciya zaije yayi



Godiya suka mishi suna mishi sai da safe sauran ledojin ya d'auka yayi waje tausayinsu Aliyu fal ransa


Atak'aice da k'yar Bashir yayi Nafila raka'a biyu na godiya ga Allah dan amatsayinsa na cikakken Namijin mai lafiya daya samu wajen wata hud'u bai kusanci mace ba amatse yake


Aranar ya maida Haleema cikakiyar mace bayan komai ya Lafa Haleema barcin wahala ya d'auketa Fateema ta fad'o mishi arai dan haka kawai yakasa mantawa da ita dan itace First love d'insa kuma uwar yayansa haka kawai yake jin rashin dadi daya samu arziki bata gidansa yanzu ko awane hali take oho

Ko awane gari take aure baisani ba a haka ya ringa tunane tunane ganin barci yak'i d'aukansa yasa ya mik'e ya nufi band'aki dan ya tsarkaka jikinsa ya d'aura alwala yazo yayi sallah
*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*



*WANAN SHAFIN NAKI NE TAKWARATA PHEEYNER NAGODE SOSAI ALLAH YABAR ZUMUNCI*



*MASOYANA NAGA SAK'ONKU TA HANUN FADILAH Y KHAN NASO NA ZAYYANO SUNAYENKU NA MUKU GODIYA AMMA KUNYI YAWA DA HAKA DAI NAKESO NA MUKU GODIYA DAN NAGA SAK'ONINKU NAGODE KWARAI DAGASKE*




*AMININ MUTUM BIYU MUNAFIKIN MUTUM D'AYA KAI DAI KAWAI KA GA MUTUM SANIN CIKINSA SAI ALLAH,MUTUM NE ZAI NUNA MA SHI MASOYINKA NE AGABAN IDONKA AMMA ABAYAN IDONKA GUNDUMEMEN MAKIYINKA NE YA ALLAH KA CIGABA DA TONAWA MAKIYANMU ASIRI*



Page 70-75


Sati biyu kenan da auren Bashir da Haleema
Soyayya mai zafi ce ta shiga tsakaninsu sakamakon ladabi da biyayya da Haleema take yiwa Bashir ga kunya duk wani Abu datasan zai farantawa Bashir rai shi take yi bata tab'a gaida Bashir a tsaye,

Bashir kuwa da wanan halayen nata ta k'ara samun matsayi a zuciyarsa yaji yana k'ara Santa babu abinda yafi burgeshi da ita kamar yanda ta janyo yaransa jikinta Yanzu Nura kullum yana mak'ale da ita Bashir sai yanzu yasan yayi aure, godewa Allah yake kullum da ya bashi mace tagari



B'angaren Fateema kuwa ba k'aramin wuya take sha a gidan Lado ba Dan zainab da maimuna sako ta sukayi agaba duk wanan rashin kunyarta tuni ta ajiye shi a gefe Dan ko da maimuna kawai aka barta ta isheta haka suke tulo mata kayan wankin yaransu tana ji tana gani dole tayi Dan ranar da suka fara kawo mata kayan wankin da ta k'i yi Maimuna ba k'aramin jibgarta tayi ba Dan tafita k'arfi nesa ba kusa kasancewarta 'yar lukuta da mazaunanta ta zaune ta ta jibgeta ta kuma hanata abinci kasancewar itace da girki adaren ranar Fateema taci kuka ta gode Allah Dan har zazzabi ne ya rufeta,Ainau ce kawai taringa rarrashinta tayi nadama aranar yafi cikin kwando ita da ko wankin y'ay'anta bata yi bashir ne yake yi sai gashi kwad'ayinta ya janyo mata tayi wankin yara Tara wankin ma mai dan karan datti


Adaren ta kuduri niyyar barin gidan in kowa yayi barci aikuwa wajen k'arfe goma sha biyu na dare bayan Ainau tayi mata sallama taje ta kwanta ta mik'e ahankali tafito daga d'akinta da takalmanta a mak'ale a hammata sadaf sadaf ta ringa tafiya tana waige waige ahaka ta isa bakin k'ofa


Turus tayi da taga k'ofar a rufe da kwado hawayen bak'inciki ne ya hau zubo mata dan taso ayau tabar gidan Lado Dan ta gaji da irin wanan zaman marinar da take yi na rashin yancin kai


Tunda tazo gidan take gudawa sakamakon irin abincin da take ci

Zaman dirshan tayi a bakin k'ofar ta rushe da kuka tana "kaicona nayi nadamar abinda nayi yau agarin kwad'ayina na rabu da uban yayana mai sona na rabu da yarana Allah sarki Hameeda Y'ata tafini hankali Dan ta sha cewa Umma mufa masu kud'ine wlh Dan akwai 'yar ajinmu har rok'on abinci take yi mu kuwa Umma Abbanmu yana siyo mana abinci bamu tab'a roko ba Hameeda kina fad'ar haka zan kwad'a miki mari ko nace kifita daga idona ubanku mitsyacine Ashe kinfini gaskiya Abbanku mai Kud'i ne ooo Allahna ka dubeni da idon rahama ka yanke min zaman gidanan ka sa Lado ya sakeni"


Motsi ta jiyo kamar za'a fito tayi Sauri ta mik'e ta nufi d'akinta aikuwa tana shigewa Lado yafito Dan da yamma ya dawo


Fateema rufe idonta tayi da sauri da taji alamar an bud'e k'ofarta anshigo Lado a bakin k'ofa ya tsaya yana k'are mata kallo can yafara kicin kicin cire gajeran wandon dake jikinsa



Fateema da kankantar da idonta tayi tana kallonsa da sauri ta mik'e cikin Fad'uwar gaba tace "Lado lafiya mai kake nema a d'akina"?


Lado ko kulata bai yi ba sai da yagama cire gajeran wadonsa ya nufeta yana "Hakkina nazo na k'arba"


Wani irin hantsilawa Fateema tayi daga kan gadon ta koma can gefe cikin rawar jiki Dan idan akwai abinda yafi d'aga mata hankali arayuwa bai wuce Lado ya kusanceta ba Dan ko d'oyin hammatarsa da warin baki kawai da take shak'a ba k'aramin hautsina mata kayan ciki yake ba ballantana uwa uba in yace zai sadu da ita ba k'aramin azaba take sha ahanunsa ba Dan haka yake zuwar mata tamkar dabba kuma baya gajiya


Cikin tsananin tsoro Fateema tace "bangane hakkinka kazo k'arba ba Lado naga banice da girki ba Maimuna ce da girki tayaya zaka zo k'arbar hakkinka awajena


"Ai ba sai kina da girki zan k'arbi hakkina ba ko kina da girki ko bakida girki duk lokacin Dana ga dama zan iya zuwa na k'arbi hakkina karfa ki manta dubu d'ari na biya sadaki banda dubu goma goma da na ringa baki kinga kuwa dole duk lokacin Dana bukaci na dirji kud'ina nazo"


Lado yace yana nufar inda take a tsaye

Fateema ware muryarta tayi ta Saki ihu da iya k'arfinta zainab da Ainau sun jiyo ihunta maimuna da inta fara barci kamar gawa ita ce kawai bata jiyo ihun Fateema ba


Lado da Sauri ya toshe mata baki ya wurgar da ita akan gado ya afka mata kamar dabba


Fateema sabida tsananin azaba babu abinda takeyi sai juyar da kai dan hawayen ma kasawa tayi ahaka Lado yagama budurinsa ya mik'e ya barta sai da ya fice daga d'akin Fateema ta fashe da matsanacin kuka Dan Lado fyade yake mata take zazzafan zazzabi ya rufeta ko sau d'aya barci bai yi gingin d'aukarta ba a idonta aka yi sallar asuba har gari ya waye amma ta kasa tashi Dan kanta kamar ya fad'o Dan azaba


Sai da maimuna ta gama abincin karyawa suka gama ci tukuna Maimuna ta kankaro kanzo ta bawa danta tace yakai wa Fateema d'aki taga alama yau mulki take ji shiyasa tak'i fitowa


Lokacin da d'an maimuna ya shiga d'akin Fateema akwance dai yaga Fateema sai hawaye ke zubo mata muryarta har ya dashe dungurar da abinci yayi yana Neman ficewa daga d'akin Fateema tayi Sauri ta tsayar dashi tana ya taimaka ya kira mata Ainau yaron bai ce komai ba ya fito daga d'akin Fateema ya nufi d'akin Ainau ya gaya mata sakon Fateema


Ainau dak'yar ta mik'e ta fito Dan tun jiya daddare take ciwon Mara da baya

Dak'yar ta d'aga k'afarta ta shiga d'akin Fateema agefen Fateema ta zauna tana tambayarta mai yafaru take kuka


Fateema wani kukan ta k'ara fashewa dashi tace mata ta taimaka mata kanta ciwo yake kamar zai rabe gida biyu ta samo mata magani tasha


Ainau hawayen tausayine ya zubo mata Dan ita kanta da sassafe taje ta samu lado akan ya bata kud'i ta siyi maganin yace mata taje ta jika maganin shawara tasha shawara ce take damunta


Ainau cewa tayi sai dai ta tambayo mata su zainab ko suna da maganin ciwon kai amma ita bata dashi dak'yar ta k'ara mik'ewa ta fito waje


Maimuna ce mata tayi bata dashi sai zainab ce ta bata panadol ta kaiwa Fateema tasha


Atak'aice sai wajen k'arfe goma sha d'aya Fateema ta iya mik'ewa ta nufi band'aki tayi wankan tsarki tazo tayi alwala tayi sallah idonta a kumbure sabida kukan da tasha.


Tunda ga lokacin Fateema ta mik'a al amuranta wajen Allah ta dage da addua babu dare babu rana akan Allah ya kawo k'arshen zamanta a gidan Lado


Har ta saba da ayyukan gidan da jarrabar Lado wulak'anci iri iri Lado yake mata har ya kai ya kawo har dukanta yake wai shi in yana ganinta haka kawai sai ya ringa jin haushinta


Ahaka ta samu wata hud'u a gidan Lado acikin matsanacin hali babu abinda take yi da ya wuce addu'a duk dare da tunanin yaranta Dana Bashir take barci.


Watarana suna zaune da Ainau a tsakar gida bayan sun gama wanke tulun kayan wankin yara suna hira Fateema tana rik'e da jaririn Ainau dan wata uku Lado ya shigo gidan Fuskarsa a murtuk'e


Atare suka mik'e hankalinsu a tashe dan basu tsammaci zuwansa ba wajensu ya nufa gabansu kuwa ya cigaba da Fad'uwa agaban Fateema ya tsaya adai dai lokacin da su Zainab suma suka fito daga d'akinsu suka zubawa Lado ido cikin mamakin dawowarsa ayanzu



Lado Hannu ya zura a aljihunsa ya zaro wata takarda ya mik'awa Fateema yana "wanan takardar sakinki ne na sakeki saki biyu dan na samu wata sabuwar inji yanzu haka sati mai zuwa d'aurin aurenmu dan haka ayau nake so ki tafi gidanku ga kud'in mota nan ki tattara kayanki nabaki minti talatin ki had'a kayanki"

Fateema sabida tsabar murna zubewa tayi akasa taringa godewa Allah Ainau hawaye ne ya hau zubo mata tana dama har da ita Lado ya saka Fateema kuwa godiya ta hau yiwa Lado tana Allah ya saka mishi da alheri ya bashi zaman Lafiya shi da amaryarsa d'akinta ta nufa da Sauri ta sako Hijabinta babu abinda ta d'auka daga hijabi tayo waje dasauri dan gani take idan ta k'ara mintina a gidan Lado zai iya janye sakin da ya mata



zainab da maimuna jikinsu ne yabi yayi sanyi da suka ga Ainau ta rungume Fateema tana ta kuka fashe Fateema itama kukan rabuwa ta ringa yi da Ainau dan sun shak'u da ita sosai sabo mai dadi ga dole su rabuwa dak'yar Fateema ta janye Ainau daga jikinta tana karta damu insha Allahu bazata tab'a mantawa da ita ba zata ringa tayata da addu'a itama


Ahaka suka yi hanyar waje zainab da maimuna suma suka rakata suna sai watarana idan Allah ya kaddara zasu k'ara had'uwa


Fateema share hawayenta tayi tabi maimuna da kallo dan har ga Allah bazata tab'a manta maimuna a rayuwarta ba dan ta daku ahanunta murmushi tayi ta k'ara karewa gidan kallo ta juyo ta kalli Ainau ta share mata hawaye ta k'arbi jaririn Ainau tayi mishi addu'a ta mik'awa Ainau shi Ainau sai kuka take kamar ranta zai fita



Ainau na k'arbar d'an ta juya da Sauri tafara tafiya dan gani take Lado zai iya zuwa yace ya fasa atakaice Fateema kukan farinciki ta fashe dashi a lokacin data ganta azaune a mota sun dau hanyar kano damke takardar hanunta tayi sosai kamar za'a k'wace mata takardar.

*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*






Page 75-80




Wajen k'arfe biyar suka iso kano Fateema wani irin farincikine ya ringa ratsata a lokacin da ta sauka daga motar ta lumshe ido ta k'ara shak'ar iskar kano gani take kamar daga kurkuku tafito



Adaidaita ta tara suka dau hanyar gidansu sai kalle kalle take kamar wata bak'auyiya


Tun kafin su k'arasa k'ofar gida tafara k'ok'arin sauka daga adaidaita sahun sabida murna gani take kamar ta shekara rabonta da gida

Mai adaidaita sahun
Bai gama tsayawa ba ta duro daga adaidaita sahun ta cilla mishi kud'insa ta shige gidansu da gudu tana kwad'awa Inna wuro kira


Inna wuro dake kwance ba lafiya sakamakon jininta da ya hau tun lokacin da su Fateema suka tafi da sati d'aya wani yasamu Baffa ya gaya mishi Lado d'an karya ne babu wani saudiya da ya kai Fateema k'auye ya kaita tun daga lokacin jinin wuro ya hau sakamakon yawan tunani da take yi tun tana rashin Lafiya

Please Login or Register in order to submit comment