Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda ya faru dashi,ya kuma had'ashi da Fateema, Sa'eed a lokacin murmushi yayi yace masa banda abunsa ai ba sai ya sha wahalar Neman matar aure ba,ya manta kanwarsa Haleema ai shima shaida ne akan irin tarbiyar gidansu,Bashir kuwa sai a lokacin ya tuna sa'eed na da kanwa Haleema,yarinya mai hankali,da tarbiya,uwa uba ga kunya kyau kam ba laifi tana dashi dai dai gwargwado,hasken fata kawai Fateema zata nuna mata,ai cikin kankanin lokaci Bashir ya tura manyansa gidansu Sa'eed Dan sun fahimci juna shi da Haleema da dukkan alamu zata rik'e mishi yayansa bisa amana,sati uku aka sa rana,inda Bashir yace su bar mishi komai a hanunsa shi zai yi,karsu wahalar da kansu,Dan suma basu da wani k'arfi wanan kenan.




Sai Kun jini jibi sakamakon mid term exams da zamu fara gobe,idan kuma nasamu sarari gobe zakujini insha Allahu
*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*




*THANKS ALOT MAH WELL WISHERS MAY ALLAH BLESSING BE WITH OLL OF YOU*🙏🙏🙏


*WANAN SHAFIN NAKUNE MASOYANA NA HAK'IK'A WLH BAN HAD'A SANKU DA KOWA BA,UMMIE (momyn Shukra waleeda and sadeeq) MARIYA BABA(Marubuciyar Rayuwar Mufeeda) INA MIK'A SAK'ON GAISUWATA GAREKU ALLAH YA BARMU TARE*❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤



Page 55-60



Fateema tunda ta gama cin awara ta gyara zamanta sosai taringa kallon titi,mamaki fal cikinta,tambayoyi take San yiwa Lado,amma babu Fuska,hankalinta ne ya fara tashi da taga sun bar kan kwalta sun yanki wani kwana suna ta tafiya,,gonaki ne da gidajen kasa suke ta wucewa, babu ko alamar gidan bulo, gabanta yankewa yayi ya fad'i Dan wani tunani ne ya darsu a ranta na ko dai Yankata lado zaije yayi,d'aurewa tayi tace " Lado wai ina zamuje ne, ina zaka kaini,ba saudiya kace min zamu tafi yau da safe ba,mai ya had'amu kuma da kauye,"? Ai tamkar da dutse take magana,Dan Lado ko motsi bai yi ba,ballantana ya juya ya kalli direction d'in da take,ai Fateema tana ganin haka ta fashe da kuka tana ta Shiga uku ta lalace,kuka take sosai,har ta janyo hankalin passengers d'in dake cikin mota,suka hau tambayarta mai ya faru take kuka,Lado wani mugun tsawa ya daka mata tayi sauri taja bakinta tayi shiru,ahaka suka yi tafiya mai Nisan gaske, Fateema duk tabi ta gaji,duwawunta sai Zafi yake,sadak'arwa tayi Lado d'an yankan kai ne,siyar da ita yayi zai kai ta ayanka,dabara ce ta fad'o mata na ta ringa tofa mishi adduoi watak'ila Allah yasa yaji tausayinta ya fasa siyar da ita,adduoi ta farayi taringa tofa mishi miyau d'in bakinta mai kauri,Lado da ya d'auka abun wasa ne, yaga dai dagaske tana sane take tofa mishi yawu,juyawa yayi fuska a had'e ya kalleta,ita kuwa tayi Sauri ta mayar da yawun da take shirin tofa masa,ta kau da kanta ta cigaba da adduoi azuciyarta,sai da passengers d'in motar suka sauk'a gabad'aya kafin suma su sauka,Fateema ware ido tayi sosai tana kallon kauyen,tunda take bata tab'a zuwa kauye irin wanan ba,babu abinda kake gani a kauyen kamar guntattakin gidaje,sai kara da dake zube ako ina,Lado ana saukesu ya hau tafiya,Fateema da sauri tabar kalle kallen da take tabi bayansa aguje Dan ya d'an yi mata nisa,tana tad'oshi ta kamo rigarshi ta baya tana "Lado nifa bangane ba,ina zaka kaini wai,?ina Saudiyar,? Mai Muke nema awanan mugun kauyen da babu gidan bulo ko d'aya sai gidajen kasa," Lado doke hanunta yayi,yace " inkin ga dama ki biyoni in baki ga dama ba,ki cigaba da tsayuwa kina kalle kalle" lado yace yana cigaba da tafiya

Fateema kuka ta fashe dashi tabi bayansa a guje,ahaka suka ringa tafiya tana kuka tana kalle kalle,sai da suka samu minti 30 suna tafiya kafin,Taga Lado ya nufi wani gida dayafi kowane gida kyau a kauyen,Dan ginin bulo ne har da fenti,dan k'ara sauri tayi ta tado shi,suka shiga gidan a tare,sallama Lado yayi,yara suka fara fitowa da gudu gudu suna ga baba ga baba oyoyo oyoyo", Fateema nanata sunan da suka kira Lado dashi tayi,ta saki baki tana kallon ikon Allah,matansa ne suka fara fitowa daga d'akunansu suma fuskarsu d'auke da farinciki,biyu da goyo d'ayar kuma da ciki,Lado yaron daya d'auka ya ajiye,yana amsa sannu da zuwan da matan suka mish,ya juya ya kalli Fateema da ta saki baki tamkar sokuwa tana kallonsu,"ke kishigo mana tsayuwar mai kike yi anan"?Lado yace fuskarsa a d'aure, matansa atare suka juya lokaci guda suka kalli inda Fateema take tsaye,Dan Sam basu ma lura da ita ba,yanayin shigar ta da k'unshi hanunta kawai suka gani,suka gane sabuwar amarya Lado yayi, Ainau da itace amarya farinciki ne ya lullub'eta ta nufi wajen Fateema,Dan dama tana Neman wacce itama zata had'a kai da ita, Dan uwargidan Lado zainab da Maimuna sun had'e mata kai,
Hanun ta kai zata ruk'o hanun Fateema,Fateema ta janye hanunta da sauri,tabi cikinta mai tsini da kallo,ta dawo da kallonta fuskarta,murmushi Ainau tayi tace " ki shigo mana kika tsaya daga nan" wani mugun harara Fateema ta mata tace "ke kuma daga ina zaki wani ce na shigo bazan shigo d'in ba Dalla matsa daga gabana da wani jibgegen cikinki"dariya su zainab suka kwashe dashi Dan sunji dad'in abinda Fateema tayiwa Ainau,Fateema wajen Lado ta nufa fuska a d'aure ta kama kug'u tana " Lado wai uban me muke yi anan ne,?suwaye wanan,?gidan uban waye wanan? Lado murmushi yayi ya mik'e tsaye ya kalleta sama da kasa yace "uban aure ne ya kawo ki nan,wayanan kuma matana ne,ga uwargida zainab,ga mabiyinta nan,maimuna,ga ta uku nan Ainau,ga ki kuma cikon ta hud'u kuma amarya,ga yarana nan,uwargida tana da biyar,Mabiyinta nada hud'u,Ainau kuma tana d'auke da Cikin ta goma idan Allah ya sauketa lafiya,nan kuma gidana ne", Fateema tunda ya fara magana k'irjinta ke dukan goma goma,Marin kanta tayi Dan ta tabbatar da ba mafarki take ba,zafin Marin da ta kaiwa kanta ne yasa ta gasgata ba mafarki take ba,wani mugun ihu tayi ta cakumi wuyan rigar Lado tana "idan ka isa Allah ya tsinemin,wlh sai ka sakeni,Dan kutumar ubanka dama kai dan k'arya ne bansani ba saudiyar da kace zaka kaini kenan?ina lefen dakamin? Kace min Kai Dan siyasa ne? Kacemin matarka ta rasu,? Kan uba wlh baka isa ba sai ka sakeni shege tsi"wani bahagon mari Lado ya d'auketa dashi,ya jera mata wasu tagwayen marin dayasa kunnuwanta suka daina jin komai,zainab ce taje da sauri ta rik'e mishi hannu da taga yana shirin k'ara mata wani," haba mai gida a ina ka tab'a jin ranar da amarya ta tare ana dukanta,haba mai gida bai kamata ka daketa ba gaskiya,ai da sai ka k'yalleta tunda ita mace ce"

Lado fusge hanunsa yayi yace"wanan yarinya da kike gani wlh bata da kunya Sam,bata da tarbiyya,bata da mutunci Sam,sai na koya mata hankali,na saita ta zamu zauna lafiya,zainab,maimuna,Ainau ga Fateema nan itace wacce na aura,inaso kafin na tashi daga barci,Ku gaya mata komai na gidanan,da tsarin gidanan,Dan ayau nakeso ta k'arbi girki,tunda dama wacce take da kwana itace zata yi girki,kuma ba buduruwa bace da za'ace sai anyi mata girki,kafin ta k'arba"daga haka Lado ya nufi wani b'angare dake can Dan nesa da alama nan ne b'angarensa,Fateema da a k'arshen maganarsa,kunnuwanta suka dawo dai dai,ta ji mai yace,mik'ewa tayi daga zaman borin da tayi ta fashe da kuka tafara tsalle tana "amma Lado Allah sai ya tsine maka albarka,Allah ya tsine maka dai dai gwargwado,bazaka gama da duniya lafiya ba,wlh sai na bar gidanan,wlh sai ka bani takardata ko ta tsiya ko ta k'arfi" Lado wani irin juyi yayi,taku d'aya ne ya kaishi inda take tsaye,ya rufeta da duka kamar an aikoshi,sai da su zainab suka had'a hannu suna jansa kafin ya cikata,ya nufi d'akinsa ya d'auko wata murtukekiyar dorina,har a lokacin bakin Fateema bai mutu ba zaginsa kawai take tana tsine masa,ganinsa da tayi da dorina ne yasa tayi sauri ta rufe bakinta,


Lado nunata yayi dorinar yace "maza maimaita abinda kikace yanzu,maimaita ina jinki" Fateema gwalo ido tayi tana kallon dorinar cike da fad'uwar gaba,jikinta sai rawa yake,"k'aramar 'yar iska kawai ai da kin maimaita abinda kikace,ai tunda kika nunamin bakida mutunci wlh dakaina zan fad'a miki dokar gidana,da tsare tsarensa kuma ya zama dole kibi wlh ko kici ubanki,Dan abokanan zamanki ma da haka suka saba,ke kina jina," Lado yace yana nuna Fateema da dorinar,da sauri Fateema ta girgiza kanta "yauwa yanzu haka lokacin girkin rana yayi,ki tashi ki had'a itace ki d'ora ruwa,kizo ki barza gero,inkin gama,ki tsince wake,Dan yau dayake talata ne da rana,wake da gero muke ci,sai ki daka kuli kuli muci dashi,daddare kuma ki barza dawa akai mana nika,ki tuka mana tuwo da miyar karkashi,gobe kuma da safe shi zaki dumama mana muci,da koko,da rana kuma kiyi mana dambu,daddare kuma kiyi mana tuwon gero,da miyar kuka, ranar Alhamis da safe zaki soya mana dankali 'yar Hausa da shayi bunu,da rana kuma kimana faten tsaki,daddare kuma kiyi mana tuwon massara, inaga aranar zaki fita daga girki,amma bari na fad'a miki sauran ranakun abinda ake dafawa,ran jumma dasafe kosai muke yi da koko,da rana kuma muci taliya 'yar Hausa da mai da yaji,daddare kuma muci rogo da kulli,ranar asabar kuma muke shan shayi da bredi,da rana adafa mana dambun massara,daddare ayi mana tuwon massara,ranar Lahadi,da safe dumame muke ci,da rana ayi shinkafa da wake da mai da yaji,daddare ayi tuwon shinkafa da miyar taushse,atakaice sau d'aya muke dafa shinkafa asati,kowane rana muna da nauin girkin da mukeyi,kwana uku uku kowace takeyi inta k'arbi girki,ko ina gari ko bana gari,sanan kan yarana a had'e suke Dan haka kullum da safe kowace tana yiwa yarana wanki,dan bana San kazanta,sanan sharar tsakar gida safe da yamma, sanan idan ina gari duk wacce take da girki,tana bani hakkina sau uku arana, ya dai danganta da yanda naji inada bukata,in a koshe nake zai iya fin sau uku," zainab Ku gaya mata sauran ,zan shiga daga ciki idan tayi gardamar yin wani Abu kuzo Ku fad'amin,anjima ina tashi daga barci,zan kira azo a gyara mata wancan d'akin, a d'auko wanan k'aramar katifar asa mata,maimuna da yamma ki rakata wajen dilalliya ta zabi gwanjuna da kuncen kayan da take siyarwa Dan bata da kaya Dana jikinta kawai tazo" daga haka Lado ya mik'e ya nufi b'angarensa,


Fateema sabida tsabar tashin hankali,da firgita da tayi da maganganun Lado kwanciya tayi akasa flat,ta d'ora hannu aka tana "wayyo Allahna wayyo rayuwa,wlh ban iya surfe ba,wlh ban tab'a yi ba,innalillahi wa innailahi rajiun yanzu duk yawan gidanan ni zan ringa girki,girkin ma bana arziki ba,har da su gero da wake,wayyo Allahna wayyo ni Fateema na tonawa kaina Asiri,Bashir ka zo ka taimaki uwar yayanka zan mutu,Baffa,Inna wuro,kudaina murna na tafi saudiya,wlh kauye aka kawoni,Wayyo Aliyu,Hameeda,Sumayya.Nura kuzo Ku ceci uwarku,Allah sarki Bashir bawan Allah ashe Kai mai kud'ine bansani ba,Ashe kai dan aljana ne,duk rashin mutuncin da nake maka nake zaginka baka tab'a d'aga ido ka kalleni ba,sau d'aya ka tab'a dukana,a gidanka abinda raina yakeso nake yi,shinkafar ma munaci da miya,amma kuwa nan sau d'aya asati,sai yanda aka dani,kaicona wayyo ni,Bashir hakinka ke bibiyata,kasha fad'amin inringa godewa Allah a matsayin daya ajiyeni,idan ban godewa niimarsa ba ,wataran zan godewa Azabarsa,aikuwa gashi banga komai ba tukuna,wayyo Bashir,danasani ranar dakazo na bika,wayyo Bashir,ka sha fad'amin *Y🅰TSUN H🅰NUN MU ba d'aya bane* inka fi wani wani yafika Ashe da gaskiyarka yau naga Wanda kafi nesa ba kusa ba" duk magangunan da take Lado yana daga d'aki yana jiyota,mik'ewa yayi a fusace yafita waje, ya d'aka mata tsawa yana "dalla Mallama tashi ki d'ora mana girkin rana kina b'ata mana lokaci," Fateema cikin tsananin rawar jiki ta mik'e a dirirce tana ina murhun,dariya su zainab suka kyalkyale dashi,banda Ainau dake tayata kuka sabida tsananin tausayinta,Dan itama hauka ne kawai batayi ba ranar da lado ya kawo ta gidan,dan ita cewa yayi London zai kaita,maimuna ganin Lado ya shige d'aki yasa ta matsa kusa da Fateema tace "duk wanda ya hau motar kwad'ayi a tashar wulak'anci yake saukeshi kad'an kikagani sai ma gobe," ta juya suka tafa da Zainab suka nufi d'aki,Fateema kuka ta k'ara fashewa dashi, Ainau ta kamo hanunta tana rarrashinta atakaice Ainau ce ta taimaka mata suka surfa geron suka d'ora abincin rana,Fateema sai kuka take kamar ranta zai fita, suna nan azaune,Ainau nata rarrashinta,Lado ya fito daga d'akinsa daga shi sai gajeren wando ya tsaya daga bakin k'ofa yana hamma da mik'a,Fateema d'auke kanta tayi Dan ta tsani ta bud'e ido taganshi bata tab'a sanin haka yake da muni ba sai Yanzu,hannu ya d'aga yafara yafito Fateema,Ainau kuwa cikin tsananin tausayawa tacewa Fateema taje Lado na kiranta Dan ta Riga da tasan kiran dayake mata,Fateema k'ara d'auke kanta tayi tacewa Ainau "ni mai zan je inyi mishi",

Ainau murmushin k'arfin hali tayi tace "hak'uri zakiyi kije inkika ga yana haka hakkinsa zaki bashi"

"Kutumar uba wanan wane irin akunyanci ne bangane hakkinsa zan bashi ba,wayyo Allahna wanan wane irin masifa ne dawane zanji,awara hamsin ne fa kawai a cikina tayaya zan bashi hakkinsa"



Ainau ganin Bashir ya nufo inda suke yasa ta mik'e da sauri tana "wlh kije idan bahaka ba kika bari ya sameki anan,wlh mugunta zai miki keda fitowa daga d'akinsa sai hud'u" daga haka Ainau ta nufi d'akinta da sauri, Fateema mik'ewa tayi tace "inka isa Allah ya tsine min,wanan wane irin tumasanci ne,sai kace d'an akuya,naci awarar Hamsin kazo wani godai godai dakai babu kunya babu tsoron Allah kace in baka hakkinka wlh baka isa ba"


Bashir gadan gadan ya nufi kanta yace "zan kuwa kwata ta k'arfi,zagaya tsakar gidan suka farayi suna guje guje,Fateema sai ihu take yi.
*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*


*DEDICATED TO FATTY AZLAND*


🎂🎂🎂🎂🎂🍪

APPIE BUFF DAY AZLAND

_May this day bring countless happiness and endless joy and live with peace and serenity_

🎂 🎂 🎂 🎂 🎂

_Age doesn't matter unless you are a cheese_

🎂 🎂 🎂 🎂 🎂

_Age is what ever you think it is so you are as old as you think you are_

🎂 🎂 🎂 🎂 🎂

_statistics show that the more you live the more you have_

_Birthdays are good for you! 💗 💗 May God bring light and happiness to your entire life_

*keep calm and celebrate your day*

*Happy birthday 🎂 🎂 🎂 🎂 🎂 🎂 🎂*

*MRS LAMEEDO*



Page 60-65





Ihu Fateema taringa yi sosai suna zagaye tsakar gidan

Lado ganin tana Neman ta Tara mishi jammaa ne yasa ya daka mata tsawa


Fateema kuwa ta tsaya agigice taku biyu yayi ya damko hanunta

Aikuwa kokawa suka farayi sosai Fateema ta ringa kai mishi cizo da yak'ushi tana

"Wlh bazan yarda ba wanan wane irin masifa ne jamma'a kuzo Ku taimakeni Lado zai kasheni"


Lado cak ya d'auketa yayi hanyar d'akinsa da ita yana "wlh yau zaki yabawa Aya zak'inta"


Wurgar da ita yayi akan gado Fateema ta mik'e da sauri tana Neman guduwa atak'aice k'arfi da yaji Lado ya k'arbi hakkinsa cike da mugunta dan ba wai dadi yaji ba illa ma gajiya daya Tarawa kansa,Dan kokawa suka ringa yi da Fateema shi kuwa ya ringa kai wa d'uwawunta duka


Fateema kuwa sabida tsabar azaba da wahala da tasha a hanun Lado kasa k'wak'waran motsi tayi sai hawaye ke zubo mata atake ta tuna Bashir bawan Allah da in zai karb'i hakk'insa ta ruwan sanyi yake bi da ita yayi ta lallab'ata


Amma sai Gashi Lado ta k'arfi da yaji ya k'arb'i hakk'insa har dasu dukan d'uwawu,babu ma d'an aike ahaka ya afka mata kamar wani dabba ga warin baki da na hammata


Share hawayenta tayi ta mik'e dak'yar ta jawo zaninta tana k'ok'arin d'aurawa

Lado wani mugun kallo ya mata yace "ke kuma da kika mik'e ina zaki"?



Fateema hawaye mai zafine ya zubo mata tace cikin rawar murya "zanje na duba girkin dana dorane"


"Koma ki kwanta Dan ban koshi ba su Ainau zasu duba girkin"

Lado yace fuska a d'aure

Kuka Fateema ta fashe dashi cikin tashin hankali tace

"Lado bangane baka koshi ba abinci ce ni da zaka ci ka koshi wanan wane irin jarraba ne Lado tun safe awaran hamsin ce aciki na banci abinci kirki ba sai durzata kake yi kamar kayan wanki Lado Haba lado baka da tausayi ne"?


Fateema tace tana k'ara fashewa da kuka mai cin rai

Dariya Lado ya k'yalk'yale dashi yace

"Mai abun tausayi kuma Fateema ak'arbar hakk'ina lokacin da kika ringa amsar dubu goma goma a hanuna ke kina tausayina ne? Sai yanzu Dan zan fanshe kud'ina zaki wani cemin bana tausayinki awara ba abinci bane?ke kin ma ci awarar Hamsin wata ma bata samu na hamsin d'in ba"


Fateema Hannu ta d'ora aka tana "Nashiga uku na lalace na janyo wa kaina masifa da balai Lado kayi min rai wlh bazan iya jurewa ba zaka kasheni"

Lado wani dariyar yak'ara k'yalk'yalewa dashi yace

"Ko da yake jeki ki gama girkin ki dawo in kinci abinci watak'ila kya fi bani had'in kai sosai kuma wlh kika k'ara yunkurin k'ok'awa dani Dan zan k'arbi hakkina wlh sai na miki duka Dan dubu d'ari na bayar sadaki"


Ai fateema cikin kiftawar ido ta wuntsula daga kan gadon tayi waje da gudu a k'ofar d'akinsa ta k'arasa d'aura zani tana tsinewa Lado a zuciyarta


Ainau ta hango a gindin murhun da turtsetsen cikinta tana raba abincin kamshi man kulli kuwa ya cika gidan
Take taji cikinta na k'ara kukan yunwa da d'an saurinta ta k'arasa gindin murhun Ainau ta d'ago ta kalleta tana mata sannu"


Fateema akan Ainau ta huce Dan masifa ta rufe Ainau dashi tana "Sanun me kike min ciwo nake yi da zaki wani cemin sannu"

Ainau rik'e baki tayi cikin mamaki tace

"Allah ya baki hak'uri naga kinsha aiki ne shiyasa na miki sannu"

"Aikin uban me nayi da zaki min sannu"

Ainau ganin da tayi Fateema ba mutunci gareta ba yasa bata tanka mata ba ta cigaba da raba abincin Dan dama taga yara sun fara kukan yunwa kuma Fateema bata fito ba shiyasa ta fito Dan ta taya Fateema zuba abincin

Ainau yaran ta fara kira d'aya bayan d'aya suka ringa zuwa suna d'aukar abincinsu ko kallon inda Fateema take bata k'ara yi ba

Abincin data zuba afaranti mai d'an yawa ta d'auka ta mik'e dak'yar Dan cikinta ya tsufa haihuwar yau ko gobe

Fateema ganin Ainau zata tafi bata ce ga abincinta ba yasa tayi sauri tasha gabanta tana
"Ni baki bani
abincina ba naga zaki tafi"

Murmushi Ainau tayi tace "ga naki can da maigida had'a muku nayi ki kai muku can d'akinsa Dan wacce take da girki tare suke ci da mai gida"

Ashar Fateema ta luk'a tace "da uban mai gida kika had'a mana haka kawai Dan rashin mutunci bazaki zuba min abincina daban ba sai kin had'a mana da d'an bunsurun mijinku wlh bazai yiwu ba"


Ainau wani mamakin Fateema ne ya k'ara rufeta ta gasgata maganar Lado dayace Fateema bata da mutunci bata da tarbiyya dole sai ya gyara mata zama aikuwa tunda abun hakane dole ta fita daga hark'ar Fateema


Ainau bata ce komai ba ta ratsa ta gefenta ta tana "ke kika sani nidai na fita hakkinki"


Fateema tsaki tayi ta k'ara dura mata wani ashar d'in ta janyo kular ta zuba abincin awani kwanu dake ajiye ta fara ci Dan yunwa take ji sosai

Sai da Fateema ta kusa cinye abincin tas dan sabida yunwar da takeji tunani tayi shinkafa tasamu take ci ba gero da wake ba

Sai da taci ta koshi ta ture kwanun daga gabanta ta Koma can inuwa ta zauna Dan dama abakin murhun ta zauna taci abincin.


Tunani ta fara yi na yanda zata gudu daga gidan Dan agaskiya bazata iya zama da Lado awanan k'auyen ba Bashir ne ya fad'o mata arai da yaranta take ta fashe da kuka


Su zainab suna daga d'aki suna jiyo kukanta sai dariya suke suna shewa Ainau ce kawai bata sa musu baki a shakiyancin da sukewa Fateema ba Dan maimuna sabida bak'in hali har wankakkun kayan yaranta ta had'a akayan wanki Dan Fateema ta wanke




Lado kuwa da Fateema tabar d'akin barci ne yayi awon gaba dashi

Fateema ganin tana ta zaune har k'arfe uku batayi wanka ballantana akai da tayi sallah ne yasa ta mik'e ta fara dube duben inda zata ga band'aki acan wani lungu ta hango band'akin ta nufi band'akin ta d'auko bokiti tazo tana duba inda zata samu ruwa,manyan bokitai masu murfi tagani agefe guda uku ta nufi wajen Dan ta d'ebi ruwa tana bud'e bokiti guda d'aya zainab uwargidan Lado ta lek'o da sauri tana "aaa karki sake ki d'ibar min ruwa inkina bukatar kiyi wanka kije ki ja ruwa arijiya"

Fateema ganin zainab ta fita masifa ne yasa ta rufe bokitin ta bud'e na tsakiyar aikuwa ko gama bud'ewa bata yi ba Maimuna ta fito tana "kul kika tab'a min ruwa kinje kin gama shan dad'inki zaki wani zo ki d'iba min ruwa ina maza rufemin kije kija ruwanki kuma bokitin hanunki ma ki ajiyemin nawa ne"


Zuwa wanan lokacin ran Fateema ya b'aci a masifance tace "banza kawai dad'in ubanki na sha kaddara ce tasa na auri wanan bunsurun mijin naku mai warin k'ashi da d'oyin hammata wai ke nan kishi kike yi akansa ki kwantar da hankalinki ni ba sanshi nake yi ba hasali ma babu wanda na tsana sama dashi naso ace kinsan mijina uban y'ay'ana sai kinsan wanan jakin da kike kishi akansa ba mutum bane"


Maimuna itama a hasale ta nufi wajen Fateema ta fusge bokitin daga hanun Fateema tana "eeee naji idan jaki nake kishi akansa ai kema jaka ce tunda kika aureshi sabida kwad'ayin abun duniya babu wani kaddara dayasa kika aureshi San zuciya ne yasa kika aureshi watak'ila ma kika rabu da uban yaranki sabida shi ai wlh tunda kika nuna min bakida mutunci bazan raga miki ba agidanan rashin mutunci zan ringa miki kala kala banza akuya"


Fateema sabida tsabar takaice data rasa mai zatace durk'ushewa tayi ta fashe da kuka Maimuna tayi tsaki tabar gurin


Ainau sarkin tausayi ji tayi tausayin Fateema ya rufeta ta mik'e da turtsetsen cikinta ta nufi wajen Fateema

Su zainab zagin Ainau suka fara yi suna ta fiye shishigi ita kuwa ko kulasu bata yi ba


Ta d'aga Fateema tana rarrrashinta hanun Fateema ta rik'e ta kai ta band'akin ta d'auko
Bokitin wankanta daga d'aki tazo ta zuba ruwa ta kinkimi bokitin da k'yar ta kai wa Fateema band'aki ta Koma ta d'auki sabulun wanka da soso ta kai mata har a lokacin Fateema kuka take

Ainau hak'uri ta bata da ta d'aina kukan haka tayi wanka tafito tayi sallar


Dak'yar Fateema tsayar da kukan da take tayi wankan tsarki dana sabulu ta fito a tsakar gida ta tarar da Ainau a tsaye da buta ahannu,mik'a mata butan Ainau tayi


Fateema ta k'arba tana mata godiya alwala tayi Ainau tace ta biyota d'akinta


Sallaya Ainau ta shimfid'a mata ta d'auko mata wani doguwar rigata da hijabi ta bata Dan tayi sallah

Godiya Fateema ta k'ara yi mata tasa Riga da hijabin ta tada salla sai da tayi azahar kafin tayi la'asar Dan lokacin sallar la'asar yayi


Fateema rabon da ta ja carbi har ta manta sai gashi sabida masifar da take ciki ta d'auki carbi tana ja ta Dade tana adduar Allah ya kawo k'arshen zamanta a gidan Lado har Bashir dasu Nura tayiwa Addua

Tana shafawa ta juya ta kalli Ainau ta k'ara yi mata godiya Ainau tace babu komai an zama d'aya


A d'akin Ainau ta zauna ta zuba tagumi babu wanda ya k'ara magana acikinsu


Ainau ganin shirun yayi yawa yasa tace "ni kuwa in baki shawara mana idan bazaki damu ba"


Hawaye Fateema ta goge tace "ina jinki"


"Nace mai zai hana ki kwantar da hankalinki kisama wa kanki zaman Lafiya Dan idan kikace zakina d'agawa kanki hankali wlh ke zaki sha wuya Dan daga mai gida har matan nasa ba raga miki

Please Login or Register in order to submit comment