Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tab'aki shine bakyaso,sanki fa nakeyi kuma aurenki zanyi" Fateema saura kiris ta hankad'ashi amma tana tuna zai mata shopping ta fasa hankad'ashin.
*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*




*IN DEDICATION TO ALL MEMBERS OF SECRET BEHIND EVERY WOMAN GROUP, ONE LURV*
💞


*JINJINAN BAN GIRMA GAREKU MASOYAN YATSUNMU BA d'aya BANE BAN MANTA DAKE BA AYSHA ABBAS YAR ADUAR,FADEELA Y KHAN MEELA ADEEL*


*TWINEEY I WISH YOU BEST LUCK IN YOUR UP COMING EXAMS*


*AZLAND TAWAN ALLAH YA MAIDA MUKU ABINDA YAFI ALHERI YA TONA MUSU ASIRI ALFARMAR ANNABI MUHAMMAD SALLALAHU ALAIHI WA SALAM*




PAGE- 45-50



Fateema ganin da tayi yafara shasha fata yana wani shin shinata ne yasa ta hankad'ashi tana "AAA mai haka kafa fara wuce gona da iri,wanan wane irin Abu ne inka San ka matsu dani haka ka turo gidanmu mana muyi auren ka huta"


Lado kuwa D'an rungume tan da yayi hankalinsa ba k'aramin tashi yayi ba,da sauri yace "aikuwa zan turo manya na gidanku asa mana rana sati biyu Dan gaskiya idan ina ganinki haka komai zai iya faruwa"


Fateema kau da kanta tayi zuciyarta fal da farinciki zata auri d'an siyasa nan da sati biyu,hararo kanta ta fara yi a hakimce abayan mota taje gidan Bashir ganin 'yay'anta daga nan kuma ta fito ta shiga gidan khadija ta mata rashin mutunci ta fito,wani murmushi ta k'ara saki adai dai lokacin da ta k'ara jin Hanun Lado akan cinyarta,juyowa tayi ta cire hanunsa daga cinyarta tana "to daina tab'ani haka ka bari lokaci yayi"


Lado murmushi yayi aransa yana tunanin idan ba auren Fateema yayi ba, ba zai samu abinda yakeso ba,kud'i ya Ciro daga aljihunsa ya k'irga dubu goma kamar yanda ya saba bata, Fateema ansar kud'in tayi tana "mun fasa zuwa shopping d'in ne"?


Lado cewa yayi " ee ki bari gobe sai muje yanzu naga dare yayi"


Fateema bud'e motar tayi tace mishi to "shikenan ka gaida gida sai goben" ta fito daga motar tana d'aga mishi hannu,sai da ta daina hango shi ta shige cikin gidan tana k'irga kud'in da ya bata,Inna Wuro dake hira da Baffa hango Fateema da tayi tana k'irga Kud'ine yasa ta mik'e da sauri ta nufi wajen Fateema,Fateema cusa kud'in tayi a breziyarta ta had'e rai tana "Inna wlh gwara ki koma bazan baki ko sisi ba,Dan ni yanzu Tara kud'i nake yi aure na ya kusa"


Inna wuro langab'ar da kanta tayi tana " haba tawan ko d'ari biyar ne ki bani mana," Fateema girgiza mata kai tayi tana ita bazata iya ba wlh yanzu haka ma indomie da kwai zata siyo tazo ta dafa ita bazata iya cin tuwo ba,daga haka ta nufi d'aki ta cire kayan jikinta tasa tsofaffi ta fito tayi hanyar waje Dan ta siyo Indomie da kwai,Inna wuro da Ashar ta bita har ta fice tana taga alama idan ma tayi auren bazata ringa kawo mata arziki ba.




B'angaren Bashir kuwa 'yan uwa da abokanan arzik'i sako shi suka yi agaba da zancen aure,dan kanensa har sintirin zuwa suke gidansa akan ya kamata yayi aure ya samu mai kula da yaran,Dan Hameeda bata yi hankalin da zata iya kula da kanenta ba, kuma amatsayin dayake ayanzu ya kamata ace yana da mata,Bashir kuwa duk ce musu yake yana nan ya na Neman macen da zata iya kula da yaransa ba wacce zata zo ta gallazawa yaransa ba,aikuwa hakan da suka ji ne yasa suka fara mishi talan zuka zukan 'yan matan Wanda yasan da a lokacin da yake siyarda robobine babu Wacce zata kulashi, sai gashi babu kunya babu tsoron Allah, sabida San kud'i su suke biyoshi har gida,shawara ya yanke zai gwada fateema yaga ko zata dawo gidansa,idan ya gwada ta yaga batayi hankali ba tana nan da San kud'inta zai hak'ura da ita ya nemi matar aure,Dan agaskiya yana tsoron ya auro macen da zata zo ta ringa gallazawa y'ay'ansa gwara Fateema ta dawo ta rik'e y'ay'anta kuma zai so ace tazo taci arziki yanzu tunda in zai yi adalci bai kamata Dan ya samu kud'i yaje yayi wani auren ba kamata yayi ya dawo da ita tunda ba laifi sun kwashi shekaru suna cikin talauci kafin ta zuciya ta tafi gidansu,da wanan tunanin Bashir ya samo tsofaffin kayansa da suka yage suka kod'e Dan ajiyesu yayi Dan tarihi,ya ajiye da zumar ran lahadi da baya shiga kasuwa yasa yaje gidansu fateema.


Lado kuwa tunda ya bar gidansu Fateema yafara tunanin hanyar da zai bi ya samu kud'i ya aureta Dan ya kamu da matsanacin sha'awarta,ya kuma ga alama bazata yarda taba shi had'in kai ya samu abinda yakeso kafin suyi aure ba,dabara ce ta fad'o mishi ya nufi wajen maigidansa Alhaji zubairu,yana zuwa ya zube agabansa yafara kuka,Alhaji zubairu hankalinsa ba k'aramin tashi yayi ba ya hau tambayarshi mai ya faru,Lado karkata kai yayi yafara sharara masa karya akan mahaifiyarsa zaayi wa operation a ido ,ana bukatar kud'i wajen dubu d'ari biyu gashi bashi da ko sisi Alhaji zubairu ya taimaka mishi,Alhaji zubairu mamaki ne ya rufeshi dayaji abinda yace Dan kwana hud'u kenan da yazo ya sameshi akan mahaifinsa yana can yana fama da ciwon siga an rubuta mishi magungunan dubu sabain bashi da kud'in da zai siya,dubu d'ari ya d'auka ya bashi alokacin nan kuwa da kud'in ya ringa zuwa yana yiwa Fateema karya,Alhaji zubairu mai da mamakin da yake yi yayi Dan yana tunanin watak'ila dagaske Lado yake,dubu d'ari uku Alhaji zubairu ya d'auko ya bashi yace Allah ya sauwake ya bada lafiya,zai yi tafiya ne da yaje ya dubo mahaifiyar tasa,Lado kiris ya rage yayi wa Alhaji zubairu sujada da yafara mishi godiya,cikin tsananin farinciki ya bar gidan Alhaji zubairu, ya nufi wajen tsofaffin banzan da basu da aikin yi sai dai ayi hayansu,bayani ya musu na abinda ke tafe dashi,suka ce mishi ba komai ai sun Riga da sun saba yi mishi aiki,ce musu yayi yana so ran lahadi su kai mishi dubu d'ari gidansu Fateema, su nema mishi aurenta zai samo hayan akwatuna da kaya su tafi dashi suce musu nan da sati biyu suke so ad'aura auren,atakaice cikin kwana biyu lado ya samu hayan duk wani Abu dayake bukatar na aure banda dubu d'arin da shine kawai nasa.




B'angaren Fateema kuwa tunda lado ya kirata yace manyansa zasu zo ran lahadi ta rasa inda Zata sa ranta Dan dadi,har rawa Inna wuro tayi tace burinsu ya cika zata auri mai kud'i,Fateema kuwa cewa tayi da yanzu fa tana can gidan mistsiyaci Bashir tana fama da 'yar Hausa yanzu ne tasan zata yi aure, ita bama zata je wajen y'ay'anta ba sai tayi aure,taje a motarta Dan Bashir yasan tafi k'arfinshi ita matar mai kud'ice.




Ran asabar tana zaune a motar lado suna hira Lado yace mata,kayan lefen da zaa kawo mata gobe tsadaddun kaya ne babu kayan kasa da dubu hamsin,karta kaiwa kowane tela ta bari sai sunyi aure sun tafi saudiya sai ta bayar acan ayi mata Dan can sunfi iya dinki,akwai guda biyu dinkakku aciki shi kawai zata sa,sanan kuma karsu wahalar da kansu wajen yin kayan d'aki Dan ba anan zasu zauna,duk da gobe zai kai ta taga gidan da zata zauna indai suka zo Nigeria,sanan akwai motoci uku da zai mallaka mata,zai bud'e mata shago,Fateema sabida tsabar farinciki rungume lado tayi taringa mishi godiya,lado kuwa sai dariyar mugunta yake mata Dan kauyensu zai kai ta inda matansa suke da yayansa,ahaka Lado ya cigaba da cikata da karya har sukayi sallama ya tafi.


Aranar Fateema kasa barci tayi ita da Inna wuro sai zayyano wayanda zasu yiwa wulak'anci suke idan anyi auren.




Washegari kuwa k'arfe biyu na rana tsofaffi nan suka sako manyan riguna da Lado ya hayo musu,suke je a katon katon jeep guda biyu,jiki na rawa Baffa ya musu iso har tsakar gidan da suka shimfid'a katuwar tabarma,suka zauna suna wani yatsuna fuska,suna kalle kalle,d'ayan cikinsu dayafi dukansu rama sabida yunwa cewa yayi"ooo yanzu kuma nan gidan kuma lado yazo neman aure," d'ayan shima yamutsa fuska yayi yana "To Alhaji mamman ya zamuyi tunda ya dage 'yar mitsiyata zai aura ai babu yanda zamuyi"

Baffa sunkuyar da kai ya ringa yi kamar zai musu sujjada ya ringa suyi hakuri karsu zuga lado ya fasa, tsaki suka yi suka cigaba da kalle kalle suna zaginsu baffa a fakaice sai da suka gama ci musu mutunci tukuna suka cewa baffa ya samo yara a d'ebo akwatuna,ai Baffa cikin rawar jiki yayi waje ya samo matasa yadawo yace musu suna waje, sai da suka kwashi mintuna kafin ramammen nan ya mik'e da mukulli a hanunsa yayi waje,boot d'in motar ya bud'e matasan nan suka fara fito da akwatunan suna shiga dashi gidan,sai da suka shiga da akwatuna goma sha biyu,Baffa kamar yayi tsalle dan murna,Fateema dake jikin window tana kallon duk abinda ke faruwa,ganin irin akwatunan da aka fara shigo dasu ne yasa ta fara tsalle tana shala,Inna kuwa zaninta ta cire ta ringa rawa tana fateema tayi goshi,shigowar Baffa ne yasa suka tsaya suka nufi wajenshi da sauri,baffa cewa yayi,ya za'ayi yanzu su samu kud'in tukwici a basu Dan kayan da suka kawo ba wasa bane,bai kamata ace basu bada tukwici ba,Inna Wuro cewa tayi wane irin tukwici zasu basu ai masu kud'i ne baza ma su k'arbi wani tukwici ba,Fateema cewa tayi aa ya kamata su basu wani abun kar suyi karanta da yawa,kud'add'en da take tarawa ta d'ebo dubu hamsin ta mik'awa Baffa,Baffa kuwa ya k'arba yayi waje da sauri, tsuguna wa yayi yana basu hak'uri su kuwa suka mik'e suna su zasu tafi nan da sati biyu masu zuwa zasu zo a d'aura aure, dubu d'arin mai d'an kumarin cikinsu ya d'auko ya ajiye akan akwati yana ga sadakinta nan,Baffa ganin d'aurin dubu dubu yasa jikinsa ya fara rawa yana musu godiya, (Chaii talauci bai yi ba😂😂😂 wlh Allah ya mana tsari da talauci da kwad'ayi Ameen)



Baffa har bakin motar ya rakasu,ya mik'awa musu dubu hamsin d'in yana ga tukwici,'yar rige rige suka yi wajen k'arba Wanda hakan ya d'an bawa Baffa mamaki,d'ayan ganin yanda baffa ya bisu da kallo ne yasa yayi sauri ya wayance yana "bari dai su k'arba su kaiwa dangin lado sabida karsu d'auka gidan mitsiyata lado ya zo neman aure,ahaka Baffa ya ringa musu godiya suke shige cikin mota suka tafi.

Suna Dan yi nesa da gidan suka yi parking suka fito da wanan dubu hamsin d'in suka raba,suka ce kar su fad'awa Lado an basu tukwici.


Baffa kuwa yana shiga cikin gidan yaje ya samu su Fateema akan akwati suna ta fito da kayan Ciki suna gani,Fateema kuwa sai rawa take,Baffa wasu tsalla tsallen shadoddi daya ga ta fito dasu ya nuna mata yace ta bar mishi,Fateema cewa tayi ya kwantar da hankalinsa kafin ta tafi zata bar mishi,Ahaka suka ringa ganin uban kayan suna murna.



K'arfe biyar na yamma lado ya zo k'ofar gidan ya kira Fateema awaya yace yana waje, Fateema kwalliya tayi sosai ta sa sabuwar atamafar da ta d'inka ta mishi d'inkin Riga da skirt, ya kuwa, matseta sosai, fitowa tayi tana tafiya akasaitance Lado ya fito daga mota yana 'inye amarya kinsha kyau,kin sha kamshi,anya kece kuwa," Fateema murmushi tayi da ya k'ara fito da kyanta,tayi mishi wani fari,binta yayi da kallo tunda ga sama har kasa,ya tsayar da idonsa akan hips d'inta da ya fito sosai a skirt d'in dan ba laifi Fateema Nada diri,Lado lashe lebb'e yayi yace " Allah ya kai damo ga harawa nasan zan huta anan," murmushi Fateema ta k'arayi bata ce komai ba,lado tsayuwarsa ya gyara yace mata "ya kika ga kayan naki sunyi kyau"? Fateema girgiza kai tayi da sauri tace " kyaun ma ai ya wuce misali,Dan bakasan murnar da nayi da ganin kayan ba,unguwanan yanzu labarin lefena kawai akeyi" dabara ne yazo wa Lado Dan yana tsoron Fateema ta tab'a kayan Dan bashi da kud'in da zai biya in ta tab'a, ce mata yayi"aikuwa yanzu Dana taho naji wasu samari suna labarin lefen wai zasu hauro daddare su kwashe kayan,sabida sunsan da gani an narka dukiya a akwatunan," Fateema cikin tsananin tashin hankali ta dafe k'irjinta tana "na shiga uku na lalace ni nasan za'a rina wlh Dan kaf unguwa nan babu wacce aka tab'a yiwa lefe irin wanan,yanzu ya zanyi" murmushin Nassara lado yayi yace "aganina mai zai hana yanzu mu tafi da akwatunan mu ajiye a gidanki Dana gaya miki zaki zauna indai muka zo Nigeria, kinga kin ma huta sai kisa wanan dinkakkun guda biyu," Fateema gyad'a kanta tayi da sauri tace hakane bari ta fad'awa su Inna,ciki ta shige da sauri ta fad'awa su Baffa,nan da nan kuwa suka ce ta samo yara afita da akwatunan kar abiyo dare a sace,Lado ganin an fara fito da akwatunan yasa ya sauke ajiyar zuciya,Bashir kuwa adai dai lokacin ya shawo kwanar gidansu Fateema, Dan da daddare yaso yaje ,amma sabida gwajin da yake so yayi mata,ya nufi gidansu da yamma da kod'adun kayansa,Ta baya ya hango wata a tsaye ta kama kug'u kayan jikinta sun matse ta bayanta duk awaje,mamaki ne ya rufeshi yana tunanin ba dai Fateema bace tayi wanan shigar ba,ahaka ya k'arasa k'ofar gidan yayi sallama,Fateema dake tsaye tana fad'awa yara suyi hankali da akwatunan ta juyowa tayi da sauri ta da ji muryar Bashir,atare gabansu ya fad'i,Dan Bashir gani yayi ta k'ara Haske tayi wani kyau,Fateema ita kuma gani tayi Bashir haskensa ya fito yayi wani k'iba kyaunsa ya k'ara fitowa,da ta kare mishi kallo sosai zata hango jin dadi atare dashi sosai,kod'add'un kayan jikinsa tabi da kallo ta kyalkyale da dariya,har zatayi magana ta juya ta kalli Lado da ya zuba musu ido,wajen Ladon ta nufa ta tsaya a kusa dashi,tace mishi Dan Allah tana zuwa minti biyu,Lado gyad'a mata kai yayi,ita kuwa ta nufi wajen Bashir dake tsaye yana binta da kallon mamaki,tsayawa tayi agaban Bashir tace "mai robobi lafiya mai kake nema awajena ko kazo ka fad'amin yunwa ta kashe y'ay'ana"? Bashir kallonta ya ringa yi tunda ga sama har kasa,k'irjinsa na dukan uku uku sabida bak'incikin shigar da tayi ,d'aurewa yayi yace "Haba Fateema da girmanki da yayanki kikayi wanan shigar fisabillilahi," tsaki Fateema tayi tace " ina ruwanka dani mai robobi naga yanzu ni ba matarka bace ina ruwanka da shigar danayi"

Bashir ce mata yayi "Fateema da ruwana dake mana tunda ke uwar y'aya ana ce nazo ne Fateema muyi magana ta fahimtar juna Dan Allah ki yarda na maidake d'akinki ki cigaba da kula da yaranmu,bakisan abinda Allah zai yi ba nan gaba,ba zama lailai na dauwama a talauci ba ki tausayawa yarana ki dawo d'akinki"


Fateema wani shewa tayi ta mishi kallon tara saura quarter tayi wani juyi agabanshi tace "kalleni da kyau mai robobi nayi maka kama da matar talaka,ai ni nan da kake gani na Allah ya dubeni da idon rahama ya kawo min mai kud'i ka ganshi can yanzu haka ma saura sati biyu bikinmu,dazu nan aka kawo min kayan lefe na gani na fad'a Allah ya yanke min zaman talaucin danayi a gidanka mai robobi ai yanzu na fi k'arfinka,ka samo wata ka aura tun wuri Dan ni ba sa'arka bace yanzu,ka samo wacce zaka ringa bawa d'ari uku kud'in cafene kullum,da 'yar Hausa tana ci,amma ni kam matar Alhaji lado ce,ka dubi himilin kayan lefena,Allah ya rabani da tsiyar gidanka,Dan Allah ni kama tafi Dan ce mishi nayi mijina cutar TLC ce ta kamashi ya mutu, ina nan zanzo na kwashe yarana insha Allahu kaje ka ji da talaucinka kai kadai, yanzu haka ma kantamemen gidan da ya Gina min zanje ingani,ni kaga tafiyata" juyawa tayi ta nufi wajen lado da ya cika yayi fam hak'uri tafara bashi,shi kuwa ya rufeta da fad'a hak'uri ta ringa bashi harda rik'e hanunsa,Lado fusge hanunsa yayi ya bud'e motar ya shige,itama tayi sauri ta bud'e motar kafin ta shiga sai da tayiwa Bashir gwallo ta shige,Lado yaja motar suka tafi.




Bashir bak'inciki takaice, da kishi ne ya hana ya motsa daga k'ofar gidan,ahaka yabi motarsu da kallo har sai da ya daina hangosu,sai da ya samu minti 30 atsaye kafin ya iya Jan k'afarsa yana "na tausaya miki Fateema,ba mai robobin da kika sani bane ada,wanan Alhaji Bashir ne bakida rabo".
*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*


*Kuyi hakuri yau typing d'in ba yawa nayi baki ne kunga bakonka annabinka babu yanda zan bar baki na ringa typing, da kujini shiru gwara indan yi muku ko ba yawa ayi maneji pls*🙏🙏🙏🙏🙏


Page 50-55





Lado basu tsaya a ko ina ba sai wani k'aton guest house,da ace Fateema tana da ido ya kamata ta gane hakan,fateema washe baki tayi adai dai lokacin da maigadi ya bud'e musu gate Dan lado kud'i yake bawa mai gadi, da haka ya ringa yaudaran wayanda ya aura, da sunan gidansa ne,mai gadi yana rufe gate d'in ya tafi da gudu ya bud'e musu k'ofar mota,Fateema kuwa sai da ta gama shan kamshi ta gama yatsine yatsine ta fito daga motar ita a lailai matar mai kud'i,mai gadi murmushi yayi aransa yana "yarinya bakisan dawar garin ba", Lado mai gadi yayiwa magana akan ya shigo musu da akwatuna,yayi gaba Fateema ta bishi a baya tana kalle kalle,zuciyarta fal da farinciki,a Palo suka zauna,Fateema ta cigaba da kalle kalle,tana yaba kyaun palon ahaka mai gadi ya fara shigo da akwatununan,sai da ya gama shigo dasu lado ya matsa kusa da ita ya zauna tare da rungumota,Fateema tureshi tayi tana "kafara ko ka bari mana ingama ganin gidan nawa," Lado murmushi yayi yace aransa "zaki ga gidanki ganin idonki", a fili kuwa cewa yayi " tashi muje in nuna miki d'akunan gidan,"Fateema mik'ewa tayi da sauri tabi bayan lado,in banda b'atar basira,da kan Fateema dake rawa yaci ace ta gane guest house ne sakamakon d'akuna rututu da ya nuna mata da gadaje iri d'aya,bedsheet d'in ma dake shimfid'e akan gadon duk sun Dan tsufa,Fateema kuwa tsalle murna ta ringa yi tana hawa kan gadon tana saukowa,Lado kuwa dariyar mugunta ya ringa mata,Fateema kuwa ta hau ce mishi zata d'ebo yaranta ta basu d'aki guda d'aya ,shima ya d'ebo yaransa a basu d'aki guda d'aya,Lado ce mata yayi karta wani damu,ai akwai gidan da yake ginawa,yaransu kowane nada d'akinsa,Fateema rawa ne kawai bata yi ba,Lado kuwa ganin da yayi tana hawa gado tana saukowa yasa yabita kan gadon ya daneta yafara wasani da ita, har da zata hankad'ashi ta tuna ai sun kusa aure, Mallam Lado kuwa ganin bata tureshi ba yasa ya cigaba da abinda yake yi,Fateema kuwa ganin abun ya fara wuce hankali,har ya cire Riga yasa ta hankad'ashi tana yayi hak'uri ita bazata yarda ya Santa awaje ba har sai an d'aura musu aure, Lado da hankalinsa ma ba a jikinsa yake ba janyota yayi yace to bazai mata komai ba amma ta barshi ya samu nutsuwa,ahaka Fateema ta barshi ya jagwalgwalata duk tabi ta gaji ga d'oyin hammata dana baki,har zata mishi magana akan ko dai baya brush da aski ne,sai kuma ta fasa dan bataso ta b'ata mishi rai,basu suka bar gidan ba sai bayan sallar magriba,dan Fateema sai da ta shigar da akwatunanta cikin d'aki afad'arta gwara ta ajiye akwatunanta da kanta,Lado shi dai babu abinda yake yi sai dariyar mugunta,ahaka ya dawo ya sauketa a gida ya koma guest house ya kwaso akwatuna dan ya mayar wa masu shi,Fateema kuwa tana shiga gida a tsakar gida ta baje ta runga bawa Inna Wuro labarin gidanta har da k'ara gishiri da maggi Inna wuro kuwa sai murna take.



Ahaka kwanaki suka ringa tafiya lokacin biki na matsowa,Fateema amarya sai gyaran jiki take,ta saro caro white ta rufe ido ta ringa shafawa babu dare babu rana,aikuwa wani irin d'au tayi tana d'aukar ido,nan da nan ya sa mata side burn na gefen fuska,wasu kana kana nan pimples suka fito mata,banda hannyenta da suka yi zebra color white and black most especially wajen yatsunta,bata ma damu ba,Dan gani take tana zuwa saudiya zata chanja mai ta cigaba da amfani dashi.


Ranar juma'a da ya cika sati biyu da kai kud'i gidansu Fateema aka d'aura auren Fateema da Alhaji Lado,aranar kuma Lado ya zo ya d'auki amaryarsa da kansa shi kadai dan yacewa 'yan rakiyar amarya,jirgi zasu bi su tafi,suma gobe zai aiko akai su a jirgi su ga Fateema,Fateema kuwa matsuwa tayi ma su tafi Dan ta kagu ta ganta a airport, nan kuwa Lado karya yake, kudin kwana d'aya yaje ya biya musu a hotel,washegari zai kaita kauyensu da matansa suke,Fateema kuwa mamaki ne ya rufeta data ga ya kawosu hotel,ta tambayeshi mai suke yi anan,ba yau yace jirginsu zai d'aga ba,Lado ce mata yayi akwai wasu kud'i daya ke jira akawo musu ne kafin su tafi,Fateema kuwa jin ya ambaci kud'i yasa ta zauna akan gadon d'akin tana karewa wajen kallo,Dan tunda take bata tab'a zuwa hotel ba,atakaice da k'yar Lado ya iya hak'uri Fateema ta ci kazar amarcin da ya kawo,Dan Fateema kamar mayya take indai taga nama ko kaza,babu d'an kunyar ita amarya ce sai da ta cinye kazar tas har da k'ashi,ta sud'e hanunta ta ture ledar tana gyatsa tare da Hamdala,Lado kuwa dama itace tashi kazar,janyota yayi shima yafara maida kwad'ayinsa Dan ya dade yana jiran ranar,aikuwa Fateema aranar ta yabawa aya zakinta Dan Lado irin bugun 'yan kauye ne,sai da yasa ta daina ganewa kwata kwata tafara rokonshi ya cikata,Lado kuwa cewa yake bata isa ba sai ya fanshe kud'insa.


Washegari sai da ya k'ara durzata San ranshi yace ta shirya su tafi,Fateema a galabaice tace mishi ita yunwa take ji ya siya mata abinci kafin su tafi,Lado tsawa ya daka mata yace ta shirya karta b'ata mishi lokaci,Fateema kuwa cuno baki tayi ta luk'a mishi ashar,shi kuwa ya d'auketa da wani wawan Marin da yasa ta ga stars( readers inaga fa ta d'auka Bashir ne bawan Allah da take takawa San ranta,nan bata San lado na kauye da bayasan raini ne ba) ai Fateema ba shiri ta saka kayanta tabi bayanshi,Lado ko wanka baiyi ba ballantana akai ga yayi sallah ahaka yaja motar ya nufi gidan Alhaji zubairu ya ajiye motar ya shiga cikin gidan yayiwa Alhaji zubairu sallama da zai tafi kauyensu yayi jinyar mahaifiyarsa sai nan da sati d'aya zai dawo,Alhaji Zubairu dubu ashirin ya d'auko ya bashi yaringa yiwa mahaifiyarsa addua'r samun sauki,Lado godiya ya ringa mishi ya fito daga palon ya nufi wajen Fateema dake cikin motar sai zare ido take,bud'e motar yayi yace ta fito su tafi,Dan dama ya Riga da ya bawa Alhaji zubairu mukulin motarsa,Fateema ce mishi tayi Ina zasu tafi,kallon da ya watsa mata ne yasa ta sauko daga motar,shi kuwa ya rufe motar yayi gaba tabi bayansa,atakaice Fateema tana ji tana gani Lado ya tare adaidaita sahu ya kaisu tasha suka hau motar gumel,mamaki duk yabi ya rufeta so take ta tambayeshi ina motarsa,sun fasa hawa jirgin ne amma ba dama, Dan ya d'aura fuska sosai,yunwar da ya ringa damunta ne yasa ta d'aure ta ce ya taimaka ya siya mata Abu taci yunwa take ci,Lado ko kallonta bai yi ba sai da motar ta d'an tsaya ana checkup ya siyi auran hamsin ya mik'a mata,Fateema ci kawai tayi Dan tayi maganin yunwa.






B'angaren Bashir kuwa tunda ya bar gidansu Fateema yaci alwashin ya hak'ura da Fateema zai nemi mace tagari mai hankali ya aura,anan ya duk'ufa ya fara Neman mace mai hankali da tarbiyya da bata kwad'ayin abin duniya,abokinsa sa'eed yacewa ya taya shi neman mace mai wanan qualities d'in Dan babu abinda ya b'oyewa Saeed akan

Please Login or Register in order to submit comment