Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyar gero kwanu biyu ledar Maggi dunkule,da gishiri sai manja da man kulli kwalba ,abinda dai wanan Karin bai siya ba shine itace,kalanzir ya siya Rabin gallon, da ya kawo kayan abincin Fateema tsalle tayi ta dire tace Allah ya sauwake ta k'ara cin shinkafa 'yar Hausa, ta Riga da ta saba da yar gwamnati taci tuwon semo babu abinda zata yi Dana massara,Bashir ko kallonta bai yi ba ya shige da kayan abincin kitchen,yace dama ai ya fad'a mata idan kayan abincin sun kare zata iya tafiya gidansu tunda dama abinda ya dawo da ita kenan,Fateema girgiza jiki ta Ringa yi tana ita dai ta fad'a mishi yasan yanda zai yi ya siyo musu irin kayan abincin da ya kare ita da ya'y'anta bazasu iya cin tuwon massara da 'yar Hausa ba,Bashir ce mata yayi inta San bazata iya ba ta tafi gidansu abinda yake da k'arfinsa kenan ya siya,bazai je yayi sata akanta ba,daga haka ya kad'a kansa ya bar gidan.




Fateema kuwa ganin da gaske dai dole ta fara cin 'yar Hausa indai baso take yunwa ya kasheta ba,tunawa tayi da gidan Khadija take ta tuna wulak'ancin da tayiwa Khadijar,tunanin hanyar da zata bi ta koma gidan Khadijar ta fara yi,wani dabara ne ya fad'o mata arai take tayi amana da shawarar da ta yanke,da yamma shiryawa tayi ta nufi gidan Khadija babu kunya babu tsoron Allah,k'irjinta na d'an dukan uku uku ta shiga gidan,Khadija na zaune a Palo tana kallo ita da y'ay'anta,sallamar Fateema taji kamar a mafarki ta waiga da sauri, ganin da gaske itace yasa ta had'e girar sama da ta kasa ta amsa sallamar tana "lafiya mai kike nema a gidana" Fateema marairace fuska tayi ta shiga palon ta samu kujera ta zauna ta fara matsa hawayen karya,su waleed mik'ewa suka yi suka fara ficewa daga palon, dan indai mahaifiyarsu tayi baki barin gurin suke,khadija sai da ta tabbatar da yaranta sun bar palon ta juyo ta kalli Fateema da ta sunkuyar da kai tana share hawaye, " Mallama Lafiya mai kike nema a gidana wai ko rashin mutuncin kika zo ki k'ara min har cikin gidana"



Fateema kuka ta fashe dashi tana "khadija kema kinsan ban isa na wulak'antaki ba wlh ko giyar wake nasha bazan iya miki wulak'anci ba,mantawa nayi ban fad'a miki ba ina da aljanu da suke sawa nayi rashin mutunci,tun ina yarinya k'arama suke shigeni, to Ashe ranar da kika shiga gidana sune suka motsa min nayi miki rashin mutunci,Abbansu Aliyu ma har ya saba dasu,to wlh basu sakeni ba sai jiya,Hameeda ce ma take fad'amin kin shigo na miki rashin mutunci bansani ba wlh Khadija kema kinsan ban isa na wulak'anta ki ba"




Khadija mamakin irin karyar da Fateema ta sharara mata ne ya rufeta,Khadija tace


"Amma aljanunki dake saki kiyi rashin mutunci basu tashi saki rashin mutunci ba sai da na shiga gidanki,kuma basu tashi motsa miki ba sai da muka muku abun alheri,suka sa kika d'auke k'afa daga shiga gidana,hmm Fateema kenan ai na Riga da na karanceki tas,kice min kayan abincinku ne ya kare shiyasa kika shigo,Fateema Allah yasan duk abinda nake miki wlh Dan Allah nake miki,ina kuma zaune dake ne da zuciya d'aya Ashe ke ba da zuciya d'aya kike zaune dani ba,kina zaune dani ne sabida kwad'ayin abun duniya dan haka Fateema wlh na dawo daga rakiyarki,bazan iya zama da Wanda yake zaune dani Dan abun hanuna ba Dan haka ki tashi nima ki fitarmin daga gida"


Fateema d'agowa tayi cikin tsananin mamaki tana kallon khadija dan bata tab'a tunanin zata iya mata haka ba,


" ki tashi nace ki fita"

Khadija tace tana mik'ewa tsaye dan wani irin haushin Fateema take ji,


Fateema jiki a sanyaye ta mik'e tace " ba komai khadija ngd da wulakancin da kika min "

"Eee fita na miki wulak'ancin Kafin na miki ke kika fara yimin"


Fateema ficewa tayi tabar Palon zuciyarta na suya,tana isa gida ta zube atsakar gida, zagin khadija ta fara yi ta na tsine mata,addu'a ta ringa yi Allah yasa su talauce,masifa ta runga janyo musu da jafa'i, yanda take jin zuciyarta da za'a bata bindiga tsaf zata harbe khadija ahaka su Aliyu suke dawo daga makaranta suka sameta tana ta surutu ita kadai kamar mahaukaciya,Nura zama yayi a kusa da ita yace yunwa yake ji,Ashar ta liliyo mai tana ba sai yayi ta jin yunwar ba,ita dai da hanunta bazata iya dafa shinkafa 'yar Hausa ba.



Aranar ko attempting d'in Dora girki bata yi,ta kuma hana Hameeda ta d'ora a fad'arta gwara mitsiyacin ubansu ya dawo yazo ya tarar basuyi girki ba,dan bazasu iya cin tuwon massara da shinkafa yar hausa ba,



Ahaka Bashir ya dawo ya same su sunyi cirko cirko,Nura kuwa ya rik'e cikinsa sai kukan yunwa yake, hankali a tashe ya nufi inda suke yana tambayarsu abinda ya faru,

Fateema mik'ewa tayi ta rik'e k'ugu tana "Yunwa muke ji shine abinda ya faru," Bashir shima mik'ewar yayi yace " bangane yunwa kukeji ba mai yasa Baku yi girki ba"


"Fateema wani mugun kallo ta mishi tace "mai zamu girka ai babu abinci a gidanan,abincin da ka kawo na dabobbine mu kuwa mutane ne kaga babu yanda za'ayi muci abincin dabobbi"


Bashir ransa ne ya masifar b'aci da yaji abinda Fateema tace ce mata yayi "Abincin Dana kawo kika raina kike ganin na dabobbi ne wasu suna can Neman quaternshi suke basu samu ba,indan ke bazaki ci ba,ai sai ki dafawa yaranki suci,Dan su nasan zasu ci,amma sabida rashin mutunci irin naki,da rashin hankali kin bar 'yayanka da yunwa,yanzu ace kamar Nura rabonsa da abinci tun safe,ke ko tausayinsu bakya ji, fateema a gaskiya bazan jure irin wanan rashin hankalin a gidana ba,indai zaki na barmin yara da yunwa gwara ki tafi gidanku na cigaba da kula da yayana Hameeda yanzu ta girma da zata iya kula da kanenta bana San tashin hankali"


Fateema tsaki tayi tace " mudai bazamu ci 'yar Hausa ba Dan muringa da mun saba da 'yar gwamnati kasan yanda zakayi damu"


Bashir cewa yayi "banida na gwamnati zaki iya tafiya gidanku ina gwamnatin kikeso kici"



Hanun Nura ya rik'o yace mishi yayi hak'uri ya daina kuka yanzu nan zai dafa mishi Abu yaci,daga haka kitchen ya nufa ya d'ora ruwa,ya samu faranti ya auna shinkafar yafara tsinta,Fateema tsaki tayi ta shige d'aki tana ita dai gidansu zata tafi bazata iya ba,da taimakon Hameeda ya dafa musu shinkafa da mai da yaji,a babban faranti ya zuba musu gabad'aya suka zauna a tsakar gida suka fara ci,Fateema dake jikin window tana kallosu had'iyar yawu ta ringayi cikinta na kugin yunwa, Dan rabonta da abinci tun safe,addua ta ringayi Allah yasa su rage in sun kwanta taje taci.



Bashir kuwa sai da suka ci suka koshi shi da y'ay'ansa,kasancewar dare yayi sosai wajen k'arfe goma na dare ,ce musu yayi suje su kwanta tunda sun koshi, mik'ewa suka yi d'aya bayan d'aya suka nufi d'akinsu,Bashir sai da ya tabbatar dukansu sun kwanta ya tofesu da addua ya fito daga d'akin ya d'auki farantin da suka ci abinci ya kai kitchen ya ajiye ya rufo k'ofar kitchen ya nufi d'aki,Fateema kuwa tana ganin ya nufo d'aki tayi sauri ta hau kan gado ta kwanta ta rufe ido,Bashir kuwa yana shiga d'akin gyatsa yayi tare da hamdala ya cire doguwar rigar jikinsa daga shi sai dogon wandonsa ya kwanta ya juya mata baya cikin 'yan mintuna kuwa barci yayi awon gaba dashi,Fateema kuwa tana rik'e da cikinta dake mata zafi tana addua Bashir yayi nisa a barci taje taci sauran abincin da suka rage,sai da ta lek'a Bashir ta tabbatar da yayi nisa a barci ta duro daga gado tayi sadaf sadaf ta fice daga d'aki ta nufi kitchen da sauri,farantin ta bud'e da sauri,hankalinta ne ya tashi data ga ba komai a farantin,da sauri ta janyo tukunyar ta bud'e taga kanzo ne an ma zuba ruwa acikin tukunyar,ashar ta kunduma tana "amma wanan mutumin ko mitsiyaci shine zai juye duk abinci,yanzu ko mai zanci" zubar da ruwan tayi ta d'auko cokali ta fara kankare tukunyar kamar mayya,kankarewa take da hannu bibiyu tana ci,Bashir duk abinda takeyi yana kallonta,wajen kitchen d'in ya nufa yana "wane dabban ne daddaren nan yaje yana kankarewa mutane tukunya, Fateema wurgi tayi da tukunyar tayi sauri ta mik'e tana k'ok'arin fitowa daga kitchen d'in fuskarta a d'aure an ma manta bata wurgar da cokalin hanunta ba,Bashir dariya ya kyalkyale dashi yana " Ashe kece a kitchen d'in,abincin dabobbin kika je cine"


Fateema cikin borin kunya ta fara masifa tana " Allah ya kiyaye mai zanyi da abincin dabobbi ai wanan sai ku, ni ruwa nazo na d'iba na sha"


Bashir dariya ya k'ara kyalkyalewa dashi yace "naga alama,Ashe ruwan a tunkuya yake kuma da cokali ake zuwa a d'iba ai da kin fad'amin mu rage miki ai da mun rage miki,gashi yanzu kinyiwa kanki kinzo kina kankaran tukunya"


Fateema wurgar da cokalin hanunta tayi ta fashe da kuka bak'inciki tana mishi Allah isa,Bashir dariya ya ringa mata ya juya ya koma d'aki,fateema kuwa sabida tsananin kunya da k'yar ta koma d'akin ta kwanta zuciyarta fal bak'inciki.



Washegari Bashir da kansa yayi musu abin kari Dan yasha alwashin ya daina jiran Fateema tayi musu komai,sai da suka tafi makaranta ya kuma d'ora girkin rana Dan so yake insun dawo su samu abinci suci,inyaso idan ya dawo ya musu na daren,Fateema kuwa tana daga d'aki yunwa yaci ya cinyeta addua ma ta ringa yi Allah yasa ya kirata yace ta d'ora Karin safe,amma abun mamaki dakansa ya musu abin karyawar,tana ji tana gani suka cinye,Dan Nura dayace ina na Umma,Hameeda had'a baki suka yi wajen cewa ai Umma bata shan koko,nan kuwa addua take su kawo mata ko da ba siga ta sha



Bashir sai da ya gama girkin rana tsaf ya juye abincin a kula ya kai d'akinsu Aliyu ya b'oye ya fito ya nufi band'aki yayi wanka yazo ya shirya zai fita ko kallon Fateema bai yi ba,fateema ganin dagske fita zai yi bazai ajiye mata kud'in cafene ba yasa ta mik'e da sauri ta ruk'o rigarsa tana "mai kake nufi yau bazaka ajiye kud'in cefane bane ko me"?


Bashir doke hanunta yayi yace " wane kud'in cefane,ke da baki iya cin yar Hausa da tuwon massara ba,wane cafane zan ajiye,ai daga yau na daina ajiye cafane,da kaina zan ringa yiwa yarana girki,Dan bazan yarda kiringa barmin y'ay'a da yunwa ba, kedai da bazaki iya cin 'yar Hausa ba sai ki San nayi,"


Fateema cakumo wuyan rigarsa ta k'ara yi tana "to wlh ka sakeni na tafi gidanmu bazan iya zama da yunwa ba,dawane zanji ga talauci ga yunwa,Allah kabani takardata na tafi gidanmu nagaji da zama dakai gwara na tafi gidanmu,"


Bashir wurgi yayi da hanunta yace "bazan bada takardar ba ki kaini duk inda zaki kaini,Gidanku kuma ban hanaki tafiya ba," Bashir yace yajuya ya bar gidan,har k'ofar gida Fateema ta bishi tana luk'a mishi ashar,tana zaiyi mamaki bazai dawo ya Tarar da ita ba,ciki ta koma da sauri,ta fara had'a kayanta a akwati tana gama had'awa ta fito daga gidan,ta rufo k'ofar ba ko sisi a hanunta ahaka ta nufi gidansu,har k'ofar gida Dan sahu ya kaita,ta sauka ta shiga ciki Dan ta k'arbi kud'insa ta bashi a tsakar gida ta Tarar da Inna wuro da Baffa da alama dai Baffan bai fita ba,sallamar da tayi ne ya katse musu maganar da suke suka juyo suna amsa sallamar fuskarsu d'auke da mamakin ganinta,Fateema kuwa dayake tasan ta kan makirci,kuka ta fashe dashi ta zube akasa,ta fara birgima tana ta shiga uku ta lalace,sallati su Baffa su kayi suka nufi wajenta da sauri suna tambayarta mai ya faru




Ai kamar zugata suka yi ta cigaba da ihu tana rik'e cikinta,sallamar Dan sahu da suka jiyo daga zauren gidan ne yasa Baffa ya nufi zauren,Mai adaidaita sahun mik'a mishi akwatin yayi yace asallameshi tafiya zai yi,Baffa tambayarsa yayi nawane kud'in Dan sahu ya fad'a mishi ya d'auko kud'in daga aljihunsa ya mik'a mishi ya kinkimi akwatin ya koma ciki,har lokacin Fateema kuka kawai take tana rik'e ciki,sai da Baffa ya daka mata tsawa tayi shiru ya k'ara tambayarta abinda ya faru,Fateema karkata kai tayi tafara zuba karya tana fyace majina,cewa take kwana uku kenan rabonta da abinci,Bashir baya bata abinci,duk dare sai ya mata shegen duka,karya iri da sharri iri iri ta ringa zubawa Bashir,Inna wuro da dama irin matan nan ne masu kwadayin abun duniya Dan dama tana jin haushin Bashir a fad'arta k'ashin tsiya ne dashi Bashi da kashin arziki,itama Ashar ta hau zubawa Bashir tana Dan wulakanci ga talauci ga yunwa har da su duka alamarin,(no wonder like mother like daughterπŸ€”πŸ€”) Baffa dayake shima sai yanda akayi dashi Dan inna wuro ta gama dashi,shima tofa albarkancin bakinsa ya hau yi yana tunda abun nashi yazo da haka dakansa zai je gidan ya bashi takardar 'yarsa,Inna wuro mik'ar da Fateema tayi dake ta sharce majina suka nufi d'akin,ta d'auko mata taliya da wake da mai da yaji da take siyarwa da safe wanda yayi ragowa,Fateema cikin rawar jiki ta fara cin abincin kamar bata tab'a ci ba,Inna wuro kuwa ganin yanda take aika loma bakinta yasa tayi ta zagin Bashir tana ya bar 'yarta da yunwa.





Bashir kuwa da yafita sai da ya biya ta makarantarsu Aliyu ya fad'a musu inda ya b'oye abincin ranarsu yace insun koma suci.


Lokacin da yaje gida bai yi mamaki ba dasu Aliyu suka fad'a mishi basu samu fateema ba Dan dama yasan za'ayi haka,bai ko damu ba ya rarrashi su Aliyu da Fateema tayi tafiya Dan haka su kwantar da hankalinsu zai cigaba da kula dasu,kitchen ya nufa Dan ya d'ora girkin dare Hameeda tace mishi ai ta musu girki,har sunci sun zuba mishi nashi a flask,wani irin farinciki ne ya rufeshi Dan yasan bazai sha wahala ba Hameeda ta iya girki zata kuma iya kula da su Sumayya Dan tama fi Aliyu yayanta girma,zama yayi a tsakiyarsu yaci abincinsa ya ringa basu labari hankalinsa kwance,gani yake ma kamar da bata nan yafi sakewa yafi jin dadi.
*YπŸ…°TSUN MU*🀚🏻🀚🏻🀚🏻🀚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*






Page 30-35




Bashir aranar rayya daren yayi yana nafil nafili yana adduar Allah ya bud'a masa,dan sai da yaje ya kwanta yaji zafin abinda Fateema tayi mishi,dan kawai bashi da kud'i ta tafi gidansu bata ko duba yaran dake tsakaninsu ba,uwa da aka sani da tausayi,bata tsaya tayi tunanin wa zai kular mata da yaran ba,wane hali yaran zasu shiga ba,ta sa k'afa tabar gidan, bai samu barci ba sai k'arfe uku na dare.




Fateema kuwa hankalinta a kwance bayan ta gama cin taliyar ta hau bawa Inna wuro labarin irin talaucin da suke yi,tacewa Inna wuro inta samu Bashir ya bata takardarta zata d'ebo y'ay'anta Dan kar suma yunwa ta kashesu,Inna wuro da sauri tace mata karta sake ta d'ebo yaranta hauka take yi,bata San in ta d'ebo yaranta kashewa kanta kasuwa zata yi ba ai gwara tabar yaran awajen Bashir inyaso sai ta ringa zuwa tana dubasu,duk abinda ta samu sai taringa kai musu, Fateema kuwa dayake shashasha ce cewa tayi yaushe baffa zaije gidan ya k'arbo mata takardarta Inna Wuro ce Mata tayi ta kwantar da hankalinta goben nan zata sa Baffa yaje ya k'arbo mata haka kawai da kyaunta da komai ai tasan tana gama idda zata samu wani Alhajin ta Aura, wani farinciki ne ya rufe Fateema da taji abinda tace tuni tafara hararo kanta a matsayin Khadija da irin wulakancin da zata yiwa mutane,har gidan Khadija zataje ta rama wulakancin da ta mata, ahaka suka shantake suna hira,har akayi sallar azahar babu Wanda ya tashi cikinsu yayi Sallah,sai da cikinsu ya fara kukan yunwa,Inna wuro tace ta tashi ta d'ora musu jellof d'in taliya 'yar Hausa,Fateema jin da tayi Inna Wuro tace taliya 'yar Hausa zata kuma dafa musu yasa tace ya za'ayi taci taliya dazu yanzu kuma ta kuma cin taliya, babu shinkafa ne ta dafa musu da miya, dariya Inna wuro tayi tace akwai shinkafa mana matsalar tana da tsinta da yawa kafin ta gama tsincewa zata Dade,gaban Fateema ne ya fad'i da taji abinda tace bata ce komai ba ta nufi wajen da aka ajiye murhu tana zancen zuci.


Daddare kuwa Inna Wuro da kanta tayi girkin dare tuwon dawa tayi da miyar kukan Fateema tana ji tana gani ta ringa tura tuwon dawan Dan gudun yunwa,abinda ba'a tab'a yi a gidan Bashir ba,sai da ta kwanta zatayi barci su Nura suka fad'o mata arai,ahaka barci yayi awon gaba da ita, tana tunanin y'ay'anta.



B'angaren Bashir kuwa washegari da sassafe ya tashi su Aliyu Dan sunyi wanka ya d'ora musu ruwan shayi Dan ya d'anyi ciniki jiya,k'arfe bakwai da rabi su ka gama karyawa,har k'ofar gida Bashir ya rakasu sai da ya daina hangosu ya koma ciki.


Baffa kuwa da sassafe Inna wuro tace yaje gidan Bashir ya k'arbowa Fateema takardar sakinta Dan Fateema ta gama zama da Bashir tunda bashida mutunci bai ga Wuyan da fateema ke sha a gidansa ba yake dukanta,
Bashir kuwa yana rufe k'ofa baffa ya k'araso gidan

,Bashir kuwa yana komawa ciki shinkafa ya zubo afaranti Dan ya tsince Dan so Yake ya ringa yi musu girkin rana kafin su dawo daga makaranta,yana cikin tsintar shinkafar yaji ana kwankwasa k'ofar gida, ajiye farantin yayi, ya mik'e yayi waje, yana bud'e k'ofa yaga Baffa mahaifin Fateema atsaye ya d'aura fuska sosai,Bashir mamaki ne ya rufeshi daya ganshi,rusunawa yayi yafara k'ok'arin gaishe shi,Baffa ya dakatar dashi yana mik'a mishi Hannu,d'agowa yayi ya na kallonsa Dan bai gane mai yake nufi ba "ba dogon surutu ne ya kawo ni kabani takardar 'yata kawai Dan Baka da mutunci 'yata zaka ringa bari da yunwa tayi kwana uku bata ci komai ba,sanan kazo ka rufeta da duka,kana hauka ne,kai yanzu ahaka na baka 'yartawa,arame a kanjame,yarinya fara ta koma bak'a k'arfi da yaji, ai tunda abun naka yazo da haka har da su duka kabani takardar kawai ta gama zaman aure a gidanka ta ringa zuwa tana duba yayanta"


Bashir mamakin Baffa ne ya rufeshi yafara k'ok'arin magana,dakatar dashi Baffan ya k'arayi yace bayaso yaji komai ya bashi takardar 'yarsa kawai,Bashir a zuciye ya shige cikin gida ransa a matuk'ar b'ace d'aki ya nufa ya janyo drawers d'in gaban mudubi ya fara Neman biro, bai samu Biro ba sai pencil,da alama nasu Aliyu ne wani memo ya yaga ya rubutawa Fateema saki d'aya ya koma waje ya mik'awa Baffa dake tsaye yana hure hure kamar fad'a zai yi da wani,k'arbe takardar yayi yace "anjima zan turo akwashe kayanta" daga haka ya kad'a kansa yatafi Bashir bayansa yabi da kallo har ya b'ace wani irin bak'inciki da tafasa zuciyarsa taringa yi take hawaye ya hau zubo mishi,ciki ya koma ya zube akasa yana "talauci bai yi ba,yanzu da ina da kud'i Fateema da mahafinta bazasu yimin haka ba,shikenan sai kana da kud'i za'a mutuntaka asan darajarka,Ya Allah kaga wulakancin da bayinka suka min akan banida kud'i Allah ka bud'amin kayi min arziki alfarmar annabi SAW" yace yana share hawayen fuskarsa,farantin shinkafar ya jawo
Dan ya cigaba da tsinta ya k'ara ji ana kwankwasa k'ofar,mik'ewa yayi ya nufi waje yana tunanin ko Baffa ne ya dawo,yana bud'e k'ofar yaga
Alhaji Ahmed atsaye,murmushi ya saki ya fito daga gidan suka fara gaisawa hanunsu rik'e da juna bayan 'yan gaishe gaishe da tambaye tambaye Alhaji Ahmed yace masa "Bashir zuwa nayi na fad'a maka abin farincikin da ya sameni da kuma cigaba da na samu,an k'ara min girma awajen aikina kuma yanzu haka anyi min transfer zuwa Lagos gobe nan zamu tafi nida iyalina,Bashir har kyautar miliyoyin kud'i aka bani sabida na tserar da kayan wani Hamshakin mai kud'i duk da cin hancin da aka ringa bani mai tsoka ina k'in k'arba Dan haka shine nima nace Allah ne ya d'aukaka ni ba ikona bane ba dabarata bane,dan haka nace nima bari zanyi maka alheri,zan maka kyauta mai tsoka Dan yana da kyau idan Allah ya maka wani niima kaima ka dubi Wanda Bashi dashi kayi masa,sai Allah ya k'ara bud'a maka ta hanyar da baka yi tunani ba,Bashir ga wanan kud'in miliyan shidda ne inaso kaja jari,kar kuma ka sake kayi min godiya,Allah zaka yiwa godiya,


Wanan filin dake gefen gidana na bar maka kyauta akwai takardun filin a ciki,

Jiya nasa Khadija ta had'a kayan sawarmu bama bukatar komai na amfanin gida duk muna dasu acan, Dan haka duk wani Abu dake cikin gidana na bar maka duniya da lahira,idan ka kwashe komai
Iyayena zasu dawo gidan da zama"




Alhaji Ahmed yace yana k'ara miki mishi jakar Hanunsa,ganin da yayi Bashir bai motsa ba yasa ya tab'a shi firgigit Bashir ya dawo hayyacinsa Dan tunda Alhaji Ahmed ya ambaci miliyan shidda yayi suman tsaye duk sauran maganganun da yake yi bajinsa yake yi ba,kasa k'arbar jakar yayi yace "Alhaji kana nufin dubu shidda ko miliyan shidda,murmushi Alhaji Ahmed yayi yace mishi "k'arbi dai Allah ne ya baka"


Bashir zubewa yayi akasa yayi sujada,Alhaji Alhmed kuwa hakan da yayi yasa ya k'ara jin dadi a zuciyarsa Dan ba kowane mutum bane zai samu abun farinciki yayi sujadar Shukur( sujjada ce da akeyi ta godiya ga Allah idan kasamu wata niima ko burinka ya cika akan wata bukata taka)


Sai da Bashir ya dade kafin ya d'ago,yana d'agowa yaje rik'e k'afar Alhaji Ahmed ya fara mishi godiya yana kuka Dan ko amafarki bai tab'a tunanin zai rik'e dubu d'ari takansa ba ballantana akai ga ya rik'e miliyan shidda,Alhaji Ahmed d'agoshi yayi ya damka mishi jakar yana girgiza mishi kai da bayasan wanan godiyar da yake masa,Allah ne ya bashi Bashir kasa daina mishi godiyar yayi,har Alhaji Ahmed yayi mishi sallama ya tafi,


Bashir kuwa d'aukar jakar yayi ya shige gida ya kulle k'ofar d'aki ya shige ya ajiye jakar akan gado ya zuge jakar d'aurin dubu dubu ne acike a cikin jakar sai takardu guda biyu warware takardar yayi,yaga na filin da Alhaji Ahmed ya bar mishi ne,Bashir girgiza kansa yayi Dan ya tabbatar ba mafarki yake ba,ganin dagaske ne ba mafarki yake ba yasa ya fashe da kukan farinciki ya d'aga hannunwansa sama yana k'ara godewa Allah,rufe jakar yayi,ya nufi band'aki yaje ya d'aura alwala yazo ya ringa zuba nafilili yana godewa Allah,atakaice Bashir sai da ya kuma komawa gidan Alhaji Ahmed yace ya taimaka mishi yasa mishi kud'in a bank kafin yayi tunanin abinda zai yi da kud'in,Alhaji Ahmed tambayarshi yayi ko yana da account yace mishi Bashi da account,Alhaji Ahmed da kansa ya raka shi bank ya bud'e account aka sa mishi kud'in godiya da addua kam Alhaji Ahmed ya sha shi awajen Bashir.


Baffa kuwa yana zuwa gida ya tarar da Inna wuro tana tayiwa Fateema fad'a akan tace ita bazata iya cin dumame da koko ba ,ya za'ayi ta baro gidanta da ake shan koko da kosai nan kuma azo a had'ata da dumame da koko ina laifi Inna wuro ta bata taliyar da wake da mai da yaji da take siyarwa taci,Inna wuro ce mata tayi bazata iya bata taliyar ta ba ta siyarwa ce inzata ci dumame da kokon gwara taci in ba haka ba kuwa ta wuni da yunwa, kuka Fateema ta fashe dashi tana ita tama fara Dana sanin zuwa gida,ahaka Baffa ya shigo ya samesu ya bawa Fateema takardar sakinta,Fateema duk cika bakin da ta ringa yi Bashir ya saketa tana ganin takardar sakin ta fashe da kuka haka kawai taji kuma tana danasanin abinda tayi,tana tuna irin talaucin gidan Bashir kuma sai taji gwara da ya saketa Dan tasan yanzu tana gama idda zata samu Wani mai kud'in ya aureta,a takaice tana ji tana gani Inna Wuro ta siyar da Taliyar,dolenta taci sandararen tuwon da koko,sawa tayi aranta zaman da zata yi a gidansu na d'an lokaci ne tana gama idda zatayi

Please Login or Register in order to submit comment