Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai yayi,atakaice sai da suka gama shan shayin ya haska musu suka k'arasa Home work d'insu ya rakasu su kwantar ganin bai ga Nura a d'akinsu bane yasan Fateema tafiya tayi dashi su kwana tare,d'akin Fateema ya nufa,akwance ya ganta tayi rashe rashe tana ta barci,Nura kuma yana daga gefenta,d'aukar Nura yayi ya maida shi d'akinsu Aliyu ya rufo musu k'ofar ,yafito ya koma d'akin Fateema,kulle k'ofar yayi ya cire rigar jikinsa daga shi sai dogon wando ya zaro tsohuwar belt d'insa ya rufe Fateema da duka, Fateema kamar a mafarki taji sauk'ar belt a jikinta,mik'ewa tayi tana ihu,Bashir kuwa ya cigaba da dukanta,zagaye d'akin Fateema ta fara yi tana zaginshi tana "Bashir talaucin naka kuma hauka ya saka da zaka ringa dukana Allah ya isana ban yafe ba shege mitsiyaci,babu irin kalar zagin da bata mishi ba,Bashir ganin bakinta bai mutu ba duk da dukanta yake bata fasa zaginsa ba yasa ya ware iya k'arfinsa ya ringa dukanta,dan ya zuciya abinka da mai hakuri bai iya zuciya ba , Fateema da taga ba hali zai iya kasheta da ranta hakuri ta koma ta Ringa bashi tana ta tuba ta daina,sai da Bashir ya mata lilis ya gaji dan kansa ya kyalleta, ya koma gefe ya fara magana cikin b'acin rai "na gaji da wulakancin da kike min bakida hankali bakida tunani,bakisan darajar aure ba,ni zakiyiwa cin mutunci agaban wata,dan kinga ina kyalleki,ni na d'orawa kaina talauci da zaki na min gori kullum,agaban 'yayana haka zaki sani agaba kiyi ta zagi kamar kinsamu danki,wanan kashedi nayi miki wlh duk ranar da kika kuskura kika k'ara zagina sai na miki dukan da yafi wanan"

Kuka Fateema ta k'ara fashewa dashi tana "wlh Bashir sai ka San ka dakeni,wlh ka daki aurenka,gobe da safe gidanmu zan tafi bazan iya ba ga talauci ga duka Allah sai ya saka min mugu azzalumi wlh na gama zaman gidanka,dan bazan cigaba da zama alluran talaucinka inya motsa ma kazo ka rufeni da duka ba"

"Sai me in kin tafi gidanku ki tafi gidanku nima zan fi samun kwanciyar hankali kibarni da yarana mu cigaba da zama a talaucinmu,angaya miki idan babu ke bazamu cigaba da rayuwa ba, gobe da safe ki tabbata kafin na dawo daga massallaci kin tafi gidanku gidan arziki,Mara mutunci kawai da yaranki hud'u har yanzu baki mallaki hankalin kanki ba, keda jaka baku banbanci jahila kawai"

kuka Fateema ta k'ara rushewa dashi tana "ka bani takardata
in samu shaidan ka sakeni dan bana fatan ina bar gidanan Wani Abu ya dawo dani,kuma in zan tafi da yarana zan tafi wlh dan bazasu zauna dakai yunwa ta kashe su ba"


Bashir mik'ewa yayi yace " basai ki tafi dasu nagani ba, da alama har yanzu baki daku ba tunda kina da bakin magana," gurinta ya Nufa ta kwasa da gudu tana zaginsa,atakaice aranar daga Bashir har fateema babu Wanda ya runtsa dan Fateema bata gaji da zaginsa ba shi kuma bai gaji da dukanta ba.



Pls kuyi maneji dakyar nayi wanan wlh

*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*



*NOTE*- *NAYI MISTAKE AWAJEN NUMBERING INSTEAD OF NASA 15-20, 10-15 NA KUMA SAWA DON HAKA ZAN CIGABA DAGA 20-25*





Page 20-25



"Banji dadin daka b'oyemin halin da kake ciki ba,aganina mun Riga da mun zama d'aya,wai ace muna mak'ota dakai kana cikin wani hali na bukatar taimako,kuma kasan inada halin da zan taimaka ma,amma ka kasa fad'amin,yanzu kasan mutane insuka San halin da kake ciki, gamu mak'ota *MUGUN MAK'OCI* ( *LITTAFIN FIRDAUSI SODANGI*) zasu ringa ce min Dan sun San ni mak'ocinka ne kuma inada halin da zan taimaka maka,yanzu badan Khadija ta shiga gidanka ba bazan tab'a sanin halin da kake ciki ba,gaskiya banji dadi ba,daga yau karka k'ara min haka,Alhaji Ahmed yace yana kallon kod'ad'iyar rigar jikin Bashir



Murmushi Bashir yayi yace "Ngd sosai Banida bakin gode ma sai dai na maka adduar gamawa da duniya Lafiya,insha Allahu bazan sake ba indai ina bukatar taimakon zan nemeka"


Alhaji Ahmed murmushi yayi yace "ko kai fa karka k'ara b'oyemin komai,duk wani Abu daka San kana bukata ka fad'amin zanyi maka insha Allahu sai dai idan abinda ka nema d'in ya fi k'arfina"


Bashir d'an dukawa yayi alamar zai mishi godiya Alhaji Ahmed yayi sauri ya rik'oshi, Hannu ya zura a Aljihun wandonsa ya zaro d'ari biyu bundle d'aya ya mik'awa Bashir yace ya rik'e a hanunsa,in case in wani Abu ya taso, sanan anjima akwai masu wiring, ya musu waya zasu zo su musu connecting daga gidansa su ringa samun wuta,idan engine ma suka kunna zasu ringa samun wuta,



Bashir tunda ya damka masa dubu ashirin,hawayen farinciki ya hau zubo mishi Dan rabon da ya rik'e dubu biyar ta kansa ya manta,Alhaji Ahmed kuwa ganin hawaye na zubo mishi yasa ya k'ara jin tausayin Bashir d'in yanzu akan ya bashi dubu ashirin da bai fi ya kasheta Arana ba Bashir ke Hawaye,Bashir share hawayen Fuskarsa yayi ya fara mishi godiya,Alhaji Ahmed ya azza Hannu a leb'enshi alamar yayi shiru,Bashir kuwa ya cigaba da mishi godiya,Alhaji Ahmed juyawa yayi ya shige gidansa,Bashir kuwa sai da ya Dade atsaye yana juya kud'in Hanunsa kafin ya iya Jan k'afarsa ya shige gidansa.



Yana shiga gidan, ya tarar da Fateema tana ta soya dankali,tana wani waka,ga kwai wajen guda goma data ajiye agefenta da Alama so take idan ta gama soya dankalin,ta soya kwan,d'agowa tayi tana amsa sallamar da yayi,idonta ya sauka akan kud'in Hanunsa,ajiye cokalin hanunta tayi da sauri ta rage wutan,ta mik'e ta nufi gurinsa, cikin fara,a,Bashir sakin baki yayi yana kallonta Dan rabon da ma yayi sallama ta amsa ya manta ballantana akai ga tayi far'aa,Fateema kuwa tana zuwa kud'in hanunsa ta k'arba tana "Aaa Abban Aliyu wanan kud'in fa," Bashir wani mamak'in ne ya k'ara rufeshi dan rabon da ta ambaceshi da Abban Aliyu har ya manta da mitsiyaci take kiransa,ko matacce dan tace talaka matacce ne mai kud'i ne rayayye,fusge kud'in yayi daga Hanunta yace "ina ruwanki da kud'ina nifa kidaina shiga hark'ata tunda bakida mutunci,yanzu ke bakiji kunya ba da kika dawo,ai na d'auka inkika tafi babu abinda zai dawo dake sai gashi babu kunya babu tsoron Allah kin dawo sabida kayan abinci,ai kayan abincin zasu kare ne,insun kare sai ki tafi gidanku,sanan wanan uban kwan da kika debo duk ayau zaki soya acinye gabad'aya"?



Fateema ranta bak'aramin b'aci yayi ba da maganganun da ya fad'a mata amma sabida kud'in da ta hango a hanunsa yasa ta dane b'acin ranta tace "nifa ba Dan kayan abinci na dawo ba ni banma San ankawo kayan abinci ba,Baffa ne yadawo dani,kuma ya min fad'a kwai kuma naga mun Dade bamu ci ba shiyasa na d'ebo dayawa Dan kowa yaci ya koshi" tsaki Bashir yayi zai rab'e ta gefenta ya shiga d'aki yaji anyi sallama awaje, juyawa yayi ya nufi k'ofar gidan yana amsa sallamar,d'aya daga cikin Wanda ya kawo musu kayan abinci ne yake sallama hanunsa rik'e da wani ghana must go Dan madaidaci,mik'a mishi Ghana d'in yayi yace mishi Alhaji Ahmed ne yace ya kawo mishi,Bashir hannu yasa ya k'arbi Ghana must go d'in yana mamakin mai kuma Alhaji Ahmed ya bayar a kawo masa, godiya ya mishi yace ya gayawa Alhaji Ahmed yana mishi godiya, d'aukar Ghana d'in yayi ya shiga ciki,a lokacin Fateema ta gama kwashe dankalin tana soya kwai,ganin Bashir da tayi da Ghana must go ya shige d'aki ne yasa ta juya kwan dasauri ta ajiye farantin tana kashe risho ta nufi d'akin,Bashir kuwa yana shiga d'akin ya bud'e Ghana d'in,shadda da yadikane aciki dinka ku gasu a goge sai kamshi suke,Bashir zaro su ya fara yi,daga Ghana yana ajiyesu akan gado,zuciyarsa fal farinciki,Dan yana cikin rashin sutura na kaya,kayansa baifi kala biyu ba suma duk sun kod'e shadda kala biyar yadi kala biyar haka Alhaji Ahmed ya aiko mishi dash,har da takalmi mai kyau da tsada guda biyu,ahaka Fateema ta shigo ta same shi yana dad'aga kayan sai murmushi yake.


Fateema itama washe baki tayi ta zauna a gefensa tana "Masha Allah gaskiya Alhaji Ahmed yana da kirki,Allah ya saka mishi da alheri kamar yasan bakada kaya,wanda kake dashi duk sun kod'e anjima idan mun gama cin abinci ma shiga mu da yara muyi musu godiya" Bashir shaddar da ya kara a jikinsa ya ajiye yace mata "ya kamata" fuskarsa a d'aure jikin Fateema ne yabi yayi sanyi data ga yanda Bashir yake d'aura Fuska da alama dai bazata samu abinda take so ba ganin yana kwashe shaddar yana mayarwa cikin Ghana d'in ne yasa tace " Abban Aliyu wai yana ga kana wani d'aura Fuska ne Dan ka samu kud'i ko wani abun nayi ma"?


Bashir wani mugun kallo ya mata yace "nima bangane yanda kika kwantar dakai kina min magana ahankali ba,ki kirani da mitsiyacina mai robobi,ki min magna a tsawace dashi na saba"




Fateema tuni taji ranta ya b'aci tace mishi " ooo Bashir tun ba'aje ko ina ba kafara neman ka wulak'antani akan ka d'an samu kud'i,lailai Allah yasan manufar jaki da bai yi shi da kaho ba Dan da kana da kud'i Allah ne yasan irin wulak'antancin da zaka yi,dadin abunda dai mak'ota ne suka taimaka maka kuma asanadiyata ba kai ka nemo kud'i ka kawo mana kayan abincin ba" Bashir tsaki yayi yabar mata d'akin ya nufi band'aki dan yayi wanka,mik'ewa tayi ta koma kitchen tana surutai kamar dai yanda ta saba,flask d'in Bashir ta samu ta zuba mishi dankali da kwan,ta K'wallawa Hameeda Kira tace tazo ta d'auki sauran dankalin ta kai musu Palo,atakaice tare suka ci dankali da kwan,suka sha shayi mai kaurin gaske,duk cinsu aranar sai da suka ture sauran dankalin, Bashir kuwa daya fito daga wanka ko kallon dankalin da ta ajiye mishi a d'aki bai yi ba dan ji yayi Sam baya jin yunwa,shiryawa yayi cikin wani yadin da Alhaji Ahmed ya aiko mishi dashi yayi masifar kyau,dubu d'aya ya kirga a kud'in da aka bashi kyauta yafito waje,a tsakar gida ya samesu azaune, tunda ya fito Fateema ta zuba mishi ido dan wani kyau taga yayi ya k'ara zama saurayi,shi kuwa Bashir d'aura Fuska yayi sosai ya isa inda suke ya mik'a mata dubu dayan jiki na rawa ta k'arbi kud'in ta fara kirgawa ganin dubu d'aya ya bata yasa ta mik'e da sauri tabi bayansa,dan yana bata kud'in ya juya,"Bashir ya zaka bani dubu d'aya bayan uban kud'inan Dana gani a Hanunka," Bashir ko juyowa bai yi ba ya fice daga gidan, Fateema juyowa tayi ta koma ciki tana dura mishi ashar,Aliyu ta bawa d'ari hud'u tace ya siyo musu nama miya yau dadi zasu ci,atakaice Fateema sabida samun guri,girki tayi wajen kala uku dan tace yanda suka Dade suna cin tuwo da yar Hausa dole yanzu suci abinda ransu keso tunda yanzu suna da kayan abinci,sai da yamma ta shiga gidan Khadija dan tayi mata godiya,bayan sun gaisa Khadija tayi mata ya mai jiki, Fateema ta fara yi mata godiya na sunga abin alheri,Khadija mik'ewa tayi tace zata bar mata palon indai bata daina mata godiya ba,da haka suka dan fara hira,khadija ta fara mata Nasiha na ta girmama mijinta ta daraja shi ta nemi yafiyarsa dan bata kyautawa mijinta ba ,naseeha da wa'azi Khadija ta ringa yiwa Fateema sosai,Fateema kuwa ta ringa gyad'a kai kamar gaske nan kuwa yana shiga kunenta na dama ne yana fita a kunenta na hagu,sai wajen biyar ta baro gidan Khadija ta koma gida,tana zuwa gida ta tarar masu wiring d'in har sun gama sun had'a musu kayan kallo,su Hameeda kuwa tsabar murna kamar su shige cikin plasmar,Fateema ita cikin murna ta zauna a tsakiyarsu suna kallo,kiraye kirayen sallahr Magirba ne yasa ta mik'e ta nufi kitchen dan ta d'ora girkin dare duk da abincin da suka yi da rana yana nan dayawa bai kare ba.





Bashir kuwa yana isa shagonsa ya raba kud'in hanunsa gida biyu,yasa rabi a aljihunsa ya d'auki sauran Rabin,ya fara bin 'yan uwansa marasa k'arfi da suka Fishi talauci yafara raba musu dubu d'ai d'ai dan su sai su fi wata d'aya basu rik'e Dari biyu ta Kansu ba,dan su abinda suke siyarwa bai fi na naira d'ari biyun ba,godiya suka ringa mishi suna mishi addua dan acikin Wanda ya bawa kud'in akwai Wanda ya baro gidansa babu abinci,Bashir kuwa farinciki ne yabi ya ishe shi yau shima yasamu abinda ya taimaki wasu har suna mishi addu'a ahaka ya wuni a shagonsa cikin tsantsar farinciki,gashi aranar ba laifi yayi cinikin robobi sosai dan sai da ya k'ara saro wasu da kud'in da ya rage awajensa.

Bashir bashi ya dawo gidan ba sai wajen k'arfe Tara na dare tunda ga waje yaga alamar wuta a gidan,wani farinciki ne yabi ya rufeshi,dan Rabonsu da wuta a gidan tun lokacin da nepa suka yanke wutan,sanadiyar basa biya,wajen shekara biyu kenan,a palo ya tarar dasu Fateema suna kallo,Nura dake barci da wuri shima idonsa biyu,sannu da zuwa suka mishi Fateema kua ta d'auke kanta kamar bata Ganshi ba,juyawa yayi yabar palon ya koma d'aki,sai da ya cire kayan jikinsa ya janyo farantin da aka d'ora kulollinsa akai,bud'ewa yayi yaga tuwon semovita ne da miyar danyen kubewa har da bushashen kifi,da sauri ya wanke hanunsa yafara loma dan rabonsa da irin wanan cimar har ya manta sai da ya cinye tas bai rage komai ba ya wanke hanunsa ya d'auki kulolin ya kai kitchen har zai fito daga kitchen d'in idonsa ya sauka akan indomie mai uban yawa,a wani kwanu,bakuma a rufe ba,mamaki ne ya rufeshi ya sunkuya zai d'auki indomie, yaga wani kwanu shima a rufe bud'ewa yayi yaga shinkafa da miya ne ya ishi mutane hud'u suci har da ragowa,ji yayi ransa ya masifar b'aci,kwanuka biyun ya d'auka ya fito waje ya hau k'wallawa Fateema kira,Fateema kuwa ganin kiran da yake mata bana hankali bane yasa ta mik'e da sauri ta fito ta same shi,Bashir kwanukan hanunsa ya nuna mata yace " mai wanan"? Fateema sai da ta lek'a kwanukan ta yamutsa Fuska tace "abinci ne mana Wanda muka ci dazu da rana"

"Fateema yanzu abinci har kala biyu kika dafa sabida almabuzarranci,har yayi wanan ragowar Wanda idan kika dumame ya ishe mu muci daddare har mu bawa almajirai sauran,amma duk da ragowar abincin ranar sai da kika kuma girkin dare"



Fateema wani kallon up and down tayi mishi tace "to akan an dafa abinci da yawa dan muci mu koshi shine kake wani tada jijjiyoyin wuya kamar kud'inka kasa ka siya,shinkafa da doya mukaci da rana,dazu kuma na dafa mana indomie da muka ji yunwar yamma, haka kawai sai muki ci mu koshi muna kallon kayan abincin yaushe rabon mu da irin wanan abincin ai inaga tun Aliyu na jaririr,su Aliyu ma kuwa basu tab'a tasowa sunga wanan cimar a gidansu ba sai dai su gani a gidan mak'ota,dan haka dan na dafa dayawa suci su ture karka ga laifina"



Bashir mamakin kalamanta ne yasa ya kasa magana can ya d'aure yace "ke yanzu idan haka kike dafa abincin mai uban yawa kuci Ku zubar da sauran ai abincin saurin karewa zai yi,kuma da kuka rage ai sai Ku bawa almajirai sauran abincin,da ki bar abincin a bud'e gobe da safe ki zubar"

"To kuma kawai dan muna gudun abincin kar ya kare sai muk'i ci mu koshi,ko ya kare abincin ba sai ka siyo wani ba,nidai kam girki mai yawa zan ringayi yanda yayana zasu ringa ci su koshi"

Juyawa tayi ta nufi Palo tabarshi a tsaye da kwanu a hannu,Bashir girgiza kai yayi,ya hanyar waje da kwanukan dan ya samu almajirai ya basu abincin.




Daddare bayan sun kwanta wajen k'arfe goma sha d'aya na dare,Fateema sai juyi take ta kasa barci shi kuwa Bashir tun goma da rabi barci yayi awon gaba dashi,juyawa tayi tana kallon Bashir dake barcinsa cikin kwanciyar hankali,tak'ara jin wani masifaffar sha'awarsa na taso mata,dan tun yamma ta ringa jin wani feelings,rasa yanda zata yi ta tashe shi tayi dan da kunya ma tace ya biya mata bukatarta,dan wata wajen d'aya da rabi kenan yana binta ta bashi hakkinsa tana k'i tundaga lokacin data ce mishi sai ya ringa siyo mata kayan Dadi zata na bashi hakkinsa bai k'ara nemanta ba ko da wasa,dabara ce ta fad'o mata ta mirgina kusa dashi ta rungumeshi kamar barci ne yasa tayi hakan bata sani ba,Bashir jin da yayi an rungumeshi kamar a mafarki ne yasa ya bud'e idonsa da sauri ya mik'e ya tureta daga jikinsa yana "ke ki gyara kwanciyar mai haka"?


Fateema bud'e idonta tayi ahankali kamar mai barci ta matsa daga kusa dashi ta koma ta kwanta,Bashir sai da yaga ta matsa daga kusa dashi shima ya koma ya kwanta,Fateema kuwa dan rungumeshin da tayi
Hankalinta ya k'ara tashi juye juyen ta fara yi ta rasa inda zata sa kanta wani dabara ne ya k'ara fad'o mata ta mik'e ta ta fad'a jikinsa tana ihu,Bashir a firgice ya tashi ta kuwa rungumeshi gam jikinta na rawa, Bashir janye jikinsa yayi daga nata dan duk abinda zai sa hankalinsa ya tashi ba so yake ba," ke wai me haka ne"?



Fateema k'ara matsawa ta farayi jikinsa tana "wlh wani abune yake tsoratani tundazu "


"Mai wani abunda ke tsoratakin"?

Fateema rasa amsar da zata bashi tayi can dabara ya fad'o mata k'ofa ta kalla ta sa ihu ta fad'a jikinsa ta rungumeshi tana shafa k'irjinta a nashi da yake d'aurin k'irji tayi ba komai a jikinta,k'ofa ta ringa nuna mishi da hanunta tana " kaga abun can a bakin k'ofa," Bashir amatsayinsa na lafiyayyen namiji tuni jikinsa ya amsa abinda tayi mai amma sabida wulak'ancin da ta mishi yasa yayi sauri ya janye jikinsa daga nata ya mik'e yana " ni fa banga komai a d'akinan ba haka kawai kin hanani barci,idan tsoro kike ji ki tafi d'akin su Aliyu ki kwanta in kuma bazaki je ba bari na kira miki Hameeda ta tazo ta tayaki kwana,ni na kwanta a Palo," Fateema ganin da gaske yake har ya isa bakin k'ofa ne yasa ta duro daga kan gadon ta sha gabanshi ta kau da kanta tana "wasa nake ma babu wani tsoro danake ji Hakkina zaka bani"


Bashir gyara tsayuwarsa yayi sosai yace "mai kikace,k'ara maimaita abinda kika ce"


Kunya ne ya rufe Fateema ta k'ara cewa " Hakkina zaka bani"


Dariya Bashir ya kyalkyale dashi yace "na fara siyo miki madara da tsire ne da zan baki hakkinki, ai nima na dade da daina sha'awa tun lokacin da kika ce min sai na ringa siyo miki kayan dadi kafin ki bani hakkina,tuni na maidaki tamkar namiji d'an uwana bana jin sha'awarki ko kadan ballantana na baki hakkinki,ki jika kayan ki kisha nima bana so, bazan iya ba"


Yana gama magana ya fice ya bar mata d'akin,Fateema zubewa tayi akasa dan bakinta ya yanke mata wuya gashi tana cikin wani irin hali,ahaka ta raba dare tana juye juye dak'yar barci yayi awon gaba da ita, Bashir kuwa yana barin d'akin a Palo yayi shimfid'a ya kwanta zuciyarsa fal farinciki dan banza banza shima ya rama abinda tayi mishi.


Wasa wasa sai da sukayi sati biyu Fateema na bin Bashir ya bata hakkinta shi kuwa ya ringa gwara ta yana gasa mata magana tamkar dai yanda take gasa mishi magana,sai da yaga dai dagaske idan bai bata hakkinta ba zata iya shiga wani hali dan har kuka take mishi kafin ya bata hakkinta duk da shima d'auriya ce yake yi shima a matse yake.



Tunda Fateema ta shiga gidan Khadija ta mata godiya bata k'ara komawa gidan ba,tun khadija na aikawa taji ko lafiya mai yasa bata shigowa har ta gaji ta daina aikawa,Fateema kuwa daina shiga gidan Khadijar tayi sabida tana ganin abinda yasa take shiga gidan kullum dama sabida abincin ne,tunda yanzu suna dashi bata ga abinda kuma zata shiga gidan tayi ba.


B'angaren ita da Bashir kuwa yanzu kullum cikin fad'a suke dan Fateema Sam bata iya tattali ba,sau hud'u take dafa abinci a rana,abincin ma inta tashi dafawa mai yawan gaske take dafawa,Wanda ko Rabin rabinsa bazasu iya ci ba, kuma in yayi ragowa ba zata bawa almajiri ba sai dai washegari ta zubar, madara da bournvita kuwa ya Dade da karewa ko sati biyu bai yi ba dan haka kawai zata d'ebo madara da bournvita ta kwab'a ta ringa sha,dai dai dasu Aliyu girki kala biyu take musu inzasu tafi makaranta,basa iya ma cinye kala d'aya sabida da yawa take zuba musu sai tace gwara 'yan makarantar su San yaranta suna cin dadi,Bashir kuwa ba dama ya mata fad'a yana mata magana zata mishi gori tace mishi ai ba shi ya siya ba,kuma ita dole ita da yaranta suci su koshi,ahaka rayuwa ta ringa tafiya kayan abincin ya ringa karewa, Bashir kuwa hankalinsa ne yafara tashi da yaga yanda kayan abincin suke dab da karewa dan yasan abinda yasa suke dan zaman lafiya bata biyoshi tana cin kwalar rigarsa sabida kayan abincin ne,abincin da Alhaji Ahmed ya aiko musu dashi indai Fateema tanada tatalli bata almabazarranci zai iya musu wata hud'u sai gashi ko wata biyu abincin bai yi ba ya kusa karewa.




Khadija kuwa tunda taga Fateema ta daina shigowa hankalinta ya dan tashi,da kanta ta shiga gidan,a Palo ta tarar dasu Aliyu suna kallo,tambayarsu tayi ina ummansu suka ce mata tana d'aki,Hameeda tacewa taje ta gaya mata tazo,Fateema da bata Dade da fitowa daga wanka ba,tana zaune tana shafa man da Khadija ce ta tab'ata Hameeda tana gaya mata sakon Khadija,taja tsaki tace taje tace mata barci take yi ita bata San takura,Hameeda kasa motsi tayi tace "umma ummansu waleed fa nace miki tazo tana kiranki"


Fateema harara ta watsa mata tace "Ummansu Waleed d'infa uwata ce kije ki fad'a mata barci nake yi"duk maganar da suke Khadija tana jinsu,tsananin mamaki ne ya hana ta tayi motsi dayake khadija irin matan nan ne masu masifaffen zuciya mik'ewa tayi a fusace ta nufi d'akin Fateema ta tsaya daga bakin k'ofa ta d'aga labulen tace "Fateema ai basai kin ce tace min barci kike ba,ai da dakanki kika fito kikace min na fitar miki daga gida bakya San ganina,ba laifinki bane ni nakawo kaina kike wulak'antani,na d'auka ke matuniyar kirkice dan Allah kike zaune dani Ashe ba haka bane,kina shigowa gida na ne sabida kwad'ayin abun duniya,amma yanzu tunda kin samu dole ke ma ki tattarani ki watsar ki nemi ki wulak'antani, ba komai Fateema ngd da abinda kika min insha Allahu bazaki k'ara ganin k'afata a gidanki ba" sakin labulen tayi ta fice ta bar gidan,Fateema kuwa suman tsaye tayi dan bata tab'a tunanin Khadija ta jiyo abinda tace ba,d'aga kafad'arta tayi irin ko a jikinta ta cigaba da shafa manta.



Khadija aranar kam har kukan bak'incik tayi na wulak'ancin da fateema tayi mata,kasa hak'uri tayi sai data gayawa Alhaji Ahmed abinda ya faru,hakuri ya bata yace watak'ila tayi mata wani abune bata sani ba,amma ta koma ta tambayeta gobe ko wani abun tayi mata dan yasan haka kawai bazata mata haka ba,Khadija jinsa kawai tayi amma aranta wani tsanar Fateema take ji.
*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*





*ALLAHUMA INNAKA AFUWUN TUHIBBUL AFUWA FA AFU ANNA*


*LA ILLA HA ILALLAHU WAHADAHU LA SHARIKALLAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHA'IN QADIR*



*RADITU BILLAHI RABBA WABI ISLAMA DINA*


*SUBHANALLAHI WALHAMDULILLAHI WA LAILLAHA ILAL LAHU WA LAHU AKBAR*



*DEDICATED TO AUNTY SIS ALLAH YA BARMIN KE YA RAYA SULTAN*💞💞💞💞💞



Page 25-30



Ahankali lokuta suka ringa shud'ewa wasa wasa su Bashir suka koma gidan jiya dan gabad'aya kayan abincin sun kare babu ko da k'wayar shinkafa,Bashir D'an kud'ad'en da ya Tara dasu ya siya musu kayan abinci kamar yanda ya saba shinkafa ce 'yar Hausa zai auna kwanu biyar,wake kwanu biyu,masara kwanu

Please Login or Register in order to submit comment