Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai aurenta, Bashir kuwa yana zaune a Palo yana ta jiran yaga Fateema tazo ta hura ice ta d'ora ruwan koko,amma har bakwai bai ga ta fito ba,tunani yayi da rigima take nema,hakan ne yasa yafito ya nufi gindin murhun ya fara k'okarin hura iccen,Hamida da sauri ta nufi gindin murhun tace ya kawo ta hura ta iya,cikin minti biyar Hameeda ta hura iccen ta d'ora ruwan kokon,Bashir d'ari biyu ya mik'awa Aliyu yace ya siyo kosai na d'ari da Hamsin,suga na hamsin,Aliyu k'arba yayi da sauri zai fice, Fateema da duk abunda suke yi tana jinsu,ledar kayan shayin nan da khadija ta basu ta d'auko tayi waje,tsayar da Aliyu tayi tace ya dawo,juyawa suka yi gabad'aya suna kallonta ciki har da Bashir da yasaki Baki yana kallonta cikin mamaki Dan bai San mai yasa ta tsayar da Aliyu ba,Fateema ta kalla tace " ke idan ruwanan ya tafasa juyo ki kawo mana d'aki musha shayi,dan yau bazaku sha koko da kosai ba,haka kawai koko da kosai na Neman yi mana tsiro idan shi bai gaji ba mu mun gaji,Aliyu maza maida mishi kud'insa Sumayya da Nura da gudu suka nufi d'akinta suna murna zasu sha shayi,Bashir tsananin mamaki ne ya hana yayi motsi ballantana akai ga yayi magana,Fateema ganin Aliyu da Hameeda basu motsa ba suna nan atsaye kamar an dasa su ne yasa ta d'aka musu tsawa tana su d'aurayo kofina su kawo su sha shayi,ta juya ta shige d'aki,

Bashir wani irin bak'inciki ne ya rufe shi,ya juya ya kalli su Hameeda dake mishi kallon tausayi, yace suje su sha shayin kar su makara daga haka ya mik'e ya nufi Palo ya zauna ya buga tagumi yana tunanin yanda Fateema take shuka mishi rashin mutunci iri iri sabida kawai bashi da kud'i,abokinsa ya tuna Salisu jiya da yamma dayazo yana bashi labarin irin taimakon da matarsa take mishi,ko bai ajiye ko sisi ba zata yi 'yan dabaru tayi girki,yabon kyawawan halayyar matarsa ya ringa yi,yana cewa Bashir yana nan yana addua Allah ya bud'a masa,matarsa zata ji dadi Dan ta mishi hallaci arayuwa duk da mugun talaucin da yake fama dashi bai sa ta guje shi ba,shi kuwa take ya tuna fateema,ya tuna irin rashin mutuncin da take mishi har wani lokaci take bashi idan bai samu kud'i ba zata rabu dashi, Fateema kuwa bayan Hameeda ta ajiye ruwan zafi da kofinan mik'ewa tayi Dan ta lek'a Bashir ko yana tsakar gida dan burinta yaga had'in kaurin da yayanta zasu sha,ganin baya tsakar gidan ne yasa tayi tunanin yana Palo,dayake d'akunan falle falle ne d'akuna biyu Palo d'aya sai kitchen da band'aki,cewa su Aliyu tayi su d'auki ruwan shayin su tafi palo su sha,mik'ewa suka yi gabad'aya suka nufi palon,Fateema ta bisu abaya da ledar kayan shayin,shigowarsu ne ya katsewa Bashir tunanin da yake ,ya d'ago yana kallonsu,a yagance Fateema ta zauna a kusa da bashir tana bud'a ledar kayan shayin , bredin ta zaro daga ledar da peak na ruwa guda uku,sachet d'in bournvita guda biyar,ta ajiye akusa da bashir tace "kaga yau dai da shayi zamu karya,shayin ma mai kauri,mun gaji da shan koko da kosai,Dan Allah dubi summayya da Nura,sun kasa ma rufe bakinsu sabida murnar zasu sha shayi da madara,Ya kamata kasan yanda zaka yi ka ringa kawo mana irin wanan cimar,"Aliyu ne ya katse maganar da take yi yace " Umma muna yin latti fa ki", katse shi tayi da sauri tana dalla rufe min baki,makarantar gwamnati har wata makaranta ce da zaka ringa tsoron Latti,dalla wuce ka d'auko min wuk'a in hud'a wanan madara,Aliyu mik'ewa yayi yafita waje,Bashir dai yana zaune ya sunkuyar dakai baice komai ba dan shi kadai yasan mai yake Ji azuciyarsa,atakaice ahaka Fateema ta had'awa su Aliyu shayi mai kauri ta basu bread yanka biyar biyar, itama ta had'a nata tana sha tana gasawa Bashir magana,su Aliyu nagama shan shayin suka mik'e suka tafi makaranta,Bashir yana ganin sun fita ya jawo Fateema ya had'e hannyenta ya fara magana cikin b'acin rai "Fateema na gaji da wulak'ancin da kike min a gidanan,ina matsayin mijinki baki San darajata,baki San mutuncina ba,duk maganar da yazo bakinki fad'a min kawai kike yi anya kina so ki gama da duniya lafiya kuwa,? Kinsan kuwa sai kinbini sau da k'afa zaki samu aljanna nan hakkina dake rataye a wuyanki kink'i ki bani,sabida kawai ina talauci Fateema,Fateema a tunaninki,zan dauwama haka a talauci,a tunaninki Allah baya sane dani,? Yanzu idan Allah ya bud'amin bazaki ji kunyar abinda kike min ba,agaban yayana kiyi ta min rashin mutuncin da kika ga dama,Fateema fusge Hannayenta tayi da k'arfi taja da baya tana mishi wulak'antaccen kallo tace " ahaka zan bika sau a k'afa kana fama da mugun talauci,mai kake min da zan bika sau da k'afa ai wlh Bashir da ace nasan irin wanan rayuwar zan zo nayi a gidanka wlh da bansoma auranka ba,kaf kawayena babu koma baya kamar ni, ni a tarihi ma ban tab'a jin talauci irin naka ba,babu abinda ka iya da ya wuce ka kawo mana 'yar Hausa da garin massara kazo kana bubud'a hanci wai nan ka siyo kayan abinci,in dare yayi ka wani matso wai na baka hakkinka,bazan bayar ba mai robobi indai hakkinka kakeso ka ringa siyo min kayan dadi,ina ci amma kuwa matsawar ba ka siyomin komai ba wlh bazan tab'a bayarwa ba kuma wlh ina k'ara sanar dakai kasan nayi tun wuri idan bahaka ba wlh gidanmu zan tafi kaji na gaya ma,Bashir tunda ta fara magana yake girgiza kai zuciyarsa na masa suya,cewa yayi "idan nafa ra bin matan banza awaje Fateema karki ga laifina," wani irin shewa Fateema tayi tace " wacce ma zata yarda ta bika kana fama da talauci,ai sai da kud'i matan banzan zasu yarda su bika mai robobi,gwara ma in mafarki kake yi ka farka,inkana da kud'i kaji dadi,in baka da shi kuma kasha bak'inciki ni kaga tafiyata barci nake ji wanan had'in kaurin da nasha yasa ina jin barci,kai kuwa kaje ka sha kokonka da kosai kayi ta tsulla fitsari," Fateema tace ta bar palon, ta bar Bashir a zaune baki asake,atakaice ahaka Bashir ya fito daga gida ya nufi shagonsa bayan rashin mutunci iri iri da Fateema tayi mai kamar jiya akan dai ya ajiye d'ari uku ayi cefanan rana da dare.


Fateema yanda dai ta Saba yana fita take fita itama ta nufi gidan Khadija,kwalliya tayi sosai da doguwar rigar material d'in da Khadijar ta bata,ta yafa mayafi ta shiga gidan khadijar tana gab da isa palon khadija,khadija ta fito zata raka wani yayanta da ya dawo daga tafiya ya biyo su gaisa,murmushi khadija tayi lokacin da taga Fateema tace ta shiga daga ciki tana zuwa tayi rakiya tadawo,Fateema to tace tana gaida yayan Khadija ta shige palon,bayan minti biyar da zamanta a Palo tana sana'ar tata ta kalle kalle,khadija ta shigo da sallama tana dariya,sai da ta kawowa Fateema abun da zata sa abakinta tukuna ta zauna suka gaisa still Khadija a lokacin dariya take,Fateema tambayarta tayi da wai dariyar mai take ne khadija tace "Wlh yayana ne yabani dariya,gaskiya kinyi kyau Fateema ba karya wlh baki ga yanda kayan nan ya amsheki ba,Ashe haka Jan Abu ke miki kyau aikuwa ina da wasu jajjayen kayan zan k'ara miki ki cigaba dayiwa oga kwalliya " murmushi Fateema tayi dan arayuwarta tana so ace tayi kyau,dan ita mace ce ma'abociyar San ado da kwalliya sai dai kash mitsiyaci take aure, bazai iya siya mata koda hoda ba ballantana akai ga sutura,cewa tayi " khadija bar zugani dan Allah ni banyi wani kyau ba," murmushi khadija tayi tace " wlh dagaske nake baki ga kyaun da kika yi ba dan bakisan dariyar ma danake ba,yayana ya d'auka ke buduruwa ce shine yace min wanan fa nace mishi tab ai ke tsohowa ce da auranki da yaranki hud'u danki na fari ma zai yi sha uku,jikin acuci ne dake", Fateema wani irin farinciki ne ya rufeta take shaidan yafara ingizata akan ta sako bashir a gaba ya saketa dan tasan indai ya saketa tabbas zata samu mai kud'i ta aura tunda gashi ma yayan Khadija ya d'auka ita ba matar aure bace,tuni tayi amanna da wanan tunanin nata, a filli kuwa murmushi kawai tayi bata ce komai ba,ahaka dai suka ringa hira da khadija kamar dai yanda suka saba tana gab da kammalla girkin rana Fateema tayi mata sallamar ta tafi gida dan tasan za'a biyota da abincin.




Tundaga lokacin Fateema ta sako bashir agaba rashin mutuncin yau daban na gobe daban bata girmama shi ko kad'an agabansu Aliyu zata yagashi taci mishi mutunci,in dare yayi ma bazata barshi yayi barci ba haka zata tayi mishi gori tana zaginshi,abinci kuwa ta dade da daina girka mishi,Bashir tuni yafara rama sabida rashin kwanciyar hankali,har fargaba yake yazo gida,inkuwa yazo gida yayi ta Allah Allah kenan gari ya waye ya fice daga gidan,in yana tafiya ahanya yayi ta surutai kamar wani mai tab'in hankali,nan kuwa tsabagen tension ne,Fateema kuwa tasan salo salo datake tana maula a gidan khadija,Khadija dayake mai bayarwa ce bata tab'a gajiya dasu ba,idan ma fita zatayi ta kan aiko musu da d'anye tace su dafa, kayan yaranta su waleed,kayansu da ya d'an tsufa da basa sawa bawa Fateema take yi dan 'yaran nasu kusan sa'anine,ahaka Bashir ya cigaba da Hakuri da fateema bai tab'a tanka mata ba,k'arfi da yaji ya maidata mahaukaciya sai dai ta k'araci banbaminta ita kadai,Fateema kuwa ta d'orawa kanta balain sai Bashir ya saketa, tunda ga lokacin da khadija tace mata yayanta ya d'auka ita buduruwa ce tasan indai suka rabu zata auri mai kud'i.


Watarana Nura autan ta bashida Lafiya aranar bata shiga gidan khadija ba sabida tana jinyarsa,Khadija kuwa jin da tayi shiru fateema bata shigo ba yasa ta aiki 'yar aikinta ta tambayo mata ko Lafiya fateema yau bata lek'o ba,Fateema fad'awa 'yar aikin khadija tayi abinda ya hanata shigowa aikuwa fitar 'yar aikin da minti goma sai ga Khadija ta shigo gidan lokacin k'arfe biyar na yamma,kujera 'yar tsuguno Fateema ta d'aukowa khadija ta zauna,suka gaisa khadija ta tambayeta ya mai jiki, Fateema cewa tayi da sauki a lokacin da take k'ok'arin mayar da k'wallan dake Neman zubo mata dan acikin yaranta tana masifar San Nura bata San ko kud'a ya tab'a shi,Khadija Hannu takai ta tab'a jikin Nuran takuwa ji zafi zau,d'auke hanunta tayi dasauri tana "subhanallahi Fateema kun kaishi asibiti kuwa",

Fateema da dama kiris take jira ta fashe da kuka,kuka ta fashe dashi tana "ina fa muka je asibiti,ko magani bai sha ba mitsiyacin ubansa tun safe ya fita yace zai nemo kud'i asiya mishi magani tun safe ban ganshi ba,burinsa dama ya kashe min 'yay'a wlh ni nagaji da auren mutumin nan wanan masifa Dame tayi kama ace kud'in magani ya gagari Bashir,abinci ma dak'yar muke ci,gidan nan yanda kika San aciki aka hallici sauraye,ba dole d'ana ya kamu da zazzabin cizon sauro ba" tunda tafara magana Khadija ta saki baki cikin tsananin mamaki tana kallon Fateema ba wani Abu bane yasata mamaki kamar yanda fateema ta ringa zagin mijinta,


"Haba fateema da iliminki da komai kike zagin mijinki akan bashi da kud'in siyan magani haba fateema wlh idan akace min zakiyi haka karyatawa zanyi,haba dan Girman Allah miji ai ba wasa bane kika sani ko kud'in ne bai samu ba shi yasa kika ji shiru,tunda safe mai yasa baki zo kin fad'amin ba,gaskiya fateema baki d'aukeni yanda na d'aukeki ba dan da kin d'aukeni da tuni kin aika an fad'amin na aiko miki da kud'i in ta kama ma na turo driver ya kai Ku asibiti," fateema share hawayen dake tsere a kumatun tayi tace "haba Khadija da gajiya wlh dole ki gaji damu zan iya ce miki kece cinmu da shanmu,nan sutura ke kike bamu nida yarana,shekara goma sha biyar muna cikin tsananin talauci,bamu da abinda muke ci daya wuce koko da kosai,tuwon massara da shinkafa 'yar Hausa,yarana suna dawowa daga islamiyya sai dai su tafi makota suyi kallo,bamuda kayan kallo,ko wutan ma babu a gidan,kullum a duhu Muke,Khadija sai ki ga laifina dan na zagi Bashir"

Fateema tace tana k'ara fashewa da kuka,tausayin fateema ne ya lullub'e khadija tace " duk da haka Fateema bai kamata ki zageshi ba addua ya kamata ki taya shi dayi, Allah ya bud'a masa dan bashi ya d'orawa kansa talauci ba,wlh ahaka kunfi wasu nesa ba kusa ba dan Y🅰TSUN MU BA D'AYA BANE KAFI WASU WASU SUN FIKA,wlh wani ma fateema bashida inda zai kwana,Ku kuna ma ci sau uku arana,wlh wani yana can bashida cin yau ballantana na gobe ,mijinki yana k'ok'ari duk da halin da yake ciki zuciyarsa bata mutu ba yana nan yana Neman halal d'insa kuma Allah maji rok'on bawansa ne yana sane daku" Bashir ne ya shigo gidan a d'an guje da paracetamol a hannu dan tun safe da ya fita baiyi cinikin komai ba babu irin kud'in da bai nema ba bai samu ba,yanzu haka bokitansa wajen shidda
Ya bawa mai chemist kafin ya yarda ya bashi maganin.


Khadija ce kawai ta amsa sallamar da yayi,Fateema wani mugun harara ta watsa mishi ta cigaba da goge wa Nura jiki da ruwan sanyi,Bashir gabansa ne ya d'an fad'i da yaga khadija a zaune dan yasan fateema tsaf zata yaga shi agabanta aikuwa bai gama tunanin da yake ba fateema tace " kayi asara wlh bashir,ace dan cikinka bashi da Lafiya ka kasa siya mishi magani haba wanan talauci dame ya yi kama,"khadija cikin tashin hankali ta daka mata tsawa tace " fateema kinada hankali kuwa mijinki kike zagi, Ashe haka kike " Bashir da ji yake dama kasa ta tsage ya shige,sunkuyar da kansa yayi zuciyarsa na mugun tafasa bai tab'a tunanin rashin mutuncin Fateema ya kai tayi mishi wulakanci agaban mak'otansu ba,Khadija hak'uri tafara bawa bashir,Bashir ya d'ago a kunyace yace babu komai,wurinsu ya nufa ya tsaya daga gefe yana k'ok'arin tab'a jikin Nura,Fateema d'aukeshi tayi da sauri tana "ka barshi kawai ya mutu tunda dama abinda kake so kenan" ta shige d'aki tana kuka,Khadija wani irin tausayin Bashir ne ya rufeta tace mishi " Abban Aliyu dan Allah idan ba zaka damu ba zan turo driver ya kaiku asibiti zan bashi kud'i Abban waleed baya nan ne da na biku dan Allah ka yarda akai shi asibitin kaga jikinsa yayi zafi dayawa bazai yiwu abashi magani off head ba,Bashir dan babu yanda zaiyi ne dan arayuwarsa yana Jan girmansa da talaucinsa bayaso yaga ya kai kukansa gurin wani ,akan dole yace mata to shikenan sun gode da sauri Khadija ta fita tabar gidan aikuwa cikin minti biyar sai gata ta dawo tace ga drivern awaje, suje su kai shi dak'yar ta shawo kan fateema ta yarda suka tafi dan dagewa tayi abar Nura ya mutu kawai tunda abinda Bashir yake so kenan.
*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_





*YA ALLAH KAJIQAN ANTY BILY, ALLAH KAGAFARTA MATA, ALLAH KA HASKAKA MAKWANCINTA, ALLAH KASHAYAR DA ITA RUWAN ALKHAUSARA, ALLAH KASADAMU A GIDAN ALJANNAH, ALLAH KAYIMATA RAHAMA DA SAURAN MUSULMI BAKI D'AYA😭👏*





*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞




*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*




Page 10-15


Drivernsu khadija asibitin da su khadija suke zuwa ya kaisu dan nan tace ya kaisu,aikuwa suna shiga ciki aka k'arbi Nura Dan khadija ta Riga da ta musu waya, a dogwayen bencina dake harabar asibitin Bashir ya zauna,Fateema kuwa sai zirga zirga take in sun had'a ido da bashir ta zuba mishi harara,Bashir kau da kansa yayi dan shi kadai yasan irin rashin mutuncin da zai mata in sun koma gida Dan Fateema ta kai shi bango talauci ai ba hauka bane,sai da suka samu minti 3O a zaune kafin Wata Nurse ta fito daga d'akin ta ruk'o hanun Nura,Bashir kuwa yana ganinsu ya mik'e Fateema itama wajensu ta nufa da sauri ta d'auki Nura tana tab'a jikinsa,Nurse d'in bayani ta fara yiwa Bashir da zazzafan zazzabi ne yake damunsa sakamakon cizon sauro,anyi mishi allura ga magunguna nan,su ringa bashi sau uku arana,sanan suyi k'ok'ari su ringa kwana a net dan gujewa cizon sauro,godiya Bashir yayi mata ya k'arbi magungunan yayi gaba Fateema sai da tabi keyarsa da harara tace "mitsiyaci sai wani hura hanci yake kamar shi ya biya kud'in maganin" duk abinda tace Bashir yana jinta girgiza kai yayi yana Allah Allah suje gida yaci uban ta Dan abinda tayi mishi agaban khadija ya masifar k'ona mishi rai,idan bai dau mataki akanta ba nan gaba ma k'ara yarfa shi zata yi agaban mutane,driver na parking Bashir ya sauko daga motar ya shige gida,Fateema kuwa sai data k'ara gyara zaman Nura a cinyarta tana jiran driver yazo ya bud'e mata k'ofar, dan tunda ta zauna agidan baya ta tafi duniyar tunanin itama wataran haka driver zai ringa tuk'a ta tana daga bayan mota,maganar driver ne ya dawo da ita tunaninta yana ta sauka mana sun iso,Wani kallo Fateema ta mishi tace ya sauka mana ya bud'e mata k'ofar motar baiga da yaro ahanunta ba,ko da babu yaro ai aikinsa ne,Iliya driver dayake shima dan ayi ne bud'a baki yayi yace "sai ki bari idan kin zama hajiya sai na ringa bud'e miki k'ofar mota amma ba daga cin arziki ki wuce gona da iri ba,Fateema wani mugun kallo ta mishi tace "zan fad'awa khadija abinda kayi min Mara mutunci kawai," bud'e k'ofar tayi ta fito tana zaginshi Illiya driver kuwa ya ringa mata dariya "yana samun wuri lailai Allah yasan manufar jaki da bai yi shi da kaho ba, da Fateema ce take da kudi da tayi wulakanci" ya ja motar ya tafi.




Fateema kuwa ahaka ta shiga gidan tana surutai ita kadai,A tsakar gida ta tarar dasu Aliyu a zaune,a gefensu kuwa wani katon kular ne da alama abinci Khadija ta aiko musu dashi da dan saurinta ta k'arasa wajensu ta ajiye Nura "Tana badai kun cinye abincin ba"? Babu Wanda ya kulata ayaran dan gabad'aya hankalinsu ya koma kan Nura suna mishi Sannu,da azama ta bud'e kular taga shinkafa da miya ne da naman Rago,Hannu ta tsoma a kular ta d'au nama yanka d'aya ta jefa abaki tana "nasan duk kun tsame naman kun cinye," Hameeda ce tace basu ma bud'e abincin ba tunda aka kawo suka ajiye,Fateema mik'ewa tayi tace " to nima bari nayi sallar nazo muci abincin,Autana ina zuwa bari nayi sallah nazo nabaka abinci kaci kasha magungunanka," Bashir yana shigo gidan ya wuce band'aki yaje ya d'aura alwala dan an Dade da iddar da magriba,yana zaune akan darduma yana jiran ayi kiran sallahr ishai ya nufi massallaci duk abinda Fateema ta ringa yi yana jinta girgiza kai kawai yake yana mai jin tsanar halinta aransa,Fateema d'akinta ta shiga bayan ta d'aura alwala ganin Bashir akan sallaya yana Jan carbi yasa tayi tsaki ta bar d'akin tana surutai.

Palo ta koma tayi sallarta agurguje ta fito ta zauna akan tabarma ta jawo kular tace wa Hameeda ta d'auko musu farantin su juye abincin,Hameeda mik'ewa tayi ta d'auko farantin da plate da spoon,ta ajiye,Fateema juya abincin tayi afarantin tana "wanan plate d'in kuma fa wa za'a zubawa a ciki" a dan tsorace Hameeda tayi kasa da murya yanda Bashir bazai ji mai tace ba, tace " Abba zaki zubawa abincin naga ba'ayi girki ba" Wani ashar Fateema ta kunduma mata Bashir yayi sauri ya runtse idonsa "bazan zuba mishin ba ya kawo ne da zan zuba mishi,ke da Aliyu na lura kun iya munafirci,ga itace can jeki had'a Ki d'ora mishi 'yar Hausa ina shi ina cin 'yar gwamnati munsamu 'yan arziki sun kawo mana abincin dan muci kar mu mutu da yunwa zaki Wani CE in zubawa Wani can ke tashi ma kibani guri yau bazaki ci abincin ba,kai kuma da ka tsareni da ido kana kallona idan bazaka ci ba kai ma tashi ka bani guri," Fateema tace tana hararar Aliyu, Hameeda da Aliyu mik'ewa suka yi ahankali suka nufi Palo ransu a mutuk'ar b'ace sun tsani wanan wulakancin da Ummansu take yiwa Abbansu,Bashir kuwa fad'ar bak'incikin da tafasa da zuciyarsa ke yi b'ata bakine dan tsabida tsabar b'acin rai jikinsa har rawa yake dan duk abinda Fateema tace yana jinta, mik'ewa yayi a fusace ko mai tuna oho ya koma ya zauna,kirayen kirayen sallah isha da ya ringa jiyowa yasa ya mik'e ya fita waje yana dab da fita ya jiyo muryar Fateema tana " haka dai babu ko sisi a aljihu sai aukin zuwa massallaci," Fateema abincinta taci ita da Summayya da Nura hankalinta kwance,ta bawa Nura magungunansa tana surutai ita kadai.



Khadija kuwa tun da ta koma gidanta take tunanin hanyar da zasu bi su taimaki Bashir,dan yau ya bata tausayi,Kawai sabida bashi da Kud'i Fateema take zaginsa bata tab'a tunanin Fateema bata da mutunci bata da hali ba sai yau,ita daya kamata ace ta ringa kwantar wa da mijinta hankali itace ma take tayar masa,haka kawai taji Hallayen Bashir ya burgeta duk da talaucin da yake hakan bai sa ya wulak'anta kansa yaje Neman taimakon wasu ba,Alwashi tasha na zata yiwa Alhaji Ahmed magana su San yanda zasu taimakeshi dan yana bukatar taimako,su suna nan hankalinsu kwance basu San mak'ocinsu na cikin Wani hali ba,ahaka Iliya driver ya dawo ya sameta sallamar da yayi ne ya katse mata tunanin da take,amsa sallamar tayi tana tambayarshi ya mai Jikin an kwantar da Nura ne ko an mishi Allura sun dawo,Illiya driver ce mata yayi tare suka dawo yana tunanin alluran aka mishi,mayafinta ta d'auka zata fita ta dubo Nuran ta jiyo horn d'in motar Alhaji Ahmed,komawa tayi ta zauna.


Sai da yayi sallah yaci abincin tafara gaya mishi halin da Bashir yake ciki,ta k'ara da ya kamata su taimakeshi dan yana bukatar taimako hakkinsu ne su taimaka mishi,anan ta k'ara gaya mishi irin wulak'ancin da Fateema tayi mishi agabanta sabida kawai bai kawo magani da wuri ba, Alhaji Ahmed girgiza kai yayi cikin tsanin tausayi yace ba komai zasu taimaka musu shi bai tab'a sanin su Bashir na cikin mawuyacin hali haka ba dan suna yawan had'uwa a massallaci su gaisa Wani sa'in ma tare suke fitowa daga massallacin kuma kafin su rabu yana fad'a mishi inda wata matsala dan Allah kar ya b'oye masa ya fad'a mishi,amma Bashir ce mishi yake yi babu wata matsala dan Wani zubin yana d'aukar kud'i ya bashi amma kememe zai k'i k'arba yace ya gode, Khadija cewa tayi yana hakan ne dan gudun wulak'anci ko raini,dan wasu masu kud'in suna da wanan amma abinda Bashir bai gane ba ba kowane mai kud'i ne yake da wulak'anci ba,ahaka suka ringa tataunawa a k'arshe Alhaji Ahmed ya tambayi Khadija dame dame ya kamata su taimakesu dashi,anan Khadija ta hau lissafo mishi abubuwan da zasu taimaka musu dashi.




Bashir kuwa daga massallaci kud'i yaje nema awajen abokinsa salisu dan yasan Hameeda da Aliyu basu ci ko mai ba dan su zai tafi neman kud'in amma in ta shine zai iya kwana da yunwa dan yama Riga da ya saba kwana da yunwar, ko da abincin ma bak'incikin da Fateema kawai take cusa mishi ya isa yasa ya kasa cin abincin,dak'yar ya samo d'ari uku awajensa shima d'ari shidda ce dashi rabawa suka yi,ahanya ya siyi bread dan hamsin hamsin guda biyu ya siyi ruwan shayi a gurin masu shayi ya nufi gida,a lokacin da ya shiga gidan Fateema har ta shige d'aki tayi barci,Aliyu da Hameeda kawai ya tarar a tsakar gida suna zaune suna Home work da fashashiyar touch light d'in da baya ci sosai sabida rashin battery, ganinsa da suka yi ne yasa suka mik'e suna mishi sannu da zuwa,amsawa yayi ya mik'a musu bredi da shayin,aikuwa da sauri suka k'arba dan dama yunwa suke ji,juye shayin suka yi a k'ofi suka zubowa Bashir, girgiza musu kai yayi yace ya koshi suci kawai, badan ransu yaso ba suka fara shan shayi da bredin dan sun San baici komai ba fad'i

Please Login or Register in order to submit comment