Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi.




Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya ayau aka d'aura auren Fateema da Isah driver aranar ta kuma tare har da su Haleema akai amarya gidan Isah driver maidaidaicin gida ne kayan da Bashir yayi wa Fateema shi ya taimaka gidan ya k'ara haskawa yafito yayi kyau duk da wasu kayan sai maidasu akayi sabida babu wajen da za'a ajiye su Haleema da suka zo tafiya fateema rungume su Aliyu tayi tana fashewa da kuka mai cin rai Haleema ce ta ringa rarrashinta da ta kwantar da hankalinta zata ringa kawo mata su Nura akai akai Aliyu Hameeda da sumayya da suka gane aure fateema tayi suma kukan suka ringa yi da k'yar Haleema ta rarrashesu ta banb'are Nura daga jikin Fateema suka tafi

Fateema bayan tafiyarsu Haleema tunani tafara yi na irin rayuwar da zata fara yi a gidan Isah driver da y'ay'ansa jikinta ne ya k'ara sanyi da tuna y'ay'an Isah driver dukansu y'an mata ne da kuma alamar bazasu amsheta amatsayin matar babansu ba dan tunda aka kawo ta ta ringa jiyo shewarsu babu Wanda ya lek'o yayi mata sannu Fateema tana nan azaune tana tunane tunane har k'arfe Tara na dare babu Isah driver babu dalilinsa bacci taji ya fara fusgarta hakane yasa ta kwantar dan dama bata da tsarki aikuwa tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita




Isah driver kuwa bashi ya shigo gidan ba sai wajen k'arfe goma sha d'aya na dare dan yana wajen majalisa yana hira dan akwai shi da zaman majalisa da sa ido sai ya kai k'arfe goma sha biyu amajalisa sai da ya kulle ko ina ya lek'a y'ay'ansa yaga uku sunyi bacci sauran ukun kuma na dane Dane awaya bai ce musu komai ba ya rufo musu k'ofar ya nufi b'angaren amarya Fateema


Motsin rufe k'ofar ne ya tashi Fateema daga barci tayi sauri ta mik'e zauna tana sunkuyar dakai
Isah driver cewa murmushi yayi yace " amarya amarya amarya kinsha kamshi Ashe har kin fara barci"

Fateema bata ce komai ba ta k'ara sunkuyar dakai Isah driver kuwa zama yayi agefenta yace


"Amarya kinga na manta shaf ban shigo mana da dan kayan ciye ciye ba sai dai kiyi hak'uri gobe zan siyo mana"



Fateema k'ara sunkuyar da kai tayi tana mamakin abunda Isah driver yace ya za'ayi yace ya manta bai shigo da komai ba alhalin sabon aure yayi jin hanunsa akafad'arta ne yasa ta d'ago da sauri suka had'a ido murmushi ya sakar mata yana "amarya hawo gadon sosai mana"


Fateema ganin ya fara k'ok'arin cire rigar jikinsa ne yasa tayi sauri tace "banida tsarki fa al'ada nake yi" nan da nan Isah driver ya d'aura fuska yace "al'ada kuma"?

Da sauri Fateema ta gyad'a kanta gabanta na fad'uwa sakamakon wani tunani da tayi na ko dai shima irin lado ne

Isah driver cewa yayi "gaskiya kin k'wareni ya za'ayi yau ina ango kice min al'ada kike yi gaskiya banji dadi ba"

Fateema bata ce komai ba inbanda rawa da jikinta ya ringa yi Isah driver jawo ta yayi yace " ko dayake bari na dan rage zafi ya zanyi" ahaka ya fara murzata sai da ya samu nutsuwa yarabu da ita nan da nan bacci yayi awon gaba dashi



Fateema tana ganin bacci ya d'aukeshi ta sauk'o daga kan gadon ta koma Palo ta zuba tagumi tana tunanin irin mijin da ta aura ita dai tasan bazata tab'a samun miji irin Bashir ba Sai dai kawai ta hak'ura ta zauna ahaka amma bawai dan tana jin dadin zaman aure ba.


Wata uku kenan da auren Fateema da Isah driver babu laifi tana samun kulawa daga wajen Isah driver matsalarta k'waya biyu ce yaran Isah driver sun rainata basa bata girma ko k'adan rashin mutunci suke mata kala kala dan dukansu babu 'yar shekara goma sha hud'u 'yar Isah driver ma ta fari tafi Fateema girma dan haka Fateema shak'arsu take sosai ita take musu girkin da zasu ci ko wanke wanke basa tayata ballantana akai ga shara ita take komai a gidan Isah driver kuwa shima kamar tsoronsu yakeji baya iya tsawatar musu idan suna mata rashin mutunci Fateema kam har gajiya ma take yi da kuka dan tasan komai aka yi mata ita tajawa kanta dan da bata rabu da Bashir ba da hakan duk bai faru ba matsala ta biyu da take fuskanta shine Isah driver yana da zafi da zuciya Abu kad'an zata yi ya rufeta da fad'a yayi ta fushi da ita ga zaman majalisa baya dawowa gida sai sha biyun dare har ta Riga da ta saba idan taga irin zafin zuciya da saurin fushin Isah driver takan tuno Bashir bawan Allah da Bashi da saurin fushi ko kad'an ga hak'uri nan ma takan yi kuka ta godewa Allah dan tasan ita ta jawo wa kanta abinda ke d'an faranta mata rai shine su Aliyu da Haleema ke kawo mata akai akai ganinsu da take yi yana sata farinciki babu abinda ta nema ta rasa arayuwarta dan Kud'in da Bashir ya ba ta ta juya tana 'yan sana'ointa ga kud'in da Haleema take bata indai tazo


Zaman gidan Isah driver ne yasa ta k'ara hankali tasan rayuwa dan Isah driver baya jure rainin hankali ko k'adan gashi da saurin fushi sai ayanzu ta gane ba kud'ine kwanciyar hankali da farinciki ba zaman lafiya ma da fahimtar juna yafi komai farinciki




Ahaka Fateema ta samu shekara biyu a gidan Isah driver abunda yasa ta d'an samu saukin matsalarta shine yaran Isah driver da suka fi d'aga mata hankali sunyi aure saura yaransa biyu Adnan d'an da ta Haifa da Isah driver yana da shekara d'aya da rabbi ta k'ara samun wani cikin.


B'angaren Bashir kuwa arzikinsa k'ara bunk'asa yake sakamakon yawan sadaqa da zakka dayake idan kaga Bashir ayanzu bazaka yarda shi bane dan ya zama dan lukuti jin dadi da kwanciyar hankali ya zauna masa har kasashen waje suke fita shi da y'ay'ansa Haleema kuwa ta zama bussiness woman har Dubai take zuwa saro kaya Bashir da Alhaji Ahmed kuwa zumunci suke sosai dan har ziyara suke kaiwa junansu asanadiyarsu Haleema da Khadija suka k'ula kawance Bussines d'in ma tare suke yi




B'angaren lado kuwa amaryar da ya auro bayan da ya saki fateema tana yin kwana biyu ya k'ara k'yallaro wata tsallelliyar dan duk acikin Matan da yake aura tafi su kyau aikuwa jiki na rawa ya dawo gida ya saki Ainau

Ainau a lokacin da ya saketa ji take kamar an mata bushara da gidan aljana aguje ta had'a kayanta ta d'auki d'anta suka bar gidan ji take kamar tayi tsuntsu ta isa gidansu


Lado sati biyu da sakin Ainau ya auro falmata Lado yana masifar san falmata dan duk amatan da yake aura tafi su dandano da juriya nan kuwa bai San falmata tsohuwar yar duniya bace tana ma d'auke da cutar HIV akan Falmata ya ringa wulak'anta sauran matan nashi tunda ya auro ta ya daina kulasu duk rowa da mak'o irin na lado bayayiwa falmata dan wani irin so yake mata tamkar wacce ta asirce shi Falmata kuwa nan tsabar duniyanci ne yasa ta siye zuciyar Lado falmata da siyasa da bariki tarunga sa shi yana sakin sauran matan nasa sai da ya zamana dagashi sai ita wata uku da aurota yafara rashin lafiya tun yana yi atsai tsaye sai da ta kai shi ga kwanciya mai gidansa ne ya d'au nauyin kai shi asibiti gwajin farko da aka masa aka gano yana d'auke da cuta mai karya garkuwar jiki Lado yanajin abinda likita yace ya suma ruwa likita ya yayafa mishi aikuwa yana farfad'owa ya saki ihu yana ya shiga uku ya lalace Falmata ta cuceshi atak'aice falmata guduwa tayi tabar lado amatsanacin hali Lado kuwa yaci kuka ya gode Allah take ya fara nadamar abubuwan da yayi d'aya bayan d'aya yabi matan da aura yaringa Neman yafiyarsu matan kuwa suka ringa godewa Allah dayasa suka rabu dashi bai sa musu cuta ba



Ahaka rayuwa ta ringa tafiya b'angaren Fateema ma ba laifi kullum cikin godewa Allah take dayasa ta gane gaskiya ta gane ba komai kud'i ke iya siya ba dan har ta koma ga mahallicinta bazata tab'a samun kwanciyar hankali da jin dadin da ta samu a gidan Bashir ba dan duk da tana da kud'i bata rasa komai ba ta rasa wani b'angare na rayuwarta ko ta fanin ma yaranta da basu taso agabanta ba.







Anan na kawo karshen novel d'in yatsunmu ba d'aya bane kuskuren danayi a ciki Allah ya yafemin darasin dake ciki Allah yasa al umma su amfana ina Neman yafiyar duk wacce na tab'a b'ata wa rai arashin sani thank you all for giving me the support


HEART YOU
*AUNTY SIS*
*UMMAN IRFAN*




Compiled by Princess Aysha Muhammad
Copied by Umar Dalha

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment