Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba

"Yaya nima rok'onka nakeso nayi akan ka maida Ummansu Aliyu d'akinta ko dan zuriar dake tsakaninku su Nura ma zasu so su taso agaban mahaifiyarsu kayi hak'uri ka yafe mata duk abinda tayi ma duk da bansan mai ya had'aku da ita ba ka dubi yaran dake tsakaninku kayi hak'uri ka maidata"


Tunda ta fara magana Bashir ya zuba mata ido har tagama maganar kallonta yake yi bai yi magana ba Haleema kuwa ganin shirun yayi yawa yasa tace

"Kayi shiru ko bakaji mai nace ba"

Murmushin k'arfin hali Bashir yayi yace " naji mai kikace mana"

"To bakace komai ba"Haleema tace tana ruk'o hanun Bashir

Bashir shima ruk'o hanunta yayi yace "naji abinda kikace sadiya amm inaso kisan wani abu da zan iya dawo da Fateema d'akinta da na Dade da dawo da ita bazan iya dawo da ita ba Haleema duk da bazan iya gaya miki dalilan da yasa bazan iya dawo da ita ba

Ni na zauna da Fateema nakuma San halinta ture ma abinda tayimin a gefe idan na dawo da Fateema gidanan wlh sai ta hanaki zaman lafiya muna zaman zaman mu batun yara da kike magana ai mutuwa na iya rabasu da mahaifiyarsu kinga dole su hak'ura dan haka kibar zancen nan"


Haleema ajiyar zuciya ta sauke tace
"Nidai kowane irin haline da ita ka dawo da ita d'akinta ballantana ma ina kyautata zaton babu abinda zai had'ani da ita idan kana ganin ma zata d'aga ma hankali idan ka had'amu waje d'aya sai ka raba mana gida dan Allah yaya ka dawo da ita dan nima ina sa kaina amatsayinta ne ka manta duk abinda tayi ma ka yafe mata kasan mu mata kwakwalwar kifi garemu bamuda zurfin tunani sai munyi Abu daga baya muke ganewa abinda mukayi ba dai dai bane Allah ma muna mishi laifi ya yafe mana dan Allah ka yafe mata ta dawo ta rik'e y'ay'anta dan yanzu inka k'i dawo da ita wlh wasu ni zasu ringa d'orawa laifi dan gani zasuyi ni na hanaka ka dawo da uwar y'ay'anka pls yaya"


Murmushin tak'aici Bashir yayi yace "Haleema kenan dan bakisan abinda Fateema tayi min bane shiyasa kike cewa na dawo da ita wlh abinda Fateema tayi min ba kowane namiji ne zai jure ba nidai na yafe mata amma bazan iya dawo da ita ba Haleema dan Allah kibar zancen nan"


Haleema hanunsa ta k'ara damkewa da k'arfi tana "nasan ai ka yafe mata burina kawai ka manta abinda tayi ma ka dawo da ita d'akinta yaya duk da bansan mai ya had'aku ba hak'uri ,zakayi dan y'ay'anka dan wasu mazan ma dan yaransu suke zaune da matansu dan da zakaga abinda wasu matan suke yiwa mazajensu suke hak'uri dasu dan yaransu zakayi mutuk'ar mamaki yanzu dan Allah idan su Nura suka girma suka ji labarin ka rabu da mahaifiyarsu kuma kak'i dawo da ita mai zakace musu in suka tambayeka?"


Murmushi Bashir yayi yace " zan fad'a musu abinda mahaifiyarsu tayimin nak'i dawo da ita yaran yanzu ma basu da mantuwa sosai Aliyu da Hameeda zasu ina gaya musu dalilin da yasa nak'i dawo da mahaifiyarsu zasu tuna abinda tayimin sadiya zan dai iya yafewa Fateema abinda tayi min amma bazan iya manta abinda tayi min ba dan har jibi abubuwan da tamin yak'i goguwa araina indai zan tuna sai naji tamkar ayanzu taringa yimin rashin mutuncin"

Magana haleema ke k'ok'arin yi Bashir ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu yace " pls Haleema kibar zancen nan haka matso kiyimin tausa na gaji"



Haleema zuba mishi ido tayi ganin he is serious ya d'aure fuska yasa ta matsa kusa dashi ta fara mishi tausan




Ahaka kwanaki suka ringa shud'ewa Fateema tabi ta rame sabida tunani duk sintirin da taringa yi tana zuwa gidan Bashir Bashir ko kallonta baya yi dan tun yana ma iya saurarnta har yakai ko ta zo baya saurarta haka zata k'araci zamanta dasu Hameeda ta tafi Haleema kuwa itama tana bala'in tausayin Fateema tun daga lokacin da tazo ta sameta akan ta tayata bawa Bashir hak'uri ta kuma bata labarin abubuwan da ta yi wa Bashir take jin tausayinta sosai kamar tayi mata kuka dan itama babu irin rok'on da bata yiwa Bashir ba akan ya dawo da Fateema d'akinta amma yak'i yace sai dai idan ana mutuwa a dawo Fateema kuwa data GA ba haza hak'ura tayi ta daina zuwa ta duk'ufa da adduar idan tana da rabon komawa gidan Bashir zata koma idan babu rabo kuwa dole ta hak'ura


Inna wuro kuwa babu yanda bata yi da Fateema akan suje gurin mallamai suyi musu addua ta koma gidan Bashir dan tun ranar da Bashir yasa driver ya kawo su Aliyu su gaisheta da buhun hunan kayan abinci da kud'i dubu ashirin hankalinta ya k'ara tashi ganin Fateema tak'i bata had'in kai suje wajen mallamai yasa ta fara zuwa ita kad'ai mallamai kud'in Inna Larai kawai suka ringa ci suna bata rubutu da kwalli akan Fateema tasha rubutun ta ringa sa kwallin Bashir zai maidata ta d'akinta Inna larai kuwa inta kawo rubutun Fateema bata sha dan tasan b'atawa kanta lokaci kawai zatayi inna wuro kuwa Fateema in tak'i sha ta yi ta surfa mata zagi kenan tana ce mata 'yar bak'inciki.


Pls Kuyi min hak'uri wlh nima na matsu nagama novel dinan ni ban ma tab'a novel d'in da ya Dade haka ban gama ba next page d'ina zan gama insha Allahu pls you guys should bear with meπŸ™πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™
*YπŸ…°TSUN MU*🀚🏻🀚🏻🀚🏻🀚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*


*WANAN SHAFIN NA DUK WANDA YAKE KARANTA YπŸ…°TSUNMU BA D'AYA BANE DA FANS D'INA MASU K'AUNATA ALLAH YA BARMU TARE DA BAZARKU NAKE RAWA*



*INSHA ALLAH AWANAN PAGE D'IN ZAN KAWO K'ARSHEN WANAN NOVEL D'IN YπŸ…°TSUNMU BA D'AYA BANE DARASIN DA KE CIKI ALLAH YA BAMU IKON AMFANA DASHI KUSKUREN CIKI KUMA ALLAH YA YAFE MIN*


*TSOKACI*



*READERS PLS INASO KU AJIYE SAN ZUCIYA A GEFE KARKU BI SAN RANKU ABINDA YASA NACE HAKA SHINE KOWA DA YANDA YAKESO NOVEL D'IN YA KARE WASU SUNA SO BASHIR YA MAIDA FATEEMA D'AKINTA WASU KUMA BASA SO BASHIR YA MAIDA FATEEMA D'AKINTA ABU D'AYA NAKESO KUGANE DARASIN DA LITTAFIN KE K'UNSHE DASHI DA KUMA WA'AZANTARWA DUK WACCE TAKE BIN NOVEL DINAN DAGA FARKO HAR ZUWA INDA NA TSAYA IN YA AJIYE SAN ZUCIYA AGEFE DAKANSA ZAI GA FATEEMA TA CANCANTA TA KOMA D'AKINTA KO BATA CANCANTA BA KARKU MANTA FATEEMA MACE CE MAI SAN ABUN DUNIYA DA RASHIN DARAJA AURE DA RASHIN SANIN DARAJAR MIJI FATEEMA MACE CE DA BATA DA GODIYAR ALLAH BASHIR BAI TAB'A HANA FATEEMA CI DA SHA BA AMMA ME AHAKA SAI DA FATEEMA TA RAINAWA K'OK'ARIN DA YAKEYI KARKU MANTA IS EASILY TO FORGIVE BUT HARDLY TO FOEGET QUIET OLRYT FATEEMA TA TUBA TAYI NADAMAR ABINDA TAYI AMMA FA DALILIN NADAMAR TA SHINE WUYAN DA TA SHA A GIDAN LADO NI NAYI IMANI DA ALLAH DA ACE LADO MAI KUD'IN NE FATEEMA BAZATA TAB'A WAIWAYAR BASHIR BA IDAN KUWA FATEEMA TA KOMA GIDAN BASHIR DARASIN LITTAFIN BAI FITO BA DAN ANUNAWA MASU HALI IRIN NA FATEEMA KODA SUN TSULA TSIYARSU ZASU IYA KUMA SAMUN ABINDA SUKESO KUMA WLH MASU HALIN FATEEMA NA NAN DA YAWA KARKA RAINA ABUNDA ALLAH YA BAKA INKANA GANIN WUYA KAKE SHA KA DUBI YπŸ…°TSUN HANUN MU ZAKU GA TSAYINSU BA D'AYA BANE IN WANI YAFIKA KAFI WANI HAKA RAYUWA TAKE ALLAH YASA MUDACE ALLAH YA RUFA MANA ASIRI DUNIYA DA LAHIRA MASU HALI IRIN NA FATEEMA ALLAH YA SHIRYESU SUGANE DAMA D'AYA CE INTA WUCEKA TA WUCEKA KENAN HAR ABADA*



Page 100πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š






Ahaka lokuta suka ringa shud'ewa kwanaki suka ringa zama watani shekara biyu kenan Fateema na sa rai Bashir zai maidata d'akinta amma shiru Bashir bai tab'a waiwaiyarta ba ko da taje gidan da sunan tazo ganin yara bata samun fuska a gurinsa

Inkuwa ta tunkareshi da maganar yayi hak'uri ya maidata d'akinta magana d'ayace dai yake k'ara jadada mata tayi hak'uri bazai iya maidata d'akinta ba Fateema tayi kuka tayi nadamar abinda tayi k'iri k'iri tana ji tana gani yaranta zasu zo mata weekends gidansu su kuma juya su tafi ganin dai dagaske Bashir yake ba maidata zaiyi ba yasa ta fara hak'ura addua taringa na Allah ya cire mata sanshi a zuciyarta dan haka kawai kuma Allah ya jarrabceta da sanshi


Inna wuro kuwa gajiya tayi da zuwa wajen mallamai dan ta gano kud'inta kawai suke ci kuma abin mamaki tana ta fafutukar Fateema ta koma gidanta ne sabida suma su ringa d'an samun abun arzik'i amma abun mamaki Bashir yana kyautata musu da kud'i da kayan abinci indai zai sa akawo su Aliyu sai ya had'osu da kud'i ko kayan abinci musamman ma yake ware kud'i masu d'an k'auri yace subawa Fateema Fateema kuwa hakan da taga yana yi ne yasa tayi tunanin wataran zai iya maidata tunda yana aiko mata da kud'i yana kuma kawo musu kayan abinci



Bashir kuwa yana haka ne kawai dan zuriar dake tsakaninsu da kuma zaman da tayi dashi a lokacin da bashi dashi har na tsawon shekara goma sha biyar


Baffa kuwa ganin suna samun abun arziki awajen Bashir duk da bai maida Fateema d'akinta ba yasa ya sako Fateema agaba da ta tsayar da wani acikin zawarawanta ta aureshi dan Bashir bazai tab'a maidata ba ta hak'ura kawai haka Allah yayi bata da rabon ta koma gidan Bashir


Fateema shawarar Baffa tabi ta tsayar da wani Isah driver dan shine kawai acikin zawarawanta bashida mata dan matarsa ta rasu sauran kuwa duk suna da mata Fateema bata San Isah driver Sam dan babu yanda zata yi ne kawai yasa zata aureshi kafin tace yafito sai da tasa akayi mata bincike sosai akansa dan tana gudun irin abinda ya faru abaya binciken da akayi mata ya nuna Isah driver matarsa ta rasu shekara biyu da suka wuce yana da yara shidda


Atak'aice cikin dan kankanin lokaci Isah driver yakai kud'in aurensa gidansu Fateema aka sa musu rana wata d'aya kacal ana saura sati biyu auren Fateema da Isah driver ranar wata asabar Haleema ta kawo su Aliyu gidansu Fateema da kayan arziki kamar dai yanda dai suka saba zuwa lokacin da suka zo Fateema na kwance a d'aki muryarsu Nura da taji a tsakar gida ne yasa tafito daga d'akin da sauri Nura aguje yaje ya rungumeta ita kuwa ta d'aga shi sama nan da nan kuwa hawaye ya zubo mata na tausayin kanta dan nan da sati biyu zatayi aure taje ta rik'e 'y'ay'an wani sauk'e Nura tayi k'asa ta nufi wajen Haleema dake tsaye da Irfan dan shekara d'aya a hannu k'arbar shi tayi tana musu sannu da zuwa Haleema amsawa tayi itama fuskarta d'auke da murmushi tausayin Fateema fal aranta dan indai zata ganta sai tausayinta ya rufeta dan dai babu yanda zata yi da Bashir ne ya maida Fateema dan tun daga lokacin da ta ringa rok'onsa akan ya maida Fateema alokacin da Fateema Tayi yayin zuwa gidansu Bashir yaja mata warning sosai akan duk lokacin da ta k'ara masa maganar Fateema sai ranta ya b'aci dan shi yasan da yayanta Fateema tayiwa abinda tayi masa bazata tab'a yarda ya maidata ba yace mata ai tana da yaya zata iya had'a Fateema da yayanta amma shi bazai maida Fateema ba matar da ta kashe shi da baki tun kafin ya mutu tundaga lokacin Haleema bata k'ara mishi zancen Fateema ba



Fateema tabarma ta shimfid'a musu suka zauna gaisawa sukayi fara yi da Haleema kafin ta juya ta amsa gaisuwar dasu Aliyu suke mata binsu tayi da kallo cike da sha'awar yaranta duk sun girma masha Allah ga ladabi da biyayya da suke dashi ta nan kam tana jinjina wa Haleema na irin tarbiyar da ta bawa yaranta da kuma yanda take kula dasu dan kana ganinsu zaka San suna jin dadi dan idan suka zo mata ita kad'ai takan bugi cikinsu taji ko Haleema na cin zalinsu


Inna wuro da ta fito daga d'aki tana yiwa su Nura wasa ne yasa ta dawo daga tunanin da ta tafi Haleema da sauri ta sunkuyar da kanta tana gaisheta duk da bata da tabbacin Inna wuro zata amsa Inna wuro d'auke kanta tayi kamar bataji gaisuwar da take mata ba dan ta masifar tsanar Haleema dan aganinta itace silar dayasa Bashir ya k'i maida Fateema


Fateema babu yanda batayi da ita ba akan ta dai na jin Haushin Haleema ba laifinta bane amma Inna wuro tak'i dan indai Haleema zata zo gidan bazata tab'a sakar mata fuska ba ballantana akai ga ta amsa gaisuwar da take mata


Fateema da ranta ya b'aci sanadiyar k'in amsa gaisuwar da Haleema tayiwa Inna wuro mik'ewa tayi ta rik'e hanun Haleema tace Mata ta taso su shiga daga ciki dan idan ba ciki suka shiga ba habaice habaice Inna wuro zata tayi


Haleema kuwa da sauri ta mik'e suka shiga ciki Inna wuro kuwa ta buga tsaki hanun Nura ta rik'e tana tambayarsa mai zata dafa musu su ci dayake inna wuro na bala'in ji da jikokinta suma su Aliyu suna jin dad'in yanda take wasan jika da kaka dasu anan kowa ya hau fad'ar abinda zaici





Fateema kuwa da suka shiga cikin d'aki d'an k'aramin fridge d'in da Inna ta siya da kud'in da Bashir ya ringa aiko musu tana siyar da pure water da kunun aya ta bud'e ta d'auko mata pure water da kunun aya Haleema murmushi tayi tana mata godiya adai dai lokacin da ta amshi ruwan da ta zuba mata a k'ofi


Fateema zama tayi agefenta ta d'auki Irfan tana mishi wasa cewa tayi "a ina kika baro Atif d'in baki zo dashi ba"?

Haleema k'ofin hanunta ta ajiye tace " yana gurin yaya dashi ya tafi kasuwa"

Fateema cewa tayi " Allah sarki kice Atif ya zama dan kasuwa"

Murmushi Haleema tayi bata ce komai ba Fateema magana ta fara yi "Haleema nafa samu miji nan da sati biyu masu zuwa za'a d'aura min aure"


Haleema cikin tsananin Farinciki tace "kai amma naji dadi Umman Aliyu Allah ya sanya alheri yanzu da bamu zo ba da bazaki fad'a mana ba sai dai kawai muji kinyi aure"?


Haleema mik'a mata Irfan tayi da ya fara rigima tace "ko Baku zo ba zan fad'a muku mana aure na uku ma mai na wani fad'e"

Haleema bata ce komai ba sakamakon ganin Fateema na hawaye take taji itama hawayen na shirin zubo mata Fateema magana ta cigaba da yi

"Haleema ga amanar yarana nan ahanunki duk da nasan kina iya k'ok'arinki kina kula dasu banida abinda zance miki sai dai nayi miki godiya ba asan raina zanyi auren nan ba dan dai yariga da ya zame min dole ne sai nayi San zuciyata da k'wadayin abun duniya ya janyo min rabuwa da uban y'ay'ana da y'ay'ana banga laifin Bashir da yace bazai maidani d'akina ba dan ni na jawo wa kaina yanzu inaji ina gani zanje in rik'e y'ay'an wani amadadin y'ay'ana babu ko d'igon San wanda zan aura a zuciyata aurene dai kawai zanyi dan in rayya sunar ma'aki Haleema kinsan zuciya bata da k'ashi ina k'ara rok'onki ne daki rik'e amana Allah ya Riga da ya kaddara yarana bazasu taso agabana ba ke zaki rik'esu nikuma zanje na rik'e y'ay'an wani dan Allah ki kuma tayani Neman yafiyar Abban Aliyu dan ni nasan da wuya ya iya manta abunda na mishi na wulak'anta shi Haleema na tozarta shi ban d'aukeshi amatsayin miji ba na wulak'anta aure ni nasan idan bai yafemin ba bazan tab'a ganin dai dai arayuwata ba hakkinsa yayi ta bibiyata kenan duk da yace ya yafemin ki k'ara nema min yafiyarsa dan Allah"


Fateema ta k'arashe maganar tana fashewa da kuka Haleema itama kukan ne ya k'wace mata dan tana da rauni da tausayi dak'yar ta had'iye kukan da take tace

"Insha Allahu umman Aliyu zan k'ara nema miki yafiyar Yaya ki kwantar da hankalinki Allah ya Riga da ya kaddara Baki da rabon sake zama da Yaya ne amma ni nasan yaya ya yafe miki karki damu y'ay'an yaya tamkar y'ay'ana ban tab'a musu kallon bani na haifesu ba yanda zan kula dasu Atif haka zan kula dasu Aliyu dan Nima banida tabbacin ko zan rayu da y'ay'ana mutuwa na iya rabani dasu dole wata ce zata rik'emin su kinga idan ban rik'e naki da amana ba Nima babu Wanda zai rik'e nawa da amana ki kwantar da hankalinki baki rabu dasu Aliyu ba koda kinyi auren yanda suke zuwa ganinki a gida haka ma zasu na zuwa gidanki indai mijinki ma zai yarda har kwanaki ma zasu ringa zuwa yi miki"


Fateema share hawayen fuskarta tayi tace " nakuwa gode Allah ya saka miki da alheri dan nasan samun irinki awanan zamanin zai yi wuya"

Haleema murmushi tayi itama ta share hawayen Fuskarta

Ahaka suka cigaba da hira basu Haleema ne suka bar gidan ba sai wajen sallar magriba har wajen mota Fateema ta rakasu hannu itama ta ringa d'agawa su Nura har sai da ta dai na hangosu ta Dade atsaye tana tunanin badan San zuciya da rashin rabo ba da yanzu itace a gidan Bashir take fantamawa haka ita da ta Dade tana mafarkin mallakar motar kanta sai gashi Haleema har mota biyu gareta 'yar yarinyarta da ita watak'ila ita bata ma tab'a sa ran zata mallaki motar kanta ba sai gashi Allah ya bata har guda biyu duk k'waday'inta da San abun duniyarta da rufewar da idonta yayi ta wulak'anta Bashir a k'arshe dai ga yanda ta k'are mata daga auren lado ta dawo zata auri Isah driver ahaka ta juya ta shiga ciki tana tunane tunane a tsakar gida ta samu Inna wuro sai fad'a take yi akan ta sakarwa Haleema fuska alhalin munafuka ce Fateema bata ce Mara komai ba ta shige d'aki



Haleema kuwa bayan sunci abinci dare take fad'awa Bashir auren fateema nan da sati biyu Bashir murmushi yayi yace ansamu mai kuma kwasa kenan Allah ya sanya alheri daga haka bai k'ara cewa komai ba Haleema bata ji dadin abinda Bashir yace ba amma bata nuna mishi ba tace mishi "wane gudunmawa kake gani ya kamata muyi mata"

Bashir juyawa yayi ya kalli Haleema yace "kowane irin gudunmawa kikace ayi mata shi zaayi mata badan kuma halinta ba wallahi dan darajarsu Aliyu"

Murmushin farinciki Haleema tayi tace "to shikenan mungode mu da yara" anan ta hau mishi lissafin abubuwan da zasu yiwa Fateema Bashir rik'e baki yayi yace "wanan uban kaya haka da kike lissafowa sai kace ni zan aureta"

Murmushi Haleema tayi tace " ai dan yaranka zakayi"

Bashir cewa yayi " bawani yara kawai dai so kike ki tsarani yaushe ne d'aurin auren"?


"Nan da sati biyu dai tacemin bansan yaushe ne d'aurin auren ba"

"To shikenan Allah ya kaimu rai da lafiya"

Daga haka Bashir ya mik'e ya nufi d'akinsa.


Bayan kwana biyu da zuwan su Haleema gidansu Fateema Bashir ya aikawa da Fateema kayan d'aki nagani na fad'a duk wani Abu daya shafi kayan cikin gida babu abinda Bashir bai siya mata ba tunda aka fara shiga da kayan cikin gidan Fateema keta kuka dan bata tab'a tunanin Bashir zai mata abun alheri haka ba bayan irin rashin mutuncin da ta mishi Inna wuro kuwa tsabar farinciki addua ta ringa zabgawa masu shigo da kayan tana ce musu siyiwa Bashir godiya Fateema tana nan a tsaye har suka gama shigo da kayan da ya kusa mamaye tsakar gidansu drivern Bashir mik'awa Fateema wani k'aton envelope yayi yace gashi Bashir inji Bashir Fateema hannu tasa ta k'arba tace ya k'ara yiwa Bashir godiya yana ficewa Inna wuro ta matsa kusa da ita tana ta duba envelope d'in taga menene a ciki



Fateema bud'e envelope d'in tayi d'aurin yan dubu dubu ne guda biyar sai wani farin takarda da aka nad'e a ciki hannu tasa ta Ciro takardar ta ajiye envelope d'in aikuwa caraf In a wuro ta d'auki envelope d'in ta fara zaro kud'in dake ciki jikinta sai rawa yake




Fateema da ta koma gefe warware takardar tayi ta fara karanta sak'on dake cikin


*ASSALAMU ALAIKUM DAFATAN KINA CIKIN K'OSHIN LAFIYA NA RUBUTO MIKI WANAN GUNTUN SAK'ON NE SABIDA NA BAKI SHAWARA NAJI LABARIN ZAKIYI AURE FATEEMA ALLAH YA SANYA ALHERI YASA MUTUWA CE ZATA RABAKI DA MIJINKI DUK ABINDA NAYI MIKI NAYI NE SABIDA ALLAH DA KUMA YARAN DAKE TSAKANINMU SHAWARAR DA ZAN BAKI KUWA ITACE KIJI TSORON ALLAH KI ZAUNA A GIDAN MIJINKI LAFIYA KI SANI SHI ZAMA NA AURE IBADA NE KIBI MIJINKI SAU DA K'AFA SABIDA KISAMU ALJANARKI KI GIRMAMA MIJINKI KI KYAUTATA MISHI DAN MIJI BA ABUN WASA BANE KARKI SAKE KI YI IRIN RAYUWAR DA KIKAYI AGIDANA A GIDAN AURENKI DAN BA KOWANE NAMIJINE ZAI IYA JUREWA BA KI KUMA SA ALLAH ARANKI SAMU DA RASHI NA ALLAH NA KI RINGA GODEWA ALLAH A DUK HALIN DA KIKA TSINCI KANKI DAN IDAN BAKI GODE MASA BA ZAKI GODEWA AZABARSA DAN ALLAH KIJI TSORON ALLAH DUK ABINDA ZAKIYI KIRINGA YI DAN ALLAH DUK ABINDA MIJINKI YA KAWO MIKI KI RINGA GODE MASA KINA AMSA DA HANNU BIBIYU KISANI KE YANZU BA YARINYA BACE KARKI YI ABUNDA ZAI SA AURENKI YA KUMA MUTUWA INA MIKI FATAN ALHERI A RAYUWARKI KAMAR YANDA NA FAD'A MIKI ABAYA BANYI MIKI IYAKA DA Y'AY'ANKI BA DUK LOKACIN DA KIKA SO ZAKI IYA ZUWA KI GANSU DUK LOKACIN DA KIKA BUKATA ZA'A KAWO MIKI SU GA DUBU D'ARI BIYAR NAN KI JUYA KIRINGA SANA'A IDAN KINA NEMAN TAIMAKO KISAMU HALEEMA KI FAD'A MATA INSHA ALLAHU ZANYI K'OK'ARI NAGA NAYI MIKI KO DAN ZURIAR DAKE TSAKANINMU ALLAH YA BAKI ZAMAN LAFIYA MA'ASALAM*

Fateema kuka ta fashe dashi bayan ta gama karanta tace "insha Allahu Bashir zan gyara halina zan bi mijina sau da k'afa"


Kuka sosai Fateema ta ringa yi tana kuma danasanin abinda tayi dan tasan ta rasa nagartaccen miji

Inna wuro kuwa ta d'auka kukan farinciki Fateema takeyi shi yasa bata bi ta kanta ba ta sungumi kud'in tayi d'aki


Aranar da yamma Inna wuro da Baffa suna zaune a tsakar gida suna ta yaba halin Bashir na kirki Fateema kuwa tana kwance a d'aki tayi lamo kamar mai bacci nan kuwa tunani take yi sallama suka jiyo daga waje Baffa ya mik'e ya fita waje driven Bashir ne dai ya sake dawowa wani k'aton akwati ya sauk'o dashi daga boot d'in motar yace Haleema ce ta aikoshi ya kawo wa fateema Baffa rik'e baki yayi yace ya shigo dashi drivern kinkimar akwatin yayi ya shiga dashi ciki Inna wuro kuwa mik'ewa tayi da sauri tana "wanan akwatin fa daga ina"?


Baffa ne ya bata amsa da matar Bashir ce ta aikowa fateema da akwatin Inna wuro rik'e baki tayi tana mamakin halin Haleema sai yanzu ta yarda da zancen fateema da tace Haleema Nada kirki d'aki ta nufa ta kira fateema da ta zo taga akwatin da Haleema ta aiko mata dashi


Fatima mik'ewa tayi tabi bayanta a lokacin har driven yajuya ya tafi Fateema mamaki ne ya rufeta da taga akwatin da Haleema ta aiko mata dashi bata gama mamaki ba sai da ta bud'e akwatin taga himilin kayan dake ciki kamar lefe kukan dad'i ta fashe dashi dan bata tab'a tunanin kirkin Haleema ya kai haka ba


Inna wuro kuwa cewa ta ringa yi "Ashe haka matar Bashir take da kirki bansani ba wlh na d'auka munafika ce"


Fateema bata kulata ba ta cigaba da d'ad'aga kayan Baffa kuwa addua kawai ya ringa yiwa Bashir da Haleema Baffa yace zai nemi Bashir ya masa godiya fateema kuwa bayan tagama ganin kayan d'aki ya shige ta kira Haleema awaya ta ringa zuba mata godiya tana ta tayata yiwa Bashir godiya bata da abinda zata gode musu dashi atak'aice sai da Haleema ta kashe wayar dan Fateema har kuka ta ringa

Please Login or Register in order to submit comment