Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abbanku ya dawo dani d'akina"


Fateema tace tana cigaba da kuka


Hameeda duk da ba wani gane maganar Fateema tayi ba itama hawayen ne ya hau zubo mata ta d'ago fuskar Fateema tana "Umma kiyi hakuri ki daina kuka zamu rok'i Abba yabarki ki dawo gidanmu akwai d'akuna dayawa Umma da zaki zauna muma munfi San ki zauna a gidanmu"


Fateema mik'ewa tayi hanunta rik'e dana Hameeda tace "Hameeda kedasu Aliyu kusa Abbanku agaba kuyi ta mishi kuka kuce dan Allah yadawo dani in ba haka kuma zaku bar gidan kinji ko"


Gyad'a kai Hameeda tayi Fateema ta cika hanunta tayi hanyar waje sai kallon k'aton gidan take yi tana tunanin yanzu duk wahalar data sha da Bashir har na tsawon Shekara goma sha biyar Bashir bai gani ba sai dan yanzu yayi kud'i zai juya mata baya ai duk abinda tayi mishi bata cancanci irin wanan matakin daga gurinshi ba


Atak'aice ahaka Fateema taje gida tana tunane tunane adaidaita sahu na sauk'eta a k'ofar gida ta shige gidan da gudu tana k'walawa Inna wuro kira


Inna wuro dake zaune tana mirjin taliya hankali a tashe ta mik'e tsaye da ta jiyo muryar Fateema tana kuka


Fateema atsakar gidan ta zube tana "Inna nashiga uku na lalace inna nayiwa kaina Bashir Ashe yayi kud'i bansani ba Inna Bashir yace bazai maidani d'akina ba Inna Bashir yayi aure wlh idan kika ga su Aliyu yanzu bazaki ganesu ba"
Fateema tace tana k'ara fashewa da kuka


Inna matsawa tayi kusa da Fateema zaninta na kuncewa

"Nifa bangane mai kike nufi ba Kiyi min bayani dalla dalla"


Fateema tsayar da kukan da takeyi tayi ta hau bawa Inna Labari babu abinda ta b'oye mata a k'arshe ta k'ara da "wlh Inna ina cikin wani hali idan Bashir bai maidani d'akina ba ni bama dan kud'insa nakesan ya maidani d'akina ba Inna kinga yanda Bashir ya k'ara had'uwa kinga yanda yake kamshi ba kamar Lado ba ai yanzu Babu Wanda zai yarda idan aka ce Bashir shine wanda yayi wanan mugun talaucin Inna ki taimaka min na koma gidana dan Allah kisa Baffa yaje ya rok'i Bashir watak'ila yaji nauyinsa"


Tunda Fateema ta fara magana zufa ya hau karyowa Inna wuro sai fifita take yi da hannu babu abinda ya d'aga mata hankali kamar jin da tayi Bashir yace bazai maida Fateema d'akinta ba Inna wuro cewa tayi


"Fateema ai bamu ga ta zama kice Bashir yayi kud'i ai inda adalci bai kamata yace bazai maida ki ba dan ke kika zauna dashi kika sha wahala dashi har tsawon shekaru amma yanzu da yayi kud'i sai yace bazai maida ki d'akinki ba karki damu da kaina zanje gidan idan an kwana biyu zan siyi Abu na kai da zumar naje ganin jikokina daga nan sai na rok'eshi ya maida ki d'akinki karki damu"


Fateema ajiyar zuciya ta sauk'e da taji abinda Inna wuro tace sai a lokacin hankalinta ya d'an kwanta dan ta San Bashir zai ji nauyin Inna wuro ya maida ta d'akinta



Daddare Fateema juye juye ta ringayi ta kasa barci duk motsin da zatayi fuskar Bashir take gani a idonta dan haka kawai taji tana masifar sansa har yanzu kamshin turarensa na nan daram ajikinta inta shak'i kamshin sai ta lumshe ido


Kanta ta fara hararowa a k'aton gidanan Bashir ya maida ta d'akinta dan har ga Allah yanzu ba kud'ine agabanta ba Bashir kawai takeso aranar kwana tayi tana tunanin Bashir bacci kuwa da ya saceta mafarki taringayi ta koma d'akinta.





B'angaren Haleema kuwa tunani tasa aranta da kishin fateema aranar ahaka ta wuni sukuku babu walwala ahaka Bashir ya dawo ya sameta babu irin tambayar da Bashir bai mata ba akan ta fad'a mishi abinda ke damunta amma Haleema tace mishi babu abinda ke damunta kanta ne kawai yake ciwo nan kuwa kishi tasa aranta




A tak'aice bayan kwana biyu da zuwan Fateema gidan Bashir Inna wuro ta shirya ta nufi gidan Bashir da biscuit da alewan da zata kaiwa su Aliyu tsaraba.
*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*



*WANAN SHAFIN NAKU NE MASOYANA NA ASALI MASU K'AUNATA BANIDA BAKIN DA ZAN GODE MUKU KUN D'ADE KUNA NUNA MIN K'AUNA ALLAH UBANGIJI YA D'AUKAKU YA K'ARA MUKU BASIRA DA ZAKIN HANNU THANKS ALOT FOR DEDICATING A WHOLE BOOK FOR ME*



*ACTION BABY* *(ABOKIN YAYANA*)

*MASHKURAR SADNAF*
( *DA BAZARKI UMMANA*)

*JINJINAN BANGIRMA GAREKU*

*MAIMUNA*
*HAJIYA HAUWA*
*SEEEMAH*
*SAMEERAH*
*MANCY*
*DA SALMAN SADNAF*
*ALLAH YA NUNA MIN RAN AURENKI NA NAD'O K'AFA TUNDAGA KANO NA TAHO LAGOS*😍😍😍



Page 90-95




Inna wuro bata sha wahalar gane gidan Bashir ba dan ta gane kwatancen da Fateema tayi mata tundaga nesa ta saki baki da hanci tana kallon gidan magana ta fara yi ita kad'ai tana "kan uba Yanzu Bashir ne mai wanan kantamemen gidan tabdi ai ko zanyi yawo tsirara wlh sai na San hanyar da zan bi Bashir Ya maida Fateema d'akinta kai ina ai batun Bashir yace bazai maida Fateema d'akinta ba ai bai taso ba dole ne Fateema ta dawo gidanan muma ta sama mana d'aki d'aya mudawo nida Baffa kai kai"gwaram taji tabige da wani pole taja da baya da Sauri tana mulmula goshinta Dan agarin kallo gidan ma batasan ta k'auce daga hanya ba


Sai da ta gama mulmula goshinta ta nufi gidan tana zancen zuci tana zuwa bakin gate ta fara kwankwasawa gate d'in da k'arfi mai gadi ne ya bud'e mata gate d'in ya tambayeta wa take nema

Inna wuro ce mishi tayi mai gidan take nema wajensa tazo maigadi ganin datijuwa ce yasa ya bud'e mata k'ofar Inna wuro da saurinta ta shige tsayawa tayi tana k'arewa ko'ina kallo
Inna wuro tunda take bata tab'a ganin had'ad'en gida irin wanan ba kokwanto ta Shiga yi da anya nan ne gidan Bashir wajen mai gadi ta koma tace mishi "dan Allah nan ne gidan Bashir mai robobi"?

Maigadi cikin mamaki yace "bangane nan ne gidan Bashir mai robobi ba Dama bakisan gidan da zakije ba nan ba gidan Bashir mai robobi bane nan gidan Alhaji Bashir ne gama shi can ya hau motarsa zai fita"


Inna wuro da Sauri ta juya ta kalli Inda mai gadi yake nuna mata adai dai lokacin da Bashir ya shige motar Haleema kuma ta sunkuya suna magana Inna wuro da Sauri ta nufi wajensu Bashir dake magana shi da Haleema akan Fateema Dan tun jiya daddare Hameeda taje ta samu Haleema tana rok'onta da ta tayata rok'on Abbansu ya dawo da Umma Haleema haka kawai jikinta yayi sanyi ta kuma ji tausayin Hameedar ya rufeta take duk kishin da take ji akan fateema ta cireshi aranta dan itama take tasa kanta amatsayin Fateema itama zata so ta dawo gidan uban y'ay'anta dan yaranta ma zasu so suga sun taso agaban uwarsu da ubansu alokacin shafa kan Hameeda tayi tace ta kwantar da hankalinta zata yiwa Abbansu magana tun adaren bayan sun kwanta da Bashir taso tayi mishi maganar ganin kamar agajiye yake yasa bata fad'a mishi ba sai yanzu da ta rako shi ta fara mishi maganar

Bashir ne ya fara hango Inna wuro da sauri ya fito daga motar yana cewa Haleema ga mahaifiyar Fateema nan



Adai dai lokacin Inna wuro ta k'araso Inda suke ta kalli Bashir ta kalli Haleema

Bashir d'ukawa yayi har k'asa ya gaisheta Inna wuro kuwa ta amsa da fara'arta tana satar kallon Haleema
Haleema itama har k'asa ta tsuguna ta gaisheta Inna wuro ta amsa tana kallon gwala gwalan dake jere ahanunta


Haleema mik'ewa tayi tace mata bismillah su shiga daga ciki Inna wuro tabi bayanta Bashir kuma ya rufe motarsa yabi bayansu tun kafin su k'arasa palon Inna wuro ta ringa kalle kalle har suka isa palon

Inna wuro a k'asa take k'ok'arin zama Bashir yayi Sauri yace ta zauna akan kujera mana Inna wuro zama tayi akan kujerar ta ajiye ledar hanunta ta ware ido sosai tana k'arewa palon kallo

Bashir kuwa a k'asan carpet ya zauna ya k'ara gaisheta sai alokacin Inna wuro tayi Sauri ta dawo da hankalinta kan Bashir tana amsa gaisuwar Bashir adai dai lokacin da Haleema ta ajiye mata kayan motsa baki tana kuma gaisheta Inna wuro amsawa tayi tana kuma bin Haleema da kallo sai zancen zuci take yi


Bashir dai sunkuyar da kansa yayi yana jiran yaji mai ya kawo Inna wuro maganar Inna wuro ne yasa ya d'ago Inna wuro cewa tayi

"Wai ina 'yan jikokin nawa ne banji motsinsu ba kuma su nazo gani"

Bashir murmushi yayi yace "inna ai da baki wahalar da kanki zuwa ganinsu ba awanan asabar d'in nake shirin kawo su su gaisheki suna makaranta wlh kuma basa dawowa dawuri sai can yamma dayake makarantar tasu had'e yake da islamiyya suna tashi dagana boko zasu fara na islamiyya"

Inna wuro cewa tayi
"Kai amma banji dadi ba naso ganinsu wlh Dan inata kewarsu na Dade ban gansu ba"

Bashir murmushi ya k'ara yi yace "Allah sarki karki damu Inna zan kawosu asabar dinan insha Allahu zasu zo su gaisheki"

"Allah yasa ka kawo min su ran asabar d'in"inna wuro tace tana satar kallon Haleema dake zaune acan gefe a zaune

" insha Allahu zan kawo miki su Inna
Inna ki Dan sha ruwa mana"? Bashir yace yana nuna mata ruwan roba da lemo da soyayyen kaji dake ajiye agabanta

Inna wuro murmushi tayi ta Kalli kajin sai da ta fara had'iyar yawu ta d'aure tace "aaa alhamdulillah ni a koshi nake Dama jikokina nazo gani tunda bansame su ba shikenan ni tafiya zanyi" nan kuwa ranta ya biya kazar ji take kamar ta sa hannu ta d'au cinya d'aya ta kai bakinta


Bashir cewa yayi "inna dan bakisamu jikokinki ba shiyasa bazaki sha ruwa ba"

Inna wuro murmushi tayi tace "eee ai Dana samesu Dana sha ruwan" tace adai dai lokacin da ta kuma wurgawa Haleema harara Dan so take Haleema ta tashi tabar palon sabida taji d'ad'in magana aikuwa had'a ido sukayi da haleema
Haleema kuwa tayi sauri ta mik'e tabar palon tana mamakin halin Inna wuro tsohuwa da ita amma tana taya 'yarta kishi



Inna wuro kuwa ganin Haleema tabar palon ne yasa tace "Bashir Dama inaso nayi amfani da wanan damar na baka hak'uri akan abinda Fateema tayi ma wlh tun a lokacin da ta dawo gida akan kun samu sabani da ita naso in dawo da ita d'akinta to kasan ka haifi d'a ne baka haifi halinsa ba yarinya nan babu irin fad'an da ban mata ba inaji ina gani ta tsarawa mahaifinta gaskiya da karya shi kuma ya hau dokin zuciya yazo amsar mata takardar sakinta kaga ko auren da tayi na biyu nan babu hanuna a ciki Dan shawara na ringa bata akan karta sake ta auri wani gwara ta dawo gidanka Dan kai mutumin kirki ne amma kirkiri yarinya nan tak'i jin maganata taje tayi auri wani can sai gashi ko shekara batayi ba ya sakota tana dawowa nace mata hakkinka ke bibiyarta ya za'ayi ta rabu da mutumin kirki irinka tayi tunanin zata dace ta auri mai irin halinka eee d'adin ma danaji Allah bai sa ta haihu da wancan data aura ba dan haka nace bari dai na baka hak'uri dan Allah ka manta abinda Fateema tayi ma kayi hak'uri ka maidata d'akinta ko dan yaran dake tsakaninku kaga suma yara zasu so su taso agaban uwarsu karka kayi tunanin ka auri wata zata iya kular ma da yara duk kulawar da zata musu ba kamar uwarsu ba kuma naka sai naka wlh itama da zarar ta samu nata d'an ko 'yar zata rage kula da y'ay'anka dan ta samu nata itama so sone amma San kai yafi dan haka nake kuma rok'onka kayi hak'uri ka yafewa Fateema nasan tayi maka ba dai dai ba ka maidata d'akinta "



Tunda ta fara magana Bashir ya sunkuyar dakansa tun kafin ma tayi nisa da zancen yasan amsar da zai bata dan dama yasan ba jikoki tazo gani ba zuwa tayi taga gidan ta kuma rok'i ya maida Fateema d'akinta dan ya dade da sanin halinsu



Bashir d'agowa yayi yace "Inna ai na dade da yafewa Fateema dan nasan Allah yariga da ya hukunta aure dake tsakanina da ita ya k'are Fateema ni bata min komai ba abinda take ganin yafi mata alheri tayi
Kuma abinda yafi mata alherin shine rabuwarmu Inna kuma zancen yaran da kike magana lokacin da Fateema zata tafi ai bata duba yaran dake tsakaninmu ba ta tsallake yaran ta tafi uwa da aka Santa da rauni da tausayi haka tabar D'an k'aramin d'anta Nura Wanda a lokacin bai wuce shekara uku ba kuma Inna ai akwai yara dayawa da basa tasowa agaban uwarsu da ubansu dan mutuwa ma na iya raba uwa da y'ay'anta kuma yaran bazasu fasa rayuwa ba kuma Alhamdulillahi Inna wlh wacce na aura nasan halinta ko yara goma zata Haifa babu abinda zai sa ta tab'a juyawa yarana baya dan ita ta tallafi y'ay'ana a lokacin da suke maraicin uwa Inna kiyi hak'uri ki yarda da kaddara Allah yariga da ya hukunta Fateema ba matata bace sai mun rabu ahalin yanzu gaskiya bazan iya auren Fateema ba dan Allah yabani wacce tafita alheri kiyi hak'uri bawai naki jin maganarki bane an Riga da anzama d'aya ko dan yaran dake tsakanina da ita zata iya zuwa taga y'ay'anta a duk lokacin da taso dafatan kin fahimceni Inna"


Inna wuro tunda Bashir yafara magana zufa ke karyo mata babu abinda ya d'aga mata hankali kamar arzikin dake shirin subuce musu

Murmushin k'arfin hali Inna wuro tayi tace "nagane Bashir karka damu Allah yasa hakan shi yafi alheri ni zan tafi sai ka kawo min jikokin nawa ran asabar"


Bashir mik'ewa yayi da sauri ya fara k'walawa Haleema kira Haleema dake d'aki akwance aguje ta sauk'o ta samu Bashir


Bashir ce mata yayi Inna wuro zata tafi Haleema murmushi tayi ta kalli Inna wuro dake mata mugun kallo tace
"Inna har zaki tafi"?

Inna wuro da take ji kamar ta shak'e Haleema cewa tayi " eee tafiya zanyi jikokina dama nazo gani kuma ban samesu ba"

Haleema murmushi tayi tace "zasu zo ai insha Allahu"

Daga haka sama ta nufa da sauri tace tana zuwa gabanta sai fad'uwa yake na kallon da Inna wuro ke mata Bashir kuwa yana ganin Haleema ta hau sama ya k'irga dubu ashirin ya mik'awa Inna wuro yana gashi ta sha ruwa ahanya Inna wuro da sauri ta amshi kud'in tana "angode Allah ya saka da alheri Allah ya k'ara bud'i ta soka kud'in a zaninta Bashir bai yi mamaki yanda tayi saurin amsar kud'in ba dan dama ya dade da sanin halinta tun kafin ya auri Fateema inyaje gaisheta yana bata wani Abu zata yi Sauri ta amsa babu irin d'an alkunyan nan na aa barshi anya ayi haka hanyar waje tayi Bashir yabita abaya yana mata Godiya da kuma ta gaida Baffa


Haleema suna fita waje ta sauk'o da gudu da leda a rik'e ahanunta atamfa turmi biyu masu tsada da mayafai guda biyu sai hijabi ta sako aledar dan ta bawa Inna wuro

Ad'an guje tabi Inna wuro dan har ta kusa kaiwa gate Haleema mik'a mata ledar tayi tana " Gashi ba yawa ki gaida gida"

Inna wuro k'arbe ledar tayi daga hanun Haleema ta doka mata harara tana "gida yaji" daga haka ta cigaba da tafiya

Haleema mamakin Inna wuro ne ya k'ara rufeta sai da Inna wuro tabar gidan ta juya ta nufi wajen Bashir dake shirin tada motarsa tunanin abinda Inna wuro tayi mata fal ranta to idan Inna wuro tayi mata irin wanan ina ga kuma Fateema.



Inna wuro kuwa data hau adaidaita sahu gani take kamar mai adaidaita sahun baya sauri dan ta matsu taje gida tabawa Fateema labari dan tsadaddun atamfofin da Haleema ta bata ya k'ara d'aga mata hankali tasan Bashir lailai ya zama hamshakin mai kud'i

A k'ofar gida ta samu Fateema atsaye tana ta d'aga wuya Inna wuro da ta hango a adaidaita sahu yasa ta nufi wajen adaidaita sahun da sauri dan tafi k'arfin awa d'aya awaje tana jiran Inna wuro ta dawo

Inna wuro duk Santa da kud'i bata tsaya k'arbar chanji ba dan ta matsu ta fara bawa Fateema labari tun a kafin su shiga gidan Fateema ta fara tambayarta ya sukayi da Bashir


Inna wuro sai da ta cire hijabin jikinta har dankwalli ta zauna a k'asa dan taji dad'in bawa Fateema labari

Kud'in da Bashir ya bata tafara cirowa daga zaninta ta mik'awa Fateema tana k'irga nawa ne


Fateema jiki na rawa ta k'arbi kud'in tana k'irgawa tana gama k'irgawa tace dubu ashirin ne

Inna wuro gyad'a kai tayi ta tura mata ledar da Haleema ta bata tace ta duba ta gani


Fateema bud'e ledar tayi ta fito da tsalla tsallan atamfofin da mayafai da hijab tace mata "nagani Inna Wai duk na menene ya kuka yi da Bashir Inna ya hak'ura zai maidani"?


Inna wuro ajiyar zuciya ta sauk'e tace " ke Bashir yanzu ba k'aramin mai kud'i bane dubu ashirin ya d'auka ya bani kiga fa atamfofinan super Holland ne wanan matar tasa ce tabani da zan taho"

Katseta Fateema tayi da sauri tana "Haba inna ni ina ruwana da abinda suka baki ni kifad'amin kawai yanda kuka yi da Bashir"

Inna wuro cewa tayi "ai dadina dake gajen hak'uri ina nuna miki abinda Bashir ya bani ne sabida ki San Bashir yanzu ba k'aramin mutum bane ya wuce tunaninmu dole sai mun tashi tsaye zaki iya komawa gidansa dan babu irin rok'on da ban mishi ba akan ya maidaki d'akinki yace ya gama zaman aure dake"anan Inna wuro ta hau bata labarin duk yanda sukayi da Bashir

Fateema dafe k'irjinta tayi tace "Inna yanzu Bashir bai dubi girmanki ba yace bazai maidani d'akina ba"


Inna wuro cewa tayi "kwarai dagaske wlh toka ya shafawa idonsa yace bazai maidaki d'akinki ba amma nifa banga laifinsa ba dan da alama wanan tsinaniyar matan nan tasa bata barshi haka ba asirice shi tayi dan haka gwara mu mik'e tsaye idan ba haka ba kina ji kina gani zata mallake komai na Bashir baki isa ki koma gidansa dan haka kizomu bazama muje wajen mallamai inta kama ma har da bokaye suyi yanda zakiyi ki koma gidan Bashir idan ba haka ba wlh bamuda rabon arziki"



Fateema shiru tayi tana nazarin maganar Inna wuro can sai tace "inna nifa ba kud'in Bashir ne agabana ba yanzu wlh ni shi nakeso inaso kuma na koma in rik'e y'ay'ana"


"Dalla rufemin baki karki bari na kwad'a miki mari ana zancen arziki waye yake maganar so kinada hankali kuwa ko dai tsine miki akayi ya ina fad'a miki musan nayi tun wuri kizo kina cemin ke yanzu ba kud'insa ne agabanki ba shi kikeso to ai shi yanzu ma baya sanki kwata kwata indai ta so zaki bi wlh kina da Rabon shan wahala dan haka gwara kisan nayi tun dare bai yi miki ba banza shasha"

Daga haka Inna wuro ta mik'e ta kwashi kud'inta da atamfofi ta shige d'aki tabar Fateema a zaune tana nazarin maganganunta.
*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*


*WANAN SHAFIN NAKI NE AUNTY KAUSAR LUV ALLAH YABARMU TARE*


*JINJINAN BAN* *GIRMA GAREKI*
*MD MD RUKAYYA ALLAH YA BIYA MIKI BUK'ATUNKI NA ALHERI*

*UMMUN IRFAN STAY BLESSED ILYSVM*



Page 95-100



Fateema ta Dade a zaune tana sak'a da warwara Inna wuro sai data Adana kud'inta da atamfarta ta k'ara fitowa daga d'aki ta zauna akan tabarma ta kalli Fateema data had'a tagumi tsaki Inna wuro tayi tace



"Ai fateema naga alamar bakida rabo a duniya Dan da kina da rabo bazance miki ki tashi mu bazama muje gurin mallamai mu nemi taimako ba har ki wani tsaya tunani"


Fateema hawaye ne ya zubo mata tace wa Inna wuro

"Inna nayi nadamar abinda nayi ayanzu nasan mai hak'uri bai iya fushi ba Inna ai tunda Bashir ya baki hak'uri yace bazai iya maidani d'akina ba nasan babu yanda za'ayi ya maidani d'akina inna nayiwa Bashir abubuwa sosai da ba kowane namiji ne zai iya jurewa ba"


Inna Wuro katseta tayi tana "yanzu dai so kike kicemin kema kin hak'ura kin karaya Bashir bazai maidaki d'akinki ba duk wahalar da kika sha a gidansa ya tashi a banza kina ji kina gani 'yar k'aramar yarinya ta rabaki da mijinki da y'ay'anki da dukiyarsa aikuwa in hakane kin tafka babbar asara da bazaki mik'e kiyi duk abinda zakiyi Bashir ya maidaki d'akinki ba"


Fateema kuka ta fashe dashi tana "Inna to ya zanyi ya maidani d'akina babu irin rok'on da ban mishi ba yak'i kema kinje yace bazai maidani ba ya zanyi"


Inna wuro rai a b'ace tace "kinada yanda zakiyi mana dan ubanki ki zo mu bazama muje gurin mallamai inta kama har gurin bokaye a asirce shi ki koma d'akinki in bahaka ba wlh kina ji kina gani babu ke babu arziki ak'arshe ma ki kuma samo wani mitsiyacin ki aura ke kinsan kud'in da Bashir yayi yanzu kuwa Dan baki ga dankwalla dankwallan kajin da aka kawo min ba ga wani madara mai d'an k'aran sanyi da aka had'omin dashi ki tashi muje wajen Abuwa ta rakamu wajen mallaminta yayi mana addua ki koma gidan Bashir"

Fateema girgiza kai tayi tace "Inna ni ban yarda da wanan mallaman ba kud'inmu kawai zasu cinye mana kibari kawai zan cigaba da sintirin zuwa gidan Bashir ina rok'onsa ya maidani zan kuma dage da addua Inna kema dan Allah kiringa tayani da addua"

Inna wuro tsaki tayi tace "aikuwa kina da rabon shan wahala dan ko sujadda zakiyi wa Bashir bana jin zai maidaki d'akinki ana nuna miki gabas kina yamma sokuwa kawai sai kije kiyi ta yi"


Fateema bata ce komai ba ta mik'e ta nufi d'aki ta kwanta akan katifa tana tunanin yanda zata shawo kan Bashir ya maidata d'akinta


B'angaren Bashir kuwa daddare bayan sun gama cin abinci suna zaune a Palo suna kallo Hameeda ta matsa kusa dashi tayi k'asa da murya tana

"Abba dan Allah kayi hak'uri ka yafewa Ummanmu duk abinda tayi ma ka dawo da ita gidanan"


Bashir shiru yayi ya zubawa Hameeda ido Hameeda kuwa ta sunkuyar dakanta hawaye na zubo mata juyawa yayi ya kalli Haleema dake kallonsu Haleema kuwa ta kau dakanta dawo da kallonsa yayi wajen Hameeda yace "Hameeda ki kwantar da hankalinki babu abinda Ummanku tayi min idan ma tayi min na yafe mata zata dawo gidanan amma ba yanzu ba kinji ko"

Hameeda gyad'a kanta tayi yace "yauwa maza jeki cigaba da kallonki"

Hameeda mik'ewa tayi ta koma kusa da summayya suka cigaba da kallo


Bashir mik'ewa yayi ya nufi d'akinsa jiki asanyaye tausayin Hameeda fal ransa dama zai iya dawo da Fateema d'akinta da ya dawo ita ko dan yaran dake tsakaninsu amma Sam bazai iya dawo da ita ba dan yasan Halin Fateema yasan sabida yayi kud'i ta dawo wajensa kuma har gobe ya kasa manta irin wulak'ancin da tayi masa dan a duk lokacin da ya tuna ransa kan b'aci ya rasa mai ke masa dad'i ya kuma ji ya tsani fateema yana nan akwance yana tunani Haleema ta shigo d'akin da sallama


Amsa sallamar yayi ba tare da ya kalleta ba Haleema zama tayi akusa dashi tace "Yaya dan Allah ka tashi muyi magana ta fahimtar juna dazu mun fara magana kace inbari sai ka dawo"

Bashir kallonta yayi da jajayen idonsa dasuka rine dan wani mugun wulak'anci da Fateema tayi mishi ya tuna take yaji ransa b'aci tamkar yanzu Fateema tayi mishi abun abinda yake bashi mamaki bai wuce yanda har gobe in ya tuna wulak'ancin da Fateema tayi mishi yakanji kamar yanzu tayi mishi
mik'ewa yayi ya zauna yace "ina jinki"

Haleema k'asa tayi da kanta ta fara magana cikin rauni dan har ga Allah tausayin su Hameeda ne kawai zai sa tace Bashir ya maida Fateema d'akinta badan ranta naso

Please Login or Register in order to submit comment