Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inda bashir yake ba


Mai gadi ne ya bud'e k'ofar yace mata wa take nema

Fateema tunani ta fara yi na wa zata ce tana nema can dabara ta fad'o mata tace matar gidan take nema


Mai gadi har da zai fad'owa Haleema kafin ya barta ta shiga ciki amma da ya tuna gargadin da Bashir ya masa akan duk Wanda yazo Neman shi ko Matar gidan yabarsu su shigo dan bayasan wulak'anci arayuwarsa watak'ila ma masu neman taimako ne



Mai gadi bata hanya yayi yace bismillah amma suna can wajen lambu masu gidan tabi ta wancan flawowin suna can


Fateema shigewa tayi da sauri tana mishi godiya

Tana kaiwa tsakiyar gidan kafin tabi hanyar da mai gadi ya nuna mata tsayawa tayi ta saki baki tana kalle kalle in banda zikiri babu abinda take yi dan tunda take arayuwarta bata tab'a ganin had'add'en gida irin wanan ba hayaniyar da take jiyowa daga wajen lambu ne yasa ta dawo hankalinta ta nufi wajen tana cigaba da kalle kalle



A lokacin Bashir da Aliyu da Nura suna sanye da farin armless iri d'aya da dogon wando suna ta buga ball Bashir inka ganshi a lokacin da su Aliyu bazaka gane su ba dan wani irin kyau da k'iba Bashir yayi ya k'ara zama wani giant



Haleema tana zaune ita da Hameeda da Sumayya suna zaune akan wani had'ad'un kujeru dake wajen suna kallonsu Bashir Haleema tana sanye da wani doguwar Riga tayi parking gashinta tayi wani fresh itama kana kallonta zaka San tana d'auke da ciki ko wata biyu ko uku su Hameeda sun k'ara zama 'yan mata suma sunyi kyau masha Allah sai tafawa su Bashir suke suna a goal sumayya kuma tana kwance ajikin Haleema tana shan madara Haleema ita kuma tana wasa da gashinta




Fateema daga d'an nesa ta tsaya ta zuba musu ido gwanin ban sha'awa dan Sam babu Wanda ta gane a cikinsu duniyar tunani ta tafi na wataran Bashir ya zama mai kud'i suma sun Gina irin wanan gidan suna irin wanan wasanin


Ihun da su Hameeda sukayi na a goal ne ya dawo da ita hankalinta adai dai lokacin da Bashir yaje ya rungume Haleema yana murnar ya cinye su Aliyu ai kamar cewa akayi ya kallo corridor d'in sukayi ido hud'u da Fateema gabansa ne ya yanke ya fad'i yace "Fateema"!


Fateema wani irin da baya tayi data ga Bashir jikinta ne ya hau rawa ta nuna shi da yatsa tana "Bashir"!

*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*


*NEVER EXPOSE YOUR SECRET TO ANY ONE SOME ONE YOU TRUST SO MUCH MAY TURN TO BE THE ONE EXPOSING YOU*



*INA MAMAKIN GAJEN HAK'URIN WASU READERS D'IN WAI BAZASU BARI SUGA YA K'ARSHEN NOVEL ZAI KASANCE BA SAI SU HAU YIMA K'ORAFIN GA YANDA YAKAMATA KAYI HABA DAN ALLAH KU TSAYA KU GA K'ARSHENSA MANA*



*JAN HANKALI*

*KAMAR YANDA NA FAD'A A BAYA DUK WACCE TAGA GYARA A NOVEL D'INA KO SHAWARA TAKE SO TA BANI K'OFA A BUD'E TAKE ZANYI ACCEPTING GYARAN KO SHAWARAR DA HANNU BIYU INSHA ALLAHU*


*BAIWAR ALLAH NAGA K'ORAFINKI AKAN IDAN FATEEMA TA KOMA GIDAN BASHIR NA B'ATA LITTAFINA DARASIN DAYAKE CIKI BAI FITO BA HABA BAIWAR ALLAH MUNA YIWA ALLAH LAIFI MA MU NEMI YAFIYARSA YA YAFEMANA BALLANTANA MU ABU D'AYA NAKESO MURINGA YI ARAYUWA IDAN WANI YAYI ABU KAI MA KA RINGA SA KANKA AMATSAYIN WANDA YAYI ABUN DAN NASAN IDAN KAINE ZAKA SO KAIMA KA SAMU SECOND CHANCE KA GYARA KARKI MANTA BABU LAIFI FATEEMA TA D'AN JI JIKI KUMA KO BABU KOMAI BASHIR ZAI IYA MAIDATA KO DAN DARAJA ZURIAR DAKE TSAKANINSU AMMA KUMA MUTUNCI DA KIMARTA DOLE SU RAGU A IDON BASHIR DAN SHI MUTUNCI MADARA NE IDAN YA ZUBE K'ASA SHIKENAN DAFATAN KINGANE NAGODE SOSAI MASOYANA MASU K'ARFAFA MIN GWIWA MASU YIMIN FATAN ALHERI ARAYUWA MAI SONKA SHI ZAI GAYA MA GASKIYA MAI SANKA SHINE ZAI GA GYARA YA GYARA MA BATARE DA CIN MUTUNCI BA MAI SANKA SHINE ZAIJI ANA CIN NAMANKA AWANI WAJE YA FITO YAYI MAGANA YACE ABINDA AKEYI BAI DACE BA MAI SANKA BA SAI AGABAN IDONKA ZAI NUNA MA SO BA ABAYAN IDONKA MA ZAI NUNA MA SO THANKS FOR D LOVE*



*FADEELA Y KHAN*
*UMMIE*
*MARYAM MRS MAIKWANO*
*SALMA B*



Page 80-85

Atare su Haleema suka juya suka kalli inda Fateema ke tsaye Aguje su Nura suka nufi wajenta suna "Umma" dan ko Fateema tafi haka bak'i babu abinda zai hana su ganeta



Gaban haleema ne ya yanke ya fad'i da tagane Fateema ce juyawa tayi da sauri ta kalli Bashir da ya saki baki da hanci yana kallon Fateema



Fateema kuwa murza idonta tayi sosai dan ta tabbatar da ba mafarki take ba tana cikin murza idonta su Aliyu suka rungumeta


Da sauri ta cire hanunta daga Murza idon da take ta zubawa su Aliyu ido kamar bata tab'a ganinsu ba shafa jikinsu ta fara yi tana tab'a kayan jikinsu cikin mamaki canzawarsu Nura ta rik'o da ya zama dan lukuti sabida jin dadi Fateema cewa tayi "babana Kaine ka zama haka Aliyu ya akayi kuka zama 'yan gayu haka? Mai kuke yi a gidanan?",


Fateema tace tana k'ara binsu da kallo


Bashir tsananin mamaki ne ya hana shi motsawa dan Fateema ba k'aramin bak'i tayi da muni ba tunani yafara yi na abinda ya sameta haka


Aliyu ne yabawa Fateema amsa da " Umma ai nan gidanmu ne Umma tunda kika tafi Abba yayi kud'i"

Ras Ras gaban Fateema ya fad'i ta d'ago da Sauri ta Kalli Bashir dake tsaye ya zuba hannu a aljihu yana kallonsu Haleema da ta gani a gefensa ne yasa gabanta ya k'ara yankewa ya fad'i Nura ne ya dib'a aguje yaje ya kamo hanun Bashir yana "Abba kaga Ummana ta dawo zo muje gurinta" Nura yace yana cigaba da Jan Hannun Bashir


Bashir murmushi yayi yace "naganta Nura maza jeka ka sameta ina zuwa"Haleema tana jin mai yace tayi sauri ta tace "yaya kuje tare mana sai kayi mata iso tashigo kasan ni bata sani ba"


Murmushi Bashir yayi yace "ai ba gurina tazo ba wajen yaranta tazo"


Yana fad'ar haka ya juya ya nufi cikin gidan

Haleema kuwa tana ganin haka tayi shahada ta nufi wajen Fateema gabanta na fad'uwa



Fateema tunda ta tambayi su Aliyu wacece waccan akusa da Abbansu suka ce Auntynsu ce komai na jikinta ya tsaya cak hankalinta ya tashi in banda rawa babu abinda jikinta yake yi dan tasan duk yanda akayi Bashir aure yayi har ta k'araso Fateema bata dawo dai dai ba sai da Haleema ta k'ara ce mata sannu da zuwa ta d'an dawo hayyacinta

Murmushi yak'e Fateema ta kirkiro tace "yauwa"

"Bismillah kishigo kika tsaya daga nan"


Haleema tace tana rik'e Hannun Sumayya


Fateema bin bayanta tayi jiki asanyaye hankalinta in yayi dubu yagama tashitashi

Fateema kafin su k'arasa palon gidan sakin baki da hanci tayi tana kallon irin had'uwa da tsarin gidan ganin motoci har uku a pake yasa hankalinta ya k'ara tashi ahaka suka k'arasa palon tana kalle kalle akasan zuciyarta tana tunanin yanda akayi Bashir yazama mai kud'i haka tunani tafara yi na yanda akayi Bashir ya zama mai kud'i


Ahaka suka k'arasa palon gidan
Fateema sallati tayi da k'arfi Wanda bata San yafito filli ba sakamakon ganin had'uwar palon inda Haleema da yara suka juya da sauri suka kalleta


Wayancewa tayi cikin kunya tana tuntub'e tayi sannu suka yi mata Haleema ta nuna mata kujera da ta zauna



Fateema zama tayi tana cigaba da k'arewa Palon kallo sai sake sake takeyi

Haleema ce tafara ce mata "Ina kwana"

Fateema tace "lafiya lau ya yaran"?

Haleema Murmushi tayi tace " lafiyarsu kalau"daga nan babu Wanda ya k'ara magana a cikinsu
Fateema kuwa in banda sallati babu abinda take yi


Haleema magana tayiwa Hameeda da turanci da "go and get something for your mum to eat(jeki samowa Ummanku Abu taci)"

Hameeda mik'ewa tayi tace "OK Aunty
(To Aunty)"

Fateema mamaki ne ya rufeta dataji suna turanci ai kamar Haleema zuga su Nura tayi suma suka hau magana da turanci


Fateema binsu Nura ta ringa yi da kallo d'aya bayan d'aya Dan gani take kamar ba y'ay'anta ba Dan y'an gayu suka zama sosai gashi kyaunsu ya k'ara fitowa Sumayya ma tafi tafiya da imaninta Dan kamar baturiya baturiya sabida hasken da tayi gashinta ya k'ara tsayi


Hameeda abun motsa bakin da ta ajiye agaban Fateema ne yasa ta d'auke idonta daga kallonsu Nura ta dawo da kallonta kan Hameeda da ta k'ara zama 'yar buduruwa tayi kyau had'a ido sukayi da Hameeda

Hameeda ta sakar mata murmushi tana "Umma bismillah gashi kici"


Hawaye ne yafara k'ok'arin zubo mata data ga yaranta suma suna Neman su maidata bakuwa abunda ya yafi d'aga mata hankali bai wuce yanda Nura dan Auta yaje ya kwanta ajikin Haleema yana Dana waya wani irin zafi taji zuciyarta na mata da taga yanda Haleema ta ringa hira dasu Hameeda da turanci gani take tana sane ma suke turancin wani k'ullutu ne ya tsaya mata a makogaro ta d'aure tace


" Baiwar Allah Ai ko banyi magana ba ya kamata ace kisan wajen y'ay'ana nazo da uban y'ay'ana

Haleema mik'ewa tayi da sauri tana "lah yi hak'uri Aunty bari na kira Yayan ai gasu Hameeda nan"

Fateema bata San lokacin da ta ja wani uban tsaki tabita da harara ba Haleema kuwa upstairs ta nufa da saurinta tana mamakin halin Fateema


Fateema kuwa tana ganin ta hau saman bene ta dawo da kallonta kan su Hameeda tana "Aliyu Hameeda Sumayya Nura kun mantani ne?ko Baku San matsayina awajenku ba?ya naga bakwa farinciki da zuwana?
Kun manta nice Ummanku"?


Aliyu cewa yayi "Umma bamu mantaki ba munsan kece Ummanmu kece ma kika manta damu kika tafi kika barmu"

Hankalin Fateema ne ya tashi take hawaye ya hau zubo mata


Haleema kuwa tana hawa sama ta nufi b'angaren Bashir a d'aki ta sameshi yana tsaye agaban mudubi yana sanye da kana nan kaya kyaunsa ya fito ainun acikin farar Riga mai dogon hannu da bak'in wando turare yake fesawa Haleema ta shigo murmushi ya sakar mata ta mudubi a lokacin da ya gama fesa turaren ya juyo yana "uwar biyu yau ko wankan baki zo kinyimin ba"

Wani so da kishin Bashir ne yaringa zagaye kowane lungu da sak'on jikin Haleema a lokacin da ta shigo d'akin Dan wani mugun kyau taga Bashir ya k'arayi take tayi tunanin watak'ila dan yaga Fateema tazo shiyasa yayi wanan kwalliyar d'aurewa tayi ta kirkiro murmushi tana


"Afuwan yaya muna hira da ummansu Aliyu ne"

Bashir rungumota yayi yana "au bata tafi ba"

Haleema narkewa tayi a k'irjinsa tace cikin rawar murya "eee bata tafi ba cewa ma tayi in kiraka"

Jin abinda tace ne yasa ya d'agota yace "ki kirani kuma mai zan mata ba wajen y'ay'anta tazo ba"

Haleema cewa tayi "ta dai ce na kiraka"

Bashir agogon hanunsa ya kalla yace "nifa sauri nakeyi yau na makara wlh ko dayake muje inaga so take mu gaisa"


Hanun Haleema ya rik'e sukayi waje

Fateema kuwa kuka ne yaci k'arfinta da taga yanda su Aliyu suke cewa ta tafi tabarsu Auntynsu ce ta ringa kula dasu

Da sauri ta fara goge hawayenta alokacin da su Bashir suke sauk'owa wani irin fad'uwa gabanta ya hau yi data hango Hanun Bashir rik'e dana Haleema zubawa Bashir ido tayi wani irin kibiyar sanshi ya ringa sok'arta Dan wani mugun kyau taga Bashir ya mata kamar Saurayi bata tab'a Sanin Bashir ya kai haka kyau ba sai yanzu


Ahaka su Bashir suka k'araso palon hanunsu rik'e da juna Fateema da sauri ta sunkuyar da kanta k'irjinta kamar ya fad'o

A kujerar dake fuskantar ta su Bashir suka zauna Haleema tana so ta bar palon ta basu guri suyi magana amma Bashir ya rik'e mata Hannu Bashir cewa yayi



"Aa Fateema kece a gidan namu sannu da zuwa"


Fateema d'agowa tayi da sauri suka had'a ido da Bashir gabanta ne ya k'ara fad'uwa dan ayanzu da taga Bashir akusa yafi had'uwa akan yanda taganshi daga nesa gani take ma kamar ba Bashir mai robobi da ta aura ba


Murmushi ta kirkiro tace cikin rawar murya "eee nice ina kwana"?


Bashir murmushi yayi sakamakon mitsininsa da Haleema take yi akan ya cikata duk abinda sukeyi Fateema tana kallonsu ji take kamar ta shak'e Haleema


Bashir yana murmushin yace "Lafiya lau Fateema ya mai gidan naki"?

Fateema hawayen da take b'oyewa ne yafara zubo mata ta kasa magana

Haleema kuwa tana ganin haka tayi Sauri ta fusge hanunta ta mik'e tana "maza Ku tashi mu tafi kitchen muje mu d'ora girki"

Su Hameeda mik'ewa suka fara yi da sauri suna nufar kitchen wanan na cewa Aunty coucous zaki dafa mana wanan nacewa Aunty Fried indomie zaki dafa mana ahaka suke shige kitchen d'in Fateema na kallonsu



Bashir kuwa wani irin farinciki ne ya ringa ratsa shi Dan ko ba a fad'a mishi ba ayanda yaga Fateema yasan tana jinjiki ganin su Haleema sun shige ne yasa ya d'an d'aura fuska Dan bayaso Haleema ta fuskanci wani Abu atsakanin shi da Fateema

Bashir cewa yayi


"Fateema ya akayi inasan zuwa kasuwa ne dan na makara"


Fateema zamowa tayi daga kujerar ta d'urkusa ta fashe da kuka

Bashir "subhanallahi yace yana "Fateema lafiya kuwa mai yafaru"?


Fateema kuka take sosai ta kasa magana d'aurewa tayi ta fara magana cikin sheshek'ar kuka tana "Bashir Kafin nace komai Dan Allah dan annabi ka yafemin abinda nayi maka ka dubi zuriar dake tsakaninmu ka yafemin nasan nayi maka ba dai dai ba wlh Bashir nasan hakkinka ne ya ringa bibiyata nasha wahala nayi dana sanin rabuwa dakai Bashir da zan gaya maka irin wahalar dana sha da ka tausaymin tiryan tiryan Fateema ta fara bashi Labarin irin wuyan da tasha a gidan Lado babu abinda ta b'oye mishi har zuwa sakin da yayi mata a k'arshe ta k'ara da " dan haka Bashir dan Allah ka yafemin wlh nayi nadamar abinda nayi maka dan Allah ina rok'on alfarmar dan Allah ka maidani d'akina insha Allahu zan gyara halina zan kasance mai bin umarninka zan ma biyaya ko k'ara ka ajiye wlh bazan tsallake ba"

Tunda ta fara magana Bashir yayi tagumi yana kallonta duk kukan da take babu lokacin da yaji d'igon tausayinta hasali ma tagumin dayayi tunano irin rashin mutuncin da Fateema ta ringa shuka mishi yake murmushi Bashir yayi yace


"Ayanzu Dana zama mai kud'i kika zo Neman yafiyata
Fateema dan Allah bakiji kunya ba da kika bud'i baki kikace na maidaki d'akinki baki San zaki nemi yafiyata sai da kikaje gidan wani kika sha bak'ar wahala"

"Fateema anya kina da kunya kuwa kin manta abinda kika yimin"

"Karki manta fa nine mistsiyacin nan mai robobi karki manta fa nine Wanda kike cin k'walar rigarsa ki zageni tas agaban yarana"


"Karki manta fa tafiya kika yi gidanku dan banida ko sisi kika tsallaka yaranki bakisan halin da zasu shiga ba"

"Karki manta fa nine mitsiyacin nan daya zo k'ofar gidanku kika min korar kare da na tafi can da tsiyata ke kinsamu mai kud'i babu abinda zakiyi dani"

"Fateema duk baki duba wanan abubuwan ba sai yanzu da kikaji labarin nayi kud'i kika kaso aurenki kika nad'o k'afa kika taho wajena Dana maidaki d'akinki ance miki nima jaki ne ance miki Nima Mara tunani ne kin dubi yaran naki alokacin danazo k'ofar gidanku ina rok'onki da ki taimaka ki dawo Sabida yaranki kin manta abinda kikace Min ranar Fateema"


Wani irin murmushin tak'aici Bashir yayi dan zuciyarsa zafi take masa sosai tamkar yanzu Fateema ta ringa shuka mishi rashin mutunci


Fateema kuwa kuka take sosai tana "wlh Bashir ba dan kud'inka na dawo ka yafemin ba wlh ban ma San kayi kud'i ba dan Allah kayi hak'uri ka bar tuna baya"


"Bashir mik'ewa yayi yace "Fateema kenan inaso ki farka daga mafarkin da kikeyi dan na Riga da nasan Fateema Lashe money akan kud'i babu irin karyar da bazata yi ba"


"Fateema da ta kasheni da bakinta sabida kud'i tace cutar TLC ta kamani"


"Fateema bata tab'a sona ba dama can sai dan kud'i dan ina da kud'i ta aureni dana talauce ta tsaneni har ya kaita da ta gujeni"


"Ayanzu kuma dana yi kud'in ta k'ara dawowa wai tana sona Fateema kenan inaso na fad'a miki wani Abu idan mafarki kike yi ki gagauta farkawa ni Bashir bazan tab'a iya maidaki d'akinki ba dan ba San Allah da Annabi kikemin ba Fateema ada nasoki amma ayanzu babu d'igon sanki ko d'aya a zuciyata dan Allah ya bani mace tagari wacce ta maye gurbinki a zuciyata Haleema nasan ko awane irin hali nake wlh Zata zauna dani bazata tab'a gujemin ba Mutuncinki ya Riga da ya zube a idona dan kinsan mutunci madara ne in ya zube a k'asa baya kwasuwa nasha fad'a miki Allah yana sane dani bai zama lailai na dauwama a talauci ba amma ina idonki ya rufe da San kud'i Wanda har ya kai ki ga kashe aurenki da kanki Alhamdulillah naji dadi da Allah yasa kika zo kikaga yanda Allah yayi ikonsa na zama mai kud'in baki zo kin kwashe yaranki ba"


"Ko ayanzu kinsan muna cikin rufin asirin Allah zan iya yafe miki abinda kika min sabida Allah da yaran dake tsakaninmu amma batun in maidaki d'akinki bazan tab'a iyawa ba dan Haleemata ta isheni rayuwa"


Wani mugun kuka Fateema ta fashe dashe har da majina ta fara magana


"Bashir yanzu idan kayi min haka kayi min adalci?

Bashir ka manta samarina nawa na kora nak'i aurensu sabida kai"


Wani mugun tsawa Bashir ya d'aka mata ransa a matuk'ar b'ace yana "ke har kinsan wani adalci kin manta yarana kika zubemin kikayi tafiyarki

Wane samarinki kika k'ora dani?
babu wani saurayi da kika k'ora dani dan a lokacin masu zuwa Neman aurenki basu kaini rufin asiri ba ai Fateema karki yaudari kanki dama can baki tab'a sona ba domin da kina sona wlh kowane irin hali nake zaki zauna dani duk runtsi duk wuya ba mata bane suke zaune da mijinsu sabida so suringa wanki a gida suna surfe sabida su rufawa mijinsu asiri

Wata ita take kwantarwa da mijinta hankali idan bai samo komai ba tayi fafutuka ta nemo suci"


Fateema gayamin wane kika tab'ayi a ciki nasan bakida amsar bani magana d'ayace kin rainawa samuna domin ni a lokacin ina ganin a rufin asiri nake kullum cikin zagina kike kina min gori akanki na kusa zama k'aramin mahaukaci akan kud'i kika gujeni kika je kika auri wani har kinada bakin magana"

Wani irin girgiza kai Bashir yayi cikin tak'aici yace "Fateema Allah ya sauwake na maidaki d'akinki Haleema ta isheni rayuwa ta rik'e min y'ay'a tamkar ita ta haifesu dan haka kije ki nemo wani mijin ki aura amma bani ba in kina zancen indawo dake sabida y'ay'anki ai baki dubi y'ay'anki ba kika gujesu"


Daga haka Bashir ya nufi k'ofa Fateema wani irin kuka ta fashe dashi ta bishi da gudu tasha gabansa ta rik'e mishi k'afa tana yayi mata rai wlh badan kud'insa ta dawo ba.
*Y🅰TSUN MU*🤚🏻🤚🏻🤚🏻🤚🏻 _ba d'aya bane_



*Written by*

💅💅 *SADNAF*💞



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*



*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


*A short and interesting story*




Page 85-90



Bashir fusge k'afarsa yayi ya rab'e ta gefenta ya nufi wajen motarsa batare da ya tsaya saurarta ba


Fateema k'ara mik'ewa tayi dagudu tabi bayanshi ta rik'e murfin motar tana


"Haba Bashir kayiwa girman Allah ka yafemin karka manta fa Allah ma muna mishi laifi ya yafemana karka wulak'antani Bashir Dan kayi kud'i" Fateema tace tana k'ara fashewa da kuka


Tunda tafara magana Bashir ya tab'e baki yana kallonta Bashir cewa yayi "Wai wane irin yafiya kuma kike nema awajena nace na yafe miki sabida Allah da yaran dake tsakaninmu yanzu kuma mai kikeso nayi miki"?


Fateema langab'ar da kanta tayi tayi k'asa da murya tana
" Bashir ai nasan ka yafemin dan Allah so nake ka manta komai ka maidani d'akina"


Bashir dariya ya k'yalk'yale dashi yace "Ashe ana mutuwa ma adawo Fateema ai nafad'a miki bazan iya maidaki d'akinki ba dan gaskiya koda na aureki ayanzu bazanyi Adalci ba dan babu sanki ko k'waya d'aya a zuciyata kidai yi hak'uri kisamu wani ki aura ni na miki alkawari duk abinda kikeso zanyi miki zan kuma baki jari insha Allahu ko dan yaran dake tsakaninmu ban miki Katanga da y'ay'anki ba duk lokacin da kike so ki gansu zaki iya zuwa ki gansu in kin bukaci ma akai miki su suyi miki kwanaki za'a kawo miki su"


Fateema wani mugun kuka ta fashe tana "Haba Bashir ya zaka min haka nasan abinda nayi maka da wuya ka manta amma ka dubi girman Allah kayi hakuri ka maidani d'akina na rik'e y'ay'ana Bashir wlh a yanzu nayi hankali bazan tab'a abinda zai Sosa maka rai ba"


Bashir dafe kansa yayi Dan ya rasa yanda zai yi ya ganar da Fateema bazai iya rayuwar aure da ita ba a yanzu


"Fateema kinsan mai nakeso kigane ni mutum ne mai tsananin kishi bazan iya auranki ba sabida bayan ni wani ya Riga da ya sanki bazan iya kwasan sauran wani ba wanin ma wanan bagidajen k'auyen Dana ganki dashi Fateema bazan iya sakin jikina dake ba ina maidaki d'akinki bazaki ji dadin zama dani ba dan na dade da gogeki a zuciyata dan haka nima kiyi hak'uri bazann"


Fateema bata bari ya k'arasa maganar da yake ba ta saki murfin motar ta rungumeshi gam gam tana "Bashir dan Allah karkamin haka idan baka dawo dani d'akina ba zan iya mutuwa wlh yau d'inan dana ganka Allah ya d'ora min wani mugun sanka wlh zan iya rayuwa da kai akowane irin hali wlh Bashir badan kud'inka yanzu nakeso ka maidani d'akina ba wlh bama San kayi kud'i ba dan Allah Bashir ka taimaka min kayi min rai"

Fateema tace tana fashewa da matsanacin kuka tare da k'ara cusa fuskarta a k'irjinsa tana shak'ar kamshin jikinsa


Bashir Tunda Fateema ta rungumeshi yake ta k'ok'arin raba jikinsa da nata dan mugun runguma tayi mishi

Haleema dake lab'e a k'ofar kitchen duk maganar da su Fateema sukeyi tana jinsu tana jin sun bar palon tafito daga kitchen da sauri ta tsaya abayan labule tana kallonsu ganin Fateema ta rungume Bashir yasa ta dafe k'irjinta cikin tsananin tashin hankali k'irjinta kamar ya fad'o sabida tsabar kishi gani take Bashir shima runguma Fateema yayi



Bashir da k'yar ya yakice Fateema daga jikinsa yace cikin b'acin rai


"Fateema wai meyesa bakida hankali ne nace miki bazan iya maidaki d'akinki ba ko ana dole ne dan Allah ki rabu dani"



Daga haka Bashir motarsa ya shige yabar Fateema data d'urkushe akasa tana kuka bin motarsa tayi da kallo har yabar gidan


Fateema kuka take sosai tana k'ara nadamar abinda tayi babu abinda ke yawo ahancinta sai kamshin turaren Bashir


Hameeda da Haleema tasata ferayen dankali fitowa tayi dan ta gaya mata ta gama feraya dankali taga Haleema ajikin labule tana lek'e


Hameeda ahankali ta nufi k'ofar dan taga wa Haleema ke lek'e Fateema ta hango a d'urk'ushe a k'asa tana ta kuka da sauri tayi waje tana "Umma"


Haleema da sauri tabar jikin labulen ta hau sama gabanta na fad'uwa tunani ta fara yi watak'ila Bashir ya dawo da Fateema inkuwa hakane tasan bora zata zama dan matsawar Fateema ta dawo taga alamar sai ta janye hankalin Bashir sabida tafita shekaru kuma tasan ayanda ake fad'a matar fari itace mata duk wacce zata shigo abayanta ne ta kuma San dak'yar idan Bashir bayasan Fateema ahaka ta shige d'akinta tana tunane tunane



Hameeda kuwa tana fita waje itama d'urk'usawa tayi agaban Fateema tana "Umma Lafiya mai yasa kike kuka"


Fateema kuka ta k'ara fashewa dashi ta rik'e hanun Hameeda tana "Hameeda Abbanku ya daina sona yace bazai maidani d'akina ba Abbanku yana so ya rabani daku"



Hameeda cewa tayi "bangane ba Umma kamar ya abbanmu baya sanki"


Fateema rungume Hameeda tayi tace "Auntynku tasa Abbanku ya koreni yace bazai zauna dani ba da Auntynku zai zauna Hameeda Ku rok'i

Please Login or Register in order to submit comment