Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki ta cigaba da juyashi occasionally har sai da manja ya ratso jikin egushi d'in sai tasa
ruwan tafashashshen nama ta zuba ta juyashi sosai sai ta rufe. wanke kpomo (ganda) tayi ,
Sai ta bud'e tukunyar ta zuba kpomo d'in ruwan zafi ta qara juyawa tayi saitarufe bayan wasu mintina sai tasa naman saniya sai ta juya bayan minti kad'an sai tasa stock fish da kifi banda juya wa tayi ta barshi ya k'ara dahuwa, for some minutes sai kisa spices dinki ki Kawo ugu leaves d'inki da kika wanke kika tsane ki xuba ki barshi live 5 minutes sai ki sauke.
To miyar egushi ta dahu gyara kitcing sukayi suka kai komai dining , lokacin sallah ne yayi bayan sun idar sallah sun fito suka ga zaid a falon ," yaya zaid barka da dare suka ce "."amsawa yayi zama sukayi suna kallon channel na qwallo da ya kama, shiru sukayi baki d'ayansu .

A fanni su hajiya qarama kuwa, Shamsiyya ce"ta d'auko qullin turaren da boka ya bata sawa tayi a kasko qamshi ya gauraye falon , gyara falon tayi tas , Hajiya qarama ce ta fito a d'aki tana cewa shamsiyya kaina fa ciwo yake yi,qamshin turaren ta shaqa sai tace...

Rubutawa da tsarawa📝
*HAD SEEYAEMAH CE🌺*

Al k'alami yafi takobi inji ni siyamah

share
comments👏🏼

Wannan page naki ne fa y'ar uwa rabin jiki keda masoyinki
Fatima kabir Dauda (ZARAH) da yusuf (IMAM).


🧑‍⚖️BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya


_FREE BOOK_

_PAGE 21_

Hajiya qarama ce ta fito a d'aki tana cewa shamsiyya kaina fa ciwo yake yi,qamshin turaren ta shaqa sai tace...

A garin Abuja kuwa shiri suke tayi Barrister Shuraim da Doctor najeeb zasu bikin abokinsu wanda suka gama karatu a london , abokansu ne suke ta qiransu a waya akan mutanen U S A ma sun iso amma su nan abuja da maiduguri nawa yake har yanzu basu iso ba.
Barrister Shuraim ne ya karb'e wayar yace"Kufa kiyayeni wato anjima ba'a had'u ba ko, to muna hanya yanzu haka kaya muke had'awa saboda three days zamu zamu,kai washe garin d'aurin aure ". Allah kawoku lafiya .
Ameen sukace "Barrister Shuraim ne yace"karfa a ishemu mu da mota zamuzo ba jirgi ba bare a ce bamu iso da wuri ba , kashe wayar yayi cikin farin ciki , tashi sukayi sallama sukayi wa mommy Amnah ce tace "yaya zanbiku" doctor najeeb ne yace"bazaki ba".
Tafiya sukayi mommy ta musu fatan alkhairi tafiya suke cikin nutsuwa saboda Barrister Shuraim baya son gudu a mota, isar su Garin,maiduguri keda wuya suka wuce direct gidan su ango, abokansu suka gani da yawa side na samarin gidan,suka shiga , Abinci a ka ajiye masu kala-kala.

washe gari gidan ya d'auki baqi kala _kala iri_iri wasu da ga some country and some town , mutanen Azare ne suka iso garin borno mommy ce qirjin ta ke dukan tara-tara bata san dalili ba addu'a taringa yi Allah sa ta tarar da alkhairi isarsu keda wuya suka samu ana ta shirin d'aurin aure ,su mommy ne suka shige cikin gidan daddy a wajen wajen abokansa ua tsaya , a wajen su ango kuwa kowa ya gama shiryawa za'a tafi d'aurin aure amma basu ga Barrister Shuraim ba , Najeeb ne ya hango shi ya qudundune a cikin blanket , zuwa yayi ya tab'a shi jikin sa yaji da zafi sai karkarwa yake ba halin magana hankalin,y'an d'aurin aure ne ya tashi ciki kuwa harda ango , Doctor najeeb ne ya masa allurar typoid , tare da d'aura masa drip lokaci ne yake tafiya har aka qira ango akan a ina suka tsaya su ake jira lokacin d'aurin aure yayi , Najeeb ne ya kwantar masu da hankali yace"su tafi d'aurin auren zai kula dashi ay yasami bacci yanzu insha allahu zuwa anjima qalau zai ta shi fita sukayi badan ransu yaso ba suna wa abokin nasu fatan samun sauqi domin Barrister Shuraim na mutane ne , d'aya a cikin abokansu wato Sir khaleel,ne yace"zai zauna tare da najeeb kar a barshi shi kad'ai , barinsu akai tare Sir Khaleel ne suke hira da najeeb a hankali,da na bayan rabuwa sunyi,nisa acikin hirar tasu suka ga alamar Shuraim yana motsa qafarsa tashi sukayi baki d'ayansu Sir Khaleel ne yashiga toilet ruwan wanka ya,had'amasa taimaka masa sukayi yayi wanka daganan suka bashi abinci yaci jikinsa yake ji wani iri amma a haka ya daure yanuna wa abokansa bakomai , bayan y'an d'aurin aure sun dawo ne sukai sallah a ka ci,abinci shiri,kowa yafara saboda zuwa dinner da za'ayi Ango da tawagarsa ciki harda Barrister Shuraim , Doctor najeeb ,Sir khaleel dama wanda ban fad'a ba , a tawagar amarya kuwa su Amal da Asiya ne suna tawagar Amarya mommy zama tayi bata biyosu ba ita a ganinta zuwa wajen dinner na yara ne .
Ga yau tunda suka zo garin maiduguri zuciyarta ke ta buga , tawagar y'an mata ne suka isa wajen,Dinner kallo ne yadawo kan,Amarya da Ango,Dj ne ya sau waqa mai sanyin dad'i y'an mata ne suka fara taka wa cikin iya rawar tare da bin waqar amarya da ango photuna ake d'auka ana cukin d'aukan photon ne Barrister Shuraim idanunsa ya hango masa prettyn sa ta mafarki baki yasaki ya na kallon ta ganin alamar zata b'ace masa ya sa shi saurin bin bayansu , jiyayi an tab'i shi ta baya ana cewa "Hi baby yakake ni suna na Annah kaifa ya sunanka?". sauri ya cigaba dayi ganin annah bazata barshi ba yasa ya juyo yana galla mata harara sau shi tayi amma mai yarasa su Amal sama ko qasa sukayi bai gansu ba.
wucewa yayi fuuuuu ya shige motarsa ran shi a matuqar b'ace gida ya nufa ya koma blanket tun y'an dinner basu tashi ba Sir khaleel ne ya hango abin da ya faru tasowa yayi yazo gun y'ab matan tambayarsu yayi maiya faru cemasa sukai basusan komai ba amma ko zai,iya taimaka musu da sunan gayen can had'e da phone number nashi ,Barrister Shuraim ya fad'amasu numbern , wucewa yayi yabarsu a tsaye Annah ce tace "Gaskiya gayen nan ya had'u ko sunansa na masu class Barrister Shuraim gaskiya ni ina sonsa kuma auransa zanyi , murmushi mai tsada da kuma ma'a noni ummi ta sake gaskiya qawata banga laifinkiba,dole a lokaci guda ki haukace a son wannan gayen saboda ya had'u ta ko'ina gaskiya qawata zaku dace,harararta annah tayi mundace ko zamu dace kike cewa kun dace na ce shikkenan , kamal ne yazo yaja su,annah yana cewa"Sorry baby nabarku anan wallahi na gamu da abokaina,wanda najima,bangansuba shiyasa, Annah ce tace"lah bakomai "aranta kuma tana cewa da baka tafi,ba ay bazanyi kamu ba , motarsa suka nufa yayi sallama da abokansa direct hanyar hotel in dasuka sauqa ya nufa , akan washe gari kuma zasu wuce Abuja .
Su Amal,da Asiya ne suka dawo cikin farin ciki bacci sukayi saboda sungaji a b'angaren su abba kuwa tad'in bayan gamo sukayi a cikin abokan,abba kowa yana tsoron tambayar ina d'ansa shuraim miyasa baizo dashi ba dake su a iya saninsu d'an uwansa sani,yace "tashi zasuyi sukoma Axare basusan a lokacin baya qasar ba .

washe gari kowa yayi wa ango da amarya fatan alkhairi daganan,mutanen Azare da abuja suka tafi su Barrister Shuraim ma tafiya sukayi domin jiki,yayi sauqi amma tunanin prettynsa yadawo masa sabo.
Bayan sati d'aya ne deputy gomna ya taho izuwa yadda yake sauqar baqi zuwa yayi ya samu sani da adamu sai matar adamu gaisawa sukayi cikin farin ciki na anjima,ba'a,gamu ba, cikin dare ne suka saka jajayen kaya harda matar adamun daganan suka d'auki qwarya ganinsu sukayi a wata fatfajiya ta matsafa murna,sukayi na sun samu qari wato matar adamu qwarya aka maiqo mata ta jini ta shanye daganan itama tayi wanka da ruwan jini,shine alamar tashiga qungiyar su kowa buqatarsa a wajen bai wuce kud'i ba amma fa banda...
Rubutawa da tsarawa📝
*HAD SEEYAEMAH CE🌺*

Al k'alami yafi takobi inji ni siyamah

share
comments👏🏼


‍⚖️BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya


_FREE BOOK_

_PAGE 22_
cikin dare ne suka saka jajayen kaya harda matar adamun daganan suka d'auki qwarya ganinsu sukayi a wata farfajiya ta matsafa murna,sukayi na sun samu qari wato matar adamu qwarya aka maiqo mata ta jini ta shanye daganan itama tayi wanka da ruwan jini,shine alamar tashiga qungiyar su kowa buqatarsa a wajen bai wuce kud'i ba amma fa banda...
Sani da shi ba kud'i ne a gabansa ba, Shi abin da yakeso bai wuce ya tarwatsa rayuwar d'an uwansa da iyalansa , kamar yadda ya fara da raba shi da d'an sa wato Shuraim kowa buqatarsa ya fad'a amma mai sai suka ga sani shine ya fad'i akasin tasu madam wato matar adamu ba'abinda ya bata mamaki kamar yadda taga yawancin manya qasar sune a wannan wajen ciki wannan daren da yake mahuta a wajen bawa amma su sun tashi domin cikar wani buri naso amma kuwa harda y'an siyasa ma'ana dai ga deputy gomna suna tare bayan dare ya tsala aka umarcesu da kowa sai yakawo jinin mutum biyu , bayan sun dawo gida deputy gomna , Anan ne yake cewa abokansa kowa yayi qoqari yakai jinin mutum biyu saboda a halin yanzu ba irin kud'i da bashi da shi kamar yadda ba irin muguntar da bai iya ba mulki kuwa yanzu yafara saboda yadda mutane suke sansa yasa yake son yafito takarar senater , Sani hankalin sa baya tare dashi domin yana tunanin ina zai samu jinin mutum biyu maganar dayake a zuciya ce tafito fili Adamu ne yabashi ansa kidnipping yara da manya zamuyi , deputy cewa yayi shikuma asibiti yake zuwa yasamu jarirai da aka haifa saboda yanzu siyasa ta gabato kuma yana son zama senater ga abinda yake damun sa yanzu ance sai yabada mutum mafi,kusanci a rayuwarsa kafin ya zama senater , wazai bada Annah! ko fulani! ?yake tambayar abonsa , Shiru sukayi suna tunani, "Ina bazan iya bada Annah ba sai dai,na bada matata fulani saboda annah itace farin cikina ita y'a d'aya tilo a gareni zan iya komai saboda annah tasamu farin ciki a rayuwa ciki kuwa ko zan rasa mulkina .
Bayan taron su ya watse kowa ya kama gabansa Alhaji adamu da matar sa suka biyo sani izuwa Azare , Baba adamu ne ya qira y'ar sa ummi akan tayi haquri sun wuce Azare bazasu samu damar zuwa ganinta ba .

Agidan,su najeeb kuwa shiri ake tayi khalifa da abdallah zasu tafi qasar madina , Amnah ce take cewa"yanzu haka zamuyi missing naka yaya khalifa , murmushinsa mai tsada yayi yace nima zanyi missing naki rigimammiyar gidanmu baki ta turo gaba, abdallah da zuwansa kenan yace"Haba littile amnah zaki fara ko ?"."Baki ta qara turo tace aa , yawwa yaya abdallah inkaje madina kasamomana aunty acen kaji?kaga yaya khalifa yama wayo yana da aunty nanah ,yawwa wai mai yaushe zamu kaimata ziyara ne kam har na qosa ku dawo musha biki wallahi"."karkidamu auta nan bada jimawa ba zamu remain two year insha allahu to karki damu kanki , "To Shikkenan Allah dawo mana dakai lafiya "."wato ke yarinyar nan san kanki yayi yawa mai laifin kice Allah dawo daku lafiya amma sai kika ware"
Harararsa tayi tace"Bakaine kafiya takurani ba agidan nan gwanda ma kaje ka zauna karka dawo ni,yaya khalifa kad'ai nake so,ya dawo"."wallahi yarinyar nan kifita a ido na kar na zare belt ina na maki duka,a,gidan nan .
Su mommy da daddy ne suka sauqo sannu da saqowa sukai ma iyayen nasu daganan Amnah taja jakar yayanta khalifa tad'auki ta goyon sa ta goya amma taqi kallan ta abdallah , qwafa yayi yace"yarinyar nan taga makoncina , khalifa ne ya ja,mar jakar shikuma yad'auki ta baya suna fitowa suka samu Barrister Shuraim,da doctor najeeb kowa a bakin motarsa mommy da daddy ne sai auta suka shiga motar sa ,khalifa da abdallah kuma motar najeeb , Drivern gidan ne yabiyosu a baya,Air pot Suka tasarwa isarsu keda wuya suka fito suna qare wa wajen kallo kamar ba yau ne suka dawo a london ba suna a ka fara qira Sunan su shuraim aka fara qira wato y'an rakiya sai su,masu zuwan su khalifa mommy ce tayiwa yaranta nasiha bayan sun d'ago,masu hannu sun shiga ne Barriater Shuraim yake jin wani,iri aransa baya manta farkon,Shigarsa jirgi zuwa egypt cikin farin ciki shima nasa iyayen suka,rakosa amma sai mai bai sake kallonsu ba tundaga wannan ranar Addu'a yake a ransa Allah yakaisu lafiya juyawa yayi yaga su mommy da daddy amnah suna d'ago masu hannu , hannu ya d'aga masu ya shiga jirgi sai dai muci Allah yakiyaye .

Mommyn su Asiya ne suna cikin mota suna tafiya Daddy yace"zamu tsaya a kaduna saboda yarinyar nan tagaisa da iyayenta , daganan mugaisa da adamu , murna a wajen Amal ba'a magana qiran yayanta tayi a waya tagaya masa zuwa su gidan yazo yagaya wa mama akwai manyan baqi su amal na hanya gidan suka gyara sai ga zarah tazo ita da mimi sukayi girkin karb'ar baqi baba yana gona ya dawo gida da zabi had'e da qwai yasa aka dafa masu qwai aka musu farfesin kaji saboda zuwan y'ar sa abin qaunarsa tare da iyayen gidanta .


Bayan isowar su Amal gida ya d'au ihu ana murnar zuwan Amal rungume mamanta tayi tana farin cikin jin d'umin mahaifiyar ta kuka tasaka mama tace"zaki fara ko ni banson shegantaka "murmushi Amal tayi tace"nayi kewarku mama "."muma munyi kewarki y'ar baban ta,ganin bazasu rabu ba yasa mommy tayi gyaran murya kunya ce ta kama Amal in ganin mommy tana ganin su , murmushi mommy tayi tace"Y'a ta yau in kuma ni kikejin kunya mimi ce shigowarsu kenan ita da zarah suka taho da gudu suka rungume Amal murmushi tayi tana mai sake qanqame qanwarta tare da aminiyar ta murna suke sosai , mama ce tace "baku ga baqi bane ,durqusawa har qasa sukayo sukace"ina yinin ku"."Lafiya qalau yarana ".
maman su amal ce take mamakin fara'ar wannan dattijuwa Amal ce tanunawa siatern ta qanwarta da aminiyarta rungumesu tayi tana maijin farin ciki a ranta, tana mai jin sonsu ya na shigarta kamar yadda son amal ya shiga zuciyarta a lokaci guda.
mama ce tayi wa mommy jagora suka shiga palour kayan abinci kala-kala aka ajiye mata farfesun naman tafara ci bata ga su amal ba tambayar mama tayi ina suke ashe har sun fita sunyi gidan su zarah Abba da daddy ta gani a zaure suna cin abinci durqusawa har qasa sukayi suka gaida abban amal yayi murnar ganin yadda y'ar sa tayi kyau sosai , usman ne ya tambayesu ina zasu"?."yaya zamu gidan su zarah ne mugaida mama ,bayan sun isa gidan su zarah sun gaida mamanta tana mamakin girma da kyau da Amal ta qara ne sai suka dawo gida mommy suka samu suna hira da mama har mama tasaki jiki da mommy suna hira da ke daga mama har mommy wayayyun mutane ne sun iya zama da mutane sunsan kan ta bi da d'an adam .
Baba yake godiya da irin ruqon dasukayi wa amal kuma yana mai roqon Allah taimakesu akan komai .
Baba bai yi niyyar barin
su tafi da amal,ba amma dayaji cewa ansata a makaranta kuma ba aiki take ba sun d'auke ta kamar y'ar su kuma sunyi wa baba alqawari duk rintsi duk wuya zasu kula da amal , Baba ne yake gaya wa Alhaji al ameen dalilin zuwar y'arsa aikatau bakomai yajawo ba sai...


Rubutawa da tsarawa📝
*HAD SEEYAEMAH CE🌺*

Al k'alami yafi takobi inji ni siyamah

share
comments👏🏼



BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya


_FREE BOOK_

_PAGE 23_

Baba bai yi niyyar barin
su tafi da amal,ba amma dayaji cewa ansata a makaranta kuma ba aiki take ba sun d'auke ta kamar y'ar su kuma sunyi wa baba alqawari duk rintsi duk wuya zasu kula da amal , Baba ne yake gaya wa Alhaji al ameen dalilin zuwar y'arsa aikatau bakomai yajawo ba sai...

Kindnipping na amal da akayi million 30 Suka buqata amma bamu da kud'in biya , qanina ne yane ma min rancen million 30 bata hanyar da za'ayi na biya kud'in sai da muka ga lokacin da aka iba mana na biyan kud'i yayi a wannan lokacin ne qanina adamu yazomin da maganar,mu kaita aikatau amma na lokaci kad'an ne saboda musami hanyar biyan kud'in kud'in yace min an biya amma zata jima ,banyarda da zuwan amal ba amma kuma adamu ya min bayani cewa shima zai koma wajen abokinsa da zama a garin Azare shiyasa nabar ta ta tafi saboda yace zaikulamin da ita akoda yaushe ina mata addu'a dani da mahaifiyarta ,amma alhamdulillah naji dad'in had'uwar ka da y'ata kuma nagode ma ku da irin yadda kuke kula da ita ,lokacin sallah yayi ku tashi mu tafi masallaci , daganan sai mu wuce cikin gida muci abinci ,masallaci suka tashi suka tafi .

A cikin gidan kuwa su amal ne suka shigo d'akin su amal suka wuce direct bajewa suka yi a katifa sai hira suke yi tsakanin Amal da asiya , zarah da mimi autarsu kenan, Hira ce tayi nisa Amal tafara magana tana cewa" Su Barrister zarah ya karatun ina fatan baya baki wahala"?." To inkana karatu va wahala in bakayi kuwa gaskiya sister da wahala "."Hakane Allah taimaka ".
Ameen suka ce.
Mommy ce take cewa mama
ay nema yau tunda mukazo ko ganinsu banyi ba har yanzu , sunje gidansu zarah qawar amal daganan kuma yanzu naji shigowarsu suna d'akinsu , mama tace su baba ne suka shigo bayan shigowarsu ne suka zauna aka ci abinci Daddy ne yake tambayar su Amal ,Mommy ce ta ansa da cewa nima kaina yanzu nagama tambayarsu saboda tun da muka zo,ban gansu ba.
Daddy ne yace"nagansu dazasu fita"
Daddy ne ya ce "Usman maza jeka ce masu su shirya yanzu zamu tafi ."
"Baba ne yace "Baza'a yi haka ba yanzu haka magrib ta kunno kai kuyi haquri zuwa gobe insha allahu sai ku tafi da safe"."Daddy ne yace "Allah kaimu saboda baya son musu da Baban Amal dan yana masa kwarjini , Usman ne ya tashi ya fita saboda yaga duk iyayensa ne a gun D'akin y'an matan gidan,ya nufa yana shiga ne idanunsa suka masa arba da Asiya , a take a lokacin yaji ya kamu da sonta , zancen zuci yafara Allah ya taimakeni da ban furta ina son zarah ba da na sha kunya yanzu lalle a yau naga matar da zan aura , ubangiji Allah kasa mata sona a zuciyarta , magana yaji ana masa yayi firgit ya ce na'am Asiya ce take cewa"Yaya Usman ina wuni , shine ya firgita yana cewa na'am sake gaida shi tayi , Ina wuni ta fad'a tana turo baki gaba sabida taga bai ansa ba bata son tana magana a mutum yayi shiru .
"cikin kulawa yace lafiya qalau qanwata ,yagida yakike ?"."lafiya qalau ta ansa masa hira suka fara a d'akin amma Asiya ta tsargu da kallon da yayannasu yake mata d'ago da idanunta tayi taga bai daina kallonta ba baki ta turo gaba tace "Yaya Usman nifa bana son kallo,duk mai kallo na ina cire masa idanu".
Dariya gaba d'aya y'an d'akin sukayi ciki,kuwa harda shi uban gayyar , cuno baki gaba tayi zata fara kuka Amal ce tace"Sorry Sister nah karkiyi kuka a gaban qanwarkimana so kike taraina kike , hawayen ta mayar tana mai jawo mimi jikinta saboda ance qanwarta ce , magrib ne tayi yaya usman ya tashi zai tafi masallaci.

Mommy da Mama ne Suka Shiga d'akin mama zatayi sallah , mama ce ta fito tasa y'an matan ta a gaba akan suzo suyi sallah,kallanta takai kan zarah tace"yaushe zaki tafi d'iyar kirki "."Murmushi zarah tayi ta ce"Mama nafa tambayi mama nah ta barni gobe fa qawata zata koma ay dole yau mu zanta munjima bamu had'u ba , Daddy da Babba ne bayan sun idar sallah ,zasu fita Daddy yace wa Baba"Agaskiya najima banga mutum mai dattako irinka ba shiyasa zan fad'a ma kad'an daga cikin sirri na wanda ko matata bata san shiba gudun kar hankalinta ya tashi nima kuma nawa ya qara tashi wato ina son sanar dakai ce wa...
Rubutawa da tsarawa📝
*HAD SEEYAEMAH CE🌺*

Al k'alami yafi takobi inji ni siyamah

share
comments👏🏼



BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya


_FREE BOOK_

_PAGE 24_


Agaskiya najima banga mutum mai dattako irinka ba shiyasa zan fad'a ma kad'an daga cikin sirri na wanda ko matata bata san shiba gudun kar hankalinta ya tashi nima kuma nawa ya qara tashi wato ina son sanar dakai ce wa...

"Ina da yara guda biyu a duniya babban namijine a yanzu haka shekararsa 25 sai qanwarsa mai bi masa tana da shekara 18 a duniya Shuraim Shine Babba a cikin,yarana kuma ina sonsa da qaunarsa yaro ne mai hazaqa da zuciya tun yana yaro qarami ya haddace alqur'ani Shuraim yaro ne kyakkyawa kamar dai yadda kaganni a yanzu mu usul fulani ne amma nima har mamakin kyau irin na yaron nan nake I na,da qani guda d'aya a duniya wato sani Amma shi har yanzun nan da na ke ma magana na kasa gane bayansa bare gabansa ni cikakken,d'an kasuwa ne duk da nasan ina da abokan gaba da yawa amma ban d'aura wa kowa b'atan d'ana ba , d'ana Shuraim bayan yagama secondry qin yarda yayi yai kasuwanci irin nawa sai ya tafi qasar egypy domin karatun law , Amma mai nida mahaifiyarsa muka kaishi air port bayan kwana biyu da ta fiyarsa a ka turo mani cewa d'ana yakamu da rashin lafiya mai tsanani har suma yake dani da d'an uwa na sani munje qasar egypt Amma Allah bai bamu ikon Ganinsa ba daga qarshe sai tattarowa mukai muka dawo bayan dawowarmu nake ganin bazan iya zaman garin Maiduguri ba saboda ba d'ana a lokacin nayi kud'in da ko jikokina basuyi aiki ba zasu zauna lafiya amma ko y'ata datake ita d'aya a yanzu ban sabar

Please Login or Register in order to submit comment