Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asiya take shirin bata mommy ta shigo d'akin yarana kufito mutafi...

By
HAD SIYAMAH

RUBUTAWA DA TSARAWA

SHEARING AND
COMMENT


BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya.
_PAGE 17_

Parking Driver yayi parking space na cikin super marker in, fitowa sukayi cikin nutsuwa da nuna,class suka tunkari mall in ,shigarsu ciki keda wuya kowa yafara neman abin buqatarsa , mommy ce take ta jido kayan qamshi da qananan abubuwa na kiching , Amal da Asiya kuwa basket in su nafarko ya cika maqil har sub fara cika na hannun Amal , basket in da'aka cika na zubawa idanu lalle kud'i yasan ayadda yake Turaruka ne kala-kala irinsu soft and gentle,anti-perspirant deodorant and sweet light .
Turaruka me masu sanyin qamshi da class suka iba , kodan sukansu masu class gwanda ni Siyamah na bar cewa na masu class suka saya kar suji ni , saboda su komai nasu namasu class ne , sabulai masu kyau da qamshi suka iba da kuma maclin , new brush , innerwears and just something like...
Basket na hannun Amal kuwa kayan maqulashe ne irinsu chaculate, biscuit , sweet , ice cream .
★★★
Layin da ake sayar da pasion na y'an kunne da sarqa suka nufa bayan sun zab'a ne suka je su kai aka lissafa Atm mommy ta bayar bayan sun ciri kud'in su ne suna gab da fita a mall in aka nunu news a, NTA HAUSA, Mommy ce ta zuba wa Tv idanu ji take zuciyar ta na , dad'a bugawa Tv take nunawa tana cewa" Shine Shine , "Shi ne wa mommy "?· "Shine yayanku ".
Ya Shuraim mommy !!!hakan yana nuni da cewa ya shuraim ya na raye , mommy tabbas a cikin satin nan yakamata muje maiduguri domin bincikar yaya.

Amal ta tsaya ganin ikon Allah sabida sam bata gane me suke nufi ba , Amal ce tace"Mommy karkidamu insha allahu za'aga yayanmu zamu dage da addu'a kinji mommy?".

"Bakomai y'ata addu'a kullum a cikin yin ta muke sai dai adage a qara akan yadda ake yi ni dama a,jikina ina jin cewa shuraim yana raye .

Tofa anayinta hakan yana nuni da cewa iyayen Barrister Shuraim suna raye ko a ina Allah zai had'a su musai je zuwa fans kuna tare da HAD Siyamah .

Gida suka koma zuciyar kowa ba dad'i horn sukayi da suka iso , gate man ne ya wangale gate parking space suka nufa , parking driver yayi mommy ce tafice da sauri Asiya a Amal ne Suka nufi wajen shaqatawa na gidan sabida zuciyoyinsu ba dad'i , Driver ne ya kwashe kayan yakai su side na masu aiki na gidan cewa yayi a shiga da kayan nan side na hajiya , gaisawa sukayi da baba ladi daganan ta karb'i kayan ta yi side na hajiya Asabe kuwa girki take yi shiyasa bai samu gaisawa da ita ba .
★★★
Amal ce tayi tagumi tana kallan furanni dake wajen da kuma yadda tsintsaye suke ta yawo a sararin samaniya , murmushi tayi tace "Besty waye yaya Shuraim ?".
"Yaya Shuraim shine babba a gidan nan shi mommy da daddy suka fara haifa , yaya Shuraim mutum ne mai hazaqa da hankali , yana da farin jini na jama'a ba manya ba , bakuma yara ba , Ranar da bazamu tab'a mantawa da ita ba a rayuwarmu itace ranar da muka raka yaya Shuraim filin jirgi domin zuwa qasar egypt karatu ta tafi qasar egypt muna waya da shi,har na tsawon kwana biyu a aranar ta ukun ce bana sani qani wa daddy da kuma abokinsa baba sani wato baba adamu , Sune wani a bokinsu na qasar egypt ya musu video recording na yaya shuraim ya fad'i ya suma jini ya na fita ta baki ta hanci d'aukarsa a kayi aka wuce da shi asibiti amma suka ce aikin ya fi qarfinsu qasar U.S A Aka wuce da shi domin bashi taimakon gaggawa , before a wuce dashi U.S A jirgin mu ta shi muka tafi egypt da baba sani,yanunamana abinda ya faru amma me zuwanmu keda wuya akace d'aya acikin y'an uwanmu yad'auke shi ya tafi dashi qasar America , amasa aiki , aranar ko kwana ba muyi ba muka wuce America Amma me ba labarin ya shuraim a qasar ba kalar hospitals in da bamuje ba , Amma ko mai kama da shi Allah bai nunamana ba.
Daganan muka dangana muka dawo A,wannan lokacin zaman maiduguri ya fita aranmu muka dawo Azare da zama ."
Kinji taqaicaccen tarihin rabuwarmu da yaya shuraim .
Amal ce tace"Ikon Allav ka bayyana shi amma baku tab'a qiransa a waya ba.

Ay wayar tasa a lokacin da mukaje qasar egypt wani doctor a asibitin da aka kwantar shi yabamu wayarsa saboda ta fad'i kuma an wuce U S A da shi , shine muka dawo da wayarsa nigeria , some times mommy sai tasa wayar a gabanta tana ganin ta taba kuka tun tana yi muna bata haquri har tafara yi a b'oye, kuka Asiya ta fashe dashi a lokacin da take bada labari.

Haquri Amal tabata sosai , daganan ta haqura , Amal ce ta tuno da nata a halin a lokacin tace"Asiya bani a ron wayar ki ?
miqomata tayi numbern ya usman tasaka ringing d'aya biyu ya d'aga .
"Assalama alaikum "
Yaya usmannnnnnnnn!
Amal!!!!!!!!
'Na'am yayanmu'
Daman ke ce? A she zaki qira mu??
Ashe bamu kad'ai muke tunaninki ba??? kwana biyu qanwata sai jajenki nake yakike???
"Baki,Amal ta turo gaba nika d'ai zan amsa tambayoyin nan yaya.
Hungo nan na,baki ga kina,kusa dani dana ranqwasheki wato ke har yanzu bakiyi hankaliba , kina wani,gida kina aiki amma kina shagwab'ar nan taki bazaki daina ba .

lah yaya wayace ma aiki nake wallahi Allah ya had'ani da,mutanen arziqi,sun d'auke ni tamkar d'iyarsu yanzu haka,ma ansani a makaranta kuma yaya phamarcy nake, "Masha allahu , Alhamdulillah naji dad'i sosai najin kin cika burunki Allah bada sa'a
"Ameeen"
Ina mama? Baba? Mimi ? qawata zarah!?
Duka suna lafiya kowa yana gaidake yanzu haka ina wajen interview na neman aiki sai,kina mana addu'a in nakoma gida zanhad'a ki da su mama , zarah ma zan had'aku zuwa gobe,insha allahu , sai anjima qanwata".
"Bye yaya"

Asiya ce tace"A gaskiya yayanki ya na sonki"
murmushi ta mata tace"tashi muje muga a wani hali mommy ta ke ciki yanzu "

Tashi suka yi suka nufi Side nasu Baba ladi suka samu ta kawo kayan da sukayo shopping gaisawa sukayi suka karb'i kayan suka haura sama , suka ajiye wasu a store wasu kuma a d'akinsu.

D'akin mommy suka nufa sallah suka samu tanayi , jiranta sukayi har ta idar bayan ta idar ne , Sukaji sai kwaranyo addu'oi takeyi "Ameem"
Suke cewa saboda mommy irin matan nan ne masu addini , bayan tagama ne Amal take cewa"Mommy kiyi haquri dukkan tsanani,tana tare da nasara insha allahu yaya Shuraim zai dawo,garemu , kuma nasan duk yadda akayi shima yanzu haka yana neman ku , mommy mai zai hana muje tsangaya -tsangaya mu raba sadaka amana sauqa a kuma taya mu da addu'a a masallatai insha allahu za'a dace ".
"Insha allahu haka za'ayi yarinyar kirki Allah ya muku Albarka"

Bayan hajiya qarama ta tafi , tabar Shamsiyya har na tsawon kwana uku a wajen boka, a ranar da zata dawo d'aukar Shamsiyya sai akai rashin sa'a mijinta yadawo bata samu damar zuwa ba , Shamsiyya ta gaji da azabar da bokan nan yake gana mata , ita ba matarsa ba amma haka yake wahalar da ita, bayan kwana biyu hajiya ba ta dawo ba , A ranar ne boka yana wajen mutanen sa marasa tsoron Allah masu zuwa,karb'an magani , Shamsiyya ce yaje tasame shi tace"ina son in hajiya ta dawo d'auka ta kar ka bata maganin data buqata a gunka ka sauya mata da wasu abu buwan nikuma ina da wata buqata, "wacce buqata kenan?".

Ina son ka sa sona a zuciyar Zaid d'a ga hajiya daga nan kasa wa,hajiya tsorona ta yadda komai nafad'a zata aikata , haka ne kad'ai zaisa na auri d'anta cikin sauqi, sai kuma waccar sadaka yallar Amal kasa ta raina kowa a gidan ta daina kallon kowa da gashi ta yadda za'a samu a koreta a gida cikin sauqi."

"An gama amma da sharad'in cewa "Aljanunmu sunce idan aka baki magani bakiyi aiki da shi yadda yakamata ba to zaki haukace daganan ki,mutu kin yarda?."
"Eh na yarda"

Hajiya qarama ce ta shirya da a alama unguwa xata alhaji
ne ya shigo motarsa ya parker , hajiya ina zuwa?
inda inda ta fara alamar bata da gaskiya kenan , Um um daman garden zani "Ohk To muje garden in naraka ki ko mushiga ciki ."
Aa mushiga ciki .
Ciki suka shiga alhaji ne yayi wanka ya ci abinci yace "Hajiya ina zaid"
★★★
Hmmmmmm Alhaji kenan !!! kuka ta fashe dashi wai anyi wa d'anta asiri sun asirce shi baya zuwa wajenta kullum yana side na mommy,zagi alhaji yafara uana biyewa matarsa sai aybanta su Daddy da Mommy ake , tashi yayi , hajiya ce tace lafiya yakatashi ?".

Lafiyar kenan zan je najawa hajiya maryam kunne akan tadaina hurewa d'ana kunne a matuqar b'ace ransa yake ya fita fuuu...

TSARAWA DA RUBUTAWA

HAD SIYAMAH

SHARE AND COMMENT



*🧑‍⚖️BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*w
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya


_FREE BOOK_

_PAGE 19_

wacece Annah ".?
Annah y'a ce wa Deputy governor na qasar agadex ita kad'ai ce y'ar sa a duniya ya shagwab'ata sosai wanda hakan yayi sanadiyar lalacewarta, Kowani Abu Annah take so mahaifinta yana bata daga qarshe bayan Annah tagama secondry ba wanda take shayi da tsoro sama da mahaifiyarta saboda ita kad'ai ce take tsawatar mata , Deputy kam sai abinda take so yake mata, Gama secondry annah mahaifinta yakai ta garin Abuja yin karatu a wata univasity ta masu hannu da shuni , Annah tun shigarta School ba'a binda tasa a gaba sai iskanci da yawan banza yau ita ce da wannan saurayin gobe wancan, Annah tazama cikakkiyar y'ar leabian, karuwanci kuwa ba'a magana sai dai ta koya ma wani bin maza kuwa a wanan school itace number One, Annah sai ta kwashe shekara guda bataje a gadex ba , sabida ta na tsoron mahaifiyarta tasan abinda take aikata wa , magaifinta kuwa tun bai zama Deputy ,a ya sakalta y'ar sa barin yanzu da yazama deputy ba'a magana sabida yace gomnati tasu ce , Duk wannan abu da Annah take aikatawa tana aikatawa ne cikin taku da kuma tsarewa batare da ko wa ya san da haka ba ,Annah yarinya ce mai wayo da saurin gane abu A dalilin haka yasa take wa qawarta wayo wato ummi .

★★★

wacece ummi?
Ummi y'a ce wa alhaji Adamu wato qanin baban Amal , ita kad'ai ce y'a a wajen iyayenta shiyasa suka sakalta ta da yawa , Ummi taka san ce yarinya mai hayaniya da son kwalliya k'yale-k'yale , ita a komai so take a ce tafi kowa Ummi tun tana secondry bata kula yaran talakawa a ce warta zasu shafa mata talauci kuma kwad'ayi ne dasu in dai baki da class ummi bata kulaki , qawayen ummi kuwa duk sun ta kud'i asalin yaran masu kud'i qawayenta shiyasa bata kula Amal y'ar gida wan babanta duk da ba wani tazara ne sosai a tsakaninsu ba ummi tafi amal da shekara biyu, ummi yarinyace wacce bata san yi ko bari va mahaifinta da mahaifiyarta ba qarami sakalta ta sukayi ba, bayan tagama secondry ta tafi makarantar gaba da secondry wato univasity , makarantar Abuja tayi ta masu kud'i anan ta had'u da annah suka zama qawaye saboda tasu tazo d'aya kowa d'an wanka ne banbanci ummi da annah kuwa shine ita ummi bata less da karuwanci amma daga qarshe annah tanunamata yin hakan shine wayewa bamai d'aukarta a matsayin first class sai dai lower class abinku da masu son asan su wasu ne tunin tafad'a harqar bin maza har ma tafi annah bin maza saboda son kud'inta amma ummi bata yin less ,wannan shine taqairaccen tarihin ummi.


★★★

Wanene Deputy governor?
Deputy gomna kamar yadda kukaji a labarin Annah uba ne wa annah asalin sa shine cikakken matsiya cine a dalilin sob kud'i irin nasa yabar agadex yakoma maiduguri yake kasuwan ci anan, yana yawan zuwa garunsu har aka auramasa fulani a garinsu , daganan ne bayan yadawo maiduguri ne yaga alamar baya samun kud'i sai ya fad'a ungiyar secret society wato ungiyar masu shan jini anan ne yayi kud'i na hauka dalili kuwa matar duk cikin da matar sa tayi yake badawa sai ana biyar ya bari tahaifa shine aka haifi annah , tunda ga kanta kuwa Allah baisake bawa fulani ciki ba , tafiya tayi tafiya lokaci wucewa yake a wannan lokacin yayi amfani da ikon sa na tsafi ya zama deputy governor ,Baba Adamu da Alhaji sani sune manyan qawayensa suma sun shiga wannan harqa ta secret society.

wanene Baba Adamu ?

。Baba Adamu mahaifine wa ummi kuma miji a wajen madam da shi da matarsa sunjima suna kidnipping shine sana'arsu A lokacin da Allah ya had'asu da deputy gomna a wannan lokacin yaji dad'in tafiya da adamu saboda Adamu yana kidnipping yara yana kawowa ogan sa deputy kuma suna karb'a kud'in jama'a ga karb'an kud'i ga a hana ka d'an ka , y'ar sa d'aya a duniya ummi wato mai sunan maman sa sun sakalta ummi da yawa Baba adamu yana da d'an,uwa mai talaka amma naya qaunar taimakon d'an uwansa komiye dalili Oho kudai biyo HAD Siyamah dan jin sauran labarin baba adamu wato a taqaice Babban Azzalumi ne.


★★★

Wanene Alhaji Sani
Alhaji sani d'a ne a wajen Baba muhammad Azare , mahaifinsu su biyu ya haifa wato shida Alhaji Al Ameen , a lokacin da mahaifinsu yazo mutuwa suna samari a wannan lokacin ya bawa Al ameen Amanar d'an uwansa sani, tun daga wannan lokacin suka bar ga ban mahaifiyarsu sabida y'an uwan ta sun zo sun tafi da ita , sukuma a wannan lokacin suka tafi neman kud'i maiduguri, sana'a suke sosai har suka manyanta wato kowa yayi aure shi al ameen baya qyashin yiwa d'an uwan sa komai amma shi kullum baya son ganin cigaban yayan nasa bayan wasu shekaru sai yafara ha'intar yayansa komai yamasa yanuna bai godeba , daga qarshe Alhaji sani ya shiga ungiyar shiga ungiyar su adamu da deputy , Alhaji sani yana da yara biyu zaid ne babba sai minal qanwarsa basu d'auko halin mahaifinsu ko mahaifiyarsu ba, matar sani ta kasance mai bin bokaye amma batasan komai a tafin hannunsa take yiba sabida yana kallan komai a qoqonsa shiyasa take ganin aikinta yana ci nan kuwa biyayya kawai yake mata wani lokaci yake jira ya miyar ta moneyyyyyyyy.
waiwaye adon tafiya yazu haka mun dawo cikin labarin gadan-gadan .
A taqaice wannan shine tarihinsu muda wo cikin labari Annah da ummi ne suka fita a compound na hotel in Room 14 suka shiga wani kyakkyawan matashi ne a d'akin yana kallonsu yace'babys ku shirya jibi zamu maiduguri Bikin aboki na ". "To"
Suka amsa washe gari ne mommyn ummi taqirata a waya ,hello! ummi" kina ina "?."mommy na d'an fita da bikin da zamu satin amma insha allahu zan dawo before ku wuce "
Amma dai kinsan idan daddyn,ki yaji ba ruwana ke dashi har yanzu ba karatu, kike ba.
Sorry mommy na daina fa .

Rubutawa da tsarawa📝
*HAD SEEYAEMAH CE🌺*

Al k'alami yafi takobi inji ni siyamah

share
comments👏🏼



⚖️BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya


_FREE BOOK_

_PAGE 20_



*
Wannan page in naki ne y'ar uwa rabin jiki kiyi yadda kike so da shi y'ar uwa ta .
Fatima Kabir Dauda (Zarah)
kyauta na baki wannan page in ke da yusuf Imam inki Boddona
Allah barku tare nagode da qauna dakike nunawa wannan littafin na Barrister Shuraim , ina yinku ko ba tuta wlh sis.


★★★

A garin Azare

Mommy Da Daddy ne suke zaune suna lunch , sai ga Amal da Asiya sun dawo Shigowarsu kenan,sukace"mommy sannu da gida."Daddy ya Aiki.?
"Alhamdulillahi yaran kirki"
Maza kuje kuyi wanka kuzo kuci abinci.Bayan sunyi wanka sun fito Suna cin Abinci, Daddy yace" Hajiya da keda yaranki ku shirya gobe insha allahu zamu tafi maiduguri d'aurin Auren d'an abokina , Dan haka kushirya da wuri ."Insha Allahu daddy ". "kwana nawa zamuyi ?"."Ranar d'aurin Aure zamu tafi washe gari mudawo sabida kuna da school."
"eh "wow am vary happy daddy." Allah kaimu goben .
da Ameen suka amsa tashi sukayi suka tafi d'aki kowacce ta d'auko mayafinta suka ce"mommy , daddy mun tafi school muna da test Anjima ". " Allah bada sa'a ya taimake ku yarana yana mai shafa kansu , mommy ma fatan Alkhairi tai musu ". Fita sukayi da ga gidan parking space sukaje" yaya zaid please ka miqa mu school "abinda suka ce kenan ."Ok bada muwa " Daman fita zanyi kuyi sauri mutafi kunsan school in naku nisa ne da ita ,"."Haba yaya zaid federal univasity ina taga nisa ,Gaba da College of education ne fa ".
"To kema mikika ce gaba da college ."
Shiru Asiya tayi dan tasan yau har sa samu sake yin magana mai tsawo da yayan nata wanda ko maganar arziqi sai yayi niya suke yinta.
Isar su school keda wuya ya ajiye su a wajen clinic ya wuce Asiya ce ta nufi nursing depertment tana da lecture , Amal kuma pharmacy department tana da exam.
Amal,ce tace "Sister in nafama text zan shigo sai mu tafi"."Dont worry sistu sai kinzo" Hannu ta d'aga mata tana tafiya lecture note in tane ya fad'i tsugunawa tayi zata d'auka taga wani hannu ma zai d'auka d'aga idanunta tayi domin ganin wani mai rawar kan ne abinda idanunta ya gani ne yasa ta sunkuyar da kanta qasa bata d'auki lecture note in ba yarigata d'auka , tashi tayi tana mai cewa Sorry sir !wallahi i dont ... wait shine abinda sir khaleel yace mata , qasa tai da kanta taji yana cewa Never mind ! Yana mai miqa mata karb'a tayi da gudu -gudu sauri-sauri ta shiga class in tasan dokarsa in dai yariga ta shiga ba ita ba yin text yau , sai da tashiga class hankalinta ya kwanta , mamakin irin tafiyar da take yakeyi wai ita a hakan sauri take , murmushi yayi yana mai cewa azuciyar shi in da nai niyyar tafiya a wannan slowly tafiyan naki ay sai na shiga class in baki shiga ba, jijjiga kansa yayi ya shiga class in tare da sallama bayan shigarsa ne kowa ya nutsu a class in text ya rubuta tare da bawa kowa paper yayi attendance daganan ne yake qiransu one after one suna fita hall suka nufa anan yayi text in bayan ya gama ne yace"Amal ta kawo masa office, knoking tayi ya bata izinin shigowa , Shigarta keda wuya tace"Sir ga text in,karb'a yayi ya ajiye yace " Amal Muhammad " d'agowa tayi jin,ya qirata da full name nata cewa yayi ina wayarki ". "Sir bani da waya!."Gashi ina son karb'an numbern ki saboda gobe zanje bikin abokina maiduguri, to ina son karb'an numbernki saboda in wani abu ya taso na gaya maki ,"." Sir ay gobe nima tafiya zamuyi".
"Ina zaki?"."zamu Borno biki".
"To Allah kaiku lafiya"
Da Ameen ta amsa .
Tashi tayi ta masa sallama zata tafi Sir khaleel ne yace"Ama ina son,kisa a ranki komai zakiyi kina yin haquri karki damu magan ganun mutane, kidage da azkhar kar ki yadda ace bakiyin addu'a ko,azuciyarki , saboda yawan addu'a yana kai,mutum ga samun nasara a rayuwa ,saboda yawan haquri , juriya , Addu'a Shine matakin nasara a rayuwa ".
Amal ce ta juyo tana murmushi tace"Nagode Sir Khaleel Ubangiji Allah saka da alkhairi".
Fita tayi tana mai jin ba dad'i ji ta ke kamar Sir khaleel yana mata wata wasiyya ne .
Depertment in y'an Nursing School ta tafi samu tayi suna lecture zama tayi suka gama tukun suka tafi gida , aikin gida sukayi kamar yadda suka saba, bayan sun gama suka shiga kitching ,mommy ce ta shigo tace"yarana,yau fa funkaso nake son ci "."Amal ce tace"To mommy sai ayi funkason tunda yanzo zamu d'aura , Asiya ce tace"ni kuma Sistu in mungama ina son cocunut biscuit saboda gobe in muna mota sai muna ci muna shan lemo , ohk badamuwa ay sai muyi before dare mun gama ,
Kayan had'i suka fara ebowa kamar haka.
Alkama (gwangwani hud'u)
Filawa(gwangwani d'aya)
Ruwan tsamiya ko tsamiyar kanti kad'an ,
Yeast (cokalin d'aya)
Sugar (cokali d'aya)
Ruwan kanwa (cokali d'aya)
Mansuya (kwalba d'aya)
roba mai murfi su ka d'auko sugar da yeast da tsamiya da kanwa suka jiqa a waje d'aya fulawa suka auna had'ata da garin alkama sukayi saisuka had'a da wannan ruwan su yeast in da ya narke juye filawar sukayi akai suka kwab'a sosai suka kwab'a saboda kar yayi gudaji basu bar kwab'in yayi ruwa ba bai kuma yi tauri ba
rufe wa sukayi yayi a wa d'aya tashi yayi suka d'ora man yayi zafi sosai kwab'in suka qara juyashi sosai ya koma ya kwanta kwab'in ya dad'a sakin jikinsa , d'an faranti suka shafe da ruwa suka rinqa gutsurar k'ullin suna sawa akan d'an farantin hud'a tsakiyar sukayi sai suka sa a cikin mai yana d'agowa yana fad'awa cikin mai a hankali .
Amal ce tace" Asiya ki Lura da funkaso in bayason yawan juyawa idan kinga k'asan ya soyu saiki juya saman shima ya soyu kuma funkaso bayason mai k'adan wajan suya yafison mai wada tacce ya sakata ya wala .Sistu miye amfani tsamiya a funkaso. Amal ce tace"amfanin tsamiya a funkaso shine bazai tab'a sha miki mai ba kuma zai miki suya tai ja tayi kyau." Amma amfi son using da ruwan tsamiya anan ba bu a kusa ne shiyasa". "Sistu ay da kin fad'a sai muje layin qasan,mu gida da ake awara subamu kad'an"."Rashin sani kuma kinga rabi kofi zamu karb'a ma ba yawa".
Nagane,sis insha allahu a gaba sai,mu karb'o .
na gane Sis,miyar me zaki yi ne"?."Miyar egushi ashe mommy tana kallonsu tana zaune a dinning Amal ce tace "cigaba da suyar fana yi miyar egushi ,"Ok fanai sauri nagama na koya kinsan ban iya miyar egushi ba.
Amal ce tace "kai sister ahaka zankaiki gidan mijin rufe fuska tayi "."tace au zaki,koyamin before nayi auren.
Miyar ta fara kamar haka tana cewa sis in zakiyi miyar egushi zaki nemi

Egushi
ganyen Ugo
Stock fish
bushashen kifi
ganda
Maggi
Palm oil (Manja)
attaruhu
Onions
Naman saniya
Daddawa yar k'adan,wasu kuma nace mata kalwa.

attaruhu ta da albasa tayi blending guri d'aya, manja tasa a wuta yayi zafi sai ta sa attaruhu da albasa da daddawa,
soyasu kad'an tayi sai egushi ta zuba a

Please Login or Register in order to submit comment