Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na,
Dubu d'ari ya d'auko ya bata yanunamata hanya yace "tafita ta qofar baya saboda in samarin garin suka ganta duka zatasha.Bare insunsan mai ta aikata,
Godiya tayi ta wuce.

A garin Abuja kuwa ayau take ranar komawa kotu kuma a yau za'ayi shari'ar qarshe kotun ce ta cika amma ba'aga nana da Barrister Shuraim ba masu yin qara ma basu samu isowa ba.
Alqaline ya hango a na turo,nana a keken marasa lafiya kotun suka shigo gaba d'aya kallo yakoma kansu...

Shearing
and
comment
like

By HAD Siyamah
BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya
_PAGE 14_

fad'i buqatarki ko kuwa saina turo manyan aljanu sun kasheki.
Aa sarki bokaye zan fad'a.
"Fad'i ina jinki"
Dafarko dai ina son asawa mijina, masifaffen sona!!!
ina son matar yayansa ta bi duniya taji bazata iya zaman,gidan ba.
Shikuma yayan mijina inason a,kashe sa."
"Dariya marar kinji boka yayi yace"a lallen ke a cikin shed'anun matanma najima banga kamarki ba , wato mutumin da yake muku komai na rayuwa zaku kashe?."
Dariya ya sake bushe wa da ita yace"aikin akwai wahala zaki iya kuwa ,cewa tayi taji tagani zata iya , Boka ne yace"aiki bazaitab'a iyuwa ba sai ta bar wannnan yarinyar dasuka zo tare ya kwanta da ita na tsawon kwana uku , bataji komai a ranta ba tace ta amince .tafiya tayi tabar wa boka shamsiyya .

.........
Washe gari Amal ce a office in Sir khaleel yana bata wani assingment dazata rabawa y'an class in assingment in individual ne ba in group ba karb'a tayi tana shirin tashi taje yace"Amal," dawowa tayi zama tayi taji yace natambayeki mana?Amma karki ce nayi shishshigi dayawa ko? lah bakomai inajinka
Samarimki nawa?
Jin kunyar maganar tayi shiru tamasa , yasake maimaitawa , Samarin ki nawa?
Amal ce tace"Ni bana kula samari amma bawai bani dasu bane ,aa kawai bani ra'ayinsu ne yanzu".
"Masha allahu"!.
Sir khaleel yace , daganan yace a gaskiya kin kyautawa kanki baikamata kifara kula samari tun yanzu ba , saboda kashi saba'in cikin d'ari na samari ba soyayyar tsakani da Allah suke ba ahalin,yanzu ina mai add.'r Allah rabaki da sharrin samarin wannnan zamanin,
"Ameeen"
nace ina godiya na tashi na tafi.

Class nakoma domin isar da saqon sir khaleel ,bayan nagama ne muka nufi compound na school in mu driver muke jira yazo shi .
sallama mukaji Anayi "y'an mata Amincin Allah ya tabbata agareku"
Amsawa mukayi "tare da ku "
Dan Allah in bazaku damu ba muna son magana daku?
Amal ce tabada amsa da cewa to akwai damuwar!
drivernsu ne ya iso tafiya sukayi sukabar wad'annan samarin a yadda suke , ganin da gaske y'an matan nan tafiya zasuyi yasa sukace please "we need your phone number?
"Bamu da waya bare har musamin numbern wayar"
wucewa sukayi suka nufi motar drivernsu ne yaja suka tafi.

Mutanen adamawa kuwa sun sha wahala sosai before su samu gidan Alhaji madaki yellow , isar su gidan keda wuya hajiya ta shiga ,
sallama take yi daga bisani hafsat ta fito duk ta rame,amsa sallamar tayi tare dagai da matar , yarinya ina matan gidan?
hajiya wakike nema ?ina neman y'ata nanah?
kuka hafsat ta fashe dashi ruwa ta bawa hajiya , hajiya ce tace"nifa kin karyamin zuciya sai dukan uku-uku qirjina yakeyi fad'amin meke faruwa?
mama !"Aunty nanah yanzu haka tana kotu nima yanzu haka shiryawa nake domin a yau ne za'a yi zaman qarshe a koma yau za'a yanke mata hukunci , "inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" y'ar nan me nana ta aikata? "mama bata aikata komai ba, zarginta ake akan ta kashe mijinta ".
"Allahumma ajirni fil masifati warazaqani khairan min ha wala quwwata illa billah, Allahumma la sahla illa ma ja'al tahu sahla wa'anta tajhanul hazna iza shi'ita sahla"

Ya Allah gamu gareka , nad'aura laifin komai akaina ,Allah ka kub'utar min da y'ata".
y'ar nan tashi mu tafi kotun kinji"
"to mama"

Hafsat ce ta shirya qannenta waje suka fito baba tagaida tace"bari tashiga gidan qanin babansu ta'ajiye qannenta , gidan ta shiga qannenta ta ajiye ta na cewa aunty na tafi kotu, "adawo lafiya hafsat"
fitowa tayi suka nufi kotun , da taza sosai tsakanin kotun da gidan su hafsat.

...............
Sahura kuwa tafiya take acikin wannan babban dajin bata san ina zata ba ko dabba Allah bai nunamata ba bare mutum tafiya tacigaba dayi bata san ina ta dosa ba , ita dai fatan ta Allah fitar da ita ta shiga cikin gari ta samu motar zuwa abuja bata so ayanke hukunci batare da ta'isa ba , sabida tasan za'a cuci baiwar Allah kud'in da suka bawa wa lauyansu kud'i ne ba d'an kad'an ba, kuma ta imani cewa tun a duniya Allah ya fara nunamata ishara bare kuma anje lahira duk dama Allah gafurur rahim ne , amma yana fa kyau kanemi, yafiyar wanda ka cuta, tana cikin wannan tunanin taganta a bakin wani kogi ji tayi ana cewa gafa can wata sabon kamun .

Juyawa tayi da niyyar guduwa amma ina mutanen su hud'u ne zagaye suke da'ita kowanne acikin su yana da makami a hannunsa , d'aya a cikin su yace mai muke jira mu aikata lahira dan wannan daga ganinta muna fuka ce , murmushin gefen baki babbansu yayi yace hakane mu bamu tsayawa tambaya , d'ayan kuma cewa yayi iskancin da yabiyo da ita gonarmu shizai fitar da ita , dariya suka bushe da ita , wata leda suka ga ta na b'oyewa ke miye wannnan? d'aya acikinsu ya tambayeta b'oyewa tasake yi batare da tayi magana ba .
mari ya wankamata , saida ta fad'i d'auke ledar sukayi suna cewa nama gasashshe , duka sukamata sai dasuka mata jiga - jiga suka ga bata motse su ka k'yaleta , d'aya acikinsu ne yace "bata motsi fa"babbansu ne yabada umarni a d'auketa asata a kogin dake kusa dasu,jefata a wannan koginsukayi sukai tafiyarsu ba d'igon imani a ransu bare tsoron Allah .

.........
A garin kaduna kuwa kwaki suka kwad'a suna ci baba ke cewa tunda adamu yakai yarinyar nan Azare har yau ko sake leqo garin nan baiyiba shikuma gashi bai karb'i numbern katin gidan da take ba , bare yaje Azare ya ga gudan jininsa,ya usman da mimi ne suke bawa baba haquri , insha allahu za'a sani nan bada jimawa ba ,mama ce tace"tabbas inaji a jikin Amal,ta na hannu mai kyau sai dai mudage mata da addu'a Allah ya taimaketa. da
"Ameen"suka amsa gabad'ayansu cigaba da cin kwaki sukayi bayan sun gama sun sha ruwa kowa ya tafi hidimar gabansa ,zarah anzama y'an school yanzu haka yau ne ranar maticulation nasu , mimi ce da yaya usman suka shirya domin hallartar wannan taron , "zarah tayi farin cikin kula da suka nunamata duk da qawarta ba ta nan , amma taji dad'i sosai .
suna hanyar dawowa gida yaya usman yake cewa qanwarsa mimi"nifa kamar son zarah nake"
'masha allahu 'yayanmu Allah tabbatar da alkhairi in ka auri aunty zarah kayi dace a rayuwarka domin mace ce mai haquri samun irin ta a wannan lokacin sai an tona,
"naji dad'i sosai na yabon my angel dakikayi amma fa gaskiya bazan iya gayamata ba."

karka damu yaya insha allahu zata soka kabarni,na shige ma gaba.
.........
A garin Abuja kuwa kallo ne yakoma kansu ,nanah da khalifa yake turota a keken marasa lafiya,
Alqali ne ya buga gudumarsa kowa dake cikin kotu ya nutsu , Shari'ar wasu akafara wacce iyayenta suka mata auren dole, bayan angama wannan shari'ar ne aka dawo kan shari'ar su nanah , Shari'a aka fara gabatarwa Alqali ne yanemi a nunamasa takardar rashin lafiyar nana a nan yaga tana fama da ciwon zuciya, Anan ne Barrister Shamsudden yayi amfani da wannan damar yace ya mai girma mai shari'a sanadin ciwon zuciyar da wacce ake qara take fama dashi tana fama da wannan ciwon sanadiyar hukuncin datake tunanin za'a yanke mata shine silar ciwon wannan zuciyar tata.

Barrister Shuraim ne ya fad'a tunani A lokacin da Deputy governnor yazo office in sa ,yana cewa"Barrister ga naira million biyar , Barrister Shuraim ne yace kud'in minene wannan?
wato Barrister wannan kud'in million biyar da kake gani somin tab'i ce ,
Bangabe ba mikakeso nama ka?
Ina son idan kunshiga kotu a zaman ku na qarshe kayi sillar yanke wa "Kozan,iya sanin dalilinka nasan yin hakan.?"
Eh to saboda budurwata ce tanemi ayi hakan ina fatan zaka iya?
"NO!NO!!NO!!!
"The deputu governor" yake magana yana cewa ,A gaskiya Barrister wannnan million biyar in bata komai bace , idan mukayi nasara insha allahu zanbaka kyautar gida,mota, million ashirin,

Barrister Shuraim ne yace"wa iya zu billahi "Ubangiji Allah ka tsareni da cin hanci da rashawa ta dalilin zamana Barrister idan muna ha'inci muna tauye wa talakawa haqqinsu to tabbas Allah zai tambayemu , dan haka ina mai roqonka daka canja wannan kuduri naka ,akan wata,budurwa zaka,sa na sab'awa mahaliccina kaima kuma kasab'a masa why!miyasa masu kud'i suke haka?.miya kaso madi yawa na masu kud'i suke da son kansu, mu talakawan ba mutane bane , komu daga sama aka sassaqo ma ".
Deputy governor ne ransa ya b'aci cewa yayi wato kai ana binka da arziqi kana gudu , kaigaka d'an talakawa jikan talakawa amma kana neman kanka da tsiya to wallahi na rantse idan bakayi abinda nasaka ba , tabbas zaka rasa aikinka, kadaisan muke da gomnati masu kud'i attajirai ,y'an kasuwa duk a tare muke dan haka ina mai baka shawara da ka canja tunani tun yanzu, nawa kake yaro, anbaka gida ,mota ,kud'i masu tsoka amma kace aa, nasan yanzu haka,ko mata baka da ita , antaimakeka ta yadda zakayi aure cikin mulki da izza , amma baka so!
Barrister Shuraim ne yace"The deputy governor mai ci a yanzu karka manta dacewa Allah shike badawa kuma shike hanawa , (Allah subhanahu wata'ala )acikin suratul taubah ayata d'ari da goma sha tara yana cewa"Ya ayyuhal lazina amanun taqullaha wakunu ma'as-sadiqin.
(O who have belived,fear Allah and be with those who are true)
Allah subhanahu wata'ala yana cewa"yaku muminai ku kasance tare da masu imani, ma'ana dai karmu kasance tare da azzalumai,irin ku anfison muzauna tare da masu gaskiya bama mai,gaskiyar ba aa masu gaskiya dan haka kana iya fita min a office, yatsa deputy yad'aga amma Barrister Shuraim cewa yayi saidai naga alkhairi insha allahu ba a binda zai sameni,sai abinda Allah ya tsaramin .

Alqali ne yace "ko Barristern mai karewa wacce ake qara yana da abin cewa , Barrister Shuraim ne yace babu my lord , "masha allahu"to koyu tayankewa nanah hukuncin zama na tsawon shekara goma a gidan yari tare da horo mai tsanani , idan kina ganin ba'a maki adalci ba kina iya d'aukaka qara zuwa wata kotun ta daban .

A lokacin maman nanah shigowar ta,kotu kenan taji hukuncin da alqali yayanke bata san lokacin da ta fad'i tana kuka ba , khalifa a lokacin fad'i yayi ya suma , nanah ce ta rugo da gudu tana mamaaaaaaaaaaaaaaaaaa!
Alqali ne yasa a ka tsayar da nanah kartaje ganin mamanta , Barrister Shuraim ne ya sunkuya yana jero addu'a .
Daga wajen kotun muka ga wata mata tashigo tana cewa"Ina da ja akan wannan shari'ar ya mai girma mai shari'a !
mekika taka akan hakan ?
Ina da shaida qwarara akan wannan shari'a ya mai shari'a.

Shearing
And
Comment
like

By HAD Siyamah

BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya


_PAGE 15_

Barrister Shuraim ne yazuba mata idanu yana qara godewa Allah daya kawo wacce zata kawo qarshen,wannan zaman.

Magana ta farayi kamar ankorota tana cewa"jama'a kuyi haquri zakuga kamar bani da hankali, to da hankalina ,nidai sunana hajiya sahura mata a wajen madaki yellow.
Hafsat!!! Barrister Shamsuddden!! Barrister Shuraim !!!

Duk sai da suka razana idanu suka zuba mata sunajiran jin mezata,fad'a ,
Dafarko dai ya,mai girma mai shari'a ina mai son sanardakai cewa "
Dani da laure , wato kishiyata, Abinda muka shuka a rayuwarmu bamai kyau bane sabida ni kaina bazan iya gayan abun da muka aikata ba , Abin da nasani dai shine mune ummul-Aba'isi na komai dake faruwa a cikin gidanmu, Bazan tab'a mantawa ba tun sanda Alhaji yana da rai muke aikata ba dad'i , Amma wait taji an tsayar da ita daga maganar datake ,
Barrister Shuraim ne yace"My lord ina mai neman afuwa a gareka na nayi magana a wajen da ba hurumina ba."
"Bakomai Barrister akan aikin ake kana iya cigaba".
"Nagode"My Lord "
Barrister Shuraim ne yafara magana , ko hajiya sahura nada abin da zata ce saboda wad'annan maganar taki tana rikitar da kotu domin har yanzu kotu bataji wani bayani daga gareki ba.
"Haka ne abinda nake son gayawa kotu shine , Nanah bata da laifin komai muke da laifi saboda mu muka kashe mijinmu domin mu gaji dukiyarsa shiyasa muka d'aurawa Nanah "
Salati a ka fashe dashi a kotun kowa yana gayan albarkacin bakinsa! ! !
Alqali ne ya buga gudumarsa kowa ya nutsu!
A kotun ana sauraran abin da alqalin zai ce , Alqali ne yace"ko Barrister Shamsudden yana da abun da zaice "
Barrister Shamsudden yace"Aa ya maigirma mai shari'a ".
Barrister Shuraim kana da abin dazakace, "Eh "ya mai girma mai shari'a .
Juyawa yayi wajen sahura , ko kina da abinda zaki iya gaya wa kotu akan rashin ganin y'ar uwarki "
"Eh to da farko dai ni da haule munfita a ranar 6/7 zamu je wajen boka akan ya kulle bakin nanah da alaqali yayi shari'a yadda muke so!
Anan dubun mu ta cika muka fad'a hannun babban mushiriki a dalilin rashin kunya da,na masa yamai da ni zakanya, ita kuwa laure guduwa tayi tun anan bansake jin labarinta ba , sai bayan wasu kwanaki da na had'u da y'an fashi duka na sukayi ta ko ina daganan bansake sanin a ina nake ba, sai wasu mutane suka taimakeni sukayi jinyata har na farfad'o daganan suka bani guzuri na taho garin Abuja ina hanya kan na iso muka ga wani waje namun daji sun kaca-kaca da nama a lokacin ne muka ga ashe gawar laure ne bayan,na tambayi mutanen wajen kowa ya shaidamin accident tayi daganan ta mutu shine a kazo jeji a ka yasar ta saboda kowa bai san musulma bace bare a mata sutura , tin daganan tsoron Allah ya qara shigata gashi dai yanzu ma na kawo kaina domin alqali yamin hukunci dai dai da abin da na aikata, saboda da azabar lahira gwanda ta duniya , durqusawa qasa sahura tayi tana neman yafiyar nanah !
Nanah ce wa tayi tayafemata Allah yafesu gabad'aya .

Alqali ne yayi y'an rubuce-rubuce yafara da cewa" am mun saurari qarar matan alhaji yello , munji bayanai daga fanni masu qara da wad'anda a ke qara dan haka a dalilin wahalar da shari'a da kukayi da,kuma sharri da akayi wa nanah !
Kotu ta wanke nanah tabar zarginta akan laifin da ba nata ba ,dan haka muna mai yanke hukunci a sahura na zama,a gidan yari d'aurin rai da rai tare da horo,mai tsanani .
Alqali ne ya buga gudumarsa aka tashi kowa yana tsinewa su sahura wasu suna,masu fatan shiriya kowa yana,gayan albarkacin bakinsa .

Wucewa a ka zo yi da sahura hafsat ce tazo tana kuka tana kama mahaifiyarta , "haba umma abin da kuka aikata kenan gashi yanzu duka yazama sillar lalacewar kwanciyar hankalinmu , umma kinji dad'i tunda Allah ya fargar da, ke da wuri , sai ki tuba ki koma ga Allah , umma zuwa wajen boka mummunan abune gashi yanzu yayi silar lalacewar komai naki a halin yanzu xaki koma gidan kaso da zama , an raba ki da yaranki y'an uwanki , kowa naki anrabaki da shi umma , gashi wannan dukiya dakike buqata ita ma anrabaki da ita , tabbas zuwa wajen boka babban tab'ewa ne a rayuwa , yanzu mumq haka kowa zaina nunamu da baki akan abin da bamu ji ba bamu gani ba , mahaifiyar mu ce ta aikata amma mu abin zaina bibiya".
kuka ta fashe dashi tana cewa"tabbas na cuceku y'ay'ana shiyasa akeso,mata tazab'a wa yaranta uba nagari , miji ya zab'awa yaran sa uwa ta gari bawai soyayya ba domin soyayya tana qarewa ubangiji Allah karemun yarana aduk inda suke daga qarshe ina mai maki wasiyya daki riqe y'an uwanki harda yaran laure tun da kinga y'ar ta babba hankali,bai,gama isar taba , ina mai godiya wa Allah dayabani,yarinya irinki mai hangen nesa , dan haka ina roqonki y'ata kidage damin addu'a Allah yafemin"

"Bakomai,umma insha allahu zamu dage damaki addu'a "
"Amma bazamu qara zama a gidaba daga yau zamu tattare mukoma gidan baffanmu bai,kamata ace muzauna a gida,mukad'ai ba ba uwa a gidan bare uba.

"Hakan yayi Allah,muku Albarka keda sauran y'an uwanki , kuka suka fashe da shi aka shiga da mahaifiyarta mota suna gani.
"Nanah kuwa a lokacin da aka yanke wannan hukunci tahowa tayi da gudu ta rungume mamanta suna murna,khalifa kuwa fad'uwa qasa yayi yana sujjada.
Barrister Shuraim ne ya d'aga hannu,yana godewa ubangiji ni'imar dayamasa baiwa akan duk shari'ar dayasa gaba sai yayi winning nata "Alhamdullillah "Allah na gode ma nasan cewa ba dabara ta bace bakuma wasu nafi ba, Ubangiji kai ne abin godiya "Sujjada ya fad'i,yana yi daganan yawuce wajen su nanah da mahaifiyarta , godiya iyayen nanah sukamasa akan,nawai niyyar dayayi da nanah , murmushi yayi yace bakomai , khalifa ne yace"mama ,baba ku tashi mutafi gidanmu "
Anya za'ayi haka d'an nan mama tace" Barrister Shuraim ne yayi magana yana cewa kawai mama kutashi muje zuwa jibi sai ku wuce adamawa .
"Baba ne yace bakomai wucewa sukayi izuwa gidan su Barrister Shuraim "
Tarb'a ta ta mutunci mommy ta musu ,irin ansansu sosai in nan akamusu sauqa ta ban girma hajiya mama har da kukanta na son da aka nunamasu...

Shearing
And
comment.

BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya.
_PAGE 16_

Jajanta abinda ya faru sukayi a tsakaninsu ,daganan Daddy yake gayawa alhaji cewa"yi wa yara auren dole babban qalubale ne a cikin rayuwarsu saboda bazasu tab'a aikata abinda ya dace ba komai zasunayi a matsayin biyayya kamar dai Nanah datake da kishiyoyi a dalilin son da bata nunawa mijinta ba, yasa har suke amfani da wannan dama suke azabtar da ita , gashi har hakan takai mu da shiga kotu Allah ya taimakemu muna addu'a shiyasa komai yazo mana da sauqi, "Tabbas alhaji wannan haka yake kuma izina ce a garemu, damu daku baki d'aya domin adlilin yin auren dole yaya ta wacce muke uwa d'aya uba d'aya, ita guduwa tayi tabar gidan tabi wanda take so ! har yau bamu sake jin d'uriyarta ba mahaifinmu tun kafin ya,mutu ,ya sa mukayi ta neman ta Allah bai had'amu da ita ba , har ya,mutu ya koma ga mahaliccin sa kullum sai yayi maganarta a matsayinsa na mahaifinta , yana cewa bahaka yakamata yamataba , kuma ya yafemata ita ma in mun had'u ta yafemasa,
Amma duk da hakan banyi tunani kar nayi wa tawa y'ar auren dole ba , ni anawa tunanin ay mu muka kawo ta duniya kuma muna da haqqin zab'a wa y'ar mijib zama ashe su yaran yanzu ba'a masu haka"·

Daddy ne yace"haka sai dai Allah kyauta ya kuma kare na gaba , ita kuma y'ar uwarka Allah bayyanata "
da "Ameen"
suka amsa baki d'ayansu.

A b'angaren su nanah abinci ta kwanta bacci domin hutawa.


Azare
............

Isar su gida keda wuya suka zube a palour suna cewa"wash Allah mommy yau mungaji sosai wallahi a school in nan ".
"Masha allahu , yarana sun fara zama y'an makaranta ay da baku san karatu kuke ba yanzu ne zakusan kunfara karatu yaran kirki".
Dariya muka yi baki d'ayanmu muna cewa "haba mommy duk wahalar da muke sha in"
"Eh mana "
"yanzu kutashi ku je dinning kuci abinci , kuyi wanka , ku huta zuwa bayan isha zamuje shopping , "To mummy "
wuce wa sukayi abinci sukaci daganan suka wuce d'aki Amal ce tafara karatu abin da aka musu a school , Asiya kuma tana chart a wayar ta.
★★★
waya ce take ringing sai da zata katse aka d'aga
daga can wajen wanda ya qira yake cewa.
"Assalama alaikum ya ke ma'abociyar kyau da kwarjini"
Amal ce ta amsa "wa'alaikassalam "
waka ke magana?
"Kina magana da wani bawan Allah ,."
mekakeso?
ni ke nakeso!
inafatan zaki sani a d'aya daga cikin manemanki .
"A gaskiya kayi haquri ni ba soyayya a tsarina yanzu , nabarka lafiya.
qit ta kashe wayarta ta kwanta tana mai cillar da wayar gefe, lafiya sistu na , me aka ce maki a wayar ranki zai b'aci , haba sistu kizama mace mana akan me saurayi zai sa ranki yana b'aci kingane ba besty va wai haka bane kawai ba soyayya a tsarina yanzu bana son na had'a karatu da aure.
Aure!
kikace sistu haba !sai ka ce ba mace ba , miye dan an maki aure yanzu a yanzu haka fa kina just seventeen years amma kike maganar yarinya gaskiya ke ba yarinya bace kuma in anmaki auren lokacin dakika zauna muna ina.?"
Besty bawai auren ne matsalar ba sharar ,ba ma sharar ba , wanke-wanken ,hmmm nifa ma girkin, ba girkin ba kula da mijin .to besty dan Allah ta ina zanfara natafi school tun arround 7:30 nadawo 5:00
Haba sistu sai,kace bake ke gayamin gaskiya ba , kinfasan cewa idan ka tsaya
kallan kwad'o to wataran a juri zu rafi ,
idan kin yi auren ki karatun ma zaki fiyinsa yadda yakamata domin mijinki zainabaki kulawa yadda yakamata kema zakina akula dashi .Maganar Shara ,wanke-wanke, girki , tsafta ta gida da kuma ta jiki na rantse cewa baki da matsala ta wannan fannin saboda ni kaina agunki nake koyan abu da ya wa a halin yanzu , Dan Allah sistu,karkisa a qidar wasu mata a ranki na sai,kin gama karatu kiyi aure , karatun mai zai maki,abun da kaso saba'in cikin d'ari a duniya kallan y'an iska suke wa mata duk da bahaka bane , kuma a wannan zamanin damuke ciki,bako wani namiji ne yakeson mace wayayya ba ma'ana wacce tayi boko iya boko dan haka,kimaida hankalinki ki nutsu kisan mai,kike yi".

"Haka ne besty tabbas kingaya min gaskiya a lokuta da yawa mu y'ay'an talakawa muna d'aura wa kanmu buri nayin karatu saboda mugama musamu aiki muyi kud'i mu taimaki y'an uwanmu, Amma bayan kasami wannan jin dad'in rayuwar mijin aure sai ya gagara ,sai,muzo muna cewa y'ay'an masu kud'i su bada karatunba su da auren masu kud'in amma mu sai anyi da gaske kisami wani d'an talakan a haka ma yana ja maki aji, masu auren masu rufin asiri acikin mu sune wanda basuyi karatun ba , kinyi karatu kud'in dakike samu ya qare a cefanan gid a shiyasa ake cewa mazanmu basu da rufin asiri sun bar wa,mace gida , hmmmm Allahu ka yafemana , wato yanzu auren qwarya tabi qwarya ake "

Amsa

Please Login or Register in order to submit comment