Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyad'a mar kamar qadangaruwa . fita khalifa yayi yabar ta ita da Barrister Shuraim .

Amnah ce tana dawowa sukayi karo da khalifa .Hi yaya khalifa whare are you going? Am daman ina son na je in sayo ma beauty Ice cream ne sabida zuciyarta tayi sanyi".

Murmushi Amnah tayi tace"yayanmu kafad'amin gaskiya fa son nanah kake? kai yafara sosawa alamar bashida gaskiya .

Amnah ce taqara cewa"um um fa yaya khalifa in kana sonta ka fad'amin kaga qawata ne zan sameta na gaya mata".

Gaskiyane qanwata ni bantab'a so ba amma tunda na d'aura idona akan nanah inji ina sonta kuma ina tausaya wa rayuwarta dan haka na baki amanar beauty nah in zamu tafi madina kina kulamun da ita yanzu remain 3 days a koma kutu kuma tasami sauqi naji yaya najeeb yana cewa anjima zai sallameta kuma kinga wad'annan police in bazasu barta ba sai anmaidata gidan kaso amma insha allahu zannamata addu'a Allah fitar da gaskiya".
"Ameeen"Amnah tace.

yaya khalifa amma yanzu wani hukunci ka yanke a ranka?

Auta na yanke yanzu daganan inna sayi ice cream zan wuce wajen yaya najeeb zancemasa dan Allah kar a sallameta har sai randa za'a koma shari'a kuma hakan ma saboda kar Alqali yayi magana zance a turota akeke saboda asan bata da qarfi ko Auta".? Daga bayansu sukaji Ana musu tafi juyawar da zasuyi sukaga Abdullah ne murmushi yayi yace"yayi kyau mutumina ay na ganoka wato soyayya zaka fara kabarni gaskiya to zance wa daddy kar ya fita dakai waje dan ba karatun zakayi ba ,kayi haquri mana mutumina 2 years zamuyi fa mudawo kasan masters ba 'a jimawa , hakane amma gaskiya nikam ina son nanah kuma zangayawa daddy muna dawowa gida".

To Allah ya taimakeka yaya shuraim ba sonta yake ba.

Amnah ce tayi magana"aa yaya abdullah yaya shuraim fa kawai tausayinta yakeji amma ba sonta yake ba .Saboda ya sha fad'amin yana mafarki da wata kyakkyawar budurwa".
To uwar zigi kamar a gabanki yayi mafarki har wani kike qari ki fa kiyayeni Abdullah yake magana"

Baki amnah ta turi gaba Allah yaya bana so zaka fara aikinnaka ko?To wallahi saina gayawa daddy ya gaggauta fita daku waje amma fa yaya khalifa kayi haquri zan nakulama da beautynka before ka tafi sai ka saya mata waya sabida kuna gaisawa zan b'oyemata wayar har sai,ta fito".

"Aa ni in aikin mai nake tare zamuje ta zab'i wayar da take so ".

To zan biku kaji yayanah nakaina .
"To" autar mu maza kima wajen beauty kikulamin da ita nanda 1 hours zan dawo insha Allahu .

Abdullah ne yaraka khalifa wani restaurant daje kusa da hospital in take away guda uku yasaya sai ice cream dakuma fresh milk .

Amnah ce takoma d'akin hira ya samu nanah tanayi wa Barrister Shuraim na ahalinta dake anaso marar lafiya yanasamun farin ciki shiya sa ya biyeta shigowar Amnah tacigaba da basu labarin .
Amnah ce tace"Aunty beauty amma yanzu idan angama shari'a Allah yabamu sa'a bazaki koma gidan azzaliman nan ba ko?eh Amnah Allah yataimakemu ayau in nan wani qarfi nakeji dashi ko yanzu a ka koma kotu insha allahu ina da shaida ta da zata sa a yarda dani."masha allahu"Barrister Shuraim yace .Amnah ce tace amma saikin huta agidanmu da mumayar dake adamawan ko . Barrister Shuraim ne ya Amsa da eh.

Su khalifa ne sukeyin knoking na qofar Office in doctor najeeb sukayi bada izinin shigowa Doctor Najeeb .

Shiga sukayi Zama sukayi a kujeran gaban tebur da Doctor .

Khalifa ne yace"yaya Najeeb dan Allah kar ka sallami beauty yau kabari sai ranar da za'a shiga kotun please yaya kar kace aa".

Doctor Najeeb ne yayi gyaran murya yafara da cewa"khalifa maike damunka ne?Baka da hankali ??zaka zo kasameni akan kar na sallami patient ina . Why I say why ? What is the reason ?ehyeee khalifa ?".

Abdullah ne yace"yayanmu ba haka bane kawai dai bro ina yana son Nanah ne bayason abinda zai tab'a lafiyarta .yayanmu kafahimta yanzu fa inka sallami Nanah gidan Kaso za'a mayar da ita before a koma kotun ,kuma fa haryanzu brother na bai gayawa Nanah yana sonta ba! Idan ka bar Nanah a hospital in nan ba'a kyautamasaba".

Doctor najeeb ne yahau masifa ta inda ya shiga batanan yake fita haquri suke tabasa , amma idonsa ya rufe sai fad'a yaketayi , Barrister Shuraim ne ya shigo office in yasamesu cirko-cirko ,tambayarsu yayi maike faruwa? Abdallah ne yayi qarfin halin fad'amasa duk abinda suka fad'awa yaya najeeb ."

Dariya yayi yace "to y'an qannena naji maza kutafi kuji da yaqin dake gabanku nikuma zan lallab'a maku wani tuzurun ya fad'a yana dariya.


suna ta murna .

sukaqarasa d'akin da sallama a bakinsu .

Khalifa ne yazauna a kujeran da take opposite da Nanah . Kallon Nanah yafara yi kamar bai San da mutane a d'akin ba , Nanah data Kula da kallon da yake mata bana qarewa bane sai ta sunkuyar da kanta . Abdullah da amnah ne suke ta gulmarsu a wannan lokacin ne khalifa yace"am am am beauty nah ".d'ago da idanunta tayi tana kallon sa .

Khalifa ne yace"beauty nah zaki iya aurenah zaki iya Zama dani amatsayin mata da miji ?."

D'ago da idanunta tayi tana kallon sa tana nazarin fuskarsa . Kuka Nanah ta fashe dashi tace masa"am say sorry yaya khalifa ni yanzu a tsarinah ba aure bazan iya yin aure ba a ahalin yanzu saboda nayi aure banji dad'in auren ba sai ma matsala da ya haifarmun.

Sorry kidaina kuka beauty nah karkimanta dacewa so gamon jini ne kuma a kallo d'aya dana maki na tabbatar da ina sonki qasa ya tsuguna yana magana yana cewa please beauty kar laifin wani ya shafi wani".
Nanah ce tace 'A dalilin auren da nayi yanzu shine sanadiyyar shiga na kotu zaka iya auren wacce takashe mijinta?".

Dariya khalifa yayi yace'kidaina fad'an haka saboda nasan bake ki ka aikata ba kuma ko ke kika aikata tabbas in kina sona zan aureki domin nasan cewa lokacin da Allah ya kwasa ma a duniya yanayi zaka tafi sai dai ace akwai silla , dan haka kiyi haquri kidaina d'aukan haka a matsayin komai domin wasu mutanen basa yarda da qaddarar da Allah ya d'aura musu , beauty ina mai roqonki da karki shiga cikin irin wad'annan mutanen kuma kidaina cewa kekika kashe mijinki domin zuciyana bazaifi iya d'aukan wad'annan maganan ba naroqeki beauty dan Allah in kina sona!!! Karki b'oyemin please karki wahalar da zuciyana beauty . Zuciyana bazai iya d'aukan hakan ba na roqe ki . Please yaya ka tashi kadaina durqusamin dan Allah .

Bazan tashi anan ba har saikin gayamin kina sona ko baki sona!!!!!.?

Yaya khalifa in nace bana sonka nayi qarya domin Kaine mutum na farko da ina cikin wannan halin na mutuwa ko rayuwa yace yana sona! Bazan watsa ma qasa a idanu ba amma ni a yanzu auren ne bazan iya yi ba .Why not? Ina tsoron matsalar dazata qara faruwa ni banzauna nayi karatu nasan karatu nayi ba , umhmmm kuma ni auren nayi shi banji dad'in yinsa ba gwanda na koma gaban iyaye nah na zauna."

"Aa beauty baza'ayi haka ba kidaina jin tsoron komai na roqe ki dakibani dama akaro na biyu na gwada sa'a ta please!

"Bakomai yaya khalifa nabaka dama kanemi,soyayyata da kanka Allah yabaka,sa'a

da" Ameen " y'an d'akin suka amsa .

.........A gidansu inna laure kuwa da hajiya sahura , yaran gidan ne suke ta rizgar kuka !a yau kwana uku ba labarin,iyayennasu sun had'a kansu yaran gwanin sha'awa idan kagansu kuma zaka tausayamusu sabida ko abinci basa iya ci." Hafsat ce tafita zuwa wajen malaman addini tanabada sadakar kud'i anayiwa mahaifansu addu'a Allah sa suna hali mai kyau .

to "Ameen"Amma,badanhalinsu ba.
y'ar gidan hajiya laure Afrah sa'ar hafsat wacce take ji dakanta a gidan duk wannnan abu da yake faruwa a gidan ita batanan batamasan anayiba sai a yau tadawo gisansu ta riske labarin b'atan iyayenta ko ajikinta , saboda tasan ba wani damuwa da rayuwar ta mahaifiyarta tayiba duk da mahaifinsu mai kud'i ne ita dai,kawai a je ayi karuwanci a kawomata kud'i shiyasa bata son mahaifiyarta tun batason fita har abin yazama mata jiki acan kuwa wajen y'an iskannata sunan da suke fad'a mata shine meesha baby ."

...................................
A garin Azare kuwa Zaid ne yajuyo domin ganin wanda yamasa wannnan aika-aikar Asiya ta kalla ta runtuma da gudu side nasu , ita kuwa amal kafeta zaid yayi da manyan idanunsa , huremar idanun tayi tace"lafiyarka kuwa sai kace wani maye kake ta kallona ".?

Ya bud'e baki zai yi magana kenan sai Amal takuma cewa...

By HAD Siyamah


comment

And



share


BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY A
ND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya


_FREE BOOK_

page 12

Shut up !Banson maganan banza kaji ko"?.

Magana yafara kamar haka ke wacecce?daga ina kike?mekikeyi a gidanmu? Duk A Amal ita kad'ai yayi wa wannnan maganar .
Dafarkodai wacce tambaya kake so na amsa ma ?".

Dukansu . Murmushi Amal tayi tace" A yanzu bani da time but I take promise zan fad'a maka ."

Ta gefensa Amal ta wuce side nasa ya shiga abinci yaga anjera masa kala-kala bud'e culars in yafara kad'an yaci abincin ya bud'e fridge ya d'auko bottle na giya ya kafe kansa sai da ya shanye tas bottle guda ya yasar da bottle in yayi a dustbins layi yafara yi daganan ya d'ale saman dinning in ya kwanta da takalminsa a qafarsa ya kwanta bacci yafara ko a jikinsa da abinda ke faruwa dashi.

*************

Amal kuwa isarta side nasu keda wuya ta hango Asiya a kan 2sters tana ta bacci cikin takura tashin ta tayi tace"sistu wake-up ".

Tashi tayi muka koma d'akin mu baccin ta ta cigaba dayi duk a tsorace take nikuma wanka na shiga after na fito a toilet saina zauna gaban mirror lotion nake shafa wa honey bees daganan na goge maiqon fuskana humra na shafa a jikina na d'auko doguwar Riga nasaka yane kaina nayi da gyalen rigar ,perform na d'auko na fesa kala-kala a jikina masu sanyin qamshi .

Fita nayi zuwa parlour fresh milk da cake na d'auko kan dining na hau na ci cikin nutsuwa nake ci daganan na shiga kitchen domin d'aura sanwar dare mommy da daddy basu nan girki nafara kansu dawo nake son gamawa Asiya kuwa wanna mutumin ya tsoratata shikuma ba komai yamaataba take tsoron sa .

Girki na nagama sakwara miyar egushi da jellop in spaghetti tasha kayan lambu da busashshen kifi . Gamawa nayi namana kunun shinkafa , jerasu nayi a dinning na dawo zan goge kitchen kenan naji a bayana ana cewa sannu da aiki sistu . murmushi nayi nace"sannu da bacci sisina". Dariya mukayi gabad'ayanmu daganan Asiya ta karb'e dustern hannu na tagyara kitchen in .

Magrib ne ya gabato mukaje mukayi sallah muka karanta alqur'ani mukayi sallah isha . Fitowarmu keda wuya a d'akin muka ga mommy da daddy sun dawo sannu da dawowa muka musu suka haura saman domin yin wanka daganan sai su fito muci abinci .

Parlourn muka dawo muka zauna a 2sters kallo muka kunna remote muka d'auka muka zab'i channel MBC Bollywood muka saka alokacin ana haska film in kalhonaho kallon film in muke cike da nisha'i.

*********
Dare ne yafara a time in ne zaid yafara motsa qafafunsa tashi yayi yaga a yadda yake kwance kunya ce takama shi danma Allah yasa ba wanda ya shigo ,toilet ya nufa wanka yayi yafito da alwala masallacin gidansu ya nufa sallah yafara gabatarwa wato sallah la'asar , magrib and isha bayan ya idar ne yana kuka yake roqon Allah yafemasa a abinda yake aikata wa a b'oye batare da kowa yasan me yake ba daga shi sai Allah daya haliccesa.


Addu'a sosai zaid yadinga daga qarshe yana addu'a yana kuka a kan Allah ya Shiryi iyayensa bayan yagama ne yanufi side in yayan daddynsa wato Alhaji al'ameen ."Assalama alaikum "ita ce kalmar da tafito a bakin zaid .
"wa alaikassalam "suka amsa baki d'ayansu , shigowa ya qarasa yi durqusawa qasa yayi yace"Daddy good day, na same ku lafiya?".

Daddy ya amsa da lafiya qalau yaron kirki .
juyowa yayi gefen yace" mommy momcyna barka da dare, ya gida?ya aiki?".


Alhamdulillah !Zaidu bawan Allah !!!
Ya school yaron kirki?."
lafiya qalau momcyna .
maza tashi muyi dinnner daddy yafad'a tashi yayi suka fara cin abincin , suna cikin cin abinci daddy yace"Zaid ga ATM Card nawa gobe insha allahu ina so kaje kayiwa Amal registration a makarantar su Asiya".
"TO" zaid yace daga bisani ya juyo ya kalleni yace"zuwa gobe ku shirya da wuri arround 7:30 zamu tafi sai kushirya da wuri kunji ko "?.

"Eh yaya zaid insha allahu zamu shirya da wuri ."
............Washegari Amal ce ta shiga kitching ita kuma Asiya tana gyaran gida mommy ce tafito tace"yarana maza kuje ku shirya kunsan halin yayanku .
No mommy zamu gyara maki gidan before mutafi ".
Gama gyaran mukayi breakfast mukayi yau bamujira mommy da daddy ba saboda muna sauri d'aki muka wuce wanka na fara shiga bayan na fito daga wanka Asiya ta shiga Arabian gown nasaka perfumes na sha fa ajikina masu sanyin qamshi da farar humra jar rigace gown da duwatsu a jikin ta golden, Powder nashafa na rage maiqon fuskata sai man baki danasaka , na d'an zana kwalli a idona nikaina,nasan nayi kyau saidai mahassadi yace bahakaba , yane kaina nayi da gyalen rigar takalmi cover shoe nasaka , jaka na d'auka golden sai walqiya nake kunsan ni banayin makeup mai hayaniya , nafison simple makeup.
Asiya ce tafito a wanka ,wow naji tana cewa gaskiya sistu kinyi kyau , Shiryawa Asiya tayi irin shigata tayi Amma ita rigarta pink ce .
Fitowa mukayi kamar zamu gasar kyau jakar makaranta Asiya ta d'auka tasa a bayanta , compound na gidan muka fita a bakin motar yaya zaid muka tsaya , hira muka fara muna jiran fitowarsa , bayan ya fito ne muka gaida shi .
fad'a muka fara akan kowa tana cewa ita zata shiga gaba daga qarshe Barin Asiya ta shiga nayi.
Tafiya muke cikin Slow harmuka iso school in isar mu keda wuya yawuce direct collinvest nacikin school registration akamin daganan muka je libry muka d'auki Asiya gida muka dawo.
yaya zaid ya ban mamaki a yau ko magana baimanaba fa , isar mu gida keda wuya , Garden muka wuce zama mukayi muna shan iska kawai dariyarsa muke ji ta gefen damanmu.
.... ......................................... ...........
Agarin Abuja
Maganayake yanacewa "beauty yanzu kinyarda dani ?".
"Aa nadai baka dama akan kanemi soyayyarka a gareni kaji ."
"To gode beauty insha allahu sainazama jarumi a cikin jarumai a zuciyarki ".

Barrister Shuraim ne yake had'a tarun hujjojinsa saboda gobe za'a koma kotu , zuwa yayi yace wa nanah ina fatan a wannan karon zaki bamu had'in kai yadda yakamata saboda muna son muyi winning wannan shari 'ar Insha allahu , Fita Barrister Shuraim yayi gida ya wuce direct domin ya huta .


"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un "
why mom me namuku tunda kukakawoni baku tab'a zuwa ganina ba gashi yanzu ana shirin yankemin hunkuncun a binda banyiba why?why??why mom???
please kitaimaka kizo mugana before namutu mom please na roqeki dan Allah ina cikin halin da bamai iya fitar dani sai Allah da ya hallicceni sai kuma addu'arku my mom

By
HAD Siyamah

Share
And
Comment

like .


BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya


_page 13_
Farkawa nayi da salati a bakina ,"Allahumma ajirni fil masifati wara zaqani,khairan minha wala quwwata illa billah"Gumi nake sharce wa , tabbas ba mu kyautawa y'armu a binda muka mata ba , na rantse da Allah a yau ko alhaji bazai yardaba , sai naje naga y'ata .
Sallah na tashi nayi , daganan na d'auko jakata nafara sa kayana a ciki , ina cikin sa kayan ne alhaji ya shigo , lafiya hajiya naga kina had'a kaya ina zakije?
"Nagaji Alhaji nace nagaji da abinda kake min saboda kaga ina ma biyayya shiyasa karabani da gudar jinina kamata auren dole ,Duk da haka bai isheka ba , har saida kahana ni zuwa gareta a yau y'ata auren ta shekara d'aya amma bantab'a ganinta ba kamar yadda bata tab'a ganina ba , Alhaji baka kyauta mana ba , bansan mai wannan y'ar taka tama ba ka yanke wannan d'anyen hukunci kuma tabbas nasan cewa yarinyata ba lafiya take ba dan ga ta nemeni , Alhaji a halin da ake ciki yanzu nayi nisa banajin qira dan haka kasani,ko kabini ko kazauna wannan damuwarka ne ina fatan kagane mai nake nufi ko?."
Alhaji ne yace"haba !haba !!haba hajiya!!!
"Kinsan kwa mekike cewa? Nifa mijinki ne , bai kamata kimin irin wannan miyagun kalaman ba , kuma dakike maganar zuwa garin Abuja kinmanta cewa ke sarkuwarsu ce me zai kaiki gidan yara , haba mana masoyiya kiyi haquri please!,"
koma dai me zakace kace a bar yaudarata da wannan kalmar, ta masoyiya nifa ma kaga inzaka Bismillah shirya mutafi in bazaka ba kaga tafiyata".

"Ya salam nikam,yau me ke faruwa ?da matata ne kwata-kwata nakasa gane kanki a yau kin canjamin , matar da ko musu batamin a yau kike min shouting".

Sorry kagane ba!wallahi wani mummunan mafarki nayi , to a binda yasa ban fad'a ma ba , kasan cewa mafarki kala uku ne , anfison mutum ya fad'awa mutane kyakkyawan mafarki , amma in kayi mummuna da ga shad'an ne ba'aso kafad'a , in kayi mafarkin ruwa kuma ance shi kasa a ranka before ka kwanta ."
Dan haka ni nawa mafarkin ba'a son fad'ansa .
Jikin Alhaji ne yayi sanyi !Magana ya fara yi , tabbas sai yanzu nagane mai kike nufi , ke mace ce, kuma uwa dole ne in abu zai faru da yaranki zaki ji ajikinki , bakamar mu maza ba .dan haka ina addu'ar Allah sa, y 'armu tana lafiya".
"Ameeen"hajiya tace Alhaji ne,ya shirya kayansa suka nufi garin Abuja ayau abuja tana,da manyan baqi daga Adama yola.

A garin Azare kuwa
Dariya mukaji yanayi,yana cewa "haba josep kasan nifa yanzu nayi hankali , ba kamar da ba."dan haka ma kabar min wannan maganar" joy"take ko wa kace mata tayi haquri dan ni yanzu nayi nisa da U.S A,nida komawa kuma sai wani sanadin dan,haka,yanzu nama yi hankali zan,xauna a gida nafara aiki ,amma nabar garin U.S A,saboda kai shaidane akan abinda muke aikatawa ni "ZAID"nawa addinin bai koyar dani haka ba, amma nake biye muku mune zuwa club mune wajen y'an mata , mune shan kayan maye , ya salam !!!Allah natuba josep irin wad'annan maganan in ina tunawa kaina har wani ciwo yake nabarka lafiya ."
"Zuwa mukayi muka durqusa a gefe mukace yaya zaid meke faruwa dakai?wani abunne??me aka maka ???fad'amana kaji ,kaga mu qannenka ne ,du Amal ce mai fad'an haka ".
Bakomai qannena kawai wani abu ke damuna kuma bazaku tab'a fahimtar hakan ba a yanzu ".
Tashi yayi ya tafi side na mahaifiyarsa zuwansa,keda wuya yasamu minal tajawo trolly nata zata koma makaranta.
Yaya barka da wannan lokaci?
Barkadai,Mommy fa tana ina? "mommy sunfita ita da shamsiyya har yanzu basu dawo ba , shiyasa zan wuce nagaji da jiransu ,dan bansan yaushe zasu dawo ba , nagaji da zaman gidan gwanda na koma school. "OHK"nagane Allah kaiki lafiya.
"Ameen" tace wucewa tayi side na momcy shigarta keda wuya tasamu muna zaune muna shan kayan drinks hankalinmu kwance,sannu da zuwa aunty minal, "yawwa sannu ina momcy?"tana d'aki muka bata ansa , haura wa sama tayi wajen mommcy gaisawa sukayi momcy tamata nasiha a kan tazauna da kowa lafiya makaranta wajen qaro ilimin zaman rayuwane zakiga mutane kala-kala cristan , yarabawa ,hausawa ,fulani da dai sauransu kowa da irin nasa al'adar dan haka ina mai hanaki shiga sabgar yara ma rasa tarbiyya kinji ne ko?."
"Eh " naji mommcy .
"kiyawaita addu'a aduk in da kika tsinci kanki , banda huld'a da yaran banza irin y'an lesbian ,y'an shaye-shaye ,y'an iskan makaranta dai gaba d'aya Allah tsaremu ,saboda hausawa nacewa abokin b'arawo b'arawo ne ,haka abokin d'an iska d'an iska ne , Dan haka Allah kaiki lafiya ya kuma dawo dake lafiya, ayi abinda akaje yi banda zuwa,party da qawaye ko birthday domin komai yana iya faruwa anan bare a halin yanzu in bakaje irin wad'annan abu-buwa ba sai ace ma bagidaje to gwanda acemaki bagidajiyar a bar ki da mutuncinki."
Rungume momcy minal tayi tana godiya tabbas momcy ke uwace jajirtacciya nagode Allah saka da alkhairi tabbas mai sonka shiyake ma fad'a wanda baya sonka a hanyar da bata dace ba yake d'auraka. "
tashi minal tayi zata tafi momcy ne ta dakatar da ita , turare masu kyau da humra momcy tabata ,tafiya tayi tana godiya.
palour tafito tasamemu cemana tayi sisters na tafi makaranta .
tashi mukayi muka rakata har bakin mota muna mata Allah kiyaye hannu take d'agamana muma muna d'agamata .
...............
A qauyen jauro kuwa wata zakanya ce tashigo tafar wa mutanen qauyen, kowa ya shiga tashin hankali daga qarshe samarin garin ne sukayi shirin fita yaqi , fitowa sukayi kowa da makamai a hannunsu far mata suka fara amma ihu take takasa basu damar kasheta , wani babban malamin garin a ka qira yana kallan wannan zakanyar yace "ku saurara kudaina farmata ina son kujawota ta biyoni bukkata nabata wasu magani na wuni guda indai abinda nake zargine tabbas zata samu waraka insha allahu " .
Zakanyar nan aka jawota sai bukkar malam , samarin nan ne suka tafi malam ne yayi addu'a ya watsa mata ruwan addu'ar daganan ya had'a maganin gargajiya yabata ta sha watsamata wani ruwan addu'ar ya sake ay kuwa sai ga zakanya tayi wani irin juyi , daganan tai tsalle fad'owa tayi sai ga mutum sukutu'm .

Tambayar duniya ammata taqi magana sai dai cewa da take , Dan Allah bayin Allah kutaimakeni ku maida ni gida , ina son fad'awa kowa abin da yafaru a daina zargin baiwar Allah kan nabar duniya namutu da haqqinta , dan Allah natuba .
"Malam ne yake magana yace yarinya mai ya faru?mai kike cewa banganeba??
"Baba kayi haquri in kaji Abinda na aikata nasan bazaka,taimakeni ba ."
Amma zan gaya ma .
"Baba najima ina bin bokaye duk wani boka idan naji labarinsa sainaje garesa , Acikin shahararrun bokaye bayadda bansaniba, har takai takawo mun raba mijinmu da danginsa , mahaifiyarsa , duk mun rabashi dasu,Daga qarshe labari qarin aurensa ya riskemu munyi baqin ciki sosai amma sai muka d'auki alqawari kashe mijinnamu kuma mu d'aurawa Amaryarsa, yanzu haka tana gidan kaso.
"Baba ne yace innalillahi wa inna ilaihirraji'un" yanzu y'ar nan abinda kika aikata kenan!
Baba wannan shine abu mafi qanqanci damuka aikata nagaya ma sauran manyan bazan iya gaya da bakina ba, domin ni kaina tsoron sharrina nake , daga qarshe dai boka nayiwa tsaurin ido yamayar dani zakanya ita kuma qawar tafiyata guduwa tayi".
"Ya salam "in kana duniya zaka sha kallo !yanzu haka ki aikata yarinya ! Amma ni yarinya zan taimaka miki.
Amma bada qarfina ba da kud'i

Please Login or Register in order to submit comment