Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

.amma inshà Allah next week zandawo daga d'aya b'angaren naje tace to Allah kaimu hira suka cigaba dayi daga bisani sukayi sallama suna cikin farin ciki"

Amnan ce " ta sauqo qasa tana farin ciki .


Abdullah ne yace" kunga autar gidanmu autar momynta "fuska na shagwab'e nace"Allah ya Abdullah bana so . Ummm "autar dadynta miye bakiso " shagwab'e fuska nayi ina dira qafa nace"ya shuraim kace yadaina tsokana ta " haba amnanmu amnan mama . Kuka na fashe dashi ina cewa "wayyo Allah na ya shuraim kaji harda ya khalifa ko " rabu da su autar momynta zan sab'a musu barni dasu. Kamar daga sama naji ya najeeb yana cewa "am am am, am mai sunan tsofi dira qafa nayi tayi a qasa sai ga momy ta fito tace" kubarmin auta nah ta huta saboda haka na yanke hukunci fa dadynku ya dawo a bar min y'ata ta huta Abdullah da khalifa zaku tafi madina kuyi karatu aa momy mukam American Zamu tafi momy ce tace"bamai kaiku American madina zaa kaiku saboda kuyi hankali gaskiya momy ni nafison madinan Abdullah yace"nikam nafison American.


A garin Azare ...................
Kamar daga sama naji ana cewa" Asabe! Asabe!! Asabe!!! Ina baquwar inji momy Asabe ne tace "Amal haura sama ana qiranki kiyi a hankali in kin dawo b'angaren mu masu aiki .

Juyo wa nayi namata murmushi nace "to baba Nagode sama na haura wata kyakykyawan budurwa nagani a wasu luntsuma-luntsuman kujeru tana Shan ice cream . Kallon ne ya koma sama domin tsarin parlourn saman nan dana gani ko a gidan president iya kaci .

"Murmushi naga wannan budurwar tamin tace ya sunanki?".
'Amal sunana nace mata , "wow nice name sunanki mai dad'i hannu naga tamiqomin wai muzama friend , nima hannu namiqa mata muka qulla .
Tsalle naga ta daka tana cewa"ummi dady !!! Nayi new sister kuma ina sonta .

"Momy ce tace Masha Allah yarana to Allah ya raya manaku "(ameen) suka amsa .

"Dady ne yace yasunanki y'ata" Amal nace masa , yayi kyau to nizan wuce sai na dawo , Allah ya kiyaye na ji wannan budurwar tace nima sai nace" dady Allah kiyaye (ameen) yace naga momy ta raka shi qasa wannan budurwar ce tajawoni muka shiga d'akinta had'uwar wannan d'akin tsaya gaya muku b'ata time ne saboda komai na room in fari da pink ne .

Zama mukayi tace min baki tambayeni sunana ba ?". Murmushi namata nace"ay ban kai matsayin tambayar sunanki ba hajiya qarama " raina ga ya b'ata tace"bana son haka sis ni a matsayin y'ar uwa tajini na d'aukeki saboda na taso ban San kowa ba sai ummi na da daddy na yayanah ya rasu yau tsawon shekara takwas a Time in ina da shekara goma .

Rayuwar gidan akwai munafurci sosai a cikinta shiya sa ummi na bata yadda da y'an aiki yanzu haka ma dakikaga an d'aukeki aiki sawa ummi tayi a nemo ma ta yarinya wacce bata fini ba sai Allah yasa aka sameki ". Gaskiya kaina ya d'aure ko zaki iya Bani labarin familyn nan. "bakomai zan baki inshà Allah amma bayanzu ba"nasan mai kike son tambayata to nidai sunana Asiya amma zaki iya cemin sistu kamar yadda nake fad'a miki. Yanzu ta shi ki shiga wanka inkin fito sai muci abinci daga nan mu zagaya gidan ko . Magana nake sonyi amma ni Amal ina tsoron ran sistu na ya b' aci ni a nawa ganin amatsayin y'ar aiki nake amma sai gashi ta d'aukeni amatsayin da bana tunani wato sister nata , tab'ani naji anyi juyawar da zanyi naga sistu ne tunanin mai kike ?ta tambayeni bakomai nace mata na tashi na shiga wanka .

"Shigata toilet keda wuya naga Abun da ban tab'a ga ni ba . Wato wani glass kamar mirror amma bansan amfaninsa ba banga bucket ba bare na d'auka nayi wankan kawai Kan toilet na hau nayi wankan da abin wankin tailes na saman gini hmmmmmm nikaina nasan nayi qauyanci bayan nagama nafito .
Kaya sistuna naga ta ajiyemin wata abaya ce duk jikin ta duwatsu abayar ruwan golden colour ce lotion na sha fa da powder sai lips a bakina wani kyau naga naqara da na ganni a mirror kwalli nasaka a idona daga bisani nad'auki underwears nasa nad'aura wannan abayar akai wani kyau naga na qara sai na fesa turare masu qamshi da sanyi , humra na hango dake ni ma a bociyar qamshi ne na d'auka na fesa.


Salati naji ana yi a bayana juyawar dazanyi naga sistu ce da qaton plate a hannunta cike da mayan marmari da su snacks sai drinks .

Qarasawa kusa da ita nayi na karb'a na ajiye a Kan table na d'akin . Magana naji tayi ta nacewa" gaskiya sistu kin had'u ke kyakykyawa ce sosai kinga yadda kikayi kyau kuwa kamar mai zuwa gasar kyawawa , Chan cha d'i kyau haka gaskiya kinfini kyau zo muyi picture " murmushi namata dake daman ni gwana ce wajen murmushi had'e da da jijjiga kai na. Ashe ta d'auki photon ba qaramin kyau mukayi ba duk da bansan ta d'auka ba".

Abinci mukaci daga nan mu ka shigo parlourn ummi muka gani mukace ummi sannu da gida . "Yawwa yaran kirki photon da mukayi muka nuna mata . Ummi cewa tayi"sai kace y'an biyu kawai asiya tafi Amal haske ne ". Amma nima fa bawai baqa bace kyakykyawa wace ni ajin qarshe . Fita mukayi bamu zarce ko ina ba sai wani site a cikin gidan da bansan da shi ba shigarmu keda wuya naga wani budurwar yarinya xaune sanye da glass tana karanta daily news gaisa wa mukayi naji sistu tace"ina mama "tana sama wannan yarinyar tace a shekare bazaifi shekara uku ta ban ba .

Sama muka haura muka gaida mama wani kallon banza naga tanamana fitowa mukayi mukai sallama da ta qasan .

Lambun muka nufa amma sai naga kamar abinda akamana Bai damekiba na fad'a wa asiya dariya tayi tace" chab baki San halinsu bane ay yau baa mana komai bama.


Ringing na wayanah naji alamar cewa message ya shigo dubawa nayi domin ganin mai saqon yake cewa gashi dai kamar haka(Amincin Allah ya tabbata a gareka habibyna barka da dare abin qauna, samuwarka a cikin rayuwata ya samar da canji da k'aruwar farin cikina, ta hanyar sauraron muryarka mai tausasa zuciya da kuma kasantuwata a tare dakai a cikin rayuwarka mai tsari, kuma a yanzu duk wani abu dazan furta bazai wuce ince ina k'aunarka ba, sannan kuma kana d'aya daga cikin mutanen da bazan tab'a mantawa dasu ba har k'arshen rayuwata I love you my whole life, fatan barci mai dad'i gareka abin k'auna, Ina Sanka son da bansan iyakar shiba, ina mai fatan Allah ya bani kai,a matsayin miji, I LOVE YOU. Forever and ever .

Dariya ma ni message in yabani .

By HAD Siyamah 😯🖊📝
Alqalami yafi tajini

Share and
Comment


*🧑‍⚖️BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

K'ungiyace da tayi fice wajen nazartan aiki da ilimi haka zalika k'ungiya d'aya tamkar da dubu , tayi fice wajen kawo muku littafan Hausa domin fad'akarwa da kuma nishad'antar da masoyanta .



_FREE BOOK_

Page 7


Dariya nayi nace baki da aikin yi hafsat ,wayana na mayar gefe nacigaba da bacci na , a lokacin na fad'a wata duniyar da bansan da ita ba .


Gudu nakeyi acikin wannan jeji amma har a lokacin bankama wad'annan mutanen ba yarinya ce sai kuka naji ta nayi tana neman taimako amma ina azzaliman mutanen nan biyoni da gudu suke,nima ina gudu akan zan karb'o wannan yarinyar daga hannun mutanen , saman wata qatuwar bishiya na hau a lokacin suka daina ganina suka wuce min yaqarsu na fara ta baya ashe mugu bashi da kama akwai wasu da yawa a bayana. harbina naji anyi dafe wajen nayi amma duk da haka ban haqura ba naci gaba da tafiya akan na karb'o wannnan yarinyar , dukana naji ana yi "lafiya bro kake ta haki acikin bacci kamar wanda yayi fad'a da zaki ko kura. "hmmmmmm sai alokacin nagane cewa mafarki nake ba a gaske hakan ke faruwa ba . Bance masa komai ba na shiga toilet domin watsa ruwa wani irin ciwo naji zuciya ta namin wanka nake amma hankali na yana Kan wannan mafarkin danayi . To waye wannnan yarinyar tambayar danayi wa kaina kenan, taimakon mai take nema ,suwaye suke binta mai tamusu , miyasa ban kama su ba to ma Dole ni zan taimaketa. tabbas a cikin wannan mafarki nawa akwai ayar tambaya Dole akwai abin da ke shirin faruwa dani. fitowa nayi a toilet na shin fid'a sallaya na kalli Gabar domin gabatar da sallah acikin wannan Daren da kowa yana bacci amma ni ina sallah.

Sallah nayi sosai na roqe ubangiji akan duk abin da zai faru dani Allah yasa ya Zama alkhairi , ubangiji Allah karkad'oramin abinda bazan iya ba , Allah ka taimakeni ka kawo min d'auke acikin wannan mafarki nawa , wannan sharia damuke yi Allah kabamu saa kar alqalin nan ya yanke hukuncin da bashi ba . Shafa addua ta nayi na koma kan bed na kwanta ,addua nake araina saboda a yanzu naji sauqin abin da ke faruwa dani acikin raina .

Bayan sati guda hafsat na qira a waya nace mata mu had'u a wajen restaurant da ke bayan gidan sardauna.

Y'ar qaramar c.d ne a jikin aljihuna hafsat ce ta qaraso wajen welcome namata nasa aka kawo mata kayan sha da motsa baki citake a nitse muna hira da ita daga qarshe nace"hafsat wani taimakon ki nake nema amma sai zuwa nan da two week " bakomai mai kake so Nama? "Akwai shariar dazamuyi nan da two week inshà Allah amma before nan . ina son sanin cewa " wacecce ke? "Murya na gyara nafara magana kamar haka ni sunana hafsat madaki yellow mahaifina yana da mata uku y'ay'a shida , na taso a gidanmu naga iyayena basu zaman lafiya a tsakaninsu hakan har ya shafemu y'ay'an bamu zumunci a tsakaninmu a lokacin da iyayena sukaji mahaifina zai qara aure a time in suka had'e kansu kamar basu fad'a sun sayar da komai nasu sunje gun boka akan a fasa auren amma hakan Bai yiwuba sai da akai auren daga qarshe sun koma gun bokansu yace musu aure sai anyi shi ba fashi , a yadda na fahimta wannan bokan kud'in su kawai yake ci saboda duk aikin daya musu baya yiwuwa daga qarshe nace musu su daina wahalar da kansu malavxvmin mu na islamiyya yace mana bakyu zuwa wajen boka domin hakan shirka ne had'a Allah da waninsa, sallar su ta kwana arba'in. Bata karb'u ba to ma ay baa kwana arba'in ba Ku koma ba a lokacin suka min duka kwana goma sha biyu a akwance a gadon asibiti babban Abun da ke damuna shine matar da mahaifina ya aura bata sonsa hakan yasa suka rinqa d',aura mata sharri kala-kala daga qarshe maganan nan danake ma mahaifina ya mutu kuma nasan iyayena su suka sa masa magani a abinci yaci ya mutu , shiyasa bana yiwa kowa a gidan mu biyayya a yanzu haka ciki kuwa harda mahaifiyata.

Kuka na gama a lokacin nace "kaji ta qaicaccen tarihina . Taaziyar mahaifina yamin yace"yanzu ina amaryar gidan Ku?" .

Kuka na rushe da shi nace"tana hannun y'an San da . "Miyasa? Sunqalamata sharri akan ita takashe abbanmu . Kuka na rushe dashi a lokacin barrister shuraim yace"hafsat je gida ki huta Zamu had'u a waya zuwa anjima naga abinnan yana damunki dayawa ". Gida na tafi domin na huta .


Tunani na fad'a wato ita hafsat mutuniyar kirki ce iyayanta ne sai a hankali, kodan ba zab'inta bane haka Allah yake yi yafitar da matacce daga jikin rayayye , yakuma fitar da rayayye da jikin matacce . Ahalin yanzu hafsat rayayyace .


Tabbas ni shuraim nayi wa hafsat mummunan fahimta baikamata nabarta tana sona ba nasan ba aurenta zanyi ba , bama wannan ba ahalin yanzu ina da qwararan hujja in anje kotu kamata na san mai zan gayawa alqali , qirane yashigo wayata doctor najeeb nagani a rubuce d'agawa nayi hello! Kana ina daga d'aya b'angaren naji anfad'a ganin ina hanyar dawowa gida qit ya kashe wayar sa .


A garin Kaduna kuwa zarah ce tazo gidan su Amal tana gayawa mama tasami admission na law a school of law dake garin Kaduna ,"murna mama ta tayata alokacin take yiwa ta y'ar addua Allah ka tsaremin y'ata aduk inda take kasa tana cikin farin ciki, murmushi nayi nace"ameen summa ameenu mama . Gida na tafi ina kewar aminiyata Allah sarki Amal Allah cikamaki burinki na fad'a ina shiga gidanmu .

y'an mata uku na hango suna tafiya cikin nutsuwa a school in su federal univasity dake cikin garin Azare hall naga sun nufo domin yin lecture , lecture a kafara naga dokoki kala-kala iri-iri , asiya na tab'a nace sistu ruwa zansha "ayya sorry sis da ruwa a jakata d'auki kisha "thanks sis ashe tambaya lecturer yake kawai naga yanuna ni yace"what is drug according to world health organizatio. bayani namasa sosai akan shaye -shaye da samari ke fama da shi a yanzu daga qarshe test yayi mana gani yayi banayi yace"what wrong ?" nothing . paper ya miqo min had'e da biro rubutu yaga na fara amma bansa reg number nawa ba .


cewa"yayi nabiyo shi office "after mun,gama nabishi office . what is your name ?"yace min . am by name Amal . miyasa baki da reg number . ni ba y'ar school in bane . nabashi answer , "ohk keda wa kikazo?Asiya nabashi answer a taqaice domin naqosa da tambayar dayake min . miyasa bakiyin school in ke ?
"ya Allah na qosa a tambayar wannan mutumin fa na gaya azuciyata. sai nace masa"ni a shekarannan result ina ya fito sai next year zan shigo.
ohk kikawomin takardun ki zuwa gobe saboda banga amfanin zuwanki rakiyaba . sir amma ay sun fara lecture ?"ba,matsala saboda baa gama shigowa school in ba har yanzu . kina iya tafiya . thanks sir .

Fitowa nayi a office in, mata nagani suna ta leqen office in sir khaleel .

Dabar su asiya na nufa ina zuwa nace "hira kuke sha ne " eh wlh d'aya acikin y'an matan gun tace , drivern mu ne yazo sallama muka musu muka tafi gida.

Isar mu gida ke da wuya nawuce kitchen na d'auko mana abinci asiya kuma ta shiga wanka bayan ta fito na shiga na watsa ruwa nafito . abinci muka ci muna hira bayan mungama asiya tace"sistu muje mu gyara gidan tashi nayi nafara shara asiya kuma tayi moping , damuka gama sai mukai wanke -wanke tare .girki muka fara muna cikin girki asiya tace"sistu d'azu me kikayi a office in sir khaleel ' dariya nayi nace mata"bakomai sis kawai ya tambayeni miyasa bani zuwa school? "To ke miki kace masa . Nace masa result ina ne Bai fito da wuri ba . Amma yace nakawo masa result ina zuwa gobe .

To Allah yakaimu amma kibari in daddy ya dawo Zamu bashi labarin abin da ke faruwa sai ya saki a school in ko amma please sis kar mu bari yasaki a school in . Lah sis baifa ce zaisani a school ba. Mommy ce daga bayan mu muka ji tana cewa yayi kyau yarana kuna da tunani mai kyau . Yaushe kuka dawo a school in? Mommy tun yamma muka dawo bacci kike shiyasa bamu tashekiba . " Haka ne me kuke dafa mana ? 'Amal ce tace"mommy muna dafa tuwon shinkafa miyar egushi da farfesun kaji sai kunun shinkafa . Well-done yarana to fana tayaku saboda magrib ta musa yanzu daddynku zai dawo . mommy ce takama mana muka qarasa girki .

Bayan mungama sai muka shiga d'aki domin yin sallah bayan mun idar , asiya tace"sistu d'aura min suratul tauba ,karanta mata nayi daga nan nayi tilawa sai muka maida sallar isha'i , qasa muka sauqo domin yin dinner . daddy da mommy muka kalla a dining hannu na , asiya taja muka qarasa dinning .


A fanni su Asabe kuwa , Asabe naji tana cewa "gaskiya impossible ace wannan yarinyar daga zuwanta tazama kamar y'ar gida mu muna xaune a fanni y'an aiki ". Shamsiyya naji tana cewa"gaskiya ne adda Asabe ina bayanki hundred percent akan mai zaa ce ni ina zaune a gidan nan shekara da shekaru a gidan nan amma bayan parlourn qasa ban tab'a hawa na sama ba .ita kuma wannan baquwar daga zuwanta har ake mata komai ko a side na y'an aiki bata tab'a zuwa ba. Asabe cetayi tagyaran murya tace"ke shamsiyya baki San cewa da safe dazan gyara parlourn qasa ina tunanin baquwar nan baa parlourn qasa ta kwanaba, kuma fa na ga da safe Amal tare da hajiya qaramar suka tafi school. Dogon tsuka naji anja daga gefe juyawa yadda akai tsukar nayi ladi na kalla tana cewa"wa maiyasa Asabe kike biye wa shamsiyya yarinya qarama y'ar cikin ki kina aikata ba dai dai ba ."?

Akan mai zaku cutar da Amal ko wa na ji kuna cewa , karfa kumanta daga qauye muka zo garin nan matar gidan nan ita da Alhaji sun d'auke mu aiki basu mana qeta har xakka ana bamu a gidan nan a azumi kuwa haka ake raba mana kud'i fa , abamu buhun shinkafa da sugar mu raba wa y'an uwanmu na qauye abinci kuwa yanzu mun fi qarfinsa sai dai mu bawa wani akan wani banzan dalili naku zaku zo kuna cewa zaku illata baiwar Allah Ku miyasa kuka fi son kanku akan wasu ne. Baki shamsiyya ta murgud'a tana cewa"wai dan Allah miyasa baba ladi kike haka , miyasa baki son cigabanmu ke kullum baki da aiki sai waazi to fana gaya maki gaskiya wlh kinji nayi rantsuwa ta y'ay'an musulmai sai na had'a, wa yarinyar nan muna furcin da tunda aka haifeta baa tab'a had'a mata ba daga qarshe sai ta bar gidan ni nakoma matsayin da take dashi a gidan nan.

"Dariya baba ladi tayi tace"waye baisan halinku ba shamsiyya ko ki man ta time in da aka kawo new house maid , gidan kuka had'a mata sharri ta bar gidan to tabbas na rantse wannan baku isa kusa a koreta ba sai dai in zaku had'a muna furci naku Ku had'a dani.

fuu ta tashi ta bar wajen nima y'ar d'aukomaku rahoto sai da na tsorata .

A garin abuja kuwa a yau ne ranar dazamu koma kotu tun safe na hango mana barrister shuraim yana shiryawa kotun naga yanufa mutan e-ne ciki a cikin wannan kotun da qir nake iya hango mutanen da nasani , kotun ce naji tayi shiru alamace nace wa alqali ya buga gudumarsa kowa shiru yayi kamar ruwa ya cinyesu.

magana na farajin anayi kamar haka "da farko dai sunana barrister shuraim muhammad al'ameen ni ne barristern dake kare wacce ake qara yamai girma mai shari'a ina mai neman alfarmar da abani dama in nuna wata shaida danake da ita ta qarshe a cikin wannan kotu mai albarka ". kotu ta baka dama barrister.



sai mun had'u a page 8 dan jin yadda zata kaya zamuji cewa "menene burin masu aikin gidan alhaji al'ameen a kan amal

shin minene burin shamsiyya akan amal

zata sa a kore ta agidan ko baba ladi zata hana.



shin miyasa amal,take d'ari -d'ari da daddy.



daddy zai d'auki amal amatsayin y'arsa ko a a


shin micece hujjar barrister shuraim da yake da ita a kotu .



koma dai miye ku biyoni Siyamah a cikin wannan labarin mai suna barrister shiraim .

karku manta labarin barrister shuraim qir-qirerren labarine haka xalika idan wannan labarin yazo daidai da rayuwar wani to a yi haquri a kasi a ka samu .


wannan labarin yanzu aka fara shi tabbas yanzu aka fara domin akwai sarqaqiya had'e da munafurci , soyayya haquri duk acikin wannan labarin .

kudai ku biyo ni HAD Siyamah don jin yadda zata kaya .



karku manta

comment and share

domin gyara ko shawara sai a tuntub'eni a watsapp number na
08137873838



*🧑‍⚖️BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


manazarta writters association k'ungiya d'aya tamkar da dubu masu nazari, aiki ,da ilimi burin k'ungiyar akoda yaushe shine ta fad'akar kuma tana nishad'antar da masoyanta bata rubuta littafi dan nishad'i kawai aa sai dan a fa'i dantu da littafin had'e da nishad'i baki d'aya


_FREE BOOK_

page 8


Dinning muka qarasa kujerun dinning in muka jawo muka zauna amal ce tace "daddy good night "
daddy yace "good night my daugter how ave you"
"am fine daddy how was your work?"

"Alhamdulillah daugter" daddy yace.

Asiya ce tace " daddy barka da hutawa ya aiki ?"


daddy yace "Alhamdulillah auta nah " dariya mukayi gabad'ayanmu cikin farin ciki .


Asiya da amal naji sunce"ummi barka da gida ya aiki ya hutawa?"

lafiya lau alhamdulillah y'ay'an kirki .


Dinning in naji ya yi shiru sai qarar spoon nake ji daddy naji yace"wannan abinci haka waya dafa tuwon nan ?" sistu ce ta dafa asiya tace.

"masha allahu! daugter yau kina da kyauta ta daban a gidan nan" asiya ce taturo baki gaba tace " daddy nifa .?"

"banda ke ummi tace "
kuka naga asiya ta fara sai kace wata qaramar yarinya haquri daddy yabata yace itama zai bata kyautar.

mommy naji tace" nifa alhaji banason sakalta yarinyar nan da kake yi komai take so sai ka mata yarinya shekaranta 18 amma bata san ta girma ba ".?

to hajiya yanzu mekikeso ayi?


ummi tafara magana kawai kadaina sakalta y'ar nan alhaji komai take so sai kana mata sai kace itace yarinya .

"to hajiya waye yarinya yanzu a gaban mu in ba ita ba kinsan impossible narasa d'ana abin alfaharina da na mallaka a duniya , kuma yanzu autar nawa ma danake gani nake jin dad'i kice bazan sota ba."


ummi ce tace "yi haquri alhaji ba haka nake bufi ba amma kasan cewa ako da yaushe a nason mumini ya yarda da qaddararsa mai kyau ki marar kyau ,kuma ubangiji Allah subhanahu wata'ala yana gwada bayinsa masu tsoronsa dan yaga in ya d'aura musu jarrabawa zasu cinye ko ba zasu cinyeba , Alhaji kabi duniya a sannu fa , saboda ga ni a yanzu kana ganin ina kewar nawa a halin amma ban isa zuwa garesu ba , ummi take fad'an haka cikin kuka , shikuma d'ana ina masa addu'a aduk halin dayake ciki ina ji a jikina yana hannu mai kyau , Allah ka bayyanar mana da d'anmu ".

(Ameeen) mukace ni amal a raina nake cewa wato kowa a duniyar nan akwai jarrabawar da ubangiji ke d'aura masa wato jarrabawar wani ta fi tawani in dai banayi rashin fahimta ba a zancen ummi , to so take tace d'anta ya b'ata ko ba ya tare da ita , tabbas d'a na kowa ne , wannnan kenan shine dalilin dayasa suka riqe ni a matsayin y'ar da suka haifa tabbas rabuwa da iyaye akwai wahala , saboda har yanzu a raina inajin ciwon rabuwa da nawa iyayen amma ya na iya haka Allah ya rubuta kuma gashi Allah yasa ina hannu mai kyau , yadda ummi suka riqeni da amana Allah kasa nasu d'an yana hannu mai kyau na fad'a a zuciyata , hawaye yaba zuba a idona ".

ya salam naji ummi tace "my daugter what wrong with you ? what happen??".

murmushi nayi nace"ummi gida na tuna

Please Login or Register in order to submit comment