Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka fito sukai breakfast daga nan sukayi ma momy sallama suka wuce tabisu da fatan alkhairi ;

Suna fita ,suka ga amna tanajiransu su sauk'eta a school before su wuce sauk'eta sukayi sai suka wuce dr najeeb ne yasauk'e br shuraim a lawcourt saboda ayau suna da wata sharia .


Agarin kaduna kuwa abban amal yatura a turomasa k'aninsa baba adamu mimi ce ta dawo abba "yace yana zuwa "bayan adamu yashigo abba ya koromasa labarin, abin da ya faru tsakaninsa da yan kidnipping ,nannauyar ajiyar zuciya ya sauk'e sai yace yaya har fa million 30 ! 30 !! 30 !!! 30 fa yaya ,kace suna so a ina zamu samu kud'innan, abba ne yace dan Allah adamu karu famin asiri ko agun abokan aikinka kasamamin, murmushi yayi wanda bawanda yasan ma anarsa sai fa shi da allah dayahalicce shi.

Cewa yayi bakomai yaya akwai k'udin wani abokina da muke kasuwanci a maiduguri , yaban a jiya sai mu ara aciki kafin ya buk'aci kud'insa ,godiya sosai abba yamar sai ya tafi gida zuwansa keda wuya yace amarya albishir tace goro fari tas ,murmushi yayi yace daga gidan yaya nake yanzu haka burin mu na farko yacika sauran na biyu dole a yau na sanjamiki gida 🏣saboda farin ciki kinsan a halin yanzu target namu yacika amma bantab'a sanin



............... burin mu ns farko yacika saura na biyu inshà Allah damu da y'armu garin Zamu Bari mukuma Azare da Zama tare da wani a bokina naji labarin duk abin da na masa yanzu haka yayi k'udi yafi da saboda yanzu anaji dashi a garin Azare ; k'iran wannan mai kama da samudawan ,yayi akan ya fito da Amal bakin titi, gashinan zuwa d'aukanta yaje yad'auko ta a matsayin yabiya k'udi an bashi ita tana, ganin baba adamu duk wata k'iyayya data ke mar tanema tarasa d'an uwa mai dad'i da gudu tazo ta rungumeshi gida suka wuce,domin yau gidansu kamar gidan biki haka ya koma na farin cikin dawowar Amal gida ta shiga, baba adamu ya wuce wani waje y'an uwa kowa murnar ganinta yake yi yana rungumeta k'anwar mama "tace a barmin y'ata tahuta maza jekiyi wanka kici abinci ki huta "bayan tagama a binda aka umarceta tayi ,sai ga k'awarta Zarah tazo magana tamata akan Exams nasu na k'arshe a neco, a school ansa an mata dabatazo ba, saboda kowa yasan k'ok'arin ta yanzu sai dai jiran result ,to Allah ya taimakamana , muga result mai kyau inji Amal , Zarah "tace Bari nabarki kihuta zuwa gobe zan dawo inshà Allah."

Amal ce tarufe Ido tafad'a tunani a kan maganar dataji wanda sukayi kidnapping nata suna fad'a to wazai kaita ai katau meta musu miye had'insu da i yayenta ,koma mi ne ne suna da alak'a da wad'annan mutanen tasani amma aranta tayi alk'awarin bamai sanin wannan zance zata rok'i i yayenta akan suyi hak'uri in an musu maganar zuwanta ai katau subarta tabbas tananne zatayi bincike yadda yaka mata zatayi aikin kuma zata lallab'asu su sata a school daga k'arshe tayi bincike tana son tasamu babban matsayi in ta dawo gida saboda mahassada suji tsoron ta ,tunda har ai katau suke fatan mata zatayi amma zasu sha mamakinta , bacci ne yad'auki Amal sai magrib ,mama ta tasheta tsoro taji kar mama ta mata fad'a saboda takai magrib sai taga a kasin haka araina ni siyamah dake Lab'e inajinsu ina kuma Kawo muku rahoto nace Banda abin Amal keda Ake murnar dawowar ki wazai miki fad'a ,Amal tace mama yanaji gidan shiru? mama tace kowa yatafi gidan sa, tunda kindawo kowa yau yana cikin farin ciki ba iya, muka d'ai ba ,bayan sunyi sallah magrib su kayi karatu ,da lazuminsu sai su kayi sallah isha daganan abba da usman sunzo shigowa gida sai hannu Ake basu suna musabaha a namasa barka da dawowar Amal. yana haye hak'wara saboda farinci sai Godiya yake wa mutane ,gida yashigo suka hallara domin yin dinner sun gama suna cikin farin ciki Amal tana basu labarin yadda akasaceta agogo suka kalla karfe 11:00 abba yace kowa yatafi ya kwanta yaya usman yafara tashi yace Allah tashemu lafiya Amal da mimi suka tashi suka ce mama , abba , bissalam mama da abba suka baru a parlourn .

Agarin Abuja barrister shuraim yad'auki wayar sa lab'ewa nayi ajikin window domin d'auko muku rahoto , hello! Bro kana ina? daga d'aya b'angaren banji mai a kace ba kawai naga yace ohk ;sai ka k'araso wayar sa yad'auka had'e da rigarsu ta barrister ya fito harabar kotun gumi naga yana ta sharewa daga bisani motarsu tadanno kai bud'e masa motor yayi yashiga brother yadai na ganka haka, saidai godiyar Allah, bro wata sharia mukayi yau d'innan wai kasan mai yafaru kuwa yace aa sai ka fad'a ,gida suka iso horn yabuga gate man ya bude brother ina sauraranka to Bari na watsa ruwa nayi lunch ,sai na baka labarin haka kuwa akayi ,sungama cin abinci suna xaune gaba d'ayansu y'an gidan yafara cewa bro kanajiba yace eh "wata yarinya ce tana da wanda take so, iyayenta suka hanata aurensa suka bata zab'insu mijin da aka auradda ita a wani d'an uwansu matansa biyu itace ta uku bata sonsa shiyasa takasa zama dashi daga k'arshe ma ya rasu yanzu haka ita sauran matansa suka d'aura kisansa amma muna iya bincike alk'ali ya d'aga shari'a zuwa bayan wata biyu insha allahu ,Allah sarki su amnah sarkin kuka harta fara ,tashi barrister shuraim yayi yatafi lambu .......


*ina godiya gareku masu min fatan alkhairi a littafina harma da masu karantawa su wuce b a tare da like ko comment ba duk ina godiya👏👏👏👏*


*HAD SEEYAEMAH CE🌺*
my watsapp number 08137873838



*🧑‍⚖️BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*


_FREE BOOK_ *👨🏻‍🎓BARRISTER SHURAIM👨🏻‍🎓*

page 4

......... Barrister shuraim , ne ya tafi lambu zuwan sa lambu keda wuya yazauna bakomai kidamunsa a yanzu ba kamar wannan Sharia da suka yi, wato duk damuwar da kake ciki wani yafi ka yarinya k'arama da ita an d'aura ma ta laifin da bata yi ba yanzu mai yakamata yayi ne a ransa yake fad'an haka ,ashe amna ta bi yo shi lambun duk abin da yake fad'a ta na jin sa plastics chairs dake kusa tad'auki d'aya Zama tayi tace yayanmu a gaskiya wannan Sharia taku ta yau ta ban tausayi dan Allah yayanmu ta durk'usa har k'asa kar ka bari wannan yarinyar a d'aura ma ta laifin da bata yi ba please yaya, "calm down auta , inshà Allah ba abin da zai faru nima na damu sosai" 'yanzu yayanmu mai ka shirya a Kan hakan, "eh to kinsan hausawa ,nacewa da zafi-zafi ake dukan ice ,yanzu, fa na tashi naje na watsa ruwa sai na tafi kotun wajen yarinyar I na son jin wa su bayanai da ga gareta , to yaya Allah kiyaye adawo lafiya , please zan raka ka "to auta je ki shirya ni ma fa na shirya just around 30 minute kin shirya , in ba haka ba na tafi na barki "da gudu ta tafi momy ta ga ni a parlourn 'kekuma daga ina, "lambu gun yayanmu shirya wa zanyi zan raka shi unguwa" bata ji mai momy zata ce ba ta haye sama ta shirya around 20 minutes ta sauk'o, tana jiran sauk'o war yayan sai ga shi ya sauk'o momy ya sake gaida wa suka mata Sallama suka tafi ta bisu da addua Allah kiyaye ;

Shigarsu mota ke da wuya, bai zame a ko ina ba sai prison gidan horo kenan ,suna zuwa bai wani sha wahala ba saboda I.d card nasa da ya nuna ,yarinyar yasa aka fito masa da ita, amna ce"ta k'a re ta da kallo yarinya ce k'arama , bazata wuce 18 to 20 ba amma wahalar zaman gidan prison yamiyar ta kamar y'ar 35 , ta yi bak'i sosoi, Zama tayi suka gaisa da barrister daga bisani ya tambayeta sunanta 'cemasa tayi Nana a tak'aice dan da dukkan Alamo sun nuna ita miskila ce ' "cewa yayi kind'auki alk'awarin fad'a min gaskiya" kai ta jinjina masa , 'good ya fad'a, "Ina son kimin summary na rayuwarki anan ne zan gane ta ina zan taimakeki" kallonsa tayi had'e da murmushi" tace , sunana Nana kamar yadda na fad'a ma a baya ni da iyayena haifaffun garin adamawa ne nida iyayena da kuma yayuna , a lokacin da zaa min auren zumunci, ina da wanda nake so da na fad'a sai abbana yace baxan masa raini ba, kamar yadda yayarsa tayi ma iyayensu ban san yayar tasa ba, saboda ance tun ba'a yi auren mamana ba ta gudu baa kuma San inda take ba, sai ni auta , sai ni auta zan musu raini,hmmmm wanda nakeso wani d'an school namu ne amma iyayena suka hana ni aurensa suka aura min d'an uwansu , a ce warsu gwanda na auri d'an uwana, gida bai k'oshi ba baa ba na waje, saboda suna hango min gabana tayi kyau, na yi biyayya anyi auren an Kawo ni garin abuja matansa biyu yaran sa biyar a lokacin da ya aure ni bana Kula kowa a gidan, ko shi bana Kula wa bare kuma y'ay'ansa da matansa amma kullum abinda ake had'a min da ban a gidan bana ce wa komai tunda mijin da ake fad'a akansa ni ba sonsa nake ba" ' zaman gidan akwai munafurci a tsakanin matan gidan da yaran gidan bazan tab'a mantawa ba ranar wata Monday da safe Alhaji muka tashi muka ga ya mutu ! da aka je asibiti sun tabbatar mana da guba a ka sa masa ya ci ya mutu a ranar abinci na yaci da'a kazo bincike sai aka ce nice na kashe shi , hmmmmm bani da bakin magana tunda abinci na yaci kuma kowa yasan bana sonsa , bayan kwana uku da mutuwarsa matan sa suka kai k'arata aka rufeni a prison ,kayan prisoner nasa ka tun da ga lokacin suke cin karen su ba babbaka nikuma yau wata na shida anan ba abi mini hak'k'i na ba sai fa d'azu, iyayena basu san mai yake faruwa ba saboda su fulanin adamawa suna da kunya akan yaransu, kuka ta fashe da shi !sosai akan ko lauya ba ta da shi , "rarrashinta barrister yayi akan ta bashi address na gidan ta ,ya na son tattaunawa da matan mijinta ,ta bashi address na gidan had'e da cewa gidan Alhaji madaki yello , what! Amna ta Gaya da k'arfi "gidansu wata ya'r ajin mu ce fa hafsat" ' yaya cewa yayi bakomai abin ya ma zo mana da sauk'i tunda haka ne d'an sandan dake tsaye a wajen ne ya ce tund'azu lokacin Ku yayi labarin na ta ne yaban tausayi! shiyasa ban yi magana ba ,Sallama suka musu suka tafi , suna tafiya a mota yace zan saki wani aiki auta "name fa yaya , I naso hafsat ta za ma k'awarki kisan duk sirrin gidan su nabaki sati shida kikawo min labari mai dad'i ni kuma before two weeks yaci ka mukuma kotu ,zansan yadda akayi na nemo shaidu"bakomai yaya na d'au wannan promise d'in" gida suka koma suna shiga magrib yayi sallah sukayi suka zauna ana isha suka maida sallar isha amna da momy suka zauna zaman jiran dady da sauran yaran gidan su dawo a yi dinner , Sallamar su muka jiyo gaisawa aka sake yi daganan muka wuce dinning area domin yin dinner ;


A garin Kaduna kuwa baba adamu ne ya sallami yaransa wanda sukayi kidnapping na Amal daga nan ya d'auki wayarsa ya k'ira abokin sa na Azare akan nan da wata biyu zuwa uku zai dawo Azare da Zama a sama masa gida mai kyau wanda baxaifi 10 million ba , abokin sa "yace la bakomai ina da wani gida a federal low-cost sai ka zauna anan in kazo" Godiya sosai ya masa daga bisani ya kashe wayar ya na jan dogon tsuka ko tsukar mai yaja oho!

Todai bamu sani ba,

Bayan wani lokaci Zarah ta bi yo wa Amal su tafi islamiyya suna zuwa makaranta suka samu ya ustaz bai zo ba ,daba suka kafa suna ta hira abinsu sai wata acikin su tace neco fa ta fito d'azu , sai kunga murna a gurin Amal da Zarah baa magana, suna cewa ana tashi a school zasu koma gida su karb'i one thousand su Ciro, k'awarsu ne "tace sai kunje da registration number a baku ,suka ce ay ko mungode kinfi sarkin garin Ku a yau , Malam ne ya shigo suka watse bayan ya karb'i hadda ya musu k'ari ko wa nasa da ban sai time na sallah yayi bayan sunyi sallah anyi break sai aka dawo class ya ustaz ne ya fara musu nasiha akan "cewa suna yawan yin azkhar safe da yamma a duk inda suka tsinci Kansu suyi hak'uri da rayuwa wataran tana dad'i watar kuma akasin haka daga k'arshe kuma yace Ku yawai ta karanta wannan adduar acikin sujjada in kuna sallah;

A cikin suratul furqan aya ta 73
Allah subhanahu wata ala yake cewa wallazina yak'uluna saiku cire wannan Ku fa d'i tagaban Rabbana hablana min az wajina wa zurriyatina qurrata aa yunin waja Al na lil muttak'ina i ma ma.
Every sallah, every time you remember,recite this prayer as sincere as you could and as many times as possible, daga sanda mutum ya auri mata ko mijin da bai dace ba to ya shiga uku 😢 ,Balle kuma aka haifi fitsararrun yara, takaici a duniya ga k'ask'anci a lahira , Allah mana tsari🙏
Suka ce , Ameen gaba d'aya y'an class d'in ya ustaz ya kuma cewa ,Gaskiya addu'a ce mai tsadar gaske ,lalle kar muyi wasa da ita su Amal jikin su yayi sanyi suka ce inshà Allah ya ustaz , ya kuma cewa abokin Zama na nufin miji ga mace, mata ga namiji , y'ay'a sanyin idaniya kuwa na nufin y'ay'an da suka san ciwon kansu kuma suke k'ok'arin faranta ma iyayensu a ko da yau she .wannan Allah ya sanya ka shugaba ga bayinsa masu tsoron Allah , maana kazama shugaba acikin iyalenka walau mace walau namiji , to mai ya rage wa mutum a duniya da lahira in ya samu wannan ??? Gaba d'aya ajin suka amsa da babu kuma muna Godiya Malam da wannan addu'a inshà Allah daga yau Zamu fara ta kullum acikin sujjadarmu a sallah , Amal ce tace ya ustaz kace mu yawai ta karanta
RABBANA HABLANA MIN,AZ WAJINA WA ZURRIYATINA QURRATA AA YUNIN WAJA,Al NA LILMUTTA K'INA I MA MA .
I na son qarin haske a Kan hakan , Malam ne yace , Tab'a ce da ake karantawa dan rok'on Allah ya bawa bawansa abokin Zama mai nagarta da kuma zuriya abin Al fahari .
Fassarar shi ne, "ya ubangiji ka sanya a gare mu, abokan rayuwa da y'ay'a da za su kasance sanyin idaniya a gare mu .wannan kasan ya mu jagorori ga bayin ka masu tak'awa !"
Allah ya sa mu dace suka amsa da ameen ,lokacin tashi yayi kowa yatafi gida , a hanya Amal ke cewa zarah yau jiki na yayi sanyi tabbas ya ustaz ya fad'a mana kalama mai tsada insha allahu za muyi amfani da wannan addua , Amal ce ta iso gida sukayi sallama da zarah zuwa gobe insha allahu da safe zasu had'u.

by
HAD Siyamah 📝
Al k'alami yafi takobi🖊️

my watsapp number
08137873838 ,don gyara ko shawara k'ofa a bud'e take

share and
comments👏🏼


***️BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*


_FREE BOOK_

Page 5

Zarah ce ta zo gidan su amna zasu' fitar da result nasu, Amal ce tace" mama sai mun dawo " Allah kiyaye min ku a a na (ameen) suka ce suka wuce, tafiya suke suna hira har suka iso café Sallama suka yi suka shiga wajen, mutane ne da yawa a wajen , an mata mekukeso ? "Neco results muke so " 'ohk give one thousand , one thousand sukabayar aka fitar mu su;

Wow Masha Allah! alhamdulillah!! Zarah" nine credit fa alhamdulillah !!!
Zarah ma nine credit ne da ita ,murna sukayi an wajen suka musu congratulation Amal da Zarah "suka ce thanks " gida suka tafi suna nisha'i a hanya Amal"tace Zarah kinsan mezan karanta kuwa "Zarah tace aa "hmmmmm pharmacy doctor nake son Zama "Masha Allah a wata , namiki murna Allah bada sa'a "(ameen summa ameen) " nikuma Amal ina son Zama barrister Zarah" "hhhhhhhhhh waya ga barrister Zarah ,yi ta dariya my best friend kina sani nisha'i wallahi😀😀😀wai barrister Zarah, sunan ya bada citta hmmmmm kita dariya zaki Zama barrister ,"ke banson iskanci baza ma kimin fatan alkhairi ba sai kice nayi ta dariya😁 (AYITA DARIYA😀) "sorry my friend nayi mistake , tuba nake 🙏🙏🙏 aya feni "ohk don't worry ay dan kinsan bana iya fushi dake ne , shiyasa kikemin haka"

Zarah ce ta fara shiga gida sai amal ita ma tashiga gidansu , shigar ta keda wuya taji baba yana cewa" adamu bazan bar Amal ta tafi aikatau ba akan wani dalili , Ku I , inshà Allah zan yi aikin wahala tare da albashi na nabiya ku'in nan banta*a sanin cewa koda bayan raina bazaka kulamin*a*a na ba sai yau " ' yaya kayi ha*uri bansan ranka zai b'aci ba , Amal ce yashigo rungume babanta tayi tana cewa"inshà Allah baa bin da zai sameni baba kayi hak'iri kamin addua naje nayi aikin nan ni ajikina ina jin alkhairi ne zai sameni a ma ko ina aka kaini" murmushi babanta tayi zai yi magana yaji mama nacewa"addua kawai Amal take buk'ata nima tabbas ajikina ina jin Amal sai ta Zama wani abu a rayuwa amma Alhaji kayi hak'uri nasan mai kake ji a ranka kar ka manta ni fa uwa ce nafika sanin cewa Amal zata iya aikin nan ko bazata iya ba ;
Munsan tarbiyyar da muka bawa y'ar mu , ina da garantin cewa Amal bazata bamu kunya ba "baba ne yace tabbas ke mace- ce ta gari na kasa fahimtar hakan har Saida kika fahimtar dani Nagode -nagode macen aljanna, juyawa yayi yace wa "baba adamu bakomai Allah kaimu next week in " ansa kowa yayi da(ameen) baba adamu yayi Godiya ya tafi ;

A garin abuja kuwa hafsat ce ta Kawo wa babbar aminiyar ta ziyara wato amna , horn tayi mai gadi ya bud'e shiga cikin gidan tayi suka gaisa da mama dasu yaya Abdullah da khalifa , hira suke mama take cewa yasu mamanki "lafiya lau suke momy " ' Masha Allah, amna ce tace" tashi mu haura sama " haura sukayi suka fara hira , hafsat take cewa " banga fa jarumin nawa ba "amna tace'wakenan, harararta tayi🙄 tace" yaya shuraim mana, ohk tashi muje ya na lambu , murmushi tayi tace" kinsan yana gidan dan iskanci kika barni anan "😏hmmmmm so kike naje nace yaya shuraim k'awata tana sonka dan Allah kasota ko kuwa maikikeso nace masa;
Eh nafiso kice masa ina sonka , " lalle hafsat baki da hankali ni bazaki zubar mana da class naki ce kina son wani namijin batare da yace yana sonki ba "to y'ar ba in ciki , ay nasan lambun kimga tafiya ta zanje nace masa ina sonsa ♥'to Allah kiyaye matar yaya sai kin dawo , lambun ta nufa ta hango barrister shuraim a zaune yana duba wani file zuwa kusa dashi tayi tace " Amincin Allah tare da rahamarsa su tabbata a gareka masoyina♥kuma abin qauna ta , d'ago da kansa yayi domin ganin mai maganar yayi tunanin babynsa ta mafarki ce ke magana sai ya ga a akasin hakan , cigaba da kallon file na gaban sa yayi;

* A garin Kaduna kuwa Amal da Mimi ne suke ta aikin gida, mamansu kuma ta na girki , mama ce tace" Amal kinga yanzu saura kwana uku ki tafi , abin da zan fad'a maki shine kike yayi kanki a duk inda kike , banda shiga abin da bai shafeki ba, ki kuma kare mutuncin ki , karki bari kud'i ko wani Abun yasa kimanta da tarbiyyar damuka baki , ki yawaita yin sallah akan lokaci azkhar karki manta dashi , domin duk abin da wani zai maka na mugunta ,inkana yawan yin sallah akan lokaci azkhar to komai zaizo ma da sauk'i daga k'arshe ina son ki na hak'uri akan komai




*🧑‍⚖️BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*


_FREE BOOK_


page 6


. . . . . To yayanah yanzu fana Kira mutuniyar ka a waya naji ya ake ciki bata shigo ta min Sallama ba ta tafi "Dariya yayi "lafiya yayanah kake dariya haka" hmmmmmm "Wlh kawai hafsat k'awarkinnan kallon tubran nake mata har fa ta saki jiki dani kinsan yanzu haka harda karb'an numbern wayanah kai k'awarki da abin da dariya take wai har da cemin ......... Meta cema?cemin tayi masoyina!!! Ya sake tuntsirewa da dariya .


Murmushi nayi nace"yaya fana haura sama naqira ta a waya nasha labari duk abin da tace zan zo na Gaya ma" Zama naga yayanah ya gyara yana Danna laptop nashi yana bincike a ciki. Ji nayi yace" mekike leqowa amnah ta laptop ina ?" Naji yaya yana fad'a bakomai yaya nace masa .

Sama na haura na d'au wayanah contact ina na duba nasamu numbern hafsat .

Hafsat ce ta fita a gidan bata zarce a ko ina ba sai a gidan su . Gida ta shiga da Sallama ta na zabga murmushi . "Tsawa naji an daka min sai da na tsorata!!! Daga gidan uban wa kike ? Kai na d'ago domin ganin mai min tsawar nan . Bakowa nagani ba sai mamansu nawwal ce akaina wato kishiyar mamanah masifah naji tarufeni da shi ke ke ke ! Hafsat ba magana nakemiki ba . Daga gidan uban wa kike "

Raina ne ya b'aci nace mata" daga wajen tsohonki nake kinji ko baki ji ba nasake maimata miki " banga ma fad'ar haka ba naji ta d'aga hannu ta wanke ne da mari bata sauqe hannunta ba nima na d'aga nawa na rama.

"Ke kinkosan wa ce ce ni?

Bansani ba sai kin fad'a na gaya mata haka "to ki ki yayeni saboda uwar ki ba wata bace a guna bare ke" tsaki na buga nace mata "hmmmmmm abin da tsohuwa ta koyamiki kenan ni ta wa uwar bata koya min raini ba domin ance in ana so kaga ne mutumin kirki to daga gidanku ake gane waye kai " duka na zatayi nace mata"kul karki fara kinji big momy ."enough , never mind ko ajikina baidameni ba.


"Wayanah naji tana ringing picking nayi nace" hello qawata yagida ya jindad'i yakike zan shiga d'akinmu nake fad'an haka daga d'aya b'angaren naje ance haba matar babban yaya shine tafiya ba sallama , sorry wlh kinsan ina farin ciki ne shiyasa ban tsaya miki sallama ba

Please Login or Register in order to submit comment