Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rayuka
tayaya zan iya fuskantar wannan mahaukaciyar
macijiya?
.
ANAN muka kawo karshen littafin tarkon
mutuwa na bakwai 7
,
Zaku jini a littafi na takwas 8 nan bada dadewa ba.

TARKON MUTUWA
BOOK 8 PART A

Lokacin da nasmal yaji tambayar da hatyan
yayi masa ta cewa
ta yaya shikadai zai iya kare miluyoyin rayuka
kuma ta yaya zai iya fuskantar wannan
mahaukaciyar
macijiya
saiya kyalkyale da dariya
lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa y dubeshi
yace
yakai abokina inaso ka sani cewa bawai don kafi
kowa
karfi da iya yaki
ba ne akace kai zakayi wannan aikiba sai saboda
kaine yanzu kake kan kadaminka
ma'ana duk wani jarumi mai sa'a yanzu
abayamka yake
kuma duk wanda yaja dakai saiyaci kasa
taurari sun nuna hakan kuma masana tarihi
da masu binkice sun tabbatar da cewa kaine
jarumi na farko wanda yaja da sarki shamsal
a nahiyar ku yakai labari
her gaba da gaba kunyi dashi amma bai sami
nasara akan
ka ba
shin kana da wata tambayar ne wacce kake son
jin
amsarta yanzu?
lokacinda jarumi hatyan yaji wannan tambaya
sai yayi
shiru
yana dan tunani ya kasa cewa komai
daga can kuma saiya dago kansa ya dubi
nasmal yace
wacce irin jarrabawa zakuyi mini acan birnin
wacce indai na tsallaketa zan iya kareku daga
sharrin
wannan macijiya?
idan her zan haye jarrabawar nan na kareku
mai yasa bazanyi kokarin kare sauran kasashen
duniyaba
wadanda zasu fuskanci wannan matsala?
dajin wannan batu sai nasmal yayi murmushi
sannan
yace
komai mukaddarine babu wani shiri ko sihirin
da zai iya
sauya kaddara
hatyan ya gyada kai yace mai yasa kana
matsayin dan
sarki guda amma ka taho daji farauta akasa
haka
batareda ka hau dokiba
alhalin tafiyace ta tsawon kwanaki uku?
nasmal yace
mu agarin mu duk wanda yakeyin doguwar
tafiya akan
doki ragone
amfanin doki kawai shine ayi ado da biki dashi
yanzu sai muci gaba da tafiya domin mu isa can
gida
akan lokaci
saboda nasan jama'armu zasu kosa da
isowarmu
koda gama fadin hakan sai yarima nasmal ya
juya
ya nufi hanyar da zata kaishi her birnin nasu
da ganin haka sai sadirat ta rugo wajen hatyan
tace
waishin maganganun me kuke tayi ne?
ko kallon ta hatyan baiyiba ya juya ya nufi
nasmal
yana mai cewa zakiji komai idan muka isa can
birnin su
cikin hanzari itama tabi su hatyan sunata yin
sauri
domin su riski yarima nasmal
Acan birnin sarauniya badi'atul nauwara kuwa
lokacin da ta kadaita acikin turakarta tareda
tsohuwa ummulkhairi afarkon dare saita mike
tsaye
ta tube kayanta dake jikinta ta dubeta tace
saiki fara aikinki
dajin haka sai tsohuwa ummulkhairi tayi
murmushi tace
haba ranki ya dade shin kin mantane cewa
nan acikin turakarki ta barci muke ai saidai
mu karasa cikin kewaye ki shiga cikin bahon
wanka
tunda wanke jikinki za'ayi gaba daya
badi'atul nauwara tayi murmushi ba tareda tace
komaiba
saita shige izuwa cikin kewaye ummulkhairi na
biyeda ita
abaya
nantake badi'atul nauwara ta shige cikin bahon
wanka ta
zauna
itakuma ummulkhairi saita bude jakarta ta debo
wani
garin magani
ta zuba acikin ruwan bahon ta kama cuccuda
jikin
badi'atul nauwara
aikuwa sai bakin shunin ya dinga ya ribga fita
tamkar ana wanke kura da ruwa
nanda nan fatar jikin badi'atul nauwara tayi
kyau kamar
yadda take da
sannan taje ta caba ado na fada sannan sukaje
gaban
madubi
suka tsaya ummulkhairi na gyara mata adon
koda badi'atul nauwara ta karewa kanta kallo
taga tsananin kyawunta da allah ya bata kuma
ta tuno
da cewa wanda takeso yana can cikin hatsari
sai nantake idanunta suka ciko da kwalla har
hawaye ya
zubo mata
bata an karaba
koda ta fahimci cewar ummulkhairi taga zubar
hawayenta sai kunya ta kamata
don haka saita yunkura cikin sauri domin ta
goge
hawayent
sai ummulkhairi tayi farat tace
kada ki tsayarda wannan hawayen naki ya
shugabata
domin zubarsace kadai zai rage radadin dake
cikin
zuciyar ki
ki sani cewa uwar gidana ma mai girma anisa
kullum sai ta zubar da irin wannan hawayen
naki
kuma akan irin dalilinki ma'ana matsalarku
dayace
koda jin wannan batu sai badi'atul nauwara ta
juyo da
sauri ta kama kafadun ummulkhairi ta ruke da
karfi tace
waishin me kike nufi da wannan batu naki?
ummulkhairi tayi ajiyar zuciya sannan tace
keda kawarki anisa kunason saurayi daya
kuma dukkanku
baku taba son waniba faceshi
kowacce acikin ku zata iya sadaukar da soyayyar
ta ga
'yar uwarta
saboda aminci da kauna duk ku biyun kun boye
sonda
kukeyiwa hatyan
zangaya miki wani sirri guda daya bisa gaskiya
sirrin kuwa shine anisa ce ta fara son hatyan
tun kafin ki sanshi amma tunda suka rabu basu
sake
haduwaba sai
awannan karon da ya baro kasarsu
shikansa har gobe yana da burin sake haduwa
da ita
domin baiga fuskartaba awancan lokaci
dolene kusan hanyar da zakubi ku warware
wannan matsalar taku acikin sauki yadda
dayarku
ba zata rasa rayuwarta ba kokuma taci amanar
'yar
uwarta
lokacin da ummulkhairi tazo nan azancenta sai
hankankalin badi'atul nauwara ya dugunzuma
ainun ta
rasa abinda ke mata dadi
aduniya kuma saita kamu da tsananin mamaki
ta dubi
uummulkhairi tace
yanzu keda duk kinsan wadannan abubuwa
amma baki sanar daniba donme zakiyi mini
haka?
ummulkhairi ta numfasa tace idan her na sanar
dake
wannan al'amari tamkar naci amanar uwar
gijiyata ce
tunda itama ban sanar da ita abinda na saniba
nice na matsa akan saina biyoki zuwa nan
sannan zan
wanke miki wannan shuni
domin mu tattauna akan wannan matsala
ki sani cewa
uwargidana anisa tana tsafi kuma tsafi yana
tasiri akanta
ke kuwa bakya tsafi kuma tsafi baya tasiri
ajikinki
ninan da kike ganina na kasance gawurtacciayr
matsafiya
don haka nasan abubuwa da yawa ayanzu haka
babban makiyin masoyinku wato sarki shamsal
yana
turawa su hatyan
mugayen masifun da zasu hallakar dasu
da farko
ya tura musu sihirtattun zakuna da kadoji sun
tsallake
sharrinsu
yanzu kuma zai tura musu da dabbar da tafi
dukkanin
dabbobin duniya bala'i da hadari
wacce ake kira da uwar macizai
kodajin wannan batu sai idanun badi'atul
nauwara suka
zazzaro
kuma hankalinta ya dugunzuma ainun fiye da
koyaushe
ta dubi uummulkhairi tace
tabbas na sami labarin uwar macizai awajen
mahifina
ya gaya mini cewa babu wani matsafi da zai iya
taso uwar
macizai
daga barcin da takeyi face wani boka guda daya
kuma bokan yafi shekara dari da hamsin da
mutuwa
tayaya yanzu zakice sarki shamsal zai taso ta?
ummulkhairi tayi ajiyar zuciya tace ba sarki
shamsal bane
zai taso taba
bokansa ne daizur kuma yakasance jika ga
wancan bokan
daya mutu
na tamanin da takwas kuma ya gaji duk wani
sihirin tsafi
daya bari
tunda mahaifinki ya baki labarin uwar macizai
kinsan duk irin bala'in da zata haifar aduniya
idan ta
bayyana
manyan bokayen duniya sun gano cewa mutum
dayane
zai iya kashe wannan macijiya
bokayen dake nahiyar bakaken fata sunyi imani
cewa
jarumi hatyan ne zai iya kashe wannan macijiya
amma mu anamu binkicen na nahiyar fararen
fata
munyi imani babu wanda zai iya kashe wannan
macijiya
face jarumin da baya tsafi kuma tsafi baya tasiri
jikinsa
sannan kuma dolene ya kasance ma'abocin wani
sabon
addini wanda ake kira musulunci
kaf nahiyar bakaken fata babu wani jarumi da
baya tsafi
kuma tsafi baya tasiri ijikinsa
awannan nahiya tamu kuma kece kadai jarumar
da take
da wannan baiwa
amma kuma baki kasance ma'abociyar wannan
sabon
addini ba
shin kinsan wannan addini wanda ake kira
musulunci?
kodajin wannan tambaya sai sarauniya badi'atul
nauwara
tayi shiru
tana tunani izuwa wasu 'yan dakiku sannan tayi
farat tace
mahaifina ya bani labarin wannan addini kuma
ya bar mini wani littafi wanda yake dauke da
cikakken
bayani akan wannan addini da yadda ake
shigarsa
kodajin wannan batu sai farinciki ya turnuke
ummulkhairi
tace ya zama wajibi ki shigeshi idan har kinason
ki ceto
rayuwar masoyinki
kuma ki ceto dubunnan ruyukan dake wannan
nahiyar
tamu da kuma nahiyar bakaken fata
da zarar kin gama karanta wannan littafi gamida
shiga
cikinsa
saikiyi shiri kibisu jarumi hatyan izuwa wannan
birni
da suka nufa na bakaken fatav domin acan ne
macijiyar
zata fito ta cikin teku
idan ta gama dasu jarumi hatyan da wannan
birni zata
dawo
ta rushe duk kasashen dake wannan nahiya
hatta birnin sarki shamsal
kuwa domin shikansa boka daizur bai isa ya iya
sarrafa
macijiyarba ya shugabata idan baki hanzarta yin
abindana umarceki ba kawarki anisa da
masoyinki hatyan
zasu rasa rayuwar su
kafin ummulkhairi ta ta gama rufe bakinta tuni
sarauniya
badi'atul nauwara
ta falfala da gudu izuwa cikin daki
sai takama bude buden akwatunan da aka tara
aciki
wadanda sunfi guda dubu ta rinka binkice su
daya bayan
daya
A can birnin sarauniya anisa kuwa lokacin da....
TARKON MUTUWA
BOOK 8 PART B

A can birnin sarauniya anisa kuwa lokacinda
sarki
shamsal ya baiwa boka daizur umarnin
taso uwar macizai da gaggawa sai boka daizur
ya fiddo madubin tsafinsa ya ajiyeshi agabansa
ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi
sudai wadannan kalmomicguda dari ba uku ne
kuma
boka daizur na gama karanta sune uwar macizai
zata
farka daga barcin da take
koda boka daizur yazo kan kalma ta casa'in da
biyar
sai kawai sukaga an banko kofar dakin da suke
ciki
afusace cikin tsananin fushi sarki shamsal ya
mike tsaye
yana mai zare takobinsa
kawai saiyaga sarauniya anisa ta shigo tareda
dakarunta
na yaki kimanin su dari uku
kowannensu ya dana kibiya akan baka sun saita
sarki
shamsal da boka daizur
afusace anisa ta dubi sarki shamsal cikin daga
murya tace
saboda kawai ka hallaka mutum biyu kacal
zaka fito da abin da zai iya hallaka duniyar gaba
daya
wannan wanne irin rashin imani ne hade da son
zuciya
to kasani cewa idan kuka ci gaba da kokarin
aiwatar da
wannan nufi naku
kaida bokan nan naka kibiyoyi dari ukune zasu
nutse
ajikinku
yanzu alhakin kasheku ba ahannuna yakeba
kuma ka sani cewa ba wai tsoronka nakejiba
tundaga farkon zuwanka amma ka sani cewa
kazo gabar
da dole sai nayi kokarin dakatar dakai
sa'adda sarauniya anisa tazo nan azancenta sai
sarki
shamsal ya turbune fuskarsa yace
yake wannan karamar karuwa vkiyi sani cewa
ni murucin kan dutse ne ban fitoba saidana
shirya
tayaya kike tunanin cewa zaki iya hanamu
aiwatar da
wannan babban aiki to ga fili ga mai doki sai mu
zuba mu
gani
maza bisa kanki
maza kisa dakarunki su harbemu idan her
kibiyoyin naki
zasu iya cutar damu
kafin sarki shamsal ya gama rufe bakinsa tuni
anisa ta
baiwa dakarun nata umarnin suyi harbi
koda kibiyoyin suka fito daga cikin baka sai suka
kame
asama suka kama da wuta gaba dayansu suka
kone
kurmus
suka zube kasa amatsayin toka
faruwar haka keda wuya sai sarki shamsal ya
mike tsaye
yana mai kyalkyalewa da mahaukaciyar dariya
sannan
yace
Yanzu kuma me zaki iyayi?
shin zakiyi amfani da karfin sihirinkine wanda
yafi namu?
kai boka daizur maza ka karasa wannan aiki
nikuma ka barni da wannan sarauniya naga iya
gudun
ruwanta
nasan kin gama da hadimaina da suke waje
amma ki sani
inzaki hada gaba daya dakarunki su zo su hadu
anan basu
isa su tsayarda muba
her boka daizur ya budi baki zaici gaba da
karanto
wadannan dalasiman tsafi sai sarauniya anisa ta
daka
masa tsawa ya tsuke bakinsa sannan ta dubi
sarki
shamsal afusace tace
tun daga kuruciyata zuwa girmana nake tanadi
akanka
domin tun zamanin iyaye da kakanni
masarautarku suke
kuntatawa
masarautun da suke wannan nahiya tamu ka
sani cewa
dan hakkin daka raina shike tsone maka ido
tabbas ka fini
shekaru
kafini karfin damtse amma baka fini iya yaki da
tsafiba
kawai na boye tawa baiwarne amma yanzu zan
nunata
idan ka kasheni sai kuci gaba da aiwatar da
nufinku
idan kuma nice na kasheka shikenan na kawo
karshen
mulkin zaluncinku awannan nahiya
anisa na gama fadin haka saita cire rigar da
take jikinta
mai kama da alkyabba tayi wurgi da ita saigata
cikin
shigar yaki
wadansu tufafine ajikinta na bakar fata kuma
matsatstsu
takalmin kafarta ma na bakar fatane dogo iya
kauri mai
madauri
wata zabgegiyar takobice agadon bayanta
nantake sarauniya anisa ta dubi dakarunta tayi
musu
wata inkiya
nantake suka fice daga dakin suka turo kofa
suka rufe ta
waje harda sa makulli
anisa ta dubi sarki shamsal cikin alamun
tsananin kiyayya
tace
na sallama rayuwata don ceton masoyina
hatyan
da 'yar uwarsa sadirat da kuma miliyoyin
rayukan
da kakeson salwantarwa ka sani cewa
nida sarauniya badi'atul nauwara ne muka
taimakawa
hatyan ya tsira daka dukkanin harinka
acan teku inda kuka rutsashi kana shirin sare
masa hannu
badi'atul nauwara ce tazo ta naushi bayanka
kafin ka juya ta daukeshi daga wajen
anan garin kuma nice na batarda duk wata
shaida
alhalin yana cikin wannan gidan sarautar aboye
abinda yasa kuka kasa gano hakan da karfin
sihirinku
shine
sarauniya badi'atul nauwara tama cikin garin
nan kuma
kasan cewa
tsafi baya tasiri indai tana wuri
koda gama fadin haka sai anisa ta gyara
tsayuwarta ta
zare takobinta sannan ta gyara rukon
garkuwarta
awannan lokaci fuskar sarki shamsal ta fara
gyatsine
saboda tsananin fusata don haka sai shima ya
zare tasa
takobin cikin kakkausar murya yace
na rantae da girman kabarin ubana sainayi miki
kisan
wulakanci
tunda dasa hannunki acikin zagon kasan da
akayimini
kuma koda annobar uwar macizai bata hallaka
kawarkiba
sai na bita har birninta nayi mata irin kisan da
zanyi miki
kodajin wannan batu sai anisa ta bushe da.
dariya tace
yanzu nan kai aganinka zaka tsira da rayuwarka
ne
her ka cika wannan buri da kake furucinsa?
idan baka saniba ka sani domin na fuskanci
kana da
jahilci
akan sanin tarihin duniya her kullum kuma har
abada
mulki da zalunci baya dorewa
kafin kai anyi manyan sarakuna da suka fika
karfin
damtse
dana sihiri da karfin mulki da zalunci amma
akaron
banza suka dinga gushewa
kafin anisa ta gama rufe bakinta
tuni sarki shamsal ya dako tsalle daga inda yake
tsaye
tamkar daga kan sifirin yake
ya kawowa sarauniya anisa mugun sara
akafadarta
da nufin ta tsargeshi gida biyu
ba zato ba tsammani sai yaga ta kare saran
ba tareda karfin saran yasa ta fadi kasaba kafin
ya kawo
mata wani harin tuni
ta doki kirjinsa da gwuiwar kafarta ta hagu,
saboda karfin dukan saida yayi baya taga taga
amma ya tsaya cak ya sake taso mata suka sake
kacamewa da azababben yaki
mai matukar ban tsoro da ban al'ajabi
shidai sarki shamsal yana yakin ne da dukkan
karfinsa
cikin kunar rai domin zuciyarsa tafarfasa take
kamar zata
kone
yana mai yiwa kansa tambaya cikin zuciyarasa
yana mai
cewa
yanzu dama akwai macen da zata iya tarata da
yaki
awannan nahiya amma ban saniba?
tayaya wannan yarinya t iya yaki haka kuma ta
kasance
mai bakin zafin nama irin wannan
gamida tsagwaron karfin damtse?
shikuwa daizur jikinsa ne ya kama kyarma
saboda
tsananin tsoro
domin baiyi zaton anisa ta kai wannan
matsayiba
kuma duk abinkicensa na tsafi bai taba ganin
sirrintaba
saida sarki shamsal da anisa suka shafe sa'a
guda suna
wannan gumurzu
acikin wannan daki
ya zamana cewa sun lallata duk wasu kujeru da
kayan
alatu da suke cikin dakin
amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar
jikin
dayaba
shikuwa boka daizur dayaga masifar tayi yawa
saiya
rikide
ya zama dan mitsitsi tamkar kuda
ya makale acan saman rufin dakin yaci gaba da
kallon
wannan gumurzu
LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMENT
TARKON MUTUWA
PART 8 C
lokacin da sarki shamsal yaga sun shafe tsawon
sa'a guda suna kaiwa juna sara da. suka cikin
tsananin zafin nama juriya da bajinta amma
babu wata nasara kuma anisa bata gaji ba
saiya ja da baya ya gyara tsayuwarsa yana
tunanin salon fada da zai sake
dashi da Ita awannan lokaci duk hannayensu
radadi suke
saboda gajiyar ruke
kotar takobi kuma duk takubban nasu sun
daauki zafi
sosai
kamar acikin wuta aka gasa su
koda anisa taga sarki shamsal ya danja da baya
sai
tayi masa dan murmushi na yarda da kanta tace
nasan kayi mamaki yadda nake da kwarewa
da juriya irin taka ba komai ya jawo hakanba
face nayi binkice akanka sosai kuma na samu
duk irin
horon daka samu
sarki shamsal ya maidawa anisa martanin
murmushi
yace
ai abu daya zakiyi ki burgeni me zai hana mu
zubar
da makaman mu mu gwada 'yar kashi?
koda jin wannan batu
sai anisa ta sake bushewa da dariya tace
ashe bani d hankali kenan
idan her baka manta ba ai tunda farko na gaya
maka ccewa kafini karfin damtse to sabodame
zanyi
gangancin jarraba nawa akan naka?
ka sani cewa indai akwai takobi ahannuna
karfin damtsenka ba zaiyi ta siri akaina ba
amma idan kana shakkar hakan
to ka sauya salon yakin naka k gani zaka sha
mamaki
yau sai na rushe dukkan burinka na duniya
kuma cikin biyu dolene daya ya faru ko ni na
kasheka
ko kuma kai ka kashe ni ko kuma muyi ragas
sa'adda sarauniya anisa tazo nan azancenta sai
sarki shamsal ya bushe da dariya sannan yace
ke karamar karuwa ki sani cewa duk wanda
ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, ke sa'ar
dana ce don
haka
na fiki wayo kuma nafiki sanin tuggun yaki
na fiki shan gwagwarmayar duniya kuma na fiki
sa'a
yau shekara ta arba'in da bakwai kenan ina kan
sharafina
duk abinda nasa agaba na sainaga bayansa
don haka ke baki isa ki rushe mini burinaba
caraf saii anisa ta tari numfashinsa tace
wannan shine babban kuskurenka arayuwa
domin kana mantawa cewa dolene mai laya
ya kiyayi mai zamani, ka sani cewa sarki goma
zamani
goma
mu 'ya'yan yanzu kwakwalwarmu tafi taku.
TARKON MUTUWA
PART 8 D

mu 'ya'yan yanzu kwakwalwarmu tafi taku
dogon nazari
gamida
hangen nasa da kuma basirar binciko abubuwan
cigaba
wannan dogon surutun da mukeyi bashida
amfanin
komai face bata mana lokaci kawai mu gani
akasa
ni burina ka sauya salon yakin naga yadda ta
kaya
kafin sarki shamsal ya bude baki yace wani abu
tuni anisa ta dako tsalle daga inda take ta kawo
masa sara
,naushi, da bugu da hannayenta da kafafunta
duk alokaci guda cikin bakin zafin nama sarki
shamsal
yayi kokarin kare duk hare harenta amma duk
da haka
saida
ta sami nasarar yankansa akan kwanjinsa na
hannun
dama kuma ta doki kirjinsa yaje ya manne ajikin
garu
kawai sai gani tayi kamar an cilloshi daga cikin
baka
kafin tayi wani yunkuri shima y rama abinda
tayi masa ya yanketa akan cinyar hannunta na
dama
kuma ya daki kirjinta ta fadi kasa wanwar
saboda karfin
dukan
nasa ya ninka nata harsaida ta furzar da jini
daga bakinta
tana kwance akasa sai sarki shamsal ya dako
tsalle
ya kawo mata suka aciki da takobinsa
anisa ta mirgina can gefe guda ta kaucewa
sukar takobin
ta doki kasa
ta lume kafinya zaro takobin ta mike tsaye
zumbur
sun sake kacamewa da azababben yaki saida
suka sake
shafe wata sa'a gudar suna wannan dauki ba
dadin
ya zamana cewa kowannensu ya sake samun
nasarar
yankar abokin
gwaminsa sau biyu
wato dai kowannensu anyi masa rauni uku
amma saboda
azabar naci da juriya
basu fasa ci gaba da artabun ba
koda sarki shamsal ya fahimci cewar bashi da
tabbacin
samun nasara
akan sarauniya anisa saiya daga kansa sama ya
dubi boka
daizur
wanda ya zama dan mitsitsi ya daka masa
tsawa yace
wai shin me kake jirane ai tunda na tare maka
wannan
hatsabibiyar
maza ka karasa aikinka
koda jin haka sai boka daizur yai wuf ya fiddo
madubin tsafinsa yaci gaba da karanta
wadannan
dalasiman tsafi daga inda ya tsaya
al'amarin daya dugunzuma hankankalin
sarauniya anisa
kenan
ta kara zage damtse wajen kokarin kaiwa boka
daizur hari
domin ta hallaka shi amma sai sarki shamsal
ya tareta suka cigaba da bakin artabu mai
matukar ban
tsoro
wanda komai zai iya faruwa
kafin cikar rabin sa'a boka daizur ya gama
karance
wadannan dalasiman tsafi
faruwar hakan keda wuya sai uwar macizai
wacce ke kwance akan karkashin teku tana barci
na tsawon shekaru dari da arba'in ta yunkura
ta taso izuwa saman tekun, yunkurin da tayine
yasa tekun tayi girgiza ta kama ambaliya
ashe wannan tekun mahadace
ta dukkan tekunan duniya
hakan ne ya haifar da girgizar kasa ako'ina
acikin duniya
ya zamana cewa tekun ta kama ambaliya ruwa
na shiga gari yana cinye mutane da gidaje
babu inda ba'aga wannan tashin hankalinba
don haka anan birnin sarauniya anisa tana cikin
yin
wannan yakida sarki sshamsal ne tekun ta balle
ta fado cikin gari gaba daya gidan sarautar
saidaya ruguje
kuma ya nutse acikin ruwa, mutane da yawa
suka hallaka wasu suka jirkita sarki shamsal da
boka
daizur
kuwa akan wani akan wani katako suka dafe
ruwa ya tafi dasu bisa taimakon karfin sihirin
tsafinsu
suka tsira
itama sarauniya anisa tsafi tayi t kira wani
sihirtaccen
tsuntsunta
ta dira akansa ta kama shawagi asararin
samaniya
tana ganin irin mummunar barnar da ruwa yayi
mata
wanda ya haddasa asarar dubunnan ruyuka da
dukiya
mai yawan gaske
saboda bakin ciki da takaici nantake sarauniya
anisa
ta fara zubar da hawaye ,bisa dole ta sauko
kasa
izuwa cikin ruwa ta fara kokarin ceton
rayukansu
Al'amarin su jarumi hatyan kuwa ya rage saura
baifi
sa'a daya da rabi su isa birnin su yarima
nasmal ba
kawai sai suka jiyo rurin uwar macizai adaidai
lokacin da
ta
yunkura ta taso sama daga cikin tekun
nantake kasa ta kama girgiza
babu shiri su hatyan suka ruke hannayensu
don kada su fadi kafin su nemi matsera
kasa ta fara tsatstsagewa
daga bayansu tana ruftawa kasa tana kusantata
babu shiri duk su ukun suka falfala da
azababben gudu
har hatyan yayi dan nisa saiya tuna cewa ai 'yar
uwarsa
sadirat
bata da karfin gudu irin nasa don haka saiya
waigo
da baya a firgice yana mai tsayawa
hatyan ya kurma uban ihu sakamakon hango
abindake
shirin faruwa
kasa ce ta zabtare adaidai inda sadirat take
ta tafi izuwa kasa zata nutse
ba zato ba tsammani sai yaga yarima nasmal ya
dako
tsalle
izuwa gareta ya cafo hannunta
kuma nantake ya rikide ya zama katon tsuntsu
yayi sama
da ita
ya juya da baya ya tunkaro hatyan
dukda tsananin gudu irin na hatyan sai gashi
zaizayar kasa na neman cimmasa domin tazarar
dake tsakaninsu bata wuce taku biyuba
saura taku daya kacal kasar ta cimmasa ne
tsuntsu
nasmal
ya sureshi yayi sama dashi sai gashi su biyu
shida 'yar
uwarsa
suna reto ajikin kafafun tsuntsun
adaidai wannan lokacine suka iso birninsu
yarima nasmal
tun daga sama sukaga irin mummunar barnar
da girgizar
kasa
ta haifar musu sai hankalinsu ya dugunzuma
saboda fiye da rabin gidajen birnin sun lume
acikin ruwa
ga gawarwaki nan na mutane da dabbobi suna
yawo akan
ruwa
har asannan kuma kasa bata daina girgizaba
lokaci guda kuma sai komai ya tsaya cak!
aka daina girgizar kasar
ashe ba komai ya janyo hakanba face uwar
macizai ce
ta tsaya cak!
abakin gabar teku baya ta gama fitowa da
dukkannin
jikinta
gaba daya kawai saita daga kanta sama ne
ta dubi gabas da yamma kudu da arewa tana
shakar
numfashi
da kamshi sirrin yin haka kuwa shine tanaso
ta jiyo inda kamshin hatyan da 'yar uwarsa
sadirat yake
ta kai farmaki wajen ashe abinda ya hana ta jiyo
kamshin
nasu
shine girman fuka fukan tsuntsun
tsuntsun yaci gaba da tafiya dasu acikin sama
harsaida suka iso tsakiyar gidan sarautar birnin
wanda kadan daga cikinsa ne ya ruguje kuma
tuni
a lokacin ma'aikata nata kokarin gyara gamida
kwashe.
ruwan dayayi ambaliya acikinsa
sarki da mukarrabansa na kai kawo acikin gidan
sarautar
suna kallon masifar da ta faru kawai sai sukaji
wata iska
mai karfi acan sama
koda suka daga kawunansu sama sukaga katon
tsuntsu
dauke da mutane biyu suna saukowa kasa
sai suka kamu da tsananin farinciki
nantake garin ya kaure da kade kade gamida
bushe bushe da kuma wake wake
wani gagarumin buki ake kamar ma an manta
da wannan
masifa data faru
tsuntsun na sauke su hatyan da sadirat sai
shima ya rikide ya zama nasmal ya rungume shi
yana mai cewa lale marhaban da dana babban
gwarzo
tabbas saura kiris mu fita daga muguwar
fargabar
da muke ciki tundaga gashi ka kawo mana
wanda muke sa ran zai kare mu daga wannan
masifa
koda gama fadin hakan sai sarkin ya janye
jikinsa daga
cikin na nasmal
yaje ga hatyan ya rike masa hannu suka gaisa
yace
marhaban da jarumi hatyan daga makeri satyan
kuma almajirin sarkin mafarauta na birnin
bindal
dukda cewa hatyan ya san al'amarin tsafi sai da
yayi mamakin yadda wannan sarki yasan komai
haka dangane dashi
〇 sarki ya cire hannunsa daga cikin na hatyan
ya mikawa sadirat itama suka gaisa ya dubeta
cikin murmushi yace
sannu da gwagwarmaya 'yata hakika kin
fuskanci
tsananin fargaba acikin wannan tafiya amma
kiyi hakuri
komai ya kusan zuwa karshe da izinin abin
bautarmu
da yake sadirat bataji yarensa ba bata san me
yafadaba
saitayi kasake tana kallonsa, al'amarin daya sa
dariya ta kwacewa hatyan kenan ya dubeta yace
barka da zuwa yayi miki gamida jajen wahalar
da
mukasha
kodajin haka saita rissina ga sarki tana mai nuna
alamar godiya awannan lokaci ne mahaifiyar
nasmal ta
ratso ta tsakiyar taron ta rugo gareshi
suka rungume juna tana mai murnar
dawowarsa
mahaifiyar tasa ta juyo ta kurawa sadirat hannu
sannan ta dubi nasmal tayi masa murmushi
gamida inkiya wacce tasa sarki da dukkan
jama'ar dake
wajen
banda hatyan da sadirat suka bushe da dariya
nantake sadirat taji ajikinta cewa lallai akwai
wani abu
akasa
wanda ya shafi dan sarki kuma ya shafeta
tunda saida aka kalleta kuma akayi inkiyar
sannan akayi wannan dariya
adaidai wannan lokaci ne babban boka na birnin
ya ratso cikin taron yaransa biyu na biye dashi
bokan ya kasance dogon mutum mai kirar
samudawa
kuma mai suffar jarumai
indai a fagen jarumtakane birnin kaf
yarima nasmal ne tsaransa basu taba jarraba
jarumtakar junaba amma kowa na shakkar kowa
ana kiran wannan boka da suna aimar
aimar ya gaji bokancin birnin ne awajen ubansa
kuma fiyeda shekaru dari biyu baya zuriyarsuce
ke ruke
da wannan mukamin
aimar ya kasance matashi kamar yarima nasmal
kuma mutum ne mai tsananin kishin kasarsa
da jama'arsa wani abun mamaki shine da
yarima nasmal
da boka aiman basa ga maciji
amma kuma basu taba zage zage ba ko fada
saidai kace na ce kuma duk masifar da zata
sami daya
dayan bazai taimaka masaba
atakaice dai akwai tsama q tsakaninsu wannan
tsama ta
samo asaline
tuun suna yara 'yan kimanin shekaru tara tara
abindaya faru shine wata rana sa'adda suka
shiga daji
farauta
sai suka hango wata barewa acan nesa dasu
kadan
nantake sukayi gasar cewa babu wanda zai
harbi barewar
da kibiya saidai suyi gasar gudu
wanda duk y kurewa barewar gudu ya kamata
ta zama
tasa
agaban sarki da mahaifin aimar aka kulla
wannan gasa
nantake kuwa aimar da yarima nasmal suka bi
barewar
da gudun tsiya
izuwa cikin jeji tun su sarki na hangosu harsai
da suka
bace musu da gani
shidai karfin gudu baiwane kawai ba tsafi bane
ko tsagwaron kwarewa yarima nasmal yafi
aimar karfin
gudu da juriyar daukarr lokaci
amma shi aimar din maguji ne na gaske don
haka
da farko sa'adda suka fara tseren gudun sai da
suka shafe
rabin sa'a suna gudun kafada da kafada aka
rasa wanda
zai tserewa wani
idan nasmal yaga aimar ya dan bashi tazara
sai shima ya dage ya riskeshi duk wannan
abindake
faruwa tazarar su da barewar batafi kamu goma
ba
koda suka sake shafe rabin sa'ar sai aimar ya
fara sarewa
saboda gajiya aikuwa sai nasmal ya bashi
tazarar tsawon
taku biyar
kawai sai gani yayi baifi saura taku biyuba
tsakanin
nasmal da wannan barewar
aikuwa sai aimar yasa kafa ya tade nasmal ya
fadi kasa
yanaji yana gani wannan barewar ta tsere cikin
tsananin
fushi
nasmal ya mike tsaye ya zare takobinsa yayi kan
aimar
kawai sai aimar ya tsaya cak yana kallonsa yana
murmushin mugunta
koda nasmal yazo dafda aimar ya daga takobin
sa sama
sai ya kasa sara masa
aimar ya tuntsure da dariya yace
maza ka kashe magajin dirkan wannan birnin ai
kasan
hukuncin kisane
koda jin wannan batu sai jikin nasmal yayi
TARKON MUTUWA
PART 8 2D

n ai
kasan
hukuncin kisane
koda jin wannan batu sai jikin nasmal yayi sanyi
ya sauke hannunsa kasa kuma ya maida
takobinsa
ya dubeshi afusace yace
daga yau nida kai babu abota babu taimako
kuma babu
yarda her abada
Lokacinda boka aimar ya iso gaban ssarki shima
da
yaransa guda biyu
sai suka rissina suka gaida sarki sannan aimar
ya durkusa
yace
ya shugabana munyi babban sa'a da nasmal ya
rikide ya
koma tsuntsu
alokacin daya daukosu hatyan da 'yar uwarsa
domin girman fuka fuknsane ya hana uwar
macizai
jin kamshin su hatyan har suka iso nan gidan
sarautar
amma da zarar daya daga cikinsu ya fita daga
nan zataji
kamshin sa ta taso
idan kuwa ta taso komai da kowa saiya hallaka
yanzu muna da damar da zamu gabatar da
wannan gasa
domin mu gani ko jarumi hatyan ne bakon
jarumin da
zai iya kashe wannan uwar macizan
koda boka aimar yazo nan azancensa sai kan
hatyan ya
daure yace
a ransa au har a yanzunma babu tabbacin cewa
nine zan
iya kashe wannan macijiya harsai an gudanar
da wata
gasa
aikuwa indai hakanne to tsafi ya zama shirmen
banza
tunda baya iya tabbatar da abu guda daya
lokacin da sarki shamsal yaji batun boka aimar
sai yayi
murmushi yace
wannan yayi kyau yanzu tunda day uwar ba zata
motsa ba face daya daga cikin wadannan baki
ya fita
daga cikin nan muna da dan kwanciyar hankali
saboda haka sai bakin namu suje suci abinci
su huta inyaso saida yamma mu gabatar da
wannan gasa
gama fadin haka keda wuya sai yarima nasmal
ya kama
hannun
hatyan ya jasu domin su tafi makwancinsu
amma sai aimar yayi wuf ya sha gaban sadirat
ya dubeta cikin murmushi kuma ya bude baki
cikin
yarenta yace
lale marhaban da zinariya abar kyalkyali wacce
na dade ina jiran ganin haskenta ya sadirat
'yaga makeri
satyan
Cikin tsananin mamaki sadirat ta bude baki
da nufin ta tambayi aimar yadda akayi ya santa
kuma ya iya yarenta ,amma sai nasmal ya shiga
tsakaninsu ya dubeshi yace
baka da ikon yin magana da wadannan baki
nawa face da
izini na
Wannan yasa nima na tsaya anan.
wannan ci gaban 8 D ne shiyasa nasa 2D.
Part E Loading.....
TARKON MUTUWA
PART 8 E

Gama fadin hakan keda wuya sai nasmal ya
kama hannun
hatyan dana sadirat ya jasu da sauri
suka nufi wani bangaren

Please Login or Register in order to submit comment