Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuci zarafin
kowaba acikin wannan birni nawa koda kuwa
bawane mara 'yancin kansa
ku sani sarki shamsal ya amince da wannan
sharadin don haka duk wanda ya sabashi
acikinku zai fuskanci hukunci mai tsanani
kodajin wannan batu sai shugaban hadiman
tsoho lamiz ya ciza lebensa cikin alamun takaici
bai san sa'adda zancensa na zuci ya fito fili ba
yace
wannan shine kuskure na biyu da sarki shamsal
ya tafka
tsoho lamiz yayi dan tunani na tsawon yan
dakiku
kadan sannan ya dubi sarauniya anisa yace
kafin mu shiga kowanne sako da lungu na
wannan gidan sarauta don gabatar da namu
binciken munaso kisa a tara gaba dayan bayi
hadimai da barorinki awancan babban fili na
wannan gida
munaso suyi layi sahu sahu na maza daban na
mata daban domin mu fara aikinmu akansu
kodajin wannan batu sai anisa tayi murmushi
tace
wannan mai sauki ne
nan take anisa ta kirawo sarkin dogarai ta bashi
wannan umarni kafin cikar sa'a daya an gama
tara wadannan hadimai acikinsu kuwa harda
sarauniya badi'atul nauwara wacce tafito
amatsayin baiwa bakar fata sanye da tufafi irin
na bayi wulakantattu
awannan lokaci badi'atul nauwara na kan gaba
alayin farko kuma acikin jerin bakaken fata ta
saje dasu babu yadda za'ayi mutum ya gane
cewa ita baiwace
lokacin da tsoho lamzis ya durfafi inda badi'atul
nauwara ke tsaye sai zuciyarta ta kama daka
domin ji take kamar lallai sai ya ganeta
tundaga nesa ya kura mata idanu ya nufota
gadan gadan harya iso daf da ita amma kuma
saiya wuceta ya dubi ta kusa da ita yayi mata
tambayoyi sannan ya kara gaba har suka gama
binciken gaba daya barori da bayi bai sake
dawowa kan badi'atul nauwara ba
adai dai wannan lokacin akaji an buga tambari
ashe sarki shamsal ne ya shigo cikin wannan
babban fili
tundazu ya farka daga barci amma sai daya
gama
kintsawa sannan ya fito kai tsaye sarki shamsal
ya taho inda tsoho lamzis ke tsaye da zuwansa
sai tsoho lamzis suka russina agareshi
suka kwashi gaisuwa sannan ya dubesu cikin
fara'a yace
aikinku yayi kyau naji dadi danaga zuwanku kun
fara gabatar da aikin shin yanzu kun kammala
da
wadannan hadimai ne?
dajin wannan tambaya sai tsoho lamzis ya
girgiza kai yace
a'a bamu gama da suba saura baiwa guda daya
wacce nake zargi akanta kuma nakeson nayi
mata tambayoyi
sarki shamsal ya ce wannan babu laifi kuci gba
da aikinku nizan koma masaukina idan harkun
gama gano abinda muke nema a aika min da
sauri nazo
lamzis ya rissina yace angama ya shugabana
nantake sarki shamsal ya koma masaukinsa
shikuwa tsoho lamzis saiya fito da badi'atul
nauwara da hannunsa ya kirawota ta nufo inda
yake tsaye zuciyarta tana daka
ita kuwa sarauniya anisa wacce take zaune acan
gefe daya bisa wata kujerar mulki ranta ne ya
baci
ta murtuke fuskarta kuma ta dora hannunta
guda
daya akan kufen takobinta jira kawai take taga
asirinta ya tonu ta dau mataki
awannan lokaci tsohuwa ummulkhairi tana
zaune
daf da ita a hannun damanta
kawai sai ummulkhairi ta dafa hannun sarauniya
anisa suka hada idanu tayi mata murmurshi
gami
da kada kai alamar cewa
ta kyantar da
hamkalinta
lokacin da badi'atul nauwara ta iso daf da tsoho
lamzis saita zube kasa bisa guiwoyinta saboda
yasan cewa babu yadda za'ayi sarauniya
ta durkisa masa
tabbas tunda yaganta ya lura da tsawon ta da
kwarjininta irin na badi'atul nauwara acan
asaninsa badi'atul nauwara tana can birninta
to tayaya za'ace harta rigasu isowa nan alhalin
ita bata tsafi kuma tsafi baya tasiri akanta
abinda baisaniba shine akwai hikimar da akayi
waccan badi'atul nauwara dasuka gani ba
gaskiya bace
wata baiwace matukar kama da badi'atul
nauwara afuska datsawo amma siffofin jikinsu
sun banbanta aiun
bayan badi'atul nauwara ta durkusa agaban
tsoho lamzis a tsakaninta na bakar fata tana
mai
sunkwui dakai kasa
saiya dubeta yace dago da fuskarki ki kalleni
ba tareda wata gardamaba kuwa saita dago kai
ya kura mata idanu nantake zuciyarsa ta sake
karaya domin badi'atul nauwara daya sani
kwayar idanunta fararene kal !
wannan kuwa bakine sannan waccan tana da
yalwar gashin gira
wannan kuwa dan kankanine
abinda bai sani ba shine dattijuwa ummulkhairi
ce tayi aikinta ta sanya wani abu acikin idanun
badi'atul nauwara wanda ya maida su bakake
kuma ta rage tudun gashin girarta
tsawon 'yan dakiku lamzis yana nazari da
mamaki sannan ya dubeta yaja num faa shi
ya dubeta yace tsawon shekara nawa kenan kike
bauta awannan gidan sarauta?
cikin wata irin kakkausar murya badi'atul
nauwara ta budi baki tace
tun zamanin sarki dainus mahaifin sarauniya
anisa
aka kamo mahaifiyata awajen yaki alokacin
inada
shekaru hudu
kodajin wannan batu acikin wannan kakkausar
murya sai jikin tsoho Lamzis ya karayin sanyi ya
dubeta yace
tashi ki tafi banida sauran zargi akanki
hakadai su tsoho lamzis sukaci gaba da
bincikensu sai da suka shiga ko ina acikin gidan
sarautar amma basuga su hatyan ba
akarshene suka dudduba bayan gari ko zasu ga
sawun kafa kona doki mai nuna alamar cewa
basu ganiba
bayan sun kammala wannan bincikene sai tsoho
lamzis ya kadaìta dasu sarki shamsal
amasaukinsa
ya dubesu cikin nutsuwa yace ya shugabana
babu ta yadda hatyan da 'yar uwarsa zasu iya
ratsa wadannan birane har su fice daga cikin
nahiyarnan tamu ba face da taimakon wasu
daga
cikin sarakunan mu
da kuma bokayenmu ayanzu nagamsu cewa
basu sami nasarar hakkaba da karfin tsafiba
lallai akwai masu mulkin dasuka munafirceka
sukayi amfani da tsananin hikimarsu da
basirarsu
wajen boye wadannan makiya naka
ina ina mai tabbatar maka da cewa a yanzu su
hatyan da yar uwarsa sun shiga wata nahiyar
don
haka sai kai tunani kaida bokanka kusan irin
matakin daya kamata ku dauka,
mu kam munyi iya yinmu babu sauran abinda
zamu iyayi......... yauwa sai wani jikon idan baku
gajiba
munci gaba
TARKON MUTUWA
Littafi na Shida 6
Part 6 C
.
.
Koda tsoho lamzis yazo nan azancensa sai
zuciyar sarki shamsal ta kama tafarfasa kamar
zata kone saboda tsananin fushi don haka sai ya
takarkare ya kwarara uban ihu dakyar boka
arzur
da tsoho lamzis suka rarrasheshi ya dawo cikin
hayyacinsa sannan tsoho lamzis ya dubi boka
arzur yace
yanzu saikayi bincike ka gano inda su hatyan
suke ayanzu kusan abinda zakuyi
kodajin haka sai zuciyar boka arzur ta buga da
karfi tsoro ya da baibayeshi saboda yasan cewa
tsafinsa yaki yayi tasiri awannan birni kuma bai
gayawa sarki shamsal gaskiyar al'amarin ba
adai dai wannan lokaci dasu sarki shamsal
sukeyin wannan tattaunawa ne sarauniya anisa
ta dauki sarauniya badi'atul nauwara tareda
dattijuwa ummulkhairi ta fitar dasu daga cikin
birnin
gaba daya ta wata barauniyar hanyar daban
wacce tasa aka basu dawakai da guziri suka
nausa daji suna masu tunkarar birnin sarauniya
badi'atul nauwara kafin suyi bankwana saida
badi'atul nauwara ta dubi sarauniya anisa cikin
alamun tsananin damuwa gami da karayar
zuciya
tace yake kawata hakika bansan irin godiyar
dazan miki ba bisa hadin kan da kika bani wajen
kubutar da wadannan marayu wato hatyan da
yar
uwarsa sadirat babu abinda zance sai fatan
alheri agareki idan baki mantaba abaya kince
dani nayi tunani akan yadda zamu dinga bawa
su
hatyan kariya bayan sunbar wannan nahiyar har
izuwa lokacinda hatyan zai iya dawowa ya dauki
fansa akan sarki shamsal
nikam banyi tunanin komaiba akan hakan amma
nasan cewa ke tuni kinyi kuma kinyi shiru akan
hakan saboda haka nabar miki amanar hatyan
kodajin haka sai mamaki ya turnuke anisa tayi
shiru kamar bazata ce komaiba daga chan kuma
sai ta dubeta tace bazan iya karbar wannan
amanarba face kin amsa tambayar danayi miki
abaya
cikin matukar kaduwa badi'atul nauwara tace
wace tambaya kenan?
anisa tace shin kin kamuda son jarumi hatyan
ne?
badi'atul nauwara tayi ajiyar numfashi tace
saboda me kikayi mini wannan zargin kuma me
yasa kike son sani?
anisa ta sake yin murmushi tace
saboda me zaki amsa mini tambaya ta da
tambaya?
badi'atul nauwara ta kada kai tace mubar
wannan maganar yanzu kawata kije ki aiwatar
da
duk abinda kike ganin cewa ya kamata
tana gama fadin hakan saita kada linzamin
dokinta ta juya ta nausa cikin daji cikin hanzari
ummulkhairi ta kada na ta dokin da sauri ta
bita
abaya
ita kuwa sarauniya anisa hankalintane ya
dugunzuma tabi badi'atul nauwara da kallo
saboda tabbas yanzu ta tabbatar da abinda take
zargi wato babu makawa kawarta ta kamu da
son
saurayin da fiyeda shekaru shida da suka
gabata
ita ta kamu da tsananin sonsa
nantake tafada cikin kogin tunani…………..
soyayyar sarauniya anisa ga jarumi hatyan ta
samo asaline tun kimanin shekaru shida da suka
shude wata rana sa'adda tayi badda kama ta
shiga birnin bindal amatsayin yar kasuwa suna
shiga cikin birnin sai keken dokinsu ya sami
matsala yazamana cewa wilin tayar keken ya
karye nan take aka basu shawara sukai gidan
sarkin makera a gyara musu
batare da bata wani lokaciba akayi musu jagora
izuwa gidansu jarumi hatyan awannan lokaci
anisa ta lullube gaba daya jikinta da wadansu
bakaken tufafi masu kauri kuma ta rufe fuskarta
da wani bakin kyalle mai dan shara shara
idanunta kadai ake iya gani
da isarsu sarauniya anisa kofar gidansu jarumi
hatyan sai sukaga mahaifinsa a zaune acikin
makera yanata aiki itadai sarauniya anisa sai
tayi zamanta acikin keken doki hadimanta guda
hudu da suke tareda ita sai suka sauko sukaje
wajen baban hatyan suka sanar dashi
matsalarsu
nan take sarkin makera yaje ya duba wilin tayar
daya karye sannan ya dubi shugaban hadiman
yace
nawa zaku biya na sauya muku wannan taya da
wadda ta fita kwari wacce zata iya shekara
goma nan gaba ba tarda ta sami matsalaba?
kodajin wannan tambayar sai hadimin ya juya
ya
dubi sarauniya anisa don yaji ra'ayinta
kawai sai tayi murmushi tayiwa hadimin magana
cikin yaren kurame
hadimin ya juyo ya dubi sarkin makera yace
uwargidana tace tanaso ka sauya mata gaba
daya tayoyi hudun kuma ka fadì nawa kake
bukata zata biyaka
kodajin wannan batu dai mamaki ya turnuke
sarkin makera yace aransa duk yadda akayi
wannan mata ba 'yar kasuwa bace wadda ta
saba juya taro da sisi
domin shi dan kasuwa baya kashe kudi haka
sai dai basarake
sarki makera ya dubi hadimin yace
ku biyani dinare dari uku
hadimin ya dubi sarauniya anisa ita kuma saita
yi
masa inkiyar ta yarda kawai
sai hadimin ya bude jaka ya fiddo dinare mai
yawa ya kirga dinare dari ukun ya baiwa sarkin
makera
sarki makera ya dubi yaransa biyu dake faman
aiki acikin makera wadanda suka kasance
samari
masu karfi yace
kuzo ku kwance tayoyin keken dokin nan domin
a
daura sababbi
ba tareda bata wani lokaciba sai kartin biyu
suka
debo kayan aiki suka fara kokarin kwance
notikan da suka daure tayoyin amma sai notikan
sukaki kwantuwa saboda dukkansu sunyi tstasa
tuni awannan lokaci anisa ta sauko daga kan
keken dokin ta koma gefe daya ta zauna tana
kallon abinda yake faruwa
nan fa wadannan katti suka gaji ainun batareda
sun iya kwance koda noti dayaba
al'amarin daya ya bai wa kowa mamaki kenan
awajen
shikuwa sarkin makera sai yazo ya dudduba
keken dokin ya kare masa kallo tsaf sannan ya
dubi anisa yace
ranki ya dade amma wannan keken dokin a
birnin
sin aka siyoshi ko?
cikin mamaki babban hadimin ya dubi sarkin
makera yace
yaya akai ka sani?
sarkin makera yayi murmushi yace
ai babu wata babbar kasa aduniya wacce banje
cikinta na koyi aikin kiraba
wadannan yara nawa basu da karfin da zasu iya
kwance notin birnin sin amma akwai wani
yarona
guda daya zai iya yanzu baya nan amma yana
daf da dawowa
kodajin wannan batu sai mamaki ya kama anisa
ta kirawo babban hadimanta tayi masa rada
akunne sannan ya dawo wajen sarkin makera
yace uwargidana tace
idan her yaron naka yazo ya iya kwance tayoyin
wannan keken dokin zata baka ninki uku na
kudin
gyaran da zata biya yanzu
idan kuma ya kasa kwancewa to ita zata kwance
da kanta,
amma ba zata baka ko sisi ba a kudin gyara da
kayi
ba tareda shakkar komai ba sarkin makera yayi
murmushi yace
nayarda da wannan sharadi
gama fadin hakan keda wuya saiga jarumi
hatyan
ya dawo daga farauta yana sanye da wata
tsohuwar riga wacce ta matseshi sosai
awannan rana ya fafata yaki da wani
murgujejen
zaki adaji dakyar ya kasheshi
kuma zakin yayi masa wani rauni guda daya
agadon bayansa
tundaga nesa hatyan ya karewa kowa kallo tsaf
akofar gidan nasu
koda yaga wadannan yaran mahaifinsa guda
biyu
atsaye agaban keken dokin suna ruke da kayan
aiki sun hada zufa saiya gane abinda ke faruwa
tun kafin ya iso gurin ya karewa anisa kallo
domin ya gano budurwace ko babbar mace
amma saiya kasa tunda arufe jikinta yake da
tufafi masu kauri kuma ta rufe fuskarta
da isowarsa ko kala baice da kowa ba saiya
karbi
abin kwance notin daga hannun daya daga cikin
kattin biyu ya fara kokarin kwancewa
dafarko saiyaji notin yaki kwantuwa amma daya
tara karfinsa waje guda sai nan da nan notin ya
juya alokacinda kwanjin hannayensa ya kumburo
rigar tasa ta dare
nanfa anisa ta kura masa idanu tana mamaki
azatonta bazata sami sadaukin da zai iya
kwance wadannan notikan ba........sai gashi ni
99% na
kunce kuma anan zan tsaya sai wani jikon idan
baku sake
gajiyaba
Daga taskar Shuraih Usman
Inkiya 99%
TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Post:- Shuraih Usman
Littafi na Shida 6
Part 6 E
.
.
lokacinda anisa tazo nan atunaninta sai ta juya
ta
koma cikin gidan sarautarta, ta wata boyayyiyar
hanya ta musamman
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU ABIRNIN
SARAUNIYA ANISA BAYAN TA SAMI NASARAR
FITAR DA SU HATYAN IZUWA NAHIYAR GABANSU
Al'amarin jarumi hatyan kuwa tunda suka fada
cikin nahiyar gaba sai suka tsinci kansu cikin
farinciki gami da kwanciyar hankali tamkar basu
da wasu makiya dake farautarsu
tunda suka nausa acikin dajin suna tafiya her
tsawon yini guda basu hadu da wani mugun
abuba sau tari idan ma suka hango wata
dabbar
daji mai hadari kafin su risketa sai ta sauya
hanya
ta basu wuri
abu daya ne ya sosa musu rai ba komai bane
face sauyin yanayi basu taba ganin daji irin
wannan ba hatta duwatsu da bishiyoyi da
tsuntsayen ma ba irin wanda suka saba gani
bane
sai da rana ta fadi sannan su hatyan suka yada
zango abakin wata korama mai dauke da ruwa
garai garai gwanin ban sha'awa yake saboda ni
imarsa ta kyawawan bishiyoyi tsirai gamida
koramu
bayan hatyan da sadirat sunci abinci sun sha
ruwa sai suka zauna abakin wannan korama
suna
kallon yadda ruwa ke kwaranya acikin nishadi
tsawon yan dakiku dayan su baice uffan ba
daga can sai sadirat ta dubi hatyan alokacinda
idanunta suka ciko da kwalla tace
yakai dan uwana yanzu shike nan bamu da ikon
komawa birnin mu bare har mu nemi inda
kabarin
iyayenmu yake mukai musu ziyara?
kodajin wannan tambayar sai nan take shima
hatyan yaji idanunsa sun ciko da kwalla kafin ya
ankara hawaye ya subuto masa don haka sai ya
janyo sadirat ya rungumeta yace
ki kwantar da hankalinki yake yar uwata nayi
miki
alkawarin komai daren dadewa sai mun koma
birnin bindal mun dauko fansar ran
mahaifinmu,
kuma ina mai tabbatar miki da cewa bokana na
nan araye bai mutuba
kuma nasan ya binne gawar iyayenmu a inda
babu wanda ya. sani
kodajin wannan batu sai farinciki ya lullube
sadirat ta janye jikinta daga nasa ta dubeshi
cikin
murmushi da nufin tace wani abu
kwatsam sai suka ji wani irin gurnani mai ban
tsoro ya cika dajin daga kowacce kusurwa kuma
gurnanin ya dinga karuwa yana kusanto su
al'amarin daya firgita sadirat kenan ta koma
bayan hatyan ta kankameshi
lokaci guda sai suka hango wadansu manyan
zakuna sama da guda dubu daga gabasa da
yamma kudu da arewan dajin
cikin zafin nama hatyan ya mike tsaye zumbur
yana mai goya sadirat a gadon bayansa ya ruga
izuwa cikin koramar dake gabansu,
suna fadawa cikin koramar sai suka ga ashe
acike takeda wadansu irin manya manyan kadoji
tunda suka zo duniya basu taba ganin kadoji
masu girmansu ba
kafin hatyan ya yi wani yunkuri tuni wani kada
ya
make sadirat da jelarsa
sadirat tayi sama ta fada can gefen koramar ta
baje akasa sumammiya jini na zuba akanta
cikin zafin nama hatyan ya daka tsalle ya kamo
reshen wata bis
TARKON MUTUWA
Littafi na Shida 6
Part 6 E
.
.
lokacinda anisa tazo nan atunaninta sai ta juya
ta
koma cikin gidan sarautarta, ta wata boyayyiyar
hanya ta musamman
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU ABIRNIN
SARAUNIYA ANISA BAYAN TA SAMI NASARAR
FITAR DA SU HATYAN IZUWA NAHIYAR GABANSU
Al'amarin jarumi hatyan kuwa tunda suka fada
cikin nahiyar gaba sai suka tsinci kansu cikin
farinciki gami da kwanciyar hankali tamkar basu
da wasu makiya dake farautarsu
tunda suka nausa acikin dajin suna tafiya her
tsawon yini guda basu hadu da wani mugun
abuba sau tari idan ma suka hango wata
dabbar
daji mai hadari kafin su risketa sai ta sauya
hanya
ta basu wuri
abu daya ne ya sosa musu rai ba komai bane
face sauyin yanayi basu taba ganin daji irin
wannan ba hatta duwatsu da bishiyoyi da
tsuntsayen ma ba irin wanda suka saba gani
bane
sai da rana ta fadi sannan su hatyan suka yada
zango abakin wata korama mai dauke da ruwa
garai garai gwanin ban sha'awa yake saboda ni
imarsa ta kyawawan bishiyoyi tsirai gamida
koramu
bayan hatyan da sadirat sunci abinci sun sha
ruwa sai suka zauna abakin wannan korama
suna
kallon yadda ruwa ke kwaranya acikin nishadi
tsawon yan dakiku dayan su baice uffan ba
daga can sai sadirat ta dubi hatyan alokacinda
idanunta suka ciko da kwalla tace
yakai dan uwana yanzu shike nan bamu da ikon
komawa birnin mu bare har mu nemi inda
kabarin
iyayenmu yake mukai musu ziyara?
kodajin wannan tambayar sai nan take shima
hatyan yaji idanunsa sun ciko da kwalla kafin ya
ankara hawaye ya subuto masa don haka sai ya
janyo sadirat ya rungumeta yace
ki kwantar da hankalinki yake yar uwata nayi
miki
alkawarin komai daren dadewa sai mun koma
birnin bindal mun dauko fansar ran
mahaifinmu,
kuma ina mai tabbatar miki da cewa bokana na
nan araye bai mutuba
kuma nasan ya binne gawar iyayenmu a inda
babu wanda ya. sani
kodajin wannan batu sai farinciki ya lullube
sadirat ta janye jikinta daga nasa ta dubeshi
cikin
murmushi da nufin tace wani abu
kwatsam sai suka ji wani irin gurnani mai ban
tsoro ya cika dajin daga kowacce kusurwa kuma
gurnanin ya dinga karuwa yana kusanto su
al'amarin daya firgita sadirat kenan ta koma
bayan hatyan ta kankameshi
lokaci guda sai suka hango wadansu manyan
zakuna sama da guda dubu daga gabasa da
yamma kudu da arewan dajin
cikin zafin nama hatyan ya mike tsaye zumbur
yana mai goya sadirat a gadon bayansa ya ruga
izuwa cikin koramar dake gabansu,
suna fadawa cikin koramar sai suka ga ashe
acike takeda wadansu irin manya manyan kadoji
tunda suka zo duniya basu taba ganin kadoji
masu girmansu ba
kafin hatyan ya yi wani yunkuri tuni wani kada
ya
make sadirat da jelarsa
sadirat tayi sama ta fada can gefen koramar ta
baje akasa sumammiya jini na zuba akanta
cikin zafin nama hatyan ya daka tsalle ya kamo
reshen wata bishiya dake cikin koramar yana
reto akanta
ai kuwa sai wani kada ya wangame bakinsa ya
kawo masa hadiya
hatyan ya daka tsalle daga kan bishiyar ya
kaucewa harin kadar
koda kadan ya cafi bishiyar sai ya gatsata ta
rabe biyu duk da cewa kaurinta yafi kamu
ashirin
hatyan na fadowa kasa sai ya tsinci kansa
atsakiyar miyagun zakuna sama da guda dubu
uku
koda ya dubi can gefensa ya hango 'yar uwarsa
sadirat kwance cikin mugun hali sai ya kwarara
uban ihu cikin tsananin fushi yayi wuf ya zare
takobinsa ya afkawa zakunan
SHIN JARUMI HATYAN ZAI KUBUTA DAGA
HANNUN WADANNAN MIYAGUN ZAKUNA DA
KADOJI?
WANE HALI 'YAR UWARSA SADIRAT KE CIKI! ?
ZATA RAYU NE KO MUTUWA ZATAYI?
YAUSHENE HATYAN ZAI SAKE SADUWA DA
ANISA DA KUMA BADI'ATUL NAUWARA?
YAYA ZAIYI DA SOYAYYAR MATAN BIYU?
YAUSHENE ZAI DAWO BIRNIN BINDAL DON
DAUKAR FANSA AKAN SARKI SHAMSAL?
MU HADU ALITTAFI NA BAKWAI DON JIN
CIGABAN WANNAN LABARI,
INA MAI BAKU HAKURI MEMBER NA WANNAN
GROUP DIN NA MAZA GUMBAR DUTSE MAI
ALBARKA,
END OF DISCUSSION

TARKON MUTUWA
Littafi na bakwai
Part 7A
.
Lokacinda hatyan ya fadawa wadannan
dubunnan
manyan zakuna ya zamana cewa yana kai musu
sara
da suka ta ko'ina cikin bakin zafin nama da
jarumtaka
sukuma suka rinka kai masa mangari, cizo
yakushi suna yanyameshi, amma saboda zafin
namansa da tsagwaron jarumtakarsa sai suka
kasa samun nasarar yakusarsa shimaa kuma
duk da cewa yana makesu suna zubewa kasa
saiyaga sun taso zumbur sunci gaba da kawo
masa mugayen hare hare saida suka kusan
shafe rabin sa'a suna mugun artabu ba tareda
dayansu
ya sami nasara akan dayaba
awannan lokaci hankalin jarumi hatyan ya
dugunzuma
ainun saboda kaifi da tsini baya tasiri ajikin
zakuna kuma. ko kadan babu alamar gajiya
atareda zakunan kamar ko yaushe kara musu
kuzari akeyi, shikuwa saiya fahimci cewa idan
aka
cigaba da wannan fafatawa ahaka her izuwa
tsawon wani lokaci to tabbas zai iya jigata
zakunan su cimmasa amma babban tashin
hankalinsa shine batun 'yar uwarsa sadirat
da take kwance magashiyan acan gabar
koramar
kuma baisan halin da take ciki ba
nan take hatyan ya aiyan a ransa cewa lallai
wadannan zakuna sihirtattune na musamman
idan kuwa hakane to turosu akayi musamman
don su kasheshi tareda 'yar uwarsa sadirat
babu wanda ke dauke da wannan alhakin
face sarki shamsal
tabbas wannan dayane daga cikin irin mugayen
tarkunan da sarki shamsal ya kafa musu
koda gama ayyana hakan
acikin zuciyarsa saiya fara tunanin hikimar
dazai yi amfani da ita wajen ganin ya gaggauta
kawar da wadannan zakuna dabara ta fadomasa
ya gane cewa saidaifa yayi amfani da tsagwaron
karfin
damtsensa da kuma dabarun fada saboda
yayi kokarin amfani da karfin sihirinsa na tsafi
yakiyin
amfani saboda ansha gabansa awannan fannin
acikin shammace gamida tsananin fushi sai
jarumi hatyan
ya shammaci daya daga cikin zakunan ya gabza
masa wawan naushi a idonsa guda daya
saboda
karfin naushin take ruwan idon zakin ya tsiyaye
zakin yayi tsalle sama yayi wata irin kururuwa
mai ban tsoro ya fado kasa tim
ya baje wanwar ko shurawar kirki baiyiba
koda
jarumi hatyan ya ga ya sami nasara saiya kamu
da tsananin farinciki kuma ya kara kaimi yaci
gaba
da bugun zakunan cikin zafin nama da
jarumtaka
aikuwa nandanan yaci karfinsu ya bazar da
sama
da guda dari shida tabbas idan kaji ana ki gudu
to sa gudune baizoba lokacinda zakunan suka
ga hatyan yana ragargazar 'yan uwansu suna
zama
gawa sai suka tarwatse suka kama gudu acikin
daji
dukkaninsu suna neman wajen buya
koda jarumi hatyan ya ga zakunan sun watse
daga wajen sunbar gawarwakin 'yan uwansu
birjik
saiya rugo da gudu izuwa inda sadirat ke
kwance
da isarsa daf da ita sai ya durkusa yana shirin
tallafo
kanta kenan saiyaga ta bude idanunta ta
dubeshi
cikin murmushin karfin hali
cikin tsananin farinciki yayi sauri ya cire wani
kyallen dake jikinsa ya daure raunin dake kanta
saboda her asannan raunin bai daina digar jini
ba
sannan ya dauke ta da hannu biyu yakaita bakin
wani dutse yayi sauri ya bude jakar guzurinsa
ya fiddo magani ya shafa akan raunin nata
kuma ya bata tasha ta hadiya sau uku
faruwar hakan keda wuya sai taji karfin jikinta
asannan ne ta sake dubansa cikin murmushi
akaro na biyu tana mai gyara zamanta tace
yakai dan uwana nayi farinciki dana ganka
araye inda ace ka tafi ka barni bansan yadda
zan cigaba da rayuwaba, koda ta tsawon dakika
guda kuwa lokacinda sadirat tazo nan
abayaninta
sai jarumi hatyan yayi murmushi yace
ai nine zance da
kin tafi kin barni bansan yadda zan cigaba da
rayuwaaba
babu mamaki hankalina ya gushe
nan take koma na hadiyi zuciya na mutu
saboda
bakin ciki tunda bani da sauran kowa aduniya
sai........
kafin hatyan ya gama fadin abindake bakjnsa
sai sadirat tayi sauri ta rufe bakinsa da tafin
hannunta tace karka fadi haka domin
inaji ajkina cewa
muna da sauran rayuwa awannan duniya
bazamu mutu ba harsai munga bayan makiyan
mu
alkawarine sai mun dawo birnin bindal
mun dauki fansa
akan sarki shamsal da dansa
yayinda sadirat tazo nan abayaninta sai farinciki
ya
lullube hatyan ya rungume ta akan kirjinsa
yana mai cewa, kinyi gaskiya yake 'yaruwata
lallai duk wuya duk rintsi sai mun cika burin mu
sadirat ta numfasa tace waishin yanzu menene
abinyi agaremu? shin zamu yada zango ne anan
tsawon wadansu 'yan kwanaki ko kuwa zamuci
gaba da tafiyane har mu riski garin dake gaban
mu
dajin wannan tambaya sai jarumi hatyan yayi
ajiyar zuciya sannan yace
yake 'yaruwata ci gaba dayin wannan tafiya
tamu ayanzu yana da matukar hadari saboda
akwai matsananciyar gajiya ajikina sakamakon
gwagwarmayar da nayi da wadancan sihirtattun
zakuna koda jin wannan batu sai mamaki ya
kama
sadirat tace yanzu kana nufin kace duk wannan
masifa da kuma shiga aiki ne na sihirine?
hatyan ya gyada kai yace kwarai kuwa kuma
wannan masifa somin tabi ce kawai abinda
nakeso dake kawai shine lallai ko yaushe ki
kasance kina tareda ni
kada ki kuskura ki rinka nisanta dani
koda
kuwa da tazarar taku ukuce
sadirat ta gyada kai tana mai nuna cewa zata
kula
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GASU
JARUMI HATYAN
BAYAN SUN SAMI NASARAR FITA DAGA CIKIN
NAHIYARSU
GABA DAYA INDA SUKA SHIGA SABUWAR
NAHIYA TA BAKAKEN FATA
Lokacinda tsoho lamzis ya fita ya bar boka
daizur
da sarki shamsal a zaune sai boka daizur ya
kasa fiddo madubin tsafinsa
kawai sai ya runtse idanunsa yayi kamar yana
bincikene, al'amarin daya fusata sarki shamsal
kenan
ya daka masa tsawa yayi firgigit kamar wanda
ya farka daka barci, sarki shamsal ya dubeshi
yace
kada ka bata mini lokaci abanza kawai ka dauko
madubinka ma tsafi ka binciko mana mugun
halinda su hatyan suke ciki tunda tuni mun
aika musu da zakunan sihirin da zasu hallakasu
aduk inda suke
koda jin wannan umarni sai boka daizur yayi
sauri
ya zura hannunsa acikin aljihun wandonsa
jikinsa na rawa ya fiddo madubin ya ajiye shi
agabansa cikin matukar karfin hali kuma
zuciyarsa
na daka ya dora tafin hannunsa na hagu akan
madubin ya shafeshi, ba zato ba tsammani
sai boka daizur yaga madubin nasa ya washe
daga duhu zuwa haske nan take saiga hoton
duk abinda ya faru gasu jarumi hatyan nan
acikin daji da yadda hatyan ya fafata da
wadannan
zakuna harya kashe wasu da yawa daga cikin su
koda gama ganin abinda ya faru sai fuskar
sarki shamsal ta kama gyatsine saboda tsananin
fushi ya kasa cewa uffan harsaida boka daizur
ya shafi madubin tsafin nasa yayi baki sannan
ya dubeshi yace
yanzun nan zamuyi shiri mubi su jarumi hatyan
izuwa wannan nahiya da suka shiga ta bakaken
fata
lallai sai mun cimmasu nayiwa hatyan da 'yar
uwarsa kisan
gilla, kodajin wannan batu sai idanun boka
daizur
suka zazzaro ya dubi sarki shamsal cikin
matukar firgici
yace
haba ya shugabana shin ka mantane cewar
yana daga cikin dokokin magabatanka cewa
jininku baya shiga wata nahiyar?
idan kuwa ya shiga bazai dawoba araye
kuma
saiya rasa komai da kowa arayuwarsa
idan her kabi su hatyan
waccan nahiyar bazaka taba cika burinka ba
akan sa kuma ba zaka koma birninka na bindal
ba
abinyi kawai shine muci gaba da tura musu
mugayen tarkunan da basu isa su iya tsallakesu
ba
komai sa'arsu da nasararsu lokacinda sarki
shamsal yaji wannan bayani na boka daizur
sai hankalinsa ya dan kwanta ya sunkwui da
kansa
kasa yana mai tunani da nazari daga can
saiya dago da kansa ya dubeshi yace
jiya da daddare lokacinda muka dan runtsa
nayi wani mafarki daya dan sosa mini rai lallai
akwai wani bakon abu dayake faruwa abirnin
bindal
inaso ka duba mini yanzu domin muga ko
menene
abinda ya faru bayan tafiyar mu
koda jin wannan batu sai boka daizur yaji
zuciyarsa
ta buga da karfin gaske, al'amarin daya sa shi
kansa
ya firgita kenan kuma ya kamu da tsananin
mamaki
domin bai san dalilin dayasa yaji tsoro ya
shigeshi ba
amma saiya dubi sarki shamsal cikin murmushi
yace
haba ranka ya dade yanzu her akwai wani abu
wanda zai faru abirnin bindal ya baka tsoro
aiko ma menene da zarar mun koma zamu
kawar dashi cikin dakika daya
kafin boka daizur ya gama rufe bakinsa, tuni
sarki shamsal
ya tari numfashinsa yana mai cewa
ai dan hakkin daka raina shike tsone maka ido
irin wannan sakacin nakane yasa hatyan ya
wanzu abinrnin bindal
ba tareda mun sani
boka daizur ya rissina yace
hakika abinda ka fada gaskiyane
amma ka sani cewa taura biyu bata taunuwa
alokaci daya domin hankalinka zai iya rabuwa
biyu
idan kuwa ya rabu ana samun rashin nasara
zaifi kyau mu gama da matsalar su hatyan
domin tafi kowacce matsala hatsari
sa'adda sarki shamsal yaji wannan batu saiyaja
dogon
numfashi gamida ajiyar zuciya sannan yace
yanzu menene mugun abu na biyu wanda zamu
turawa su hatyan lallai inason su hallaka kafin
su isa wannan

Please Login or Register in order to submit comment