Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

arzus bin sharkuf idanu cikin firgici
shekarar da boka arzus ya sauka anahiyar
yayi
abubuwan al’ajabi da yawa wadanda suka
daurewa mutane kai yazamana cewa ana
girmamashi kamar za’a bauta masa komai
tsananiin cuta indai bata ajali bace,to indai
boka
arzus yazo ya tsaya akan mutum to sai ya
warke
ya mike sumul tammkar bai taba cutaba
komai talauci idan mutun mulki yake nema
sai ya
samu ba neman suna ko daukaka,
bisa wannan daliline sarakan nahiyar sukayi
ca
akan boka arzun kowannensu na zuwa da
bukatarsa yana biya masa
amma sarkin birnin bindal wato mahaifin
sarki
shamsal ne bai taba zuwa gareshiba saboda
shi
yana ganin shi bashida wani abu da zai nema
awajensa saboda Allah ya horemasa lafiya
daukaka gami da arzikin da babu me
kamarsa
awannan nahiyar, bisa wannan daliline
yazamana
cewa ansami rashin jituwa tsakanin koka
arzur da
sarki
watarana boka arzur na tare da manyan
sarakuna guda uku na nahiyar a gidansa
dake
can tsakiyar wani daji wanda ake kira jahal
sai
kawai aka hango wani abu a can sama
tamkar
tauraruwa ya taho yana feshin wuta kuma ya
nufo inda boka arzur ke zaune.
Nan take wadannan sarakuna uku tare da
gaba
dayan hadiman boka arzur suka firgice suka
ruga
da gudu suka kama buya a cikin gidan,ya
zamana
cewa boka arzur kadai aka bari a zaune,ko
alamar tsoro babu a tare da shi,saboda ya
yarda
da kansa ma sai ya dora kafarsa daya bisa
dayar
ya kurawa wannan tauraruwa idanu yana
jiran
isowarta.
sai da ya rage saura baifi taku biyarba
tsakaninsu sai tauraruwar ta fado kusa da shi
agabansa
ta rikide ta zama sarkin bindal a cikin
gagarumar
shigar yaki.
nan fa wayanda suka boye,suka fara firfitowa
suna kallon ikon Allah,kawai sai akayi kallon
yan
dakiku sannan boka arzur yayi murmushi ya
mike
tsaye daga kan kujerar da yake zaune ya
dube
shi yace”lale marhaban da kai,”wanan
Sarki mai
daraja tabbas nayi farinciki da wannan
ziyarar
taka wacce ban taba zatoba don haka nayi
maka
alkawarin zanbiya maka duk irin bukatar
dakazo
mini da ita
kodajin haka sai sarkin bindal ya turbune
fuska
yace banzo gareka don neman wata bukataba
saboda baka da abinda bani dashi na zone
na
baka umarni katashi daga cikin yankin kasata
inason ka hada naka da anaka ka bar mana
nahiyarmu acikin kwanaki uku kacal inba
hakaba
kuwa zaka rasa rayuwarka
nine kadai sarkin da kowa yake shakka a
wannan
nahiya anayi mini ladabi kamar abin bauta
amma
yanzu komai na neman dawowa gareka
to ka sani ba’ayin sarki biyu agari daya na
fuskanci
cewa idan na kyaleka kaci gaba da
harkokinka da
sannu zaka raba mu da mulkinmu
koda sarki yazonan azancensa sai boka arzur
ya
takarkare ya bushe da dariya lokaci guda
kuma
ya turbune fuskarsa yace
yakai wannan sarki ka sani cewa tinda nazo
wannan nahiya da niyyar na mulketa, da
acikin
daredaya zan gama da ita .to amma nazone
sabo
wani buri guda daya wanda ya rage mini
arayuwata
Koda kuwa ban cika wannan burin a
zamaninku
ba sai na cikashi ana yayanku ko
jikokinku,burin
kuwa shine ina so na hattama wani sihirin
tsafi
wanda na farashi tun ina da shekaru tara
aduniya
wannan tsafi bazai kammalu ba har sai
sarakai dari
da daya sun durkusa a gabana bisa
gwiwoyinsu na
dafa kawunansu yayin da sukazo neman
bukata
,wato nasa musu albarka ahalin yanzu
sarakuna
arba’in da dayane jal suka durkusa agareni
ina
neman hamsin da takwas kuma dole sai
awannan
nahiya takune zan sami wadannan sarakunan
da
nake nema saboda haka babu wanda ya isa
yasa
nabar wannan nahiya face ba na num fashi
adoron
kasa ko mujima ko mu dade kai ma sai kazo
ka
durkusa agabana idan baka durkusa mini ba
sai
danka ko jikanka yazo ya durkusa mini
gama fadin hakan keda wuya sai boka arzur
ya
bushe da dariyar mugunta yayita kyakyatawa
kamar ba zai dai naba
al’amarin daya matukar fusata sarkin bindal
ke
nan kawai sai ya zare takobinsa ya dako
tsalle
daga inda yake tsaye tamkar an harboshi
daga
cikin baka cikin bakin zafin nama boka arzur
ya
kaucewa mummunan saran da sarki ya kawo
masa wanda saura kiris ya sare masa kai
kawai sai akaga shima boka arzur ya daga
hannunsa sama takobinsa ta baiyana yatari
sarki suka ruguntsume da azababben yaki ya
zamana cewa suna kaiwa junansu sara da
suka
cikin zafin nama juriya da bajinta ta ban
al’ajabi
sai da suka shafe sa’a guda suna bakin
artabu da
kyar kowanensu ya sami nasarar yankar
abokin
gwaminsa shi dai sarkin bindal agefen
hannun
hagu ya yanki boka arzur
shikuma boka arzur akan cinyar dama ya
yanki
sarkin bindal raunin baiyi wani zurfi sosaiba
koda sukaga cewa jarumtakarsu tazo daya sai
suka koma yakar juna da karfin sihirin tsafi
wohoho masifa ba’asamata rana wadannan
sarakuna uku dake wannan wurin tareda
hadiman
boka arzur sunga turnuku irin wanda basu
taba
ganiba kuma sunga tashin hankali wanda ya
firgitasu sukaji kamar su haka rami su shige
ciki
hatta bishiyoyi da duwatsu dake cikin dajin
sai da
suka rinka farfashewa suna karyewa .saboda
bala’in da jaruman biyu suke haddasawa
wani lokacin sai su rikide su zama manyan
dabbobin daji suyita gumurzu shikansa dajin
girgiza yakeyi kamar kasa zata rufta duk
abinda
yake cikinta ya rufta ciki
ahaka sai da suka shafe sa’a uku suna
masifaffen
yaki har sai da kusan ko ina ya kama da
wuta
adajin asannan ne boka arzur da sarkin
bindal
suka jugata ainun suka zube kasa sunata
faman
yin haki da numfashi kamar ransu zai fita.
sai da suka dan jima kwance akasa suna
hararar
juna sannan sarki bindal ya mike tsaye ya
dubi
boka arzur cikin tsananin fushi da kiyayya
yace
narantse da girman iyayena daga yau babu
wani
sarki dazai kara zuwa gareka ya durkusa
agabanka muddin ina numfashi adoron kasa
kodajin wannan batu sai boka arzur ya mike
tsaye zumbir yace nima na rantse . da gemun
ubana har abada zuriyarka bazasu zauna
lafiya ba
har tsakanin iyaye da ‘ya’ya sai an sami
sabani
kuma sai wannan masarautar tabar
hannunku ta
koma hannun wayanda ma basu gadaba
dajin wannan batu sai sarkin bindal yayi
girgiza
ya zama tururuwa ya cilla izuwa cikin
kololuwar
sama ya bace acikin gajimare tamkar bai taba
wanzuwaba
WANNAN SHINE ASALIN TARIHIN
DANGANTAKAR BOKA ARZUR DA GIDAN
SARAUTAR BIRNIN BINDAL
TARKON MUTUWA
5 B

boka arzur makiyin ubankane babu hujjar da
zatasa ya soka kawai zaiyi amfani dakaine
don
biyan bukatarsa dazarar anci moriyar ganga
za’a
yar da koranta ne
zaka yi nadamar wannan butulci dakyiwa
mahaifinka kuma saika zubarda hawaye da
idanunka
kafin ta gama rufe bakinta tuni yarima
yadaka
mata tsawa yana mai cewa
don me bazanci amanar mahaifina ba alhalin
ya
juya mini baya tun daga ranar da hatyan ya
sare
mini hannu daga wannan ranar ya
tsaneni,yadaina nuna min so da kauna
jama,a
sun
fuskanci cewar bazai taba bani karagar ba,
saboda na zāmana sarki yanzu tafi duk inda
kikeso kije
domin tafiyar taki zata fiye mana alheri gaba
daya,
dajin haka sai mahaifiyar yarima ta juya ta
fuce
da sauri afusace tafice daga cikin fadar tana
zubar da kwalla saboda bakin ciki da takaici
ma
ko waigowa bata sakeyi ba
shikuwa yarima koda yaga mahaifiyar tasa ta
tafi
saiya bushe da dariyar farinciki sannan ya
dubi
sarkin dogarai yace
inaso yau da yamma ku zagaya gida gida ku
kamo min gaba daya ‘yan matan garin nan
da
zawarawa matasa banda tsofaffi kuzo min
dasu
nan
kodajin wannan batu sai boka arzur ya yi wuf
ya
dakatarda sarkin dogarai ya kama hannun
yarima
yajashi izuwa gefe daya inda babu wamda
zaiji
abinda zasu tattauna ya dubeshi yace
idan kaci gaba da wannan huldar ta mata
duk
abinda mukasa agaban mu rushewa zaiyi
kodajin wannan batu sai hankalin yarima ya
dugunzuma takaici ya turnukeshi ya rasa
abinda
ke masa dadi aduniya saboda a iya
rayuwarsa
babu abinda ransa yakeso sama da yiwa
mata
fyade
cikin alamun tsananin damuwa yarima ya
dubi
boka arzur ya ce
shin zan iya tura dakaru zuwa wasu kauyuka
adebo min wadan nan mata?
boka arzur ya kada kai yace
ya shugabana dolene fa ka kawar da wannan
halayya taka idan har kanaso kayi nisan
kwana
akan karagar mulki,, domin zina gami da
zubar da
jini suna lalata sihirin tsafin danakeyi yanzu
kodajin haka saiya juya da sauri ya fice daga
cikin fadar cikin matsanancin fushi ya nufi
bangaren da turakar sarki take
da shigarsa cikin babban falo na sarki
shamsal
sai yayi arba da wani babban hoto na sarki
shamsal wanda wani kwararren mai zane ya
zana
an sakale wannan taswira acan saman bango
koda yarima ya kalli wannan hoto sai yaji ya
tsani mahaifin nasa fiyeda ko yaushe don
haka
sai ya zare takobinsa ya daka tsalle sama ya
datsa hoton gida biyu ya fado kasa
karar sare hoton ne yasa hadimai suka rugo
da
gudu izuwa cikin falon, sai sukaga hoton sarki
shamsal agabansa kuma arabe gida biyu sai
gaba dayansu suka sunkuyar da kansu kasa
kawai sai yarima ya daka musu tsawa yace
su
fice daga cikin fadar gaba daya
kafin kace me?
sun fice gaba dayansu babu ko mutum daya
nan take yarima yaje inda aka ajiye tambulan
kayan shaye shaye
kawai saiya suri tambulan din giya guda daya
ya
kafa abakinsa
yakama kwankwada harsaida giyar ta kare
kaf
ko digo daya babu saura sannan yai jifa da
tambulan din kasa ya fashe
yana tangadi ya nufi cikin turakar barci,, har
wadansu kuyangi guda hudu sun biyoshi
abaya
saiya daka musu harara suka koma da sauri
kawai saiya banko kofar dakìn ya fada kan
gado
ya baje
nantake kuwa ya kama barci harda munshari
acikin garin bindal kuwa tuni labari ya riski
jama’a cewa
boka arzur ya hana wannan sabon azzalumin
sarki yin mugayen halayensa bisa hakane yan
mata da zawarawa suka kamu da farinciki
hakama iyayensu
nanfa iyaye da sauran mutanen gari suka ci
gaba
da tsegumi iri iri wasu suce ai har mulkin
zaluncin da sarki shamsal yakeyi ada yanzu
zai
ragu tunda an sami sauyin sarki wasu kuma
suka
dinga cewa ai babu tabbacin hakan sai dai
abinda
aka gani tunda boka arzur ne ke mulkin
birnin
afakaice tunda sai abin daya fada akeyi
wannan shine abinda yafaru abirnin bindal
bayan
tafiyar sarki shamsal
Acan birnin askandariya kuwa jarumi hatyan
da
‘yar uwarsa sadirat tunda suka bingire akan
gado
suka kama barci tamkar gawa
dayansu bai farkaba har sai da dare ya raba
tsakiya
dai dai wannan lokaci ne jarumi hatyan ya
farka
yana mai bude idanunsa a hankali.ba tare da
jin
wata gajiya ko tsamin jiki ba
sai ya mike zaune ya dubi yar uwarsa sadirat
yaga ko motsin kirki batayi sai yayi murmushi
sannan ya mike tsaye ya kama kai kawo
acikin
turakar yana mai mamakin yadda akayi yaji
kwarin jikinsa tamkar wani abu bai taba
lafiyarsaba
nantake tunani iri iri ya fara fado masa
arai,da
farko yace yanzu idan sarki shamsal ya iso
garinnan ya riskemu nida yar uwata ai mun
jefa
anisa da badi’atul nauwara acikin masifa
lallai yana da kyau agoben nan mu bar
garinnan
mu kara gaba
wai shin da gaskene anisa tana sona kamar
yadda naga alamun cewa badi’atul nauwara
tun
haduwarmu ta farko?
tayaya zan hada soyayyar aminai guda biyu
kuma
gashi kowacce acikinsu tayi mini halaccin da
bai
kamata na juya mata baya ba koda gama
fadin
hakan sai hatyan ya lura ai
wannan daki da suke ciki bashine dakin da
aka
saukesuba da farko
to yaushe aka dawo dasu nan basu saniba
amsar da hatyan ya kasa baiwa kansa kenan
alokcin da hankalinsa ya dugunzuma
sakamakon
rashin ganin kofar fita daga wannan daki da
suke
ciki
cikin kaduwa da mamaki hatyan ya shafa
dukkanin bangwayen dakin amma yaji shiru
kamar maye yaci shirwa
hakadai yaci gaba da dube dube da tabe
tabe
gami da leke leke har karkashin gado amma
duk
baiga wani wuri mai alamar kofar fita ba
domin
ko ina a shafe yake
adaidai wannan lokacine sadirat ta farka
daga
barcin koda taga hatyan yanata lalube kuma
ta
lura cewa an sauya musu daki
sai itama hankalnta ya tashi,ta tashi tsaye da
sauri tasha gabansa tana mai cewa wai me
ke
faruwa naga an chanja mana masaukin mu?
kodajin wannan tambaya sai hatyan ya dawo
cikin hayyacinsa yayi ajiyar numfashi sannan
yace
ina ganin dai saboda tsarone yasa aka
kawomu
nan
babu mamaki su sarki shamsal sun iso sun
fara
bincike
kodajin wanna batu sai saidira taji zuciyarta
ta
buga da karfin gaske fiye da ko yaushe nan
take
jikinta ya kama kyarma
koda ganinhaka sai hatyan yayi murmushi ya
dafa kafadarta yace
ki kwantar da hankalinki yake yar uwata kiyi
sani
.cewa babu abinda zai samemu kuma ina
tabbatar miki da cewa idan har sarki shamsal
na
nan to yau zai mutu
kodajin wanan batu sai sadirat ta sake firgita
ta
dubi hatyan cikin firgici tace
yakai dan uwana kada ka kuskusra kace
zakayi
wani abu domin baka da nasara akan sarki
shamsal yanzu sai dai nan da wadansu
shekaru
kamar yadda bokaye suka fada
hatyan yace nidai banyi imani da duk
maganganun bokayeba abinda na yarda
dashi
kawai shine sa’a da rabo
kin sani cewa ke baki isa ki hanani aiwatar da
duk abindana so yiba don haka kawai ki zuba
ido
koda gama fadin hakan sai hatyan yaci gaba
da
neman kofar fita daga cikin dakin ita kuwa
sadirat sai hankalinta ya dugunzuma ainun
fiye
da ko yaushe
kwatsam sai su kaga wata kofa akasa ta bude
da kanta saiga matattakalar bene wacce tayi
sama
TARKON MUTUWA
5 C

Al’amarin da ya daure musu kai kenan suka
fahimci cewar inda suke dakin kasa ne, har
hatyan ya yunkura zai hau kan matattakalar
benen ya fice sai ga sarauniya anisa ta shigo
ta
cikin matattakalar benen tare da wasu
hadimanta
guda uku anisa tayiwa hatyan wani irin kallo
na
zargi gamida dan guntun murmurshi tace
kadaina tunanin zaka kaiwa sarki shamsal
harin
bazato don kawar dashi
domin bazaka taba samun nasara ba kamar
yadda yar uwarka ta fada maka haka
al’amarin
yake, karonka da sarki shamsal na farko kayi
matukar sa’a da kawata badi’atul nauwara
ta
kawo maka dauki
idan ka kuskura ka sake tarar sarki shamsal a
karo na biyu mutuwa zakayi indai ni ko ita
bamu
kawo maka daukiba
koda sarauniya anisa tazo nan azancenta sai
mamaki ya turnuke hatyan
nan take ya gane cewa tabbas itama
sarauniya
anisa tana da abinda take takama dashi
walau
tsafi ko jarumtaka tunda tana fadin cewa
zata
iya bashi kariya
yana cikin wannan tunanin anisa ta katseshi
tace
yanzu gari ya waye kuma tun adaren jiya
sarki
shamsal da bokansa suka bincike ko ina
acikin
wannan gidan sarautar nawa suna nemanka
basu
gankaba
a yanzu haka suna chan akwance suna barci
nan
da cikar kamar sa’o’i uku wasu kwararrun
hadimansa masana iya bincike zasu iso
garinnan
idan suka iso kuwa sai sun gano inda kuke
saboda haka dolene sai kun fice daga
garinnan
yanzu a sirrance
ku sani cewa tafiyar sa’a biyu da rabi kacal
zakuyi abangaren kudu ku fice daga cikin
wannan nahiya gaba
wadannan hadiman nawa suna tare dani
zamuyi
muku rakiya izuwa iyakar kasata da nahiyar
dake
gaba kuma zamu kawar da duk wata shaida
da
zata nuna sawunku ko wata alama ta cewar
an
fita daga garinnan
yanzu sai kuyi sauri ku dauki kayanku mu tafi
domin bamuda isasshen lokaci koda
sarauniya
anisa tazo nan azancenta sai jarumi hatyan
yaji
wani irin bakin ciki ya turnukeshi badon
komaiba
sai saboda ya ayyana aransa cewa takowanne
hali sai ya kaiwa sarki shamsal harin bazato
har
masaukinsa
ba tareda wata gardamaba sai hatyan da
sadirat
suka dauko jakunkunansu
anisa da hadimanta guda uku suka yi musu
jagora suka fice daga cikin gidan sarautar ta
wata barauniyar hanya wacce komai
kwakkwafin
mutum bai isa ya iya gano akwaitaba
can bayan gidan sarautar bangaren kudu
suka
fito ta karkashin kasa kuma ta cikin wani
rairayi
wandaya lullube wata kofar katako
dafitowarsu sai suka mayarda kofar suka rufe
rairayi ya lullube tamkar bata taba
wanzuwaba
agurin
tuni sun iske wadansu kosassun dawakai
guda
shida daure awajen suna harbin iska
akan dawakai biyu akwai guzuri na matafiya
kawai sai sarauniya anisa ta dubi hatyan tace
ku kama wadancan dawakan biyu masu
dauke da
guzuri ku hau sune naku
kafin dayansu yayi wani yunkuri tuni anisa ta
kama daya daga cikin ragowar dawakan ta
hau
koda hatyan yaga irin hawan dokin da tayi
sai ya
kamu da mamaki domin da gani kasan cewa
ta
kware kuma sai manyan jarumaine suke yin
irin
wannan hawan
alokacin da tayi tsallene rigar jikinta ta
bayyana
tana sanye da matsatstsun tufafi na fatar
damisa
wadanda suka bayyana gaba dayan siffofinta
kuma a sannan ne gashin kanta dake daure
ya
zubo kasa harkan duga duganta
koda jarumi hatyan yayi arba da wannan
kyakkyawar sura tata saiya dimauce
domin a sannan ne ya gane cewa tafi
sarauniya
badi’atul nauwara komai na kyan sura, kyan
fatar
jiki da kuma kyawun fuska
batare da bata lokaci ba suka sukwani
dawakan su
da gudu izuwa cikin daji sarauniya anisa ce
akan
gaba
ai kuwa nan da nan ta baiwa su hatyan
tazara
mai yawa sadirat ce acan karshen baya
sannan hadimanta guda uku, tsakanin
dokinta
dana hatyan akwai tazarar kimanin taku
ashirin
koda ganin haka sai shima ya karawa nasa
dokin
kaimi ya zabureshi da gudun gaske
koda anisa ta fiskanci cewa hatyan ya karawa
dokinsa kaimi don ya kamota sai itama ta
karawa
nata dokin kaimi
nan danan tazarar dake tsakaninsu ta sake
ninkawa takai kusan taku arba’in
koda sadirat da sauran hadiman sukaga an
musu
nisa sai suka kara zage dantse
lokacinda hatyan yayi iya yinsa yaga ya kasa
kamo sarauniya anisa saiya fusata ya daka
tsalle
sama daga kan dokinsa ya dirgo kasa yaci
gaba da falfalawa da gudu da kafafunsa shi
kuwa
shikuwa dokin nasa saiya bishi a baya
wohoho! wanda Allah ya baiwa kyautar baiwa
babu
yadda za’ayi dashi sai kallo
kafin cikar dakiku arb’in tuni hatyan yazò ya
gifta
sarauniya anisa akan dokinta harya bata
tazarar
data bashi
yana riskarta yayi mata murmushin sai kinzo
hatyan yaci gaba da gudu har izuwa wasu
dakiku masu yawa
kwatsam ba zato ba tsammani saiyaji taku
bayansa
al’amarin dayai matukar bashi mamaki
kenan
domin shi azatonsa babu wani doki ko
bil’adama
da zai iya cimmasa agudu face sarki shamsal
nan take yaji zuciyarsa tadan buga da karfi
kawai
saiya tsaya ya juya domin yaga kowanene ke
shirin cimmasa
ba zato ba tsammani sai yaga ashe anisace
itama ta duro daga kan dokinta itama taci
gaba
da gudu
cikin matùkar mamaki yayi sauri yaci gaba da
gudun don karta wuce she
nan dai suka jera sai gashi ya kasa tsere
mata
al’amarin dayai matukar bashi mamaki
kenan
waishin dama akwai wanda yake da. irin
baiwar
da muke da ita nida sarki shamsal?
saida suka shafe kusan rabin sa’a suna
gudu
sannan ne sarauniya anisa ta fara rage karfin
gudunta
koda ganin haka sai hatyan yayi murmushi
yasan
cewa adade anayi sai gaskiya
kuma sai miya ta kare sannan ake sanin maci
tuwo
ko tafiyar dakika goma basù karasaba sai
kawai
yaga anisa ta zube kasa sharaf tana haki
sai hatyan a kyalkyale da dariya yace
iyakar juriyar taki kenan a gudu
kodajin haka sai anisa ta maida masa da
martanin dariya ta dubeshi alokacin daya
zauna
dishan daf da ita yana haki tace
ai nan ne daf da iyakar nahiyarmu da
nahiyar
dake gabanmu
daganan tafiyar sa’a shida kachal zakayi ka
shiga
nahiyar kasashen bakaken fata
kodajin wannan batu sai hatyan ya jiwata irin
matsanaciyar damuwa tazo masa tamkar
yace
ya fasa ci gaba da tafiyar
waishin rabuwa. da anisa ce bayaso kokuwa
ya
gaji da wannan gudun ceton ran da
sukeyine?
amsar daya kasa baiwa kansa kenan
duk su biyun sai sukayi shiru har izuwa
tsawon
yan dakiku adaidai wannan lokacine suka
fara
hango hadiman anisa da sadirat bisa dawakai
daga chan nesa da kuma nasu dawakan guda
biyu
hatyan yayi ajiyar numfashi yana mai dan
sunkwui dakai kasa yace
yake wannan sarauniya yanzu gashi zamu
rabu
kuma banida tabbacin zamu sake saduwa a
wannan rayuwa keda kawarki badi’atul
nauwara
kunyi mana taimakon da bamu da abinda
zamu
saka muku dashi nida yar uwata
kodajin wannan batu sai tayi murmushi tace
ai
rabuwarmu anan ba itace rabuwarmuba duk
inda
kuke muna tare daku kada ka damu abu
daya
nake so dakai
ka zamo mai halacci kuma kayi hukunci bisa
adalci ga duk mutuminda mu’amala ta
hadaka
dashi
kaso mutum gwargwadon yadda yasoka abu
na
karshe ka kula da kanka karka bayarda
zuciyarka
ga kowa sai wanda ka tabbatar da cewar
shine
yafi dacewa dakai
sa’adda anisa tazonan azancenta sai jarumi
hatyan ya dubeta cikin matukar mamaki
gami da
rashin fahimta yace
ya shugabata gaskiya kin batar dani ko ince
wadannan maganganun naki sunfi karfin
fahimtata
shin zaki fahimtar dani?
dajin haka sai anisa tayi murmushi tace
kada ka damu da sannu zaka fahimci komai
anan
gaba
abu na karshe dazan sanar dakai shine idan
ka
isa gari na gaba kada ka yarda da kowa face
wanda ka karanci halayyarsa,, ka fahimceshi
amatsayinka na bako duk inda ka shiga ka
boye
baiwarka kuma ka kankantar da kanka ga
jama’ar
gari ta hakane kadai zaka san sirrin gari da
jama’ar sa
ka jajurce wajen neman halak babu ruwanka
da
haram
ko zalunci kayi taimako ga mai bukatarsa ka
zamo mai tausayi da jin kai
hakan zaisa kasake nasara bisa duk abinda
kasa
agabanka
daga yau ka jajurce wajen bawa kanka horon
yaki da fada idan har kanason kadauki fansar
ran
iyayenka akan sarki shamsal
domin karo dashi sai an shirya koda kuwa
shekarunka sunkai lokacinda da bokaye ke
fadi
da wannan furuci nake yi maka bankwana sai
mun sake saduwa nan da wani lokaci kadan
domin
lokacin komawata birnina yayi domin
hadiman
sarki shamsl masana bincike sun kusa
karasowa
gama fadin hakan keda wuya sai gasu sadirat
sun
iso nantake hadiman nan uku suka fara goge
sawayen dawakan nasu
ita kuwa anisa saita rungume sadirat tana
mai yi
mata ban kwana
taja dokinta ta kama ta hau ta zabureshi da
gudu
alokacin da hatyan ya bita da kallo zuciyarsa
cike da wasu tambayoyi gamida rashin
fahimta
su kuwa hadiman nan uku sai suka ci gaba
da
aikinsu na share sawayen dawakan kuma
kowannensu na ruke da dokinsa ar sukayi
nisa
da ganin haka sai hatyan da sadirat suka
kada
dawakansu suka tsallaka nahiyar suka nausa
cikin daji
KU SHA RUWA mukoma bakin fahama
zamushiga
LITTAFI NA 6

TARKON MUTUWA

Littafi na Shida 6
Part 6 A
.
.
Sarauniya badi'atul nauwara nata faman sharar
barci akan gado sai kawai taji hasken ranaya
dallare mata idanu
tana bude idanun ta kuwa sai tayi arba da
kawarta sarauniya anisa zaune akan kujera daf
da gadon da take kwance ta kura mata idanu
tana yi mata murmurshi
badi'atul nauwara ta mike zaune zumbur ta
dubi
anisa cikin kaduwa da firgici tace
me ake ciki? ina su hatyan? ina fatan dai asirin
mu bai tonu ba
kodajin haka sai anisa ta kyalkyale da dariya
Sannan tace
ai tuni su hatyan sun shiga wata nahiyar babu
yadda za'ayi sarki shamsal ya sake ganin su
sai dai kawai zasu iya haduwa da mugayen
tarkunansa akan hanyarsu yanzu kece kadai
matsalata
cikin firgici badi'atul nauwara ta sake duban
anisa tace
tayaya akayi na zama matsala agareki?
anisa tace nan da cikar sa'a daya jal kwararrun
hadiman sarki shamsal zasu iso masa bincike
tabbas zasu iya gano wannan daki da kike ciki
yanzu
kinga kuwa idan suka ganki zargi ya tabbata
akan mu
hanya dayace zamu bi mu kawar da wannan
matsala
cikin zakuwa badi'atul nauwara ta ce wacce
hanya ce kenan?
anisa tace dolene mu batar da kamanninki
yadda
babu mai shaidaki
hakan bazai taba yiwuwa ba face mun shafe
gaba
dayan jikinki da bakin lalle wanda sai an kwana
bakwai ana wanke shi sannan zai fita tabbas
idan aka shafe ki dashi zata za'ayi ke bakar
fatace kuma komai kwakkwafin mutum bai isa
ya
iya shaidaki ba
sai bayan sarki shamsal ya bar garinnan sannan
za'a wanke miki wannan lalle
kodajin wannan batu sai hankalin badi'atul
nauwara ya dugunzuma ainun saboda ko kadan
batason abinda zai taba lafiyar jikinta kai gani
takema kamar idan aka shafe ta da wannan
lalle
shikenan har abada haka zata kasance
amatsayin bakar fata
yayin da anisa ta lura da wannan damuwa tata
saita dubeta cikin murmushi tace
indai kin yarda dani amatsayin aminiyarki to ki
cire duk wata damuwa dake ranki ko kuwa kina
tunanin cewa zan iya cutar dake ne?
kodajin wannan tambaya sai anisa tayi
murmushi
cikin yake tace
haba yake kawata ai amana guda daya ce
nayarda a shafeni da wannan lalle amma ina
neman alfarma guda daya
ki sani cewa inbanda mahaifiyata duk fadin
duniyar nan babu wanda ya taba ganin
tsiraicina
don haka wanda duk zaiyi wannan aiki inason
ya
kasance macece kuma mai shekaru irin na
mahaifiyata...hmmmmm amma banda matan
yanzu duk
samari sungama......
kodajin wannan batu sai sarauniya anisa tayi
murmushi tace
aikuwa kamar kin sani mai wannan aiki wata
kwararriyar macece wadda ahalin yanzu
shekarunta sunkai arba'in da shida duk duniya
babu wanda yakaita kwarewa a iya kunshi kuma
itace ta kirkiri wannan lalle da kanta
yanzun nan zata zo tayi miki wannan aiki ba
tareda bata lokaciba
gama fadin hakan keda wuya say sarauniya
anisa
ta kama hannun sarauniya badi'atul nauwara
suka mike tsaye tare sannan ta jata suka fice
daga cikin dakin suka nufi wani bangare daban
na gidan sarautar
yar gajeriyar tafiya sukayi suka iso kofar wani
karamin daki da zuwansu sai suka tsaya chak
anisa ta dubi badi'atul nauwara ta tura kofar ta
shiga tana shiga sai zuciyarta ta buga da karfin
gaske sakamakon yin arba da ummul khairi
bakomaine ya haddasa hakanba face kasa gano
inda tasan wannan mata
tabbas ta taba ganinta a wadansu shekaru da
suka shude kuma tafi tunanin cewa tana yarinya
ne karama
nandai badi'atul nauwara ta turo kofar dakin
tasanya sakata da hannunta alokacin da ummul
khairi ta dago kai ta kura mata idanu tanayi
mata
murmushi
amma idanunta cike suke da kwallah
al'amarin dayai matukar kada sarauniya
badi'atul
nauwara kenan kuma ya bata mamaki
don haka batasan sa'adda ta durkusa kasa
agabantaba ta dubeta cikin girmamawa tace
yake wannan ma'abociyar kunci ina dalilin
zuwan
kwallah a idanunki sakamakon ganina?
sa'adda ummulkhairi taji wannan tambaya sai
hawayenta ya zubo tace
yake 'yata yanzu ashe dama 'ya zata iya
mantawa da uwarta?
rabona dake tun sa'adda da mahaifiyarki ta
kawo
ziyarar karshe nan garin
nice wacce tayiwa mahaifiyarki kunshi da kitso
harya zamana cewa munshaku ainun dake
agidana kike kwana dare da rana bama rabuwa
idan ban mantaba idan an bude gashinki akwai
wani tabon ciwon kuna da kika yi adakina da
wutar jin dumi alokacin da ake wani hunturun
sanyi
koda gama fadin hakan sai ummulkhairi ta yiwa
badi'atul nauwara nuni da wani katon madubi
dake manne ajikin bango tacè
jeki gaban wancan madubin ki kwaye keyarki
mu
gani
batareda wata gardamaba sai badi'atul nauwara
taje gaban madubin ta juya masa baya ta kwaye
gashinta daya zubo kasan keyarta ai kuwa saiga
wannan tabon wutar
nantake ta tuno da inda abin ya faru
alokacin batafi shekara bakwai ba aduniya
gama tunanin keda wuya sai badi'atul nauwara
ta ruga izuwa ga ummul khairi ta rungumeta
tana
mai zubar da hawaye tace
tabbas ke uwace agareni domin tun ina karama
kin wanke dukkan jikina bainda wata fargaba
atare da ke
tana gama fadin hakan ta kama cire tufafin
jikinta
da kanta har sai da tayi zigidir agaban tsohuwa
ummulkhairi ita kuwa ummulkhairi saita dauko
wani akushi cike da wani bakin lalle mai kyalli
da maiko na musamman ta kama shafeshi
adukkan jikin sarauniya badi'atul nauwara
da zarar ta shafa lallen sai badi'atul nauwara
taga nan take lallen ya bushe ajikinta
kuma ya saje da fatarta tamkar dama can bakar
fatace ba faraba
al'amarin dayai dugunzuma hankalinta kenan
jikinta ya fara kyarma amma sai ummulkhairi ta
dafa kafadarta tace
kwantar da hankalinki yake 'yata kiyi sani cewa
ina wanke wannan lalle kamar yadda ruwa yake
wankè datti ajikin tufafi
dajin haka sai hankalin badi'atul nauwara ya
kwanta ta saki jikinta akaci gaba da shafeta
kafin rana ta fadi tuni hadiman sarki shamsal
kwararrun iya bincike sun hallara abirnin
askandariya
sudai wadannan hadimai su dari da ashirin da
dayane kuma an zabosune daga kasashe daban
daban acikinsu mutum dayane jal aka dauko
daga birnin bindal
gaba dayansu tsofaffin dakarun yakine wadanda
suka kware wajen iya leken asiri kuma kallo
daya
zakayi musu kasan cewa yan duniya ne
wadanda
sukaga jiya sukaga yau
kuma sukasan dukkan kissa da tuggun rayuwa
da isowar wadannan hadimai sai aka yi musu iso
har cikin fadar sarauniya anisa inda ta taresu
hannu biyu ta shaida musu cewa ubangidansu
sarki shamsl yanzu haka yana chan ma
$aukinsa yana barci sakamakon ya kwana yana
bincike da kansa abirnin
kodajin wannan batu sai shugaban hadiman
wani
dattijo dan shekara saba'in wanda duk gashin
jikinsa farine fat babu baki sai yayi ajiyar zuciya
cikin takaici saboda yasan cewa sarkì shamsal
ya tafka kuskure na farko
nandai saraunya anisa ta dubi shugaban
hadiman
tace
yanzu za'akaiku masauki domin ku je ku kwanta
ku huta kuma a kawo muku abinci
dajin haka sai shugaban hadiman yace
a'a ranki y dade ai dokar wannan aiki namu
bamacin abincin kowa sai wanda mukazo dashi
...............
..anan zantsaya kada nacikaku da surutu dan
haka kowa
yan sirara yasaki ransa yahuta kafin muci gaba
da
sankamowa.
TARKON MUTUWA
Littafi na Shida 6
Part 6 B
.
.
Muna fatan zaki bamu hadin kai bisa duk abin
da
muka bukata domin idan kika ki
za'a iya samun sabani tsakanin ki da mai girma
sarki shamsal
lokacin da shugaban hadiman yazo nan
azancensa sai zuciyar anisa ta buga da karfi
domin ta fahimci cewar ta hadu da tsohon dan
duniya wanda zai iya tono asirinta amma sai ta
dake bata nuna alamar karayar taba ta dubi
Tsohon da kwarin guiwarta tace
zan baku cikakken hadin kai amma bisa irin
sharadin da ke tsakanina da sarki shamsal
sharadin kuwa shine ban yarda

Please Login or Register in order to submit comment