Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su ritsaku acikin tekun nan su
hallakaku .
kuyi hakuri da ban iso akan lokaciba har sarki
shamsal yaci karfinku ya kusa hallakaku
adai dai wannan lokacine jirgin ya iso bakin
wannan gaba
koda ma'aikatan sukayi arba da sarauniya
badi'atul nauwara sai suka zube kasa suka
kwashi gaisuwa
nantake sarauniya badi'atul nauwara taja
shugaban ma'aikatan gefe daya suka tattauna ba
tare da bata wani lokaci ba aka shiga cikin
jirginnan aka dauki jarumi hatyan aka shigar dashi
cikin wani keken dokin suka zauna akaja aka
tafi dasu izuwa cikin gari.
tafiyar su keda wuya sai ma'aikatan tashar jirgin
suka janyo wannan jirgin wanda su hatyan
sukazo a cikinsa izuwa gefe daya suka cinna
masa wuta harsaida ya kone kurmush
tokarma sai aka kwasheta duka aka watsa ta
acikin tekun yadda babu wata shaida da zata
nuna alamar cewa akwai alamar jirgin da yazo
wajen.
al'amarin su sarauniya badi'atul nauwara kuwa
lokacin da suka baro bakin tashar jikin ruwan sai
suka ci gaba da tafiya ba sassauci
harsuka iso birnin askandariya
wani abu daya daurewa hatyan kai shine duk da
cewar ko ina ga hotunansu nan amanne acikin
birnin,jikin katangun,bishiyoyi ,da gidaje kuma
basa yin tafiyar data wuce rabin sa'a ba tare da
sun iso inda dakarun birnin keyin bincike ba
amma duk inda sukazo da zarar anga wannan
keken doki da suke ciki sai abasu hanya
su wuce ba tare da an bincikesu ba
ko cikin keken dokin ba ba'a lekawa
bisa wannan daliline sadirat ta kasa hakuri ta
dubi sarauniya tace
ya shugabata ni fa wani abu ya shige mini duhu,
me yasa tun a bakin tashar jirgin ruwan nan banga
an tuhumemuba
alhalin gashi ko'ina an baza hotunan mu nida
dan'uwana ,ana nemanmu ruwa ajallo?
yanzu ma da muka shigo cikin garin nan naga an
zuba tsaro ko'ina
wasuma daga cikin dakarun idan suka leko waje
daga cikin keken dokin ina hada idanu dasu
amma sainaga sunkawar da fuskarsu sunci gaba
da harkokinsu.
koda sadirat tazo nan azancenta sai sarauniya
badi'atul nauwara ta kyakyace da dariya sannan
tace
ai mulkin babban birni mai tarin al'umma da
karfin arziki anahiyar nankaf banda birnin bindal
babu birnin dayafi nawa daukaka shikansa
wannan birnin na askandariya yana kasan nawa
kuma sarauniyarsu kawata ce
aminiyata tun kuruciya akwai zumunci mai karfi
atsakaninmu tun iyaye da kakanni.
tunu na tattauna da ita akan matsalarku kuma
mun gano cewa zaluntarku sarki shamsal yayi
hatta kashe iyayenku da dansa yayi da kuma
yunkurin yi miki fyade duk munje munbi diddigin
komai bisa wannan daliline muka dauki alkawarin
taimakon ku har izuwa lokacinda zaku sami
damar ficewa daga wannan kasa
Dukda cewa jarumi hatyan na cikin mawuyacin
hali na rashin lfy,ko kyakkyawan motsi baya
iyawa
amma tunda ya farajin muryar sarauniya badi'atul
nauwara sai farin ciki ya turnukeshi ,yayi ta satar
kallonta ,da zarar yaga ta juyo zasu hada idanu
sai yayi saurin kautar da idonsa haka dai
sarauniya badi'atilnauwara da sadirat sukaci gaba
da hira har suka iso gidan sarautar birnin
askandariya
gidan sarautar yakawatu ainun kamar yadda aka
kawata gidan sarautar sarauniya badi'atul
nauwara
da isowarsu tsakiyar harabar gidan sarautar dai
suka iske sarauniya anisa a tsaye tare da
hadimanta da kuyanginta suna jiran isowarsu,
nan take aka fiddo jarumi hatyan daga cikin
keken dokin aka dorashi akan wani gado mai
kama da makara aka shige dashi izuwa gidan
sarautar
koda akazo giftawa dashi ta gaban sarauniya
anisa sai tayi masa kwakkwaran kallo guda daya
ta yi murmushi.
sannan ta kautar dakai ta nufi inda sarauniya
badi'atul nauwara take ta rungumeta cikin farin
ciki tana mai cewa
lale marhaban da babbar kawata kuma babbar
aminiyata awannan lokaci,
tuni sadirat tabi hadiman da suka dauki hatyan
da sauri abaya.
sarauniya anisa ta kama hannun sarauniya
badi'atul nauwara tajata suka nufi turakarta suna
tafe suna hira cikin nishadi da farinciki tamakar
'yan uwan da suka jima basuga junaba.
da isowarsu cikin turakar sai aka kawowa
badi'atul nauwara abinci da abinsha sama da
kala goma sha tara aka zube agabanta bisa
wani babban teburi take sarauniya anisa tayi
mata tayi har badi'atul nuwara ta yagi cinyar
kaza takai bakinta da nufinta ci,saita fasa ta
ajiye
al'amari da yayi matukar baiwa sarauniya anisa
mamaki kenan ta dubeta tace
me yasa kika ki cin abincin?
badi'atul nauwara tace
tayaya zan iya cin abinci ba tareda abokan
tafiyarmuba
maza kisa akaini inda aka kaisu domin naga halin
da suke ciki,
ina fatan dai tuni kin baiwa likitocin umarnin suje
su duba lafiyar jikinsu?
kodajin wannan batu sai sarauniya anisa ta
kyalkyale da dariya tace
kawata kenan lallai idan kaga kare yana lasar
takalmi to dauka zaiyi
damuwarki akan hatyan ta fara yin yawa ,anya
kuwa baki kamu da sonsa ba?
kodajin wannan tambaya sai badi'atul nauwara
tayi murmushi sannan tace
da ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki?
tsananin tausayinsu ne yasa nake damuwa da
al'amarinsu kin sani cewa na tsani zalunci
mun dade ni dake muna tunanin hanyarda zamu
bi mu kawar da zalunci awannan nahiyar amma
mun kasa saboda al'amarin yafi karfinmu.
masana da masu bincike sun gano cewa wannan
yaro hatyan shine zai kawo sauyin komai
awannan nahiya bisa wannan daliline na siyar da
rayuwata kuma nayi karambanin wasa da
karagata domin ceto rayuwarsa
kinsani cewa idan sarki shamsal ya gano cewa
ina da hannu akan taimakon su hatyan
saiya yakeni ya rushe mulkina ya dawo da
birnina karkashin nasa
yanzu ke atunaninki duk nayi wadannan abubuwa
ne saboda soyayya?
sarauniya anisa tayi dariya akaro na biyu tace
babu abinda mutum bazai iya yiba akana soyayya....wlh
kuwa ko nima ina yin fin hakan indai akan so ne ni
auwzab badaga nan ba
.
amma babu komai ai sannu bata hana zuwa
saidai adade ba'aje ba
shi so baya buya komai daren dadewa sai ya fito
fili.
abu na biyu da nakeso na sani shine yanzu ba ke
kadai bace acikin tarkon sarkin shamsal ba.
nima ina ciki tunda na baiwa su hatyan masauki
nasa akula da lafiyarsa,kuma na boye shi
atakaice dai ni dake yanzu duk masu laifine duk
hukuncin da za'a yanke miki nima shi za'a yanke
mini.
koda gama fadin haka sai sarauniya anisa ta mike
tsaye ta kama hannayen sarauniya badi'atul
nauwara ta rukesu tace
kwantar da hankalinki yake kawata kiyi sani cewa
har abada asirinmu bazai tonuba awajen sarki
shamsal.
da farko kije ki ziyarchi kabarin iyayenki
ki yi musu addu'a saboda babban kokarin da
sukayi miki ya zamana cewa bakyayin tsafi kuma
baya tasiri ajikinki.
wannan daliline yasa sarki shamsal bazai taba
gano cewa kece kika ceci su hatyanba.
sannan duk wata shaida da zata nuna akwai
hannunki ataimakon hatyan na
gogeta,baza'a taba ganintaba.
hatta jirginki wanda su sarki shamshal suka gifta da
shi asama lokacin da suke kan jibgegen tsuntsun
tsafi .
idan sukazo garinnan sai sunyi bincike akansa.
nasani cewa kinbar jirgin ya nutse a karkashin
ruwa.
don haka tuni na tura an dauke jirgin daga
karkashin ruwa an batar dashi sannan kuma nasa
an kera irinsa sak.
an kawoshi bakin tashar jirgin ruwan garinnan
yadda idan su sarki shamsal sunzo zasu riske shi
kuma nashirya komai zasu tarar da cewa jirgin na
fatakene.
duk irin binciken da sarki shamsal zaiyi bazai iya
gano komaiba.
a yanzu haka suna tafe izuwa birnin nan.
shi da kansa, boka daizur amma babu abinda zai
faru.
harsu gama bincikensu su kara gaba.
ni kawai tashin hankalina daya ne sarki shansal
bazai daina bin su jarumi hatyanba.
kuma bazai daina farautarsuba.tabbas akan
hamyoyinsu ma na gaba sai ya dana tarkunan
mutuwa na farautarsu
wadanda sai da tsananin rabo ne zaisa su tsira da
rayukansu.
lokacin da sarauniya anisa tazo nan azancenta sai
badi'atul nauwara ta kawo gwauron numfashi ta
ajiye sannan tace
hakika duk abinda kika fada gaskiyane to amma
muddin ni dake zamuci gaba da basu kariya aduk
inda suke babu abinda zai samesu.
kisani cewa tsiransu shine tsiranmu domin duk
ranar da suka fada hannun azzalumi sarki shmsal
muma asirinmu ya tonu domin zai sami damar
ganin duk irin taimakon da muka basu.
koda jin wannan batu sai hankalin sarauniya
anisa ya dugunzuma ainun tayi shiru tana
nazarin al'amarin acikin zuciyarta.
abinda nakeso dake shine ki yi mana tunani akan
hanyar da zamubi muci gaba da bawa su hatyan
kariya har zuwa lokacin da hatyan zai koma
birnin bindal ya dauki fansar abinda akayi masa.
nima zanje nayi nawa tunanin daga yau
zuwa kwanaki uku in yaso sai kowannan mu yazo
da tunaninsa
muga yadda zamu hada karfi da karfe don cikar
burin mu.
yanzu zanje na kwanta na huta don kawarda
gajiyar tafiyar dake tare dani.
koda gama fadin haka sai sarauniya badi'atul
nauwara ta juya ta fice daga cikin turakar
sarauniya anisa ta nufi inda masaukinta yake
wanda ya kasance wani kasaitaccen gida acikin
gidan sarautar inda aka saba bata aduk sa'adda
ta kawo ziyara wannan gida
akwai kuyangi, barori da kuyangi da hadimai da
sauransu
PLS LIKE AND COMMENTS
TARKON MUTUWA

Littafi na hudu
Part 4 B
.
.
Tawuce tashiga masaukinta ta kwanta
amma sai takasa
bacci saboda tinanin su jarumi hatyan sai
tai karo da
shugaban dakarun da yake gadin gidan
yace ina zataje
haka??
Kodajin wannan tambaya sai sarauniya
badiatul
nauwar tayi murmushi tace ba wata
matsala,
kawai dai nakasa barcine shine na yanke
shawarar na fito na kaiwa abokan tafiyata
ziyara
domin naga halin da suke ciki musamman
ma
maralafitar
kodajin wannan batu sai shugaban dakarun
yayi
dan guntun murmushi yace ai suma yanzu
barcin sukeyi da dai zaki hakura saida safe
zaifi
miki kyau
badi'atul nauwara ta gyada kai tace a'a na
damu
kwarai ko kallo daya nayi musu zai wadatar
basai na tashesuba,
na rokeka dakayi mini jagora izuwa
masaukin
nasu domin ni ban saniba
ba tareda wata gardama ba shugaban
dakarun ya
juya ya nufi wani bangare na daban na
gidan
sarautar,, badi'atul nauwara na biye dashi
abaya,
koda suka iso inda masaukin su hatyan yake
sai
badi'atul nauwara taji zuciyarta ta buga da
karfin
gaske kuma nan take hankalinta ya
duguzuma
ainun fiye da koyaushe ,
ba komai ne ya janyo hakaba face tsananin
kishi
gamida tsananin mamaki,
abindaya fara fado mata arai shine yanzu
dama
akwai wannan kasaitaccen guri acikin gidan
sarautar nan, amma anisa bata taba
saukata
acikinsa ba duk da irin amanar dake tskanin
mu?
gama yiwa kanta wannan tambaya keda
wuya sai
taga ashe sabon gini ne abindaya kara
firgita ta
kenan tace aranta
tabbas anisa tana son hatyan to amma
yaushe ta
fara sonsa alhalin ma bata taba ganinsa ba
sai
yau din nan?
hakadai badi'atul nauwara tacigaba da
wannan
zargi acikin zuciyarta har suka iso masaukin
kai tsaye shugaban dakarun ya nuna mata
kofar
shiga turakar dasu hatyan ke kwance ya
juya ya
barta awajen
cikin sanyin jiki ta nufi kofar ta murda
mabudin
kofar ahankali ta dan jawo kofar kadn
koda ta leka ta hango hatyan tare da
yar'uwarsa
sadirat kwance akan gado suna ta faman
sharar
barci sai zuciyarta tayi sanyi nan take taji
wani
irin farinciki ya lullube zuciyarta saida
sarauniya
badi'atul nauwara ta shafe kusan sa'a guda
tana
mai kurawa hatyan idanu tana murmushi
batareda tasan cewa ta dade awajenba
gyaran muryar shugaban dakarun ce yasa
ta
firgita kamar wacce ta farka daga barci ta
waigo
ta dubeshi afirgice
shugaban dakarun ya rissina kansa na
kallon
kasa yace
ranki ya dade kin dade anan a tsaye gashi
har
alfijir yakusan ketowa.
daji haka sai badi'atul nauwara taji kunya ta
kama hamma da yake tasan cewa baisan
abinda
take kalloba sai tayi murmushi tace hakane
ai
hakanne kadai zai deben kewar rashin
barcin yau
tana gama fadin hakan saita juya ta koma
masaukinta ta kwanta
wani ikon Allah kuwa kwanciyarta keda
wuya ta
kama gyangyadi.
kafin cikar wasu yan dakiku barci mai nauyi
ya
saceta inda ace wani ya shigo cikin dakin
awannan lokaci da ba karamar kunya
zatajiba,
domin ambaton sunan jarumi hatyan takeyi
acikin
mafarki.
barcin sa'a daya da rabi kacal badi'atul
nauwara
tayi kawai sai taji ana tashinta afusace ta
bude
idanunta da nufin taga wanda ya tasheta
da fada
cikin mamaki sai taga ashe sarauniya anisa
ce
da kanta take tashinta,
cikin hanzari gami da mamaki badi'atul
nauwara
ta mike zaune ta dubi anisa tace
lafiya kuwa na ganki a daki da sassafe
haka?
anisa tayi dan guntun murmushi cikin
alamun
yarda da kai tace
sarki shamsal tareda dakarun sa da bokansa
sun
iso nan da kankanin lokaci zasu iso fadata
kodajin wannan batu sai badi'atul nauwara
ta
firgita domin bata taba jin zuciyarta ta buga
da
karfiba irin yanzu tamkar bata kasance
jaruma ba
koda anisa ta fahimci hakan saita kyalkyale
da
dariya sannan ta dubeta tace
haba kawata yanzu saboda kawai na ambaci
sunan sarki shamsal saiki firgita haka,,
shin kin mantane cewa ke jarumace ta
gaske
mai tsananin sa'a da rabo bisa duk inda
kikasa
agabanki?
shinkin mantane. cewa tsafi baya tasiri
ajikìnki?
banga dalilin da zaisa ki daga hankalinkiba
tunda
baki da tsautsayi
kodajin wannan batu sai badi'atul nauwara
ta
gyada kai tace
ni bana shakkar duk abinda zai sameni
tunda duk
tsuntsun daýaja ruwa shi ruwa ke duka
tsorona shine abinda zai sami hatyan da
yar'uwarsa sadirat zaifi kyau na rasa
rayuwata
amaimakon rayuwarsa ta salwanta.
sa'adda sarauniya anisa taji wannan batu
sai
tadanyi dan murmushi mai kama da yake
sannan
ta dafa kafadarta tace ki kwantar da
hankalinki
yake 'yar uwata kiyi sani cewa babu abinda
zai
sameki ko hatyan da'yar uwarsa sadirat
muddin
ina kina tare damu ayanzu shine abu na
narko da
zai fara rufa mana asiri tunda tsafin su sarki
shamsal bazaiyi tasiri ba.
ahalin yanzu tuni na boyesu jarumi hatyan
da'yaruwarsa sadirat acikin wannan gidan
sarautar a inda babu mai iya ganinsu komai
irin
tsananin binciken da zasuyi don haka kema
zam
boyeki a irin wannan wuri tashi muje na
kaiki.
cikin sauri badi'atul nauwara ta bi sarauniya
anisa a baya alokacinda ita anisa ta surfafi
bangon kudu na cikin dakin
da isarsu sai anisa ta shafi wani zane na
tsuntsun dawisu take bangon dakin ya rabe
gida
biyu sai ga wata hanya zururu izuwa cikin
wani
gidan kasa, maidauke da matattakalar bene
kawai
sai anisa ta dubi badi'atul nauwara ta ce
nagina wannan wurine saboda irin wannan
rana
ta yau kishiga ciki zaki sami komai dakike
bukata
koda zaki zauna acikinsa babu abinda zaki
rasa
saidai kawai kadaici dazai sameki,
cikin tsananin alamun damuwa badi'atul
nauwara
ta dubi anisa tace
meyasa bazaki kaini can inda kika boye su
hatyan ba na kasance tareda su.
wai shin me yasa kika ba su masaukin da
yafi
nawa daraja?
anisa ta sake duban badi'atul nauwara cikin
murmushi a karo na biyu tace
kiyi hakuri kawata ayanzu bani da lokacin
dazan
iya yi miki cikakken bayani
amma da zarar sarki shamsal da bokansa
sun
gama binciken su sun tafi zamu zauna kiji
bayanin komai,
kin san koni wacece kuma kin yarda dani
dari
bisa dari har abada bazan taba cutar
dakeba,
kamar yadda kema bazaki cutar daniba,
don haka kawai kiyi duk abinda na umarceki
dayi.
kodajin haka sai badi'atul nauwara ta juya
tabi
cikin wannan bango daya bude ta taka
matattakalar bene izuwa gidan kasa ita
kuwa
sarauniya anisa sai ta sake shafar saman
wannan zanen tsuntsun dawisu
nan take bangon daya rabe biyu ya koma
ya hade
tamkar bai taba rabuwa ba
faruwar hakan keda wuya sai sarauniya
anisa ta
juya da sauri ta fice daga cikin wannan
turaka
tana fita ta iske dakarunta masu take mata
baya
da kuma manyan hadiman ta suna jiranta
nantak suka rufa mata baya izuwa fadarta
tuni a wannan lokaci sarki shamsal da boka
daizur
sun iso cikin gidan sarautar sarkin fada yayi
musu jagora izuwa cikin fadar
sarauniya anisa tana zaune bisa karagar
mulki ga
fadawanta da sauran jama'arta sun
kewayeta
ana tafiyar da harkokin mulki saiga boka
daizur
da sarki shamsal sun shigo cikin fadar sarkin
fada nayi musu jagora
tun daga nesa da sarauniya anisa ta hango
su ta
mike tsaye daga kan karagar mulkinta
fuskarta
cike da annuri da gami da murmushi tatari
su sarki
shamsal tana mai nuna tsananin farincikinta
da
ganinsa
koda ta iso daf dashi saita kama hannun
sarki
shamsal na dama ta sumbaci saman
hannun
cikin girmamawa tace
lale marhaban da sarkin sarakuna kuma
jarumin
jarumai na wannan nahiya gaba daya,
ya shugabana banyi mamaki da wannan
ziyara
takaba ta bazato tunda kana farautar
makiyanka
guda biyu
kodajin wannan batu sai sarki shamsal da
boka
daizur sukayi shiru sannan sarki shamsal ya
dubi
anisa yace
hakika kinyi gaskiya yake wannan sarauniya
anisa tace tun dazu da na ji labarin
shigowarka
birnina nasa aka gyara maka masauki kuma
akayi
maka masauki tanadin abincin da kafiso
gami da
ababen sha
akwai tsala tsalan yan mata wadanda suka
kware
wajen debe kewa
kuma akwai abinci da abinsha irin wanda
kafi so
arayuwarka.
kodajin wannan batu sai sarki shamsal ya
tirbune
fuskarsa kamar an aiko masa da sakon
mutuwa
al'amarin dayai matukar razana sarauniya
anisa
kenan taji hantar cikinta ta kada kuma taji
kamar
ta saki fitsari awando amma sai ta dake don
kada
sarki ya fahimci rashin gaskiyarta ta dan
russina
tana mai sunkwuyar dakai kasa tace
ka gafarceni yakai wannan sarki idan
wannan
batu nawa ya bata maka rai
kodajin haka sai sarki shamsal ya takarkare
ya
bushe da dariyar muganta tamkar baya da
wata
damuwa,, lokaci guda kuma sai ya hade
fuskarsa
ya dubeta yace
yake wannan sarauniya kiyi sani cewa a duk
lokacin da muke kan farautar abokan gaba
bama ci kuma bama sha kuma bamayin
nishadi
tamkar zakin dayake fama da
matsananciyar
yunwa kuma yagama karade daji yana
neman
abinci bai samuba
ina mai tabbatarmiki da cewa ni yanzu
babu wani
mahaluki wanda na yarda dashi awannan
nahiya
tamu.
a takaice dai ban yarda da kowaba don
haka
kowa zai iya cutar dani ya boye abokan
gaba ta
danazo nema dakaina cikin wannan birni
naki don na
bincika ko ina da ina,
tun kafin na fara binciken ina mai
shawartarki da
idan kinsan inda wadannan makiya nawa
suke
toki hanzarta fito dasu ki damka minsu
ahannuna
idankuwa kikaki kuma na samesu acikin
birninki
na rantse da gemun mahaifina saina baje
wannan
birni naki gaba daya
nayiwa kasa ado da jinin jama'arki duka ko
kazarku guda daya bazata tsira da
rayuwrtaba,
sa'adda sarauniya anisa taji wannan batu
saita
danyi guntun murmushi mai nuna yarda
dakai
ba tareda alama ta fargaba ba tabbas kowa
agidansa sarkine
cikin jin izzar mulki sarauniya anisa ta gyara
zamanta akan karagarta ta mulki tana mai
dora
kafarta daya bisa dayar
sannan tace
yakai wannan sarki mai daraja kayi sani
cewa
kofofin ko ina da ina acikin wannan birni
abude
suke agareka
domin kayi bincike idan her ka kamani da
wani
laifin boye makiyanka nayi maka alkawarin
zan
kashe kaina agaban idanunka.
kodajin wannan batu sai mamaki ya kama
kowa
da yake wajen
nantake jikin sarki shamsal yayi sanyi amma
sai
sarki shamsal ya sake duban ta cikin
alamun
rashin yarda kuma ya maida mata da
martanin
murmushi na mugunta yace
nayi farinciki da wannan mataki da kika
dauka
ina mai sanar dake akwaì hadimaina
wadanda
suka kware ainun wajen iya bincike
suna nan tafe izuwa wannan birni naki nan
da
gobe da yammaci tare dasu zanyi wannan
aiki
inaso ki bani izini na shiga koina acikin
gidajen
birnin.
TARKON MUTUWA

Littafi na hudu
Part 4 C
.
.
Dajin wannan batu sai sarki shamsal ya yi
kwafa
cikin kunar rai yace
aikuwa indai muka kama su jarumi hatyan
acikin
wannan birni sai na wulakanta wannan
sarauniyar
ainun wulakancin da bata taba ganiba
arayuwarta
nan take shamsal ya juya ya dubi anisa cikin
murmushin yake ya ce
shikenan na amince da wannan sharadi
naki
amma ki sani cewa zan iya fara bincikena
ako
yaushe daga yanzu
kuma ko cikin turakrki ne zan iya shiga
babu
hijabi
dajin haka sai sarauniya anisa tayi
murmushi
ayau dinnan babu wata kofar dakin da za'a
rufe
awannan gidan sarautar hatta kofar dakin
barcina
kuwa inayi maka lale ako yaushe.
anisa na gama fadin hakan saita mike tsaye
daga
kan karagar mulkinta ta dubi sarkin gida
tace
akai sarki da bokansa masaukinsu,, kuma
duk
sa'adda yake son fara bincike kayi masa
jagora
ka nuna nasa ko'ina acikin gidan
sarautarnan
sarkin gida ya rissina yace
angama ya shugabata nan take sarauniya
anisa
ta juya ta nufi kofar fita daga
awannan lokaci sarauniya anisa tana sanye
da
wata doguwar riga irin tasu ta mulki wacce
ta
kasance matsatsiya kuma launinta shudine
anyi
mata adon furanni da zaren zinare
gaba daya surorin jikinta sun fito karara
acikin
wannan riga don haka sarki shamsal baisan
sa'adda ya rudeba,, kuma ya kidime duk da
cewa
shi arayuwarsa mace bata dameshi ba
nan take sarki shamsal ya ayyana aransa
cewa
baitaba ganin mace mai kyauwun surar jikin
anisa ba arayuwarsa
anisa ta kasance kyakkyawar budurwa
kamar
sarauniya badi'atul nauwara amma ta fita
tsawo
da kadan kuma ta fita cikar zati da cikar
sura
tanada yalwar gashin kai na musamman
domin
kalarsa ba baki bane shudine kuma haka
aka
haifeta dashi,
ruwan kwayar idanuntama shudine
wadanda suke
matukar kara mata kyau
bisa wannan daliline ko yaushe anisa
takeyin ado
da shudin sutura
kowa yana al'ajabi da wannan baiwa tata ta
shudin idanu da shudin gashi babu wani da
namiji
dazai yi arba da sarauniya anisa baiji kyanta
da
surar jikinta sun bashi sha'awa ba face ya
kasance mara lafiya
ita kanta tana alfahari da wannan baiwar da
Allah
ya bata hatta yan uwanta mata sunayin
sumbatu
akan hakan,
akwai lokacin da sarauniya badi'atul
nauwara ta
dubeta tace
yake kawata kiyi sani cewa inda ni namijice
to da
saidai na mutu a kokarin samun soyayyarki,
idan kuwa na rasaki saidai na mutu gwauro
domin babu irinki aduniya ban taba jiba ko
labari,
kodajin wannan batu sai sarauniya anisa ta
kyalkyale da dariya sannan ta hade fuska
tace
ai kuwa duk wanda zai mallaki zuciya ta ina
tausaya
masa
cikin mamaki badi'atul nauwara ta dubeta
tace
bangane kina tausaya masa ba kamar yaya
kenan?
anisa tayi murmushi tace
kafin na aminta dashi na bashi soyayyata
saina
bashi wahala tamkar ransa zai fita saboda
wadansu mugayen jarrabobi zanyi masa
badi'atul nauwara tace kekuwa wadanne
irin
jarrabobi zakiyi masa?
anisa tace wadannan kuma sirrine na barsu
acikin zuciyata bazan iya fadawa kowaba sai
mai
tsantsanin lura da kaifin tunanine zai iya
ganosu,,
ko ya gansu da idanunsa ayayin da abin
yake
faruwa idan muna tare.
ficewar anisa keda wuya daga cikin fadar sai
sarkin gida ya wuce gaba,, sarki shamsal da
boka
daisur suka bishi abaya har suka isa
masaukinsu
gidane guda acikin masarautar wanda akayi
na
musamman don saukar sarakuna irinsu
sarki
shamsal
komai na kawa dana jin dadin rayuwa an
tanadeshi acikinsa,
hadimai kuwa gasunan birjik, kai kace suke
yiwa
sarauniya anisa hidima
bayan sarki shamsal sun zauna acikin wani
babban falo sai aka kawo musu abinci dana
sha
kalakala masu daraja,,
nantake kamshin ya cika falon gaba daya,
boka
daisur baisan sa'adda ya wangame
hancinsaba
ya faralumshe idanu
koda kuyanginda suka kawo abincin suka
juya
suka fice daga cikin falon sai boka daizur
yayi
wuf yakai hannun sa izuwa kan wata
katuwar
kaza ya yago cinyarta zai kai bakinsa,, sai
sarki
shamsal ya daka masa tsawa
ba shiri ya jefar da cinyar kazar sarki
shamsal ya
dubeshi a fusace yace
baka da hankali ne daga kawo abinci zaka
kamaci?
kodajin haka sai boka daisur ya bude
idanunsa ya
fara karanto wadansu dalasiman tsafi
kawai sai ya bude idanunsa ya dubi sarki
shamsal yace
babu wata guba acikin wannan abinci,. ba
tareda
fargabar komaiba suka kama cin abincin
harsaida
suka gama kimtsa cikinsu dayansu baice
kalaba
asannan ne sarki shamsal ya mike ya
juyawa
boka daisur baya yace
maza ka sakeyin bincike ka gani ko anan
cikin
gidan sarautar aka boye su hatyan
da'yaruwarsa
sadirat kai kodama binciken naka ya nuna
basa
nan to bazamu fasa namu bincikenba na
zahiri,
ni yanzu zanje na kwanta domin na rama
bashin
barcin da mukayi amma dare na rabawa
zan tashi
mu fara aiki
sarki shamsal na gama fadin hakan sai ya
nufi
cikin dakin barcin yaje ya kwanta akan wani
luntsumemen gado yayi rub da ciki nan
take
kuwa barci ya saceshi harda minshari,
al'amarin boka daizur kuwa saida
kuyanginda
suka kawo musu abinci suka dawo suka
kwashe
kwanukan abincin suka fice sannan yatashi
ya
rufo kofar falon da tagogi
sannan yazo ya zauna ya fiddo madubin
tsafinsa
ya ajiyeshi akan wani tebur dake gabansa
ya
shafeshi da hannunsa na hagu domin yaga
duk
abinda ke faruwa acikin gidan sarautar ako
wanne lungu da sako
kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga
madubin
tsafin yayi bakikkirin babu alamar haske
al'amarin dayai matukar firgitashi kenan
yayi wuf
ya
dauke madubin tsafinsa ya zurashi a aljihun
rigarsa ya mike tsaye cikin razani, gami da
tashin
hankali.
tabbasyanzu ya tabbatar da cewa tsafinsa
bashi
da wanì amfani awannan birni
nan take mamaki ya baibayeshi ya kama
tunani
da mamaki inda ya tambayi kansa acikin
zuciyarsa yace
mene dalìlin dayasa tsafi yaki aiki agarinnan
alhalin ma yayi aiki agarin sarauniya
badi'atul
nauwara, kuma yayi tasiri duk da cewa ance
ita
bata tsafi kuma baya tasiri ajikìnta
koda daizur yazonan azancen zucinsa,, sai
zuciyarsa ta buga da karfi yace
anya kuwa sarauniya badi'atul nauwara na
nan
acikin birninta?
ai indai tana birninta babu yadda za'ai
tsafina
yayi tasiri.
to amma kuma lokacin da mukayi bincike
munganta afadarta amma sau daya kuma
kafin
mu fara bincikenmu ne
anya kuwa bayaudarar mu tayiba ta rigamu
zuwa
garinnan, idan kuwa hakane to tabbas da
hannunta aboye su jarumi hatyan
kai ammafa abinda kamar wuya saboda
batayin
tsafi kuma babu wani abin hawa dazai
kawota
kafin mu iso tunda dai mu akan tsuntsun
tsafi
mukazo
yanzu idan na gayawa sarki cewa tsafina
yaki
tasiri agarinnan to zai fusata ainun yace na
raina masa hankali tunda nace dashi yayi
aiki
abirnin sarauniya badi'atul nauwara
banida abinyi yanzu face nasa ido sosai
akan
binciken da zamuyi yanzu,, tunda dai ina
zargin
cewa badi'atul nauwara tana cikin garinnan
idan kuma tana nandin to itama sarauniya
anisa
tana da hannu gabaki dayansu tunda dama
kawartace tun kuruciyarsu
koda boka daizur yazo nan a tunaninsa
saiya baje
akan doguwar kujera,, amma sai daya dade
yana
tunanin zuci gami da zulumi sannan barci
ya
daukeshi,
TO ANAN AKAZO KARSHEN LITTAFIN TARKON
MUTUWA NA HUDU SAI MUN HADU A
LITTAFI
NA BIYAR 5 TARKON MUTUWA

TARKON MUTUWA LITTAFI NA BIYAR
PART A & B

Kash ! rashin sani yafi dare duhu hakika
masu iya
magana sunyi gaskiya da sukace ga magani a
gonar yaro amma bai saniba
Ashe mabudin dakin kasa inda aka boye su
hatyan da yaruwarsa abakin kofar shigowa
falon
take,sai andaga daddumar da ma ake takawa
sannan a zare wani tubalin zinare da aka
shimfida akasa akayi ado dashi,kuma na
farko
Sannan zata bude a taka matattalalar
benen izuwa kasan
da daddumar sai da boka daizur ya dafa ya
tattaba tubalin zinaren duka, gamma
tunaninsa
da basirarsa batakai kan ya care tubalinba
.
bayan sun gaji da bincike basuga komai ba
sai
sarki shamsal ya dubi sarauniya anisa yace
ki gafarcemu yake wannan Sarauniya kiyi
sani
cewa aiki ne yajanyo muka saki wanna
wahala
ayanzu dai bamuga Komai ba amma hakan
ba
yana nufin mun cire zargi daga ranmu
baneba
kamar yadda nake fada miki abaya zamu
fara
yin bincike na biyu yayin da hadimaina
kwararrun iya bincike suka iso ayau dinnan
yanzu nida bokana Zamu koma masaukinmu
mu
kwanta domin Rama barcin da muka rasa a
yanzu
ba zamuci gaba da bincikeba sai da farkon
yammaci gama fadin Hagan keda wuya sai
Sarki
shamsal da boka daizur sika juya suka fice
daga
cikin turakar suka isa masaukinsu,
suka koma suka fara sabon barci ba tareda
sunyi
kalaciba,
wanna shine abin da yafaru abirnin
askandariya a
Daren dasu Sarki scandal suka hallara zuwa
kashe gari
acan birnin bindal kuwa tin lokacin da
Sarki scandal
yabar gari domin tafiya
farautar babban abokin gabarsa wato
hartayn sai
aka shiga wata babbar masifa wacce ta
dugunzuma hankalin gaba daya masu mulki
da
manyan Gari baki daya ba komai bace wanna
masifa ba
face mulkin yarima zainur ya shirya rundina a
cikin
Daren kawai sai wayar gari akayi akaga an
kama gaba daya manyan garin wadanda
suka
kasance amintattun sarki shamsal wadanda
zasu
iya sadaukar da rayuwar su dominsa an
kashesu
sauran yan majalisar kuwa da manyan gari
sai
gasu sun taru afada gaban yarima don yin
mubaya a yana zaune akan karagar mulki
wani
bakon boka ma abocin kwarjii yana tsaye
abayansa
Yarima yanata kyakyata dariyar mugunta
yagaji
a wannan lokaci fadar tayi tsit babu abinda
akeji
kai bawai acikin fadarba har acikin gari ma
duk
inda ka gifta sai dai kaji tsit saboda tsananin
firgitar da jama’a sukayi saboda sun sami
labrin
cewa yarima zainur ya yi juyin mulki
nan take yan mata da zawarawa suka farayin
hijirar sirri don kada zaluncin sabon sarki ya
fada
kansu
bayan yarima zainur yayi dariyar farinciki ya
gaji
saiya dubi gaba daya yan majalisar dake
cikin
fadar da dukkan fadawa da dakaru wadanda
har
izuwa wannan lokaci a firgice suke kamar
kace
kyat su saki fitsari awando
yarima zainur yayi ajiyar numfashi cikin
murmushi yace
yaku jama’ata kuyi sani cewa komai nisan
jifa
kasa zai fado ina mai tabbatar muku da cewa
lokacin zaman mahaifina akan wannan
kujerar
mulkin ya kare har abada bazai sake zama
akan
wannan kujeraba.don haka yanzu sabon sarki
sabon birni sabuwar rayuwa
kamar yadda nayi muku alkawari tun adaren
jiya
kowannenku zan linka.masa albashinsa kuma
zan
rinka kyautata muku
sabanin mahaifina da wani hakkin nakuma
cin yewa yake
abinda nake bukata daku kawai shine kada
dayanku yasa mini ido akan harkokina ko
yace
zai ja dani indai kukayi hakan zaku sami arziki
mai yawa daga gareni wanda baku taba
samuba
nasani cewa hankalinku a tashe yake akan
tunanin cewa idan sarki ya dawo bazai
kyalekuba
kasheku zaiyi
to ku kwantar da hankalinku ku sani cewa
babu
abinda sarki zai samo awannan tafiya face
ajalinsa
tabbacin haka shine gaba daya bokayen dake
wannan nahiyar tamu sunyi bincike sun
tabbatar
da hakan
wannan boka da kuke gani kusa dani shine
boka
arzus bin sharkub shima ya tabbatar da
hakan
bisa wannan dalili nema yazo ya zauna tare
dani.
domin biyan wata bukatarsa wacce ta
kawoshi
wannan nahiya tamu tsawon shekara talatin
baya
bai sami damar cikata ba
koda yarima zainur yazo nan azancensa sai
gaba
daya mutanen da suke cikin fadar suka kamu
da
tsananin mamaki kuma dukkaninsu suka
kurawa
boka

Please Login or Register in order to submit comment