Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koken kartin da hatyan
ya karya .
adai dai wannan lokacine wannan matar mai gidan
abincin ta taho da sauri wajen hatyan tace ina
kuma zaku tafi baku biyani kudin babbar barnar
da kukayi min ba?
kodajinhaka sai hatyan yayi murmushi
yace nawa zamu biyaki?
matar tayi masa wani murmushi irin na
karuwanci tace
tunda dai kaine ka biya dinare hamsin charaf sai
sadirat tace
haba yan wadannan tsofaffin kujerun da teburan
da aka karya sune dinare hamsin
sai matar ta rufe sadirat da fada tace
shin bakya ganine anfasa min tambula da kofuna
guda dari
ko kece mannadinin hari sai an biyani dinare
hamsin ko kuwa rijiya ta bayar guga ya hana
dajin haka sai hatyan ya tari numfashinta yace
kadaki danu ga dinare dari ma
nan take ya debo dinare dari ya bata .
ai kuwa sai matar ta daka tsalle ta sumbaci
hatyan agoshi sannan tace idan kuna neman
gurin kwana a unguwar daisul nake gida mai
lamba goma
kofata abude take agareka basai ka biya ba
shidai hatyan baice da ita kalaba kawai sai ya
dafa kafadar sadirat yace zo mu tafi
nan take takobin dake hannunsa ta rikide ta
koma sanda
sadirat ta kama sandar suka nufi hanyar fita
daga gidan abinci
amma sai wannan boka da dakarun birni kimanin
su saba'in suka sha gabansu
Bokan ya dubi hatyan fuskarsa a murtuke yace
kana zaton zaka iya yaudarar kowane da dan
guntun sihirinka na tsafi?
to nagane ku ko ku su waye
kaine hatyan wannan yarinyar kuwa yar uwarka
ce
sadirat
kune wadanda aka baza hotunanku ako ina cikin
garinnan kuma sarki shamsal ne yake nemanku
ruwa a jallo
kuna zaton zan iya bari ladan dinare dubu dari ya
wuceni?........
TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- prince auwal auzab
Post:- AA Misau
Littafi na biyu 2
Part 2C
.
Koda bokan yazo nan azancensa sai wannan
mace mai gidan abinci ta zazzaro idanu cikin
tsananin mamaki
jikinta na kyarma ta kurawa hatyan idanu
hatyan ya dubi bokan cikin murmushi
na yarda ka gane ko mu su waye amma ina mai
shawartarka daka cire hannunka daga cikin
wannan lamari idan kuwa
kaki to zakayi biyu babu
ma'ana ka rasa ladanka sannan kuma ka rasa
lafiyarka
idan ka matsama ranka ma zaka rasa haba day~
kodajin wannan batu sai wannan bokan ya bushe
da dariyar mugunta yace
ai inda ba kasa nan ake gardamar kokawa
fa ga fili ga mai doki sai akasa tseren muga
abinda
zai faru
da jin haka sai hatyan ya tura sadirat ta koma
bayansa sannan ya daga sandarsa sama
take ta sake zama takobi
ai kuwa shima bokan sai ya zare takobinsa ya
dubi dakarun sarkin yace
ku ku koma gefe daya ni zan kamasu a hannu mu
tafi dashi gidan sarki
ba tare da gardama ba dakarun suka koma gefe
daya
dasu da sadirat da mai gidan abincin
suka zama yan kallo
nan take su hatyan suka ruguntsume da
azababben yaki mai tsananin ban tsoro da ban
al'ajabi.
sai da suka shafe kusan dakika tamanin suna
kaiwa junansu sara da suka cikin zafin nama da
juriya da bajinta ba tare da dayansu ya sami
nasara akan dayaba
koda hatyan yaga zai bata masa lokaci sai yaja
da baya ya dubeshi cikin murmushi yace
yakai wannan boka hakika na yarda ka iya
yaki amma bari na gwada karfin damtse mu gani
kafin bokan yace wani abu tuni hatyan yadako
tsalle ya gabza masa wawan naushi a fuska
saboda karfin naushin saida ya kife da ribda ciki
alokacin dahar hakoransa guda sukayi fitar burgu
daga bakinsa ya baje kasa sumamme
koda ganin abin da faru ga bokan sai dakarun
suka firgita suka ja da baya suka baiwa su
hatyan hanya suka wuce
ita kuwa wannan mata mai gidan abinci sai ta
biyo hatyan da gudu ta sha gabansa tace
amma fa ka cika gwarzon jarumi mai tarwatsa
maza
don Allah ka dawo izuwa aininhin siffarka mana
naga kyakkyawar suffarka
dajin haka sai hatyan yayi murmushi agareta
yace
kada kidamu zamu sake haduwa
kawai sai ya juya ya dubi wandannan dakarun na
garin idan kuka sanar da sarkinku kun gammu
sai na kasheku dayanku bazai tsiraba
ku fadawa bokan nan wannan sakon idan ya
farfado daga suman da yayi
yana gama fadin haka ya kama hannun sadirat
yajata suka fice daga gidan abincin suka sake
nausawa cikin gari
suna tafiyar sauri sauri gudu gudu
acan gidan abinci kuwa wannan boka bai
farfadoba daga dogon suman da yayiba sai
bayan
rabin sa'a
afirgice ya mike zaune ya kama kalle kalle
kawai sai yaga an gyara wajen fes kamar ba'ayi
yakiba agun.
duk karyayyun kujerun da teburan an kwashesu
an
zuba wadansu sababbi
ga kostomomi azaune suna cin abinci kowa na
harkar gabansa
dakarun da sarki ya hadashi dasu kuwa don
aiwatar da wannan aiki babu ko mutum daya
daga cikinsu
koda ganin haka sai ya mike tsaye zumbur ya
fara neman wannan mata mai gidan abinci
kawai sai yaji an taba kafadarsa ta baya
afirgice ya waiga sai yaga ashe wadda yake
nemace
cikin alamun tsananin damuwa da zumudi
ya dubeta yace
yake sardila ina wadannan yaran sukayi?
sardila tayi dariya sannan tace ai kayi babban
kuskure da bakayi amfani da karfin sihirinka ba
tun farko
boka azwan ya numfasa yace ai wannan yaron
ba karamin takadiri bane
nasan tsafinsa babbane.
abin danake so dake shine zan zuba ido akan
gidanki domin zai iya kawo miki ziyara tunda dai
kin bashi adreshinki
yanzu zan koma gidan sarauta na sanar da
sarauniya halin da ake ciki domin ta karo mini
yawan dakaru
ai komai hatsabibancinsa sarkin yawa yafi sarkin
karfi
kada ki kuskura ki barshi ya sake guduwa idan
har yasake dawowa
koda gama fadin haka sai boka azman
ya ruga waje ya kama dokinsa ya kwance ya
haye kuma ya zubureshi da gudu izuwa gidan
sarki

shidai wannan babban birni ana kiransa da suna
madinatul sarkuf
kuma yana karkashin mulkin wata sarauniya mai
suna badi'atul nauwara
badi'atul nauwara ta kasance kyakkyawar
budurwa ta gaban kwatace kuma shekarunta
ashirin da daya cif cif wato ita da jarumi hatyan
sa'annin juna ne
badi'atul nauwara shahararriyar mayakiyace
kuma basadaukiya
wadda tasha jarumantaka ne anono domin uwarta
ce shugabar sadaukai ~ na kasar gaba daya
mahaifinta kuwa wanda tagaji sarautar a
hannunsa
shine sarkin yakin birnin kafin ya zama sarki
amma shi ma yau shekararsa shida da rasuwa.
mahaifiyarta ta rasu sakamakon ciwon hanta da
yaci karfinta
badi'atul nauwara bata tsafi kuma baya tasiri
akanta
saboda tsananin jarumtakarta da iya yakinta
da sanin tuggun yaki wanda mahaifinta ya koyar
da ita shi yasa duk sarakunan dake kusa da ita
suke shakkarta.
jama'ar gari kuwa suna matukar kaunarta saboda
yawan adalcinta
aduniya babu abinda badi'atul nawwara ta tsana
kamar zalunci
taga adalci a tsakanin talakawa da masu mulki
da attajirai ta kanyi amfani da kudin baitil mali ta
siye kayan abinci a hannun manoman garin ta
rage farashinsa ta siyarwa da talakawa don
magance yunwa da talauci akasar
wannan halayya ta sarauniya badi'atul nauwara
tasa yan majalisarta da manyan attajiran kasar
suka tsaneta
kuma sun sha shirya hanyar da zasubi su kawar
da
ita daga kan mulkinta amma sun kasa
bisa dole suka hakura suka barta akan karagarta
lokacin da sakon sarki shamsal ya riski
sarauniya badi'atul nauwara taga hoton jarumi
hatyan dana yar uwarsa wadanda shekarunsu
basu kai talatin ba
sai bata dauki abinda wani mahimmanci ba
saboda taji ajikinta cewar duk yadda akayi ba wai
laifi sukayiba zaluncin sarki shamsal ne kawai
ya fado kansu
Abinda tayi kawai shine ta kirawo azman ta
hadashi da dakaru ashirin kacall tace ta dora
alhakin kamo hatyan a hannunsa.
tayi hakan ne don kada ace batayi komai ba
amma tasan cewa boka azman da wadannan
dakaru basu isa su kamo wadannan masu laifiba
tunda harma suka iya guduwa daga birnin
shamsal.
'ya'yan sarakai dana attajirai da dama na wannan
birini sun nemi auren sarauniya badi'atul
nawwara
amma sai taki yarda da dukkaninsu
lokacin da fadawanta suka matsa mata akan ya
kamata tayi aure domin ta kare martabarta da ta
masarautarta
sai ta dubesu tace
duk wadanda suke sona da aure ba don Allah
suke sona ba sai domin dukiya,mulkina,da
kyawuna.
da yawansu suna son su aureni ne saboda su
sa; lusuranci da wannan gidan sarautar
domin wata rana mulkin ya koma gidansu.
bazan taba yin aureba koda zan tsufa na
mutu akan karagata ba
face na.sami masoyi wanda zai soni soyayyar
gaskiya ba tareda da yasan koni wace ba
kuma.saina.tabbatar da cewa.badon
kyawuna.yake sona ba
sannan kuma dolene yafini karfin damtse da
jarumtaka
ta hakane kadai nasan cewa zai iya kare.hakkina
da mutuncina.
sarauniya badi'atul nauwara na zaune acikin
fadarta. fadawa da manyan mutanen gari
ana.zaune ana yin fadanci
saiga boka azman ya shigo cikin fadar aguje
kuma adimauce
da zuwansa gaban karagar sai ya zube akasa
yana rawar murya da jiki yace .
ya shugabata yau naga wadannan masu laifi
wadanda sarki shamsal yake nema ruwa ajallo.
kodajin wannan batu sai fadar ta rude da mamaki
gami da kace na ce
harsaida sarauniya badi'atul nauwara ta daga
hannu sannan akayi tsit tamkar mutuwa tagifta
badi.iatul nauwara ta ce
a ina kagansu kuma yaya akayi baka kamosu ba?
nantake boka azman ya kwashe labarin abinda
ya faru agidan abincin sardila ya zaiyane
kodajin wannan labari sai jama'a suka sake cika
da mamaki akaci gaba da hayaniya .
ita kuwa saruniya saitayi shiru tana tunani har
tsawon .yan dakiku
dagachan sai ta dago da kai ta dubi boka azman
tace
tabbas wannan mai laifi ba karamin jarumi bane
zanso nayi arba dashi naga irin jarumtakar tasa a
zahiri
abinda nakeso dakai shine zan kara baka dakaru
guda arba'in ku sake nemansu.
tunda dai duk irin kamannin da mai laifi zai juye
sai ka ganeshi zaku iya kamoshi.
boka azman ya dubi sarauniya cikin alamun
tsananin damuwa kamar zaiyi kuka yace
ya shugabata dakaru sittin fa kenan kacal kika
bani
ai kamata yayi ki bani dakaru dubu dari domin
hatsabibancin wannan mai laifin ya wuce yadda
kike zato
kodajin haka sai sarauniya tayi murmushi tace
kai dai kawai kace ka tsorata dashi amma yaushe
ace
akan mutum daya jal zan baka dakaru dubu dari.
kaje kayi aikinka kawai idan ka kasa ni zan yi da
kaina.
tana gama fadin hakan sai ta mike tsaye ta
kirawo shugaban dakaru tace
maza aje a bawa boka azman karin dakaru
arba'in kuma a bashi kudin abincinsu dana
wahalhalinsu.
kaji aikin mai adalci wacce bata danne hakkin
kowa shugaban dakarun ya russuna yace
an gama ya shubata
nantake shida boka azman suka fice daga fadar
ita kuma
sarauniya badi'atul nauwara ta shige izuwa cikin
gidan sarautar nantake fadawanta ma suka
watse .
kowa ya kama gabansa.
lokacin da sarauniya badi'atul nauwara ta shige
can cikin kuryar turakarta ta sanya kayan barci
sai ta zauna akan gefen gadonta
alokacin da wata kuyangar ta kawo mata ruwan
inibi a kofi ta karba ta dan kurba
kadan sannan ta jiye kofin.akan tebur
har ta yunkura zataje ta kwanta sai maganganun
boka azman suka fado mata arai .
nan take ta mike tsaye ta dauko taswirar fuskar
jarumi hatyan da yar uwarsa sadirat ta kura
musu idanu har izuwa tsawon dakiku
take ta gane cewa ai wadannan matasa yan
uwan junane dolene su kasance uwa daya uba
daya
sabodame sarki sarki shamsal yake neman
wadannan yan uwan biyu a raye
ko a mace ko a raye har ma ya sanya lada mai
tsoka.haka ga duk wandaya kawosu?
tabbas ina bukatar naji cikakken labarin
wadannan yan uwa domin nasan hanyar da zanbi
na taimakesu
tunda dai suna cikin kasata a halin yanzu.
idan har inason jin labarinsu kuwa dolene sai dai
nayi bad da kama na tafi nemansu da kaina
gama fadin hakan keda wuya sai sarauniya
badi'atul nauwara ta baje akan gadonta domin
tayi barci
inyaso idan dare ya soma yi sai tayi bad kama ta
shige cikin garin.
al'amarin su jarumi hatyan kuwa lokacin dasuka
sake karadawa cikin gari sai ya dafa sadirat
akafada
nantake suka sake rikidewa suka koma 'yan mata
guda biyu kuma bakaken fata don kada wani
wanda ya gansu a gidan abinci ya sake ganinsu a
siffar almajirai
da dan jagora ya shaidasu .
nan dai suka ci gaba da tafiya ko waige basayi
harsaida suka je karshen kasuwar sannan suka
zauna
sukayi kamar ciniki sukayi don bagarar da masu
farautarsu .
lokacin da sadirat taga sun shafe lokaci
maitsawo zaune awajen saita dubi
hatyancikin.alamun damuwa tace waishin zaman
me muke tayine a nan wurin?
baka tsoron a sake shaidamu azo da dakaru
masu yawan gaske ayi mana shigar rago?
kodajin wannaan tambaya sai hatyab yayi
murmushi yace
waishin sau nawa ina fada miki cewa indai kina
tareda ni ki daina tsoron kowa?
akwai dabarar da nake shiryawa wacce ita kadai
zamubi mu tsira da rayuwarmu mu kwana hankali
kwance
inyaso da asubah .kafin gari yayi haske sai mu
kara gaba........
AA Misau
TARKON MUTUWA
Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Part 2 C

Haka dai hatyan yayita jan sadirat da hira har
magaruba tayi
adai dai wannnan lokacin ne sardila mai gidan
abinci ta taso daga sana'arta
ta gaban su hatyan ta wuce amma ko kallon su
hatyan batayiba.
sai da ta danyi nisa da tafiya sannan hatyan ya
kama hannun sadirat suka mike tsaye suka
kwashe kayansu da sauri suka bi bayanta cikin
sanda da buya ba tareda tasan suna binta ba.
sai da suka yi nisa da barin harabar kasuwa
sannan aka iso wani wuri mai kama da daji
sannan hatyan ya baiyana tsulum agaban sardila
acikin ainihin siffarsa.
tana ganinsa ta firgita ainun ta wangamebaki
zata rusa ihu
amma sai yayi wuf ya toshe mata baki da tafin
hannunsa
ya dora mata wuka akan.wuyanta yace
idan kika yi mini ihu saina yanka ki.
kiyi duk abindana umarceki idan kina son ki tsira
da
rayuwarki.
gama fadin hakan keda wuya sai ya janye
hannunsa daga kan bakinta
alokacin ne tayi doguwar ajiyar zuciya
ta dubeshi cikin alamun tsoro tace
me kake so nayi ma?
awannan lokacin ne sadirat ma ta fito daga cikin
duhuwar da take boye ta tsaya abayan hatyan.
hatyan ya dubi sardila yace
so nake ki kaimu gidanki mu kwana amma ba
wancan gidan da kika saba kwana ba .
ki fadi ko nawa kike so mu biyaki.
kodajin wannan batu sai hankalin sardila ya
kwanta tayi murmushi tace
shin zaku iya biyana dinare dubu daya.
dajin haka sai sadirat tayi farat tace
haba kwana dayan da zamuyi jal
shine saimun biya dinare dubu
to nawa ne kudin gidan gaba dayansa
sardila tace karfa kimanta cewa masu laifine zan
boye na basu mafaka.
me kike zaton zai faru idan asirina ya tonu?
duk abindana mallaka agarin nan sai sarauniya ta
kwace kuma karshe aturani kurkuku
duk da cewa kuwa sarauniyar mu mai adalci ce
gama fadin hakan keda wuya kawai suka hango
boka azwam tare da dakaru da gudu sun fito
daga cikin kasuwar
cikin hanzari duk su ukun suka fada cikin
kodajn wannan batu sai hatyan ya kyalkyale da
dariya yace
kome kike takama dashi ni daidai da kene.
ina shawartarki daki gagauta ficewa domin muma
tafiya zamuyi mu bar muku birninku tunda kun
matsa mana
sarauniya ta sake bushewa da dariya a akaro na
biyu tace ai bakin alkalami ya riga ya bushe .
babu ta inda zaku iya fita daga garin nan batare
da an kamakuba.
nan da cikar rabin sa'a dakarun sarauniya
kimanin dubu dari uku zasu zo suyiwa unguwar
nan kawanya kunsan kuwa sarkin yawa yafi
sarkin karfi
kuma kasani cewa ko tsafi kuke takama
dashi tofa baya tasiri acikin garin nan.
saboda sarauniyar mu bata tsafi kuma baya tasiri
akanta.
tana gama fadin haka sai ta zare takobinta tana
mai gyara tsayuwarta ta dubi hatyan tace .
ka mika wuya ko na yi maka raunin da zaka mutu
da tabonsa.
koda sarauniya tazo nan ajawabinta sai shima
hatyan ya zare takobinsa
kuma ya gyara tsayuwarsa kamar yadda tayi
yace
"na rantse da kabarin iyayena idan ban sami
nasara akanki ba kema baki isa ki sami nasara
akaina ba "
gama fadin hakan keda wuya sai duk su biyun
suka ruga da gudu izuwa kan juna suka
ruguntsume da azababben yaki mai matukar ban
tsoro da ban al'ajabi wanda ya firgita sadirat
ainun ta ruga izuwa karkashin wani katon tebur
na karfe dake tsakar gidan ta dunkule jikinta
tamkar bushiya
amma saboda shegen naci nason ganin
jarumtakar mutum biyun sai ta ci gaba da kallon
gumurzun nasu
sai da suka shafe kusan rabin sa,a suna kaiwa
juna sara da suka cikin bakin zafin nama da
bajinta ba tare da dayansu ya sami nasara ba,
koda ganin haka sai suka sauya salon fadan suka
hada da tsalle gami da kwance kwance da kuma
kai naushi da bugu.
da zarar hatyan ya sami nasarar naushin
sarauniya a fuska ko a kirji kafin ya kaimata wani
naushin sai kaga ta rama kamar yadda yayi mata
nanfa suka hadawa junansu jini da majina
tun suna yin fadan da karfin jikinsu da kuzarinsu
sai daya zamana cewa dakyar suke iya
daga hannayensu
kai da gani kasan cewa karfinsune yazo daya
suna cikin wannan haline sukaji ana kwankwasa
kofar gidan da karfi
dajin hakan sai sarauniya ta ja da baya ta daina
fadan sannan ta daga muryarta da karfi tace
ku dakata anan waje kada wanda ya shigo
take su hatyan suka gane dakarun sarauniya ne
sukazo kuma ga yadda suka jiyo dudufniyar su
da alama suna da yawan gaske
kawai sai sarauniya ta mike tsaye ta fuskanci
jarumi hatyan ta cire mayafin data rufe fuskarta
dashi
koda su hatyan sukaga kyakkyawar fuskarta da
jikinta sai suka rude
sarauniya badi'atul nauwara tasa hannunta ta
goge jinin dake jikin lebenta sannan ta dubi
hatyan cikin murmushi tace
nice sarauniya badi'atul nauwara mai mulkin
wannan birni mai suna madinatul salkuf.
yanzu haka dakaruna sun iso wannan
unguwar sun zagayeta babu ta inda zakubi ku
iya guduwa ku tsira amma zan kubutar daku
saboda dalili daya.
dalilin kuwa shine
naji kayi rantsuwa da kabarin iyayenka
hakan ya nuna mini cewa ku marayune kamar ni
wato baku da iyaye .
duk da cewa banji tarihin rayuwarkuba kuma
bansan laifin da kukayi wa sarki shamsal ba.
amma jikina ya bani cewa kuna da gaskiya
zaluntarku kawai zai yi .
zan baku dama ku gudu amma yakai wannan
gwarzon jarumi kayi sani cewa ina binka bashin
wannan fada.
lallai sai mun sake haduwa domin mu fitar da
raini
na dade ina neman jarumin dayake da karfin
damtse da iya yaki irin... auwzab... nawa ban samuba sai
kai
a yanzu
dolene mu karasa yakinmu .domin mu banbance
tsakanin aya da tsakuwa anan gaba idan muka
sake haduwa anan gaba .
ku zauna acikin gidannan ku kwana.kada ku
fito sai asubah tayi.
asubah nayi ku nufi yammacin garinnan.kuyi ta
tafiya zaku iski tashar jirgin ruwa .
ku hau jirgi ya ketare daku iyakar wannan kasa
tawa zaku riski wani gari agaba.
zan baku gudun mawoyin da zasu ceceku.
koda ta gama fadin hakan sai ta juya ta fice
daga cikin gidan.
tana fita sai ta janyo kofar gidan ta rufe inda tayi
arba da dakarunta tare da boka azwan yana
jagorantar su.
sun ruko saldirat a hannu sunyi cirko cirko.
kawai sai sarauniya badi'atil nauwar ta dubi boka
azwan tace
ku saki saldira bata da hannu akan boye
wadannan masu laifi domin basa cikin wannan
gida .
maza ku ruga gaba dayanku izuwa gabashin
birnin nan.
can sukayi da gudu bisa dawakai kada ku barsu
su ketare iyakarmu.
kodajin wannan batu sai boka azwan da gaba
dayan dakarun suka ruga izuwa inda dawakansu
suke suka hayesu suka zaburesu da gudu suna
masu tunkarar gabashin birnin .
tafiyar su keda wuya sai sarauniya ta dubi
sardila tace
shiga ki baiwa su hatyan kulawa mai kyau .
asuba nayi ki tashesu daga barci subar garinnan.
tana gama fadin haka sai ta juya tayi tafiyarta ta
kutsa kai cikin unguwar tana mai rufe fuskarta
tamkar bata kasance sarauniyaba.
sardila ta fada cikin gidan da sauri ta rufo kofa.
kamar yadda sarauniya ta tsara haka al'amarin
ya kasance .
asubah nayi sai sardila ta tashesu daga barci
suka kimtsa sannan sukayi bankwana.
nantake hatyan ya bude jakar guzurinsa.
ya debo dinare dubu da biyu ya mikawa sardila
yace.
ga kudin hayar gidanki dana abincinki.
dajin haka sai sardilat ta kasa karbar kudin kuma
nantake idanunta suka ciko da kwallah har
hawaye ya zubo mata tace
yaya ina matsayin marainiya zan kasa taimakon
marayu yan uwana?
maraicine yasa na taso acikin irin wannan
rayuwa da kuka ganni aciki
tun ina yarinya shekara takwas aduniya na iya
aikin wahala domin na tserar da mutuncina
karuwanci sata da caca duk nayi agarin nan
amma ban taba taimakon wani da darhami
dayaba arayuwata.
ahalin yanzu na mallaki gidaje da gonaki,shanu
da tumaki barkatai,
idan an lissafin masu arzikin garinnan dolene
asani acikin su.
duk abinda nayi muku na bar muku domin nabar
tarishi arayuwata cewar nataba taimakon yan
uwana marayu da wannan haramtacciyar dukiyar
dana tara
ku sani idan natuna wannan dukiya sai naji na
tsani kaina kuma naji mutuwa
kawai nake sonyi domin bata da amfani
rayuwata. dan babu da uwa ko masouyin kwarai.
koda sardilat tazo nan azancenta sai ta fashe da
kuka al'amarin daya kara karyar da zuciyar
hatyan da sadirat kenan suma sukaji suna
matukar tausayinta don haka ba susan sa'adda
suka rungumeta ba duk su biyun suka fashe da
kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani
atsakaninsu saboda suma nasu maraicin suka
tuno.
sai da suka dan jima kankame da juna sannan
suka janye jikinsu daga cikin nata
nandai suka kwashe kayansu tayi musu rakiya
har izuwa bayan gari inda suka hau dawakansu
suka sukwanesu suka durfafi hanyar da sarauniya ta
umarcesu subi.
tun kafin su isa inda tashar jirgin ruwan take
hatyan yayi tsafi suka sake rikidewa izuwa siffar
fatake kuma mazaje yan kimanin shekaru arba'in
da daya.
da isarsu bakin gabar jirgin ruwan sai suka iske
wani babban jirgi ya gama lodi wanda jama'ar
dake cikinsa akalla sunkai dari shida da arba.in.
shidai wannan jirgi hawa biyune ma'ana akwai
dakaru akasansa da samansa.
sai kuma can karshen saman inda mutum ke
ganin ruwan tekun afili.
mafi yawan jama'ar dake cikin wannan jirgi
fatakene wadanda suka nufi birnin askandariya
domin can ne inda jirgin ya nufa.
indai mutum ya isa birnin askandariya tofa yana
daf da fita daga nahiyar gaba daya.
saida su hatyan suka ninka kudin shiga jirgi
sannan suka sami damar shiga jirgin sannan suka
sami damar shigar da dawakansu.
aka kai dawakan inda aka tanada don dawakai
nanma suka biya kudin shigar dasu.
daga nan aka tafi dasu izuwa dakinsu suka shiga
suka baje akan shimfida cikin farin ciki bisa
ganin cewa suna daf da tsira da rayuwarsu daga
sharrin sarki shamsal
Anan muka kawo karshen littafi na biyu.

07067470752

TARKON MUTUWA
Abdul'aziz Sani Madakin Gini
TYPING: PRINCE AUWAL AUZAB
POSTED: SUNUSI SAS
FACEBOOK: www.Facebook.com/Sunusi.ahmadstk

littafi na uku 3
PART A

Kawai sai sadirat ta rungume hatyan cikin
farinciki mara misaltuwa tace shikenan mun tsira
daga sharrin abokan gabarmu
yakai dan uwana yanzufa saura kiris mufice daga
wannan nahiya gaba daya.
kodajin wannan batu sai hatyan yayi doguwar
ajiyar zuciya cikin alamun karayar zuciya yace
akwai matsala yake yar uwata.
kiyi sani cewa har acikin wannan jirgi da muke
akwai yan leken asirin sarki shamsal da yawa.
tun afarkon shigowarmu cikin jirgin nan na
fahimci hakan.
inba don mun chanja kamannin muba da farat
daya zasu gane mu.
duk da hakan sai munyi mugun taka
tsantsan,gaskiya sarauniya badi'atul nauwra
tabamu babbar gudun mawa wacce ba zamu
taba mancewa da ita ba.
inbadon ita ba da yanzu bamu iso nan ba.
sardila ma ta taimakemu sosai
ni ina mamakin irin wannan sa'a tamu ma har da
muke haduwa da masoyan da suke taimakon mu
alhalin basu sanmu ba muma bamu sansu ba
ki sani cewa ko isasshen barci bamu isa mu
dinga yi ba acikin wannan jirgi domin makiya
zasu iya amfani da damar hakan su gane ko mu
su waye su cutar damu.
kada ki manta cewa a mace ko araye sarki
shamsal yake son ganinmu.
kodajin wannan batu sai hankalin sadirat ya
dugunzuma tace to yanzu yadda bamuyi wani
barcin kirkiba jiya da daddare yaya zamuyi
yanzu?
nifa kaina har ciwo yakeyi saboda jin barci.
hatyan yace yanzu ke ki kwanta kiyi barci ni
kuma zanyi gadinki idankika tashi daga barcin
dan kanki sai nima na kwanta kiyi gadina ammafa
da zarar kinji wani motsi komai kankantarsa ki
tasheni daga barci
saboda komai zai iya faruwa ako yaushe kuma
kadaki yarda da kowa acikin jirgin nan koda kuwa
ma'aikatan jirgin ne.
dajin haka sai murna ta kama sadirat ta kwanta
ta kama barci abinta tamkar ba'a cikin tashin
hankali takeba.
shikuwa jarumi hatayn sai ya dubi hoton zanen
wani gunki dake jikin bangon dakin na wata
sarauniya .
nantake sai ya tuno da sarauniya badi'atul
nauwar nanfa ya tuno da lokacin da suka fafata
kazamin yaki da ita kawo izuwa lokacin data
kwaye fuskarta
suka yi arba da juna.sannan ya tuno da irin
maganganun da ta yi masa da yarda akarshe ta
taimakesu suka fice daga cikin birninta har suka
iso wannan waje .
koda jarumi hatyan yazo nan atunaninsa sai yaji
akaron farko yaji son ya sake ganin wani mutum
wanda suka taba haduwa kuma suka rabu.
ma'ana babu abinda yakeso a.rayuwarsa sama
da sake saduwa da sarauniya badi'atul nauwara.
to wai shin menene dalilin da yasa naji ina son na
sake ganinta?
amsar da hatyan ya kasa baiwa kansa kenan.
ashe ita ma sarauniya badi'atul nauwara ta tsinci
kanta itama cikin irin wannan hali wanda hatayn
ya tsinci kansa acikinsa wannan dare lokacin data
koma gidan sarautarta
ta shiga cikin turakarta ta kwanta akan gado
bayan ta sanya rigar barcin ya gagareta
domin nantake ta shiga tuna duk abubuwan da
suka faru tsakaninta da jarumi hatyan.
abin daya fara burgeta a tare dashi shine
tsananin jarumtakarsa da juriyarsa ta yaki
gumurzu wacce ta zamo iri daya da tasa
abu na biyu shine da yakara burgeta shine
alokacin data bayyana fuskarta da jikinta a
gareshi
bataga yayi irin dimaucewar da maza suke yi ba
idan suka ganta.
kuma bataga yayimata kallo ba wanda yake nuna
yana sonta ba.
kawai dai yayi mata kallon mamaki bisa ganin
kyawun da Allah ya bata.
anya kuwa hatyan bashi bane irin namijin da na
dade ina nemaba .
wanda nake ganin cewa shine yafi dacewa da ya
zama abokin rayuwata.
to ai kuma hatyan ba sa'a na bane akalla na
girmeshi da tazarar shekaru takwas zuwa tara.
koda yake ai babu ruwan so da girma,kudi ko
matsayi idan har hatyan shine irin masoyin da
nake nema to tabbas zanyi masa ragowar
jarrabobin da zan tabbatar da hakan da zarar
mun sake saduwa.
haka dai sarauniya badi'atul nauwara taci gaba
da yin wannan tunani har barci ya saceta bata
sani ba.
Acan birnin bindal kuwa lokacin da sarki shamsal
yaga gaba daya dakarun guda dubu dari hudu
wadanda aka tura farautar su jarumi hatyan
izuwa kowanne bangare na kasar sun dawo babu
wata nasara
sai ransa ya baci kuma hankalinsa ya
dugumzuma ainun yarasa abinda ke masa dadi
aduniya .
nantake sarki shamsal ya tura aka kirawo masa
boka daizur ya dubeshi yace
yakai abin dogaron bindal kayi sani cewa abari
ya huce shi yake kawo rabon wani.
duk da cewa mun baza dakarun mu da yan leken
asirin mu izuwa dukkan kasashen dake wannan
nahiya kuma mun baza hotunan wadannan yara
ako'ina.
zuciyata na yawan bugawa da karfi akan wannan
al'amari inaji a jikina cewar wannan yaro zai iya
tsallake dukkan tarkokin mu.
bazan iya ci gaba da zaman ranar da za' akawo
min labarin cewa an kamasuba a wata kasa .
kasani cewa idan har ya sami nasarar fita daga
wannan nahiya tamu abune mawuyaci mu iya
kamashi kuma komai daren dadewa sai ya dawo
kasar nan cikin gagarumin shiri domin daukar
fansa gami da karbar karagata.
abinda nake so dakai shine kaje kayi shiri kazo
mu tafi farautar wannan yaro a yau dinan ba
zamu dawo gidaba face mun riskeshi mun tsinke
masa kai.
asannan ne zan sami nutsuwa da kawanciyar
hankali
lokacin da sarki shamsal yazo nan a zancensa sai hankalin
boka daizur ya dugunzuma ainun fiye
da ko yaushe ya sunkuyar da
kansa kas yayi shiru yana tunani har zuwa
tsawon yan dakiku daga chan.
saiya dago da kansa ya dubi sarki shamsal cikin
alamun damuwa yace
ya shugabana tashin hankalina dai
guda dayane.
yanzu idan zaka tafi wa zaka barwa jiran
karagarka?
kodajin wannan tambaya sai sarki

Please Login or Register in order to submit comment