Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har kusan rabin sa'a dayansu bai sami
nasaraba tmakar karfi yazo daya.
al'amarin daya fusata jarumi hatyan kenan.
kawai sai ya sauya salon yaki ya hada da tsalle
da kwance kwance gami da kai naushi da bugu
hannu da kafa .
ai kuwa nantake labari yasha banban sabida cikin
kankanin lokaci ya fara kuntata zainur sqboda bai
iya irin wannan salon yakin ba sosai kuma gashi
zafin naman hatyan ya ninka nasa sau goma.
tun yarima zainur ma iya maida martanin sara da
suka har sai daya kasa yazamana cewa da
kyarma yake iya kare kansa.
ana cikin hakne hatyan ya shammaci zainur ya
gabza masa wawan naushi afuska da kafa.
daboda karfin naushin saida yarima yayi
katantanwa sau hudu atsaye kafin ya dawo
haiyacinsa tuni hatyan yasa takobinsa ya sare
masa hannunsa na dama.
take ya tsinke ya fadi kasa
yarima zainur ya kwallara uban ihu sakamakon
tsananin zafi da zugin da yaji ya durkushe kasa
bisa gwuiwarsa guda yayinda jini ke tq bulbula
daga dungulmin hannunsa nasa
kawai sai hatyan ya tsaya akansa ya tofa masa
yawu a fuska agaban talakawan gari yace
yau ina karfin naka kuma ina sarautar taka.
ina hannun da kake yiwa yan mata fyade dashi?
dajin wadannan tambayoyi sai hawayen takaici
ya zubowa yarima zainur ya dubi hatyan yace
naramtse da girman abin bauta sai mahaifina ya
dau fansa akanka.
idan yakamaka ba zai kasheka ba sai ya yanke
maka dukkan hannayenka da kafafunka tukunna.
kodajin haka sai hatyan yasake tofawa zainur
yawu yace
inba don nadau alkawarin sai nakashe mahaifinka
agaban idanunka da yanzu zan kasheka amma
bakomai nasan cewa daga yau baka da hannun
yiwa yan mata fyade na taimaki talakawan
garinnan.
idan ka koma gida kagayawa mahaifinka cewa
nin3 jarumin da bokaye suka gaya masa cewa
zan karbi karagar mulkinsa don haka.ya zauna ya
jira ranar dawowa ta.
tabbas yanzu yafi karfina bazan iya dashiba.
amma zanje nayi shiri na dawo gareshi alokacin
daya dace .
koda gama fadin hakansai hatyan ya ruga izuwa
inda sadirat take zaune tana kuka ya
kama.hannunta ya tasheta tsaye yace
yake yar uwata zamanmu a garinnan ya kare
.dolene mu tafi izuwa inda zan tserar da
rayuwarki
iyayen mu sun mutu bamu da hujja ta sake zama
anan .
wanda ya rage mana kawai shine sarkin
mafarauta.
idan muka zauna agarinnan zamu janyo masa
kisa.
gama fadin hakan keda wuya sai hawaye ya
zubowa hatyan yaja sadirat izuwa inda dokinsa
yake ya dorata akai.
shima ya hau kan dokin yayiwa sarkin mafarauta
kallon karshe duk su biyun suna zubar da hawaye
.
ko tsinke su hatyan basu dauka ba amatsayin
guzuri kawai sai suka zaburi doki suka nausa
cikin daji
nan danan suka bace bat tamkar basu taba
wanzuwaba.
awannan lokacine zainur ya mike tsaye da kyar
yana tangadi kamar wanda yasha giya ya bugu
ya cire rawanin wani badakare ya nannade
dungulmin hannun nasa dakyar amma sai ya
kasa zama akan dokin ya kwanta cikin matukar
karfin hali ya kamo linzamin dokin ya dan ja.
dokin ya kama tafiya a hankali ya nufi hanyar da
zata mayar dashi gidan sarauta.
maimakon yarima zqinur ya isa gidan sarautar
acikin sa'a daya saidaya shafe sa'a biyu saboda
ya kasa sarrafa dokin yadda zaiyi sauri
dokin na isa kofar gidan sarautar sai yarima ya
fado daga kansa ya baje kasa sumamme .
a guje dakaru sukazo suka daukeshi suka tafi
dashi izuwa ga sarki.
koda akazo da yarima gaban sarki ya takarkare
ya kwarara uban ihu sannan ya kwallawa
likitansa kira. nan da nan kuwa saiga likitan yazo.
nanfa ya kama aiki akan yarima amma yarima
bai farfadoba sai bayna sa'a guda.
yana bude idonsa sai sarki ya dubeshi fuskarsa
nayin gyatsine yace
wanene yayi maka wannan danyen aiki?
yarima zainu ya budi baki yace hatyan ne dan
gidan makeri satyan.amma na kashe satyan.
kodajin haka sai sarki shamsan ya dafe kansa da
hannayensa biyu kuma ya durkusa kasa cikin
tsananin takaici ya dakawa yarima tsawa yace
.
cikin tsanani takaici ya dakawa yarima tsawa
yace
me yasa kaje gidan satyan bana hanaka zuwa
ba?
duk yadda akayi satyan nada ya mace kuma kayi
yunkurin yi mata fyade koma kayi mata hakane?
yarima ya budi baki yace hakane
dama satyan nada da babban jarumi haka wanda
har ya iya sare ma hannu?
yarma yace kwarai kuwa ni arayuwata ma in
banda kai ban taba ganin wani jarumi mai
irin jarumtakarsa da zafin namansa ba.:
kuma yace na gaya maka cewa shine jarumin da
zai karbi karagar mulkinka a hannunka
tabbas yasan yanzu kafi karfinsa amma ka
saurari dawowarsa cikin gagarumin shirin yaki.
koda jin haka sai sarki yahamsalya sake kwarara
uban ihu a karo na biyu wanda ya firgita duk
wata halitta dake gidan sarautar
kawai saiya mike tsaye zumbur ya shige cikin
dakinsa yayi gagarumin shirin yaki sannan ya
tura
aka kirawo sarkin yaki ya bashi umarnin a shirya
dakaru kamar guda dubu hudu su rabu izuwa
gabas da yamma kudu da arewacin birnin, su
bazama neman hatyan dan makeri satyan,
nantake sarkin yaki yaje ya cika umarni
shikuwa sarki shamsal sai ya hau dokinsa tare da
tsirarun dakaru suka tafi izuwa gidan makeri
satyan
kafin su sarki su iso gidan makeri satyan tuni
gaba
daya mutanen dake unguwar sunyi hijira sun
gudu izuwa wadansu unguwoyin sabo da sun san
halin sarkinsu na rashin imani dolene hatyan ya
shafa musu kashin kaji
shi kuwa sarkin mafarauta tuni ya dauke gawar
satyan data matarsa ya tafi dasu chan wani jeji
ya bunne su yana kuka da bakin ciki sannan
shima ya sake nausawa cikin daji rataye da
jakarsa ta guzuri da nufin ya tafi kenan har
abada bazai sake dawowa birnin bindal ba tunda
dama bashi da kowa face wannan abokin nasa
guda daya wato satyan gashi an kasheshi.
lokacin da sarki shamshal da tsirarun dakarunsa
suka iso kofar gidanmakeri satyan sai suka iske
unguwar tayi tsit tamkar makabarta
nantake sarki shamsal yasa dakaru suka shiga
cikin gidan satyan suka duba ko ina amma basu
ga kowaba.
suka shig gida gida nan ma basu ga kowa ba.
al'amarin daya fusata sarki kenan yace 。:
akona gaba daya gidajen dake ungwar kuma aje
ayi bincike agano mazauna unguwar akamosu
akawo su fada.
nantake dakaru suka cinnawa gidajen unguwar
wuta gaba dayansu suka kone kurmus.
mazauna unguwar kuwa daya bayan daya aka
dinga kamosu ana gana musu azaba suna bada
bayanin abin daya faru amma duk da haka ba'a
kyalesuba
domin akarshe kurkuku aka akaisu aka kulle
bayan sunsha muguwar wahala sannan ne sarki
ya sami labarin cewa hatyan ya dauke 'yar
uwarsa sadirat akan doki sun gudu.
abinda yasa dakarun da aka tura farautarsa basu
ganshiba shine
yafi sa'a uku da tafiya don haka yayi
musu nisa sosai .
dama kwanaki bakwai sarki shamsal ya baiwa
wadannan dakaru guda dubu dari hudu akan suje
suzo da jarumi hatyan da 'yar uwarsa sadirat .
kowacce runduna tadakaru dubu dari saida ta
dangane da karshen iyakar birni bindal aranar da
kwanaki bakwai suka cika
koda sarki shamsal yaji cewa ba'a gansu ba sai
ya kamu da tsananin mamaki gami da tsananin
fushi kuma hankalinsa
ya dugunzuma ainun.
ya zamana cewa ko barcin kirki bayayi saboda
kullum sai yayi mafarki mai ban tsoro .
acikin mafarkin sai ake nuna masa cewa ga
jarumi hatyan ya dawo birnin bindal tare da
miliyoyin dakarun yaki an kachame da azababben
yaki an kone gidan sarautar .
bisa wannan daliline sarki shamsal ya tura aka
kirawo masa bokansa abin dogaronsa boka
daizun ya sanar dashi halin da yake ciki kuma ya
bukaci ya samo masa mafita .
nan take kuwa boka daizun ya zuba alkalumansa
na tsafi ya shiga aiki.
bayan yayi dan dogon bincike saiya dago kai ya
dubi sarki shamsal lokacin da ya jike sharkaf da
gumi kuma idanunsa suka kada sukayi jawur
kamar garwashin wuta babu kyan gani sannan
yace
ya shugabana hakika al;amarin wannan yaro
akwai rikitarwa.
domin akwai sa'a da nasara acikin harkokinsa
tabbasa idan har ba'a gano inda yakeba an
kasheshi ba
to sai wannan mafarki naka ya tabbata
abinda na iya gani kawai shine wannan yaro tuni
ya fita daga kasarka tare da yar uwarsa domin
tafiya ya rinka yi ba dare ba rana.
kai lokacin da dokinsa ma ya sare goya yar
uwarsa yayi abaya yayita gudu da ita har tsawon
kwananki ashirin ba tare daya tsayaba.
ko sau daya bai tsaya ba don ya huta saidai
kawai yasha
ruwa ya mikawa yar uwarsa abinci da ruwa taci
ta sha yana kan gudun saboda yasan cewa an
biyo bayansa
yanzu haka yashiga wata kasa amma na kasa
gano bangaren da take.
duk yadda akayi wannan yaro yana da sirrin batar
da sawun hanya .
anya kuwa ba shida watal halaka da mafarauta
ba ?
kodajin wannan tambaya sai sarki shamsal yayi
shiru yana tunani har zuwa tsawon lokaci sannan
ya dago kai ya dubi boka daizur yace mahaifinsa
aminin sarkin mafarautane .
kodajin haka sai boka daizur haba shiyasa na
kasa
ganin komai akan wannan yaro
kayi sani cewa duk garinnan babu wanda yakeda
karfin sihirin tsafin sarkin mafarauta .
ni kaina awajensa nayi kartun tsafi amma har na
kammala bansan rabin nasa ilimin ba.
daga bayane nashiga duniya nasamo wadansu
sirrikan amma duk da hakan ina shakkar sarkin
mafarauta
.
Toh mun kawo karshen littafi na daya , in sha Allah gobe zamu fara littafi na biyu,
Al Amin Misau ke magana

TARKON MUTUWA
Abdul'aziz Sani Madakin Gini
07067470752
Typing. Prince Auwal Auzab
Post. Sunusi SAS

Littafi na biyu 2
Part 2A
.
Duk inda sarkin mafarauta yake ka tura aje azo
maka dashi amma bari na bincika naga inda
yakedin.
koda gama fadin haka sai boka daizun ya zura
hannun cikin aljihu ya fiddo madubinsa na tsafi
ya ajiye a gaban sarki sannan ya shafi madubin
da hannunsa na hagu maimakon madubin yayi
haske ya nuna abinda ake so a gani sai yayi
duhu dudum ba a ganin komai ko da ganinin haka
sai boka daizun yayi ajiyar zuciya yace
hakika ai sarkin mafarauta yaudararka yayi kuma
yaci amanarka tabbas da taimakonsa wannan
yaro hatyan da 'yaruwarsa suka sami nasarar
guduwa
kodajinhaka sai bakin ciki ya turnuke sarki
shamsal yasake kurma uban ihu akaro na biyu
kamar zai fashe da kuka
sai daya shafe kusan dakika dari da ashirin yana
huci da numfarfashi tamkar wani kumurcin maciji
sannan yace
yakai abin dogarona kayi sani cewa zama bai
kamaniba
dakaina zan tafi farautar wanna yaro domin na
kasheshi tungabanin lokacin da zai dawo ya
riskeni harcikin masarautata ya cini da yaki
taimakon da nake nema awajenka guda dayane.
inason ka banj hadimanka na aljanu kamar guda
dari biyar wadanda zasu dauki manzannina
sukaisu izuwa ga dukkan kasashen dake wannan
nahiya tamu .
zasu kai wasiku ne gami da hotuna masu dauke
da taswirar hatyan da yar uwarsa
acikin kowacce wasika zan gaya kowanne
sarki dayasa abaza hotunan hatyan abirni da
kauye duk inda aka gansu akamasu a tsare su
akurkuku.
sannan kuma zansan ya lada mai tsoka na
dubban darhami ga duk wanda ya sami nasarar
chafkesu.
inason cikin kwananki uku kachal agama rarraba
wadannan wasiku da hotuna
kodajin wannan batu sai boka daizun ya kyalkyale
da dariyar mugunta yace
ya shugabana hakika kazo da shawara mai kyau
domin itace hanyar da zakabi ka hana hatyan da
yaruwarsa samun damar fita daga wannan nahiya
kuma acikin kankanin lokaci zasu dawo hannuka
tabbas kwakwalwarka tana aiki sosai gami da
hangen nesa
kodajin wannan zuga sai sarki shamsal ya bushe
da dariyar farinciki yashiga yiwa kansa kirari
batare da bata lokaciba sarki shamsal ya tura
akazo da wani makocin satyan sannan aka
kirawo masanin zane
take makocin ya baiyyana kamannin fuskar
hatyan da fuskar yar uwarsa sadirat
cikin kankanin lokaci mai zanen yafitar da
taswirar tamkar sune awajen ba zanasu akayiba
shikuwa boka daizun sai yayi tsafi takardar zanen
ta tsaga kanta har guda dubu dari .
daga nan kuma sai aka tara manzanni aka
rarraba musu wasiku da hotunan hatyn.
dayawa aka kirawo aljanu suka tafi dasu izuwa
dukkan kasashen dake nahiyar
++ AUWZAB
al'amarin yarima zainur kuwa sai daya kwana
ashirin da daya akwance yana jinyar dungulmin
hannunsa sannan ya warke ya sami karfin jikinsa
.
duk lokacin daya kalli dungulmin hannunsa kuma
ya tuno da cewar bai sami nasarar yiwa sadirat
fyadeba .
saiya fashe da kukan bakinciki daga wannan
lokaci
yammatan birnin bindal suka sami nutsuwa da
kwanciyar hankali domin yarima zainur bai sake
yiwa wata fyadeba.
kawai ma sai yazamana cewa ya daina neman
mata koda karuwai kuwa
kuma bashi da wani buri wanda yafi yaji cewa an
kamo hatyan da yaruwarsa sadirat
idan har sukazo hannu to yaci alwashin saiya
cika burinsa akan sadirat agaban hatyan kuma
yayi amfani da lafiyayyen hannunsa ya sare
hannun daman hatyan
kullum yarima zainur cikin sambatu yake na fadin
wannan buri nasa kamar wanda ya zautu .
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU ABIRNIN
BINDAL BAYAN KASHE IYAYEN JARUMI HATYAN
SUKUMA SUNYI GUDUN HIJIRA TARE DA
YAR'UWARSA SADIRAT SUN NAUSA DAJI BA
TARE DA SUNSAN INDA SUKA DOSA BA.
al'amarin su jarumi hatyan kuwa lokacin daya
zaburi dokinsa da gudu izuwa cikin daji
sadirat na goye abayansa saisuka ci gaba da
tsala gudu akan doki baji ba gani kamar ba zasu
taba tsayuwaba.
saida suka shafe sa'a uku suna yin gudu sannan
dokin ya fara gazawa ya zamana cewa ya rage
karfin gudunsa kai sai da takai cewa ma dokin ya
galabaita ya
fara sassarfa kamar zai durkushe kasa
koda ganin haka sai jarumi hatyan ya ja linzamin
dokinsa ya sauka .
saukarsu keda wuya sai hatyan ya saki dokin ya
kadashi ya ruga izuwa wani bangaren dajin
cikin kaduwa sadirat ta dubi jarumi
hatyan tace
ya zaka sallami dokin alhalin bamu san iyakar
inda tafiyarmu zata yankeba.?
kodajin wannan tambaya sai jarumi hatyan yayi
doguwar ajiyar zuciya yace
ai wannan doki amfaminsa ya kare awajenmu
tunda ya taimkemu wajen bawa makiya tazara
mai yawan gaske
amma idan mukaci gaba da fiya dashi sawayen
kofatonsa ne zasu tona mana asiri.
yake yar uwata ki kwantar da hankalinki kiyi sani
cewa indai kina tare dani babu abinda zai
sameki.
sadirat tace
ni kaina ina jin hakan ajikina amma abinda nake
jiye mana shine yankewar guzuri ni kam
Hankalina atashe yake saboda naga abincin daya
rage acikin jakarka kadai.
kodajin wannan batu sai hatyan yai murmushi
yace ai indai muna cikin jeji ji nake kamar muna
gidane agaban umma.da.abba
kodajin haka sai idanun sadirat suka ciko da
kwalla,
hawaye ya subuto mata ta rungume hatyan
kuma ta fashe da kuka tana mai cewa
yanzu shikenan mun rasa abba da umma har
abada.
kuma ko kabarinsu bazamu sake ganiba?
wata.kilama a.filin Allah akabar.gawarwak
insu
anan zasu bushe harsu dai daice
sa'adda jarumi hatyan yaji wannan batun na
yar uwarsa sadirat sai shima zuciyarsa ta karaya
har hawaye ya.subuto masa ya dubeta yace
gawar iyayenmu bazata tabeba domin na
tabbatar da cewa sarkin mafarauta zai kwashesu
yayi musu kabari
kada ki manta cewar komai daren dadewa sai
munkoma birnib bindal na dauki fansar ran
iyayenmu
lallai saina.kashe sarki shamsan agaban idanun
yarima zainur kuma na haye kan karagar
mulkinsa domin kawo karshen zaluncinsa.
yanzu dai bari mu nemi inda zamu dan yada
zango muci abinci mudan huta
sannan muci gaba da tafiya.
kodajin haka sai mamaki da tsoro ya
kama.sadirat tace
yanzu kana nufin kace adaren nan zamuci gaba
da tafiy maimakon mu sami inda.zamu fake mu
kwana?
hatyan yace ai tsayuwar mu adaren nan har takai
ta sa'a guda hatsarine agaremu saboda na
tabbatar
da cewa sarki ya turo dakarunsa subiyo
bayanmu kokarina shine mufuta daga kasarnan
gaba daya mu shiga wata kasar .
daga chan ma ci gaba da tafiya harsai
mun fice daga nahiyar nan gaba daya
sannan zamu sami kwanciyar hankali .gama fadin
haka keda wuya sai hatyan ya kama hannun
sadrat ya jata suka kara gaba amma saitaga ya
kan sunkuya kasa ya debi kasa ya shinshina
kuma taga ya sauya hanya .
al'amarinda yayi matukar bata mamaki kenan ta
dubeshi tace
waishin mene.ma'anar wannan abu da kakeyi?
hatyan yace inayin haka ne domin na gano zamu
samu rafi a kusa domin musa kuma muyi
guzurinsa da yawa kiyi sani cewa ruwa yafi
abinci
mahimmanci arayuwar dan adam domin zamu iya
kwananki bakwai babu abinci amma ba zamu iya
jure kishirwa ta yini ukuba
aikuwa kamar tsafi sai sadirat taga sun iso kusa
dawata korama mai dauke da ruwa garaigarai .
ruwan tafiya yake da gudu yana kwaranya kasan
wani dutse .
cikin farinciki suka ruga izuwa bakin koramar
suka sa hannayensu suka kwarfo ruwan suka
sha.
daga nan sai htyan ya bude jakar guzurinsa
yadauko abinci wanda bai wuce loma gomabaa
suka ci tare suka sake kora ruwa
gama hakan keda wuya saiya cika battocin su da
ruwa
ya mika mata ta rike yace yanzu zan goya ki
abayana zanyi gudu dake na tsawon kwanaki
ashirin.
duk sa'adda kikaji kishurwa ko yunwa ki dauki
abincin da yake cikin battarki kici kuma kisha
ruwan battarki
ki sani cewa a tsawon kwana ashirin ba zamu
tsaya ba domin ki huta koda kuwa kin gaji da
zama abayana
lokacinda hatyan yazonan azancensa sai sadirat
tayi mai kallon mahaukaci tace ni bantaba jin
inda bil'adama ya yita jure guduba harna
tsawon kwanaki ashirin ba baci basha ko kuwa
kana nufin wani
aljanin zamu hau?
wai shin idan ma wata lalura ta kamanifa
tafitsari ko kashi?
kodajin wadannan tambayoyi guda biyu sai
jarumi hatyan ya bushe da dariya yace aikuwa
zan baki mamaki saboda ni tun ina da shekara
goma aduniya duk sa'adda na shiga daji farauta
sainayi kwana ashirin ina gudu baci sai shan
ruwa.
kuma wannan gudu da nakeyi tsere nake da wata
sihirtacciyar bauna harsai na kure mata gudu na
risketa mun fafata kazamin yaki
akarshe saidai wuya tasa ta juya da gudu ta
barni
gudun kwana ashirin da nakeyi dadai yake da
tafiyar kwana saba'in da tara akan doki
wannan gudu nawa baiwa ce zallah
ina nufin da ita aka haifeni
kodajin wannan batu sai mamaki ya turnuke
sadirat.kuma hankalinta ya sake kwanciya taji ta
sake samun nutsuwa ta cewar wannan kani
nata.zai iya kareta daga sharrin sarki shamsal
batare da bata lokaciba kuwa sai hatyan ya
rankwafa sadirat ta hau bayansa ya goyata
sannan ya daureta tamau ajikinsa
battar ruwansa kuwa na ruke ahannunsa na
dama takobinsa kuwa na.sakale a cinyar sa
tadamansa
kawai sai ya falfala da azababben gudu izuwa
cikin daji nanfa sadirat ta dinga ganin abu kamar
wasa.
domin saboda karfin gudun hatyan har tashi
sama yake yana tsallake gajerun bishiyoyi da yan
duwatsu da kwazazzabai .
wani lokacin kuma sai taga kamar akan iskar
cikin sararin samaniya suke tafiya saboda karfin
gudun
sau tari bata sanin sa'adda barci yke dauketa
kuma.duk sa'adda da ta farka da taji kishirwa sai
ta bude battarta ta kwankwada.ta koma barcinta
.
abu dai kamar wasa sai suka shafe kwana
ashirin
suna.tafiya.
tuntana kirga kwanakin har lissafin ya kwace
mata ta manta
abinda yafi daure mata kai shine tunda aka fara
wannan tafiya bata gajiba kuma bataji kashi ba
ko fitsariba.tamkar bataci ta sha ba
abinda kawai takeji shine yunwa da kishirwa
kuma.da.zarar taji su din sai ta dauko abincinta
da battar ruwanta wadanda suke jikinta kawai
taci kuma tasha........
TARKON MUTUWA
Abdul'aziz Sani Madakin Gini
2 B
A ranar kwana na ashirin dinne suka hango kofar
wani babban gari daga nesa
awannan lokaci safiyace
cikin farinciki hatyan ya tsaya da gudu ya kira
sunan sadirat
amma sai yaji shiru bata amsaba
koda yadan waigo sai yaga ashe barci takeyi
nan take ya kwanceta daga
bayansa sannan ya shimfideta akasa.
asannane yaji wata irin muguwar gajiyar
gudun dayasha ta zo masa gamida
matsananciyar yunwa
don haka baisan sa'adda ya sulale kasa ba
karar faduwar tasace tasa sadirat ta farka daga
barcin da takeyi .
tana bude ido taga hatyan akwance akasa jikinsa
na kakkarwa tamkar mai cutar farfadiya
cikin rudewa ta kamoshi ta dora kansa akan
cinyarta ta yayyafa masa ruwa
nantake yayi dogon ajiyar numfashi ya budi baki
dakyar yace
da ita ta bashi abinci
cikin rawar jiki ta bude jakar guzurinsa ta fiddo
abinci wanda bai wuce loma biyarba
tarinka bashi abaki da hannunta
abincin na karewa ta kora masa da ruwa
asannanne hatyan ya dan dawo cikin hayyacinsa
ya dubeta yace
nagode da kika ceceni daga yunwar kwana
saba'in da tara
cikin tsananin mamaki ta dubeshi tace bangane
yunwar kwana saba'in da tara baca, nake cewa kayi
gudun kwana ashirin zamuyi?
hatyan yace ai guduna na kwana ashirun daidai
yake da tafiyar kwana saba'in da tara akan doki
kinga kenan tafiyar da mukayi yanzu ta kusan
wata ukuce
wannan ne dalilin da yasa komai saurin dakarun
da sarki shamsan zai turo su kamamu
bazasu iya riskarmu ba
yanzu dai ga wani babban gari nan agaban mu
kuma dolene mu gaggauta shiga cikinsa
domin haryanzu jikina rawa yakeyi saboda yunwa
inason na sami abinci isashshe naci na koshi
ammafa bazamu iya shiga cikin garinba kai tsaye
dolene muyi yar dabara saboda tsaro
gama fadin hakan keda wuya sai ya dafa
kafadarta ya karanta wadansu dalasimai na tsafi
faruwar hakan keda wuya sai nan take shi ya
rikide ya zama tsoho rike da sanda ahannunsa
ita kuma saita zama yarinya karama yar kimanin
shekara goma
kawai sai ya dubeta yace
sunanki sahalu maza yimin jagora mushiga cikin
garin nan muna bara
batare da wata gardama ba kuwa sadirat ta
kama sandar dake rike ahannunsa tajashi
suka nufi kofar babban birnin kai tsaye bada
wata fargaba ba
da isowarsu bakin kofar birnin suka kamu da
tsanani mamaki kuma tsoro ya shigesu amma sai
suka basar
suka ci gaba da bara don kar mutane su ganesu
bakomai ne ya basu tsoro da mamaki ba face
ganin taswirar fuskokinsu
bisa takardu an lika ako ina a jikin bango baja
baja
kuma ajikin taswirar an rubuta cewa wadan nan
manyan masu laifine na sarki shamsan
don haka ana nemansu ruwa ajallo
duk wanda yakamasu ko yafadi inda suke za'a
bashi ladan dinare dubu dari ....gaskiya ni auwzab nasan
inda suke zanfada abani rabona.....
hatyan da sadirat na cikin karanta wannan bayani
abakin kofar birinin sai shugaban dakarun dake
tsaye awajen
wani narkeken katone sai ya dubesu yace kai
wannan almajiri
su waye ku kuma taya akai kuka iso nan alhalin
kai makahone shikuma dan jagoranka yaro ne
dan karami?
kodajin wannan tambaya sai hatyan ya rikirkice
irin yadda tsofaffi keyi yace
yaro harkasa hantar cikina ta kada saboda
wannan tsawa taka
mu bakine daga kasar misra kuma tare muke da
wani ayari na fatake acikin jirgin ruwa
jirgin namune yayi hadari a kusa da gabar
wannan birni naku
ya nutse akarkashin ruwa
kadanne daga cikinmu suka ragu shine muka
rarrabu acikin daji saboda firgita.
dakyar muka gane hanya muka iso nan
kodajin wannan batu sai wani can daga cikin
dakarun yace
hakika wannan makaho yayi gaskiya domin tun
shekaran jiya ire iren wadannan fatake suka
shigo garin nan suka bada labari irin wanda
wannan ya bayar
kodajin haka sai shugaban dakarun yasa aka
budewa su hatyan kofa suka kunna kai ciki
suka durfafi cikin gari kai tsaye ba tare da
fargabar komaiba
nan dai suka tambayi hanyar kasuwa aka nuna
musu .
kawai sai hatyan yace da sadirat
ki nemi babban wuri inda ake sayarda abinci mai
rai da lafiya ki kaimu
Kodajin haka sai mamaki ya kamata tace
yaya mu da bamu da kudi zakace muje wajen
abinci mai tsada ?
kodajin haka sai hatyan yayi murmushi yace
waya gaya miki bamu da kudi?
to ki sani cewa duk kudaden da sarkin mafarauta
ya tara mini suna hannuna.
ba wai abinci mai tsada ba hatta gidan kwana
mai tsada zamu kama haya
amma ba zamu wuce kwana ukuba agarinnan
zamu kara gaba
don kada asirin mu ya tonu ..ni auwzab zantonama kuwa
ehe...
kuma kinsan cewa so mukeyi mubar nahiyar
gaba daya
ba tare da sadirat tayi wata gardama ba.
sai taci gaba da jan hatyan sukaci gaba da tafiya
acikin kasuwar har suka iso wani babban gidan
abinci
kai tsaye suka kunna kai ciki
suna shiga suka iske jama'a azazzaune sunacin
abinci
ai kuwa sai jama'a suka zuba musu idanu gaba
daya.
abu na farko dai kowa yana mamakin abinda ya
kawo almajiri irin wannan gidan abinci mai tsada
haka
idan har yana da kudin siyan abincin da manyan
mutane suke siya to lallai yana da makudan
kudade ajikinsa
hatyan ya yiwa gaba daya mutanen dake dakin
siyan abincin kallo daya amatsayin shi makahone
sai yaga cewa daka dakarun birnin acikin batar
da kama sai wadansu jarumai masu kirar karfi
kuma mafi yawansu suna rike da takardun
taswirarsa data sadirat.
acan gefe daya kuma sai yaga wani boka azaune
akan tebur shi kadai
tunda suka shigo gidan bokan ya kurawa hatyan
idanu ko kiftawa bayayi
nantake hatyan yasa jinin jikinsa yasan cewa
wannan boka ya gane koshi waye
kawai sai hatyan yayiwa sadirat rada akunne
yace
muje kan wancan teburin da babu kowa mu
zauna
kuma duk bala'in da zai faru anan karki kuskura
ki tashi daga inda kike
kodajin wannan batu sai hankalin saidirat ya tashi
don tasan cewa dolene ayi fitina acikin wanan
dakin abinci.
nan sadirat ta ja hatyan takaishi izuwa teburin da
babu kowa akai suka zauna
har a sannan kallonsu akeyi da mamaki
zamansu keda wuya sai wata ma'aikaciyar gidan
abincin doguwar mace mai dan kyau
wacce shekarunta bazasu haura talatinba
tazo garesu
tadubi sadirat tace dan samari me za'a kawo
muku?
farat daya sai hatyan ya tari nunfashin sadirat
yace
ni katuwar kaza zaki kawo mini gami da shin
kafa da ruwan inibi
kodajin haka sai matar ta bushe da dariya tace
haba shiyasa jikinka yake da kyau baba
fatar jikinkama bata da alamar tsufa
dolene ka zamo lafiyayyayen namiji mai kwari
zan iya aurenka inda kana sona
kodajin haka sai sadirat ta murtuke fuskata dubi
matar tace
nidai ki kyalemin babana kije ki kawo mana
abinci kawai kuma nima irin nasa zaki kawo min
matar tai murmushi tace
babu laifi idan da yayi halin ubansa
ai barewa batayi guduba danta yayi rarrafe
koda gama fadin hakan sai matar taje ta kawo
musu abinci a farantai biyu ta ajiye agabansu
nanfa suka kama cin abincin hannu baka hannu
kwarya saboda rabonsu da cin abinci mai dadin
haka tunkafin su baro birnin bindal.
koda jama'a suka ga yanayin cin abincin su hatyan
sai suk bushe da dariya saboda azatonsu
kauyawane don basu saba cin abinci maidadin
haka ba.
wannan boka fuskarsa amurtuke bai yin dariya
kuma bai dauke kansa daga kansu hatyan ba har
suka kammala cin abincin.
bayan sun kammala cin abincin har sun wanke
hannunsu sun karasa shan ruwan inibin sai
hatyan ya sanya hannunsa acikin jakar guzurinsa
ya dauko zinare sannan ya ware iya kudin
abincinsu ya bayar
ashe daga cikin jaruman da suke zaune agefe
daya kimanin su ashirin barayine
kuma suna lura da jakar guzurin da ke hannunsu
hatyan
kawai sai daya daga cikinsu yazo wajen su
hatyan ya zare wuka ya dora awuyan hatyan ya
daka masa tsawa yace
kai tsohon banza maza ka bani jakar guzurinka
ko kuma yanzunnan na shaftarema makogwaro
tuni awannan lokaci jikin sadirat yafara karkarwa
saboda tsoro
shikuma hatyan yayi kamar yatsoratan
ya yunkura kamar zaisa hannunsa ya cire jakar
amma sai yayi wuf ya kwaci hannun barawon
ai kuwa sai barawon ya kwalla uban ihu ya saki
wukar dake hannunsa ta fadi kasa saboda ji yayi
kamar hannunsa zai karye
kawai riko yaji irinna sadaukai koda
ganin haka sai yan uwan barawon suka mike
zumbir suka zare makamansu suka afkawa
hatyan.
kafin su riskeshi tuni sandar hanunsa ta rikida ta
zama takobi
nanfa suka rugumtsume da azababben yaki
aka fara kakkarya teburan abinci jama'a suka far
kama gudu da ihu
kafin kace wani abu saura wannan boka da
dakarun birnin kawai atsaye gefe daya suna kallon
gumurzun da akeyi
sai kuma wannan mace wacce ta kawowa su
hatyan abinci atsaye gefe daya tana ihu da fada
wai an lalata mata dukiya
ashe gidanabincin nata ne
cikin abinda bai wuce dakika dari da shirinba
hatyan ya kakkarya wadannan barayi kimani su
ashirin ya zubar dasu kasa sunata koke koke
takobinsa kawai kare hare harensu ya keyi da ita
amma bata sha jikin ko dayabada tsagwaron karfin
damtse ya gama dasu
shikansa wanna boka da dakarun birini da mai
gidan abincin sunyu matukar mamakin karfin
hatyan
itakuwa sadirat tunda aka fara fadan saita
dunkule akan kujerar da take zaune ta hade kanta
da cinyoyinta.bata dagoba saida taji gidan yayi
tsit batajin komai sai koke

Please Login or Register in order to submit comment