Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jarumi hatyan da 'yar uwarsa
sadirat suna cikin kewar mahaifansu
kuma suna son su ziyarci kabarin iyayensu
sannan sunason su sake ganawa da sarkin
mafarauta
koda sarki yazo nan azancensa sai farinciki ya
lullube badi'atul nauwara tace
yakai
wannan sarki mai daraja kayi sani cewa nayi
alkawarin zanyi duk wannan abu da ka
umarceni
dayi
kuma kaima ina mai godiya agareka
ubangiji ya saka maka da alheri
nantake sarki dasu nasmal dasu hatyan
suka dunguma gaba daya
suka koma cikin gidan sarautar jama'ar gari
kuwa sai suka rude da shewa
gamida farinciki
garin ta dauka gaba daya anata kade kade
da wake wake na murnar zuwan sabon addini
dakuma samun kwanciyar hankali na kashe
uwar
macizai
duk inda mutum ya zaga agarin babu abinda
zaiji
mutane na tattaunawa face batun jarumtakar
badi'atul nauwara da kuma sabon addinin
musulunci
amasauki na musamman aka sauki badi'atul
nauwara
kuma jarumi hatyan da sadirat ne debe mata
kewa
suka ci abincin dare tare suna cikin cin abincin
ne hira ta barke a tsakanin su
badi'atul ta dubi sadirat cikin murmushi tace
yake kawata an bani labarin gasar da akayi yau
tsakanin yarima nasmal gashi babu wanda ya
sami nasara
to yanzu a tsakanin yarima nasmal da boka
aimar wa zaki zaba amatsayin mijinki?
kodajin wannan tambayar sai kunya ta kama
sadirat tace
to ai irin wannan matsalar ce akan dan uwana
hatyan
shikansa ya kasa gane macen daya dace
ya zaba amatsayin matar aure atsakanin
gimbiyoyi guda biyu
idan har zai iya fitarda zabinsa yanzu anan
gabanmu
nima zan iya fitarda nawa zabin....
SAI JAHANGO, TO ALLAH YARU'EN.
TARKON MUTUWA
LITTAFI NA TARA
Part 9 C
.
Kodajin wannan tambaya sai kunya ta kama
sadirat
to irin matsalar ce akan dan uwana hatyan
shi kansa ya kasa gane macen daya dace ya
zama
amatsayin matar aure tsakanin gimbiyoyin nasa
guda biyu
idan har zai iya fitar da zabinsa yanzu anan
gaban mu
kodajin wannan batu sai badi'atul nauwara
ta murtuke fuskarta ta sauya maganar da cewa
yanzu yaushe ya kamata muyi shiri mubar garin
nan don komawa tamu nahiyar ?
kodajin wannan batu sai hatyan yayi murmushi
yace
ai yanzu tunda mun zama ma'a bota addinin
musulunci
bamuda wani shiri saina ubangijin musulunci
saboda haka zaifi kyau mu tsaya mu dan sami
ilimi na addinin
daga cikin littattafan tarihin da suke cikin birnin
nan
don mu koyi yadda ake ibada zamufi jin dadin
fara wannan babban aiki
dake gabanmu mu jaddada addinin anahiyarmu
kafin sannan ma kan uwar mazizai ya bushe
zamu daukeshi babu nauyin komai muji dadin
tafiya tare dashi
kodajin wannan shawara sai murna ta kama
sadirat
da badi'atul nauwara saboda sanin cewa yazo
da
shawara mafi kyau da alheri
wɑɳɳɑɳ รɦiɳɛ ɑɓiɳ ɗɑyɑ Բɑʀu ɑɓiʀɳiɳ รu
yɑʀiɱɑ ɳɑรɱɑʆ
ɓɑyɑɳ รɑʀɑuɳiyɑ ɓɑɗi'ɑtuʆ ɳɑuwɑʀɑ t ɓɑyyɑɳɑ
tรuʆuɱ tɑ kɑรɦɛ uwɑʀ ɱɑcizɑi
Acan birnin sarauniya anisa kuwa bayan ta
sauko
case daga kan tsuntsun tsafi ta taimakawa
jama'ar ta dayawa wajen ceton rayuwarsu daga
annobar ambaliyar ruwa da rugujewar gidaje
saidata tara gaba dayan yan majalisarta d
bokayenta
afadarta alokacin da komai ya lafa ta dubesu
tace
yaku jama'ata dukkaninku kunga masifar data
samemu kuma ba komai ne ya haddasa hakan
ba
face bayyanar uwar macizai kuma ba kowane ya
tasheta ba face sarki shamsal saboda kawai ya
kashe mutum biyu rak acikin wannan duniya
bisa binciken da nayi yanzu na gano cewa
sama da mutum miliyan dubu uku ne suka rasa
rayuwakansu
a sassan duniya, dukiya kuwa bata da adadi
wacce ta salwanta atarihin duniya ba'a taba
samun
mugun tarkon mutuwa irin wannan, lallai sarki
shamsal ya cika mara imani
da tausayi kuma babu mai son zuciya kamarsu
to yanzu dai gashi komai ya lafa alokaci guda
shin uwar macizai
ta kashe mutane biyun da akeso ta kashe ne ko
kuwa itace ta mutu?
amsar dana kasa samu kenan domin nayi iya
bincike na
naga hakan amma madubin tsafin yaki nuna
mini
komai
al'amarin daya firgita ni ainun domin ban taba
haduwa
da matsalar dana kasa gano mafitarta ba
amadubin tsafina ba sai wannan karon
bisa wannan daliline na taraku anan inason
gaba daya bokayenmu ababan dogaron birnin
mu
kuma dirkokin wannan birnin su hada
karfi da karfi yanzu su binciko mana abindake
faruwa
domin musan matakin da zamu dauka
babban dalilina akan hakan shine yanzu fa sarki
shamsal ya tsaga jini
abinda nake nufi shine tunda her ya sami
nasarar
kashe hatyan
da 'yar uwarsa
da uwar macizai tofa nan gaba zai iya tunanin
amfani da uwar macizai
wajen murkushe dukkanin manyan sarakunan
duniya
domin ya kasance shine yake mulkin duniya
duka
yanzu na umarceku yaku manyan bokayenmu
daku hanzarta yin wannan aiki domin na zartar
da hukunci
koda sarauniya anisa tazo nan azancenta
say gaba dayan bokayen da fadawanta sukayi
tsuru tsuru
suka kama kallon junansu kawai aka race wanda
zaice kala
al'amarin daya fusata sarauniya anisa kenan
bata san sa'adda ta daka musu tsawa ba tace
shin kurame ne ku bakuji abinda na fadaba
ne kokuwa kunason kuci amanar kasarku ne?
dajin wannan batu sai babban boka na birnin
wanda ake kira da suna muzaid bin amfasi
yayi gyaran murya ya bude baki cikin rawar
murya
tamkar wanda aka cika bakinsa da laka yace
ya shugabata al'amarin nan babbane ,idan aka
tono cikinsa
zamu iya rasa addininmu d muka gada tun
iyaye
da kakanmi
zaifi kyau mu bar wannan magana kawai muci
gaba da zuba idanu muga abin da kaddara zata
kawo
kodajin wannan batu sai anisa ta zabura cikin
tsananin fushi
ta zare takobinta lokacin da jikinta ya kama
kyarma
ta dakawa boka muzaid tsawa
ya firgita ainun her hantar cikinsa ta kada
sannan ta dubeshi tace
kai muzaid na rantse da darajar iyaye na akan
kishin kasata da addinin da muka gada
ina yi make kashedi na karshe kafin takibina
tasha jinin jikinku gaba dayanku nan ka
hanzarta
sanar sani abinda ke faruwa
kodajin wannan batu sai gaba daya bokayen da
'yan majalisarta suka furgice dama dukkaninsu
sun tsufa
babu dan kasa da shekaru saba'in kuma sun
san
cewa
bazasu iya sarrafa sarauniya anisa ba da karfin
damtse kona sihiri
can sai wani tsoho mafi tsoro acikinsu wanda
baya son mutuw
yayi caraf yace
ya shugabata kiyi mana rai ni zan gaya miki
gaskiya
al'amarin daya faru tun dazu muka zauna muka
gama binkice
muka gano cewa an kashe uwar macizai kuma
ba wanine ya kasheta ba face kawarki sarauniya
badi'atul nauwara
itama ba karfinta bane sa'ace da karfin.........
......
caraf sai boka muzaid ya shammaci mai
maganar ya gabza masa naushi awuya
take mai maganar ya zube kasa sumamme
boka muzaid ya dubi sarauniya anisa afusace
yace
ba zamu gaya miki wannan sirriba saboda
bamaso
ki rushe mana addininmu don haka mun zabi
mu
bayar da jininmu don kare addininmu
maza ki hanzarta kashemu
ke muke jira
.kodajin wannan batu sai sarauniya anisa ta
kyalkyale da dariya
lokaci guda kuma ta murtuke fuskarta tace
ai kuma yanzu na gane abinda ya faru
sarauniya
badi'atul nauwara
ta sami nasarar kashe uwar macizai ne da karfin
ubangijin musulunci
saboda me kuna ganin gaskiya karara amma
zaku taketa ?
kodajin wannan batu sai gabe dayan bokayen
da
fadawanta
suka sakeyin tsuru tsuru alamomin rashin
gaskiya suka bayyana karara akan fuskokinsu
koda ganin haka sai sarauniya anisa tayi
murmushi tace
kuyi sani cewa tun ina yarinya karama 'yar
shekara tara
naga wani littafi acikin gidan tarihin kasarnan
wanda aka boye shi a inda babu wanda zai iya
daukoshi
amma saboda hatsabibanci na sai dana
daukoshi
na karance shi tsaf asirrance na mayar dashi
ba tareda wani ya gani ba babu komai acikin
wannan littafi
face tarihin ma'abota addinin musulunci da
kuma
ma'abotansa
kalmomin da akayi amfani dasu acikin wannan
addini
kunne bai tabajin kamarsu ba kuma mutum ko
aljan bashida basira ko hikimar da zai iya shirya
wannan zance
zance ne irin wanda da zarar kunne yajisu sai
dukkanin tsigar jiki ta tashi
take zuciya take karbarsa ya mamaye tsoka,
kashi da jini
saboda zance ne na gaskiya wanda babu karya
acikinsa
tun asannan ne jikina ya baini cewa lallai
wannan
addini
shine addinin gaskiya sauran addinai kuwa
mutane ne suka kirkireshi saboda son zuciya da
son duniya
kuyi sani cewa zabi biyu gareku kacal
kodai ku karbi wannan addini ku tsira da
rayuwarku
data 'ya'yanku kuma ku tsira da kasarku
ko kuma ku rasa komai da kowa domin idan
rana
ta fito hannu baya kareta
lokacin da bayyanar hasken gaskiya yazo dolene
duhun karya ya yaye
shawara ta rage ga mai shiga rijiya
ni yanzu zan tafi neman kawata sarauniya
badi'atul nauwara aduk inda take
domin na karbi wannan addini na gaskiya
ahannunta
kodai ku karbi addinin ko kuma na dawo na
share
ku
na kafa addinin gaskiya abayan babu ku
kafin daya daga cikin bokayen yace wani abu
tuni sarauniya anisa tayi girgiza ta bace bat
daga cikin dakin taron tamkar bata taba
wanzuwa ba
al'amarin daya firgita bokayen da fadawan
kenan
suka shiga duba madubin tsafi domin suga inda
take
amma sai abu ya gagara
al'amarin daya kara firgitasu kenan hankalinsu
ya dugunzuma ainun suka rasa abindake musu
dadi aduniya
al'amarin sarki shamsal kuwa lokacin nan da
kasa
ta kama girgiza dashi sa'adda ya dafe akan
wannan babbar gada da take birnjnsa
koda gadar ta karye ta rikito dashi kasa izuwa
cikin ramin dake karkashinta mai mugun zurfi
sai ya kurma uban ihu ya dimauce yamanta da
batun
ya ceci kansa ta hanyar amfani da karfin sihirin
tsafi
bisa rashin sa'a kuwa saiya fado akan wani
karfen gadar
namtake karfen ya gutsire masa kafarsa guda ta
hagu
ya baje awajen sumamme
scan cikin birnin bindal kuwa bayan komai ya
lafa anyi asarar dukiya mai yawan gaske
sai yarima zainur yayi shiri tareda dukkan
dakarunsa
suka fito izuwa wajen garin don ganin barnar da
annobar ta haddasa musu
saboda sunji karar karyewar wannan babbar
gadar
koda suka iso wajen sukaga yadda gadar ta rabe
gida biyu
sai suka cika da tsananin mamaki
suka rugo izuwa bakin ramin suna lekowa sai
suka hango sarki shamsal
akwance akasan gadar asume ga kafarsa guda
ayanke
tana zubar da jini mai yawan gaske koda
ganinsa
acikin wannan hali sai yarima zainur ya tarkare
ya bushe da mahaukaciyar dariya al'amarin
daya
matukar baiwa dakarunsa mamaki kenan
amma da yake sunsan cewa bashida imani
kamar
uban masa sai suka basar
zainur ya dubi mutum hide daga cikin
dakarunsa
yana mai daka musu tsawa
ya basu umarnin suyi sauri su sauka kasan
ramin
su dauko sarki shamsal
nantake kuwa aka zarga igiyoyi suka sauka can
kasan ramin
suka dauko sarki shamsal assume aka koma
cikin
birnin bindal
har aka ajiye sarki shamsal akan gado bai
farfadoba daga dogon suman da yayi sai bayan
sa'o'i uku sun shude
koda sarki shamsal ya bude idanunsa ya tsinci
kansa
akan gadonsa kuma acikin turakarsa saiya kamu
da tsananin mamaki kawai saiya yunkura da
nufin
ya mike tsaye amma sai yaji ya kasa sakamakon
bashi da kafa guda
nantake zufa ta karyo masa jikinsa ya kama
karkarwa
cikin tsananin tsoro ya kama mayafin da aka
lullube jikinsa
dashi ya janye shi kawai saiyaga bashi da kafa
ya tabbata ya zama musaki
koda tabbatar da hakan saiya takarkare
yakwarara uban ihu
mai tsananin firgitarwa tamkar zaki uban dawa
yayi ruri
faruwar hakan keda wuya saiga yarima zainur
ya
shigo cikin turakar shi kadai fuskarsa cike da
annuri
yana yiwa sarki shamsal murmushin mugunta
koda zainur yazo daf da sarki shamsal yadda
tazararsu
bata wuce taku ukuba sannan ya tsaya suka
dubi
juna
kawai sai zainur ya bushe da dariyar mugunta
lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa yace
duniya rawar 'yan mata na gaba ya koma baya
yakai abbanaka tuna cewa lokacin da hatyan
ya sare mini hannu guda na zama musaki saika
tsaneni
kuma ka kyamaceni yau gashi kaima ka zama
musaki
ka rasa kafarka guda kaga kenan bani da wani
laifi idan na tsaneka
agaban idanunka yanzu zanci karena babu
babbaka
zanyi duk abinda na so baka da ikon hanani
kamar yadda kake yimini abaya
cikin tsananin fushi sarki shamsal ya dakawa
yarima zainur tsawa yace
idan har kaga ka cigaba da mulkin nan to bana
numfashi aduniya
zainur ya sake bushewa da dariya akaro na biyu
sannan yace
to ai yanzu gaka kana numfashi saika hanani na
gani
motsa mana kai ba sadauki bane?
kodajin haka sai sarki shamsal ya yunkura
domin
ya duro kasa
daga kan gadon saiyaga ashe an daure
dukkanin
hannayensa biyu
da wata irin murtukekiyar sarka ta bakin karfe
itama daya kafar tasa lafiyayyar an daureta
ajikin manyan dirkokin dakin aka daura sarkokin
koda ganin haka sai sarki shamsal ya fusata
ainun
ya takarkare ya hada karfinsa waje daya ya fara
janyo
sarkokin yana ruri da kururuwa
wohoho!
mai karfi sai allah ya isa nanfa yarima zainur ya
fara ganin abin al'ajabi
tamkar sihiri domin nantake sarki shamsal ya
fara jijjigo
dirkokin ginin suka fara karyewa ginin dakin ya
fara karyewa ginin dakin ya fara rushewa
adimauce yarima zainur ya ruga waje da gudu
yana mai kwalawa dakarunsa kira
yana fitowa wajen dakin yaga wata masifar
wacce tafi wacce ya baro kuma ba komai yarima
zainur ya ganiba face
barkewar yaki acikin gidan sarautar da farko
ruwan kibiyoyi ya gani
suna zubar da dakarunsa sannan ya jiyo sautin
haduwar takubba
acan kofar fada kuma yaga wasu dakarun
afirgice suna debo makaman yaki
suna rugawa wajen fadar cikin tsananin dimauta
ya tambayi daya daga cikin dakarunsa abinda
ke
faruwa
afirgice badakaren yace dashi ai jarumi hatyan
ne
ya shigo
birnin tareda wasu dakarun bakaken fata suna
daf da isowa nan gidan sarautar
kodajin wannan batu sai yarima zainur ya fusata
ainun
ta zare takubba guda biyu ajikinsa ya nufi kofar
fadar
aikuwa tun daga nesa ya hango hatyan, nasmal,
badi'atul nauwara da boka aimar
sunayin mummunan barna
domin duk inda suka da gaba saidai kaga maza
na zubewa kasa kamar ana sassabe agona
zainur ya dubi gabas da yamma kudu da arewa
yaga ko'ina gawarawakin dakarunsa ne kwance
dukkanin dakarunsa wadanda yake takama dasu
sun zama gawa
nantake hankalinsa ya dugunzuma ya firgita
kawai saiya juya da sauri da nufin ya ruga inda
bargar dakawai take kawai sai jarumi hatyan ya
dako tsalle
daga inda yake tamkar daga cikin baka aka
harbashi
ya dira agaban zainur ya ritsashi da takobinsa
wacce ta rine da jini ya dubeshi yace
''yakai abokin gaba yau babu damar gudu
domin
yau ranace ta daukar fansa
kwatsam sai suka hango sarki shamsal ya
durfafosu
yana dingisa kafarsa guda daya janye da
dirkokin
gini
guda uku ruke da sarkoki
kowa awajen saudi yayi mamakin irin wannan
tsananin karfin damtse
irin na sarki shamsal domin awajen kaf babu
sadaukin da zai iya janyo wadannan dirkokin
masu mugun nauyi haka kuma gashi bashida
kafa
guda
koda ganinsa sai jarumi hatyan ya dubeshi cikin
murmushi yace
yau ga da ga kuma uba sannan ga makiyansu
lokacin daukar fansa yayi kamar yadda nayi
alkawari
na na daukar fansa ran iyayena agaban
idanunka
yanzu zan kashe mahaifinka agaban idanunka
caraf sai sarki shamsal ya busheda
mahaukaciyar dariya
sannan ya hade fuskarsa ya dubi hatyan yace
yakai wannan yaro aiko giwa ta fadi kasa tafi
karfin a dasa mata wawa
idan gaba dayan dakarun dake nan wajen zaku
taru
akaina ni kadai bazakubiya kasheni ba da karfin
damtsenku kona iya yakinku
lallai saina hallaka ku gaba dayanku duk da
cewa
na rasa kafata guda daya sannan na juyo izuwa
kan dana da makarrabansa
wadanda sukaci amanata nayi musu hukunci
daidai da laifinsu
kafin wani awajen yace wani abu sai sarki
shamsal
ya tsinki sarkokin dake hannunsa daga jikin
dirkokin
da karfin tsiya sannan ya suri takubba guda
akasa
ya dako tsalle a sama ya kawowa hatyan
mugayen sara guda biyu
cikin bakin zafin nama hhatyan ya kare saran
da takobinsa da garkuwarsa amma saboda
karfin
saran saida ya fadi kasa
aikuwa yana kasan y dinga kawo masa munanan
sara da suka ya kuntatashi
yana neman hallakshi
k0da ganin abindaya faru sai badi'atul nauwara,
nasmal da aimar suka rugo da gudu suka kawo
masa dauki
sauran dakarun su hatyan kuwa da 'yan tsirarun
dakarun zainur saisuka zuba ido suka zama 'yan
kallo
shima yarima zainur din saiya ruga izuwa bayan
wani ya labe yana kallon abindake faruwa
nantake aka ruguntsume da azababben yaki
tsakanin sarki shamsal da da jarumai hudu
amma sai gashi shikadai ya zame musu alakakai
sun rasa yadda zasuyi dashi
dukda cewa kafa daya ce dashi
amma yana iya juyawa ko'ina ya tare sara da
suka
sama da kasa gefe da gefe kuma ta maida
martani
kuma ya rinka hadaw da naushi da bugu
saigashi kafin dakika ashirin dakkanin jaruman
hudu ya hada musu jini da majina
kawai sai yayi wata katantanwa atsakiyarsu ya
tarwatsasu
kuma ya sami nasarar yankar kowannensu
suka fadi can gefe daya suna masu dafe
raunikan da yayi musu alokacin da jini ke zuba
wohoho dole ne ace da mijin iya baba duk
wanda
yaga irin
wannan gagarumar jarumtaka da sarki shamsal
ya yayi
awannan lokacin dolene yayi masa jinjina
cikin hanzari duksu hudun suka mike tsaye
zumbur suka yunkura zasu sake afkawa sarki
sshamsal
sai jarumi hatyan ya dakatar dasu ya dubesu
yace
wannan fadan ba naku bane ku barni dashi
da izinin ubangiji sai na sami nasara akansa
kodajin wannan batu sai jikinsu badi'atul
nauwara
yayi sanyi suka ja da baya shikuwa hatyan sai
ya
fuskanci sarki shamsal
acikin zuciyarsa yana mai cewa
ya ubangijin musulunci idan harka yarda da
imanin da nayi dakai to ka bani sa'a da nasara
akan wannan tsohon azzalumi
kamar sarki shamsal ya san abin dake cikin
zuciyar hatyan
saiya dubeshi ya bushe da dariyar mugunta
yace
ka daina kamun kafa da wani sabon addini naka
kayi zaton cewa zaka iya samun nasara akaina
zaifi kyau ka farka daga wannan mataccen
mafarki
ni zaki ne uban dawa kuma ni dodon jarumaine
da sadaukai sallamata ma mutuwa ce
hatyan yayi murmushi yace daga yau gudu ya
kare
nayi gudu kamar raina zaifita saboda tsoronka
amma yau ubangijina ya cireni mini tsoronka
kuma zakaga karfinsa
kafin shamsal ya kara cewa komai hatyan ya
ruga
izuwa kansa yana mai kwalla kabbara aikuwa
shima saiya tareshi suka ruguntsume da
azababben yaki
awannan rana su badi'atul nauwara sunga
jarumtaka irin wacce basu taba ganiba
kuma sunga gumurzu wanda ya firgita su ya
dugunzuma hankalin kowa da komai dake birnin
bindal
adalilin masifar yakin mutum saida fiye da rabin
gidan sarautar
ya ruguje gobara ta tashi awurare da dama
saida hatyan da sarki shamsal suka shafe sa'a
biyar
suna bakin gumurzun yaki hatyan ya cigaba da
ambaton ubangiji acikin zuciyarsa
hakanne yasa ya sami gagarumin karfi da
kuzarin
da yaki gajiya
kowa awajen saida yayi matukar mamaki
dakyar
da sidin goshi hatyan ya shammaci sarki
shamsal
ya gabza masa wawan naushi akunnensa n
hagu
take shamsal ya dimauce ya fita hayyacinsa
damar da hatyan ya samu kenan ya soka masa
takobi amakoshinsa
ta faso ta wuyansa ya fadi case matacce
koda yarima zainur ya ga an kashe mahaifinsa
sai ya yunkura ya ruga izuwa wajen gidan
sarautar
amma sai aimar da nasmal suka sha gabansa
suka tareshi nantake aka zuba masa sarka aka
tafi dashi gidan maza
bisa cewar sai kotu ta zauna za'a yanke masa
hukunci
nantake badi'atul nauwara ta sa aka bude wata
katuwar akwatu tasa aka fiddo kan Uwar macizai
koda jama'ar birnin bindal suka yi arba da kan
uwar macizai sai suka rude suka kama sambatu
badi'atul nauwara ta dubesu ta daka musu
tsawa
tace
nice na kashe uwar macizai da karfin ubangijin
musulunci
kuma gashi yanzu agaban idanunku hatyan
ya kashe sarkinku da karfin ubangijin addinin
musulunci
alhalin a nahiyar gaba daya babu mai karfin
damtsensa
shin zaku karbi addinin gaskiya ko kun zabi
mutuwa?
kodajin wannan tambaya sai gaba daya jama'ar
birnin
mazansu da matansu yara da manya suka yi
mubaya'a
suka hada baki sukace munyi imani da ubangijin
musulunci
nantake farinciki ya lullube su badi'atul nauwara
suka kama yiwa allah godiya
bayan komai ya lafa sai jarumi hatyan yace
to yanzu sai ki kaimu inda sarkin mafarauta
yake
amma kafin nan menene matsayina awajenki?
dajin wannan tambaya sai badi'atul nauwara
tayi
murmushi ta kwalawa sarauniya anisa kira
ba zato ba tsammani sai akaga anisa ta fito
daga
cikin wani rusashshen gini ta nufo inda suke
fuskarta cike da murmushi
da isowarta sai badi'atul nauwara tace
a addinin musulunci namiji yana da ikon auren
mata hudu
shin yanzu kin amince ni dake mu zamo matan
jarumi hatyan?
cikin tsananin farinciki da murmushi anisa tace
na amince dari bisa dari
nantake jama'a suka kaure da kabbara
shikuwa aimar saiya daga hannu akayi tsit
sannan ya dubi sadirat yace to ke kumafa?
addinin musulunci bai yadda mace ta auri maza
biyu ba
to tsakanin ni da nasmal wa zaki aura?
sa'adda sadirat taji wannan tambaya sai tayi
murmushi tace
yadda za'ayi ku koma birninku asake yin
wannnan gasar wanda duk yakai dabba kurzal
kasa to shi zan aura
Alhamdullillah
anan mukazo karshen wannan labari na tarkon
mutuwa
ina godiya gareku sakamakon kasancewa tareda
ni ayayin rubuta wannan labari tun daga na
daya
zuwa na tara da kuma baku hakuri akan rashin
posting da wuri
da wadanda suka kasance dani HABIBULLAH
KBR.
SAI KUMA NI SUNUSU SAS
NAKE CE MUKU SAI MUN HADU A WANI LITTAFIN MAI SUNA hikayoyin sadaukai.
WhatsApp 07067470752






An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment