Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

👩🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________





📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com



Sadaukarwa ga
Ama Alhj Kabir
Zeenat Deen (Shazee)
Beauty Queen
Zuwaira Madara
Zeety Mmn Hanan
Mmn Noor
Mom Heebah
Mum Namma
Ina son ku Sisters thanks for the love and support.




*Page 7*




* * * * *
Cikin dauriya da cijewa na mike tsaye lokacin da azababben bakon ciwon kaina ya kara tsananta. Ban ko dubi inda baba yake ba na danna kaina ta cikin bangon ɗakinshi na bayyana nawa ɗakin. Hannuna na dafe da kaina da ke juya min wanda nake ji bisa dukkanin alamu yau nema yake ya faskare ya rabe gida biyu. Na zube kan gadona ina mai ambaton sunan Allah, daga nan kuma ban koma sanin komai na duniya ba. Na dai ji ni kamar ina bacci sai na shiga addu'ar Allah ya tashe ni ya kuma sanya duk abinda na jin nan ya kasance mafarki ne.

Lokaci mai tsayi na shafe a yanayin fitar hayyaci ni ban mutu ba ban kuma suma ba, dan sama-sama nakan ji motsin shigowar iyayena har ma da maganganun da suke a kai na. Wasa-wasa na ci gaba da rayuwa a haka har na tsawon mako guda bana magana da kowa, ba kuma na iya cin komai. Babu abinda ke kai komo a rayuwata sai soyayya, tunanin Muhsin da lalurar sa ne suke kara yi min babakere a kowane lungu da sako na zuciyata. Tunanina ya gagara kawo komai gameda hanyar da zan bi in taimakawa Muhsin, a saboda haka na koma kamar mai cutar mutuwar 6aren jiki, bana iya yiwa kaina komai sai ummy ta yi mini. Iyakacina bin su da ido in na gaji kuma in sufe idon.

Babu abinda yake burge ni dangane da abinci, da kyar ummy na take matse bakina ta zuba min ruwan kwakwa a safe da rana da kuma yamma, a yadda nake ji waɗannan ruwan sune suka taimaka min wajen hanawa 'yan cikina mannewa su bushe saboda rashin cin abinci.

Ranar da na cika sati da kwana biyu a ranar yarima Haiman ya zo shi gidanmu cikin matsanancin tashin hankali da kaɗuwa na jin halin da nake ciki, da kuma irin lokacin da na ɗauka a hakan. Allah sarki so, ni kam na sallamawa soyayya. A ranar yarima ya bani tausayi duk da babu ɗingon son shi a raina, amma na jinjina mishi saboda bawa soyayya muhimmanci.

Lokacin da yayi arba da ni da kuma halin da nake ciki sai ya fashe da kuka, yayi zaman dirshan a gaban gadona kamar yaro ya ci gaba da kuka yana rero mini baitoci na zallar soyayya da bege. A ranar da kyar baba maalam ya lalla6a yarima ya koma gidansu. Washe gari aminiyata Rumana ce ta zo ta ganni itama cikin halin bakin ciki da nuna damuwa da ni. A nan suka wuni ita da yarima Haiman suna famar ɗawainiya da ni. Ana gab da sallar magariba ya fita domin halartar sallar jam'i shi da baba. Ɗakin ya rage daga ni sai kawata Rumana

Wadda itama take shirin tashi tayi tata sallar. Tana mikewa nayi saurin riko hannunta bayan na tattara dukkan karfi da kuzarina, Rumana ta juyo da matukar mamaki tana kallona. Dawowa tayi ta zauna bakin gadon hannunta rike da nawa, tace "sannu Na'eema kina bukatar wani abin ne?" na girgiza kai lokacin da idona suka kawo kwalla buɗar bakina na farko cewa nayi "Rumana Muhsin, nayi kewar masoyina Rumana." shiru tayi tana kallona da yanayina, hatta maganar a wahale nake yinta cikin ɗan lokacin duk na rame na fara fita hayyaci na. Hawayen dake fita daga idona ta fara share min. Tace "ki kwantar da hankalin ki Na'eema Muhsin yana nan lafiya, kar ki karawa kanki damuwa yar'uwa Allah ya baki lafiya." na girgiza kai ina kallon kawata aminiyata Rumana wadda bama 6oyewa juna sirri nida ita. Mahaifin Rumana da babana abokan juna ne wanda zan iya cewa amintakar su ce ta haifar da tamu.

Nace cikin sanyi da raunin murya "Rumana ki taimake ni ki je ki gano min halin da Muhsin yake ciki, ni kam ina jin karshen taka kasa da kafata ne ya zo." Rumana tayi gaggawar kai hannunta ta tsoshe min baki "a'a kawata, kar ki cire rai da rahmar Allah, ai cuta ba mutuwa bace da iznin Allah zaki tashi har ma ki taka kasar." ita kanta cikin dauriya take maganar tana shanye hawayen dake ko'karin zubo mata. Na yi murmushin karfin hali nace "ba zaki gane ba kawata, ni kaɗai nasan yanda nake jin jikina. Gani da rai amma banida damar mikewa ko tankwasa ga66aina, Ruma tunda nake ban ta6a jin ciwo makamancin wanda nake ji yanzu ba. Ke koda Allah ya tashe ni ma na san rayuwata batada wani amfani. Rumana ba zan rayu da Muhsin ba, ba kuma nida hanyar nema masa warakar cutarsa." hawaye masu zafi suka zubo mini yayinda wani kululun bakin ciki ya tokare mini makogwaro. Kuka nake son yi amma ya gagara sai wani tukuki na zafi da nake ji a makoshi na, wanda nake ji kamar in fasa ihu.

Rumana ma kukan ne na tausayi na ya kwace mata kallo na take irin kallon tausayi tace "ki hakuri kawata komai da kike gani a wannan duniyar mukaddari ne daga Allah, Na'eema kina da ilminki kar ki bari sheɗan ya ribace ki. Ki dage da gayawa Allah matsalar ki na tabbata zai ji6anci lamarin ki. A matsayin ki na musulma ki rungumi kaddara a yanda ta zo miki, ki yarda da yarima Haiman matsayin abokin rayuwar ki ki..." duk da cewa ina cikin yanayin ciwo mai kama da mutuwar sassan jiki, amma jin kalmar kawata saida yasa na yi karfin halin motsa jijiyoyina na ɗaga mata hannu alamar dakatarwa "ya isa haka Rumana, na gode da kauna da kike min. Amma ki bar maganar nan haka domin in kika ci gaba da yinta na tabbata cikin biyu zaki kaini ga rasa abu ɗaya. Ko dai in rasa ji na, ko kuma in rasa rayuwar gaba ɗaya. Barni da wanda nake ciki yanzu ma, na roke ki kije ki aiwatar da abinda na nema a gurin ki.

Ki nemo min labarin masoyina ko zan sami sassauci na halin da nake ciki." Kawata bata koma cewa komai ba ta mike. Sai da ta fara gabatar da salla tukunna sannan ta nufi birnin lumui ta kuma sauka a garin gabas. A lokacin yarima Haiman ya dawo daga salla shi da baba, baban ya wuce turakarsa yariman kuma ya iso gurina. Maganganun da naji daga bakinsa su suka tabbabar min da babana ya riga ya gaya masa dalilin kwanciyata a yanzu ya san abinda ya assasamin ciwon da nake yi wanda ban ta6a yin irin shi ba, ban kuma san ranar warakarsa ba.

Bayan shigowar tashi tsayuwa ya fara yi akai na na tsayin lokaci, sannan daga baya ya juya ya nufi gaban madubin dake ɗakin nawa yana karewa kansa da halittar jikinsa kallo, ya juyo ya kalle ni cikin kunci da ɗacin rai yace "yanzu saboda Allah kin min adalci kenan Na'eema?" ban tanka masa ba sai ma binsa da nayi da kallo ya ci gaba da magana "me wancan bil'adaman yake da shi wanda ni bani da shi? Ni ɗin nan fa nine jinsin ki, bayan wannan ina da martabar da za'a so ni dan ita, a halitta ma Allah bai hana ni komai na cikar kamala ba. Amma Na'eema ke duk ba kya ganin waɗannan. Na ɗibi tsayin shekaru ina nuna so da kaunata gareki amma hakan bai ta6a burge ki ba. Na'eema na yarda so ɗaya ne kuma kin bada shi ga jinsin da ba naki ba, na san har abada ba zaki soni ba." ya tsagaita maganar yana matse kwalla a idonsa.

Ni kuwa ido kawai na zuba masa kalamansa na yawo a kwakwalwar kaina ina kuma mamakin raunin zuciya irin na Haiman, shi ba wahala yayi kuka sai kace mace. Ci gaba da maganarsa ne ya katse min tunani

"Na yarda ba kya so na Na'eema, ba kuma zaki so ni ba. Amma ni zan tabbatar da soyayya ta gareki, da dai in kalle ki a haka gwara na rasa rayuwata saboda ke. Na'eema nima na shirya sadaukar da rayuwata gare ki ga soyayyar da nake miki. Gwara na mutu kan tafarkin son ki da na kalli taki mutuwar. Ki sani nan da sati ɗaya zan gama shirina na zuwa tsibirin darul iks domin samo ruwan ma'al dawa'u wa cikar burinki."

Sai naji saukar maganar yarima kamar an shimfiɗa wani hijabi ya lullu6e a kaina, kamar dai wanda yake tsaka da nannauyan bacci kuma yana mafarki...













*Nasmat* ✍
[24/1 20:39] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*MARUBUCI...*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________





📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com




Dedicated to lovely Sis 💋
Layuza Kabir
Rahma Dawaki
Aysherh
Besty Nana
'Yar Auta
'Y@r @mana
U guys means more to me 💋





*page 8*





* * * * *
Maganar babana malam da ya shigo ce ta kara tabbatar min cewa lallai ba mahafarki nake ba. Zumbur na mike daga kwance zuwa zaune ina kara yiwa yarima kallon mamaki da al'ajabin abinda naji ya fito bakin sa.

Nayi nisa ga abinda nake yi na kallon shi da wani irin yanayi wanda na kasa gane kansa.

Cikin tsawa da 6acin rai baba yace "ashe baka da hankali yarima? Ka kuwa san abinda kake furtawa? Maza fice, ka fita nace" ya karashe maganar yana nuna masa hanya da hannunsa wanda har karkarwa yake saboda tsananin tashin hankalin da maganar yarima ta haifar masa.

Yarima bai koma cewa komai ba ya 6ace. Yana aika min wani irin kallo mai nuni da cewa 'abinda na faɗa gaskiya ne' bayan fitarsa baba ma ya fita. Ya rage saura ni kaɗai zaune a kan gado na tamkar wadda aka dasa ta cikin wani yanayi mai wahalar fassarawa, ta ciki da waje kai harma da gangar jikina naji sauyi a cikin kankanin lokacin. Sai dai na kasa gane ainihin halin da nake ciki shin na farin ciki ne ko akasin hakan? Alhamdulillah dama tazo abin ya wuce wasa dan daga zaunen naji na Mike tsaye da wani irin karfi da ban ta6a jin irinsa ba. Kai kamar ma ban ta6a yin ciwo ba.

Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Na rika na nata kalmar a bakina da karfi nayi salati ga Ma'aiki (s.a.w) wanda ni kaina bansan adadinshi ba. Sannan na taka cikin irin takuna mai kama da tafiya akan ruwa luuuuu. Na isa gaban katafaren hoton nan na zanen masoyina Muhsin, sai a lokacin na tabbatar da abinda nake ji farin ciki ne irin wanda zuciya bata ta6a cin Karo da shi ba. Maganganun yarima Haiman suka shiga dawo mini, a lokacin kuma naji kwarin guiwar da ban ta6a jin irinshi ba tun daga ranar da baba ya sanar mini hanyar samun maganin cutar kwakwalwar Muhsin da kuma tsantsan haɗarin dake cikinta.

Na kalli hoton masoyina nace "Muhsin yau kukana ya kare, yau damuwa ta ta zo karshe a ya burina ya ɗauki hanyar cika..." bayyanar kawata Rumana ne ya katse min magana ta. Na mayar da kallona gareta

Wadda itama ni take kallo cikin tsananin mamakin gani na a tsaye. Ni da ta bari kwance cikin halin rayuwa ko mutuwa. Har ta isa gareni mamakin dake fuskarta bai kau ba ta riko hannayena duka biyu tace "Na'eema kece kuwa?" lallausan murmushina na sakar mata tareda jan hannunta zuwa kan ma dai-daitan kujerun dake jere a ɗakin muka zauna. Har yanzu dai idonta a kai na. Ta koma yunkurin yin wata magarar amma sai na dakatar da ita ta hanyar toshe bakinta da tafin hannuna nace "kar kina mamakin ikon Allah Ruma. Zan gaya miki komai a nutse, shin ina labarin masoyina Muhsin?" Rumana ta sauke ajiyar zuciya tareda dafa kafaɗata nan take naga sauyi sosai a fuskarta, ta canja daga yanayin mamaki zuwa na damuwa da kuma alamar tausayi. Wani irin bugu zuciyata tayi da karfi, kar dai wani abin ki ne ya sami Muhsin, "lafiya Ruma me ya sami Muhsin ɗina.?" Ta juyar da fuskarta gefe, wato ta ɗauke ta ga barin kallo na tace "bazan 6oye miki ba 'yar'uwa Muhsin ɗin ki yana cikin wani hali na damuwa, in takaice miki zance dai shima kwance yake yana kar6ar kulawa ta majinyatan bil'adama." "Innalillahi! Wa inna ilaihi raji'un" na faɗa da karfi ina share gumin da ya fara yanke mini tun lokacin da naga sauyin fuskar kawata.

"Muhsin ba lafiya? To wai ma me ya same shi?." "soyayya" kawata ta bani amsa a takaice. Na kara zaro ido wannan karon tsagwaron tsoro da kishi ne suka bayyana karara a idona "soyayya?!" na tambaye ta da karfi ina kara zaro ido "kina so ki ce min Muhsin yana soyayya da wata bil'adama?" Rumana tayi murmushi na ganin sauyi na lokaci ɗaya. Ta kara dafa ni tace "kwantar da hankalinki kawata, ina taya ki murna cewa Muhsin da kike fafutuka a kan sa shima ya damu da ke. Ya kuma kama da matsanancin son ki duk da har yau bai san cewa ke ɗin zahiri bace." na kasa gasgata abinda bakin kawata ke faɗi, tabbas na san mun shaku da Muhsin a mafarki amma taya zan yi tunanin zai kamu da so na ta wannan hanyar?

Na koma kallonta wannan karon cikin sanyin murya nace "taya kika san haka kawata?" ta koma yin murmushi a Karo na biyu sannan ta fara bani labarin data samo mini kamar haka: "Lokacin da na sauka cikin masarautar garin gabas da masoyin naki na fara cin karo kwance magashiyan a ɗakin ummasa, wasu likitoci na musamman mai martaba (mahaifinsa) ya ɗauko dan kula da lafiyarshi. Sun kuwa dage suna ta bincike da yi masa gwaji (aune-aune) amma shi majinyacin sai sambatu yake yana ambaton sunan ki da kika gaya masa a mafarki. Kalaman bakin shi ne suka tabbabar min da cewa ya kamu da son ki kawata, cewa yake, Na'eema kawata ta duniyar mafarki ina kika shiga? Ina ji a jikina wani abin ki ya same ki. Na'eema ina son ganin ki amma ban san ta wacce hanya hakan zata samu ba. Ina kaunar ki kawata Na'eema mene ne yake faruwa da ke da har yayi mana shamakin da kika daina zuwa gareni? Fatana ace lafiyar ki kalau masoyiya ta da zan san hakan da na rage jin raɗaɗi da zogin da nake ji a zuciyata. Tabbas idan na sake kasancewa da ke sai kin gaya mini inda zan rika zuwa in same ki duk lokacin da baki zo gare ni ba domin zuciyata ba zata ɗauki rashin kusanci da ke ba. Me yasa ina kwanciya ina rufe ido, ina tilastawa kaina bacci amma baki zuwa Na'eema ina kika shiga?"

"waɗannan sune kalmomin dake fita daga bakin Muhsin cikin tsananin zafin zazza6in da yake ciki. Amma 6angaren iyayensa kuma sun fara gano gaskiya tunani suke ko dai yaronsu yayi gamo da aljanu ne?

Kawata Na'eema ni kam ina cikin shakku da tsoro anya kuwa soyayyar mutum da aljan zata yuwu?"




🤔 to nima dai Nasmat abinda nake ta tambaya kenan, bari in bar sauri sannu-sannu dai.



Muje zuwa yanzu ne wasar zata fara.

Alhamdullah hakika dukkan godiya ta tabbata ga allah (s.w.a) da ya nuna mana karshen wannan littafin cikin koshin lafiya.
A matsayina na wanda yake tattara littafai na wannan marubuciyar dama sauran marubuta littafan hausa ixuwa document, wato AHMED SARDAUNA nake muku fatan alkhairi sai munhadu a cigaban littafin idan mawallafiyar wannan littafin ta saki cigaban daga naku AHMED B. SARDAUNA
👇👇
08169047840
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
LABARIN ALJANI YA TAKA WUTA
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment