Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata damisa...."

"delu taje asibitin amma yanda taga jikin Farha har kuka tayi ta jima sosai a asibitin sannan ta dawo gida munu tana daki da oganta yajima da zuwa suna can suna sheke ayarsu itada BASSAM hankali kwance tamkar mata da miji"

"Karshe dai ranar anan ya kwana"


"Wannan kenan"


" Yau kimanin watanni hudu kenan da fara jinyar Farha tana cikin kujerah tamkar yarinya ba kafa ba hannu kuma bata iya furta komai saidai ido kashi fitsari duk ajiki takeyi saidai idan anji wari a duba a wanketa mata idan ka gani sai kaji tausayin ta yarinya yar gayu kyakkyawa ta ajin farko amma takoma zaune cikin kujerar guragu=Ø-Þ


"Hajiya salma da Ashrab suna kula da ita sosai yayinda kullun munu ta keta dirka mata ruwan asiri wadan da suke kara sanyata tana komawa tamkar mahaukaciya"

"BASSAM kullun sai yazoh duba Farha wannan kulawar tasa ita takara kusanta shi da zuciyar hajiya salma maganar aurensu yayi nisa dashi a yanzu haka saurah baifi sati biyu ba a daura Auren su"

"Suna zaune adaki itada da Ashrab da Farha Ashrab ta kira sunan ta mummy!! Ta dago tace na'an Ashrab ya akayi tace mum kina ganin ba matsala a auren nan naku da Bassam kuwa"

"Ta daga mata hannu tace ya isa haka Ashrab sau nawa zamuyi magana akan wannan matsalar inason yaron nan ba wata matsala da zan fuska dan na auri muradin zuciyata dan haka bana son nakara jin kin kara wata magana"

"Ahankali Ashrab tace mummy kiyi hakuri ba wani abu nake nufi ba jikina ne yake bani kamar wani abu zai faru" dawa zai faru?"

"Ashrab tayi shiru batare da ta kuma cewa komai ba Farha da take zaune tanaji ba halin magana hawaye suka gangaro mata ke kuma kukan me kikeyiwa mutane hajiya salma ta kalleta idan kashi kikeji muje dan karki batawa mutane daki da wari.......,,

"Ashrab ta share hawayen da suka gangaro mata mum Anyah kuwa kece da bakin ki kike fadar haka ga Farha, Farhan dady ce fah"

"Eh Farha nasani sarai ni yanzu nagama yanke hukuncin zan samo mai kula da ita dan bazan yarda ta hana mun jin dadin aure ba ina fatar kin gane"

"Tamike tabar dakin"

"Ashrab tazoh kusa da yar'uwar tace kiyi hakuri da wannan jarabawar yar'uwata komai yana da lokaci zai wuce insha Allah bana tunanin mum dinmu kalau take zan cigaba da addu'ar Allah yakawo mana dauki acikin rayuwar mu........."







kuyi manage da wannan zaman yana bani wahala yanzu =ØOÞ



BAKWAYIN SHARHI


TAKUCE A KULLUN

LAURAT M BELLO


SHARE
COMMENT...........





=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



BANGARE NAH
(part of me)


=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



STORY&WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO


DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
ALKAWARI
AND NOW
BANGARE NAH
(part of me)


~BISMILLAHIR~RAHMANIR~RAHEEM~
~INA FARAWA DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI~


~MASOYANAH A DUK INDA KUKE WADAN DA NA SANI DA WADAN DA BAN SANI BA NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN GAREKU ALLAH YA BAR KAUNA INAYINKU IRIN 100% DIN NAN~




________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com






..............2þã 7þã é#2þã 8þã ............






__________________"Ameen Ashrab taji ance daga baya ta waiga cikin sauri delu mai aiki ce atsaye tana sharar tata kwallar dan taji komai daya faru"

"Ta karaso gunsu tace kuyi hakuri Allah yana tare da ku hakika ku kanku kunsan hajiya ta canja matuka Amma babu wani abunda zaku iya yi akan lamarin kadarar kuce kuyi hakuri ku cinye wannan jarabawar Allah yana tare daku"

"Ashrab ta goge hawayen fuskarta tace nasani delu tabbas akwai wani bakon Al-amari atare da mahaifiyar mu bakon lamari yashi shigo rayuwar mu wanda bamuda wani wanda zai taimake mu sai Allah"

"Da farko rasuwar mahaifin mu, nabiyu ciyon yar'uwata wanda har zuwa yanzu babu wanda yasan sillarshi, na uku rashin samun kulawar mahaifiyar mu, ki gaya mun delu tayaya zuciyoyin mu zasu daina kunah da radadi? "kowa yasan yanda mum take kaunar mu kowa yasan yanda take kula da damuwar mu Amma yanzu ki duba ki gani aure mum zatayi batada muradi ayanzu irin tayi aure kuma ma abun takaicin da yaron da bai wuce sa'an kaninta bah"..... Ya zanyi da damuwa delu ya zanyi?"=ØÞ......

"Delu zuciyar ta a dagule tace kuyi hakuri hakika kunga canjin yanayi amma bashi zai sa kuki yarda da kaddarah ba"

"Har yanzu kuna da wanda baya gyangyadi barantana bacci Kuma yace ku rokeni na Amsa muku kinga kuwa ko yanzu baku makara ba"

Farha tana zaune tanajin su Amma bazata taba iya yin magana ba bakin a daure takeji amma tana fahintar su

"Hawaye suka zubo mata kanta yana juye yawu na zuba Ashrab ta goge mata hawayen tace kidaina kuka yar'uwata kina da ni har yanzu insha Allahu bazan taba barin kiba....,,

"Kuma Allah yana tare damu"

Delu ta mike bara naje na karasa sauran aikinah, to delu na gode da kulawar ki gare mu

"Murmushin yake tayi tace kada ki damu jinku nakeyi kamar ya'yanah dana haifa"

Tafice daga dakin tanajin tausayin su cikin ranta..... Tana fita daga dakin suka hadu da mun

Wani kallon raini tayi mata tace daga ina kike tun dazu ana jiranki kitchen" na dan wanke bandakin su Ashrab ne yanzu zanje kitchen din.......taja dogon tsaki mtssssss tsohuwar kawai tace tayi shigewar ta delu ta girgiza kanta tace azuciyar ta Allah ya shirya"

Dakin hajiya Salma ta nufa tana kwance a kan sofa tashiga ciki tare dayin sallama tace mum kina hutawa ne

Eh munu ya akayi tace da ita tamike zaune

Lafiya da naso muyi magana akan sauran shirye -shiryen da bamu yiba

"Ok ba damuwa ai inaga kadanne abunda yarage koh Eh sai zancen dinner da kikace ko an fasa da sai naga kawai a fasa kinsan surutun mutane kuma kinga ciyon Farha za'ayita zance awaje"


" Ta hade girar sama data kasa saikace itace hajiyar "

"Amma mum kin ban mamaki yanzu maganar wasu banzayen ce zata hanaki rawar gaban hantsi ni aganina ki daina tunanin wasu can kiyi kawai abunda kike muradi dan idan kika daka ta mutun to ba abunda zakiyi wallahi,...... "Kuma da kike zancen ciyon Farha kema kinsan ciyon Farha ba mai warkewa bane dan Haka kadama ciyon ya dameki kawai kiyi harkar gabanki......"

"Ta nisa kumafah gaskiyar ki danni wallahi ciyon nan nata yafara isata yanzu haka tunanin nake nasamo mata mai kula da ita zaifi saboda na gaji dayiwa katuwar budurwa tsarkin kashi,..... Munu ta shegeke da dariya mai karfi tace kingane kenan"

"Dama kuma wannan ai ke kika soh tun farko naso a kaita gidan kula da musakai kikace a'a zaki iya dama nasan bazaki iya ba wallahi..,,

"Nifa da koni na haifeshi bazan dinga wahala akan shiba"

"Hajiya Salma tace nima ai kinga yanzu abun yana damuna ni yanzu bama wannan ba tunani nake ko na mayarda su itada Ashrab can bangaren baya kinga hankali kwance sai Ayi hidimar bikin nan lafiya qalau basai sun takurawa kowa ba"=Ø-ÞInnahlillahi wa'innah ilaihi raji'un MUNUBIYAH kiji tsoron Allah......,,

Tace kai Amma mum kinyi shawara mai kyau hakan yayi tace bara na tashi naje na gayawa delu tafara gyaran bangaren dan nasan yade a rufe....

Gaskiya ba'a taba zama ciki ba da wasu yan aiki danayi suka zauna amma yanzu ba kowa aciki... Tayi dariyar samun nasarah tace good
Bari na hanzarta,,

Tana fitowa daga dakin ta sheke da dariyar mugunta a fili tace kadan ma kuka gani wallahi sauran tozarci da wulakanci yana gabah=Ø(Þ

Lokacin da na mallake komai na dukiyar gidan nan na kuma kawar da duk wani makiyi nah Alokacin ne zan takarawata son rainah.....,,

Muje zuwa dai da Munubiyah kuke zancen barka kunama kenan

Kai tsaye dakinsu ta nufah bako sallama ta shiga tana shiga ta fara toshe hanci ta yamutsa fuska a wulakance tace warin me nakeji haka kamar an fasa dungen kwai..... Ashrab ta dago wari kuma Aunty aikuwa ba warin komai a dakin nan inaga dai hancin ki ne.....

"Ta yamutsa fuska ba wani hanci nah naji warin ne shi isa na fada yanzu dai ba wannan ba kufara hada kayanku zaku koma dakin baya saboda sha'anin biki kinga bazai yuyuba ace ana tsakiyar biki Farha ta batawa mutane guu da kashi ba gakuma yawun nan dasuke fita kamar fanfoh hajiya tace ku koma baya saboda kada ku takurawa mutane ana cikin sha'ani"

FARHA tana zaune acikin kujera ta runtse idanuwanta hawaye masu zafi suka gangaro mata Ashrab bakinta yana rawa tace mum ce tacedake haka

Ni ce sukaji muryar hajiya salma ta dago cikin mamaki tace mum kece kuwa?" da bakin ki kike cewa mubar cikin gida mukuma baya mum ina soyayyar da uwa takeyiwa danta take ina tausayi da tsantsar tausayinda kike mana yatafi.... Munu hehehehe tsaya malama daga magana zaki fara wasu zantuka tajuyo ta kalli hajiya Salma shige ki tafi barni da su"

"Haka hajiya Salma ta wuce sum-sum-sum batare da gardama ba ta bar dakin ....."

"Tana fita Munu tace Naga Alama har yanzu bakuyi bakinki bai mutuba wallahi Idan bakiyi hankali ba ke ma sai kashinki ya bushe
Dan haka ki kiyaye ba'a yimun gardama...... Tajuya ta bar dakin zuciyar ta a hasale"

"Delu na makale jikin labule ta fito cikin sauri tace Ashrab dan Allah bana son kina mayarwa munubiya da martani idan tayi magana na fuskanci muguwace kuma zata iyayin komai dan haka ki kiyaye bara nayi maza naje na gyarah muku sashen ba komai kuyi hakuri wata rana sai labari ta juya tallalaba ta bar dakin"


Tana fita Ashrab ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ta rungume yar'uwarta tace Ya Allah kazama gatan mu Ya Allah kayimana maganin wannan lamari ya Allah ka gaggauta bimana hakkin mu.........



ZAKU RINGA SAMU KO KADAN NE INSHA ALLAH KUYI MANAGE
PLSS=ØOÞ


TAKUCE A KULLUN
LAURAT M BELLO


SHARE&
COMMENT...........




=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



BANGARE NAH
(part of me)


=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



STORY&WRTITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO



DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
ALKWARI
AND NOW
BANGARE NAH
(part of me)



BISMILLAHIR..... RAHMANIR..... RAHEEM....






________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com




.............2þã 9þã é#3þã 0þã ..............







_____________________"Ameen na furta ahankali yaran suna bani tausayi matuka amma ba abunda zan iyayi kada nima na hadu da makircin munubiya"

Tun a ranar aka kwashe musu kayansu aka mayar dakin baya tamkar marasa gata dakin daya ne kuma karami da karamin bandaki aciki....

BASSAM yana zaune a babban palourn zuciyar shi tana matukar tausayin yaran amma bazai iya yin komai ba a gaskiya yana tausayawa rayuwar yaran kiri-kiri an rabasu da gatan su batare da daliliba haka kawai saboda son rai dakuma son abun duniya....

Munubiya tashigo palour tanta sheka dariya babu wani abunda yake damunta duniyar tana gara mata yanda take so Bassam ya kawarda kansa tamkar bai ganta ba haka kawai haushin ta yakeji

Ta kula da hakan sarai amma ta basar ta karasa gunsa ranka ya dade mijin tsohuwa

Yayi mamakin maganar ta baice komai ba ta zauna dan nesa dashi sannu da zuwa yau'wa yace batare da yakara wani dogon motsi ba... Ta gado wai lafiya naga sai wani shan kanshi kake

Ya kalleta na tsayin lokaci yace munubiya yakamata ki sassautawa iyalan nan haka, inaga abunda kike nema kinsamu ki rabuda zuri'ar gidan nan haka na rokeki da Allah,..... Tuni idanuwan ta suka canja ta dago cikin mamaki tace BASSAM da bakin ka kake tunkarata da irin wadan nan zantuka, sanin kanka bazasuyi tasiri a zuciyata ba dan haka kada ma kabata lokacin ka gurin gaya mun maganar da bazata yi tasiri bah,.... Kuma da kake zancen na samu abunda nake so inaga mantawa kayi har yanzu ban cika buri nah ba hajiya salma tana nan da ranta fah kuma har yanzu su Ashrab basu dan-dana dacin talauci ba har yanzu suna nan da gatan su

"A yanda nakejin zuciyata wallahi bazan taba barinsu ba har sai na tagayyarah su sun wulakanta sun tozarta duk wata gata dasuke tutiya da ita tatafi komai nasu ya dawo mallakina sannan zan samu nutsuwa....... =Ø(Þya dago cikin mamaki yace haba munu meya ragewa yaran nan yanzu komai na gidan nan yadawo hannun ki gatansu ya subuce musu kulawar mahaifiyar su sun daina samu basuda wani abu yanzu illah kunci da bakinci dan Allah ki sassautawa yaran nan wallahi ina yimiki gudun ranarda Allah zai wai-wayeki yayi miki kamun kazar kuku..... "Ta tintsire da dariya wow nayi mamaki da bakin ka kake fadar haka, to kayi a hankali idan baka son kaima ta shafeka dan na kula yanzu zuciyarka ba irin ta maza bace,...... Tamike zantafi Amma kasa azuciyar ka babu wani mahaluki da isa ya dakatar dani ciki kuwa har kai tafice daga palourn. hankalin takwan Ce..,,

"Dafe kansa yayi zuciyar shi tana masa wani iri baya son wannan halin na munu ayimaka rana kai kuma kamayar da sharri ai wannan ba halacci bane yakuma kudirah aransa zai taimaka iya iyawar shi....

"Tana fita dakinta ta wuce ta sabi mayafinta ta bar gidan,.... Tana fita ta tari adai-daita tashiga sunyi tafiya mai nisan gaske sannan tace dashi tsaya ya tsaya tace dashi kada ka tafi ka jirah ni anan. ya dago hajiya ba dai nisa zakiya ba dan sauri nake tajuyo afusace kaga malan ina nema ka fito ka jirah kamar yanda nace zanbiyaka ko nawane kudin ka harma da kari idan kayi hakuri........ Tajuya abunta shikuwa mai adai-daita yanajin maganar kudi ya kara gyarah zaman sa to sai kin fito, tana ta lulawa cikin dajin can na hango wata karamar bukkah a tsakayar dajin ba gida gaba babu a abaya tana isa naji tace gafara dai mugun shaidani wata irin dariya naji ta fito daga cikin bukkatar can naga mutun a zaune gajere sosai kamar ka kifashi da kwano yana washe bakaken hakoranshi yace dama na gaya miki zaki dawo......


Yakara babbaka dariya mai rikitar wa nida nake binta dan na dauko rahoton komai kamar na saki fitsari a wando saboda tsoro Amma ita munu ko a jikinta ta zauna nadawo akwai matsala mugun shaidani *BASSAM* yana son yabani matsala wallahi tun yanzu yana neman ya bujirewa bukata ta.,

Yayi wani ihu wata kwarya ta bayyanah yakira sunan *BASSAM* har sau uku amma wayam babu abunda ya ya fito ya dago yace hajiya saidaifa kiyi hakuri wannan yaron bazai taba saduda ba ki kawo wata bukatar tadago kamar yaya yanda kikaji na fada tace harda *ASHRAB* ma tana neman ta ruguza mun aiki yayi dariya yace ai babu wani wanda ya isa ya ruguza mun aiki wannan ai karamar kwaruwa ce mekike so ayi da ita kasheta za'ayi ko a haukata ta taringa bin bola

"Ko daya so nake a rufe mata baki ta daina cewa uffan, takoma kurma idan ta haukace mutane zasu dago akwai wani abu a kasa to banason kowa yayi tunanin wani abu akayi"

"Sannan sai hajiya inason bayan aurensu tayi sining din dukan kadarar su tabani komai nasu yadawo da sunana sannan daga karshe a kasheta bayan nagama karbar komai na dukiyar ta.....

"Angama sai kuma me kike so shike nan mugun shaidani yayi dariya zakiga shaidanci kuwa yayi wani irin abu saiga hajiya ta bayyanah yace itace wannan ai koh munu ta leka Eh itace yace ki dauka komai yafaru Amma da sharadi"

Ta dago sharadi kuma Eh aikin zai bada wahala domin kuwa har yanzu tanason ya'yanta dan kawai mundanne tane anyimata fin karfi Ranar da duk ta kara Ido biyu da ya'yanta to ina tabbatar miki aikinda akayi akanta ya war-ware zata koma kamar da kuma zata fahinci komai dan haka idan kin Amince yanzu zan cika aiki ana daura auren komai zai dawo hanunki "

"To abatar da yaran mana banason aikinah ya war-ware mugun shaidani,...... "Na gayamiki yaran baza'a batar dasu ba kikawo wata bukatar hankalin munu ya kai kololuwar tashi tace nifa gaskiya inason dukiyar nan bana son asami Matsala......ki kaddarah kin gama samun nasara ai aikinah kamar yankan wuka yake"

" Ya dauko wani kullin ruwa yabata yace kizuba mata a abinci idan dai taci har abada bazata taba tuna tanada wasu ya'yaba a duniya ko zancensu bazata taba tayarwa ba...... ,Ki tabbatar taci domin kuwa idan har bataci ba to asirinki yana gab da tonuwa dan tabbas zata dawo hajiya salman ta da kika sani kuma zata gane kece silar komai"

"Kada kadamu zan kiyaye yakara bata wani maganin yace wannan kibawa yarinyar zakiga abun mamaki tana murmushi ta karba ta ajiye masa makudan kudi ta tafi zuciyarta wasai har tafara jin kamshin kudi atare da ita.....tana zuwa mai adai-daitar yaja suka dawo....

"Tana shiga ta taradda hajiya salma a tsaye tana kallon bangaren da su Ashrab suke, atake gaban munu yafadi cikin sauri tace hajiya lafiya naga kamar kina cikin damuwa? Eh wallahi jina nake kamar can bangaren yana bukatata ta nuna bangaren da su Ashrab suke jiki munu har rawa yake ta ja hannunta muje ciki hajiya kina bukatar hutu,
"Haka ta janyeta suka shiga ciki suna shiga tace muje ki kwanta kinga garin akwai rana ta turata daki tasanya makulli ta rufe kofar=Ø(Þ.......



TAKUCE A KULLUN

LAURAT M BELLO


HABA MY FAN'S KUN DAINAH COMMENT FAH INASON NAGA CANJI



SHARE
VOTE&
COMMENT..........





=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ


BANGARE NAH
(part of me)

=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



STORY&WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO



DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
ALKAWARI
AND NOW
BANGARE NAH
(part of me)




________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

BISMILLAHIR.... RAHMANIR....RAHEEM...





...........3þã 1þã é#3þã 2þã ...........



___________________"Tajuya cikin sauri ta nufi kitchen tun kafin ta karasa tasoma kwallawa delu kirah delu! delu!! delu!!! na'am ta amsa ta fito cikin Sauri..... Kingama abinci ne eh tun dazu to bani na hajiya zan kaimata bata dan jin dadi ne"

"Delu ba abunda ta kawo aranta ta zubowa hajiya salma abincin ta bata tace Allah ya sauwake Ameen tace ta bar gurin cikin sauri....... „

"Saida ta biya ta dakinta ta zuba maganinda boka yabata ta juya sosai ko ina yaji sannan ta gyarah rufin abincin ta dauka ta nufi bangaren hajiya salma dashi......„

"Ta sanya makulli ta bude dakin hajiya tana zaune ta buga tagumi tarasa me yake damunta amma tabbas tasan tanada damuwa tana ganin munu ta shigo tamike yau'wa munu dama ke nake jira wallahi inaji ajikina narasa wani abu atare dani amma kuma ban san ko menene ba,.... "Jikinta har rawa yake muje kici abinci kina bukatar hutu a'a munu bana jin yun'wa yanzu muje kici hajiya inyaso kina gama ci sai muje neman abunda kikejin kin rasa din.....„

Ta janyo plate tayi shiru na tsayin lokaci kamar mai tunani sannan ta fara cin abincin.......

"Munu! tayi murmushin samun nasara aranta tace Alhamdulillah....."saida hajiya salma taci abincin sosai sannan ta ture tace munu bani ruwa nan ma tabata ruwan maganin ta daddaka sosai sai ta mike munu tana murmushi hajiya ina zuwa tace zan dan kwanta ne bacci nake ji......„

"Kin fasa fitar ne? ta dafe kanta bazan iya fitaba kaina nakejin wani iri zan dan kwanta tayi hamma tace kije kawai„...... "Tayi dariya a bayyane tace ba matsala zan tafi kamar yanda kika ce a fito lafiya...... "Ta fice daga dakin tana dariyar mugunta......„

" *BASSAM* kullun cikin tunani yake yaran hajiya salma suna bashi tausayi matuka gashi bayada wani tudun dafawa tabbas yasan halin munubiya zata iya aikata komai akan abunda takeso"

"Yazama wajibi yabi duk abunda zaiyi ahankali batare da ta fahimci komai ba.......,,


Ya tashi jikin sa ba dadi yanufi gidan hajiya salma tun daga kofar gate ya hango Ashrab tayi zaune tayi tagumi abun duniya yayimata yawa hawaye masu zafi suka mata tasanya bayan hanu ta goge ......zuciyar shi a raunane ya karasa gunta tana hangoshi ta mike ahankali ta fara magana kada ka matso kusa dani kaine silar komai babu abunda zaka gaya mun.....,,

"Jikinsa yayi sanyi matuka dama zai iya gayamata komai da yafada mata asalin yanda abun yafaru,.... Amma bazai iyaba saboda gudun faruwar wani abun yayi shiru na tsayin lokaci batare da yace komai ba...... "Sannan yasoma magana kiyi hakuri Ashrab bana nufin cutarwa agareku hasalima inajin tausayinku keda yar'uwarki Farha Amma nasan ayanzu bazaki taba fahimta taba saboda Kina ganin kamar nine silar faruwar komai"

Ta share hawayen da suka gangaro mata cikin rawar murya tace duk wanda yakeda hannu gurin ganin ya cutar damu munbarshi da Allah saboda shine babban sarki baya bacci barantana gyangyadi ta mike ta shige ciki tana sharar kwallah.......

Tausayinta yakara lullube zuciyar BASSAM ya kara jin zuciyar shi takara yi masa rauni haka kawai yana jin tausayin yaran hakan nan ya karasa shiga ciki..... Jikinsa a sanyaye ya karasa cikin gidan.... Hajiya salma tana zaune tana kallon labarai yayi sallama ya shigo tana ganinshi ta mike cikin sauri taje gunshi ta rumgumeshi..... Ya sanya hanun shi ya zagaye ta ya rungumeta sosai yana shafa bayanta...... Ya akayi ne dear...... tana jikinshi tasoma magana ina bukatar ka a kusani ne kawai nayi kewar ka sosai yayi dariya yace to gani nazoh me zan samu ta dago cikin shagwaba...... Ai karigada kasamu komai tunda munkusa zama abu daya

Ya lumshe idanuwansa haka ne muje muzauna nazoh miki da wata muhimmiyar magana...... Munu tana rakube tana ganinsu zuciyarta kamar ta fito waje saboda bakin ciki....... Hajiya salma tana jikinsa suka zauna ahankali ta dago ta kalleshi dear wallahi ina sonka bana son wani ya shiga tsakanin mu na rashin kyautawa dan Allah kayi mun Alkawarin bazaka taba cutar dani ba ayanzu banida kowa saikai kaine kadai bakejij zaka iya taimako na...... Jikinsa asanyaye yace bana nufin cutarwa atare da ke dear ko kadan bantaba tunanin yin hakan ba dan haka kiyi hakuri ki kwantarda hankalin ki na miki alkawarin bazan taba bari wani abu na cutarwa ya kusanceki ba........ Ta kara narkewa ajikinsa ina fatar haka haka kawai nakejin kamar akwai wani abu dayake neman cutar dani........ Hummmm!! Ki daina irin wannan tunanin inaga hasashe ne kawai kike yi dan haka ki kwantar da hankalinki..... Haka suka cigaba da hirar su mai dadi yayinda munubiya take can cikin bakin ciki tanaji tana gani wata kwance jikin BASSAM ba itaba abunda

Please Login or Register in order to submit comment