Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani irin lustful look Hurriya zuba mata idonta masu kaifi da kwarjini tayi da sauri Habiba ta gyara tsayuwarta sannan tace kina bukatar wani Abu a hankali Hurriya tace comb da sauri Habiba ta kawo mata comb kallon dogon gashinta takeyi wanda kwata kwata bai kama dana yan Nigeria shiryawa tayi cikin wani brown palazzo sai red riga gashinta sakwa sakwa ta daureshi Habiba na kallonta kamar zata cinye ta so take ta taba gashin taji idan nata ne Amman tsoro ya hanata takalminta ta sanya ta fita batasan inda wurin yake ba saida ta tambayi wani ya nuna mata hanyar da zata bi duk inda ta wuce kallonta akeyi tanaji a jikinta kuma tasan ana kallonta saidai ta saba ko a garinsu haka akeyi mata irin wannan kallon tafiyar ma taki karewa saboda nisan tafiyar wurin.



Uban bayi ya kirga su Amman ba mutum daya acikin mata kuma ance masu su talatin ne mamaki sosai ya kamashi don haka ya nufi inda twins suke Allah ya taimaki shawata Allah ya kara maki nasara Babu mutum Daya a cikin mata kuma su talatin ne liya da mamaki take kallonshi don ba’a taba samun irin haka ba kallon neela tayi saidai hankalin Neela kwata kwata bai tare da ita yana wani saiti daban don haka ba tare da bata lokaci ba ta kalli saitin da Neela take kallo inda Hurriya take tafiya kamar she own half of the world yadda tafiyarta take cike da izza liya da mamaki take kallon Hurriya kowa a wurin hankalin shi ya koma kanta fuskar ta fayau babu komai amman wani irin tsantsan kyau da annuri ne take fiddawa gashin kanta wanda bata daure ba duk ya zubo mata kowa bude baki yayi yana kallonta da mamaki don karime kasa shiru tayi tace uwale kamar Hurriya nike gani daga mata kai uwale tayi tace itace fa karime sanya hannunta tayi a baki tana cizon yatsa


Hurriya ba inda ta tsaya sai a saitin Bintu banda faduwar gaba ba abinda bintu keji .


Neela kallonta takeyi da wani irin mamakin gaske don tundaga kayan jikinta take kallo sannan tunda ga sama har kasa gashin kanta kam ko subira albarka bare ita daure fuska tayi ta murtuketa kamar Allah ya aikota ta taho kuyangin nabin bayanta cikin jiji da kai da isa da sarauta Neela ke tafiya har tazo inda Hurriya take tsaye kallon Hurriya tayi tundaga saman ta har kasanta gabanta ne ya shiga faduwa don tunda take bata taba ganin Epitome of beauty irinta ba the girl is almost perfect with nothing left for people to criticize not almost perfect ma she’s more than perfect kallon cramel skin dinta wanda yake glowing irin na wanda sukaji hutu. hutun ma anihin hutu ba muna hutu ba tayi wannan yarinya Anya ba cikinsu akaso ayita ba aka samu kuskure shine abinda tace kawai a ranta kallon cikakken gashinta takeyi wanda yake da yawa wanda daureshi sakwa sakwa amman dan ziri biyu na gaban gashinta sun dan sauko irin shigar da tayi bata da bambamci da irin tasu shigar Don bambamcin kayan
nasu are damn expensive while her own is cheap cikin zuciyarta tace she’s beautiful she adjusted her self trying her very best to look normal kara matsowa tayi inda Hurriya take tayi ke tace cikin tsadaddiyar muryarta shiru wurin ya dauka kusan kowa ya juyo wurin domin bama idonshi abinci liya itama kallon ikon Allah takeyi daga inda take tsaye


Neela magana ta karayi ma Hurriya cike da tsantsar mulki kuma da sarauta Hurriya dagowa tayi ta zuba ma Neela idanun ta masu matukar kyau da kwarjini

Subahanallah kawai Neela tace don side view dinta ta gani bataga complète face dinta ba sai yanzu da ta dago tabb she wishes to be her friend because the girl is fucking beautiful saidai matsalar they are not in the same classes she’s far better than her kilan idan har tace tayi friendship da ita it will be a great insult to her a cikin masarautar kamar ta Neela baiwa ta zama friend dinta kai not in this life maybe in the next life


Hurriya itama kallon ta take tana analyzing dinta don taki janye idonta daga cikin na Neela itama Neela hakan take a wurinta a cikin masu aikin da kuyangi da bayi ba wanda ya taba bata irin wannan kallon da Hurriya take bata saboda kwarjinin ta and she’s ahead of them they’re far different so they have to always stared at the flour whenever she’s around them nobody will dared to stared at her but this is a different story because Hurriya is not looking away or bowing her head kutt she’s giving her more like a deadful glared cikin isa da mulki tace Who are you Hurriya ta ta dan cije lebenta wanda kamar daman sararta ce Bintu ta rinka kallonta da pleading eyes dinta tana rokonta ta ido kada ta jawo ma kanta matsala ta taimaka

Cikin muryarta mai zaki da dadin gaske da accent dinta na Ethiopia tace Hurriya Faisait Hamood she wasn’t expecting her answer to be like irin amsar da tabata she was surprised because tasan ma aikatan su basu wani jin turanci maybe kilan tayi ayyuka gidajen masu kudi shiyasa ta tsinci irin kalmomin turanci irin haka harda kayan dake jikinta kila ma kwance ne

Cikin jiji dakai tace waye ya baki izinin wannan shigar da kikayi da gadara Neela ke maganar Liya na daga gefe tana kallon ikon Allah Hurriya shiru tayi tana kallon Kyakyawar fuskar Neela wadda batada bambamci data liya saboda tsantsar kamarsu

Neela ta fara hasala Sosai don taga yarinyar tana Neman raina ma mutane wayau kuyangarta tace ta kira mata shaho aiko da sauri aka kirashi jikinshi na bari yazo yana durkusawa kallonshi tayi ta nuna mashi Hurriya aiko a take ya gane abinda take nufi wanda daman kamar jira yake



Cikin tsantsar mugunta ya zuba mata bulala daya wadda saura kadan ta saki fitsari liya ce tazo da sauri tayi stopping dinshi tace kada ya kara dukanta wurin shiru ya dauka Neela na kallon Liya


Hurriya kam kallo daya idan kayi mata zakasan bulalar ta shigeta saidai kwata babu alamun nadama sai wasu flames ma dake fitowa daga cikin idonta Hurriya ta bama liya tausayi sosai sadai batasan tayi Abu makamancin da zai iya zamowa disgi ga yar uwarta don haka ta janye Neela suka koma inda suke kuyangin su na rufa masu baya.


Rarraba masu aiki aka farayi Har akazo kan Bintu ita Bintu ba komai aka bata ba sai mai aikin sashen Neela bayan angama da Bintu uban bayi ya karkato kan Hurriya girgiza kai yayi kadan sannan ya fara lissafo mata aiyukan da zatayi masu matukar wahala sashe biyu zatayi aiki sai kuma aikin bayi wanda wanda bayi ke irin wannan aikin saboda tsananin wahalar aikin to hadashi aka bata har aka gama lissafo mata aikin batace kala ba aikin ne masu azabar wahala aka jero mata don ko yadda uban bayin ke karanta mata ayyukan kadai ya isa kasan da gayya aka bata aikin



Bayan angama raba ma kowa aiki saida suka jira liya da Neela suka bar wurin sannan suka tafi


Uniform aka basu kusan kowa da kalar nashi uniform din don kusan kowa da matsayin shi itadai Hurriya Green and Red aka bata komawa tayi ta shirya cikin uniform din sannan ta linke kayanta ta maidasu a leda baya taje inda akeyin lodin wankin princes da princess da yaran masarautar mata da mazane a wurin banda tikar wanki ba abinda sukeyi sunayi ana zubo masu wasu kayan sai kara tila masu kayan ake ga alama ba wani Hutu daman tattare dasu Uwar bayi ta kalli Hurriya tace gashinan ki jona shiru Hurriya tayi Uwar bayi da take tsaye tana jiran amsa daga gareta jin shirun da yayi yawa ne ya sanya ta juyowa saidai mi wayam babu Hurriya babu alamunta


Hurriya har ta isa inda akeyin wankin in a polite way tayi masu magana tare da tambayarsu abinda zatayi ba bata lokaci aka nuna mata wasu kallon tsantsar hallitar kyau da gashinta sukeyi don kowa a wurin ma ba kallon musulma yake mata ba andwho cares tunda basu take bauta mawa ba kuma mutane are good in making judgement sai suyi tayi

Wanki takeyi tukuru don tanayin wanki don ta saba tunda ita takeyi ma kanta ma wanki she’s not lazy because life had taught her alot ko a garinsu duk aikin da tasan yana bada kudi to tanayinshi in order for her to make a living don haka ba wata matsala bace sosai a wurin ta don haka ta cigaba da wanki baji ba gani


Tafiya takeyi wadda kallo daya zakayi mata kasan cewar ta gaji don yanayin tafiyar ta ne zai tabbatar maka don tunda suka fara wankin babu wata magana wato a huta don kamar jakkai haka sukayita yin sukola sai yanzu dasuka gama


Cigaba tayi da tafiyar saidai dakin kamar an kara mashi nisa don taki kawo dakin har yanzu saida ta kara doguwar tafiya mai tsawo sannan ta iso dakin

Bata wani bata lokaci ba ta dauko kayanta da ta bari a wurin habiba ta nufi sabon dakin da aka nuna mata dazu a matsayin nasu


Dakin babba ne saidai bai kai wancan girma ba don wannan zai iya cin mutum ashirin saitin katifar ta ajiye kayanta duk da tanajin kiran sallah magrib da akeyi bai hanata kwanciya ba wani dogon Bacci ya dauketa Mai cike da gajiya tanaji cikin bacci uwar bayi tana mata magana akan zuwa dayan shashen da take aiki domin hada ma hakimi abinci tsoki tayi ta juya ta cigaba da baccin ta bata tashi ba sai karfe taran dare



Hurriya hamma tayi tana kara gyara dogon gashinta wanda yadan sauko mata tsoki tayi don ba abinda take bukata irin wanka da ruwan zafi a yanzu saidai batasan inda zata samu ruwan zafi don haka ta fito ko ina tarr kamar ba dare ba tayi alwalar ta cikin dakin ta shigo sannan ta sanya doguwar hijab tayi sallah


Bayan tagama rama sallolinta ta duba cikin kayanta ta zaro riga wadda batada hayaniya yar karama wadda ko cinyoyinta bata rufe ba ta sanya


Kwanciya tayi taja hijab dinta ta rufe jikinta yunwa takeji amman bazata iyacin tuwo ba a takure take sosai don tariga ta saba da abinda takeso shi takeci tanason freedom rayuwarta amman kwata kwata tasan dole zatayi hakuri da wasu abubuwan.



Manya matane su uku sai Hansa’u da barira sune cikon biyu haka suka shigo dakin su biyar suna shakiyanci suna dariya barira ce leader ga dukkan alamu yau zamusha dadi inji Hansa’u akwai sabbin zuwa ga dukkan alamu Barira ta kallesu tace saina fara zaba kafin ku zaba gaskiya Hansa’u tace angama shugaba tana dariya suwaiba ce tace ni kinsan nafison hidimar jakunna kafin dayan abun

biyun ne sukayi dariya sukace muma sai mun fara shan dadi kafin muyi rabon jakkuna dariya suka kyalkyace da ita suka zauna inda ya zamar masu kamar chamber su a dakin Hansa’u ce ta bude leda ta fiddo rake mai zaki tanasha murmushi tayi tace kai kai wannan rake akwai zaki Allah yasa yanmatan dakinan suyi zakin wannan raken dariya suka kwashe da ita


Wasila ce tace kinga nayi nan don haka duk inda taga jakunna indai na sabbin zuwa ne saida tadaukosu

Hansa’u da suwaiba sai Aliya suka tashi sukazo inda su karime suke kwance da saraunsu suna tarkato yanmatan da suke wasu kwance wasu zaune

Dukansu saida suka zaba suka darje acikin yanmatan sannan sukazo tsakiyar dakin

Hansa’u da bata iya jira don haka ta fara zame kaya ba kunya ba tsoron Allah taja mardiyya dariya suka fara suna shewa mardiya kam abinda Hansa’u ta farayi mata bata taba jin irin shi ba don haka ta fasa wani irin kuka manya manya matan da suke tsaye suka gaura mata mari mai shiga jiki ba wadda bata gauwara mata mari acikinsu suna dariya


Banda salâti ba abinda mardiya keyi Don Hansa’u ta fara janye mata suturar ta

Barira wadda take shugaba acikin su ta taso tazo wurin tana kallon yan matan uwale tayi ma alama da tazo uwale banda kyarma ba abinda takeyi nan ta fara ja da baya wata irin muguwar faduwa kasa tayi wadda suwaiba ta sanya kafa ta shureta ta fadi kasa tana dafe goshi kuka uwale takeyi mai taba zuciya tana dafe goshin ta Barira tsoki tayi dallah sakara taso kema ai dadi zakiji bamu kadai zamuj dadin ba kuma da kun saba zakuzo kuna nema dakanku kinzo kina ma mutane kuka


Wasila tayi wata shegiyar dariya sannan tazo ta take ma uwale hannu tace shegiya daga gani ma zaki yi jaraba ta kara halba ta tana tsirta mata miyau Barira tace ku shigo man da ita


Suwaiba da wasila suka kamata suka kaita har makwanci Barira don ita har wani labule gareta wanda baka iya kallon komai dake cikin wurin

Uwale sam taki bamaBarira hadin kai don cizo da tsunkuli ba wanda batayi mata da kyar Barira ta barka mata riga wani irin cizo uwale ta kaimata a cinya mai dan banza zafi aiko barira ta hankadeta uwale kam ta rugo a guje tana hawaye Barira sanya kayanta tayi ta fito itama tana bata fuska alamar taci wuya


Kallonta su Mardiya da suwaiba da wasila sukayi sukace lafiya kallon uwale da take sharbar kuka tayi tace gatanan ta kusa illata ni don haka kuyi maganinta

Dariya sukayi a tare ita kuma ta samu wuri ta zauna

Dukan uwale suka farayi wanda kamar daman abinda ya kawosu duniyar kenan don basu ji basu gani hada halbinta sukeyi cike da mugunta suna wata yar iskar dariya ita kuma uwale kuka takeyi mai ban tausayi da taba zuciya

Mutane na kallo Amman waye ya isa yace zaiyi magana don daurin gindi suka samu wurin manya ma’aikatan masarautar don sai suyi maka dukan tsiya kuma su kira mararsa imanin samarinsu suma su dasa

Su Karime kam kyarma kawai sukeyi suna kallon ikon Allah wasu kam acikin su ma kuka sukeyi



Hurriya baccin gajiya takeyi saida bata da nauyin bacci tun dazu takejin kuka da hayaniya saidai bata maida hankali ba ta koma baccin ta amman hayaniyar da kukan damunta sukeyi don duk sai juye juye takeyi cikin baccin tsoki tayi ta janye hijab din dake jikinta ta tashi takalminta kawai ta sanya ta fito ba inda ta tsaya sai wurin su wasila da su suwaiba wanda banda bugun uwale ba abinda sukeyi

Hannunta duka biyun a bayanta sai gashinta da yayi loosing tie saboda bata daureshi da kyau ba

Kamar hadin baki dukansu suka dago suna kallonta itama kallonsu takeyi wanda da alama idanunta basu gaji da bacci ba

Kallon uwale Hurriya tayi wadda take durkushe tana kuka wasila ce ta kara kai mata mari sannan ta dago tana kallon Hurriya tace ke kuma fa babu wanda tace ma kala

Hurriya Dukansu kallon yadda suke binta da kallo takeyi kamar wasu hungry lions

Barira ce ta taho tana karairaya sannan ta kalli Hurriya a izgilance tace wa kike nema tanabin long slender legs dinta wanda rigar ta ko cinya bata gama rufe mata ba ,her legs shine like a sparkling water don wani salki sukeyi na tsantsar kyau hutu da jin dadi da duk suka bayyyana

Cikin isa da kuma rainin wayau Hurriya tace Are you lesbians sai kuma tayi licking gefen bakinta taciji lebenta tace kuna neman mata ne ?kowa acikin zuciyar shi ba wanda baya muradin ta saboda basu taba ganin lafiyaryar mace mai kyau dinta ba don ko gimbiya subira albarka


Barira ce ta taho cike da iyayi da kaudi tace kina son ki tabbatar ne ?sannan ta daga kai tace ma Hurriya Eh muna neman mata sannan ta lashe bakinta tace bari kingani matsowa tayi inda Hurriya take tsaye wadda kyakyawar fuskarta take blank she looks fierce and scary don da Barira tayi gigin kallon idonta da ta shiga taitayinta


Hurriya kallon Barira takeyi wadda har tazo kusa da ita da alama kuma tabata take so tayi don har ta dora hannunta saman gashinta tana lumshe ido bude idonta tayi tar akan na Hurriya sai a lokacin taga yanayin fuskarta mai firgitawa sharewa tayi tana kokarin kai hannunta a cinyar Hurriya saidai saukar zazzafan tuwo da miyar da taji a fuskar tane ya sanya ta sakin ihun azaba don ta tabbata fuskarta ta kone wani irin kuka takeyi mai ban tausayi da taba zuciya

Kowa kallon Hurriya da ta konata da tuwo a fuskarta yakeyi babu alamun ko tsoro ko nadama a fuskar Hurriya don da alama inda akwai saura to kilan Sai ta watsa mata a ko ina na jikin Barira

Wasila ce ta taso da wani irin zafin nama da alama zata kaima Hurriya mari da sauri Hurriya ta kauce sannan ta kalleta ido cikin ido tace i dare you to slap me with your filthy hand licking lips dinta tayi sannan tace da ni Hurriya faisait Hamood na sanya an yaken yatsunki guda biyar


And duk randa kika kwatanta yin haka I promise this ta nuna mata alamun sai an yanke hannun sannan ta kallesu wanda banda kallonta ba abinda sukeyi don ko daga idonka zai tabbatar maka da duk abinda tace zatayi zata iya



Bintu hannunta rike da bakinta don mamakin yadda Hurriya ta kona Barira da tuwon da ta kawo mata yanzu saboda tasan duk yau bataci komai ba kuma ko a jikinta don yadda take acting kamar ba abinda tayi don ta san Hurriya zata iya yin fin haka indai maganar wani zai taba mata jikine

daman Bintu tunanin Hurriyar bataci abinci ba don haka tace bari ta kawo mata tuwon tare da fatan Allah ya sanya taci sai ga abinda ya faru da tuwon da Kuma Barira


Hurriya zuwa tayi ta kwanta ta mike kafafunta ta lumshe idanunta Bintu tarugo tazo tace Hurriya shiru Hurriya tayi Bintu ta kiranta yafi a kirga Amman shiru karshe ma saidai ganin bacci ya dauke tayi don alamar numfashin ta ya canza ya koma na mai bacci

🌚Masarautar Qamar

By Khadija (KMU)

Page 17&18

Karfe 6:10 goma Hurriya ta tashi
saboda ayyukan da take dasu yau murza idanunta tayi sannan tayi mika ba addu'a abakinta ba komai bata dauki komai ba don haka taje babban toilet dinsu ta kama ruwa sannan tazo tayi Alwala Tayi sallah wanka takeso tayi saboda tsamin jikin da takeji duk batajin dadi saboda Rashin cikakken wanka data sabayi don ta saba kafin tazo masarautar nan sai tayi wanka sau uku a rana kuma da ruwan zafi don batasan ruwan sanyi indai wurin wanka ne saboda ciwonta tsoki taja ba tare da ta cire hijab din sallahrba ta nufi babban kitchen


Aiki akeyi a kitchen din sosai shigowa tayi wata yar babbar mace ta gani a gaban tukunya ruwan sai tafasa yake Daidai saitin matar Hurriya ta tsaya saida tagama kallonta don kamar bazatayi magana ba cikin miskilanci tace ruwa zafi zaki bani


Dagowa inna hanne tayi don ganin isassar don batayi mata sallama ba sannan bata gaisheta ba sai ruwa zaki bani cikin tsiwa ta dago domin tsiyaya rashin mutunci saidai ganin kudin da Hurriya take mika mata datayi ya sanya tayi shiru ta fara washe baki tana toh toh miye zakiyi da ruwa yar albarka kamar don dole tace wanka amshe dari biyun inna hanne tayi tace samo bukiti in zuba maki kinji Hurriya juyawa tayi ba bata lokaci sai gata da bucket nan inna hanne ta fara zuba mata ruwan zafi masu yawan gaske har saida Hurriya tace ya isa sannan ta daina zuba ruwan



Toilet ta shiga tayi lafiyayyen wankan ta wanda tasan zataji dadin jikinta Sosai a hankali ta shafa bayanta inda zanen tatoo ke kwance a bayanta wurin saitin wuyanta lumshe idonta tayi ta cizi lebenta masu kyaun gaske sannan ta fito tana tafiya ne a hankali kuma duk da safiya ce sosai tanajin yadda ake nunata


Tana zuwa ta iske Bintu a zaune kamar bacci ma takeyi Don haka Hurriya ta shirya tsaff cikin uniform dinta wanda ta samu ta wanke jiya da kyar wadanda sukayi mata wani irin kyau na musamman fuskarta sai fidda annuri takeyi sanyi da takeji na safiya wanda yake shiga kanta ya sanya ta bude kayanta domin neman Hula Aiko ba tare data sha wahala ba sai gashi ta samu hula mai kyau ash colour hular irin ta sanyi ce duk a wurin asabe ta siye su


Bata fuska tayi don tana dadewa bata daura ma gashinta wani Abu ba don sai idan abun ya kadota sosai .shine take rufe gashinta don a shekara baifi ta rufe gashinta ba sau hudu akwai lokacin da har shekarar ta kare bata damu da rufe gashinta ba idan ba wurin sallah ba


Cikin kyankyami take rike da hular da sam bata wanke ta ba don duk kayan gwanjon duk hasken su sai ta sanya hannunta ta wanke su tas kafin ta sanya.



Warware gashinta tayi wanda ya zubo mata har bayanta sosai don ma akai akai take rage gashin kanta da batasan yadda zai rinka takura mata ba kuma data rage nan da nan yake fitowa har yafi wanda ta rage din tsawo da cika da yawa


Taba gashin tayi sannan ta dan shinshina ko yana wari kamshin coconut oil din da taji ya sanya ta dan saki ajiyar zuciya

Daure gashinta tayi Sosai yadda duk bala'inka baka iya hango tukar don ta linketa ta sanya ta cikin gashin yadda ba mai iya gane yawan gashin ko tsawonshi ko yawanshi


Bintu da ta bude idonta masu kyau ta kalli Hurriya tace kindawo daga mata kai Hurriya tayi tanabin ko ina na jikinta da kallo alamar rama kuma da yar damuwa tattare da ita

Ganin Hurriya nabin ta da kallon minene matsalar ki ya sanya ta washe baki yan hakoranta suka fito tace Hurriya jiya nazo in ganki na kawo maki abinci Amman Saita kasa ida maganar alamar kamar tana kuka ta hade kafafunta da gwiwarta Hurriya ta duko tace Bintu miye ya faru waye ya taba ki fadamin shi. Daga muryar ta zakaji alamar kulawa duk da yadda take kokarin boye emotions a cikin maganarta ,duk wani mai tsantsar fahimta zai iya fahimtar damuwa a maganar ta Amman a yadda take maganar kadai sai mutum yace bata damu ba


Hurriya kara matsowa tayi kusa da Bintu kamar tanajin tsoronta tana tambayar wai lafiyar ki kuwa ki fadamani manah itama maganar ta kubce mata da alamun shagwaba Wata irin kyakyawar runguma Bintu tayi mata sannan ta fashe da matsinacin kuka Hurriya dan ture ta tayi ta zame jikinta Bintu dagowa tayi ta kalleta da idanun ta da sukayi jajir ta kalli Hurriya da take bata fuska kamar kashi ya tabata kuka ta kara fashewa dashi Hurriya dafe kanta tayi tace ki daina kuka ki fadamin abinda ya faru shiru Bintu tayi kamar daman abinda ta jira ta fada mata kenan don haka tayi shiru kafin a hankali tace cikin muryarta mai rauni tace nayi kewar ummanah Hurriya inajin tsoro tana maganar hawaye na zubo mata shiru tayi sannan ta goge hawayenta tana kallon Hurriya data tsura mata ido tashi tayi zata mike Hurriya tace Bintu yadda ta fadi sunanta saida ya sanya tsigar jikin Bintu ta tashi don da wata irin kulawa ta fadi sunan Bintu kallonta takeyi da mamaki tace Hurriya tana zare ido  dan murmushi Hurriya tayi kadan wanda duka dimples dinta saida suka lotsa sakin baki Bintu tayi tana kallonta don tunda take a duniya bata taba ganin wanda murmushi yayi ma kyau ba irin Hurriya itakanta har goosebumps saida taji itada take ma mace kenan inaga ta fito tana murmushi bama dariya ba murmushi kawai tabb akwai matsala don ta tabatta duk inda ta matsa mazane zasu rinka binta kamar sleeves Dogs inaga tayi dariya ita kanta Bintu tunda take bata taba ganin mace mai kyaun Hurriya babu ta inda Allah ya rageta a fuskarta ko jikinta

Gyaran murya Tayi ta kalli Hurriya da kamar tana cikin good mood a hankali Hurriya cikin muryar ta mai dadi da sanyi

2 Comments On MASARAUTAR QAMAR
avatar
aysher

1 year ago

Reply

I really like this novel wlh

avatar
maryam-5-7-5

1 year ago

Reply

Pls inna bukatar

Please Login or Register in order to submit comment