Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

👑 KWALLIYA 👑

(Hanyoyin da za ki bi ki gyara jikin ki)

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌


Daga Fadila Sani Bakori
08063830828

RAMADAN GIFT

Assalamu alaikum.Barkanmu da shigowa wannan wata mai albarka watan Ramadana. Allah Ubangiji ya karb'i ibadun mu amin.
Auntyna Bashaushe ya ce in ki na da kyau ki k'ara da wanka .Amarya,Uwargida har da ma 'yanmata, wannan garab'asa ce gare ku, wadda za ku gyara jikinku da kud'i k'alilan, ba tare da kin kashe kud'i masu yawa ba wajan siyan man bleaching ,wanda amfani da shi had'ari ne ,dan zai iya b'ata miki fatar jiki ko ya sa miki Pimples ,ko sunburn, da dai dauransu.
Auntyna wannan hanya ce da za ki gyara kanki da kanki ta hanyar amfani da kayanmu na gida,wato kayan gargajiya.

Wato ita dai ranar sallah rana ce wadda Uwargida take k'ure take son kure wankanta wajan yin adon da zata birge mai gida da sauran k'awayanta da zata ziyarta.Hakan ne ya sa na ka kawo muku wannan garab'asa.

Auntyna ki sani duk adon da za ki idan ya kasance fatar jikinki na da matsala irin ta black sport, ko Pimples ,sunburn da sauran su suna tauye mi ki kyan ado.

Idan ki na so ki ga fatar ki ta yi fresh ,ki ga tana glowing, ya zama dole sai kin kiyaye wa'innan abubuwa guda Bakwai (7) da zan lissafo.

Yawan Aitaka wad'annan abubuwan guda Bakwai (7) na sanya fata saurin tsufa da Yamutsewa.

Kowane mai rai dole ne wata rana ya tsufa. Amma akwai abin da in aka yi wa fata zai sanya ta tsufa da wuri. Kuma dole ne mu yi iya kokarin barinsu. Abubuwa da suka hada da  rashin bacci da yawan gajiya da amfani da kayan kwalliyar da ba ta dace da fata ba. Yawan shan taba da kuma yawan cin naman shanu bayan an bai wa shekara arba’in baya.
1)- Gajiya: Yawan gajiya da shiga damuwa na matukar sanya fatar jiki tsufa. Idan mutum ya shiga damuwa, fatar na fitar da wani abu ‘cortisol’. Wannan ‘cortis’ din yana yi wa fata dameji. Sai a ga mutum ya tsufa da wuri. Shi ya sa sai a ga wanda yake cikin damuwa da talauci yana riga sa’anninsa tsufa da ke birni,  kuma cikin jin dadi. Don haka sai a yi iya kokarin rage sanya kai tunani da damuwa.

2)- Kayan kwalliya: Akwai wasu kayan kwalliya da ke dauke da sinadarai kamar su;  zinc odide da dimethicone da propylene suna iya sanya fata tsufa, musamman idan an yawaita amfani da su. Wasu sinadaren suna bata fuska kaikayi daga nan sai fesowar kuraje har fuska.


3)-Taba: Yawan shan taba na sanya tsufar fata da wuri domin wannan sinadarin da ke cikin sigari nicotine, wanda ke toshe magudanar jini. Shan tabar na sanya fata ta sake karfinta. A rage shan taba saboda tana janyo tsufar fata.

4)- Yawan cin soyayyen abinci da cin abinci a kan kari ba don yunwa ba na sanya fatar jiki kiba, kuma hakan zai janyo fatar fuska cika, sai a ga mutum tsabagen kiba ya fi shekarunsa.

5)- Yana da kyau mutum ya san irin nau’in fatarsa kafin ya yi amfani da kowane irin sabulu. Idan sabulu bai dace da fatar mutum ba, zai iya sanya tsufan fata.

6)- A rage cin abinci mai dauke da mai, musamman idan shekaru sun ja. Bai kamata idan an kai shekaru arba’in a rika cin naman shanu ba. Yawan cin irin wadannan  abubuwa yana janyo ciwon kafa da sanya mutum tsufa.

7)- Yana da kyau a rika samun barci a kalla awa bakwai a kullum. Rashin samun barci a kan kari na sanya tsufa da wuri.

Fadila Sani Bakori ce.


👑 KWALLIYA 👑

(Hanyoyin da za ki bi ki gyara jikinki)

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌


Daga Fadila Sani Bakori
08063830828

RAMADAN GIFT

Assalamu aliakum, barkan mu da warhaka,Ya ibada .Allah ya karb'i ibadunmu ameen.

Auntyna ki gwada wannan had'in ki gani kafin Sallah za ki ga yadda fatar jikinki za ta yi fresh tana glowing ,ta na d'auke ido kamar wata Zinariya.


Shin ko kinsan sirrin da ke d'auke da Kurkum .Gwada bin Hanyoyin nan ki sha mamaki 👇🏻

Yana da kyau a kullum bayan kin yi amfani da hanyoyin da za mu kawo mi ki ki kasan ce mai yawan wanke fuskarki, kafin ki kwanta barci, ya kasance babu maik'o a jikinta.Hakan na taimakawa sosai wajan k'ara fito da kyawun fuska.


Ki samu kurkum sai ki daka, daga nan sai ki hada da dakakkiyar alkama, sannan ki hada da man zaitun. 

Daga nan sai ki shafa a fuskarki ko a jikinki. Bayan awa biyu ko uku sai ki wanke fuskarki ko jikinki da ruwa mai dumi.

Hakan yana cire kwayoyin cutar da ke makale a kofofin fata. 

Yadda za ki yi amfani da Kurkum Wajen Gyara Fatarki Kurkum na dauke da sinadarai da dama kamar su, bitamin B6 da bitamin C da sauransu. Kuma yana rike fata yadda ba za a sami rauni ba . 

Yawan amfani da hadin kurkum na sanya fata musamman ta fuska laushi da santsi da kuma haske. Don haka, ya kamata kada a manta da amfani da kurkum idan an zo kwalliya.hakan zai kara haska fuskarki.


Amfani da kurkum na sanya sabuwar fata fitowa da wuri a inda tsohuwar ta fita 

- A sami garin kurkum da zuma cokali daya da ruwan lemon tsami kwatan kofi. A kwaba su sosai har sai sun yi laushi. 


Sannan a shafa a fatar fuska a bari ya jima na mintuna 15 sannan a wanke da ruwan dumi. Yin wannan hadin na hana kurajen fuska fesowa. 

Za a iya yin wannan hadin kamar sau daya ko biyu a sati domin samin ingantaccen sakamako. 

- Amfani da kurkum na rage gautsin fuska. A kwaba kurkum da nono ko kindirmo. Sannan a wanke fuska kafin a shafa hadin a fuska. A jira na tsawon mintuna 10-15 kafin a wanke. Za a iya jarraba wannan hadin a kullum bayan an yi wanka. 

- Idan ke mai yawan aiki a karkashin rana ce, ya kamata ki samu kurkum kadan da kindirmo mai yawa sai ki rika shafa wa a inda kunan rana ta bata fuska. kunan rana na sanya fuska ta zama kamar mai shafe-shafe don haka wannan hadin zai magance wadannan matsalolin.


 - Ko kun san cewa kurkum na magance bakar fatar karkashin hammata? To! A sami zuma kamar cokali daya sai a hada da ruwan lemon tsami kamar cokula 3-4 sai a zuba garin kurkum kadan sannan a kwaba a shafa a karkashin hammata a bari ya jima na tsawon mintuna 10-15 kamin a wanke ki sha mamaki Auntyna.

Kurkum,na taimakawa sosai wajan magance matsaloli irinsu, Pimples,Sunburn, Black sport da sauransu.


Fadila Sani Bakori ce

👑 KWALLIYA 👑

(Hanyoyin da za ki bi ki gyara jikinki)



🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌


Daga Fadila Sani Bakori
08063830828


RAMADAN GIFT



ABUBUWAN DAKE KAWO KURAJEN FUSKA DA YADDA ZA A MAGANCE SU.


Kurajen fuska suna taka mihimmiyar rawa wajan dishashewar kwaliyar uwargida,hakan ya sa yau na zo muku da hanyoyin masu sauki da za ku bi dan magance su.


Kurajen fuska na pimples matsala ce da ta'addabi matasa Mata da Maza musamman masu kananan shekaru wadan da suka fara balaga saboda samun canji daga sinadaran hormones. 

Duk da kurajen fuska suna Kama Mata da maza, Amma Mata sunfi damuwa saboda za kaga har nikab suke sanyawa a fuskokin su saboda kar aga ta’adin da kurajen su ka yi musu a fuska.

Kurajen pimples ba a fuska kadai suke fita ba suna fita a wadannan wuraren:

- Kirji 

- gadon baya

- Cinya

- wuya 

Abubuwan da suke taimakawa wajen tunzura kurajen fuska:
-  Yawan cin Abu Mai maiko.

- Amfani da mayukan da Basu dace da fatar jiki ba

- Kwayoyin cuta

- Shiga rana sosai

-  Shan wasu magunguna

Abin da ya kamata ayi domin kariyar yawaitar kurajen fuska da samun waraka sune:

1- A rage amfani da abinci masu maiko dayawa.

2- Idan kuraje suka fito kada a yawaita tabawa.


3- Idan za ki yi doguwar waya kada ki daura wayar a fuskar ki ko kusa da kurajen.


4- A samu ruwan dumi a matsa lemon tsami a wanke fuska da shi a kalla so biyu a rana.


5- Idan kurajen a kirji ko baya ka da ayi amfani da matsattsen kaya saboda samun iska.


6- Za'a iya shafa zuma bayan dan mintuna a wanke da ruwan dumi.

7- Za'a iya amfani da Damatol Wanda ake kitso da shi,ya na kashe pimples sosai Auntyna.

 Idan wadannan hanyoyin ba su yi amfani ba a tuntubi ma'aikacin lafiya domin akwai magunguna da dama masu kashe kurajen pimples.

Fadila Sani Bakori ce 🤝



👑 KWALLIYA 👑

(Hanyoyin da za ki bi ki gyara jikinki)


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌


Daga Fadila Sani Bakori
08063830828

RAMADAN GIFT


YADDA ZA A MAGANCE GISHIRIN FUSKA DA MAIKONTA.


Hanyoyin da za abi don magance Gishirin fuska da maikonta.


Auntyna ki sani duk adon da za ki in dai ya kasance kina da Gishirin fuska ko maikonta, yakan tauye adon ki sosai.Dan yana hana biyuwar powder a fuskarki.Sannan yana taimakawa sosai wajan fito da pimples da sunburn.Hakan ya sa yau na kawo muku hanyoyin da za ku bi dan rabuwa da Gishirin fuska da maikonta.


Gishirin fuska dai ana kiransa da suna white heads a Turance. Abubuwan da ke kawo shi su ne, yawan gumi a fuska ko maikon fuska. Idan mu ka yi gumi, fuskarmu takan fitar da maiko. Idan ba mu damu mun wanke fuskarmu a lokacin da ta yi gumi ba to hakan yakan taru ne sai ya zama gishirin fuska.


 Yakan faro a kan fuska. Idan muka yi kokarin cire gishirin fuskar da hannu, hakan kan janyo kurajen fuska. Saboda haka na kawo mana hanyoyi da dama da za mu bi don rabuwa da gishirin fuska.


A rika wanke fuska akalla sau biyu a rana da ruwan dumi da sabulu. Yin haka na rage fesowar gishirin fuska. Kuma yakan hana kuraje fitowa,ya kuma kara miki kyawun fuska Auntyna.


A zuba tafasasshen ruwa a kwano ko roba. Sannan mu rufe kanmu da tawul sai mu sanya kanmu a saman ruwan zafin domin fuskar ta tiriru na tsawon minti 10. Yin haka na narkar da maikon fuskar (gishirin fuska).


A samu baking soda. Za mu iya samunta a shagon da ake sayar da kayan kek sai mu kwaba a ruwa sannan sai mu shafa a fuskarmu. Bayan haka, sai mu jira ya bushe. Idan ya bushe, sai mu wanke da ruwan dumi.


Idan kuma ba za mu iya tirara fuskar ba, za mu iya sanya tawul dinmu a ruwan zafi, sannan mu matse kafin mu kai fuskarmu.

Shan ruwa kamar kofi 8 ko 10 a rana na wanke maikon fuska kuma yana hana fitowar gishirin fuska.



Lemun tsami na busar da maikon fuska. Za mu iya shafa ruwan lemun tsami da auduga sannan sai mu guge fuskarmu da shi.

Zuma na taimakawa wajen rage gishirin fuska da kurajen fuska. Mu shafa zuma a fuskarmu. Sai mu bar ta na tsawon minti 10. Sannan mu wanke da ruwan dumi.



Auntyna aguji kwantawa barci da maiko a fuska,haka kuma bayan tashi daga barci shi ma a rika daurewa ana wanke fuska da sabun da kike amfani da shi.


Idan muna son rabuwa da irin wadannan kurajen fuska da gishirin fuska, amfani da hadin gargajiya irin namu na saurin warkar da cututtukan fata. Za mu iya amfani da daya daga cikin wadan da na lissafo don magance gishirin fuska.

Fadila Sani Bakori ce


👑KWALLIYA 👑

(Hanyoyin da za ki bi ki gyara jikinki)

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌


Daga Fadila Sani Bakori
08063830828

RAMADAN GIFT

HANYOYIN DA ZA KI BI KI SARRAFA LELLE DA RUWAN SHI DON GYARAN JIKINKI

SHIN KO KINSAN SIRRIN DA KE D'AUKE DA LALLE DA RUWAN SA.


GWADA BIN HANYOYIN NAN KI SHA MAMAKI 👇🏻

Jama’a da dama sun san cewa lalle abin ado ne ga mace. Bayan haka ruwan lallen ma na da matukar amfani ga fata. Ana shuka lalle ne a wuraren da ke  da zafi. Yanayin zafin wuri ke nuna kyan launin lalle. Don haka a yau na kawo muku yadda za a yi amfani da lalle a fata.



Domin samun sulbin fuska, a jika lalle na tsawon awa biyu sannan a kwaba shi da ruwansa sai a diga man zaitun da kwaiduwar kwai sannan a shafa a fuska na tsawon minti talatin sannan a wanke da ruwa. Ana son shafa irin wannan hadi kamar sau daya a mako.


A jika lalle da ruwa sannan a zuba man zaitun da man kwakwa a rika wanke gashin kai da shi domin hana gashi tsinkewa da kuma sanya gashi laushi,


Domin magance amosanin kai; a kwaba lalle da ruwan lemun tsami kadan sannan a shafa a fatar kai a bar shi na tsawon minti goma zuwa sha biyar kafin a wanke da sabulun wanke gashi.


Ruwan lalle shi ne babban abin da ke taya lalle kamawa a fatar hannu. Ana gane lalle mai kyau ne ta ganin irin launin ruwan da ke jikin lalle.


Shi kansa lalle abin ado ne ga mata idan aka sanya shi a tafin kafa ko a hannu.


Ana wanka da ruwan lalle bayan ya tsumu domin kara launi ga amaryar, uwar gida har da ma yan mata. Za a iya jika ruwan da lalle mai dan dama ya tsumu bayan amaryar gobe ta gama wanka za ta iya watsa wannan ruwan a wankan karshe domin sanya fata laushi da launi mai kyau.


Fadila Sani Bakori ce.


👑 KWALLIYA👑

(Hanyoyin da za ki bi ki gyara jikinki)


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌


Daga Fadila Sani Bakori
08063830828

RAMADAN GIFT


HANYOYIN DA ZA KI SARRAFA LEMUN TSAMI WAJEN GYARAN FUSKA.

 


Hanyoyin da Za ki bi wajen sarrafa Lemon tsami wajen gyaran Fuska.
Lemon tsami na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwan da jama’a suke amfani da shi wajen yin abubuwa da dama.



 Lemon tsami na da matukar muhimmanci ga dan Adam musamman ma wajen gyaran fuska, saboda haka, na kawo muku yadda za ki yi amfani da shi domin gyaran fatar fuska. 




A gaba za zan kawo miki hanyoyin da za ki yi amfani da lemon tsami wajen gyara fatar fuska, sai dai ina so ki fahimci za ki iya amfani da hanya daya ce kawai daga cikin hanyoyin da za mu kawo miki, amma za ki iya amfani da sauran hanyoyin idan hanyar da kika dauka ta farko ba ta biya miki bukata ba.





- Lemon tsami da zuma; Ki debi rabin cokalin ruwan lemon tsami da kuma rabin cokalin zuma sai a kwaba su, daga nan ki shafa a fuskarki na tsawon minti 15, sannan ki wanke da ruwan sanyi. Idan kina da fata mai gautsi to za ki iya hadawa da man zaitun.




- Lemon tsami da nono;  Za ki hada rabin cokalin ruwan lemon tsami da rabin cokalin nono (amma an fi son kindirmo)sai ki kwaba sosai. Bayan haka, sai ki shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin ki wanke. A wannan hadin ba sai kin hada da wani mai ba, saboda nono na dauke da sinadarin mai.


- Timatir da lemon tsami da alkama; Ki matse ruwan timatir da na lemon tsami a wuri guda, sannan ki hada da nikakkiyar alkama, daga nan ki kwaba kafin ki shafa a fuska . Wannan hadin na taimaka wa masu yawan gumin fuska sosai. A shafa a fuska na tsawon minti 15 kafin a wanke.


Fadila Sani Bakori ce


👑 KWALLIYA 👑

(Hanyoyin da za ki bi ki gyara jikinki)


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌


Daga Fadila Sani Bakori
08063830828

RAMADAN GIFT


YADDA ZA KU SARRAFA WASU 'YA'YAN ITATUWA GUDA HUDE (4) DOMIN GYARAN JIKI DA FUSKA.


A yau na kawo muku yadda ake amfani da wasu 'ya'yan itatuwa hudu domin gyaran jikinku.Lemu,Kankana, Mangwaro da kuma Abarba,domin inganta fata da kuma haskaka ta.


Mata da dama na zuwa shaguna su kashe kudi mai yawa domin neman inganta fatarsu amma abin ba ya aiki. Don haka a yau na kawo muku hanyoyi masu sauki da za a bi domin ingantawa da haskaka fatar jiki.



1-  Lemu; Ya na dauke da sinadarin bitamin C don haka yana kare fuska daga fesowar kuraje da kuma haskakata. A samu lemun zaki mai ruwa sai a matse ruwan. Bayan haka, sai a fasa kwai a dauki doruwan cikinta a zuba a cikin ruwan lemun.
Sannan a dauko cokali a auna zuma cokali karami sai a zuba. Sannan a kwaba su sosai. Bayan haka, sai a shafa a fuska na tsawon minti 15 zuwa 20, sannan a wanke. Wannan hadin na haskaka fata sosai.


2 - Kankana; Ta na dauke da sinadaran gyara fata kuma tana hana ramukan gumi budewa domin idan ramukan gumi na nan a bude, datti zai shiga wanda zai haifar da fesowar kuraje. 


A samu kankana zalla a markada ta sannan a shafa a fuska na tsawon minti 15 zuwa 20. Bayan haka, sai a wanke da ruwan sanyi. Yawan yin hakan na haskaka fata sosai kuma na rage fesowar kuraje a fuska.


3 - Abarba;  Na dauke da sinadaran da ke gyaran fata sosai. A markada abarba sannan a diga man zaitun. Sannan a shafa a fatar jiki. Bayan haka, sai a shafa a fatar jiki na tsawon minti 15 zuwa 20. Irin wannan hadin na warkar da kurajen fuska kuma da sanya fuska haske da sulbi da kuma kyalli.


4 - Magwaro; A bare mangwaro da wuka sannan a cire bawon da kwallon. Sannan sai a markada da zuma sai a kwaba su sosai. Daga nan sai a shafa a gashin kai a bari ya jima na tsawon awa daya. Sannan a wanke kan da man ‘shampoo.’ Wannan irin hadin na karfafa gashi kuma yana sanya shi tsayi da kuma laushi.


Fadila Sani Bakori ce 🤝


👑 KWALLIYA 👑

(Hanyoyin da za ki bi ki gyara jikinki)


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Daga Fadila Sani Bakori
08063830828

RAMADAN GIFT


HANYOYIN GYARAN JIKIN MATA GUDA GOMA. YADDA ZA KI GYARA JIKINKI.

Ire-iren gyaran jiki na mata har kala goma,yadda za a gyara jiki ya yi kyau ba tare da cutar da fata ba.

Mafi yawan mata na son gyara jikinsu dan birge maigida ko kuma masoyan su, sai dai kuma akan samu akasi wajen yin amfani da abubuwan Turawa wanda suke da matsololi daban-daban sabanin yin amfani da abubuwan da ake da su na amfanin yau da kullum. 


Gyara ko tsafta abu ne mai matukar mahimmanci kuma abu ne me kyau muddin ba za a kauce wa addini ba. Hausawa na cewa “in kana da kyau ka kara da wanka” wannan dalilin ya sa yau na kawo muku hanyoyi kala daban-daban duba da wasu abubuwan karuwa game da gyaran fata har ma da wasu abubuwan dan karuwar jama’a.

Tsarabar da nake tafe da ita yau ta hada da abubuwa kamar haka:

Macen da take son fatarta ta goge ta yi kyau za ta yi amfani da:

- Lemon Tsami 

- Bawon kwai 

- Kur-kur 

A hade su waje guda a daka su a runka wanka da shi, fata zata yi kyau yadda ake bukata.

Baya ga haka akwai hadi na musamman wanda in mace ta yi shi duk tsufanta za ta koma yarinya shakaf.

- Ayaba 

- Sabulun Salo 

- Man Auduga 

- Dudu Osun 

- Dettol 

- Leman Tsami 

Shi ma za a hada su waje guda a runka wanka da shi fata tana tsantsi da laushi.

Bayan haka akwai wani hadin na gyaran fata inda za a samu:

- Ganyen Magarya 

- Man zaitun 

- Man Habbatus sauda 


A daka ganyen magaryar a zuba a cikin man zaitun da man habbatus sauda a runka wanka da shi.

Hadi na musamman da yake sa fatar mace ta zamo tana tare da sheki, da laushi, har ma aji jikinta yana wani damshi-damshi sai a samu:


- Ayaba 

- Lemon Tsami 

- Tatacciyar Madara 

- Kwai guda daya.

A sami ayaba mai kyau a bare ko a matse da hannu, ko a markada yayi laushi, sai a zuba tacacciyar madarar a fasa kwai kamar guda daya, amma farin za’a zuba, sai a matse lemon tsami a gauraya shi a shafa a jiki ya samu kamar tsayin awa daya, sai ayi wanka da ruwan zafi. Idan ana yi kamar kwana uku za a sha mamaki In sha Allah


Gyaran fata na ban mamaki ki samu:

- Man zaitun 

- Ridi 


A daka ridi, amma sai an gyara shi, an shanya ya bushe sai a daka a zuba cikin man zaitun,

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment