Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

HALIN RAYUWA



4


HAFSAT G. SODANGI

Mr. Yunus Abdullahi Dabai

1

Hakkin Mallaka (m) Sodangi
Copyright O Sodangi

GODIYA
Godiyata har kullum ga Allah take, Masanin yau da
gobe, mai kowa mai komai, Gwani mai hikima wanda
yayi halitta tasa duka bibiyu, ya kuma halicci mutum da
Aljan don su bautata mishi,
Tsira da Aminci su tabbata ga cikamakin Anabawa
shugaban Manzanni, Annabin Karshe Muhammad
(SAW) da Alayensa da Sahabbansa da wadinda suka bi
ma tafarkinsa na gaskiya har zauwa ranar Altiyama,
amin.
Godiya mai yawa gare ku makaramta litattafaina, m
kusa da na nesa, Ubangiji ya saka da alheri ys kuma Rara karfafa zumuncin da ke tsakani, na gode.

SADAUKARWA
Sadaukarwar littafin ta lyayena ce, Ahaji Chindo
Muhammad Sodangi da Hajiya Fevime Musa Sodangi,
Ubangiji ya saka muku da alheri ya kums fara muku
lafiya amin.

TUKUICI
Tukuicin littafin naki ne:
KHADIJA CHINDO SODANGI (Mrs Nasiru ldris)
2

JINJINA
Jinjinar littafin taki ce Amarya ba kya laifi (Manc
Umar) Zuhuriyya lbrahim (Mrs LAwal Chindo Sodangi),
Ubangiji ya raya Umar da imani.

FATAN ALHERI GARE KU
Fatima Abdulkadir Kazaure
Hafsat Iliyasu Unguwar Rimi
Khadija Usman Nasarawa
Nafisatu Ibrahim Muhammad
Fatima Ahmad Shehu Kaduna
Maryam Muhammad Gusau, Zamfara
Umaima Abubakar Umar
Maijidda Uba Magaji
Na gode, Ubangiji ya saka da alheri, amin.

KUNA RAINA
Hajiya Maryam (Mami) Dan Hassarn
Hajiya Jamila Ibrahim Na Bature
Hajiya A 'isha Balarabe (Jazan)
Ubangiji ya bar zumunci amin.

3

LITTATTAFAN SODANGI:
1. Uwar miji
2. Naga ta kaina
3. Rabon kwado..
16. Wacece ni?
17.Wata fuskar..
18. Mijin ta ce
19. Garin banza...
20. Ga ni gare ka
21.Biyan Bukatar rai
22. Shamaki
23. Hattara
4. Cikar alkawari
5. Wayyo duniya
6. Yi wa wani..
7. Abu naka...
8. Mata ma su duniya
9, Nufin Allah
10. Kifin na ganinka...
11. Daga kin gaskiya...
12. Da kamar wuya...
13. Mai uwa...
14. Duk daya...
15. Mata da kicin dinsu
24. Kyautata
25. Ayi dai mu gani...
26. Tabbataccen al'amari
27. In kunne ya ji..
28. Halin Rayuwa
29. Mai Daki...

Littattafan ba sa nufin yi da wani ko habaici ga
kowa, sai dai an rubuta su ne don fadakarwa da
nishadantarwa, ana neman afirwa ga duk wanda yaga
wani abu yayi kamar abinda ya shafe shi, ba da shi ake
ba dace ne kawai.
4

HALIN RAYUWA4
A wannan lokacin ba zai yiwu in iya kwatanta halin
da nake ciki, ba na tsoro, abu guda daya dai da
zuciyata ta kasa yarda da shi, shi ne a in bar Rauhani
ya yi min abin da yake son yi min, da in har shi ya yi
min hakan sai na gwammace ma kawai gara duk abin
da zai faru da ni ya faru koda kuwa wani abu ne da ya
fi hauka muni.
Tsayarwa kaina wannan hukunci da zuciyata ta yi,
sai ya zama dalilin da na samu kuzarin takarkarcwa na
kurmawa Rauhani ihu da iyakacin karfina.
A bar ni bana son aikin, a bar ni kawai na ce a bar
ni. Abinda nake ta fadi kenan.
Iskar da ke kadawa a dakin ta tsaya nan take kuma
haske ya bayyana a dakin, sai ga Mallan a zaune a
wurin zamanshi, hularshi zaune daram a ken shi, nimaa
nayi maza na mike na zauna muka fuslkanci juna ni da
shi.
Maryam kin 6ata aikinki,kin yi duk abinda aka ce
miki kar kiyi, kin yi musu, kin yi gardama, kin yi
jayayya har da kokawa. Ya tafí yana fushi yanzu ya ya
kenan?
Ban iya buda bakina nayi magana ba, balle in iya
amsa mishi tambayar tashi, saboda har lokacin ina
cikin tsananin tsoro, jikina ma bai daina 6arin da yake
yi ba. Ban sani ba ko ya gane hakanne yasa shi kawo
shawarar cewa ya sake kiran Rauhanin ya ba shi
5

hakuri, ya yi aikin da ya zo yin don kar haukan da ya
yi alkawari ya same ni.
Nayi maza na ce mishi "Aa, a bar ni kawai." "A
bar ki hauka ta same ki? nayi shiru ban amsa ba, "Kin
gwammace kiyi hauka ko?" Na sake yin shiru, "To shi
kenan tunda abinda ki ka zaba kenan, dulk abinda ya
faru da ke dai ba za a sake kawo mana ke nan mu
karbe ki ba, tunda kina cikin bijirarrun mutane masu
taurin kai.
Sakamakon taurin kai kuma nadama ne. Ina kuma
yi miki albishir da hauka kafin fitarki cikin wannan
dajin." Yana fadin hakan naji an daka min wata irin
tsawa, wanda saboda tsananin tsoro na kasa fahimtar
daga in da tsawar ta fito Tashi ki ba mu wuri."
Abinda naji an fadi kenan da karfi.
Ina jin hakan nayi maza nayi waje, yankawa kawai
nayi da gudu ba tare da na tsaya neman takalmina ko
tunanin ta ina na fito ina kuma ya kamata in dosa?
Gudu kawai nake yi a cikin jejin nan, bana ko
waiwaye ban kuma san inda na dosa ba.
Gaba daya fatana da addu'ata bai wuce in isa
gaban mahaifina kafin haukar ta same ni ba. Ina gudun
ina kokarin jaddadawa kaina har yanzu dai da
hankalina, hauka bata fara samuna ba tukuna, tunda
duk abinda nake gani ina ganewa, ina kuma iya tuna
komai nawa sai in yi maza in ci gaba da karanta
addu'ar da damna nake ta karantawa Hasbunallahu
wani' imal wakil."
6

Ina cikin haka na hango wani mutum a gabanta,
tsoro ya kara kama ni, ina tunanin ko Mallam ne ya
turo shi ya zo ya mayar mishi da ni,
Nayi kamar in juya da baya saboda tsananin
tsoratar da nayi, sai kuma naga to ai in shi dinne ma
zan iya juyawar ya sake tare ni a inda na koma din,
don haka na dake zuciyata na ci gaba da taiyata har
naje kusa da shi zan wuce naga ashe manomi ne yake
aii a gonarshi, sai dai ban iya buda baki na tambaye
shi hanya ba, saboda kar ya gane ni din bakuwar jejin
ce.
Nayi tafiya rannan har na raina kaina, amma
zuciyata bata gaji ba, ko tsayawa in huta bana yi,
kokarina kawai in fita bakin hanya ne in ga gari in ga
ta inda na bulla don na riga nasan na kauce banya.
Ina cikin haka na sake hango wani mutum da sauri
na nufi wurinsli daga nesa kadan na tsaya na gaishe
shi nayi mishi tambaya kan hanyar da zan bi in shiga
gari
Barin abinda yake yi ya yi ya taya yana lallona,
ke kuwa ya ya aka yi ki ka kawo yanzu cikin dajin
nan? Ban iya ce mishi komai ba, don haka ya gaji ya
ce min Kina kusa da gari sai dai akwai tabkeken rafi a
tsakaninki da shi, in kin iya ruwa ze ki iya bin nan ki
fada raf ki tsallaka, in kuwa kin san ba ki iya ruwan
sosai ba, sai ki bi nari don rafin yana da zurfi, in an yi
ruwa ya kawo ba karamin ta'adi yake yi ba.
7

Na ce, Na gode. Har na fara tafiya ta nan din da ya
ce, sai naji ya daga murya ya ce min kiyi ta tafiya har
sai kin ga yar gada sai ki hauta ki tsallaka za ki ga
kauye a nan za ki samü abin hawa zuwa cikin gari."
Na sake cewa "To na gode.
Wannan hanyar da ya nuna min din ita nabi nayi.ta
tafiya har na kai inda ya ce zan ga gada, gadar ta
langa-langa ne, wanda mutancn wurin suka hadu suka
yi don su rinka samu suna tsallakawa zuwa inda
gonakinsu suke in ban da gudun ceton rai nake yi babu
abinda zai sa in iya hawanta.
Na isa kauyen, a lokacin da duhun dare ya riga ya
sauka ya mamaye ko ina, ga shi babu haske ko kadan,
don kuwa babu. wutar lantarki a kauyen, babu kuma
hasken farin wata saboda watan ya kusa karewa.
A haka na wuce kauyen nan nayi tafiya har inda na
samu wani mai mashin da ya yarda ya fidda i bakin
hanya a dalilin tsananin gajiyar da ya gani a tare da ni.
A kofar gida na samu Babana a tsugune yana tashe
da fitilar kwai, daga ganin ikuma nasan ya yi
wahala ya neme ni har ya gaji.
Ina isa gabanshi na fadi a kasa ina kuka tare da
fadin "Ka yafe min Baba." Ban wani tsaya bata lokaci
ba nayi maza na attaba mishi bayanin komai, tunda
nayi saa nazo gabanshi da hankalina, shi yasa nayi
maza na gaya mishi don ya sani saboda kar haukar ta
Same ni yayi tunanin zai yi ta wahalar neman min
magani tunda ba hauka ce da zata warke ba, ka
8

taimake ni Baba ka tsare ni wuri daya kar ka bar ni in
yi ta yawo a tube irin yanda nake ganin yan uwan
mahaukata suna barinsu suna yi."
"Ke Yahcuwuna. Ya kira sunan nawa cikin wani
irin yanayi na damuwa, "Ki daina yin haka bari fadin
irin wannan maganar, ya ya ki ke yi wa kanki
mummunan fata irin wannan? Nayi maza na ce,
"Baba mai Rauhani ne ya gaya min ai har kokawa da
Rauhanin ma nayi.
Ya mika hannu ya kama nawa "Zo mu shiga gidan,
na godewa Ubangiji da ya dawo min da ke lafiya."
Baba Lantana ta galla mishi harara ta ce, "Uhun, ai kai
kam ka shiga uku, yarinya ta tafi taje ta gama barikinta
ta dawo tana dingishin ta samu wadanda suka fi
karfinta, amma kana bari kana fadin wai ka gode
Ubangiji saboda ta maida kai sakarai."
Isyaku ya yi sallama daga tsakar gida ya tsaya yayi
tambaya, "Baba wai Anti Meron ta dawo?" Da sauri
Babana ya ce, "Eh, ta dawo." Ba tare da ya tsaya
tambayar in ji waye ba, ta sake fadin "Ka ji wani irin
rainin hankali ma Malam, sai ka ce ba tare suke ba, sai
ka ce ba shi ya kawota ya ajiye ya wuce gidanshi.."
tayi maza tayi kasake ta bar maganganun da take yi ta
koma sauraron bayanin da Baba yake yi min.
Ai ba za ki yi hauka ba, ai karya yayi miki ba
Rauhani ba ne, shi mutumin ne da kanshi yayi miki
wannan abin don ya samu ya tsoratar da ke, ki yarda
yayi lalata da ke. Ba mutumin kirki ba ne, Boka ne. Ko

9
Malamin tsubbu. Ba da Rauhani ki ka yi kokawa ba,
bai yi nasara ba ne a kanki saboda ke din mutuniyár
kirki ce, uwarki ma haka, Ramatu mutuniyar kirki ce
sannan bata da tsoro.
Baba Lantana taja mummunan tsaki "Wannan
Ramatu ai bata kyauia ba da bata jaka ku ka tafi tare
ba.". Tuni sai ta bar maganar da take yi ta ni da
Mubarak muka fita yawo, ta koma ta Rauhani da
hauka don tafi yi mata dadi.
"Hauka kam ai sai kin yi tunda Rauhani ya ce sai
kin yi, to shi yana karya ne ma da za'ka ce mata ba za
ta yi ba? Ba dai har nan dama Dijan take kai ba? Ai
kuwa dai kun tsokano tsuliyar Dodo."
Sallau yayi sallama ya shigo tare da fadin "Baba
ashe ta davo?" Ai ta dawo Sallau ya sake fita ya sayo
min shayi da biredi in banda yayi wannan dabarar
watakila da haka na kwana ni da Babana ba muyi
wannan tunanin ba, balle Baba Lantana.
Kwana muka yi Babana yana rike da allon
Karfenshi yana rubutu yana wankewa yana bani ina
sha, saboda na kasa ko da runtsawa ne in yi saboda
tsananin tsoron da nake ciki.
Washegari da sassafe sai ga Yakumbo Halima da
Yaya Dijah sun iso, ita kam Yakumbo taje wajen Yaya
Dijah ne wai ta ji taje na karbo sakon ko ban je ba naki
Zuwa? Yaya Dijah ta ce, "AI ma wunin jiya ba a ganni
ba ana ta nemana kan haka suka rankayo gida don Su

10

gani na dawo ko ban dawo ba? In ban dawo ba a nufi
gidan Malami."
Sai suka zo sulka same ni, Babana ya kwashe
bayani yayi musu, suka yi wa juna barka saboda ban
yarda na ambaci sunan Yakumbo Halima cikin
bayanin da nayi mishi ba, da ban san yanda suka
kwashe ba.
Bayan fitanshi ne Yakumbo ta rinka rantsuwa wai
tana so in yarda bata san haka yake.ba, don bai taba
nuna mata ba. Yaya Dijah ta ce mata "Haba Yakumbo,
bari wannan rantsuwa da ki ke yi, za ki kai ta in da za
a cuce ta ne da saninki."
Wai a wannan dan zuwan da suka yi sai da Baba
Lantana ta sossoka musu maganganun da Yakümbo ta
tanka mata suka yi fada kaca-kaca.
Ba karamin rashin lafiya nayi ba saboda wahala da
kuma ciwon da kafafuwana suke yi, tayi a dalilin
raunukan da suka samu ta hanyar taka kayoyin da ke
watse kan hanyoyin jeji da kananan itatuwa.
Duk da halin da nake ciki na kusan kullum sai
Babana yasa allura ya cire min wata kaya a kafa, ba
wannan ne abinda yafi damuna da tsaya min rai ba,
irin tabbatar min da Babana yayi cewar shi wannan
mutumin da muka je wurinshi ba kowa ba ne illa
Boka' saboda ni da kaina na ta6a kamanta wani hadisi
da ya ce, "Wanda duk yaje gun Boka ya kuma yarda
da abinda Boka ya gaya mishi, to ya kafurta da abinda
Manzon Rahama (S.A.W) yazo da shi, in kuwa yaje

11

wurin Boka bai yarda da abinda Boka ya gaya mishi
ba, to zai yi kwana arba'in yana Ibadar da ba za a
karba ba."
To wannene mai sauki a ciki? Sai na samu kaina
cikin wani irin yanayi ma tsananin rashin lafiya a
dalilin tsananin tsoro da tasin hankali, babu abinda
nake tsoro iris mutuwa a tsakanin wadannan ban samu
yar nutsuwar zuciyaia ba sai da Babana yayi min
bayani dalla-dalla, lokacin ne na dan samu natsuwar
zuciya ta na koma yin Istigifari da kyautata zato wurin
Ubangiji tare da kudurawa raina ba zan sake ba.
Ba zan sake zuwa wurin wani ba da sunan neman
taimako akan aurena ko a kan wani dalili na daban,
dama can ban taba ba, in ban da warinan lokacin to ba
zan sake ba gaba daya lamurrana dama ga Ubangiji
suke, ga. t shin kuma zan kara maida su, in kara
dogara in har da rabon zan yi aure an ubuta cikin
kaddarar rayuwata, to zan yi. Dor nayi Imani da
kaddatsare mai kyau da mara kyau.
Sanna rashin auren in har an kame kai ba zai
zamo munnaunan kaddara ba in har ba a rinka
watsewa ba, nan take nä shiga tunano manyan mata da
suka gama rayuwarsu ba tare da sun yi auren ba, ko
suka bar shi a shekarunsu naa kuruciya suka maida
hankulansu kawai wajen yin Ibadarsu, da auren da baa
san ka'idarshi ba, ba a tsare mutunci da
sharuddodinshi ba, ai gara barin shi yafi.
12

Nan take sai naji zuciyata tana kara raya min tsare
budurcina da yin komai wajen ganin budurcin nawa
yaci gaba da kasancewa a tare da ni, matukar ina cikin
hayyacina saboda in zamo daga cikin 'yanmata masu
mutunci da ke kaiwa mazajensu 'yanmatancinsu, ko
kuma suke gama rayuwarsu su koma ga Mahaliccinsu
da abinsu a tare da su.
Kan haka sai na kara kudurawa raina cewar zan
Kara kyautata sana'ata in kara riketa hannu bibbiyu
don ta zamo min abinda zan rike wajen ganin nayi ta
karatuna, ban zamo mai dora nauyina ga kowa ba.
Kusan satina biyu a gida ban fita ko'ina ba, ina
jinyar kafafuna a kwanakin nan duka babu wata rana
da gari ya waye har yamma tazo ba tare da Baba
Lantana ta jaddada min haukan da Rauhani ya ambata
min zai same ni ba, don kuwa in ita muna yi mata
rashin mutunci muna kwana lafiya, don kawai
Faddarar wahala ta kawo ta gidanmu, ta auri tsohon
ubanmu, to ai shi Rauhani ba zamu yi mishi iya shege
ya kyale mu ba, tunda ba tsoron ubanmu ya ke yi ba.
Ko kallonta bana yi, maganar tata kuma ba ta
damuna saboda a yanzu, na ragë damuwa da
al'amarinta, ban da haka kuma nafi yarda dá maganar
Babana a kan tata, don haka ina cikin kwanciyar
hankalina, ga kuma neman auren da nasan Yaya Dijah
tana yi wa Babana, wanda nasan ba da dadewa zai
tabbata, tunda na shaida abubuwa da dama da ta
gabatar.
13

eNa soma zuwa Makaranta, wai ashe dan wannan
neman nawa da Babana yayi a gidajen makwabta da ke
kusa ma wai abin magana ne, ya madidi ake tayi da ni
da shi ana fadin wai ai gashi nan ya ki aurar da ni yana
jira sai ya samu' dan mai kudi irin Mubarak.
To ga shi nan na gaji da zaman gidan na fara gudu
ina tafiya abinda kake yi a boye zan fara fito da shi
fili. Ko kula zancen ban yi ba, balle in samu wata
matsala, tunda an yi wadanda suka fi ta, na kuma ga
wucewarsu lafiya.
Abu guda daya da yafi bani mamaki shi ne, kowa
ko kuma in ce ko wadanne mutane a gidansu sukan yi
al'amarinsu shiru. Babu mai cewa konai, amma ni da
Babana kemai muka yi sai an ce mun yi. Da ana
tsayawa á iyakacin abinda muka yin ma to da sai in ce
da sauki, amma ina sai an kara.
Ta gidin Yaya Dijah na bi da muka tashi don tasan
naji sauki har na fara zuwa Makaranta. Na same ta
cikin farin ciki an kawo mata adashenta da tayi wanda
dama tàci alwashin kashe kudin gaba daya a hidimar
auren da za'a yi wa Babana.
Dadi ya kama ni, amma ko kusa ban kai Yaya
Dijah murna da dokin auren ba, duk da kudinta take
kashewa. Ina dawowa naje na samu Babana a
runfarshi, na zauna ina shan timatir din da na dauka
saboda sha'awar da ya ba ni, muna 'yar hira ina ba shi
labarin irin kąratun da aka yi a kwanakin da ban je ba.

14
Ya ce min "Eh, ai shi karatu haka yake, in dai har
kullum kana zuwa ana yi da kai, to ba ka gane yawan
abinda ake yin ya dame ka ba, sai in ka yi fashin zuwa.
Na ce, Eh Baba." A hankali sai na shigar da
bayanin abinda na tarar Yaya Dijan tana shirin yi, shi
ne hada kayan aure don maganar tana kara karfi tana
kuma kara matsowa.
Wani irin shiru Babana yayi, ya kafawa kwandon
alayyahun da ke gabanshi ido ba ya ko kiftawa. Har
tsoro ya fara kama ni, kar dai ya ce ba ya so. Cikin
natsuwa 8ai na tambaye shi "Me ya faru kayi shiru
haka Baba?
Ya ci gaba da aikin shirya alayyahun nashi yana
daurewa saboda mna su zuwa saye yana yi min bayani,
Wato ba wai bana son auren ba ne, fitina nake tsoro.
Ta zo ta kashe kudinta da tayi ta tattalawa bata yi wa
kanta ko ya'yanta wani abu sun ji dadi ba, in zo ni
kuma ban ji dadin abin ba, wannan ta gidan må ya ya
aka kare da ita kullum tana raina abinda ake kai mata,
balle kuma a ce an je an dauko yarinya an kawo,
alhalin ba wani abu nake da shi ba."
"Kai ai ina ganin kama wannan ba za ta yi wata
fitina ba Baba. Tare muka je gidansu dazu cikin
maganganun da naji Yaya Dijan tayi mata, har da na
daki ta ce mata guda daya ne kuma bai da wani girma.
Sai naji ta ce, "Ai babu komai, shi aure in aka yi shi
zaman lafiya ake bukata ba wani abu ba.
15
Babana ya ji dadin kalamin nata da na gaya mishi,
nan take ya ce "To babu laifi, sai lkuyi." Ya mike yaje
ya dauko wani tsohon bankinshi na karfe ya kwakulo
makullin a inda yake boyewa ya bani ya ce min bude
ki dibi abinda yake ciki na dai san babu yawa, amma
je ki ki kai mata ko sabulu sai ta saya."
Na ce mishi, "To Baba." Na louma yi mishi godiya
cikin farin ciki, don kuwa bakan alama ne na shima
yana son auren.
A natse kwarai na yi wa Sallau bayani, ko ban gaya
mishi abinda za ayi da dakin bá, amma nayi kokari na
fahimtar da shi ya gane cewar bukatar dakinne ya taso,
ba son korarshi nake yi ba.
Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min "To, tunda
haka ne Mero, in rinka kwana a zauren gidan nan
mana kawai, ai shima wani babban dalki ne, in na rufe
kofar waje na rufe ta ciki ba shi kenan ba?"
Nayi maza na ce "Kwarai kuwa Sallau, to ai ma shi
kenan tunda ka samarwa kenka wata dabara. "
A haka al'amura suka ci gaba har na kai ga fita
daga dakina na koma na Sallau na kira mai gyara ya y
wa dakin gyaran da ya dace kafin mai fenti ya zo ya yi.
Ita bata yi tunanin ba dom a ranar da ake aikin ma
wuni tayi tana fadin, To tunda babu tsayayyen da zai
tsaya ya kwasa ya kai gidanshi, can inda ake ta harin
kuma uwar yarinya taja tayi damara ba dai a shiga ba,
sai dai a kare a titi.

16

Ai sai kiyi ta gyara kina fenti don ki ji dadin zama
tunda ba ki da ranar tashi." Ban kalleta ba ma balle
tasan naji abinda take fadi.
Da daddare ma da Babana ya dawo naji shi yana
tambayarta ni ina butar nan ne? Sai naji ta ce mishi, Ni
fa Mallam na wanke butocina na tura su a Rarkashin
gado, don na fara gajiya da wannan auren na zuba
ruwa a buta.
Kai baka da wani aiki sai na a baka ruwa a buta,
don haka rinka yi da na roba kawai ga su nan a bakin
famfo suma a wanke suke nayi maza na tashi na fito na
ba shi butar da nake amfani da ita, na koma dakina can ciki na zauna.
Ina jin ta tana cewa, To, ni in ban da na san in ta
kasance a kanka dolensu su bani ciki da falon da nake
ciki zan yi wannan susutaccen zaman ne? To dadin
abin duk tsiyarsu su din mata ne, mata kuma ba wani
Rarfi ne da su ba da dai suna da namiji a cikinsu ne ai
da anga tsiya to babu shi."
Ranar Laraba da sassafe bayan an idar da sallar
Asuba aka daura auren Babana da amaryarshi Safara a
Masallacin unguwar su Baba Baidu ne yaje ya karbar
mishi auren.
Yana dawowa daga daurin auren Baba Sumaye ta
rinka rangada guda tana fadin, "Kai, wannan ya da
jaruntaka take, to ashe ma tana da irin wannan kokarin
ta bar ubanta yayi ta rayuwa a cikin wannan fitinar?
Ubangiji ka yi wa Hadiza albarka."
17

Da yake Baba Lantana bata tunanin koma1 game da
Babana musamman kuma da yake tasan mu'amalah
tayi matukar ja baya tsakaninshi da Baba Baidu balle
iyalinshi, bata kawowa ranta komai ba sai kawai ta
rinka jan tsaki tana fadin "Munafukan unguwa, ko ina
ta samo wata Hadiza kuma oho."
Sai tayi maza ta sake jan wani tsakin don ta tsani
Baba Sumaye, ta tsani kuma ta jiwo muryarta tana
wata magana sai tayi tsaki tayi ashar ko ta ce
munafukan unguwa.
Tsohuwar aminiyar aminiyarta Delu, ita ce tayi
sallama ta shigo gidan, rabon da in ganta kuwa an dan
kwana da yawa, ina jin tun lokacin da ta shirya aurena
da surukinta Alhaji Muhammadu Nalami, ta gaiyaci
tsofaffin abokai don su tayata sheda isowar ta da
mallakarta shekaru hudu kenan da suka wuce.
Delu ce yau a gidan? Tayi mata tambayar cikin
wani irin yanayi na wulakanci da shirin tozartawa,
"Kun gama zagaye-zagayen gulmarmakun naku ne
kuma ki ka gaji ki ka zo wurina? To ai babu abinda
bana ji, duk maganganun da ku ke fada suna dawo
min, musamman ma ke.
Tunda ke kam ai butuluci ne yake sa ki fadar
magana a kaina, ko ma menene a tsakanina da Nalami
ai aure

Please Login or Register in order to submit comment