Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauraron bayanin nata ban san
yanda akayi ba sai ganinta muka yi ta fito tana
rungume da dan jariri Asabe tana biye da ita cikin
katon lullubi sun sa kai sun fita sun bar gidan, ganin
sun bar gidan ya sa ni nufin shiga dakin namu wai in
kwanta. Abinda na gani a tsakar dakin ya sani

105
kwallara ihun da na dawo da baya cikin sauri Sallau
ya fito ya leka cikin dakin ya tayani ganina binda na
gani, ya koma ya dauko leda ya sanya shi a ciki ya
kuma. sa omo da izal da tsintsiyar zabori ya wanke
dakin tas zuwa tsakar gida dama bayan gidan baki
daya maimakon karni da kazantar jini ya koma tsabta
da kanshin kayaiyakin da ya yi amfani da su.
Na shiga dakin nayi salla na hau gado na kwanta
cikin jimamin abinda ya faru, akan idona Asabe ta
haihu ta haifi da babu aure ba shiri nake yi da ita da
uwarta ba amma na tausaya mata tare da dan nata, ina
cikin hakan na jiyo muryar baba Lantana tana cewa ba
dai dani kuke yi ba ai za mu sa kafar wando daya ni
da ku, munafukan banza munafukan wofi matsiyatan
mutanen da basu san mutunci ba duk zaluncin
ubanku.
Na yi kasake ina sauraron zage-zagen nata cikin
zuciyata na ce, oh oh wannan mata da jarumtaka take
ko ita da su wa take yi oho.
Ina jinta ta shigadakin da Sallau yake bamuji
komai ba illa iyaka dai na jiumuryarshi yana ce mata
to nan take kuma ya yi waje, nima na fito don in
nemawa babana abin karyawa da kuma maganinshi,
lokacin ne na gane daga tafiyarshi masallaci don
sallar asuba bai sake dawowa gidan ba.
Ina daki a kwance ina sauraron shigowar babana
don ba dabi'arshi bacewucewa kasuwa daga

106
masallaci na ji muryar Salau alamar ya dawo daga
aiken da ta yi mishi na ji shi a fusace yana ce mata,
kin ganta ko mnama kin ganta ko baba kinga halin
Asaben ko? A gabanki bakinta ta ce min Agogo ne
ba?
Gabana ya yi mummunan faduwa cikir raina na
ce Agogo kuma? Ban kai karshen maganar zucin
nawa ba naji Sallau shima yana karasa nashi bayanin
to an je anzo da Agogo ya zo ya zare m ata ido yana
tambayarta' shi kadai ne su sauran me yasa bata
amabci sunansu ha sai shi? Mainakon taja ta tsaya a
kan shi kadai ne sai kawai ta tsorata ta ce wai Alhaji
Nalami ne.
Kiis ya rage in rikito kasa daga kan dan gadon
nawa saboda firgitar da nayi, nayi maza nasa hannu
biyu na dafe kirjina saboda harbawar da ya kama yi,
nayi maza na sake tambayar kaina, Ahlaji Nalami
kuma? Wannan abin mamaki da ban tsorod a yawa
suke, Nalami da Agogo su Asabe take tuihuma da yi
mata ciki, ita kuwa wane batan basira ne ya kaita yin
hakan?
Tsawon lokaci ina tunanin tsakanin biyun wanne
ne dama dama? Agogo dai shi ne mutumin da ya
jagoranci abinda Mubarak ya sa aka yiwa Sallau
wanta da suke uwa daya shi kuwa Nalami ba sai na
tsaya ina wani dogon bayani a kanshi ba ko da yake
dai baba Lantana tayi nufin badani gareshi ta kuma yi

107
mishi tayin Asaben don ta samu warware mas alar
kudin da suka shiga tsakaninsu to amma tunda hakan
bai yiwu ba wane birgewa ko sha'awa wannan
mutumin ya baiwa Asabe da har ta yarda da shi har
take tuhumarshi da zamowa uban danta? Na yi maza
na bar wannan tunanin na shirme tunda gani nake
tamkar bai shafeni ba na amsa sallamar da naji ana
kwalawa a kofar gidanmu da sauri na fita don ganin
masu salalmar, tunda na jiwo muryoyi da yawa
alamar ba mutum daya bane.
Ina fita naga an ciccibo babana rabe-rabe wai
faduwa yayi a kasuwar timatirin su nan take na kama
salati, ina yin kuka, wani daga cikin mutanen dake
rike da baban nawa ya dakamin tsawa, kaice ki ba
mutanc wuri munafuka kawai duk ba ku kuka jawo
mishi ba, ita ce fa wacce kwanaki aka yi tsiyar nan a
kanta ran daren da zan daura mata aure da wani aka
kamota a dakin wani kato wanda shi babu yanda ba a
yi da shi ba ya auretan ya ki amma don hauka da
rashin zuciya taje ta kai mishi kanta shi kuwa warda
zai auretan da ya ji labari ya cco ti ya fasa.
Wani daga bayan yace, a'a to zai fasa mana da
ka auri bduurwa fanko ai gara ma ka auri bazawara da
ma kasan abinda ka aura, ni da aka bada labarni
haihuwar yar tashi ai na dauka ita wannan din ce ta
haih:, ashe wata ce kuma daban? Wato shi 'ya' yan
nashi duk haka suke? Su matan lalacewa ta bin maza

108
shi kuma namiin kana ganinshi ba sai an yi maka
bayani ba, baki a rube ko ina kuma a fuska tabon
adda, to amma dai dan gara shi tunda ba zai dauko
mishi irin wannan maganar ba, lalacewar 'ya mace ai
babbar musiba ce ko ba komai kuma gashi ya fara
dawowa kan hanya tunda yana binshi kasuwa yana
kuma taimakonshi ba kadan ba.
Kukan da nake yi bai hana zuoiyata tunamin
maganganun nasu ba wannan wane irin rashin adalci
ake yiwa babana wato su Asabe su Sallau din ma duk
ya' yanshi ne? Ban kai karshe ba na ji wani ma ya
kama bayanin 'ya mace, nifa shi yasa ma ban cika son
haihuwarta ba na kuma yi sa'a 'ya'yana bakwai gaba
dayansu maza ne babu mace ko daya.
Wani kuma daga can gefe ya ce kai ba fa duka
matan ne haka ba in akayi sa'ar su aka dace da na
kirkin dadin al'atmari ne da su saboda su din masu
tausayi ne, shi malam Habu har da laifinshi cikin
lamarin iyalinshi don kana da hakuri ba dalili bane da
zaka zuba ido ka barwa matarka da' ya'yanka sai
yanda tayi da su ai cewa akayi ku kare kawunanku da
iyalanku daga shiga wuta to shi ya zuba ido a kan
komai ya bar mata tafi karfinshi, yaushe ake yin
haka? Haka ne haka ne suka amsa.
Suna barin gidanmu nima na fita don nemana
motar da zata daukar min babana zuwa asibit, a kan
idona ina ji ina gani nake jin mutnac suna bayani an

109
haifi shege yau a gidan malam Habu wanda ake yiwa
bayanin sai ya tambaya wane malam Habun? Sai a
tsaya bayani malam Habu mai tmnatiri, nan na wajen
kan kwana baban wannan Maryam din da kwanakin
can watannin da suka wuce aka kamota a dakin
saurayin da take kwanan gida har kan haka mutumin
da zai auretan ya fasa? Sai ace haka haka na tuna,
dattawan unguwa kuwa fadi suke yi kai malam Habu
bai yi sa'ar iyali ba.
Raina ya baci zuciyata tayi zafi hankalina ya
tashi, na rasa inda zan tsoma rayuwata in ji dadi, da
dai ace nasan abin da zafi àru kenan to da na ja Asabe
na fitar da itn daga gidanmu in ya so ko a kan titi ne ta
haihu, gaba daya sai masu magana suka mance
dabana ba shi ne uban Asabe da Sallau na asali ba
suka kuna mance da cewar bayanin da nice 'yarshi ta
asali yana da ya' ya Dina in ni ban zamo mutuniyar
kirki ba ita ta kirki ce don kuwa in dai biyaiyar aure
shi ne kirkin mace to yaya Dija ta kirki ce.
Ina kuka nas higo gida lare da direban motar da
na samo don ya tayani daukan babana, yaya Dija na
gani a gidan ta zo saboda labarin da ya je mata sai dai
kuma wai cacar baki na samu suna yi da baba
Lantana, Asabe ai mai imani ce shi yasa ta haifi nata
dan mai rai ke sau nawa kanwarki tana cikin shege
kina cire mata? Ko ance miki ban sani ba ne.

110
Wuceta nayi ko kallonta banyi ba na shiga dakin
da babana ke kwance na cewa direban shigo daga nan
kan ya shigo ta biyoni ina kuka nace mata babanmu
yana kwance kina fada da ita?
Kan tayi min magana baba Lantana ta cafe tana
zaton zan kyale ta ne take wani zuwa wai kar
'ya' yana su sake shigowa nan gidan to wannan gidan
har wani gida ne da za a yiwa mutane doka a kanshi?
Ban amsa ba itama yaya Dija ta yi shiru, ai a
shirye nake don ni din warki ce dai dai da kugun
kowa wanda duk ya shiga lamarina zan shiga nashi in
ka gayamin cuta kuma zan gaya makam utuwa,
munafukan banza munafukan wofi duk sai kun ci
gidanku a hannuna.
Muna jinta tana tayi muka fitar da babanam uka
tafi asibiti gado aka bamu ni ce kuma na zauna tare da
shi a wannan karon ko tayani kwanan da Sallau ke yi
ban yarda ya yi ba.
Ina zaune kan kujera gaban gadon babana yake
kwance ina kallon babana da halin da yake ciki,
tunani kawai nake yi na al'amuran dake ta faruwa da
mu daga wannan mu koma wannan, sai ina ganin
kamar al'amura sun soma wucewa an fara samun
sauki sai kawai wani abin ya sake tasowa a sake
fadawa cikin wata mas'alar da zan rinka ganin tamkar
tafi wacce aka baro baya tsanani.

111
Ana cikin haka naji motsi a kusa da ni, nayi maza
na daga kai don ganin ko waye? Mubarak na gani a
tsaye daga gefe kadan kuma babanshi ne
Muhammadu, cikin tsananin kaduwa da firgita nayi
maza na sauka daga kan kujerar da nake zaunen na
tsuguna a kasa karo na farko da na ga baban Mubarak
bayan faruwaral'amuran da na daina shiga
gidanshi.
Tashi maryam tashi ki hau kan kujerar ki ki
zauna. Ban iya motsawa ba ban iya tashi na hau kan
kujerar ba ban kuma iya buda bakinan a gaisheshi ba,
kuka kawai nake yi.
Ubangiji ya bashi lafiya, Ubangiji ya sa kaffara
ce, Mubarak ne ya amsa addu'ar da baban nashi ya yi
da amin.
Maganar da na ji Mubarak din ya fara yi min ta
tabbatar min da cewar bayan yayi addu'ar bai tsaya ba
tafiya yayi don haka na mike na zauna a kan kujerar
da na bari.
Kina ganin kamar akwai wani dauwamammen
abu ne a rayuwa? Duk wadannan abubuwan da kike
gani wata rana za su wuce don hakaki rinka yin
hakuri. Ya ciro kudi masu yawa ya ajiye a gefen
gadon, ki rike wannan a wurinki ni zan tafi baba yana
jirana:
Na yi maza na ce mishi bana so dauki kudinka ka
tafi da su, bana bukatar komai daga gareka. Ya yi

112

kamar bai ji ba ya juya da nufin tafiya, nayi maza na
ce mishi, da ka yardar kca daukárdon kar su zamo maka
sanadin bacin rai saboda zan iyabadasu a kaiwa ma...
Ban san yanda aka yi ba naji ba zan iya karasa
abinda na yi niyyar gaya mishin ba, wucewa yayi ya
yi tafiyarshi baftare da amsa min ba, nima na zubwa
kudin ido ina kallonsu: lokaci mai tsawo kafin nasa
hannu a kansu na daukesu na adanasu.
Kwananmu uku kafin a ka sallamomu muka
dawo gida.
Mutane suka sake tasa babana da gidan mu da ni
ma a gaba kai kace nice na haifi dan shegen.
Ina dakina ina zaune cikin damuwa da tunani iri-
iri na ji Sallau yana cewa, baba Lantana ai Asabe ta
kamanta ruwa ido 6atan 6akatantan zata yi tayi dalilin
da dan nata zai rasa madogara kamar....
Da sauri baba Lantana ta wulwulo ashar ta antaka
mishi, ya ce to shi kenan baba nayi shiru na kuma ji ni
mahaukaci ne to na rokeki ki taimakeni ki daina
tunani wajen maganar Asabe da samarinta da dantaki
samu masu hankali su rinka zuwa miki.
A wannan lokacin wata irinr ayuwa na tsunduma
yi da ba ma zai yiwu ince zan tsaya ina bada labarinta
ba, abinda dai na sani kawai shi ne ina wuni ban kai
wani abu bakina ba saboda kwata-kwata yunwa ta
rabu da cikina mafi yawancin lokaci ruwan kawai

113
nake sha saboda bushewar makogaro dake yawan
damuna.
Rannan an wayi gari da safe wankin kayan
babana nake yi saboda ya dan fara samun sauki ya yi
amfani da tsabtataccen kayaya dan ji dadi, ina cikin
yin wankin ne naji anyi sallama a kofar gidanmu,
Sallau baya nan don haka na yi maza na leka tun da
nasan babana bai mallaki karfin yin hakan ab.
A hankali nayi leken don ganin mai sallamar a
dalilin ban cika son hada ido da yaran unguwar ba,
malamina na makarantar islamiyya na hanga malamn
Yahuza da sauri na karasa fita wajen naje na tsuguna
kasa cikin wani irin yanayi na kunya da kuma
girmamawa, sannu da zuwa malam.
Haba Maryamu shirun naki ai yayi yawa shiru-
shiru shiru da ba zai yi auren ba ai sai ki dawo
karatunki, ai ba haka rayuwa talke ba komai kika gani
yana da lokacinshi shi aure lokaci ne in har lokacin
shi bai zo ba babu yanda za a yi a yi shi, watakila
mijin naki bai zo ba, ita kuma mace bata aure sai
mijinta don hakaki dawo karatu kin gane ko? Nace
mishi to malam.
Kar fa kice min to'ki zo baki dawo makarantar ba
don sau biyu ina turo yara abokan karatunki su zo su
kiramin ke ba ki zo ba.
Kamar ince mishi babu wanda ya zo ya kirani sai
naga bari in yi mishi shiru kawai. Ai ba a girman da

114
ake wuce yin karatuna addini, shi dan adam yana
rayuwa ne a kan neman ilimin sanin nahalicci don
haka ki dawo makaranta kin gane? Na sake ce mishi e
malam.
Muka yi sallama ya tafi nima na shiga gida, a
zuciyata na'rinka tunanin ko su waye malam ya turo
su kirai oho, ina cikia tunanin hakan sai kuma na
watsar na bari saboda na gane sanin ko.su waye din
ba zai amfanar da ni da komaib a.
Zuwan da malam Yahuza ya yi ya sanya ni na ji
wani canji cikin zuciyata saboda irin nasihun da ya yi
min, kwadayin karatu ya sake dawowa cikin raina, sai
dai kuma yaya zanyi in sake fuskantar yan
makarantar bayan duk irin kwaramniyar da na yi ta
fama da ita? Da wane idon zan sake kallonsu?
Wannan shi ne abinda ya fi komai tsaya min a rai.
Kwana biyu bayan zuwan malam har lokacin ban
fara zuwa makarnatar ba sai dai kumna bana jin dadin
hakan da nayi, in na yi tunanin menene ya dame ni
wanda ya sa zuciyata take yi min nauyi? Sai int una
malarn Yahuza ya tako har gidanmu ya nemi in koma
makaranta in yi ka ratu abin yi hakan ba, abinda ni da
kaina na sani ba sai an gaya min ba yin hakan rashin
girmamnawa ne ga na gaba musamman malaminka.
Rannan dai na daure na tafi gabana kuwa sai
faman bugawa yake yi, kirjina yana ta faman harbawa
da sauri-sauri, a tsarge kawai nake zaune a ajn motsi

115
mai dan karfi in akayi sai inji na kara takura in yi
kamar ni ake nunawa ko ake bada labari na.
Malam Wahuza ya yi matukar farin ciki da ganina
ya yi mana karatu ma1 gamsarwa ya yi mana kuma
nasiha kan yan uwantaka irin na musulunci tare da
bayani kan wanene musulmi? Lokaci mai tsawo ya
dauka yana bayani akan siffofin musulmi na kwarai
da Manzon rahama (S.A.W) a kai daga cikinsu akwai
kubutar musulmi dan uwanka daga sharrin harshenka
ya gama, ya y mana addu'a muka shafa nad awo
gida.
Na soma zuwa makaranta a kunya ce a darare sai
dai ba a dauki lokaci mai tsawo. ba sai na wartsake har
ma karatun nawa ya zamo daga cikin abubuwan da
suke ragemin damuwata su nutsar min da zuciyata
musamman ma da yake yayi dalilin da na koma yin
karatun Alkur'ani mai girma sosai da sosai wanda da
na daina yi saboda damuwa da rudewa in ba haka ba
ai na dade ina jin malamai suna fadin cewar shi
Alkur'ani waraka ne ga duk wata cuta ciki kuwa har
da na zuciya.
Daga komawata makarantar Islamiyya sai
mu'amala mai karfi ta kullu tsakanina da malam
Yahuza, saboda kullum idonshi yana kaina na zo
makaranta ko ban zo ba.
Ki koma makarantar oko don ki samu damar
mallakar takardarki ta karatun college, na ce a'a
116

malam ai ni bokon nan ba wani damuna yayi ba. Ya
vi murushi to at ko bai dameki ba kin rigakin yi shi
takardar da za ki mallaka ta zame miki shedar wahalar
kiken emaki yi wasa da ita, alhalin ilimin yanzu ya
ta'allaka ne a kan abidna aka gani a rubuce don
hakaki koma ki yi karatunki karki yi wasa da
lokacinki, shi lokaci da kike gani ba a wasa da shi
tsada ke gareshi, baki ji abin da wani bature mai
hikima ya fada ba? Ya ce "A man who dares to
waste an hour of time was not discovered the value
of life.
Mamaki ne ya kamani jin da nayi malam Yahuza
yana rangada lafiyaiyen turanci da bakinshi bayan na
dauka arabiya ko larabci kawai ya iya.
Shirund a nayi ya sashi tambayata ko kinfi gane
dai ki jira mijin aurenki ya zo ki yi.aurenki kawai?
Shiru nayi ban amsa ba iyaka dai kaina a sunkuye ban
kalleshi ba, amma nasna murmushi yayi kafin ya ce
min, iaina zamna jiran miji Maryam saka al'amura
masu yawa a gabanki sai ki ga ma yafi saurin zuwa
gareki tunda shima ya san bashi kadai kike jira ba kin
gane? Na ce mishi to.
Kalamai da nasihohin da malam Yahuza ya yi ta
yi min su ne suka karfafa min zuciyata da ta riga ta
karaya da al'amuran rayuwa har na rinka ji da ganin
tamkar bani da wata mas'ala ko damuwa a tare dan i
in dai ba ta rashin lafiyar babana ba ne.

117
Makarantar koyar da sana'o'in mata ta Markas
wacce Mansur ya taba bani labari na shiga da
taimakon malamina malam Yahuza shi ya karbomin
form din na cike ya mayar ya kuma biya kudin form
din gashi kuma anyi sa'a kyau ta ce form din kadai
ake saya, ajin dinki na shiga shi en.a raina tun sanda
Mansur ya ce min ya fi sha'awata da yin dinkin.
Na fara zuwa Markas mas'alolin da na fuskanta
ba su wuce na wahalar tafiyar kafar da nake yi da
kuma dawowa gida da nake yi ban samu abincin da
zanci ba sai na nemawa kaina hakan kuma na jira.
Na wayi gari rannan ina gida banje wurin koyon
sana' ata wato Markas a dalilin renar da Jumaa ce
ranar Juma'a kuma ranar hutu ce a garemu, ina
kwance kan gado na na hutawa bayan na kammala
wanke mana kayanmu ni da babana sai kawai naji
Sallau yana cewa uwarshi, kai an auná arziki yau dai
an daura auren Asabe magana ta kare.
Sauri nayi na kara maida hankalina wajen jin
maganar tasu tare da tunanin Asabe tayi sa'a itama ta
samu tayi aure dukd a cikins hegen da tayi ta haihu ni
ce dai... kan in karasa tunanin zuciyar tawa sai naji
baba Lantana ta ja wani mummunan tsaki tare da
fadin, to wani kokari kayi a hakan? Ina ce takardar
filina da ya karba kawai nace ka karbo min a
matsayin sadakin auren nata ka kasa ka karbomin nera goma.

118
Ya ce, uhun baba kenan ba ki ma san yanda akayi
ya bada nera goman bane abinda ja yayi ya tsaya a
kan nera bakwai zai bayar sai da malamin da zai
daura auren ya ce mishi bai kai rubu'u dinar din da
shari'a ta yarda a karba a matsayin sadaki ba shi ne ya
bada goamn, ni dai tunda Asabe ta samu mijin aure
zata isa gidan mijinta yau danta kuma ya samu uba ba
zai yi ta watangaririya a hanya bai san ubanshi ko
danginsu ba ai shi kenan magana ta kare a wurina.
Duk da ganewar da nayi Alhaji Nalami Asabe ta
aure kalaman da Sallau ya yi sun sani girmamashi tare
da auren da Asaben tayis aboda na gane aure daraja ke
gareshi Sallau kuma na gane natsattsen yaro mai
kuma hankali tsayaiyar tarbiya ce kawai bai samu ba.
Na fara zuwa wajen koyon sana'a ta a Markas
babu dadewa'sai kuma malam Yahuza ya sake yi min
magana kan wata babbar makaranta ta ilimin addini
mai zurfi da aka bude duk da irin kudaden da ya yi
min bayanin za a kashe kafi in so ma karatun na shige
ta saboda yaya Dija ta amince da shigar tawa ta kuma
bayar da duk wani abinda aka nema shi kuma malam
Yahuza sai ya taimaka min da manyan litattafai masu
tsada a matsayin aro kafin ta samu ta saya min nawa
in mayar mishi da nashi tunda shima ba daina karatun
ayyi ba tunda shi littafi abin ajiyewar dalibi ne.
A wannan lokacin sai na zama kusan kullum ina
da abin yi mafi yawancin lokacin ma nakan fita da

119
safe ne in dawo da yamma saboda zan tashi daga nan
in nufi can don ma dai kawai babana yana raina
kowane lokaci.
A wannan lokacin baba Lantanaa wuni take yi
tana yiwa babana gorin auren da Asabe tayi da na
hada 'yarka da shi kuka ki ai gashi ni na bashi tawa
tana kuma zaunen abin ta tsaf cikin rufin asiri da
kwanciyar hankali ga mutunci shi aure ai darajarshi
yawa ne da ita ba kowane yake samun darajar yin shi
ba.
Na jinsu bana cewa koami, iyaka dai na sani na
kuma yarda da kalaman nata duka iyaka dai can cikin
zuciyata a yanzu bani da damuwa mai yawa kan
maganar yin auren nawa na yarda na kuma gamsu da
cewar dak ullum malam Yahuza yake yi na komai
lokaci ne kowa kuma yana da nashi lokacin, Nalami
kuwa in dai shi zan aura to ina ganin kamar gara in yi
rayuwata kawai a haka ya fiyemin don haka ko kadan
bana jin zafin kalaman nata.
Ina zaune a dakina bayan na idar da sallar
magariba takardun da zan tafi da su wajen malam
Yahuza nake hadawa saboda muraja'ar da yake yi
min kan wasu darussan masu dan nauyi da nake
bukatar fahimta mai kyau a kansu, har zan yafa
hijabina in fita sai kawai naji yaro ya shigo yana cewa
wai ana sallama da Maryam a waje.

120
Na daga ido na kalli agogo cikin zuciyata na ce
kar dai Halliru ne ya z0 a wannan lokacin. Halliru shi
ne sabon saurayina da Yakumbo ialima ta turo min a
dalilin ya ce mata ta duba mishi budurwa mai hankali
da iya kwalliya kasancgwar shi dan mijinta da ta rike
ya sa ta ce bai dace da kowaccc budurvwa ba sai ni, ni
kuwa a wannan lokacin bani da wani zabi na daina
Pzaba ince ga irin saurayin da nake so ko ga irin mijin
da zan aura, aurcn kawai nake so wanda duk yazo
kuma a shirye nake zan aure shi, in dai huta babana
ma ya huta mu duka mu huta damunmu da ake yi ana
bada bayanin mu a kan idona sai ka ji dattawan
unguwar suna cewa ai nan kusa kusa duk ai babu
sauran sa'arta kai kannenta na kusa ma babu duk sun
garna yin aure sai ita kadai.
Na debi littafin nawa na rungume na jawo kofata
na rufe na yiwa babana sallama na fito da nufin in
mun gama maganar da za mu yi sai kawai in wuce na
kuma san ganina tare da litattafan a hannuna zai kara
sashi tafiya da wuri tunda yasan ina da abin yi.
Ina fita waje maimakon in ga Halliru, Mubarak
na gani a tsaye, wani irin lalataccen kallo ya yi min da
ya sanya gabana faduwa cikin zuciyata na yi maza na
ce, ban yafe maka ba zuwa kofar gidanmu da kayi ka
fadar min da gaba.
Shima malamin naki yana nema ya rikide ne ya
Zama saurayinki? Da sauri na daga ido na kalleshi

121
cikin tsananin mamaki abinda ban taba zaton wani zai
yi tunanin hakan ba don babu wata alama da take nuni
da hakan.
Idan kika kuskura na gane da wani abu a
tsakaninki zaki bar karatun naki gaba daya ki koma
Zaman gida in kumakina ganin kamar wasa nake yi to
bari in gane halkan ki gani kina nufin don yana koyar
da ke karatu a da sai kuma a yanzuki rinka kwasar
litattafaikina zuwa wurinshi kuna zama ku biyu?
A kidune nace mishi, ba fa mu biyu bane? Ya yi
maza ya katseni ko ku dubu ne ban yarda ba kar in
sake gani ko jin kin fita daga gida bayan sallar
magariba, na gaya miki.
Kuka na soma yi mishi saboda bakin cikin abinda
yake yi min, takuraw ar ta kai duk inda ta kai, komai
nake yi ya sani ko baya nan nayi in ya dawo zai ji
labari.
Cikin karfin hali na daure zuciya ta na ce mishi,
to wai ni ina ruwanka da ni ne? Ina abinda ya shafeka
da abinda nake yi, kullum sai ka shiga harkata, kullum
sai ka takurawa rayuwa ta.
Ban san dalili ba rannan sai na kasa zuwa wurin
mraja'ar da Malam Yahuza ke yi min, maimakon
washegartnma inje ban i cb a sai kawai na hakura da
muraja' ar na koma maida hankalina sosai a aji wajen
fahimtar dukkan darussan da ake yi mana.

122
Kullum dai burina bai wuce in samu lokaci in
tatawa Mubarak rashin mutuncin da zai sa ya fita
harkata kwata-kwata ba amma in na ganshi sai in kasa
saboda kwarjininshi da yake yi min nauyi a idona.
Gabatowar watan azutin ra:nadan mai girma ya
sa aka shirya mana jarrabawar da a bayanshi muka
samu hutun makaranta har sai bayan salla mu koma,
farin ciki sosai nayi a wannan. Jlokacin a dalilin
jarrabawa ta tayi kyau banda haka zan dan samu
hutun wahalar da nake yi ta zuwa makaranta da kafa
in dawo da kafa, Sannan zan dan fuskanci wani abinda
nake kuma dokin yi shi ne dinki don na dan fara
iyawa har yaya Dija ta gamsu da labarina bayan
dinkin 'ya'yanta dana dade ina yi musu ta hada min
har da nata nayi a dalilin hakan kuma ta ma karbar
min na kawayenta da abokan zamanta.
Ki natsu sosai ki yi musu mai kyau don sai ya
zamo tamkar tallan iyawarki kikayi, nace mata to.
A wannan lokacin hutun makaranta da dokin
dinkin azumi da nake yi ne ya ragemin damuwa ko
bacin ran da na samu kaina a ciki ra turowar da
Halliru ya yi a ka karbe mishi kayanshi, shi ko kayan
na gani ina so kamar yanda wasu suke fada da da ya
kawo

Please Login or Register in order to submit comment