Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in je in
shedawa yaya Dija labarin aurcn Mubarak da naji,
garin ya ki wayewa nisand aren ya kai matukar nisa
duhun daren ma ya kai iyakacin duhu, gani nake
tamkar in naje na gayawa yaya Dija tana da wani
taimako da za ta yi min ko wani amfani da zata yi
min, ko wani amfani da gaya mata zai amfanar da ni,
waiyo waiyo waiyo abinda kawai nake iya ji yana
fitowa daga cikin bakina kenan, saboda tsananin zafin
da zuciyata ke yi, da kyar na samu garin ya waye.

53
Muna hada ido da baba Lantana a tsakark gida ta
saki wani irin lallausan murmushi wanda rabon da in
ganta tana fara'a tun ranar da Nalami ya karbi
takardar filinta ya tafi, muna hada idon sai ta yi dariya
ta ce, anya ashe kema kin ji labarin, ta sake sakin
wani lafiyayyan murmushin kafin ta ce, uhun in dai
da namiji ne ai kuka ba ki ma fara shi ba tukun balle
ke da kika wulakanta jama'a a kanki ai kadan kika
soma gani. Ban tanka mata ba na sa kai na fita gidan
yaya Dija nake nufin zuwa.
Ina fitowa daga gida na kara rudewa na kidime
jikina ya dauki rawa karkar kar, cikin hanzari na juya
da baya don in koma gida, amma saboda tsananin
firgitar da nayi maimakon in shga gidanmu sai na
smau kaina a zauren gidan su baba Sumaye,
tsugunawa nayi a zauren cikin wani irin rudani,
cincirindon mutanen da na hango a kofar gidan nasu
Mubarak ne ya yi matukar razanani tafiya daurin
auren nashi za a yi ko kuwa har sunje sund awo ne?
Ban kara sanin irin rudewar da nayi ba sai da na
ganni durkushe gaban baba Sumaye ina kuka alhalin
ba abinda nayi nufin yi kenan ba.
Za ki yi kuka mana Mero za ki yi kuka kai me
sonki ma ai zai tayaki zubar da hawaye, wadannan
abubuwan da suka faru dole ai ba kananan abubuwa
bane ko ni din nan nayi kuka nayi addu'ar ubangiji ya
jikan Ramatu da rahamarsa sanda akayi bikin Dija da

54
yake tana raye ai ba a yi haka ba shiru akayi komai
aka gama cikin rufin asiri da mutunci su na murn
amuna murna, kema maraicinta ne ya ja miki shi ya sa
bana jin zafinki sosai bacin raina daya ne da kikaje
kika bashi kanki to ga abinda gari ya waya, yanzu
waye a kasa? Waye kuma a wulakance? Babu amfani
in tsaya ina yiwa baba Sumaye bayani kan cewar
banyi abinda ake zargina da aikatawa ba, tunda nasan
ba yarda zata yi ba don haka sai kawai naja bakina
nayi shiru ina sauraron abinda ake gaya min.
Ahmad Mubarak zai yi aure don yana son
daidaitawada m ahaifinshi, yin aure da kuma alkawari
na zai fita daga lamarinki gaba daya su ne ka' idojin
da ya yarda da su kafin shi Alhaji Muhammadu ya
yarda ya yafe mishi laifuffulkan da ya yi mishi, kema
kuma don baki da mai taimakon kuruciyarki ya doraki
a kan hanyar da tad ace ne ya sa aka barki kina
wannan kai kawon ana yi miki wadannan wakokin na
shakiyanci da iya shege, ni dai banga laifinsu kan
abinda sukayi ba sun mutunta dansu ne shi da ai
daraja ne gareshi sannans hi Alhaji Muhammadu shi
kadai ke gareshi in dai a kan da namiji ne sannan
ya' yanshi duk mata ne abinda ya 6atamin rai kawai
shine da basu tausayawa maraicinki ba in ba haka ba
komai kikayi ai kuruciya in ya hadu da maraici
lamarin ba karami bane sai gyaran Ubangiji, to saukia
Sunce bai zama dole a ce da dansu kadai kika lalace

55
ba don haka a matsayinsu na iyaye ya zama musu
dole su tsaya su ga yayi aure mai tsabta don neman
Zuriya mai albarka.
A zuciyata na ce wato ni in an aureni ba zaa
samu zuriya mai albarka ba saboda tunanin da sukeyi
na na riga na lalace? To in ni a lalacen nake ba da
dansu aka ce na lalacen ba? Wato in ma da dana
baiwa Mubarak kyautar budurcin nawa ya karba irin
hukuncin da za su zartar a kaina kenan? Tambayoyin
da suka rinka kai kawo a cikin zuciyata kenan kafin
lokacin da na katse maganar zuci na koma sauraron
abinda baba Sumaye ke gaya min.
Ai ita uwar goyon nashi, nayi maza na daga ido
na kalleta saboda ban gane maganar da take son yi ba,
uwar goyon wa? Cikin natsuwa ta ce min shi Mubarak
mana, na sake kallonta sai ta shiga yi min bayanin
saboda ta gane abn san komai ba kan maganar da take
nufin yi min din.
Ita Hajiya Ummulkairi ai ba ita ce mahaifiyarshi
ba, na azro ido ina kallon baba Sumaye cikin tsananin
mamaki, ban taba kawo irin wannan tunanin ba cikin
raina, saboda ban taba tunanin akwai wata
kyakkyawar mu'amala tsakanin matar uba da dan miji
ba balle har aje ana samun dama ko shagwaba irin
wacce na saba gain Mubarak yana yiwa Ummanshi ita
kuma ta bar komai da takeyi tayi ta tarairayarshi.

56
Mahaifiyar Mubarak ai Hindatu ce budurwa ya
aureta tazo ta haifeshi shi kadai zaman yaki dadita
tsallakeshi ta yi tafiyasta tunda ta tafi kuwa ban sake
jin ko da labarin ance ta zo ganinshi ba, ina ganin
kuma sanda ta barehi baifi.shekara guda ba a duniya
don sansdin mutuwar, aren ne. ya zama sanadin
yayeshi saboda shi uhen ya ce ba zaa tafi mishi da shi
ba, sai ya baiwa ita Ummulkairin shi da yake mata ce
mai hikima sai ta sa hannu biyu ta rike irin rikon da
ko ya'yanta bata yiwa haka ba, bata bari mummunan
zaman da sukayi da uwarshi ya shafeshi ba.
Na sake kallon baba Sumaye saboda tsananta
mamakina yayin da ita ukma ta ci gaba da bani
labarin da ban sani ba.
Shi Alhaji Muhammadu ai ya auri mata da yawa
a sanina nama akan idona ina ganin sun kai biyar,
iyaka dai mafi yawancinsu basu haihu da shi ba daga
ita Ummulkhairin ce sai A'indatu su ne masu 'ya'yan,
ita Ummulkhairi ya'ya mata uku su ne su Kaltume ita
kuwa dama ba budurwa ya aureta ba bazawara ce ta
ma haifi 'ya'ya biyu a can wani gidan, a cikin jikokin
ta na can gidan nema yanzu aka baiwa Mubarak din
guda daya, ai Rumasa'u ce yarinyar da zai auran.
Ban san yanda akayi ba sai kawai na tsinci kaina
da tsanar Mubarak da Ummanshi da babanshi da ma i
ta Rumasa' un tunda na santa na saba ganin tana zuwa
gidan sai dai ban taba sanin alakar dake tsakaninsu

57
ba da ya wuce na 'yar babbar yarsu ce na fassarasu a
matsayin wadansu irin mutane mayaudara marasa
adalci wadanda basu san kowa ko komai ba in banda
kansu.
Shi da ai darajanta shi ake yi a adanashi a yi
tattalin darajar shi da mutuncinshi baka barin shi ya
wulakanta a gaban jama'a balel ya je yana lalacewa
masoya da makiya suna kallo wasu na bakin cik
wasu na madalla, shi Alhaji Muhammadu ya yi nufin
adana danshi ne don ba zai yiwu ya zuba mishi ido
yana nema ya shiga wani al'amari ba, ita kuwa
Ummullkoiri sai tayi amfani da damar da tas am
wajen oshi jikarta ya aura, kunga ai ya kara zama
nata a. hakan kuma sai ta kara samunshi a hannunta
kamar yanda hikimarta tasa ta samu mijinta, to shima
malam Habu da. samun wani yayi ya daura miki aure
da shi ya kaki dakin mijinki da ya fi ye mishi barinki
da
da ya yi ana yi miki wannan wulakancin da
tozartarwar, to bai yi ba bai kuma da mafadi abokiyar
shawararshi daya ce matarshi ita kuma bata taba
shawarta mishi wani abin ariziki ba sai na sharni za
kuma ta ga yanda abin zai juya mata.
Sallama nayi da baba Suimaye na fita na koma
cikin gidanmu na fasa zuwa gidan yaya Dija.
Ina shiga gidan naga baba Lantana tare da Asabe
a zuciyata na tabbatar labarin auren Mubarak da ta ji
ne ya dawo da ita.

58
Baba Lantana sai farin ciki take yi tana
kyalkyalewa da dariya irin wacce ta dade bata yi ba,
ita mace kowacce ai tana da kufu'in aurenta in kana
da hankali kaima ba sai an gaya maka ba ni dama can
nasan wannan yaron mubarak ba zai aureta ba yaro
dan gata irin wannan ya rasa matar da zai aura sai ita,
ai kema kin san ba zai yiwu ba, a yanda yake da irin
arzikin ubanshi da îrin gatan da yake da shi habawa?
Timatiri ne fa sana'ar ubanta kowa ya sani to ko basu
lalace tare ba yaushe zai aureta? Ita ba kyau ba ita ba
gata ba, ita ba dangi ba, ita ba asali ba haka kawai? Ai
idonsu ya rufe ne kawai.a kan sun duniya ba don haka
ba da tuntuni suka gane gaskiya da akayi abin nan da
sai malam ya bi bayan Alhaji Muhammadu Nalami ya
bashi hakuri a daura' aure to baiyi ba saboda shi
agwagwane bin ya'yan shi yakeyi yanda suke so
haka ake yi don haka nunawa ido ne. dama kuma ina
addu'a na kuma san alhakina ne ya fara kamasu, nayi
nufin yi musu abin arziki in rufa mata asiri duk da
cikin da na san tana da shi na hadata da wanda nasan
zai aurcta duk da cikinta don asiri ya rufü itæ da 'yar
uwarta da taimakon ubansu suka watsa min kasa a
ido, to ai mu na nan da su. Ta yi kwafa ta mike ta nufi
dakinta.
Asabe dai ba ta ce mata ba to balle kuma ni can
cikin zuciyata dai mamaki ne ya kamani na yanda ita
da bakinta ta zauna tana bayanin gata irin na Mubarak

59
a yau alhalin kullum abinda ta saba fadi shi ne karyar
banza karyar wofi mu za a kawowa barazana, daga
karyar ziki kawai haka masu kudin suke.
A wannan lokacin sai baba Lantana ta zama bata
da wata hira sai na Mubarak da iyayenshi tayi ta bada
labarin arziki da irin alherin Alhaji Muhammadu a
wurinta a kuma bakinta naji wai ashe sabon gini aka
yiwa Mubarak din a can cikin gidansu banda haka
kuma aka saya mishi sabuwar mota, don ya yi
angwanci a ciki, ai kwarya tabi kwarya in tabi akushi
sai ta fashe, karin maganar da baba Lantana ke wuni
tan ayi kenan a yanzu.
Asabe dai bata shiga harkata ba nima ban shiga
tata ba ta dai dawo gidanmu gaba daya har da kayanta
da na watsar sai dai kuma a yanzu ba abinda yake
gabana kenan ba ina ji da kaina, ina cikin wani irin
tashin hankali da rudanin da ban san yanda zanyi in
fita daga cikinshi ba.
Gaskiya ne duk wani abinda baba Lantana ta fada
akan Mubarak da irin gatan da iyayenshi suka shirya
mishi tunda aka fara bikin ummanshi ke bin gidajen
makwabta da abinci dana sha ko kaje gidan bikin ko
kar kaje za a kawo maka nau'o'in abincin da aka girka
kala kala, ina ganin tamkar a unguwar nan gaba daya
gidanmu ne kawai bata yiwa irin wannan aiken ba.
A ranar da aka kammala bikin kuwa ina kwance
a kan gadona ina jin dirin motocin abokan Mubarak

60

da suka rakoshi wurin babanshr ya şa mishi albarka
kafin su rakashi dakina maryarshi don ance wai tunda
aka yi abin yau ne ranar farko da baban nashi ya yarda
zai ganshi.
A wannan daren bana iya kwatanta komai game
da halin da zuciyata ke ciki, iyaka dai kawai na san
kasancewar Asabe a dakin nan ba ya hanani yin kuka
ba tare ikuma da na damu da ta ni ko bata ji yi kawai
nake yi don in samu in samu saukin ciwon da kirjina
ke yi.
Ban san abinda take ciki ba sai jinta nayi ta ce,
uhun dama kin hakura kim yi shiru tunda taki mas'alar
ma ai mnai sauki ce. Ban kulata ba itama bata sake ce
min komai ba.
A wannan lokacin sai na zama babu abinda nake
sha'awa irin in ga mutane masu yan uwa da dangi a
wasu garuruwan na nesa sai in rinka jn tamkar inama
dai nice da tuni na tattara kayana na koma can inda
suke dan in samu in samu seukin 6acin ran da nake
ciki, wani lokacin kuma nice inama dai dai babana
yayi min irin abidna baba Sumaye ayi sha'awar ace ya
yi min na aurar da ni ga duk wanda ya ga damada
yanzu nima ina can gidan mijina ko ina son shi ko
bana sonshi kuma ai zan zauna darajar shi baban nawa
ne ya bani shi sannan ko bana son nashi kuma ina
ganin ba zan gamu da bacin ran da ya kai wanda nake
fama da shi ba a yanzu.

61
Ana gama bikin Mubarak kuma sai na sake zama
abin nunawa wurin 'yan mata da samarin da dama na
rike musu wuya sai da ya gama da ita sannan yaje ya
auro gal a leda, abinda suke ta fadi kenan ko naji suna
fada suna dariya bana kulasu ko kuma su yista rera
wakokin da makada da mawaka sukayi ta rerawa
Muberak din da iyayenshia wurin bikin, sai da ta kai
ma na sake daina fita waje saboda tsananin dana shiga
cikin zuciyata na rika tambayar kaina sai mace?
Kullun in za a yi maganar ta nashi bangaren da
ya gama da ni din akan furta a yansyin da bai yi kama
da aikata wani iaifi ba sai dai ma kaga tamkar ya yi
wani alin gwaninta ne ko bajinta, a nawa bangaren ne
za a yi ta a yanayi na wulakanta ko tozarta ko kurna
muna ailkata wani abin kunya da wuiakantar, kai da na
lura da kyau da yanayin da ake bayar da labarurrukan
sai na gane shi Mubarak ma sha'awa yake baiwa
mutane ga kuna gatan da iyayenshi suka yi nishi
wanda mutanen unguw8r basu gsiiya da bayar da
iabarin, bisa wanan lurar da nayi da abinda ya
sameni sai nima da kaina na yardanwar kang da
cewar ita mace ita ce mai yin abin kunya in har abin
kunyar ta zo, ita ce kuma mai tozarta in abin tozartar
ya zo, ita ce mai shiga ta wulakanta saboda ita ce mai
rauni komai ya faru a kanta yake karewa, ita ce a
kasa, ita ce take bukatar mutunci da kunya don su

62
zamo sutora a gareta, shi namiji karfi kawai yake
nema.
Dana kara tsunduma cikin tunani sai na tuna da
wasu kalmomi da na taba gani a cikin wani littafi a
hannun Mubarak, ga abin da suka ce: MAN IS BORN
FACE AND EVERY WHERE HE IS IN SHAKKLE"
Da na natsu na dawo cikin haiyacina sai na samu
kaina a yanayi na godiyar Ubangiji da ya taimakeni ya
rufamin asiri ya bana Mubarak karbar kyautar da na
yi mishi, in tuna kaina in tabbatarwa kaina ni din
budurwa ce gal a leda, shi ne abin da yafi komai
sanyaya min zcuiyata a wannan lokacin.
Bikin Mubarak da kwana goma na hangoshi
tsaye a Rfoar gidansu a dalilin fitowar da nayi za ni
shago don sayawa babana ruwan swan din da nake
amfani da shi wajen bashi magani, ban san yanda
akayi ba ina tsaye as hagon nan cikin 6ari saboda
kaduwar da nayi a dalilin hangoshi da na yi wanda shi
ne ganina da shi na farko tun bayan faruwar
abubuwan da suka faru a tsakaninmu.
Motsi na ji a bayana tare da shakar wani irin
sanyayyan kanshin da ya yi sanadin da na yi matukar
tsarguwa da zuciyata ta yi, da sauri na juya don fidda
rai daga zato saboda in samu natsuwa a tare da ni, sai
kawai idanuwanmu suka hadu an yi maza najuya don
karbar abinda nace a bani, jikina sai rawa yake yi har

63
kárkarwa tamkar sanyin hunturu ne yake kadani, cikin
wata irin kwalliya yake ga kamshi gashi in ba kuskure
nayi ba sai naga kamar kiba ya yi, nan tkae na ji
Zuciyata tana gayamin shi bai da damuwa shi dadi
yake ji, shi hankalinshi a kwance baida wata matsala a
tare da shi, da sauri na mika hannu na kar6i ledar
siyayyar tawa da ya yi nufin karba, ban 6ata lokaci
wajeu tsayawa karbar canjin ba nayi maza na bar
wurin.
To tsaya mana Mero jirani mana ai wurinki na
zo. Bai ji kunyar fadin hakan ba a gaban mutanen da
suka cika a shagon, ina jin maganganun na shi na yi
amza na kara maimakon sauri na yanka da gudu nayi
amza na shige cikin gidanmu ba tare da na saurareshi
ba.
Kwana biyu bayan nan na fita gida da sassafe
don sayawa babana kunu da kosan da na saba siya
mishi, ina zaune wurin mai kosan ina jiran ta zubamin
saboda na samu wasu a gabana da yawa sai kawai na
ganshi ya iso wurin, kallo daya nayi mishi nayi maza
na sunkuyar da kaina na.dora hannu akan guiwata
yayin da na zagaye guiwar tawa da hannayena duka
biyu, doguwar farar jallabiya ce a jikinshi duk da ban
tsaya kare mishi kallo ba nasan ta karbeshi.
Ina kwana baba? Ya soma gaida baba mai kosan
tana amsawa, lafiya lau Amadu ya ya su Hajiya da
iyalin naka? Lafiya lau. Ya amsa mata, sakun kosan

64
bai so kan Mero baba nc? Da sauri ta ce mishi ko
baizo ba ai sai a zuba mata Amadu. Nan da nan ta
zuba da yawa fiye kudin da na bata ta kunsa ta
mikomin nasa hannu biyu na karba na dora a kan
murfin kwanon kunun na dauka na kama hanyar zuwa
gida, Mubarak yana biye da ni babu halin in ruga da
gudu in tafi in barshi saboda tsoron kar kunun nawa
ya zube.
Ki tsaya mu yi magana mana Mero. Ban kula shi
ba tafiyata kawai nake yi, ban fa yi miki laifin komai
ba ballekice na za ki yi fushi da ni, ni da ke mun shiga
wani irin al'amari ne a dalilins harrin da matar
babanki ta kulla mana na kuma san ba zai yiwu ta
shanye ta gama lafiya taga yanda take so a rayuwarta
ba tunda ita sharri tasa a gaba, in ma kina da wani
tunani ko kulli game da ni a zuciyakri to ki yi
hakuriki sake kawai duk abinda kika gani kuma ya
zama dole ne kawai ya sa kika ganshi a yanda kika
ganshin, a shirye nake kuma in yi miki bayanin da zai
gamsar da ke.
Ban kalleshi ba balle in tanka mishi har muka zo
kofar gidanmu muna isowa kuwa nayi maza na wuce
cikin zauren gidanmu na barshi a can waje.
Tun daga nan na zama bana fita daga gida kai
tsaye sai na dan tsaya na yi waiwaye waiwaye in
tabbatar ban hangoshi a kusa ba.

65

Rannan ina zaune a dakina ni kadai sai ga
Isiyaku ya shigo yana sallama, na amsa sallamar tare
da bashi izinin shigowa, ya nemi wuri ya zauna muka
shiga gaisawa har da yin hira tun da dama can abokin
hirana ne, na yi ta tunanin abin da zan dan kawo
mishi ya dan taba saboda nuna girmamawa ga
bakonka ban tuna ba don bani da komai a dakin don
haka na hakura muka ci gaba da hirar a haka jimawa
can sai ya ce min, Mero ni zan tafi. Nayi maza na ce
mishi ai na gode maka Isiyaku sai dai ka shigo yau
dakin nawa babu komai a cikisnhi.
Ya yi murmushi tare da fadin, babu komai. Ya
dan karkace kadan sai naga ya zaro wata takarda daga
cikin aljihunshi ya miko min tare da takardun kudin
naira ashirin ashirin cunkus a hannunshi wai gashi in
kawo miki. Nayi maza na zuba musu ido tare da
tambayarshi menene wannan? Cikin natsuwa ya yi
min bayani, wasika ce tare da kudi ya ce in kawo
miki.
A hankali na sake tambayarshi, in ji wa? Ya dan
yi murmushi kadan kafin ya ce min, inji yaya
Mubarak mana wa zai yi mikıi irin wannan aiken in ba
shi ba? Ya baka kudi ba kawo min? Ina yi mishi
tambayar na soma kuka tun katin ya kai ga amsa min
nan da nan ya hidime ya shiga bani hakuri yana yi
min magana, to menene in ya baki kudi an shi Mero?
Yanda duk kika dauki abin fa ba haka yake ba shi

66
yaya Mubarak. Na yi maza na katseshi, dakata na fadi
hakan taré da share hawaycna da bannayena duka
biyu, maida mishi kudinshi tare da wasikar na rokeka
ka gaya mishi yayi hakuri ya fita harkata bana son
kulanin da yake yi bana so bana so, ka gaya mishi na
ce bana so. Zai yi min magana na yi maZa na salke ce
mishi, acte bana so ko kuwa dole ne?
Ya mike ya fita, ya tafi ni kuma na kwanta a nan
wurin naci gaba da kuka cikin tsananin bacin rai da
takaici, wautar kudin ce ta fi komai kona min rai wato
ni kudi ne bukatata, duk abinda akayi min na
wulakarici da tozartawa aiken kudi ya kanmata a yi
min? Na tuna kalmomin da na ji baba Lantana tana
furtawa na rainin arziki ne yasa iyayenshi suka hanshi
aurena saboda sun ga babana ba kowa bane face mai
saida timatiri, zuciyata ta sake rayamin wasu
abubuwan, ya yi aurcnshi ban kulashi ba ban shiga
harkarshi ba yana nema ya rinka shiga nawa bayan an
tabbatar min da cewär har da fita hanyita cikin
sharadin da babanshi ya'sanyå*mishi, ya amsa sanna
ne ya cce ya yafe msihi ya dawo gida; to menene
kuma ya saurä tsakanina da shi? Ban san dalilk bå sai
na samu kaina da bacin rai mai yawa da na-kasa
daurewa zaman gidan ma ya gagareni na nemi izini
wurin babana na shirya na tafi gidan yaya Dija.
Tana ganina da yar jakarta dana zbe yan
zannuwana na canji a ciki ta saki mirhushi, 'haba to

67
ko ke fa? Ai tun ba yau ba nake fama dake ki baro
unguwar nan ki zo nan mu dan kwana biyu tare ki dan
huta, ni hun ban cika son barin baba bane a gidan nan
shi kadai yanzun ma na dan fito ne kawai. Na kwashe
bayanin komai nayi mata ban 6oye mata komiba.
Cikin natsuwa ta kallehi, kin san abin da yafi
bani tausayi a cikin al'amarinki? Na yi maza na ce
mata a'a, sai kawai na ji ta ce min, wai son Mubarak
da kikeyi. Nayi maza na cem ata ni? Ta ce eh ke.
Nace la yaya Dija ni ai ba son shi nake yi ba. Tayi
maza ta ce, ke. matsa can ki bani wuri karki nemi
maidani yarınya karama mana in bakya sonshi meke
sawa ki na yin bacni rai a kanshi, meke saki kuka? Ai
so ne Mero, ya yi miki aike ba yau ko jiýa ya fare ba
ya dade yanayi ba wulakanci bane in yanzu kin daina
karba shi kenan babu 6acin rai a ciki da har za a je
ana ta kuka shawarar da zan baki ita ce ki fidda shi a
cikin ranki fito da miji kawai ki yi aurennki ga
Mansur.
Na yi maza na katseta ta hanyar fadin kai
Mansur? A'a ni yanzu bana son kowa. Ta sake zuba
min ido saboda Mubarak da iyayenshi sun ki mu shi
ne shima Mansur laifin zai shafeni, ai in ban manta ba
a nan ne mukayi maganar nan da ke cewar da Mansur
din da kuma Mbarak rdukansu daya ne wanda duk
maganar aurent a kama za a yi da shi, to ba za ki samu
mas'ala ba za ki zauna lafiya da shi za kuma ki yi

68
mishi biyaiya domin su dukansu biyun masu alheri ne
babu kuma wanda zai iyakacin lokacinki a kanshi.
Nan take nas oma yi mata kuka saboda jin irin
kalaman da ta tsareni da su na baro gide na zo wajenta
don in huta ita kuma ta zo tana yi min wasu
maganganu da suke karawa zuciyata nauyi.
Assalarmu alaikum, wai ana sallama da Mero a
waje. Sau biyu yayi maganar kafin na takarkare na
daka mishi tsawa wanda watakila tsayar da nayi
misHi'ne ya yi dalilin fusatar yaya Dija tayi maza ta
zabura ta mike tsaye ta ce min, maza tashi ki je kiga
waye mai kiran naki ai don Mubarak ya yi aure ba zai
zamo danin karewar maza a duoiya ba, da ke wata
mai zuciya ce ma da tsayawa kikayi kika fidda mijinki
nan da kwata talatin a yi bikinki ki tafi gidan mijinki
kije ki yi zaman aurcnki kowa ya huta.
Na tashi na fito don ba zan iya yin jayaiya da ita
ba.
Mubarak na gani tsaye a kofar gidan tsaye jikin
motar tashi da ga shi har ita sai wani sheki suke yi
suna daukar ido, ga dukkan alamu dai shi Mugbarak
dadinshi kawai yake ji bai da wata mas'ala a tarc da
shi, wanna shi ne abin da yafi komai bata miu rai
wato ni ce mai damuwa, ni ce a cikin bakin ciki, ni ce
rashin zuciya ya hanani samawa kaina zaman lafiya
da kwanciyar hankali, ina ma dai ace nima halina irin
na yaya Dija ne?... saurayi na yi na katse tunanin

69
nawa saboda ganin ya nufoni zai zo in da nake tsaye,
nayi maza najuya zan shiga gida, caraf naji ya kama
gyalen da nake rataye da shi ya rike, abinda ya yi
dalilin tsayawata.
Kina ganin kamar kin tsayawar da za ki yi ki
saurareni yana da wani abin da zai amfanar da ke ne?
Ni da ke ai muna bukatar fuskantar juna ne don
musan abinda muke ciki.
Kaina a sunkuye saboda nauyin shi da nake ji, muryata tana rawa alamar idanuwana suna shirin zubar
da hawaye na ce mishi, sake min gyalena bana so kar
kuma ka sake yi min haka bana so. Da sauri ya sake
min gyalen nawa, ban tsaya sake sauraron komai ba
na yi maza nas hige cikin gida na barshi nan wurin a
tsaye, maimakon in tsaya wurin yaya Dija tunda har
lokacin tana zaune a inda na barta wucewa nayi naje
can cikin dakinta na hau gadonta na kwanta ina kuka,
na kaska gane dalili, na kasa gane al'amarina, na kasa
fahimtar yanda za a yi in zama jarumar kaina in fita
hanyar Mubarak in daina ganinshi ina jin wani abu
ganie da shi, na zafi ko ciwo ko faduwar gaba a cikin
raina.
Ina kwance ina yin kukan yaya Dija ta shigo ta
sameni, nayi zaton wani fadan zata sake yi min sai na
ji ta ce min, ki yi hakuri Maryamu wani loakci zaozi
da ke da kanki za

Please Login or Register in order to submit comment