Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


HALINTRAYTWA3
Hafsat G. Sc
LTTATTAFAN SODANGI

Uwar Miji
Naga ta kaina
Waiyo duniya
Rabon kwado
Cikar alkawari
Mata da kicin dinsu
Duk daya
Shamaki
Hattara


Yiwa wani
Abu naka
Tabbataccen ál'amari
Kyautata
Wacece ai?
Ayi dai nu gani
Wata fuskar

Mata masu duriya
Biyan bukatar rai
Nufin Allah
Mijin ta ce
In kunne ya ji

Halin rayuwa
Gani gareka
Kiff na ganinka
Daga kin gaskiya
Da kamar wuya
Garin banza
Me zanu ce da maza
Masu ftowa nan gaba
Me Daki

Bugun zuciyarmu daya
Mata da kicin dinsu na
biyu (2)
Mai uwa

3

HALIN RAYUWA 3
Kartawa nayi da gudu cikin duhun daren nan na
rinka bi cikin kwararo da lunguna ba tare da ina
jin tsoro ko duhun daren ya dameni ba, ji nake
tamkar gudun da nake yi din gudu ne na ceton rai, ban
tsaya a ko ina ba har sai da na isa kofar gidan su yaya Khadija duk da nisan dake tsakanin unguwannin
namu.
Sau daya kawai na taba kofar gidan nasu na jiwo
muryar yaya Ibrahim yana tambayar wanene? Alama
dai na su ma ba su yi bacci ba.
Ni ce na amsa cikin wata irin murya mai tsananin
rawa saboda barin da jiki na ke yi.
Nan da nan na ji yana kokarin bude kofar, bai
tsaya yi min wata magana ba ya kauce daga hanya ya
bani wuri alamar wai in shiga, sai dai ban iya
motsawa ba sai da ya yi min magana da bakinshi, to
shiga mana maganar ta shi ta zamo tamkar nuni ko
tunatarwa a gareni.
Falon yaya Dija na shiga saboda ganin da nayi
mishi a bude ban ganta an an ba don haka na wuce
can cikin dakinta akan sallayarta na ganta tana salla
yayin da hawaye ke gudu a kan kumatunta, na nemi
wuri na zauna har ta idar ban mtosa ba shima yaya
Ibrahim bai shigo ba wurinshi ya shiga sai da ta shafa
fatiha bayan ta kammala addu'o'inta sannan ta juyo
gareni.

4


Wannan musiba ta kai inda duk ta lkai sai dai duk
da haka ban fidda tsammani ba zata wuce wata rana
har ki ga kina bayar da labarinta, babu abin da ya
kuma jawo mana wannan fitinar irin rasa uwar mu da
mukayi karo na farko da yaya Dija ta fito fili ta fadi
hakan da bakinta tana gama fada kuma ta kama kuka
nima na shiga tayata kukan da take yi.
Yaya Ibrahim ya turo kofa ya shigo, ke Dija
wane irni rashin hankali ne wannan? Yaya zaku hadu
kuna yiwa mutane kuka a cikin wannan tsohon daren,
wai a kanku aka soma ganin irin wadaanan abubuwan
ne balle ku ce naku yayi daban da na kowa? Ina ce ga
ta nan a gabanki in kuma kaddarar ta ce aurenshi kina
da wata hikima ne na hana hakan farIwa ni bana son
rashin hakuri.
Fada sosai yaya Ibrahim ya yi kafin ya juya ya
tafi wurinshi, nima na mike na shiga bandaki nayi
wanka na fito nazo na sanmeta kwance a kan gadonta,
na hau muka kwanta tare kowa ya yi shiru lokaci mai
tsawo har ta kai ma na soma tunanin ita kam ta samu
tayi bacci sai na jiyota tana tambayata, kin yi bacci ne Maryam?
Na ce mata, uh uh. Yaya aka yi kika fito? Ban
6oye mata komai ba na kwashe bayani na duk abinda
ya faru a daren na gaya mata.
Zumbur ta mike ta zauna a tsakiyar gadon kika
bashi kyautar budurcinki fa kika ce? Kan in san amsar

5
da zan bata kan subutar bakin da nayi nayi mata
wannan bayani tuni har ta rufeni da duka duka ukma
ba mai sauki ba, kina nufin saboda Mubarak sai ki
yiwa kanki sanadin tsiya, tana dukan tana kuka, ke
wace irin yarinya ce wane irin so kike yiwa Mubarak?
Tsananin tsoratar da nayi da abinda yaya Dija ta
aikatamin shi ne ya yi dalilin dana shanye duk wata
azaba da ta gana min abinda bai taba faruwa ba a
tsakaninna da ita.
Shi waye da zaki kai mishi budurcinki? Haba
wacce irin fitina ce wannan? Ke wacce irin shashashar
yarinya ce da bata san darajar rayuwarta ba? Bayan ta
hakura ta bar duka da kukan ne take furta irin
wadannan kalmomin abin da tayi min din nc ya yi
dalilin da bai karasa gaya mata sauran abubuwan da
suka faru ba na nemi wuri na makure vwuri daya yayin
da ita kuma ta ci gaba da tsaki tana fadin,
mahaukaciya kawai da kin cuci rayuwarki da kinja
mana bakin ciki da tozarta a cikin jama'a. Har gari ya
waye bata sake kwanciya ba bata kuma daina yi min
fada ba, namiji aka ce miki ana yi mishi irin wannan
kyautar ne? Ai ni ban san haka kike ba.
Washegari da sassafe yaya Tbrahim ya yi shiri
cikin kwalliya ta burgewa gidanmu ya nufa don
halattar daurin aurena da Alhaji Nalami kamar yanda
dama aka shirya ya shigo ya yi mata sallama ya fita.

6
Gabana ya yi mummunan faduwa kamar yanda
na san itama yaya Dija ba ta ji dadin tafiyar tashi ba
sai dai ta shanye 3aboda har yanzu fuskarte a daure
take alamar wai bata daina fushi da ni ba kan maganar
da nayi mata, a zuciyata na ce to da Mubarak ya karbi
wannan kyauta da nayi mishi ko de yaya muka kare
da yaya Dija oho?
Ina tayata aiki ina Rokarin ganin tą wartsake don
mu koma kamar yand amuke, yaya Ibrahim ya gani da
baije wajen daurin auren nan ba cikin matsuwa ta ce
min, ai ba zai yiwu ba sai a yi zaton da wani abu a
Kasa a gane ya san inda kike sannan ko ba don haka
ba ma zai yiwu ace babanmu ya kira shi hidimar
gidanmu bai je ba, ai kuma sai ya zama karnar da raini
a cikin lamarin, nace to kuma baka ne.
Ina zaune a gefen gado cikia natsuwa duk da
hucewar da na ga kamar yaya Dija tayi bai sa ni jin
wani dadi a tare da ni ba, a takure kwarai nake
zuciyata sai harbawa takeyi da sauri sauri saboda
tsananin tsoron da nake ciki.
Tashi ki yi wanka ki gyara jikinki jki karya kafin
ya dawo mu ji abinda suke ciki sai mu ma mu san
menene abin da za yi. Nace mata to.
Muna zaune a falnota bayan mun karya, jikina sai
faman bari yake yi tamkar wacce sanyin hunturu ke
kadawa babu abinda yafi komai kadani irin kallon
agogo da nayi naga karfeara saura minti gonan safe,

7

ahalin daurin auren kuma an ce ne za a yis hi da karfe
bakwai da rabi na safe, to kome yaya Ibrahim din ya
tsaya yi a can oho? Da ya dawo ai da mun san abin da
ake ciki.
Muna nan zaune a wurin muna jiran dawowar
nashi lokaci sai tafiya yake yi, yaya Dija ta gaji tace
ko me ya tsare babansu har yanzu bai dawo ba oho?
Daurin auren da aka ce tun safe za a yi shi har yanzu
ba a dawo ba. Tana yi tana kallon agogo don kara
tabatarwa kanta da lokaci.
Muna cikin hakan sai yaya ibrahim din ya shigo
gaba daya muka tsareshi da idanuwanmu sai dai babu
wanda ya iya buda baki ya ce mishi kala saboda
tsananin tsoratar da muka yi.
Yanayin shi yana nan a tsakani wato baina-baina
ko kuma kadahan-kadahan arn yi daurin auren kenan?
Zuciyata ce ta raya ain hakan Lafiya dai babansu na
ji ka shiru gashi kuuma duk jiinka yayi dabbare-
dabbare bayan sanda ka fita bar daukan ido kayanka
suke yi saboda farin su. a gyara zama akan kujera
bayan ya kwabe babbar rigar tashi da ya tube ya jefa
can gefe.
Lafiya dai babansu? Ta sake yin tarabayar a
yanayi na zuba mishi ido. Wannan al'amari ai yana da
ban mamaki gaba daya muka sake zaro idanuwa muka
Zuba mishi, yayi shiru, me yaf aru baban su? Rashin
hakuri ya sa ta sake yi mishi tambayar.

8
Tun barina gidan nan fa ba wani abu.da na sawa
bakima. Ina jin haka na mnike na nufi kici don kawo
mishi abin karyawa na shigo dauke da tiren abinci a
hannwma na sameshi yana yi amta bayani,
Samarin unguwar ne suka watsa taron mutane da
duwatsu da goruna, sanduna ba a samu damar yin
daurn auren ba.
Da sauri yaya Dija ta sake tambayarshi ba a samu
yin daurin aure ba kace babansu? Cilán natsuwa ya ce
mata, eh ai rikici babba abin ya zama.
Tana jin haka ta fadi a kasa tana sujada alamar
godiya ga ubangiji. Ya bita da kallot ana tasowa ta
shiga furta kalmomi na godiya da shukure baiyane
ta matso gabanshi tana shirya mishi abin karyawa tana
sauraron bayanin da yake yi mata, nima ina gefe ina ji
jiya ashe wai da suka ankara suka gane Maryamu bata
cikin gidan sai sukayi zaton ta sake fita ne ta sake
komawa wajen Mubarak tunda dama a can suka
kamota don haks suka sake yin gaiya guda suka koma
musu bar cikin gidansu har wajen iyayenshi da aka
duba ba a sameta ba maimakon a hakra a yi neman a
wani wuri tun da baban si da kanshi ya fito yayi
mishi magana ya ce bata wurinshi, sai ita babar taku
ta nufi ofishi 'yan sanda ta debo su mota guda tana
fadin wai iyayen nashi ne suka daure mishi gindi yana
lalata 'ya' yan muytane a gidan don haka ba zata yarda
da maganar baban nashi ba, a cikin daren suka kama

9
Mubarak suka tafi da sh1 suka tsare bayan dattawan
unguwa sunyi kokarin shiga tsakani ta ce wai bata
yarda ba aje gaban hukuma kawai don su din dukansu
munafukai ne don haka su kuma samari suka fusata
suka ce ta wulakanta musu iyaye banda haka kuma
dama shi Mubarak mai mmu'amala da su ne don haka
suka ja suka tsaya cewa zasu ga yanda za a yi a yi
daurin auren, sai da suka bari jama'a sun taru har an
sanar da isowar wakilan ango sai kawai suka firfito da
sanduna da gorori suka fadawa jama'a musamman
tawagar angon da jama' arshi wasu kuma daga can
nesa suka yi ta auna mutane suna yi musu ruwan
duwatsu, gava daya suka tarwatsa jama' a, shi dai
angon nan in dai ba karyashi suka yi ba to sun
turgudashi a wani wuri don da kyar muka kwaceshia
hannunsu, sai faman nisa uka yake yi yana neman
taimako.
Assha assha namiji da neman taimako kuma
babansu 1lallai fa da gaske ne abinda ake fadi akanshi
cewar shi din ba namiji bane daudu yake yi.
Yaya Ibrahim ya daure fuska, wane irin zancen
wofi ne wannam daga nace yana ihun kiran maza su
yit aimako kuma sai ki dangantashi da daudu kin san
ma'anar daudu kuwa? Wuya tana da dadi ne? In ka ji
fa kayi ihun kuma taimamko ai ba laifi bane. Tace
haka ne, daidai lokacin da ya mike ya nufi waje don
tafiya wajen harkokinshi.

10
Daga ni har yaya Dija babu wanda ya iya cewa
wani komai bayan fitar tashi kallon juna kawai muka
yi cikin wani irin yanayi da ba zan iya kwatantawa ba,
da kyar na iya bude bakina na ce mata wato dai duk
wani al'amari yaya Dija na ubangiji ne. Tayi maza ta
ce ai shi ne madogara ta dindindin in har ka dögara da
shi din kuma to baka tabewa.
Duk da wannan labari mai dadi da yaya Ibrahim
ya zo.da shi saukin damuwa kawai muka samu amma
ba wai mun fita daga cikinta bane muna te addu'a tare
da sauraron abinda zai biyo bayan abinda aka yi.
Ina nan zaune a gidan yaya Dija har adadin
kwanaki hudu jinin jikina har ya fara dawowa na
soma farfadowa daga mummunar gigitar danayi sai ga
YakumboHalima ta zo gidan don dama ta san ina nan
saboda aiken da yaya Dija tayi na a gaya mata saboda
ta samu kwanciyar hankali.
Muna zaune g abanta muna hira bayan ta gama
ian abincin da na kawo mata tana kara bamù albarin
abubuwan da suka faru ko ince suke faruwa sai naji ta
ce, shi kam malam Habu ai ya shiga mas'ala koma
ince ya shiga uku ina amfanin ace namiji baida
katabus komai sai yanda akayi da shi.
Da sauri yaya Dija ta ce Yakumbo bafa haka
kawai bane da abinda tayi mishi. Ke matsa can ni ki
bani wuri a kanshi aka fara yiwa maza asiri? Ai shi
asiri da kike gani bance miki babu shi ba amma mafi

11
yawancin lokaci hali yake tararwa, yauwa shima
kuma gashi nan ya gamu da hashi gamon don dazu da
safen nan nake jin albarin wai ya yanke jiki ya fadi
cikin kwandunan tunatiri a kasuwarsu sai da aka
ciccibo shi rangatanga aka kawo shi gida.
Ni da yaya Dija salati mai kafi muka kama yi
yayin da it akuma ta ci gaba da fadni, uhun menene
wannan in ba bakin ciki da damuwa ba da yake nema
ya haddasa mishi ciwon nan na zamani da ake fama
da shi na hawan jini.
Ni da yaya Dija bamu iya daukar abinda ya.samu
babanmu a yanda Yakumbo Halima ta dauke shi ba
wato a'inda babanmu ya shuka ne yake girba tausayin
shi ne ya kamamu nan take muka soma yin kuka
muna fadin, ba laifinshi ba ne Yakumbo ba laifinshi
bane kune kawai baku san abinda muguwar matar nan
take yiva baba ba na asirce-asirce da sihiri iri-iri.
Yaicumbo ta mike tsaye nuna alamar tafiya tana
fadin, to ai shi kenan ku kuka san abin yi tunda
ubanku ne ni kam ni nazo na gaya muku sai kusan
abinda kuke ciki.
Yaya Dija ta kawo kudin mota ta bata. Tana
barin gidan ta kalleni, daga irin wannan faduwar ne fa
ake rasa wani bangaren na jiki, ni yasu baba Lantana
ta ciccire mu a rayuwa in kuma.muka barta ta zama
sanadin nakasar ubanmu muna kallo to ta gama damu
don wa muke da shi kuma bayan shi din? A hankali

12
nace mata babu musamman ma da yake kullum a
cikin alkawarin neman, mana dangin ubanmu kike sai
dai har yanzu shiru. A fusace ta juyo gareni kefa ba
wani hankali ne da ke ba bakya ganin kullum a cikin
mas'aloli muke bamu fita wannan ba mu sake fadawa
wancan? Bain sake yin wata magana ba bayan fadin
haka ne da nayi.
Nan da nan muka shirya tafiya gida bayan ta tura
an gayawa mijinta halin da babanmu ke ciki, a hanya
sai kallonmu ake yi ana zunde ana nunamu tamkar dai
ba a sanmu ba, wai dan rikicin da akayi a gidan nan
ne ta ya sa mutane suke yi mana irin wannan kallon,
nace mata eh tace to ai sai su yi tayi su ne abin fada
baya yi musu kadan nace haka ne.
Muna shiga gida baba Lantana ta soma sakin
magangaiiu'ai dama da kika gudu can wajenta kika
tafi ta 6oye lki to ai zancen bai kare ba in ma kuma yi
kukayid on ku kunyatani in tozarta gaban mutane to
ba ni kuka yiwa ba ubanku kuka yiwa shi kuka
kunyata kuka tozarta kuka nunawa jama'a cewa shi
din ba komai bane a wurinku bai kuma isa da ku ba
ko ba komai kuma ni kam ai gani nan a zaune daram
lafiyata kalau shi ne bakni cikinku yake sashi yanaa
tintsirewa a cikin jama'a yana faduwa, in kuka yi
sanadinshi bukatarku zata biya tunda dama fatanku
kenan gashi can a kwance magashiyan ai cikin yardar
ubangiji bakin cikin ku ne zai yi sanadinshi.

13
Wani irin mummunan faduwar gaba na samu
abinda na tabbatar kuma shi ne itama yaya Dija
abinda ta ji kenan saboda zaburar da naga tayi ta nuf
dakin da yake kwance.
Ku daiyi a hankali kar ku takamin leda da
kafafuwanku masu datti don yanzu na gama gogeta
babu kuma komai na uwarku a ciki balle ace za a
shiga min da gadata.
Halin da babanmu yake ciki yafi gaban bayani
numfashi yake yi sama sama ga kuma karin ruwa ana
yi mishi. abinda muka tabbatar shi ne wadanda suka
dawo da shi ne sukazo da wanda ya dan dubashi da
gani har yaya-Dija kuka muke yi saboda bamu taba
ganinshi cikin halin rashin lafiya irin wannan ba.
Ai ba ku yi kuka ba tukunna sai randa kukayi
mishi farat daya ko kukayi mishi sanadin hannu da
kafa ranar ne zaku gane kunyi kuskure, ai kun san ni
dai ba-zan yi zaman jinya ba ko balle inje ina hidima
da dawaniyar najasa.
Yaya Dija ta mike tsaye ta kalleta rike da labulen
dakin nata-da tayi tace mata, matan arziki ai su ne
masu hidima da jinyar mazajensu don neman albarka
da rahamar ubangiji ai ke ubangiji ba zai yi miki
wannan alherin ba ba zai jarrabi wani da jinyar da za
ki yi hidimarshi ba balle ki samu wannan alherin.
Yaya Ibráhim ya shigo ya samesu nan take ya
soma yiwa yaya Dija fada, ke da kika zo kika samu

14
wannan al'amarin kumą mre ya kaiki tanka wata
magana. Ya juya ya fita bayan ya bamu umarnin
kintsa baban namu don tafiya asibiti.
Muna kokarin kintsa shin baba Lantana bata fasa
magana ba ba, ba dai ke ce mai daure mata gindi ba?
Yarinyar da ta san taje kwanan gida gidan saurayi an
kamata tana yin hakan yafi a kirga anyi nufin aurar da
ita don neman mata rufin asiri kin sata ta gudu taje
wajenki kin 6oye ta? To da albarkar masu albarka sai
ta durkusa a tsakiyar dakinku ta haifar muku dan
shege kuma kun goyashi a bayanku ke da ubanku da
yake biye muku, babu wanda ya sake tanka mata.
Gwajin farko a asibiti likita ya bayar da tabbacin
hawan jini ne ya yi mishi yawa yake nema ya taba
mai zuciya kan haka ya bashi gado aka kwantar da shi
a dakin masu cutar hawan jini.
Yaya Dija da mijinta suka koma gida ni kuma na
zauna tare da shi, ban san yanda akayi ba cikin dare
sai ga Sallau ya zo, sannu Mero. Na ce mishi yauwa
ba tare da na daga kai na kalleshi ba, yaya mai jikin?
Nace da sauki. Ya ja ya tsaya yana kallon baba nima
na ci gaba da al'amurana, na ce ko zan karbe ki ne
kije gida ki huta in kwana tare da shi in yaso da sate
sai ki zo ki karbeshi? Lokacin ne na san na dago na
kalli Sallau da nufin tanbayarshi shi kuma a waye
dinshi da za mu yi irin wannan canjin ji da shi?
Yanayin da na gani a tare da shi ne ya hanani yin

15
hakan cikin natsuwa sai na ce msihi a'a Sallau jeka
gida kawai abinka na gode. Bai tafin ba sai ya tsaya
muka kwana tare a asibitin, yanda kuma banyi abcci
ba haka shima bai yi ba.
Da sassafe yaya Ibrahim ya zo duba mu ya kuma
kawo mana abin karyawa da zai tafi ya kawo kudi ya
ba ni ya ce in rike a hannuna ko za a nemi wani abu,
nace mishi to tare da godiya. Yaya Dija bata zo ba sai
da ta kammala abincin ranar gidanta ta zo mana da shi
hakan Yakubo Halima ta kawo mana tuwon dare.
Mutanen unguwarmu makwabta, abokan zaman
baba na kasuwa suka yi ta zirga-zirgar zuwa don
dubashi duk wanda yazo kuma zai kawo wani dan
alheri ya bayar sai dai kalamand a suke fürtawa ne
basa yi min dadin ji kai rashin van uwa kow ani
tsayayye bai da dadi in banda haka yaushe za a ce
yarinyar da ta ja maka irin wannan tozartar tayi maka
sanadin wannan mumnunan ciwon ita ce kuma mai
yin jinyarka to yaushe ma kuma zaka warke?
Hankalina tashi yake yi a duk lokacin da na ji suna
fadin hakan in kasa fahimtar abinda na yi na tozarta
babana, kamo ni da aka yi a gidan su Mubarak ne
tozartawar da suke magana a kai ko kuwa watsa taron
masu daurin auren da yara suka yi? To ko ma dai
menene sai nake ganin tamkar in har da adalci cikin
almarin ba laifi ne da ya dace a daukeshi a doramin ni
kadai a kaina ba.

16

Tunda baba Lantana ta gane irin zirga-zirgar da
mutane suke yi wajen zuwa asibiin sai itama ta soma
zuwa kulum ta kan zo ne da tabarmarta ta shimfida a
hanyar da ta san itace tas higowar mutane tana ganin
an zo sai ta tari masu zuwan tayi musu jagora zuwa
inda babana ke kwance in suka gaisheshi suka ba da
abin da zasu bayar tayi amza ia karbe ta saka a cikin
yar fos dinta ta koma kan tabarmarta ta zauna ba
kuma zata sake tasowa ba sai wasu bakin sun zo daga
ni har yaya Dija babu wanda ya daga ido ya kalleta
balle ya ce mata kanzil.
Kwana tara baba ya yi kafin aka sallameshi a
hakan ma matsawar shi ce ta sa aka yi ta saboda
yawan maganar da yake yi bai son zaman asibiti bai
taba zuwa asibiti don kanshi ba sai dai don ya zo duba
mara lafiya, yaya Ibrahim ne ya yi duk wata
dawainiya har da biyan kudin sallamar muka dawo
gida.
Likita ya sallame mu ne bisa dokoki na a kiyaye.
bacin ranshi a kula da abincinshi banda gishiri banda
barkono banda farin magaji banda kanwa banda
yawan cin man gyada.
Tun likita yana bayanin baba Lantana ta somna
fadin, hu un wannan banda bandan ai ya yi yawa.
Yaya Dija ta kalleni cikin natsuwa bayan munje
gidamnu da baba tace min debi kayan da zaki diba mu
tafi nace mata a'a je ki kawai ni zan zauna a gida, da

17

sauri ta sake källona za ki zauna fa kika ce? Nace e,
amma ai kuma kin san gidan ba zai zaunu miki ba a
yanzu a yanda take fusacen nan ina nan ma kina jin
irin maganganun da take furtawa balle kuma ace na
tafi na barki ke kadai.
A hankali na daga ido na kalleta kafin na
tambayeta, to in muka tafi dukanmu muka bar baba a
yanda yake din nan wa zai yi mana jinyarshi? Wa zai
bashi magani? Wa zai kula da abincinshi balle ya
tsaya yaga an tsare dokokin da aka sa mishi? Tace to
kuma haka ne ta bude jakarta ta fito da kudi ta bani
tare da fadin, to rike wannan a hannunki kafin inje
gida in ga abinda zan iya hadawa nace mata to.
Na koma zaman gida tare da baba Lantana da
ya'yanta biyu ga kuma babana a kwance yana jinya
tunda ko fita runfarshi baya iyawa balea yi maganar
kasuwarsu, dan garama dai Sallau don shi kam yayi
mana mutunci kwanakin asibitin baba duka tare da shi
muke kwana.
Duk lokacin da na zo shiga dakin baba Lantana
don yiwa babana wani abu ko bashi magani sai tace
wai bata yarda ba ina shiga ne ina ganar mata sirrinta
shi ba zai sha da kanshi ba sai an bashi kamar wani
dan yaro? An wani tasashi a gaba ana shagwabashi ita bata son gulma da iya yi.

18
Babana kuwa shan maganin yake yi a kan dole
sai na yi ta rarrashi ina bashi hakuri kafin ya yarda ya
sha.
Ganin da nayi takurar ta kai inda ta kai ya sa na
shiga dakin da Sallau ke ciki yana kwance kan
katifarshi na ce mishi, Sallau kawar da katifarka ka
.koma can gefe zan yiwa baba shinfida anan don a
samu saukin mu'anala, cikin sauri ya ce min to, nan
da nan kuma ya mike ya soma yin abinda nace mishin
har ya tayani na shiga dakina na dauko katifar da nake
kwanciya a kai nad awo mishi da ita nan na shinfida
mishi ita naje na samu babana na ce mishi tashi baba
mu koma dakin Sallau don zai

Please Login or Register in order to submit comment