Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin suna naima su suburbude sa, shiyasa ya biyosu salin alin, tunda suka shigo gidan yake kalle kalle, duk da yana zuwa gidan manyan mutane, da kuma manyan yan siyasa, bai taba ganin gida da ya amsa sunansa gida ba irin wannan, duk da shima gidansa ba baya ba wajan haduwa, amma wannan ya kerewa nasa, talle masa keya akayi, "kallo aka kawo ka kayi, dalla shige mu shiga" har cikin falon suka shigar dashi, sannan daya daga cikin su ya daga waya ya kira shugaban nasu, wato MK Muhammad Kabeer, ai nan mutumin ya sake baza ido wajan kallon haduwar falon, ashai a waje baiga komi ba, kamshin turaransa ne ya fara sanar musu da zuwansa, cikin izzi da takama yake taka matakalar benan kamar bayason taka kasa, hannunsa rike da mug din coffe, dukkan su mikewa tsaye sukayi a ɗai ɗai lokacin da yake karasowa cikin falon, zama yayi yana dora kafa daya kan daya, cikin natsuwa da tarin kamala ya fara magana, "kasan abinda yasa nasa aka kawo ka nan" girgiza kai mutumin yayi, jiyai an talle masa kai ta baya, "ka bude baki kayi magana","aa Yallabai","ka kira ni da Muhammad Kabir" cikin mamaki mutumin yake kallonsa wai yau shine a gaban mutumin da dubbanin al'umma suke son haduwa dashi, duk da haduwar bata dadi bace ba, "inaso ka mayarwa marayun nan gidan su daka kwace musu","bazan iya mayar mus... ai kafin ya karasa maganar yaji an rufesa da duka, saida sukayi masa lilis, daga masu hannu MK yayi lokaci daya suka tsaya da dukansa, "yanzo zaka mayar musu ko kuwa?","wllhi tallahi zan mayar.











Shere fisabilillah.
✨✨ ZAINABU ABU ✨✨

Na

ZAINAB A BARDE



ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITER'S ASSOCIATION
(A.Y.T.W.A)



Page 19 nd 20



*LITTAFIN ZAINABU ABU NA KUDI NE, AKAN FARASHI MAI SAUƘI #200 KACAL, ZAKU TURA KUDIN TA WANNAN ACCT DIN, 0599919281 ZAINAB ADAMU, GT BANK, SAIKU TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER, 07048614405, FREE PAGE SUN KUSA KAREWA, SAIKU HANZAR TA KAR AYI BABU KU*



****

*End of free page*


"That's the best for you, bana barin zalinci ni MK, ku mayar dashi inda kuka dauko sa and make sure ya mayar wa da marayun nan gidan su","an gama Sir","you can leave" tusa kiyarsa sukayi suka fitar dashi daga falon, ajiyar zuciya Muhammad Kabir ya sauke, yana mamakin zalincin wasu mutanan, son zuciya ya musu yawa, kwata kwata basu da tausayi, taya duniya zataci gaba, ana zaluntar mararsa karfi, "daga yau zan daura damara da duk wani mai cinye dukiyar marayu, ko cin hakin wani insha Allah" ya fada a fili zuciyar sa na tafarfasa.




Haka su Asfah suka shirya suka wuce islamiya, zuciyar Asmah cike da jin haushin Asfah, amma ko kadan Asfah batama san tanayi ba, harkar gabanta kawai takeyi, a haka dai sukaje suka dawo no one talk to the other kowa bangaran mahaifiyar sa ya nufa, koda Asmah ta shiga falon tararwa tayi Mami batanan da yake itace keda girki yau, tana wajan Abee, dakinta ta shiga ta fara safa da marwa, ta wacce hanya zata bullowa lamarin nan, itafa gaskiya Asfah tana shigar mata hanci da kudun dune, "ina bazai yuba dole ne in samowa kaina mafita", Are you alright kuwa kike ta magana ke kadai?","Mami wllhi na rasa yadda zanyi da yarinyar nan","wace yarinya?","Asfah mana wllhi Mami I over hate her,"na gaya miki karki wani damu ki barni dasu, I all know what to do, wani killer smile Asmah tayi, with lots of happiness in her mind" it's okay mom let me have some rest","have your time daughter kiyi komi ba komi bane" tanaji fa ana kiraye kirayan sallar magariba, amma haka ta kwanta a kan gadonta, babu ma batun salla a lamarinta talk less of removing uniform, haka Mami ta fice taja mata kofa,



Part din Ammi ta nufa, tana zuwa ta tarar suna salla, zama tayi har suka idar, "My daughter ya school din" murmushi Asfah tayi, "school Alhamdulillah,soon xamu ma fara exam","to Allah ya taimaka, ya bada sa'a" da ameen ta amsa, "Yayan naki bai dawo bane?" Ammi ce ta karbi zanchan ta hanyar fadin, "wllhi kuwa, yau kam bai dawo da wuri ba, gashi har anyi magariba, inata kiran wayarsa amma bai dauka ba" kafin Mami tayi magana suka jiyo sallamar sa, "dan halak kaƙi an bato, yanzon nan muke maganar ka" murmushin sa mai kyau ya saki, cikin tattausan lafazi ya fara magana, "Mami barka da gida, na same ku lfy" ya fada yana zama kusa da ita, gaishe da Ammi yayi, cikin fara'a ta amsa, where have you been baka dawo gida ba da wuri?" Ammi lots of works Na samu a office saida na kammala sannan na tashi"," to Allah yayi jagora" cewar Mami tana binsa da wani mayataccan kallo, "Asfah yau babu magana" ya fada cike da so da kaunar kanwar tasa, "laa Yaya ina jira ne ku gama maganar taku","to ai mun gama, zo muje kiga abinda na siyo maku keda Asmah","to yaya ni wllhi tun banga abin bama na fara farin ciki","come with me and see, fita yayi daga falon, itama tabi bayansa da gudu, da mugun kallo Mami ta bisu tana ayyana abubuwa da dama a cikin ranta, "wllhi yaran nan suna birge ni, yadda suke son junansu, kinga ko bayan ranmu zai kula da ƙannan sa yadda ya kamata" firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data lula, ai Muhammad kareem yaro ne mai hankali da sanin ya kamata, ai yaro ne mai sharewa iyayansa hawaye" ta fada tana murmushin yaƙe, Allah ya raya manasu gaba daya" Ammi ta fada, ni bari naje wajan Abban Kareem ko yana da bukatar wani abu","to shknn saida safe" daga haka Mami ta fita daga falon zuciyar ta fal baƙin cikin ganin su da tayi cikin farin ciki.



Suna shiga daki yace ta jirasa a falonsa, zama tayi a kan kujerar shi kuma ya shiga bedroom dinsa, babu jimawa ya fito hannusa rike da manyan ledoji guda biyu, mika mata yayi, hannu biyu tasa ta karba, bude ledar tayi, kayan kwalan da makulashe ne, su chocolate dasu ice cream dasu biscuit, da dai sauran su, "ki dauki laida daya ki bawa Asmah daya","thank you so much Yaya Allah ya kara budi mai albarka","Ameen ya Allah kanwata, good night" tashi tayi ta fita, da kallo ya bita cike da so da ƙauna, zama yayi akan kujera yana shan ice cream din shima, part din Mami ta nufa, bataga Asmah ba, shiyasa ta bawa Mami kayan, godiya sosai Mami tayi, fitowa Asfah tayi ta nufi bangaran su, Mami na ganin fitar ta, ta chillar da ledar "aikin banza !




"Gaskiya Anna ni yau bazanci wainar nan ba, kullum waina nide yau ki bani naje na siyo biredi","to jikata amshi kudin nan kije ki siyo" cikin farin ciki Zainabu ta karbi kudin ta ruga a guje kamar wata karamar yarinya, girgiza kai Anna tayi, zuwa tayi ta siyo biredin, akan hanyarta ta dawowa ne, ta kalli gabas da yamma koda taga bbu kowa saita dage ta banka tusa mai karar siya, nunfashi ta sauke, "haba ai gara na fitar da ita ko naji dadi, innayi ta a hankali banajin dadi" ihu ta jiyo daga bayanta, juyawa tayi dan taga waye, Hakilu ne dan gidan mai gari, yaron da bazai wuce shaikara goma shabiyu ba a duniya, waka ya farayi yana rawa, Zainabu Abu mai tusa butt butt buttt, haka ya cigaba dayin wakar, nan fa yara suka taru a wajan suna kallo, shiko sai wakarsa yakeyi yana jujjuyawa, ranta a matukar bace take kallon yaron, abin bakin cikin ma yaran da suka taru a wajan, gashi yaƙi daina yin wakar, aiko cikin fishi ta fisgo yaron, ta fara dukansa ta ko ina, birgima yaron ya farayi yana kuka, ruwan cikin sa ta haye ta cigaba da dukansa, kansa ta fara dokawa da kasa tana dukan cikin sa, "yau saina koya maka hankali, harni Zainabu zakana tsokana, karka damu zakaci ubanka ne" ta fada tana cigaba da dukan yaron, ihu yaran wajan suka fara ganin kan Hakilu yana jini gashi ko motsi bayayi amma Zainabu bata daina dukansa ba, ganin yaran na guduwa yasata kallon gudun mai sukeyi, gani tayi kan hakilu yana jini gashi ko motsi bayayi, da sauri ta dagasa ta fella gida a guje cikin tashin hankali, tana zuwa ta kankame Anna tana komawa bayanta, "yau kuma wa kika tsokano?" cikin fisgo numfashi tace "Anna na kashe shi" dam haka Anna ta dafe kirji, "wa kika kashe yau mun shiga uku","Hakilu ne dan gidan mai gari" salati Anna tasa, "shknn yau kinja mana tashin hankali a garin nan.





*Shin wanene Muhammad Kareem, shin ko ana barinsa ya auri wadda yakeso*

*Menene alakar Abee da Abban Shahida, wace irin gaba ce a tsakanin su, mai ya hadasu haka da har Abban Shahida yake cewa gara ta mutu akan ta auri dan makiyin sa Muhammad kareem*


*wanene Muhammad Kabeer, wana irin taimako yakewa al'umma da suke matukar son sa da kaunar sa, kamar wani shugaban kasa*



*Shin ko shahida tana samun lafiya, ko tana auran masoyin ta, ko Abbanta zai hakura*



*Shin wanene BOSS*



*Shin wana mataki mai gari zai dauka akan Zainabu da ta kashe masa dansa, yau dai Zainabu an shiga tashin hankali*




*Shin wana irin makirci Mami da yarta Asmah suke kullawa*



*Ku biyo ni a cikin littafin Zainabu Abu, danjin amsar wadannan tambayoyi, karku manta yanzo fa wasan ya fara, nuce taku har kullum, Zainab A Barde*










Shere fisabilillah.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment