Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bance zanyi kuka ba saike ko?" Ya faWa da watsomin idanu.. nace to kayi ha™uri karkai fishi ka ji...?" "ya za ai nai fishi da Gimbiya?" nai dariya da rufe fuskata, "ya kika baro mutan gidan? Kin dawo lfy ina tsarabata?" nace "duk suna lpy ana gaishe ka ma" (Sir Ahmad saurayina ne kuma Malamina na boko da islamiyya mun daWe da shi tun ina SS1 shekara biyu kenan kan ta uku muke tare da shi yana sona sosai haka nima ga ha™uri da kawaici zan iya cewa ni tunda nake ban taSa ganin mutum me ha™uri irinna Sir Ahmad Wina ba duk da nima ana faWa ina da shi dan nima ha da ganan ba da gada wajan Amma, to duk nawa a ganina ban kama ™afarsa ba ko kaWan ga shi mutum ne me alheri da son jamaa kowwa nasa ne yanada faran-faran da mutane kam an yabeshi duk abun mutum bazece ga aibun Sir Ahmad ba.
Dogo ne sosai ba shida jiki fari ne sosai saSanin ni da nake ba™a baza a sakashi sahun munana ha dan ko baya daga cikinsu yana da kyansa dai-dai gwargwado.
Ba me kuWi bane Amma yana da rufin asiri daidai malamin mu ne a secondary yana Waukarmu English sannan again yana koyarwa a islamiyya shiyasa kowwa ya ganshi mlm Ahmad shi kaWai ne wajan iyayensa haka ma mamansa na sona tunda taga tilon Wanta na qaunata dan har iyaye maza ma sun shiga maganar ana jirana na ™arasa makaranta amma ni a raayina ina son ci gaba da karatu gsky Kuma ya ce Zai barni in naje gidansa).
Ya ce "ya yi ranar Monday zaa fara exam ko?" na ce "eh,"
"Kinyi karatu ince ko?" na ce "eh" "to Allah ya sa a fara a saa" na ce "Ameen dan Allah nasan an kawo question paper ka bani wadda zaa fara" ya ce "aa Ai ba haka ake ba hajiyata" nai dariya "ummm nima da wasa nake..."
Haka muka sha hirarmu ta gari da ta soyayya kafin ya tafi na shiga gida har sun kwanta ma na shige Waki na canza kaya da yin Alwala kwanta.
&&& &&& &&&
&&& &&& &&&
Ranar Monday da wuri na gama ayyukana na shirya saboda karfe 8:00 zamu shiga jarrabawa. na kammala komai na shirya na fito Baa na gani shima yau da wuri ze fita na gaishe shi nace "Baa ka rage min hanya" ya ce "to bara na fiddo mashin Win," Wakin Amma na shiga gaisheta ta amsa da min ADDU'A samun nasara na amsa da Ameen don inajin daWin aduar da takemin a raina.
Har bakin gate ya kaini ya aje kafin ya juya. na ™arasa shiga da hanzari don naga takwas Winma saura mintina kaWan, direct ajin mu na nufa na tarar anata bada sit number aka bani tawa ni ce 36 can kusa da Window naje na zauna aka fara Announcement duk Wanda yasan da jaka ajikinsa ko waya ya fito da ita.
na de fita da ledan da Nazo da ita da nazuba pen da biro da cul, don ni ko wayan ma banada ita, kowwa ya pita da nasa kafin mu zauna zaman jira. Examiners da Supervisors da Invigilators ne suka shigo don haka kowwa ya nutsu aka raba answer sheet, kafin a raba question paper. NATIONAL BOARD FOR ARABIC AND ISLAMIC STUDIES. wato (NBAIS) na fara karantawa a hankali tun daga farko har qarshe kafin kafin na sauke numfashi a hankali. ADAB da ita muka fara na janyo answer sheet na fara rubuta sunana da Admition number da sauran abubuwan da aka bu™ata... Ina cikin rubutu na ji Invigilator yana bayani da Larabci wanda be gane ba yai tambaya.
Kowwa ya du™a ana fama da biro da takarda ajin yayi tsit! ba abinda ka ke ji kowwa ya du™ufa sai goma muka fito dama 2hrs ce. nanfa aka zauna ana maida yadda akai. Muna zaune nida hamida qawata aka aiko wata yarinya Sir Ahmad na kirana a staff room na ce "to," Hamida zata fara min tsiya nace "kina cewa tak! se na faWa" tai shuru dan ta san zan iya na wuce ina mata dariya.
Wasu Qpaper ma ya bani na English zan tafi da su gida.
12:00 dai-dai muka shiga next paper ita kuma se 2:00 lokacin tashi gaba Waya.
A matu™ar gajiye na koma gida Amma na min sannu da zuwa na amsa da cire uniform ina shiga banWaki. Wanka nai da Wauro Alwala nai sallah azahar kafin na ci Abinci ina bama Amma labarin jarabawa tace lallaikam Allah ya bada saa na amsa da Ameen.

Washe gari se sha Waya na fita don ta Rana ce da mu kuma paper Waya ina zuwa anata shirye shiryen shiga nima na shiga na zauna a sit number na muka fara. biyu muka pito. Gidansu Hamida zani zan amsa sa™o tare muka tafi da ita.
Haka mukai ta fama da exam Winnan ga satin farko kwata kwata ba interval wani lokacin ma uku zami a Rana tun takwas se shida na yamma aikam Har na fige dama ni ba jikin kirki ba. Satin yana fita muka samu intervel kusan kwana goma aikam mun huta. Washe gari ranar Alhamis yakama muna da guda2 ta farko Home management practical ce, amma ba'a Sami damar yi ba wai saboda lokaci sai theory mu kai a rubuce da yamma muna da English karfe 4:00 ina bitan Qpapers en da Sir ya bani. ana Kiran la'asar muka shiga masjeed don yin laasar.
Itama shida muka fito kowwa ya nufi gida. haka muka ci gaba da zana jarrabawar cike da nasarori. tunda muka fara exam sir Ahmad be zo ba wai kar ya Wauke min hankali ya hana ni karatu, aikam na dage sosai dan ganin na ba mara Wa kunya, domin ba laifi ina da ™o™ari gsky bani da da™i™anta ko don gida ana zafafamin akan karatun,? Gefe Waya kuma ga Sir Ahmad yana dagewa a kaina,, yo ko be dage ba ai nayi don da kunya a gabanshi ace banda ™o™ari abin Kam baze daWi ba. 22/July Yau kenan ya kama zami last paper Qur'an and Tafseer ta rana ce bayan mun kammala aka haWu Malamai da Šalibai da Copper's da ´an TP ana hotuna na tarihi muna ta ban kwana ranar candy kowwa yazo da abinshi da yayi wasu sticker wasu calendar wasu memo abubuwa dai kala kala aka rarraba ni memo ne da key holder wanda Sir Ahmad ya min be min sticker ba wai baza a dinga masa yawo da hoton mata ba nace "lallaikam." Mungama abubuwan mu kafin a rabu da exchange number nikam a paper nai copy dan banada waya Baa ya ce "in mun yi candy za'a semin.
Na dawo gida kusan la'asar na zubewa Amma abubuwan da na samo tana ta gani da sa Albarka. Baa ya dawo da daddare nake nunnuna masa Abubuwan da nasamu, ya ce "to mamana ina tayaki murna Allah yai wa rayuwa Albarka" na ce "Ameen ga islamiyya kuma anata Shirin sauka ko?" na ce "eh," amma ba'a tsayar ba a August Win nan dai za'a tsayar "oh watan jibi ma kenan?" na ce "eh" ya ce "Allah ya kaimu."
Washe gari Sir Ya zo gidan mu da safe se ga shi nace "to lpy da safen nan?" Amma ta ce "le™a ki ji" na zura hijab na fice, tsaye na taddashi jikin mashin Winsa ya harWe hannunsa a ™irji yana kallon ™ofar gidan namu.. ™arasawa nai da sallama na Wan rissina ina gaisheshi ya amsa da murmushi ´an matan candy nai dariya "uhmm wlh kam Sir dan yanzu mun girma."wai Baby bazaki dena cemin Sir ba ko?" Na balalo ido.. "me zance to wanda yafi wannan?" "My love.." rufe baki da fuska nai da tafin hannuna.. (dan kam zancen ya Wan min nauyi) ya zubo min cike da shaawa yake kallona ya son wannan kunyar tawa tana birgeshi.. ya ce "kinsan Allah kina shiga gidana wannan kunyar sai na sauke miki ita tas..." Kallonsa nai da cuno Wan bakina "sannan na tsotse wannan bakin da ake cunomin tas..." ji nai tamkar na nitse don kunya, "Oh bazaki min magana ba kenan?" na shagwaSe fuska da dira ™afafu, "dan Allah Sir ka bari.." hmmm yau kina so ki rikitani bara na tafi kafin kisa yanzu na c..... ´ar ™ara nai da rufa ba ki na "dan Allah kar ka faWa..." dariya yai yana hawa kan mashin Win da mi™omin kwali na sa hannu 2 na amsa "na meye?" ya ce "wayarki ce tunda Baa ya ce sai anyi candy cikin tsananin murna na kalleshi... "Sir dgsk?" ya ce "iyyi cewa nai bazan faWa miki ba suprize zan miki, da akwai sim card a ciki sai ki kunna anjima zan Kira" kissing wayar nai cike da jin daWi "uhmmm ban ma san kalan godiyan da zan maka ba Sir.." ya ce "adana ba yanzu ba" na ce "yaushe?" ya ce "se ranar da kika zo gidana zan faWamiki kalar godiyar da nake so." "Uhm uhm.. dan Allah ka Bari." "dariya yai yana tayarda mashin Win "na bari Oya maza je gida se munyi waya" na ce "to" na juya cike da Woki.. jan mashin Win yai yana Wan murmushi da ™issima abu a ranshi.
Amma na ke nunawa wayar ina kiciniyar buWe ta a kwali TECNO ce Android me kyau da cover Win ta me zanen love a jiki Amma ta ri™e baki.. "yanzu shi haka ya dan™aro wannan uwar waya haka?" na ce "umm.." ta ce "to ajiyeta se Baa ya dawo a nuna masa aji me zai ce,ko ya?" na ce "eh hakane daidai ai."
Da dare bayan ya gama cin Abinci Amma ke masa zancen, ya ce "to shi Ahmadu anyi haka? ina shirin siya ya rigani kenan mugani? na mi™a masa ya ce "Masha Allah ta ko yi kyau screen touch ce Allah saka masa da alkhyr." muka amsa da "Ameen." ya ce "a dinga kula mamana kinga wayar nan inkinso zaki abin arziki da ita yafi komai sau™i, haka ma in abin tsiya zaka shuka yafi komai sau™i a kula a ji tsoron Allah... Yai ta min wa'azi da nasiha a kula duk da nasan baki da rawar kai zan shaidar hakan, ki cigaba a yadda na sanki." Amma ma ta Wora. akai tamin nasiha kafin kowwa ya nufi makwancinsa. ina kwance na gama komai nai Shirin kwanciya sai ga kiransa na Waga da sallama ya amsa cikin sanyinsa.. "my love"? "ina yini," na fara gaida shi, ya amsa "ina fatan gimbiyata tana lpy.." "lpy ta lau Sir na ji muryan ka sanyi lpy?"
"Wlh bana jin daWi ne Baby.." zaune na ta shi, cikin Wan fidda ido na ce "me ke damunka?" ya ce "ciwon ciki ne amma na sha magani fa" cike da damuwa nace "pls , sir ka je Asibiti," "Oh! shi sa bana son faWa miki irin haka na ce miki na sha magani zanje gobe insha Allah ki kwantar da hankalinki kinji Babyna.." ya ci gaba da lallashi na (oh ni yake ba ha™uri shi da beda lpy) mukai sallama akan gobe ze je ya ga likita.. nai ta masa ADDU'A samun lpy dan har cikin raina na ke tsananin tausayin sir wlh, ko don sanyin halinsa? Ko sonsa da nake ne? Ina haka bacci ya kwasheni.
&&& &&& &&&
Iyayen Sir sun je kaduna sakamakon matsawar da yayi dama jira na ake mu ™arasa makaranta ga shi munyi candy, da suka zo wajen Baa ne yake ce musu suje wajan en uwansa Abban zaria da Baba Alhaji su ne wakilai.
An tsayar da biki nan da watanni 2 masu zuwa don ba a saka da yawa ba ga shi saukar mu itama wata 1 duk abu ya haWe min. dan ma yanzu hada-hadar sauka muka fara, anata shirye-shirye a Makarantar mu da gayyato manyan Malamai Har da Sarki. mun Winka ankon mu kowwa hijab tai blue black da kuma Atamfa. dan Sir ne ma ya Winkamin ya hana su Baa Winka min a cewar sa ai ba komai nauyin ma ya kusa komawa kansa gaba Waya.
Yau na shirya ziyarar gidan Yaya Indo saboda daWewar da nai banje ba nai ma su Amma sallama don kwana2 nake so na yi mata, daganan zani gidan saura yayyena guda 2.
Na kammala shirina nai ma Amma sallama. na Isa gidan ´ar uwa tai ta ta murna kam da zuwana.
Da dare muna zaune da ita ta ke tambayana labarin Sir na ce "yana lafiya" Amma ta ce ma a sanar daku zancen biki an kawo kuWi da sa rana da kuma zancen saukarmu, ta ce "too..? abin ya zo kenan Allah ya nuna mana to ya ake ciki a gidan? gameda bikin"? na ce se Yaya Habeeba da Yaya Fatima sunje kun tattauna ko"? ta ce "hakane, to sai mu tafi tare in zaki wuce, na ce "ni daga nan gidan Yy Habeeba nai Kuma zani ma gidan y Fati" ta ce "dama kin bari ai musu waya duk mu haWu a gida se yafi, na ce "Allah kam Yy Indo in banje ba bazasu ji daWi ba" ta ce "aa wlh gaba kinje kibari yanzu in zaki tafi muje gidan a tattauna ko ba hakaba?" ba yanda na iya don naga ta dage na ce "to" ire²n hiranmu da ita kenan har dare ya nisa bamu sani ba ni ce ma na farga da lokaci muka kwanta.
Haka na ™are hu2 na gidan Yy Indo har ranar da zan dawo muna ta shiri an sanar da sauran ´an uwan nawa Amma na ta Shirin saukar manyan ba™i.
Bayan azahar muka sauka duk sun karaso dake duk mun fi su nisa nan fa gidan ya kacame da hayaniya anata murna da zuwan ba™i,
Bayan an nutsu an gama cin Abinci anyi sallah mun zauna aka fara tattauna batun yanda za'ai aka tsara da kuma shirin yanda bikin zai kasance, Amma ta ce tana yin wani adashi dan ankusa ma zuwa Waukan ta da Kuma wasu kuWaWe da take ajiyewa su yaya kowwa yace yanada tasa tsohuwar ajiyar aka harhaWa aka ajiye don siyan kayan kitchen da su labulaye zanin tunda gado da sauransu tunda dama ko gari banza Amma na siyan kayan kitchen Win da WaWWaya su Kofi rariya flas cokula ire-iren dai kayan tana ajiyewa saboda irin wanna lokacin gashi Kuma yazo, Baa yazo ya tarar damu ana ta hada-hada, ya ce "nima bara na zauna ayi dani..me ake tattaunawa?" Amma tace zancen kayan kitchen muke.. yai dariya "gaskiyane mamana za'a gwangwajeki" nai dariya da rufe fuskata, haka muka ci gaba da hiran mu da raha cikin nishaWi da walwala da ka ganmu kasan wanan ahalin suna cikin jin daWi.
[9/9, 21:31] E*O*W: SA˜AR ZARE

BY
NA'EEMARH SADAU=ØŸÜ

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE
FREE BOOK=ØØÜ

ELEGANT ONLINE WRITERs
'þ


Page 5ã __6ã
&&& &&& &&&
Yaune ta ke Asabar yakama ranar saukarmu kenan, filin makarantar cike yake da mutane ko Ina an zuba kujeru da rumfuna ko ina dai anyi decoration waje yayi kyau masha munsha ankon hijabanmu da niqab manyan mutane da malamai an halarta dan ba laifi kam anyi gayyata sosai kuma an amsa gayyatar.
˜arfe tara za'a fara. manyan ba™i suna zaune wajansu haka malamai da iyayen Yara kowwa an tanadar masa nasa mazaunin muma Walibai haka.
Lokaci ya cika Ina ta baza ido na hango Sir ban ganshiba har aka fara kiran Walibai domin gabatar da karatu.
Ba ni ce Waliba ta farko ba amma ni zan buWe taro da addua
Kowwa ya nutsu malaminmu da zai Kira Walibai naji ankira sunana.. na mi™e cike da nutsuwata na isa filin tare da amsar speaker na fara da zazza™ar muryata gurin yai tsit! ba abinda ake ji sai muryata ina rero adduar.. na gama tsaf sannan aka karSi speakern na Wago kaina ashe Sir ne.. na kalleshi da mamaki yaushe ya iso? don Wazu le™en duniya banganshiba, shima ya dubeni da murmushi sumsum na wuce.. akai kabbara da yaba ko™arina sannan aka fara kiran Walibai WaWWaya kowwa na fitowa ana karantawa, har aka zo kaina na fita na rera nawa dake Allah yamin za™in murya {dan indai muryace nikam ba daga nan na har tsokana na ake me muryan aljanu ko na ´an yara saboda za™inta da qanqantarta wasu suce iyayi ina sani alhalin ni banmasan inayi ba=ØÞ}.
Na kammala waje ya Wau kabbara, kowwa ya biya nasa sannan shugaban makaranta ya tashi yai jawabai aka bamu qur'anai za'ai mana karatu. Sir ne ya yimana mukai suratul Fateeha sannan mukai baqara shafin farko aka bamu Allo akai hotuna sannan aka rufe taro da addua dafatan Allah ya maida kowwa gida lafiya.
Mun koma gida aka shirya walima Yan uwa da abokan arzi™i qawayena su Hameeda an zomin sosai duk da wasu na cewa sai biki, na raba kayayyakina na walima mukai abinmu cikin nishaWi da walwala. da dare ma Sir yazo wai karSan nasa kayan waliman na Wauko masa ragowan stickern da meat pie en da mukai na bashi yace "ni fa da wasa nake miki Baby," na ce "aa ka amsa dai" ya ce "bani dai wancan Win amma sticker ai ni nayi ina ma dashi..." na ce "shikenan na barshi."
³an sauka duk an tafi yayyena ma sun wuce akan zasu sake shigowa in an kwana2 gida ya miqa daga ni se Ammata da Baa da qannena munyi waya da yan Zaria su Ameena sunce nai haquri abinda yasa basu zo ba sunje biki dangin maman su. nace bakomi my walida ma munyi waya ta ke cemin makaranta wai wani training take zuwa itama sai biki.

&&& &&& &&&
Biki ya ™arato Sangarori 2 anata shirye², dan har ma an kawo lefe dangin Amma sunzo ´an Zaria ma haka mutan kaduna ma gida dai ya Winke ba masaka anje anyi jere gidana ana faWa me kyau dashi ciki d falo se kitchen da bandaki da spare daki guda Waya se Wan filin tsakar gida se ™ofar gida. waje dai Masha Allah anmin jerena Baa yayi ™o™arin yimin kayana daidai Masha Allah sai sam barka. Komai ya Wau harami yau litinin saura kwana 3 Waurin Aure na ranar jumaa ne.
Muna zaune da daddare da sauran Yan uwana, Sir ya kirani na Wauka ya ce "ina ™ofar gida kizo ki amsa sa™o" na ce "to.." na mi™e aka fara min sha™iyanci wai ya cika zumuWi na ce "yayi Win," aikam aka Wauka "Baby bakida kunya kaza² na ce "naji" na zura hijab na fice suna min mita.
Zaune na ganshi kan mashin Winsa cikin qananun Kaya nikaina yamin kyau... bansan sanda na shagala da kallonsa na a zuciyata na ce "Sir badai iya Waukan wanka ba" na ™arasa ya kafeni da idanunsa "Amarya kinsha ™amshi" na rufe fuskata Ina murmushi ya ce "hakane ko? uhm tunda ma kikayi shuru nasan hakane kinsha ™amshin ana ta tanadarmin shi kuma" da sauri na Wago na Wan wara idanuna ina kallonshi, ya Wage gira "hakane ko? bayan ma ™amshi da wasu abubuwan nasani faWamin dame-dame? Inajinki," kunya ce ta kamani kaman na nitse cikin Wan bori da shogwoSa na ce "Sir.. ka bari mana please.." "mezan bari? daga tambaya?" "Uhm nidai kam da ka bari", ya dirgo a kan mashin Win "ok tunda bazaki faWamin ba ai zan sani ne,
amm.. yanzu shirin me kikeyi..? na ji kince zakiyi walima da zuwa ™unshi ko?" na ce "eh" "ok to ga wannan ya mi™o min kuWi da yawansu dan zasu kai kusan dubu goma sha biyar 15k na ce "Sir ai sunyi yawa," ya ce "aa ba komai da da wasu ma zan ™ara miki ne, so kiyi ha™uri da wannan Win" na ce "to" da sa hannu2 na karSa ina masa godiya ya ce "na bari ba komai ai komai nawa nasa ne don haka kar na damu duk abinda nake so in dai inada iko zan miki shi Baby matu™ar be fi ™arfina ba inshallah zan mikishi ko meye nidai fatana Allah ya barmu tare har mutuwarmu ko?" ya ™arasa da sigar tambaya yana langaSar da kai kamar wani maraya na ce "eh Allah ya barmu taren inshallah zan cigaba da maka addua ko yaushe" na faWa cikin sanyi saboda ya bani tausayi irin yadda yake matu™ar ™o™ari a kaina shi ba wani kuWi ba saidai rufin asiri amma yanada ™o™ari da son kyautatawa shiyasa kowwa nasane ji nai an hure ni da iska.. "Wai tunanin me Kika tafi ne?" na karyar da wuya "ba komi" mashin Winsa ya hau da tayar dashi "ki shiga ciki naga dare yayi na ce "tom Allah ya kaika lpy" "yabce ameen My," ya tayar da mashin Win da wucewa nikuma na koma ciki.
Amma na nunama kuWin tace to Allah ya qara buWi amma wannan kuWin be yawa ba? na ce nima haka na ce masa ta ce "to Ahmad dai baya gajiya... dama naji kuna gobe zaku ™unshin ko?" na ce "aa yayi wuri sai laraba jibi kenan" ta ce "to Allah ya kaimu."
Ranar laraba muka shirya da wuri zamu gidan ™unshin saboda in bamu je da wuri ba layi kuma ana kitso a gidan zaa haWa duk aimin muka shirya ni dasu Ameena da my Waleeda da Hameeda ma tazo muka tafi. munje bamu tadda kowwa ba dama Kuma mun tambaya tun kan mi zo, ™unshi aka fara sakamun kafin ta fara yarfamin kitso ´an ™ananu Masha Allah dama kaina akwai kyan kitso Ita kanta seda ta yaba don ya zanu yai kyau sosai sannan aka ciremin ™unshin yai jaa sosai ta fara zanamun flawer.. Hmmm nikaina nasan nayi kyau kowwa ya ganni zai yaba su Hameeda ma anyi musu dan sai kusan maghreeb muka dawo gida yini guda zubur.
muka shigo gida a gajiye ana ta mana sannu tamkar Wanda sukai aiki ko dake ™anin aikin mukai kowwa na ta yaba ™unshina ana nayi kyau. wanka mukai da sallah muka zauna cin abinci.. Sir ya kirani ya ce in yayi sallar isha'i zai shigo na ce "Allah ya kawo ka lpy". Ameena ta fara "oh ni ´asu wai shi wannan Angon baya da haquri ne? sauran kwana nawane da bazai jiraba.." na ce "gsky Ameena kinada sa ido ina ruwanki to? aah?" na mi™e na wanko hannuna

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment