Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hayakin dake tashi wanda bata san ko na meye ba a cikin makabartar na ƙara sa taji kamar ta falla da gudu. Kokowa take da duk wani sassa na jikin ta, dan kar ta kalli wuraren, ta saddar da kanta ƙasa. Ita kuwa Mama na bin tsohon a baya dan kar ya ɓace musu. Zahara tasan itama Mama cikin tsoro take amma bata son nunawa ne.

Tsoro Zahara take ji da kuma da nasanin zuwa. Nadamar kin bin shawarar Abba take yi. Haka kawai sun biyo wani tsoho dan yace musu yanada mafita akan matsalar ta ba tare sun san ko waye shi ba. Mama tace ta yarda da shi dan alamun sa na nuna mutumin kirki ne. Sai dai ko me Zahara zata ce ko zata yi lokaci ya ƙure...

Mama ce ta tsaya daga tafiyar da suke yi sakamakon shima tsoho ya tsaya. Juyowa tayi ta cewa Zahara ta karaso.

“Yi hakuri ki kara daurewa.” Cewar Mama. “Saurin yin abinda yace, saurin ganin kin rabu da wannan abun da ke jikin ki. Kin ji?” Mama ta sake faɗa.

Gyaɗa kai Zahara tayi sannan ta ƙaraso inda Mama take. Tafiya suke wannan karon da dan saurin su ganin sun cimma inda tsohon yake tsaye yana jiran su. Bayan sun ƙaraso wajen sa, ya kama hannun Zahara. Kallon ta yayi a tsanake kafin ya juya ya kalli Mama, sannan ya saki hannun ta ya ɗora hannayen sa biyu bisa kafaɗun ta da iya ƙarfin sa dan zaunar da ita. Ita kuwa Zahara kokarin tashi tsaye take amma tsohon yaki bata dama. Sannan ya cewa Mama ta ɗan koma gefe dan ya samu yin aikin sa. Mama kallon Zahara tayi da kokarin nuna mata komai zai je daidai, amma ita Zahara wannan bai ishe ta ba a yanda take cike da tsoro.

Rufe idanu Zahara tayi lokacin da tsohon ya shiga kewayar ta. Bata san kewaya ta sau nawa yayi ba, amma tasan yanada yawa. A duk lokacin da ya kewaya ta sai taji tamkar tana shakewa. Tsohon yace ta zauna bisa gwiwan ta, amma gajiyar da take ji ba zata barta ba. Ita babu abinda take so yanzu face ta bar wurin nan da sauri.

“Mama...ni.. gida..nake son..tafiya..” Zahara ta samu nasarar haɗa kalmomin nan, amma Mama bata ce komai ba. Shi kuwa kamar yana jira ta faɗi hakan, ya dakata daga abinda yake.

“Zan kira Amriya zuwa cikin jikin ki. Dan haka ba wani abu bane idan baki iya tuna komai ba.”

Da Zahara yake amma ita ba lallai bane taji abinda yace. Domin duk a gajiye take, ga kuma bukatar barin wurin da take da.

“Ayyarubo ramataniya sasiban..”
Tsoho ya shiga maimaita wannan kalmomin ba ƙaƙƙautawa a bayan Zahara. Ya shiga zuba mata wani abu a kai, ita kuwa ta daga kanta domin samun yin cikakken numfashi. Wasu ruwan ya sake fiddowa ya watsa mata wanda wannan karon suka sanyata amai bayan wasu yan mintuna. Zahara taji tamkar zata amayo da hanjin ta. Bata gani sosai amma abinda ya fito daga cikin bakin ta baki ne sosai fiye da gawayi. Wani azababben ciwo ne ya sanyaye mata jiki ta faɗi kasa kamar wani yasa ƙarfi ya ture ta. Ta kasa magana ko motsi. Fatar idanun ta a hankali ta fara yi mata nauyi. Ta kasa controlling jikin ta.

Mama kuwa tsoro duk ya kamata, jikin ta ya shiga rawa ganin ƴarta kwance a kasa. Tambayoyi suka fara yawo cikin kanta. Anya kuwa tayi abinda ya dace? Toh in fa mijin ta yayi gaskiya? Yanke shawarar korar tunanin tayi, tabi abinda zuciyar ta ke fada mata na son taimakon ƴarta. Addu'a kawai take yayin da shi kuma tsoho Malam Shehu ke warkar da ƴarta.

Shuru wajen yayi. Malam Shehu bai daina kewaya Zahara ba, kafin shima ya dagata. Numfashin Mama da kadawar iskar bishiyun maƙabartar kawai ake ji da ya bada yanayin nan tamkar a cikin horror film. Mama kallon tsohon tayi, taga alamar kamar murmushi a fuskar sa. Tana shirin ta tambaye shi dalili, ƴarta dake kwance bata motsi ta tashi da karfi tana gurnani tamkar karen zangai.

“Me kuma nake yi anan? Me kuma kake nema gare ni?”

Zahara ta tambaya amma tsohon yasan ba ita bace Amriya ce.

Mama baya tayi kamar zata fadi ganin idanun Zahara sun koma bakikirin. Duk tsikar jikin ta ta tashi, tsoro ya ƙara jigar ta ganin kusan siffar ƴarta duk ta canja.

“Me ka aikata min mugun tsoho, ka kunce ni. K cewa wannan munafukan su sake ni in tafi!” Zahara ko ince Amriya ta cewa Mama da take a rude ta kasa gane komai, domin bayan ita, Zahara da Malam Shehu bata ga kowa ba a wurin.

“Ba kina tunanin kin fimu ƙarfi ba. Sai ki nuna mana mu gani.” Cewar Malam Shehu.

Wata mahaukaciyar dariya Amriya tayi kafin tace
“Ni da kai mun san zan iya kai maka farmaki idan ina so a kuma inda nake so. Ba kamar kai ba, ni ba matsoraciya bace, ba zan nemi ɗaruruwan aljanu ba kafin na kama ka. Ni kaɗai na na ishe ka.”

“Ke fah? Baki jin kunyar yiwa bil'adama biyayya? Na ɗauka wayon ki yafi haka.”

“Idan baku sake ni ba, na rantse muku sai kunyi da nasani!!” Ta faɗa tana kubce-kubce da iya ƙarfin ta, amma ta kasa tashi daga durƙushen da take, hannayen ta a bayan ta.

“Ya isa haka Amriya. Zamu kai ki wajen mahaifin ki.”

Da jin haka Amriya tayi shuru, ta nutsu.

“Kada ka sa mahaifi na cikin wannan zancen.” Ta faɗa cikin siga mai sanyi da barazana.

“Zamu kai ki ko kina so ko bakya so.” Tsoho ya bata amsa.

“Ok, me kake so? Zan baka ko me kake so. Kana son duka dukiyar duniyar nan? Zan iya mayar da kai mutumin da yafi kowa kuɗi a duniyar nan. Ko karfin iko kake so? Zan iya maka ko me kake so yanzu yanzun nan. Kawai ka faɗa min abinda kake bukata yanzu muyi magana a nutse. Ka shafa min lafiya, kuma ka daina saka mahaifi na a ciki.”

“Oh yanzu zaki bada haɗin kai kenan? Bana son komai cikin abinda kika zayyana. Ina son ganin an hukunta ki kan abubuwan da kika aikata.”

“Oh duk kana wannan haushin ne, saboda ƴar ɓarnar da nayi kauyen ku? Come on nasan kafi haka, mu manta da komai.”

“Hakan sauki gare shi a wajen ki, dan baki da wanda kike so da gaskiya...”

“ƘARYA KAKE!” Cewar Amriya cike da karaji, har da yayi silar barbajewar gashin Zahara kan fuskar ta. Duk wannan laifin ku ne, kun raba ni da abinda nafi ƙauna a duniyar nan. Duk ku ne silar duk abinda ya faru da ku. Ku ne halittu marasa tausayi a doron ƙasa, amma bansan ta yaya kuka zama wanda Allah yafi ƙauna ba. Kun cutar da ni, alhali ni kawai rayuwa nake son yi da shi.”

Mama tuni an fara baro ta a baya, bata gane abinda Amriya ke faɗa. Tambayar kanta take, me wannan mutanen suka aikata mata da har ta zama haka.


Hausa novel

“Kece kika so yin abinda aka hana, duk sai da muka gargaɗe ki amma baki ji ba.”

“Ka yarda da ni, in har ina raye sai na kashe duk wata mace da naci karo da ita kan hanya ta. Sai na sanya ku cikin kunci kamar yanda kuka sanya ni. Kana tunanin na gama da mutanen ƙauyen Na'iya ne? Duk abinda nayi musu soman taɓi ne.”

“Kafin nan zamu kai ki wajen mahaifin ki. Shi zai daidaita miki zama.” Cewar Malam Shehu yana mai kara kusanto inda take.”

“Kuyi duk abinda ma zaku yi...!”

“Ki faɗi duk abinda zaki faɗa Amriya, amma nasan mahaifin ki ne kaɗai zai yi maganin ki domin shi kaɗai kike tsoro.”

“Kuyi ko me zaku yi, tun ranar da mahaifi na ya kore ni tare da jefa min wannan alkaba'in nima na manta da shi.”

“Ah kenan ba shaci faɗi bane? da gaske ba zaki iya shiga jikin namiji ba?”

“Hakan ba zai hana ni na wargaza su yanda suka cancanta ba. Idan ka shafa min lafiya, zan baka labarin duk abinda ya faru kuma zaka gane abokan ka aljanu ƙarya suka yi maka kan labari na.”

“Bana bukatar ji, domin kowa yasan labarin.”

“Kayi kwance kan ƙaryar da aljanu da kuma munafukan bil'adaman nan suke yaɗawa ne? Ka bani mamaki. Na ɗauka kai abokin gaba ne wanda ya kai. Ashe nayi kuskure.” Cewar Amriya.

Malam Shehu ida ƙarasowa inda Zahara take yayi, sannan ya damki gashin kanta amma Amriya ce taji zafi. Duk hakan yana faruwa ne kan idanun Mama ne da bata kuskura ko kalma ɗaya na abinda suke cewa ba. A kiɗime take sosai ganin abinda ke faruwa kan idanun ta. Irin wannan abubuwan tana ganin su kaɗai a cikin TV da fina-finai ne, a da bata yarda ba amma yanzu taga zahiri...

“Koma dai meye zaki fita daga jikin yarinyar nan da son ranki ko ta karfi.”

“Labari na da ya faru lokacin da kana ɗan ƙanƙanin ka, shine zaka ce min kasan komai. Wai a wa kake ɗaukar kanka ne?” Cewar Amriya tana dariya.

Haushi ne ya kama Malam Shehu. Ba tun yau ba yasan Amriya ta rena shi. Kuma hakan ne take yi idan tana son hassala shi. Amma ba zai barta ta tsira ba wannan karon. Cigaba yayi da aikin fitar da ita daga jikin Zahara.

“Ayyarubo ramataniya sasiban kuki kinaka kuna kiban...”

Ya cigaba da faɗin kalaman nan yana kewaya ta. Amriya da da farko ta nutsu, ta shiga ihun wahala tana murkususu. Ihun mai ƙarfi ta yanda har yasa Mama ta toshe kunnuwan ta da iya ƙarfin ta.

“Zan kashe ka, ka daina...banzan tsoho kawai..” Amriya ke cewa da iya wahalar ta.

Shi kuwa tsoho ya cigaba da faɗar kalaman sa.

“KAYI SHURU, KAYI SHURU...zan fita...zan fita.”

“Zaki fita?” Malam Shehu ya tambaye ta yana cigaba da zuba mata ruwan dake cikin kwalbar hannun sa.

“Eh, zan fita amma ba zan bika wajen mahaifi na ba.”

“Ayyarubo ramataniya sasiban kuki kinaka kuna kiban...”
Malam Shehu ya cigaba da faɗa, yana kewayar ta.

“A'A. A'A ZAN FITA, ZAN FITA AMMA BA ZAN JE WAJEN MAHAIFI NA BA... IDAN NAJE ZAI KASHE NI...ZAN RASA DUK ƘARFI NA.. KUMA BA ZAN TAƁA YAFE MAKA BA. ZAN ƊAUKI FANSA TA GA DANGIN KA DA KUMA ABOKAN KA ALJANU.”

“Barazana kike min?” Malam Shehu ya tambaye ta.

“Gargaɗin ka kawai nake.” Amriya ta faɗa tana haki kamar wacce taci uban gudu.

“Wannan yarinyar bata yi miki komai ba, baki da yancin shiga jikin ta. Har ki gallazawa rayuwar ta.”

“Ka min shuru, ka yi abinda ya shafe ka. Na shiga jikin ta saboda tana burge ni. Ina yin abinda raina yake so ne.” Cewar Amriya.

“Ayyarubo ramataniya sasiban kuki kinaka kuna kiban..”

“Na faɗa zan fita...”

“Ayyarubo ramataniya sasiban kuki kinaka kuna kiban...Ayyarubo ramataniya sasiban kuki kinaka kuna kiban, Ayyarubo ramataniya sasiban kuki kinaka kuna kiba,Ayyarubo ramataniya sasiban kuki kinaka kuna kiba..!”

Ihu Amriya ta saka na wahala, tana kuka ba ƙaƙƙautawa. Mama tambayar kanta take, meye ma'anar wannan kalmomin kuma me yasa suke cutar da aljanar.

“Ya isa, zan fita wannan karon...Zan fita.” Ta faɗa cikin kuka. “Kawai ka faɗawa aljanun ka da su rabu da ni. Ka ce musu su daina taɓa ni.”

“Zasu sake ki, idan mun je kan babban dutsen ƙauyen Na'iya wajen mahaifin ki.”

“Toh kace musu su sassauta ɗaurin da suka yi min. Dan zafi nake ji.”

“Zasu yi idan kika fita daga jikin yarinyar nan.”

Shuru tayi na kamar mintuna goma, kamar tana bacci. Malam Shehu bai ce komai ba, yana jira. Ita kuwa Mama tunani take ko dagaske zata fita daga jikin Zahara ganin irin taurin kan dake gare ta...

Murƙususun wahala Zahara ta shiga yi, tana fizge-fizge na tsawon wasu yan mintuna kafin ta faɗi kwance.

Juyawa Malam Shehu gun Mama da hankalin ta yake a tashe. Cikin sigar tabbaci yace mata. Komai yazo karshe. Ta fita daga jikin ta.

Kusa da jakar shi ya tafi, ya buɗa ya ɗauko wata laya. Yaje inda Zahara take kwance bata motsi, ya ɗaura mata a hannun dama.

“Ko me zata yi kar ta yarda ta cire wannan layar. Zan je na mayar da Amriya wajen baban ta, amma bansan me zai faru ba daga nan. Zamu iya dawowa, amma da wannan layar, ba zata ƙara shiga jikin ƴarki ba.” Cewar Malam Shehu kafin ya juya.

“Kuje muje...!” Ya faɗa cikin ɗaga sauti kafin wani iska ya ɗauke shi suyi sama su ɓace.

---------------------------------------------
See you next chapter Insha Allahu🤞
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 11

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚

A BANGAREN KHADIJA

Rufo kofar dakin tayi sannan ta zauna bakin gadon. Kuka Salmah take cen ciki ba'a jin sauti. Idan ta fara irin haka ba wanda yake iya lallashin ta, har Khadija ba abinda take iya fada da zai sassauto ta. Idan wani abun ya faru tafi son a barta taci kukan ta, hakan ne zai sa ta samu sauki a zuciyar ta kuma idan ta gama kukan zata manta da damuwar ta. Amma ganin ta cikin damuwa nasa ita ma Khadija na shiga damuwa. Amma duk da haka tafi son ace Salmah tayi juyayin ta anan kusa da ita da ace basu san inda take ba. Domin tsawon kwanaki kenan suna neman ta lungu da sako na garin, hakan ba karamin tayar da hankalin Khadija yayi ba, amma jiya wajen karfe uku na asuba lokacin da taji ana konkwasa kofa, nan da nan ta gane Salmah ce.

Fadawa jikin Khadija Salmah tayi tana kuka, lokacin da ta bude mata kofa. Khadija tayi kokarin jin inda taje amma taki magana. Tun.. jiyan shuru tayi taki magana. Tayi kokarin ta fada mata irin neman ta da suka yi ita da Ammar, amma bata nemi ta saurare ta ba.

“Na hada miki breakfast ko zaki ci?” Cewar Khadija.

Gyada kai Salmah tayi, sannan tace mata tana son a barta ita kadai kuma sai an jima zata ci abincin.

Ok, Khadija ta amsa da shi kafin ta fita daga dakin.

Zaunawa tayi falo tana jiran Ammar domin tuni tayi masa waya Salmah ta bayyana. Kuma yace mata yana zuwa nan da wasu mintuna. Salmah ta fada mata kar ta yi wani abun, amma ba zata iya hakan ba. Ba zata iya lallashin ta ba amma wata kila ta dan sauko idan suka yi magana da Ammar.

Sai da ta sake jira kamar na rabin awa kafin Ammar yazo.

“Sorry, na makale ne a gosulo.” Cewar Ammar lokacin da ta bude masa kofa.

Gaisawa suka yi sannan tayi masa iso zuwa ciki.

Ammar daga kallon sa zaka gane duk ya fita hayyacin sa. Dan kamar wanda aka kwato a bakin kura.

“Ina take?” Ya tambayi Khadija.

“Gaskiya tana cikin damuwa sosai. Kuma nasan zata ji haushi kan kiran ka da nayi. Amma nasan tana da bukatar ka a halin yanzu.”

“Kar ki damu Khadija zan yi iya kokari na. Nagode da kira na da kika yi.”

“Tana ciki.” Khadija ta fada tana nuna masa dakin ta.

Ok yace sannan ya nufi dakin.

Komawa Khadija tayi ta zauna a falo, cike da fargabar abinda zai biyo baya. Tana sa ran komai ya daidaita tsakanin masoyan.

Shiga dakin Ammar yayi cikin sanda. Ya tarar da Khadija kwance ta ba kofa baya. Yayi tunanin ko bacci take, amma yaji kamar alamun shasheka.

“Khadija nace miki sai an jima zan ci abincin. Ki rabu da ni please.”

“Ni ne.” Ammar ya fada a sanyaye.

Koda taji muryar shi, ta juyo ta kalle shi sannan ta tashi zaune da sauri. Ammar yaji ba dadi ganin yanda fuskar ta ta sauya tsabar tasha kuka.

“Me kake yi anan? Ka bar nan ko kaga bacin raina yanzu.” Khadija ta fada cikin sigar barazana. Shi kuwa Ammar ko a jikin sa domin baida tunanin tafiya yanzu bayan shafe tsawon kwanaki yana neman ta.

“Calm down please Salmah, magana kawai nake son muyi a nutse.”

“Ni kuwa nutsuwar ce bana bukata okay? Ka shafa min lafiya kawai. Kai ne mutum na karshe da zan so gani a halin yanzu.” Salmah ta fada da dan daga murya.

Fara matsowa a hankali inda take yayi.

“Ammar kar ka karaso inda nake.” Ta fada tana mai jefo masa pillow shi kuwa ya cabe kafin ya kai ga jikin sa.

“Na gane cikin bacin rai kike. Ki yarda da ni nima cikin tashin hankali nake. Bana bacci cikin dare, saboda rashin sanin halin da kike ciki. Ya kamata ki yarda da ni, ban fadawa mahaifiya ta komai ba game da ke. Na rantse miki da Allah.”

“Amma ai kai kadai kasan hakan. Ba zaka ce min taji bane haka kawai by chance dan ba yarda zan yi ba. Ka fada kawai kai ka fada mata, kuma kaci amana ta.”

“Ban san me zan yi ba dan ki yarda da ni. Please, kar ki bar wannan zancen ya ruguje mana soyayyar mu da muka gina.”

“Tuni komai ya ruguje, kana tunanin mahaifiyar ka zata yarda ka aure ni? Ko ba ka ji irin cin mutuncin da tayi min ba?”

“Ba mahaifiya ta bace zata aure ki, ni ne zan aure ki kuma ni zan zauna da ke. Idan muka yi niya zamu iya auren mu ko babu amincewar ta. Kasancewa da ke ni shi kadai ne buri na.”

“Ba zai yiwu ba hakan, ba zan so ka bijirewa mahaifiyar ka ba saboda ni. Kawai mu hakura mu manta da juna.” Ta fada tana goge hawayen fuskar ta.

“Mu manta da rayuwar da muka yi? Ko kin san me kike fada? Mu manta da duk wata soyayya da goben da muka tsarawa kan mu. Nasan kin fada ne saboda kina cikin damuwa.. amma ki bari zamu yi magana daga baya... Zan yi...”

Katse shi tayi.

“I'm sorry, amma ba na fada bane saboda ina cikin damuwa. Sai da nayi dogon tunani. Nasha wahala sosai a rayuwa ta, ba zan iya juriyar tunkarar mahaifiyar ka ba. Ta tsane ni kuma babu abinda zai canza hakan. Ina son ka da iya dukan zuciya ta da ruhi na, amma nafi son kaina a kan son da nake maka. Ba zan iya jure wannan tashin hankalin ba. Nasan zan shiga damuwar rashin ka, na kwanaki, watanni ko ma shekaru amma nasan dole wata rana zan manta da kai.”

Tsoro ne ya kama Ammar a halin yanzu, tsoron rasa Salmah. Sun sha yin fada har suce sun daina soyayya amma basu yin sati basu shirya ba, saidai basu taba yin irin wannan ba da gasken gaske.

“Please, ki daina..fadar.. haka. Kin min alkawarin jure duk wani abu da zai zo ya shiga tsakanin soyayyar mu.”

“Eh, amma ba zai yiwu ba wannan karon. Wata kila Allah bai yi ba ni matar ka ce. Kayi rayuwar ka.. nima naje nayi tawa rayuwar.”

Wani bacin rai ne ya saukarwa Ammar da yasa ya naushi bango da iya karfin sa. Take jini ya fara zuba daga hannun sa, amma shi ko a jikin sa.

“Ta yaya kika iya kallon kwayar idanuna ki ce inje inyi rayuwa ta? Kece rayuwa ta Salmah, dagaske kina tunanin zan iya wata rayuwa mai dadi babu ke? Ke ma nasan ba zaki kasance cikin farin ciki ba babu ni. Mun riga mun zama daya ko kin manta?”

Kuka Salmah take kasa-kasa, shi kuwa Ammar na kokarin ganin yayi controlling fushin sa.

“Ba zan iya ba Ammar, i'm so sorry.”

Matsawa yayi kusa da ita, ya rungume ta sosai a jikin sa... Sosai ta yanda numfashi yaso ya gagare ta. Kokarin ture shi take amma shi kuma ya kara kankame ta. Ihu ta fara har saida Khadija ta shigo da gudu cikin dakin ta raba su. Tsoro ya kamata ganin jini jikin bango da kuma hannun Ammar. Da sauri ta kalli Salmah ganin ko bugun ta yayi. Ita kuwa Salmah komawa tayi gefe ta cigaba da rera kuka.

“Ya kamata ka tafi Ammar, na dauka kazo gyara matsalar ne ba wai ka kara rura mata wuta ba.” Cewar Khadija.

“Zan dawo, kuma ba zan rabu da ke ba. Zan dawo, kuma ina so ki sa a ranki cewa ke matata ce kuma ba wanda ya isa ya raba mu. Kiyi duk abinda kike so, amma soyayya ta gare ki mai karfi ce da zan iya jure duk wata guguwa da zata shigo tsakanin mu.” Ammar ya fada kafin ya fice daga gidan.

(.....)

A BANGAREN KAMAL

“Ka cewa dan uwan ka, ya dena nema na. Lafiya lau nake.”

Murza ido yayi ya sake karanta sakon, nan ya gane ba kowa bace face Salmah. Janye bargon da ya rufa da shi yayi cike da kasala, ya sauko daga kan gadon. Kallon agogo yayi yaga karfe hudu ne na asuba, wannan ne karon farko da ya samu irin wannan baccin. A da idan ya kwanta wajen karfe sha daya, sai karfe uku yake farkawa. Amma yanzu bai bacci sai wajen karfe biyu ko uku.

Kokarin kiran number ta yayi amma bata shiga. Wata kil ta kashe wayan ta ne. A ransa yace, bai dace ma ya kira ta yanzu ba, domin yanzu haka tana bacci ne. Amma zai jira zuwa karfe bakwai ya gani.

Amfani yayi da wannan damar, ya shiga ban daki. Tunani fal a ran shi. Ba zai iya cigaba da hakan ba. Gashi dai ba bacci yake yi ba da dare, kuma hakan zai iya zamar masa wata matsala. Tun abinda ya faru da Zahara, ya kasa dena tunanin ta. Ya tambayi wani malami aminin mahaifin shi. Ya fada masa da al-qura'ani mai girma babu abinda ba za'a iya warkarwa ba. Kuma yayi masa alkawarin zai gama shi da wani da zai taimaka mishi. Yanzu abinda ya rage shine ya shawo kan Zahara. Yayi kuskure da bai amshi number ta ba, amma tinda yasan gidan su zai iya zuwa gobe. Amma bai sani ba ko wannan ita ce mafita, dan bai sani ba ko tayi maganar da iyayen ta. Ba zai iya zuwa gidan su ba haka kai tsaye. Doguwar riga ya saka, ya sauko kasa ya nufi kitchen dan ya hadawa kanshi coffee.

Yana kishingide bisa kujera a falo, bacci ya sake dauke shi. Ba shi ya farka ba, sai da konkwasa kofa da ake yi ya tayar da shi. Tv a kunne, kuma ko coffee din da ya hada bai sha ba, bacci ya dauke shi. Gashi ko sallar asuba bai yi ba har karbe dayan rana tayi. An dade rabon da ya samu bacci haka.

Ba'a daina konkwasa kofar ba, sai ma karuwa da yayi... Ya tabbatar Ammar ne. Shi da yace zai zo tun takwas. Mikewa Kamal yayi yaje ya bude masa.

“Nayi ta addu'ar kar ace ka fita ne.” Cewar Ammar lokacin da ya bude masa kofa. “Wai bacci kake ne? Yaushe ka fara bacci wannan lokacin?” Shigowa yayi ya nufi falo ba tare da ya jira jin amsar dan uwan nashi ba.

“Salmah tayi mun texte jiya.” Kamal ya fada yana zaunawa a dayan kujerar.

Dauko wayan sa yayi da niyyar ya nuna masa, amma yace ai yaga Salmah.

“Ka ga wa? Salmah? Ta yaya?”

“Khadija ce ta kira ni. Dan naje na ganta.”

“Amma ai kace min kaje gidan su Khadija bata nan. Karya tayi maka kenan?”

“Ban sani ba bro, abinda kawai na sani so take ta rabu da ni yanzu.”

Sai yanzu Kamal ya fahimci dalilin da yasa dan uwan shi ke cikin wannan yanayin.

“Bacin rai ne kawai, ka dan bata lokaci.”

“Tace min sai da tayi dogon tunani. Ina tsoron na rasa ta bro. Ji nake kamar zan yi hauka.”

“Tana cikin bacin rai ne yanzu, amma ka bata lokaci. Kuna son junan ku ba zai yiwu ku rabu ta sauki ba.”

“Zan tura su kawu gidan su, zan sa a daura auren mu ba da dadewa ba. Dan hakan ne zai sa Mom ta shafa mana lafiya.”

“Kar ka aikata hakan. Idan kana tunanin ta hakan ne idan ka auri Salmah Mom zata rabu da kai to kayi kuskure.”

“Toh me zan yi kenan?”

“Ka kwantar da hankalin ka, kayi tunani. Yanzu dai kayi kokarin daidaita tsakanin ka da Salmah. Sauran daga baya mun yi magana.”

“Ba zata yarda ba domin tasan Mom ba zata iya karban ta a matsayin suruka ba. Ya kamata na fara ta kan mom kafin naje kan Salmah.”

“Ya kamata ka tashi tsaye. Domin rayuwar ka ce, ba zaka bari kullum sai abinda mom tace ba game da rayuwar ka. Kuma kaima ka dena yi mata daukan kan nan da kake yi.”

“Kai ka fini sani, kullum tafi son ta nuna cewa ita ke kan daidai.”

“Shi yasa nake ce maka, ka lallaba ta, ka tabbatar ka shawo kanta.”

“Shikenan zan jaraba. Gashi kwana biyu na dena zuwa kamfani. Kuma har yau ban yi magana da Zahara ba. Nasan zata ji haushi na.” Cewar Ammar.

Kamal ba zai

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment