Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dan girgiza ni. A ranar nan, kafin ta tafi ta bar gyalen ta kusa da ni. Nayi tunanin koh mance shi tayi, na yanke shawarar kai mata shi gidan su kamar yanda ta kwatanta mini... Na hadu da Mami, wata kawar Mahaifiya ta da nake tunanin ita ce mahaifiyar Amriya amma matar tace min tanada 'ya kuma ta rasu shekarun baya. Ban fahimci komai ba, duk na rude itama haka. Lokacin da ta nuna mini hoton 'yarta Aisha, naga ita ce wacce na hadu da ita bakin kogi.”

Kamal bai ce komai ba, sauraron ta dai yake a tsakane. Koma dai ya girgiza da jin labarin toh jikin sa bai nuna ba. Fuskar sa babu wani alamu, har Zahara taji tsoron kar ace bai yarda da labarin ta ba. Amma duk da haka ta cigaba da bashi labari.

“Tun daga ranar, na fara gane-gane da jin abubuwa. Na daina bacci, ko nayi sai muggan mafarkai. Ban baiwa kaina wahala ba wajen yarda cewa halin da na shiga yana da nasaba da haduwa ta da wannan matar. Ban yi kuskure ba, domin bayan wasu kwanaki ina bacci, wata mata ta bayyanar min. Nan na gane Aljana ce ke son shiga jiki na. Ta ce min tana son ta taimako na.”

“Kika ce mace ce? Da kamar wuya.”

“Tun daga wannan ranar, na fara canja halaye da shiga ta. Ina jinta a jiki na kuma tana sanya ni abubuwan da bana bukatar yi. Bansan me zan yi ba dan na fita daga wannan ukubar. Har tunani na ma ita ke controlling din sa. Idan ta fita daga jiki na ma, ina ji. Ina tune da duk abinda take yi. Sai dai tun jiya, na kasa tuna komai. Kuma hakan na damuna, bansan me take iya aikatawa ba nan gaba. Yanzun haka, ina tunanin yanda zan yi na nemi afuwa gun Mr. Ammar da budurwar shi.”

“Ke kuma babu abinda kika yi? Kika barta duk tana yin wannan?”

“Toh ai ban san yanda zan yi ba na rabu da ita. Ina tsoron ta cutar da dangi na, lokacin da take min magana na tabbatar ba zata rabu da ni ba ta sauki.”

“Ki dena nuna mata kina jin tsoron ta. Bai dace ta dinga gallazawa rayuwar ki ba. Ki daina bata wannan damar. Wa kika fadawa wannan zancen kuma kina karatun alkur'ani mai girma?”

“Ba wanda na fadawa bayan kai. Duk lokacin da nake so in dauko da niyyar karantawa sai inji na kasa. Ina jin ba zan taba fita da wannan tashin hankalin ba.”

“Da farko abinda ya shafi dan uwana, ina baki shawara da karki fada masa komai yanzu. Ki bari har komai ya laba. Kuma ya kamata ki fadawa iyayen ki. Ba karamin abu bane ke faruwa da ke, ba zaki iya yin komai ba ke kadai. Kina cewa ba zaki fadawa kowa ba, saboda kar ki sa su a matsala amma rashin fadar shi zai haifar da masifu da yawa domin ba wanda zai iya taimakon ki. Kiyi maganar da iyayen ki, ni kuma bangare na zan nemi karin bayani daga gun malamai kuma zan kokarta ganin na taimaka miki.”

“Ka yarda da ni kenan?” Zahara ta tambaye shi.

“Zahara, Aljanu suna rayuwa a cikin mu. Bama ganin su amma suna tare da mu. Akwai na kwarai haka akwai bata gari. Suma suna bautawa Allah kamar mu. Shiga jikin mutane yana daga cikin zunuban da aka hane su yi. Kuma suna yin sabo kamar yanda muke yi.”

Gyada kai Zahara tayi alamar gamsuwa.

“Don haka, ki tashi tsaye. Kar ki bari ta rinjayi rayuwar ki. Bata da wannan 'yancin.”

“Nagode da saurare na kuma da yarda da ni da kayi. Wannan ne karon farko da nayi maganar, kuma naji dadi sosai.”

“Ba komai, yanzu zan iya kai ki gida. Kiyi amfani da wannan damar ki sanar da mahaifan ki. Allah kadai yasan abinda wannan Amriyar take iya yi. Mafi akasari Aljani ne ke shiga mace kuma suna iya yinsu ganin sun boye kansu cikin jikin, dan kar a kora su amma nan bayan Aljana ce mace tana komai ganin ta bayyana kanta. Zan yi bincike mai yawa akan wannan, amma kafin nan kiyi magana da iyayen ki.”

“Ok nagode sosai.”

“Shikenan, muje na kai ki gida.”

“Ban san ya zan yi ba, na mayarwa da kanwar ka ba abayar ta. Kunya nake ji na koma gidan ku bayan abinda Amriya tayi.

“Kina iya rike ta.” Yace mata. “Kar ki damu.”

“A'a..a'a..ba zan..”

Katse ta yayi.
“Kar ki yi wani dogon zance, ki dauka, zan siyo mata wasu.”


(....)

A gidan su Zahara kuwa, hankalin Mama ya tashi sosai ganin Zahara bata dawo gida ba. Jiya da ta ganta cikin jar rigar nan, jikin ta bai bata ba amma ganin kamar 'yar tata tana cikin farin ciki sai bata yi magana ba. Amma yanzu ganin ba labarin ta, ta fara da nasanin barinta da tayi ta fita.

“Ko kiran Yan sanda muke?” Ta cewa Abba da ke ta faman duba takardun sa tun dazu.

“Kina tayar da hankalin ki sosai Asiya. Na tabbatar duk inda take cikin koshin lafiya take.”

“Ban san ta yaya kake ba, har ka iya zaunawa haka. Cewa tayi zata je wajen walima ba wai zata kwana a cen ba.”

“Mu bari har zuwa yamma idan bata dawo ba, sai muje mu sanar da yan sanda.”

Konkwasa kofar gida suka ji ana yi.

“Kin gani, na tabbatar ita ce ta dawo.” Cewar Abba.

Tashi Mama tayi taje duba mai konkwasawa, hankalin ta ne ya kara tashi ganin ba Zahara din bace. Wani mutum ne da bata sanshi ba.

“Assalamu alaikum.” Cewar mutumin.

“Wa alaikum salam.” Mama ta amsa mishi.

“Dan Allah ko Zahara Usman na ciki?” Ya tambaya.

Cikin rashin yarda, Mama ta yanke shawarar kiran mijin ta. Tambayar kanta take me kuma wannan tsohon mutumin ke nema wajen 'yarta. Mijin nata ya karaso bayan wasu yan mintuna, suka cigaba da magana da bakon.

“Zahara bata nan, ko lafiya kake son ganin ta?”

“Ko zan iya shigowa? Ina son muyi magana.”

Bayan dan dogon nazari da Abba yayi, daga karshe ya yiwa bakon iso zuwa cikin falo. Mahaifiyar Zahara ta kawo masa abin sha.

“Sunana Malam Shehu.” Cewar shi. “Nazo ne daga kauyen Na'iya. Nazo nan ne saboda 'yarku Zahara. Kuma nayi iya sauri na ganin nazo na ceci 'yarku.”

“Ka ceceta daga me?” Cewar Mahaifin Zahara. “Kan me kake magana?”

“'Yar ku Zahara tana fama da shafar aljanu.”

Kallon juna Mama da Abba suka yi. Tsawon sati biyu kenan Mama na yiwa Abba maganar amma yaki yarda, gashi yau wani mutum ya tabbatar musu. Duk da haka dai Mama zata so taji ta yaya Zahara ta gamu da aljanu.

“Ni babban Malami ne a kauyen Na'iya. Aljanar da ke jikin 'yarku sunan ta Amriya. Na santa saboda ta zauna da dadewa a kauyen mu, kuma ta haifar da masifu da dama. Na shiga neman ta tsawon watanni, sai yanzu aljanun da ke taimaka min suka kawo ni nan gidan ku. A cewar su, tana cikin jikin 'yar ku. Zahara tana dab da shiga halin da 'yan matan da Amriya ta kashe a kauyen mu suka shiga. Nazo nan ne dan kawo karshen ta da taimakon ku da taimakon 'yarku.”

“Ko zan iya magana da mai daki na, na yan mintuna?” Cewar Abba. Shi kuwa malam Shehu yace ba damuwa.

Bin bayan Abba Mama tayi zuwa cikin kitchen.
“Biyan sa kika yi dan yazo ya fada min wannan shirmen?”

“Kana tunanin zan iya yin hakan?”

“Toh ni musulmi ne, amma ba yanda za'a yi na kama karairayin mutumin nan.”

“Ba karairayi bane, ba a banza ba idan yasan sunan Zahara kuma yazo ya fada mana abinda nafi gudu a yanzun nan.”

“Sauki gare shi yanzu samun sunan mutum.” Cewar Abba.

“Ni na yarda da zancen shi, kuma zan saurare shi da abinda yazo.”

(...)

A bangaren Zahara kuwa. Godiya ta yiwa Kamal ta sauka daga motar bayan ya kawo ta unguwar su.

“Kiyi yanda na fada miki, zamu sake haduwa bayan kwana biyu insha Allahu.”

“Ok, nagode.”

Tsayawa tayi har ya tada motar, kafin ta juya ta tattaka zuwa gidan su. Ta nemi da ya ajiye ta nesa da gida saboda tana tsoron kar iyayen ta suyi zaton wani abu ganin ta sauko daga cikin motar wani. Gashi bata san me zata ce ba, na kin kwananta gida toh ina ga kuma anga wani ya sauke ta a mota. Duk da haka ta tattara kuzarin ta, ta konkwasa kofar gidan.
Mama ce ta bude mata kofa. Da tsananin mamaki Mama ke kallon ta, ganin ta sanye da Abaya.

“Mama kiyi hakuri da rashin dawowa ta gida jiya.” Zahara ta fara kai hari kafin Mama. “Zan miki bayanin komai.”

“Lafiyar ki kawai na son ji.” Cewar Mama.

Gyada kai Zahara tayi, Mama tace
“Zamu yi maganar daga baya. Yanzu akwai wani abu mai muhimmanci da nake son muyi. Zo muje.”

Rufe kofar Zahara tayi, tabi bayan Mama zuwa cikin falo. Gaishe da Abba tayi da kuma bakon shi. Zaunawa tayi kusa da Mama.

“Zahara.” Tsohon ya kira sunan ta.

“Tinda gata, ina tunanin zamu je mu fara aikin.” Tsohon ya sake fada.

Kallon Mama da ta kama mata hannu Zahara tayi.

“Akwai Aljana a tattare da ke 'yata, ya kamata muyi wani abun kafin lokaci ya kure.” Cewar Mama.

Mamaki Zahara take ta yaya suka sani, amma ganin wannan tsohon yasa tace shine zai fada musu.

“Amriya tana da karfi sosai, ta gudu koda taji alamun ina nan. Tasan ina nan shi yasa ta gudu, amma dole na maido ta ta karfi a jikin ki domin na kamata. Ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce. Zan yi iya kokari na ganin bata sake cutar da wani ba. Zan fidda ta daga rayuwar ki, dan ki samu yin rayuwa mai kyau.”

Abba tashi yayi ya bar musu falon. Zahara kuwa ta yiwa Mama kallon tambaya.

“Kar ki damu, Abban ki zai ga sauyi a tattare da ke. Ni na yarda da wannan mutumin, kuma nasan zai taimake ki.”

“Idan kun shirya, muna iya tafiya.”

“Zuwa ina?” Zahara ta tambayi tsohon a karon farko da ta bude bakin ta.

“A makabarta, a nan ne za'a yi aiki.”
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 9

⚖HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSOCIATION📚

Ammar bai daina neman Salmah kowane lungu da sakon na garin ba. Haka bai daina kiran wayar ta ba da koda yaushe ake ce masa kashe take. Har kawar ta Khadija bata samun ta a waya. Wannan lamarin ba karamin tayar masa da hankali yayi ba, bai san me zai yi ba ko a ina zai neme ta ba. Gashi gobe zai koma company, bai san ko zai iya aje hankalin sa yayi aikin ba.

Kafin yace zai aure ta, sai da ya fada mata shi bai damu da abinda tayi ba a baya, kuma har yanzu hakan yake tunani. Ya hadu da ita ya fara soyayya da ita, ta dalilin son da yake mata. Kara fadawa ma yayi sonta lokacin da ta bashi labarin rayuwar da tayi a baya. Eh tayi kura-kurai amma ta tuba ta daina, kuma Allah na son masu tuba.

Bai san ta yaya Mahaifiyar shi tayi wajen gano wannan sirrin da ya boye kasan zuciyar sa ba. Haka bai san ko Salmah zata yarda idan ya fada mata baida alaka da abinda mahaifiyar shi tayi mata, kuma zai yi iya kokarin sa ganin ya dawo da ita. Bai taba kaunar wata 'ya mace ba kamar yanda yake kaunar ta, kuma zai iya shiga mawuyacin hali idan ya rasa ta. Mahaifiyar sa, mahaifiyar sa ce ba yanda za'a yi ya iya saba mata, amma tana sa masa matsi ba kamar dan uwan sa ba. Shima yana son yin gidan kansa ya koma kamar Kamal, amma ba zai iya barin mahaifiyar su ita kadai ba. Mahaifin su mai yawan tafiye tafiye ne, ita kuwa Mommy ta daina aiki, kullum tana gida. Dama dama da cikin kannenta wata ta bata rikon 'yarta Anifa, wacce take yanzu tamkar kanwa uwa daya uba daya a gare su. Ba zai iya tafiya ya bar su su kadai ba a gidan. Wannan ne yasa ya tsaya amma yana ganin hakan kusa zuwa karshe.

Yanke shawarar neman taimakon yayan sa Kamal yayi, domin yana da hanyoyi da dama a wajen manyan mutane. Wata kila ya iya samo masa private detective da zai nemo masa inda take. Bai yarda da yan sanda ba, zasu bata masa lokaci ne daga karshe suce babu abinda zasu iya akan batan ta.

A cikin motar sa, kokarin kiran Kamal yake amma baya dauka. Bayan wasu yan mintuna sai gashi ya sake kiran shi.

“Hello..” Kamal ya fara magana.

“Hello bro ya kake? I really need you. Kana ina ne yanzu?”

“Ina gida, zaka zo ne?”

“Eh.” Ya bashi amsa kafin ya juya motar sa zuwa hanyar gidan Kamal.

Lokacin da Ammar ya karaso gidan, ya tarar da Kamal yana cikin painting wani zane.

“Salmah ta bata, na kasa samun ta a waya. Kuma na duba ko'ina ban ganta ba. Hankali na ya tashi. Bata kira ka ba?”

Ajiye brushes na zanen sa yayi, ya juyo yana fuskantar Ammar.

“Kaje gidan su ne? Ban sake ganin ta ba tun lokacin da kace na kai Zahara.” Cewar Kamal.

“Yaya Zarahan take? Ban je na ganta ba da duk wannan abun dake faruwa. Mom ta gano wasu abubuwa kan Salmah kuma hakan ba karamin tada kura yayi ba. Saboda hakan ne ta bata. Ni wallahi bansan abin yi ba.”

“Ka tambayi Khadija? Kaje gidan su? Ko kiran yan sanda muke yi?”

“Na duba ko ina na fada maka. Kuma bana son saka yan sanda a wannan lamarin. Na zo nan ne, ina son kayi min wani taimako.”

“Taimako? Zan iya taimaka maka wajen neman ta, amma bani da masaniya ko kadan akan inda take.”

“A'a ina son ka taimakamin wajen samun private detective.”

“Kana tunanin ta bace da gaske? Ba zamu iya jira na karin kwana daya ba? Ina da tabbacin tana son yin nesa da duk wannan ne, na wani lokaci, ina ganin ka daina daga hankalin ka haka. Rashin ganin ta yana da alaka da abinda ka fada min yanzu.”

“Wlh bro, ni ban san me zan yi ba yanzu.”

“Da farko, kayi kokarin samun nutsuwa. Mu karawa Salmah dan lokaci idan nan da zuwa gobe bata bayyana ba, sai mu sanar da yan sanda ko kuma mu nemi private detective.”

“Kana da gaskiya.” Cewar Ammar. “Ina ga nima zan nemi gida na koma, domin na fara gajiya da halin mom.”

“Ba zan shiga cikin lamarin ku ba. Kayi abinda kake ganin ya dace.” Cewar Kamal kafin ya juya ya cigaba da painting sa.

“Ni zan wuce gida, zan zo gobe na same ka idan na tashi ban samu labarin Salmah ba.” Ammar ya fada yana saka takalmin sa.

“Ok, amma ka kira kafin ka zo. Ina son zuwa wani wuri ne goben.”

“Ina zaka je?”
Ammar ya tambaye shi amma bai bashi amsa ba. Yanke shawarar ya tafi ya bar dan uwan nasa cikin duniyar shi mai cike da abin al'ajabi. Koda ya fito daga gidan Kamal , gida ya koma. Da nasanin dawowa gidan yayi, lokacin da mommy ta tarar da shi cikin daki taci kwalliya.

“My son ka dawo? Dazu nake tambayar Anifa take ce min ka fita tun da safe.” Cewar Mom tana mai zaunawa kusa da shi.

Tashi yayi daga kusa da ita, ya dauki computer shi.

“Ina cikin aiki ne Mom.. bana son a takura min.”

“Wane irin aiki? Tashi ka shirya muna da baki yau. Tun jiya nake son yi maka magana amma sai wani gudu na kake kamar wani karamin yaro. Ba wani lokaci mai yawa a gaban ka, je ka shirya kayi kwalliya kazo ka tarbi bakin mu.”

“Mom da alamu baki damu da damuwa ta ba. Baki ga halin da nake ciki ba? Salmah ita ce wacce nake son aure, amma jiya ta sanadin ki soyayyar mu da muka gina ta shekaru ta rushe. Idan har ba zaki iya goyon baya na ba kan abinda nake so, ina tunanin nima zan bar gidan nan kamar Kamal.”

“Oh, dan kawai na kori budurwar ka, shi ne kake son juya min baya? Kana tunanin zaka iya biya na duk wata dawainiya da na da kai? Na dauke ka a ciki na tsawon wata tara, na shayar da kai kuma na nuna maka kauna. Kai kuma da hakan zaka saka min? Yarinyar nan karuwa ce, kana tunanin idan ka aure ta, 'ya'yan ka zasu samu tarbiya mai kyau? Amma ba zaka fahimta yanzu ba, sai nan gaba idan ka samu 'ya'ya masu tarbiya zaka fahimci dalilin da yasa naki aminta da yarinyar nan.”

“Kina tunanin tarbiyar 'ya'ya ta danganta da halin mahaifiyar su ne? Muna ganin yanda mata na kwarai ke haihuwar fandararrin 'ya'ya, ko kuma malaman da ke haihuwar barayi da yan fashi. Salmah tayi kura-kurai a baya kuma ta tuba. Na rantse miki yanzu, yarinyar kirki ce, idan kika yi kokarin sanin ta da kyau zaki fahimci haka.”

“Zamu yi maganar nan daga baya, je kayi wanka ka shirya yanzu dai.”

“Ni yanzu bani da lokaci, kuma bani da bukatar tarbar bakin ki da murmushin munafunci. Bansan halin da Salmah take ciki ba a dalilin ki. Ki rabu da ni dan Allah, ki je ki ji da bakin ki ke daya.”

“Ka gani koh, dalilin yarinyar nan ka fara min rashin kunya, abinda baka taba yi ba a baya. Hakan yasa na fara tunanin bata barka haka ba.”

Mikewa Mom tayi, tace
“Bari ganin kana da kusan shekaru 33, ni mahaifiyar ka ce kuma inada iko a kanka, dan haka zaka tashi ka shirya ka same ni a falo. Ko kuma na nuna maka wani bangare na fushi na da baka san da shi ba.” Ta fada kafin ta fita daga dakin kamar yanda ta shigo.”

A BANGAREN HAFSAT

Mahaifiyar ta ta fada mata komai zai je daidai. Amma ita tafi kowa sanin waye Ammar. Ita ce mace ta karshe da zai so gani a duniyar nan kuma ya tabbatar mata da hakan haduwar su ta karshe. Ya fada mata ya gwammace mutuwa da ya aure ta. Hakan ya mata ciwo amma ita ma kanta bata bukatar auren shi. Su biyu basu taba zama a inuwa daya ba kuma bata tunanin yanzun wani abu zai sauya. Abinda yasa bata ce a'a ga auren nan ba, saboda tasan mahaifiyar ta da Hajiya Karima indai suka sa abu gaba sai sun cimma masa. Bata san me zaya biyo baya ba, amma tasan zaman su ba zai yi kyau ba. Ina ma zai yarda da auren, da kowannen su ya samu yancin sa. In yaso bayan wasu yan watanni sai su rabu, sai su cewa iyayen nasu basa jituwa ne... Kuma wani bangaren na ce mata, koda sunyi auren a irin plan din nan. Suna iya kashe junan su saboda kiyayya.

“Ke kuwa Hafsat ki dan yi kwalliya mana.” Cewar Mahaifiyar ta yayin da ta sako kafa cikin mota.

“Mom, na fa shirya, ba wani karin wata kwalliya da zan yi. Na tabbatar kawai batawa kan mu lokaci ne zamu yi.”
Cewar Hafsat kafin ta yiwa motar key.

“Je a hankali kar ki kashe ni nidai.”
Rage gudu Hafsat tayi, ta cigaba da tuki ba tare da tace wani abu ba.

“Amma Mom..”

Katse ta mahaifiyar ta tayi.
“Amma me? Ke kin fi kowa sanin dalilin da yasa zamu yi hakan. Kuma kema zaki iya amfani da wannan damar, Ammar namiji ne kyakyawa mai hankali da nutsuwa, kuma kema haka. Toh banga dalilin da zai sa ta ki daidaituwa tsakanin ku ba. Kinga daga karshe kowa zai fita da rabon shi.”

Koda tana son auren Ammar, zaman su ba zai yiwu ba. Ba zata so rayuwar da zata zauna da mijin da ba sonta yake ba dalilin abinda iyayen ta ke so. Koda hakan ta faru, zata nemi takardar saki daga baya. Bata yi tsufan da zata yi irin zaman auren nan ba, tasan zata samu miji da ta fito cikin sauki.

Sun iso gidan Alhaji Yusuf, cikin rabin awa. Hajiya Karima ce ta tarbe su, tasha kwalliya da murmushi a fuskar ta.

Bayan sun yi gaishe-gaishe, Hajiya Karima tayi musu iso cikin katon falon su, sannan tasa yan aiki suka kawo musu abinci iri-iri da abun sha.

“'Yata me yasa baki zuwa ganin mu? Nan ma ai gidan ku ne, ki dinga kawo mana ziyara mana.” Cewar Hajiya Karima tana mai zaunawa kusa da Hafsat.

“Ah, kar ki damu kawa ta, zata dinga zuwa ganin ku akai-akai. Bata samun lokaci ne saboda aiki, amma yanzu da zata zama yar gida, zata dinga samun lokacin zama da ku insha Allahu.” Cewar Mahaifiyar Hafsat.

“A'a na fahimta. Har Ammar baya da lokaci na, amma kar ku damu indai zaku kasance cikin farin ciki nima haka. Zaki iya zuwa ki ganshi yana sama in kina so. Nasan kun jima baku ga juna ba.”

Kallon mahaifiyar ta Hafsat tayi, da ita kuwa take jin tamkar ta daka tsalle dan murna. Tana tunanin wannan ce damar da zata kusanta Hafsat da Ammar, amma bata san wata hanyar da zai ci mutuncin Hafsat din bace aka bude masa.

Ok Hafsat tace tare da ajiye kofin jus din dake hannun ta sannan ta tambayi inda dakin nasa yake.

Kiran Anifa Hajiya Karima tayi, tace ta kai Hafsat dakin Ammar. Kallon Hafsat Anifa tayi sannan tace ta bi bayan ta. Sama suka nufa, ta kaita bakin kofar wani daki, cewa tayi ta tsaya a nan. Sannan ta konkwasa dakin sau biyu, kafin ta murda kofar ta shiga. Ta bar Hafsat tsaye bakin kofa tana jira.

Haushi ne ya kama Hafsat, wato dakin nasa kamar wani office dan zata ganshi sai ta jira an je an nemi izinin sa, ba zata iya jira nan ba kamar wata sakarya. Murda kofar ita ma tayi ta shiga. A kishingide yake da computer bisa gwiwan sa. Bai wani yi mamakin ganin ta ba, domin ko kallon ta bai yi ba. Ita kuwa Anifa kallon ta take na ganin bata jira tayi mata iso ba kamar yanda tace mata.

“Zaki iya tafiya Anifa, zan yi magana da shi.”
Amsawa Anifa tayi cen ciki, tare da juya zata fita, harda dan bangaje Hafsat tayi da ta bita da kallon mamaki. Hafsat na tunanin me ke damun yarinyar cen, domin bata taba yi mata irin haka ba.

“Me kike yi nan?” Cewar Ammar ba tare da ya daga kai ya kalle ta ba.

Dakin Hafsat tabi da kallo, da komai yaji tsari. Kafin tace
“Nazo ganin mijin da zan aura ne, irin tarbar da zaka yi min kenan?”

Sai a wannan karon ya dago ya kalle ta. Kafin ya mayar da kanshi jikin computer.

“Kwantar da hankalin ka, nazo nan ne saboda mahaifiyar ka ta gayyato mu.”

“Mahaifiya ta ta gayyato ku, so ki fitar min daga daki.”

“Ni kaina ban so zuwa wajen ka ba, mahaifiyar ka ce ta nemi da inzo in ganka.”

“Bai zama tilas sai kin shigo nan ba. Kina iya ki tsaya a corridor sai ki juya ki koma. Ina da ayyukan da zan yi yanzu. Dan haka kina iya tafiya.”

“Ba sai ka nuna muguntar ka ba a kaina. Nasan ba sona kake ba.”

“Baki san komai ba tinda har yanzu gaki a tsaye. Ki tafi, nan zan gane kin dauki darasin da kyau.”

“Bana son auren nan nima, idan mun hada kan mu zamu iya samun abinda muke so. Muna iya yin aure, sai mu rabu bayan wasu watanni. Iyayen mu zasu shafa mana lafiya.”

“Saboda irin wannan haukan ne bana son ki tsaya nan, ki wa girman Allah ki fita kuma kar ki sake dawowa.”

Kallon sa take ba tare da tayi wani abu ba. Tana jin tamkar ta rufe shi da duka amma bata iyawa.

“Tinda haka ne, zan tafi.”

“Da kin kyautawa kanki.” Ya fada yana cigaba da latsa keyboard na computer shi.

“Amma ka san wani abu, koda na tafi zaka samu labari na nan kusa. Ka sa wannan a ranka.”

Mikewa yayi da sauri daga kan gadon sa, ya kama hannun ta, ya jata da karfi zuwa bakin kofa. Ya tura ta waje sannan ya buga kofar da karfi.

Wannan shi ake kira cin mutunci na karshe. Kuma tayi alkawarin sai yayi nadamar yi mata hakan. Ko kuma ba sunan ta Hafsat Alhaji Abubakar ba.

-------------------------------------------------------------
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 10

⚖HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSOCIATION📚

A BANGAREN SU ZAHARA

Tafiya suke a hankali cikin duhun dare, baka jin motsin komai. Zahara ji take duk wani taku da take yi, tamkar yana tafiya da duk wani kuzarin ta ne. Mama ta rike mata hannu, amma duk haka tana jin tsoro yana kamata a hankali. Bukatar kin zuwa na kara shigar ta. Shuru da

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment