Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sakamakon buguwa da tayi a bango.

Sarat ce ta kama mata ta tashi, kusan duka mutanen wurin kuwa sun kewaye su dan ganin ko tana lafiya. Kasa tsayuwa tayi, domin zafin da kanta yake mata. Amar ne ya roki Kamal da ya rakata dakin kanwar su, kafin ta warware. Matsowa Kamal yayi kusa da ita da fuskar sa dinnan marar annuri, ya dauke ta cak ba tareda yaji nauyin ta ba. Kamal yanada girma sosai, dan haka sai Zahara ta zama tamkar gashin kaza a hannun sa. Labewa tayi cikin jikin sa, shi kuwa ya nufi stairs da ita. Zahara ta kasa fahimtar hali irin na wannan mutumin, hatta numfashin sa yana yinsa ne kamar an takura masa. A ranta tana tunanin wata kila yana yin hakan ne dan ya nesanta kanshi da mata. Dagaske kyakyawa ne shi kuma cikaken namiji... Burin kowacce mace...

Yar tafiya yayi kafin yazo kofar wani daki wanda daga corridor sai shi. Ajiyeta yayi kan gado tareda taimaka mata ta cire takalminta ba tareda wanin su yace kala ba. Kamar ma baya son kallonta.

Ajiye takalman yayi karkashin gado kafin ya juya da niyyar tafiya..

“Tsaya...” Zahara ta fada tana mai mikewa daga kan gadon da duka iya karfinta.

Tsayawa tayi gabansa tana kallon shi, shi ma kallonta yake yana jiran yaji me zata ce.

“Me yasa baka son kallona?” Ta tambaye shi tana mai kara matsowa kusanshi.

Ja baya yayi kafin yace
“Ki kwanta ki huta.”

Kokarin tafiya yayi amma ta riko hannun sa na hagu. Kallon hannayen nasu yayi tareda yi mata wani irin kallon da ya sata jan jinin jikinta.

“Ban yi...”

Tayi kokarin magana amma ta kasa, daidai lokacin wani ya konkwasa kofar dakin. Ba tareda an jira amsa ba, aka budo kofa. Wata mata ce mai tsananin kama da Amar da wata matashiyar budurwa a bayanta. Dukan su sun ga lokacin da hannun Zahara yake rike da na Kamal. Da sauri Kamal ya ja baya tareda kwace hannun sa ya fice daga dakin ba tareda ya kalli matar nan ba. Zahara taji haushin katse musu magana da matar nan tayi, amma duk haka ba komai tinda dama haduwa da matar yana cikin plan dinta.

Matsowa matar tayi tareda murmushinta ta tambayi lafiyar Zahara.

“Da sauki Mama... Kawai kafata ce ke dan yimin zafi.”

Ba wani zafi da kafarta ke yi mata, amma da yake ta shirya kicihin son ganin wannan matar ta nesanta danta da Salmah toh komai ma tace.

Taimaka mata Mommy tayi ta koma kan gado, sannan ta cewa yarta ta dauko mata man sabara da tace mata ta kawo.

“I'm so sorry kan abinda ya faru. Ban ji dadin abinda ya faru dake ba, domin Dana ya nemi da in kula da bakinsa da zasu zo, kuma ayi a gama lafiya. Cikin rashin sa'a wannan mahaukaciyar da yake kira budurwar shi ta bata komai.”

“Kar ki damu Mama, na samu sauki yanzu. Ni kawai ina so...”

Kuka Zahara ta fara dan ta karawa lamarin suga.

“Kawai ina son nace mata ta daina abinda take yi ne.”

Kara rushewa da kuka tayi, Mommy ta rungumeta tana rarrashin ta.

“Fada mini komai 'yata. Ina son sanin komai. Karki ji tsoro, ina tare da ke.”

“A'a Mama... Bana son haifar da wata matsalar. Na tabbatar zata daina idan har dagaske tana son Amar.”

“Meye zata daina? Yana da kyau in sani, farin cikin dana ne ke cikin hadari. Idan kina tsoron wani zai miki wani abun, karki damu ni zan kare ki.”

“Amar ba zai ji dadi ba..” Zahara ta fada tana goge hawaye.

“Ba abinda zai sameshi. Ni na dade ina tunanin wannan yarinyar ba mutuniyar kirki bace. Nasan tana sonshi ne kawai saboda kudin sa. Nasha mafarkin zata cutar dashi.”

“Mama nasan zaki daidaita komai, ba sai na fadi wani abun ba.”

Mommy yarinyar dake tare da ita tace ta fita dan ta samu yin magana da Zahara ba tare da wani ya katse su ba. Bayan yarinyar ta fita, Mommy tacewa Zahara ta bata labarin komai.

“Salmah unguwar mu daya da ita. Tana da samari da dama... Ban sani ba ko ya dace na fada maki, amma ina tunanin... tana biyar.. tana biyar maza...”

Waro idanu Mama tayi tare da toshe bakinta kamar wacce zata saki kara. Jin maganar Zahara ta girgizata, domin tayi tsammanin jin komai amma banda wannan.

“Lokacin da Mr. Amar yace min ita ce wacce zai aura hankali na ya tashi. Na dauka ta daina komai saboda soyayyar da takewa Mr. Amar, ashe ta cigaba da aikata wannan danyen aikin nata ba tare da Mr. Amar ya sani ba. Ban so nayi mata maganar yanzu ba, domin nayi tunanin zan iya yi mata nasihar da zata daina abinda take amma koda nayi mata, shine ta rufe ni da duka...”

Mikewa tsaye Mommy tayi amma Zahara ta riko hannun ta.

“Dan Allah Mama kar ki fadawa kowa ni miki wannan maganar, domin zan iya rasa aikina.”

“Karki damu nasan me ya rage min nayi yanzu.”

AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 7

⚖HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSOCIATION📚

Hajiya Karima matar Yusuf cike da samun nutsuwa. Daman ko ba dade ko ba jima tanada kudirin raba alakar tsakanin danta da wacce yake ikirarin yana so amma abinda yarinyar nan ta fada mata yanzu, bata bukatar hade sama da kasa ganin ta kawo karshen wannan soyayyar. A ranta tace wata kila dan nata bai san da wannan ba, da bai nemi ya aure ta ba. Wani namiji ne zai so auren "Yar gantali"? Kuma koda ma ya amince da wannan alakar, Hajiya Karima ba zata taba yarda ba, haka ma mahaifin sa Alhaji Yusuf.
Kowacce uwa zata so abun kwarai ga danta kuma tasan yar aminiyar ta ita ce wacce ta dace da Ammar. Duk da dan rawan kanta amma yarinya ce da ta samu tarbiya mai kyau daga mahaifiyar ta kuma tasan ba zata taba bada kanta ga namiji ba kafin aure.

“Zan samu baccin kirki ne kadai idan Ammar ya aure ta.” Ta fada a zuciyar ta.
Saukowa tayi daga kan stairs ta shiga neman Salmah. Bata ko bi ta kan bakin da ke kokarin gaishe ta ba. A cewar ta tanada abinda yafi wannan. Iya saurin raba danta da wannan yarinyar iya saurin samun sukunin ta.
Kusan ko'ina na wajen taron ta duba amma bata ga alamar Salmah ba. Ganin mahaifiyar shi daga nesa da alamun tana neman wani, Ammar Yusuf ya nufo inda take.
“Mama, koh Kamal kike nema? Ina tunanin har yanzu yana sama. Ya kai Fatima dan ta huta. Yanzu ma nake cewa naje na ganta.” Cewar Ammar ga mahaifiyar tashi da bata daina waige-waigen neman Salmah ba.

“Ina budurwar ka?” Mahaifiyar tashi ta tambaye shi, shi kuwa a take zuciyar sa ta wani buga.
Me yasa take neman Salmah? Ya tambayi kanshi, ganin yanda ran mahaifiyar tashi yake kamar a bace, ba idea bace mai kyau ya barta taga Salmah.
“Mama kin mini alkawarin fah ba zaki yi komai ba, a wajen walimar nan.” Dan nata yayi mata tuni cikin sigar lallaba.
“Rabu da ni..! Ka fada mini kawai idan ka ganta.”
“Nasan abinda tayi bata kyauta ba, amma nayi miki alkawarin zata baiwa Zahara hakuri, idan ta dawo hayyacin ta. Na rantse miki tayi nadama.”
“Ba zaka fada min inda yarinyar nan take bane?” Ta fada da dan daga murya wanda hakan yayi silar janyo hankalin wasu daga cikin bakin.

Ganin haka yasa Ammar ya yiwa Mahaifiyar sa jagora inda Salmah take ba dan yaso ba. Lokacin da Hajiya Karima taga Salmah kwance kan gadon danta kamar wata matar shi, dandanan yanayin fuskarta ya sauya kamar wacce aljanu suka shafa.
Salmah koda jin kofa ta bude da karfi, tayi sauri ta mike daga kan gadon. Tsoro ya dabaibaye ta ganin mahaifiyar saurayin ta. Jikin ta ya shiga rawa, ta kasa yin tsayuwa kuma ta kasa komawa ta kwanta.
Juyawa tayi ta kalli saurayin nata ko Allah yasa akwai wani taimako da zai yi mata, saidai shima duk a rude yake. Ya kasa fahimtar dalilin da yasa mahaifiyar sa ke ta duk wannan alhali tayi masa alkawarin ba zata yi wani abu ba wajen walimar shi. Addu'a yake tayi a ransa, kar ta yiwa Salmah wani abun. Sai dai ya makaro.

“Eh ai dole ki zo kiyi rashe-rashe kan gado, tinda a gidan ku kike ko a dakin mijin ki...!” Cewar Hajiya Karima rai a bace.
A rikice, Ammar ya kama hannun mahaifiyar sa, ya dan jata gefe dan suyi magana a nutse amma Hajiya Karima ta fizge hannun ta ta dumfaro inda Salmah take, da tuni ita ta fahimci lallai wannan matar ba son auren su take ba. Tuni taji kunci ya mamaye ta, a ranta tace me tayi da ta cancanci irin wannan tsana ga mahaifiyar Ammar. Tasan idan har bata amince da auren su ba, toh ba zasu taba samun kwanciyar hankali ba bayan sun yi auren.
Zuciya na mata zugi, jikin ta na rawa ta duka ta kwashi takalmin ta da nufin barin gidan baki daya.

Saidai ba wannan bane Hajiya Karima take so, bata gama magana ba.

“Ina zaki je? Ban gama magana ba da ke. Yau za'a yita ta kare. Ina son idan kika bar gidan nan, ki sa a kanki ba zan taba amincewa ba dana ya aure ki. Ta yaya kike tunanin zan amince da ke a matsayin matar dana bayan kin gama yawo a hotels din garin nan. Daina kallo na da wannan idanun naki, gaskiya ce na fada. Kin dauka ba wanda zai san da wannan danyen aikin? Duniyar nan karama ce yarinya, kar ki yi abu da tunanin wai wani ba zai sani ba.”

“Mama, dan Allah.. ki daina...”

Ammar a sanyaye yake kokarin dakatar da mahaifiyar sa, saidai ita sai da ta tabbatar da ta juye duk abinda ke ranta.

“Daina taba ni Ammar, ko kasan da yarinyar nan karuwa ce? Na tabbatar baka sani ba, dan ba zaka taba yarda ka aure ta ba. Yau na bude maka idanu ka gani ko ita wacece a zahiri. Ina son ka kawo karshen alakar ka da ita yanzu-yanzu.”

Salmah... ji tayi tamkar an daba mata wuka a kirji.
“Ammar...” Ta kira sunan sa cikin dusashiyar murya. “Ammar...ya..zaka..min..haka..?” Ta tambaye shi a sanyaye.

“Na rantse miki da Allah ba ni na fada mata ba, ki yarda da ni.”

“Ba gaskiya bane, kai kadai ne wanda na fadawa. Idan baka son aure na ne, da ka fada min tun farko ba sai daga baya kazo kaci mutunci na ba cikin dangin ka. Nasan nayi kura-kurai amma ban cancanci wannan ba.” Ta fada masa a sanyaye kafin ta bar dakin, tana kuka.

“Kenan kana sane ma? Kake son ka aure ta alhali kasan ballagaza ce? So kayi ka jawo min abun kunya koh, toh ka sani Allah baya bacci.” Ta fadawa danta dake kokarin bin bayan masoyiyar sa.

Yasan irin yadda Salmah ke shiga matsanancin kunci idan aka tuna mata da wannan bangaren mai bakin duhu na rayuwar ta. Dole taji ba dadi har ma ta tsane shi. Amma Allah ne kadai shedar shi kan sanin ba shi ya fadawa mahaifiyar shi ba. Haka bai san ya aka yi ta san da wannan labarin ba. Bai taba yiwa wani wannan zancen ba. A ranshi yace zai ji da wannan daga baya, yanzun ya kamata ya nemi inda Salmah take.

A bangaren Salmah, tafiya take a titi ba takalmi a kafar ta, ba tare da tasan inda zata je ba. Tayi da nasanin fadawa Ammar wannan zancen. Ta yarda da shi ne sosai kuma tayi tunanin ba zai taba fadawa kowa ba, amma jin maganar yanzu a bakin mahaifiyar sa ya karyar mata da zuciya. Bata taba tunanin irin wannan ranar zata riske ta ba. Amma ba wanda zata zarga sai kanta. Laifin ta ne idan an alakanta ta da hakan. Tasan dole wata rana rayuwar da tayi a baya zata yi mata dirar mikiya a sabuwar rayuwar ta amma ba zata zata yi mata ciwo ba har haka.

(...)

Lokacin da Kamal Yusuf ya fito daga cikin dakin da Zahara take, library ya nufa. Tunanin yarinyar nan ne Zahara ke ta yi masa yawo a kwanya, shi kuwa nata kokarin ganin ya yakice shi amma ya kasa. Ya saba da nuna ko in kula a harin da mata ke kawo masa, amma wannan karon, ya kusan fita hayyacin sa. Wannan yarinyar da bata ko kai sa'an kanin shi ba, tana kokarin dagula masa lissafi.

Abun ya zo masa a bazata kuma a baibai, rufe idanun sa yayi da nufin korar duk wani tunani amma muryoyin dake tashi ta window dakin dake kusa da library yasa ya kasa samun nutsuwa. Dakin da mahaifiyar shi da Zahara suke ciki ne kuma window a bude take. Mikewa yayi da niyyar barin wurin amma kukan da Zahara take ya tsayar da shi. Matsowa yayi dan ganin meke faruwa, tsaye yayi cike da mamakin jin abinda Zahara ke fadawa mahaifiyar su. Yayi matukar mamakin jin maganganun ta yanda ya kasa sanin abun yi. Yace koma me yarinyar nan ta sani game da Salmah bai dace ta fadawa Mahaifiyar su ba, balle kuma dama mahaifiyar tasu makama take nema na raba masoyan.

Ba karamin haushi Zahara ta bashi ba, kuma ya yanke shawarar seta mata zama. Ya tsani shiga harkokin wasu amma wannan karon ya shafi dan uwan shi. Ya kamata yayi wani abun. Fitowa yayi daga library ya nufi dakin da Zahara take, amma tuni mahaifiyar su ta fita neman Salmah. Tarar da Zahara yayi, tayi kwance rairan bisa gado kamar ba abinda ya faru. Haushi ne ya kara turnike shi.

“Ko kin san abinda kika aikata yanzun?” Ya tambaye ta.

Zahara ta juya ta kalli kofa, sannan ta tashi zaune a hankali tace:

“Oh..kai ne... Ka dawo..? Yauwa daman bamu karasa maganar mu ba a dazun, amma idan kana so.. zaka iya rufe kofa, dan muyi maganar da kyau.”

“Ba wannan bane ya kawo ni, me yasa kika fadawa mahaifiyar mu duk wannan?” Ya tambaye ta fuska a murtuke.

Saukowa Zahara tayi daga kan gadon a hankali ta matso inda yake. Duk da fuskar shi ba annuri, dambe yake ta yi da shedanun cikin kansa dan kar ya kalli surar jikin ta da duk ta bayyana cikin doguwar rigar ta. Sai dai lokacin da Zahara ta matso dab da Kamal Yusuf, taji duk jikin ta ya saki. Dafe kanta tayi kafin ta zube kasa.

Kamal a tunanin sa duk cikin sharrin su ne na mata yayi tsaye yana kallon ta, amma ganin sai murkususu take, hankalin sa ya tashi.

“Ka..taimake..ni..dan Allah..” Zahara take fada tana kokarin tashi.

Da sauri Kamal ya karaso inda take.

“Lafiyar ki kuwa?”

“Dan..Allah..ka taimake ni..kaina..”
Idanun ta rufe amma bata daina fadin wannan kalmar ba. Kamal durkusawa yayi ya shiga kokarin tashe ta. A hankali ta bude ido ta rufe kafin ta sake budewa da sauri tana bin dakin da kallo.

“A ina nake? Ta fada kafin ta ja jikin ta da karfi ganin namiji kusa da ita.

Sunkuyar da kai tayi, ta ga rigar da ke jikin ta. A take miyagun tunani suka ziyarci kwakwalwar ta. Ko dai kidnapping dinta aka yi? Ko kuma fyade aka mata? Tunanin da take kenan. Sai dai taji hankalin ta ya dan kwanta jin babu wani ciwo tsakanin kafafuwan ta. Kanta yayi dub, ta kasa tuna komai. Abinda kawai take iya tunawa shine, tana kokarin shiryawa zuwa wajen walima daga nan shuru.

“Are you ok?” Kamal ya tambaye ta.

Ita da har ma ta manta da shi a wurin, Zahara ta dawo hayyacin ta, nan ta gane mutumin da ke kusan ta ba kowa bane face dan uwan ogan ta. Hankalin ta taji ya dan kwanta, amma wani sabon tsoron ya sake shigan ta.

“Me nake yi a nan?” Ta tambaya tana kokarin mikewa tsaye amma jin kanta ya sara mata ta koma ta zauna.

Kamal a bangaren sa bai san me zai yi ba ganin wannan drama ta Zahara. Wani lokacin ta dawo tamkar bomb dake shirye ta watse kan kowa, wani lokacin kuma ta dawo mai sanyin hali da tsoron mutane. Yanke shawarar bin wani bangare na zuciyar shi dake son taimakawa yarinyar yayi.

Kamal zira hannayen sa yayi daidai kugunta da nufin taimaka mata ta tashi amma Zahara ta saki kara tare da cewa kar ya taba ta.

“Dan Allah.. bana so.. kar ka taba ni dan Allah..”

Wata kila ta dan ji sanyi na ganin dan uwan Mr. Ammar ne a dakin, amma har yanzu bata san me take yi a nan ba. Cikin wannan shigar.

Zahara ta kasa tuna ko kadan abinda ya faru a marecen ranar nan. Abinda kawai zata iya yi shine ta tambayi wannan mutumin duk da tasan aikin Amriya ne. Ta san ita ce ta shiga jikin ta, amma a baya koda ta shiga jikin ta idan ta dawo hayyacin ta, kusan tana iya tuna komai amma wannan karon shuru ne. Kamar wacce aka debi wani bangaren na kwakwalwarta.

“Malam dan Allah ka fada min abinda ya faru..”

Shine karon farko gare ta, da ta tsaya kusa da shi amma ba karamin haushi take ji ba da yake kallon ta a cikin wannan shigar. Bata san me tayi ba da ta kare nan kusa da shi. Tana bukatar amsoshi kafin tabin hankali ya kama ta. Tana son sanin abinda Amriya tayi.

“Kinga ina ganin kina bukatar hutu.” Ya fada yana sake kokarin taimaka mata ta tashi amma ta sake ture shi.

“Ina son sanin me ya faru please...”

“Then.. tinda kin matsa. Ban san me ya faru tsakanin ki da Salmah ba amma ta ture ki ne har kika buge kika fita hayyacin ki. Shine na kawo ki nan domin ciwon da kanki yake bayan kin fadi. Sannan mahaifiyar mu tazo ganin ki, nan ne naji kina fada mata cewa ...”

Shuru yayi, ita kuwa tsoro ya kara kamata. Tana tunanin me kuma Amriya ta aikata.

“Please ka fada min komai..”

“Kin fadawa mahaifiyar mu cewa, Salmah tana bin maza a waje. Fatan kin gane me nake nufi?”

“A'a..a'a.. ba zai yiwu ba... Ba ni na aikata hakan ba..”

“Wai kina yin kamar kin manta ne? Ko kuwa da gaske kin manta abinda kika yi?”

“Please Malam, ka taimake ni na fita daga gidan nan.”
Bata san dalilin da yasa Amriya tayi hakan ba, amma ta dau alkawarin ba zata sake bari ta cutar da wannan matar ba. Ya kamata ta bar gidan nan, kafin ta sake shiga jikin ta, ta sake aikata wani abun.

“Kina son in kai ki gidan ku ne? Amma kafin nan ina son sanin meke faruwa? Ko baki lafiya ne?”

“A'a ba zan iya zuwa gida a irin wannan shigar ba. Ka fidda ni nesa da nan kafin ta dawo, please.” Ta shiga rokon sa.

“Kafin ta dawo?”

“Zan yi maka bayanin komai, bayan mun fita daga gidan nan. Nayi maka alkawari.”

Kamal kansa ya kulle, amma duk da haka ya yanke shawarar taimakon ta. Kafin su bar gidan, ya shiga dakin kanwar su, cikin kayan ta, ya daukowa Zahara doguwar jallabiya kamar yanda Zahara ta nema, ba zata iya tashi tsaye ba sai ta canza kaya.

Fita suka yi ta kofar bayan gidan ba tare da wani ya gansu ba. Kamal komawa yayi ya dauko motar sa, ya dawo ya dauki Zahara.

Suka tayar da motar, suka bace cikin duhun dare.

-----------------------------------------------------------------



AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

CHAPTER 8

⚖HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSOCIATION📚



Fitowa tayi daga cikin daki, taci karo da Kamal zai wuce ta corridor.

“Kin tashi?” Ya tambaye ta. “Ya kike jin jikin ki?

“Na gode da nesanto da kayi daga wurin nan. Amma ina ga ni zan wuce gida.”

A tsanake yake kallon ta na wasu yan dakiku kafin ya bata amsa da katuwar muryar shi da ta kusan tsorata ta.

“Ba zaki je gida ba, kin min alkawarin zaki min bayanin komai.”

“Dan Allah, ka barni naje gida. Ina tunanin shine mafita a yanzu. Bana son na saka ka a cikin abinda bai shafe ka ba. Kuma ba lallai ba ka yarda da ni idan na fada maka abinda ke faruwa da ni. Nafi son na je gida.”
“Kina tunanin, a maida ki gidan da zan yi, labarin bai shafe ni ba tuni? Ko ba komai na cancanci wannan. Kan na yarda da abinda zaki fada mini kuwa, ba zan iya cewa komai ba tinda baki fada min komai ba. Ba zan miki alkawarin yarda da abinda zaki fada ba, amma nayi miki alkawarin zan martaba duk wata kalma da zata fito bakin ki. Muje falo, zan yi order lunch sai ki min bayanin komai.”

A ranta tunani take : A'a ba zata iya saka shi a wannan labarin ba, domin Amriya zata iya cewa ta cutar da shi. Kuma in tayi hakan bata kyauta ba. Ya kamata ta bar wurin nan da sauri.

“Zan maka bayani wani lokacin, zan je wajen aiki yanzu ne.”

Tayi masa karya dan ya barta ta tafi. Bata da tunanin zuwa wajen aiki bayan abinda Amriya ta fada a kan Salmah. Bata iya ma tunanin irin kunyar da zata ji idan taje gaban ogan ta ba. Tana jin kanta tamkar wata muguwa kan abinda Amriya tayi. Wahalar ta tsaya a ita daya, ba zata so wasu su samu matsala ba ta dalilin ta. Ya kamata tayi nesa da kowa amma bata san me zata yi ba ko ta yaya zata yi ba... Tana tsoron ta cutar da mutane fiye da yanda take yi yanzu.

“Kina da taurin kai amma ni na fiki, please, kije falo kafin nayi odan abincin. Bayan nan sai ki min bayanin komai. Kar ki damu a kaina, kawai ki fada min abinda ke faruwa da ke.”

“Bai shafe ka ba Malam..” Ta fada wannan karon da dan bacin rai. Bata san ta ina ta samu wannan kuzarin ba, amma wannan ce kadai hanyar da zai sa ya fahimci bata son saka shi a matsalar ta.

“Ya shafe ni, saboda ya shafi dangina, ba zan barki ki tafi ba dan haka kina iya ihu iya son ranki. Zaki gajiyar da kanki ne kawai.” Ya fada mata shima sannan ya cigaba da tafiyar shi zuwa kitchen kamar komai bai faru ba.

“Ba..zaka..gane ba..” Ta fada tana kokarin bin bayan shi amma shi kuma ya kara sauri ba tare da ya kula ta ba.

Kofar fita ta nufa tana kokarin budewa amma ta kasa domin a rufe take, kuma babu keys a jiki. Ganin ba sarki sai Allah dole tayi yanda yace. A sanyaye ta koma falo ta zauna a daya daga cikin kujerun falon. Tsabar haushin da ya bata yasa bata lura da manyan hotunan zane. Kusan duka falon an kawata shi da zanukan. Tana tunanin shi ke zana su ganin daga gefe akwai zanen da ba'a karasa ba. Da alamu mai son zane ne shi.

Ta kusan rabin awa zaune tana kallon zanukan. Daga karshe wani ya konkwasa kofa. Kamal ne ya fito da sauri yaje ya bude.

“Yauwa nagode.” Taji ance kafin a rufe kofar. Mikewa tayi da niyyar sake gwada sa'ar ta wannan karon ko ya barta ta tafi gida, sai dai kafin ta karasa sai gashi ya shigo falon ledoji a hannun sa. Komawa tayi ta zauna. Shi kuma ya ajiye ledojin bisa table ya koma ya fita kamar yanda ya shigo. Tana kallon sa ya cika table din da kayan ci da na sha ba tare da ya kula ta ba. Bayan kai komo mai yawa da yayi daga karshe yace mata ta fara cin abincin. Plate ya turo mata gabanta, sannan ya ajiye mata coffee mai madara. Ganin ya tsare ta da ito, ta fara cin abincin. Jinta take duk a takure dan idan ta kai loma sai ta fi minti biyar bata hada ta ba.

“Ni bana cin komai sai coffee, dan haka duk wannan ke na siyowa shi. Ki ci...” Ya umarce ta.

“Ni gida zan je, bana son hankalin iyaye na ya tashi. Basu da labarin inda nake tun jiya. Ban ma san wani hali suke ciki ba yanzu.”

Aje kofin shi yayi ya bata amsa.
“Idan kika yi saurin fada min damuwar ki, zan yi saurin barin ki kije gida. Ni zan kai ki gida.”

Taurin kai gare shi ta yanda bata tsammani. Ta lura ba zai barta ta tafi gida ba har sai ta masa maganar Amriya. Tinda hakan yake so kuwa, zata fada masa.

“A makonnin baya...” Ta fara magana bayan dogon shuru da tayi. “A makonnin baya na hadu da wata mata a bakin kogi.”

Kallon ta yayi da alamar ta cigaba yana saurare.

“Tace min sunan ta Amriya kuma tana son mu zama kawaye. Tace min kusa da gidan mu gidan su yake. Haduwa ce ta bazata da

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment