Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa dan haka dole idan bata je ba zai gane. Allah Allah take kar budurwar sa taje, domin ba zata iya hada ido da ita ba. Ga kuma dan uwan shi Mr. Kamal, idan ta kai kanta har gidan su, tasan har fitsari zata iya yi a wajen. Irin kallon nan nashi.. har yau yana zo mata a munanan mafarkan ta.

Zungurar ta da taji ana yi ne a baya ya dawo da ita hayyacin ta, ta juya taga Sarat ce.

“Wane irin kaya zaki saka?” Sarat ta rada mata a kunne ta yanda sauran ba zasu ji ba.

Har yanzu suna cikin dakin meeting, duk da an kare meeting din amma basu watse ba kowa maganar walimar yake.

“Toh yaya?” Sarat ta sake tambayar ta.

Kada mata kafada Zahara tayi alamar bata sani ba. Ita ba wasu kaya gare ta, bacin jeans da dogayen rigunan da ba zata iya zuwa wajen walimar da su ba. Dan haka kawai zata yi shigar ta ne kamar yanda ta saba. Zata je ne kawai dan a san tazo.

“Muna iya zuwa muyi chopping.” Cewar Sarat, amma Zahara taki.

“Bakauya ce ke wallahi.” Sarat ta fada tare da jan tsaki. “Toh ni cancarewa zan yi, domin nasan manyan mutane zasu halarci wannan walimar, kuma ni akwai wanda nake hari. Ina son ya fada tarkona.” Sarat ta fada.

“Humm Allah ya bada sa'a.”

“Kin tabbatar ba zaki je muje ba? Zamu iya zuwa Ahmad SH Mall.”

“Akwai abubuwa da dama da zan yi, ki huta lafiya.” Zahara ta mike tsaye da niyyar barin wurin amma wani masifaffen ciwon kai da taji yasa ta koma ta zauna da karfi ta yanda tayi sanadin janyo hankalin mutane kanta.

“Zahara, lafiya?” Mr. Amar ya tambaye ta yana mai matsowa kusa da ita.

Da sauri ita kuwa Zahara tayi baya dan kar ya taba ta. Taga irin kallon da yayi mata ganin abinda tayi, hakan kuwa bai mata dadi ba. Bata son ta zamar masa wata matsala ce alhali yana da matar zai aura.

Kara kokarin riko hannun ta yayi, amma ta sake yin tsalle tayi baya.

“Kawai na dan gaji ne, kuyi hakuri dan Allah.” Zahara ta fada tare da ficewa daga dakin meeting din kamar wata barauniya.

Ta tabbatar yau, maganar ta kawai za'a dinga yi a kamfanin. Toilet ta shiga ta rufe kanta na wani dogon lokaci. Wanke fuskar ta tayi, ta dan huta kafin ta dawo hayyacin ta. Daga karshe fitowa tayi ta nufi hanyar ofishin ta, sai dai tana fitowa taci karo da Mr. Amar, jikin ta ya bangaji faffaden kirjin sa. Hakuri ta shiga bashi akan buge shi da tayi ba tare da ta gani ba.

“Kin dan jima, kin tabbatar lafiyar ki kuwa?”

“Eh, amm..nagode. Kar ka damu. Zan je na cigaba da aiki na kafin naje gida.” Ta fada da kokarin barin wurin amma ya riko hannun ta.

Oh please! Ta fada a ranta.

“Akwai wani abu da nake son baki, zo muje ofishi na.”

Kallon ta yake jiran jin amsar da zata bashi, ita kuwa addu'a take Allah ya kawo wanda zai kwace ta. Ba zata iya zama daga ita sai shi a ofishin sa ba. Bata son yayi tunanin ko ita irin marasa kamun kan nan ce.

“Ba zaki wuce minti biyar ba, daga nan zaki iya dawowa kiyi aikin ki.”

Bayan wasu yan dakiku na nazari, ta yanke shawarar bin sa. Suna shiga ofishin taji kamar yau ne ta fara shigar sa. Windows dake kusan a rufe, ga dan duhu da ofishin yayi. Duk da tana tunanin kwalwar ta ce ke nuna mata hakan, amma tana ji a jikin ta mai ofishin nan akwai abinda yake nufi da ita.

Tana nan tsaye kai a sunkuye, Mr. CEO sai da ya dan zagaya desk din ofishin kafin ya zauna kan kujerar sa. Dukawa yayi kasa kafin na dan wani lokaci ya dago hannun sa rike da wata katuwar bakar leda da ya miko mata. Sai da ta dauki yan dakiku kafin tasa hannu ta karba tana mai masa kallon tambaya.

“Naki ne, lokacin da naje Korea bayan mun gama meeting, da na samu dan lokaci, shi ne naje nayi chopping. Da naga wannan rigar, directly da ke na tuna. Shi ne na dauko ta saboda ke. Ki saka ta yau wajen walima nasan zata yi miki kyau.” Cewar Mr. Amar

Ba yanda za'a yi ta karbi wannan kyautar tashi. Yar dariyar yake ta saki kafin tace
“Sorry Sir, amma ba zan karbi wannan rigar ba.”

“Kar ki ce ba zaki karba ba, keda ko ganin rigar baki yi ba. Kuma wa ke maida hannun ma kyauta baya?” Ya fada fuska a daure, da alamar ba zai karbi ledar ba.

“Sir, kayi hakuri ba zan iya...” Katse ta yayi

“Zahara Usman ba zan karbi wannan kyautar ba, zaki iya jefar da ita idan kina so, amma ni ledar nan ba zata koma hannu na ba.” Mr. Amar ya fada wannan karon ransa a bace.

“Ok, nagode sir. Allah ya kara budi.” Tayi masa godiya kafin ta fita daga ofishin da saurin ta ba tare da ta jira ya sake magana ba.

Da ta sani da bata bishi zuwa ofishin sa ba. Duk wannan saboda Amriya ne. Ta tsani yanda take yi da ita. Ba zata sake barinta ta dinga amfani da ita ba. Gashi tana saka ta situations wandzma bata iya fidda kanta. Tana jin tsoron abinda zata iya yi mata nan gaba, amma insha Allahu ba zata sake bari tana amfani da gangar jikin ta ba.

“Zahara, sai mun hadu a walimar ko.” Cewar Sarat dake nufar stairs.

“Saratu, tsaya!” Zahara ta kwala mata kira kafin ta kai ga shiga.

“Oh ko kin yanke shawarar zuwa chopping din ne?” Sarat ta fada da tunanin ko Zahara ta sake shawara.

“A'a.” Zahara ta bata amsa. “Kawai ina son na baki wannan ne.” Zahara ta fada tana miko mata ledar hannun ta.

Amsa Sarat tayi ba tare da jira ba, tana tambayar ta meye a ciki. Ba ta jira jin amsa ba, ta bude ta ciro wata bakar kyakyawar doguwar riga. Ita kanta Zahara bata taba ganin riga mai kyau irin wannan ba, amma bata bukatar saka ta.

“Wow... Riga ce.. rigar da take ta wulakanci a duniyar fashion ce. Kin san kuwa irin tsadarta?” A rude Sarat ke tambayar Zahara ba tare da ta sauke idonta daga kan rigar ba.

“Zaki iya daukan ta.” Zahara ta fada da dan karamin murmushi a fuskar ta.

“Tsaya, wai Zahara da gaske kike? Wasa kike mini koh? Kada ki sa min rai idan kin san ba da gaske kike ba.”

“Taki ce Sarat, na bar miki.”

(....)

A hankali baki suka fara cika gidan su Mr. Amar da aka kayatar sosai. Abokai, dangi da abokan aiki duk sun zo amsa gayyata. A wani bangare cikin falon, wasu kawaye ne biyu ke hira ba tare da sun kula da karuwar da bakin ke ta yi ba.

“Karamar yarinya ce, kuma tana da dan hasken fata. Na tabbatar zata zo nan.” Cewar Salmah ga kawarta Khadija.

“Ki manta da ita, na tabbatar tayi hakan ne dan ta tunzura ki. Idan har kika biye mata kina dab da kawo matsala a tsakanin ki da Amar.” Shawarar da Khadija ke ba kawarta kenan.

“Ni ina son Amar ya gane, wannan yarinyar ba mutuniyar kirki bace, kamar yanda take nunawa.”

“Ina kara shawarta ki da ki manta da wannan. Ki yarda da ni ba abinda zai kareki da shi. Ki mayar da hankalin ki kan sirikar ki, kiyi abinda zata yarda da auren ku.”

Tunani Salmah tayi kuma ta gane gaskiya kawarta ke fada mata. Ya kamata ta mayar da hankalin ta ga dangin saurayin ta. Amma tayi alkawarin takawa Zahara birki nan kusa.

A wani bangaren kuwa, Amar ne ke ta lallashin Kamal da yayi hakuri ya tsaya har a kare walimar. Yana son da an ci abinci ya wuce gidan shi. Duk da miskilancin sa amma ya iya zuwa wannan walimar domin karfafawa dan uwan sa gwiwa wajen bayyana Salmah a matsayin wacce zai aura a yau.

“A takure nake ta yanda baka zato yau dinnan. Kasancewar ka nan zata bani kwarin gwiwa sosai. Ba zan iyawa rikicin Mommy ba idan ka bar wajen nan, amma idan kana nan zaka iya mata magana kuma ta amince.”

“Zan tsaya amma bayan dinner tafiya ta zan yi. Ka biyo ni muje tare idan baka son kwakwazon Mom. Idan bata amince ba yau, zata amince wata rana.”

“Idan da hakan na da sauki yanda kace. Well, ba zan tsayar da kai ba. Ai zaka aje Khadija ne gidan su idan an kare?”

Amar ke tambayar dan uwan sa, shi kuwa Kamal bai jin me yake cewa domin shagala da yayi wajen kallon yarinyar da ta shigo.

Ganin dan uwan nasa bai bashi amsa ba, yabi inda yake kallo da kallo, nan ya fahimci abinda ya daukar masa da hankali. Kusan duka kallo ya koma kanta. Tayi masifar kyau a cikin doguwar riga ja da ta hade da fatarta kuma tayi matching da kirar jikinta. Galala maza ke binta da kallo, ta zama tamkar gwal tsakiyar yan kasuwa a kasuwar baje koli. Wannan janyo hankalin da tayi, yasa matan wurin suka shiga kishi da ita, ita kuwa hakan take so.

Lokacin da take gida, tana kokarin shiryawa zuwa wajen walimar da bata kaunar zuwa, lokaci guda kuma taji babu abinda take bukata kamar zuwa wajen walimar. Tamkar wani abu ya shiga jikin ta. Sosai tasan irin wannan yanayin. Amriya ce ta shiga jikinta. Ta sani domin tana jin yadda kirjinta yake mata ciwo, alhali kwana biyu lafiya kalau take. Kokowa ta shiga yi da jikin nata ganin Amriya bata yi amfani da ita ba, amma ta kasa. Domin abinda take dashi yafi karfinta nesa ba kusa ba. Lokaci guda kuma, sai ta manta da kusan komai, babu abinda take tunani da ya wuce wannan walimar.

Da yan kudin dake gareta, ta ruga kasuwa siyan kayan da zata saka zuwa wajen walimar. Amfani tayi da hakan wajen siyo wasu abubuwan, irin kayan kwalliya, kananan riguna da siket, wanduna da kuma dogayen riguna. Bayan ta koma gida, sai da ta kwashe awanni da dama tana kwaliyya kafin ta gama. Har sai da ma ta shiga cikin lokacin walimar, Sai dai hakan bai dame ta ba. Lokacin da ta gama ta fito, taci karo da mahaifinta bai ko gane ta ba. Sai da tayi magana Abba ya gane yarsa ce. Baki ya saki yana kallonta da ganin irin shigar da tayi. Ba kamar matar shi ba, shi dadi yaji ganin sauyin da 'yarshi ta samu. Ita kuwa Zahara bata tsaya wani bata lokacin zagaya gidan gwadin dress dinta ba ta fice domin tuni tayi latti. Tana sanye da takalmin ta masu tsini da kuma yar hadaddiyar karamar jakarta. Dan sahu ta tsayar, tana zuwa ta tarar da Sarat bakin kofar gidan tana kara gyara kwalliyar ta. Tana sanye da doguwar rigar da Zahara ta bata. Tuni Zahara ta shiga da nasanin bata rigar da tayi, domin idan da a jikinta take sai tafi mata kyau, amma mai faruwa ta riga da ta faru. Wata kila kuma hakan ne yafi, ko dan abinda take kokarin shiryawa a yau din.

“Kinyi kyau fa kawata.” Cewar Zahara da kokarin yaba kwalliyar Sarat.

Dago kanta daga madubin Sarat tayi, tare da kare mata kallo sama da kasa.

“Wow, wai da gaske Zahara kece?” Sarat ta fada da mamaki.

“Ni kuwa da kaina. Hadaddiya Zahara.” Zahara ta fada tana wani juyi yanda Sarat zata kare mata kallo.

“Rigata tafi tsada, amma wallahi taki tafi kyau. Gashi kin bata hakkinta!”

“Eh yo ai dole, kyau ne ya hade da kyau. Ke ma ba laifi rigar ki tana da kyau. Daga Seoul ta Kasar Korea take. Mr. Amar ne yace na baki.” Zahara tayi mata karya tana kallonta cikin ido ganin ko karyar tata tayi tasiri.

Kyafta idanu Sarat tayi tare da kara matsowa kusa da Zahara tace
“Tsaya, dan Allah dagaske kike? Amar Yusuf Dan Ladi ya baki ki bani? Kai ban yarda ba.”

“Da gaske nake, ina tunanin kina birgeshi ne.”

“Amma bai taba yimin irin wannan kallon ba. Kuma idan ina birgeshi dagaske me ya hana bai bani da kanshi ba?”

“Mai yiyuwa yana son na mashi sharen fage ne.” Zahara ta fada da dan guntun murmushin munafuncin ta.

“Oh my god, plan dina na yau ya sauya kenan. Nida nake son yau na shiryawa Alhaji Al'amin, amma abinda kika fada min yanzu, zan tunkari Mr. Amar na fada mishi nima ina sonshi.”

“Toh kiyi yaya da budurwar sa?” Zahara ta tambaye ta domin tabbatar da hakan ba zai dakatar da ita ba.

“Ina ruwana da ita. Ina ce ba aure suka yi ba? Dan haka zan kwace gurbin da dama nawa ne. Mu shiga ciki domin wajen nan akwai sanyi.”

AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 6


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo

*[📝I.W.A📝]*

Koda ta shigo cikin falon duka kallo ya koma kanta. Har wani shuru ya karade falon na wasu yan mintuna tsabar ta dauke hankalin kowa dake wurin. Duk da haushin ta da Salmah take amma tasan da tayi kyau. Juyawa tayi wajen Khadija da itama ke ta faman kallonta. Zungurar ta tayi domin maidota a duniyar zahiri. Salmah a ranta tace tanada kyau amma ba wani abun ayi ta kallon ta bane, kuma ita ba zata iya saka wannan rigar ba, domin ba wata mai tsada bace.

“Ki daina kallonta dan Allah Khadija. Kina kunyatar dani.”

Cigaba da kallon Zahara tayi na wasu yan dakiku, kafin tace
“Wai dan Allah wacece wannan yarinyar?”

“Ita ce sakatariyar Amar, na tsaneta ko cen dama, karki kara bani wata hujjar da zata sa na kara tsanar ta. Ki daina kallonta.”

“Ita ce tazo tace miki kiyi hankali da guy din ki? Hum.. inda nice ke, da zan yi hankalin. Kinga yanda take kuwa?”

“Oh mayar mana da hira baya zaki yi kenan, cen dama a dame nake. Kuma ke kika ce na manta da ita. Kenan kina nufin na yarda da abinda ta fada mini? Ni nasan Amar kuma nasan ba zai taba cin amanata ba.”

“Eh da wannan yarinyar kam, ko limamin limamai zai iya fadawa tarkonta. Amma dai...” Khadija tacewa Salmah tana kallonta.

“Mtsw, ni bansan me yasa nake ta biye miki muna maganar ta ba.”

Juyawa Salmah tayi dan ta zauna kusa da Khadija, amma taga har yanzu Khadija Zahara take kallo.

“Khadi ki daina kallonta!” Salmah ta fada da dan daga murya, amma Khadija ta riko kanta tana kokarin tirsasata sai ta kalli inda Zahara take. Kokarin kwacewa take amma koda ta tsinkayo saurayin ta ya nufi wajen Zahara, zuciyarta ta bada dam.

“Maza tashi ki je..” Khadija ke fada mata, ba tare da ta janye kallonta akan su Zahara ba.

“Kwarai kuwa zan je.” Salmah ta fada tana mikewa tsaye da sauri dan kwalinta na faduwa. Ita ma ta nufi wajen su.

Suna tsaka da magana, Salmah bata san me suke tattaunawa ba amma suna ganinta suka yi shuru.

Zuwa tayi kusa da Amar tana wani shigewa jikin sa, kafin ta juyo ta kalli Zahara tace
“Sannu Zahara'u ko?”

“Yauwa sannu Salmah. Kin yi kyau fah. Kuma Zahara sunana.”

“Humm nagode. Kema bakida laifi.” Salmah ta bata amsa da murmushin ta na munafunci.

Sarat ce ta karaso inda suke.

“Sannun ku duka.” Ta gaishe su.

Tana karasowa Amar ya dauke wuta, wani irin kallo yake binta dashi. Kallo daga sama zuwa kasa kafin ya koma ya kalli Zahara da itama shi take kallo. Kan Salmah ya daure, bata fahimci komai ba. Tana ganin raini ne a gareta. Sun sha zuwa wuri mai dauke da yan mata masu kyau amma Amar bai kallon su sai dai ya maida hankalin sa gareta. Kodai ya boye mata asalin halinsa ne tsawon wannan shekarun da suka yi? Kenan Zahara tayi gaskiya da tace mijin da zata aura ba wanda take tunani bane?

Ganin irin kallon da Khadija take masa, yasa a rikice yace
“Yauwa..sannun..ki Sarat.'”

Rikicewar da yayi ta kara sakawa Salmah shakku. Ta kasa fahimtar me yasa zuwan wannan yarinyar ya saka shi cikin wannan yanayin. Ko yana cin amanarta da ita ne? Ko kuma ya taba gwada cin amanarta da ita?

“Zan iya magana da kai na minti biyu?” Salmah ta tambaye shi.

“Eh me zai hana? Afuwan ladies.”

A hankali Salmah taja hannun sa zuwa wani bangare da babu kowa.

“Amar... ko zaka fada min meke faruwa?”

“Ke dai zaki fada min abinda ke faruwa da ke. Kina yin wani abu wanda na kasa fahimta.”

“Haka ma zaka ce? Ke dai ne ke wani abu kamar wani karamin yaro sabon shigan zuwa night club. Sai wani tadi kake da matan nan a gaba na ba tareda ka damu ba, faduwa kawai yayi saura kayi yanda kake kallon su. Na kasa fahimtar meke faruwa da kai, da ba haka kake ba.”

“Ki daina min irin wannan kallon, ni ban taba yiwa waddanan yan matan wani kallo na daban da ba na dan uwa mai kallon kannen sa ba. Salmah kece ke wani abu a yanzun nan, wannan walimar na hadata ne saboda kamfani kuma saboda na bayyanawa kowa ke a matsayin wacce zan aura, dan haka please kar ki bata komai ki samarwa kanki nutsuwa domin Mommy na na wurin nan, ya kamata ki kama jikin ki kin gane?”

“Ina son mu kare wannan maganar anan Amar, ni ba wawiya bace naga yanda kake kallon wannan yarinyar... Saratu take ko wa”

Dogon numfashi ya sauke tareda dafe kansa da hannu biyu.

“Baki ji abinda na fada miki bane ko me? Zamu iya yin maganar idan kina so amma ba anan ba. Bansan me yasa kika fara zama haka ba, na fara gajiya da wannan halin naki Saly.”

“Ba haka nake ba, idan kaga ina yi saboda ka bani hujjar yin hakan ne. Bari wani wayencewa, ni da kai mun san akwai abinda ke faruwa tsakanin ka da yarinyar cen. Toh ba'a haka dani. Na gama.”

“Kinsan wani abu. Kiyi duk abinda kike ganin ya dace.” Ya fada kafin yayi tafiyar sa.

Tayi kokarin tsayar da shi kuma taga kamar zubar da aji ne. Tasan wadannan munafukan wato Zahara da Sarat abinda suke so kenan. Tana cikin wannan tunanin nata sai ta hango Zahara na nufowa inda take. Taku take daya-daya yanda take tafiya ya kara janyo hankalin mazan wurin da dama, hakan kuwa ya kara bata ran Salmah. Ba'a taba hauda Salmah irin yau ba, domin ta lura har wata baiwa ke ga Zahara ta saka mata takaici. Tun ranar da ta fara ganinta komai ya dagule mata.

“Toh yaya..?” Zahara ta fada lokacin da ta karaso kusa da Salmah. “Da alama kin fara fahimtar abinda na fada miki. Kin kira ni da ballagaza alhali ni ankarar dake ne kawai nake son yi.”

“Ya ishe ki haka!” Salmah ta fada a hankali tana dantse hakoranta dan ta daidaita nutsuwar ta.

“Kin gani idan ana son mutum makancewa ake, ba'a ganin kuskuren shi. Kin wani dauki yardar ki kin bashi kuma na bude miki ido, amma kin kasa ganin gaskiya. Na dauka ke wayayyiya ce.”

“Zahara ya ishe ki haka....!”

“Bai ishe ni ba, kinga wannan rigar da Sarat take sanye da ita?”

Iya kokarin ta tayi dan kar ta kalli rigar amma abun yafi karfin ta. Kishi ne ya turnuke ta sosai, a hankali ta daga kai ta kalli Sarat. Tana cikin magana da wata mata.

“Rigar ta an kerata a daya daga cikin manyan fashion house. Kuma kinsan wanda ya siya mata? Ko kina son mu tambaye ta? Ok”

“Sarat dan Allah minti biyu!”

Sarat kallon su take da mamaki amma duk da haka ta nufo inda suke.

“Nasan karya kike yi, zaki iya fadar duk abinda kika ga dama amma ba zan kama ba.”

“Ni ban magana sai na tabbatar inada hujjah.”

Sarat ta karaso daidai lokacin. Komai yana tafiya daidai kamar suna bitar wasan kwaikwayon da ita Zahara ta rubuta da kanta. Salmah ji take tamkar tana a cikin film din Nollywood.

“Kawata rigarki tayi kyau, tuna mini ma waye ya siya miki?” Zahara ta tambaye ta.

Irin kallon tausayi Sarat ta yiwa Zahara, kafin tace cikin kasa da murya
“Please ki daina ba'a haka nan Zahara.”

“In daina me? Ina son nasan waye ya baki wannan rigar. Zaki fada ko a'a?”

“Saurayin ki ne ya siya mata.” Zahara ta sake fada. “Wannan rigar daga Seoul babban birnin kasar Korea take. Ba sai na tsaya yi miki wani dogon bayani ba. Nasan kwanyar ki tana aiki kuma kin fahimci daga inda ta fito.”

“Na fada miki ya ishe ki haka!” Salmah ta daka mata tsawa tare da tura ta jikin bango da iya karfin ta.

Tangal-tangal Zahara tayi bisa takalminta masu tsini kafin ta fadi kasa. Karar buguwar da kanta yayi KUMM! da bango shi yayi silar janyo hankalin duka mutanen dake wurin.

Ja baya Salmah tayi cike da mamaki da tsoron irin karfin da ta sa wajen ture Zahara. Ita kuwa Sarat da mamaki ta ture Salmah ita ma.

“Baki da hankali ne ko me?” Ta fada kafin ta duka dan taimakawa kawarta.

Mutanen wurin ne suka yo kan Zahara ganin har yanzu bata iya tashi ba. Kallon Khadija Salmah tayi dan ganin ita yanda take kallon abun, itama kuwa kallon Salmah take da mamakin me ya kaita aikata wannan abun. Matsowa tayi tare da kama hannun Salmah ta janye ta gefe.

“Me yake damun ki?” Khadija ta tambaye ta. “Kin rasa hankalin ki ne ko me? Me yasa kika ture ta irin haka?”

Salmah kokarin magana take amma hawaye sun cika mata idanu. Bata so ta ture ta ba, kawai taso ta rabu da ita ne.

“Na rantse miki Khadija ba da gangan nayi ba. Ta kai ni makura ne...”

Katseta Khadija tayi
“Hakan bai baki damar kiyi mata irin wannan turar ba. Kin manta ne? Abu na farko kar ki taba nuna iya adadin fushin ki, domin hakan zai baiwa mutane damar yi dake.”

Fashewa da kuka Salmah tayi domin tasan Khadija gaskiya ta fada mata. Kokarin rarrashin ta Khadija take amma ta kasa daina kukan. Sautin tafiya suka ji a bayan su, Salmah tasan ko waye amma kunya ba zata bari ta hada ido dashi ba.

“Khadija... Dan bamu wuri dan Allah.” Ya fada.

Khadija rada ta yi mata a kunne da ta daina kukan tare da shafa bayanta kafin ta bar wajen. Goge hawayen Salmah tayi tare da juyowa tana fuskantar shi.

“Kinga abinda kika janyo koh?”

“Ita ce ta...”
Katse ta yayi.

“Bana son jin komai. Saboda abinda kika yi ya zama doli na daga bayyanawa kowa ke a matsayin wacce zan aura zuwa wani lokacin.”

“Please ka saurare ni... Ce min tayi...”

Sake katse ta yayi
“Mommy na har ta samu labari kuma tasan ke kika yi. Kina tunanin wannan abun da kika yi yanzu zata yarda da soyayyar mu? Wannan shine burin ki? Duk abinda nayi domin mahaifiyata ta yarda da auren mu.”

A hankali yake magana kamar yanda ya saba idan yana cikin bacin rai. Salmah ta fahimci irin tabargazar da ta aikata. Duk watannin nan da suka bata wajen shawo kan mahaifiyar Amar sun tashi kan banza. Yanzu take danasanin biyewa Zahara.

“Please ka bari na yi maka bayani Amar.”

Ta fada tana mai dora hannun ta daya kan hannun sa, dayan kuma a kafadar shi. Ba tare da yaji me zata fada ba ya janye jikin sa.

“Kar ki taba ni. Ba abinda zaki fada min, inada baki masu jirana. Zaki iya zuwa bangare na ko kuma ki samu wuri ki zauna har a kare.”

Kokarin tafiya yayi amma ta rike shi da iya karfinta tare da rungume shi. Bai wani kula ta ba.

“Na rantse maka ba laifina bane. Zan iya yi maka bayanin duk abinda ya faru daga farko har karshe. Wannan yarinyar ba wacce kake tunani bace, munafuka ce da take son...”

“Ya isa haka Salmah! Ba zan yarda ki zagi yarinyar da neman yanda zata gina rayuwarta ne ya kawota nan. Bansan me yasa kika yi mata haka ba, amma ina mai baki shawarar ki je ki nemi yafiyarta bayan an kare. Ko kuma ni kaina bansan me zan yi ba.”

Ture ta yayi tare da barin wurin. Sulalewa tayi jikin bango tana kuka kamar an mata mutuwa. Ta wargaza komai yanzu, ba zai taba yafe mata ba. Dole sai ta nuna masa asalin fuskar Zahara ya gane ba wacce yake tunani bace. Idan ta kyaleta haka, zata iya rusa mata aure kuma ita ce da faduwa cikin labarin...

A bangaren Zahara kuwa, taga tsantsar hauka gun Salmah, domin bata shiryawa irin haka ba. Matsanancin ciwon kai take ji

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment