Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fiddo mata kusan rabin kirjin ta waje, sai kuma wani wando jeans da ta dade bata saka ba wanda a da take ganin ba zata iya saka shi ba, ta saka shi ya dan kame ta sosai. Yau tana ji har cikin ranta wannan wandon shi ya kamata ta saka. Bakin madubi ta koma ta karewa kanta kallo tana juye-juye, tana yaba irin matching da wandon yayi da kirar ta. Rigar kuwa da kamar zata yage saboda yanda ta matse ta, tace irin wannan babu namijin da zai sha a hannun ta. Wani abun haushi da ta tuna batada kayan kwalliya ko kadan. Tsinewa kanta tayi ta yi ba adadi, kafin ta dauki jakarta ta fito zuwa wajen aiki. Haka takalmi ma da kyar ta samu na sakawa domin a cewarta babu irin fashion din nan.

Saukowa tayi kasa, ta nufi kitchen wajen Mama.

“Hello my mamashou!!!” Da ihunta ta rungume mama.

Mama kuwa daskarewa tayi a wajen na mamakin 'yar tata da kuma yanayin shigar ta. Tsayar da aikin da take yi tayi tare da juyowa tana karewa Zahara kallo. Ba zai yiwu ba, wannan ba yarta bace. Ita da ta tsani fiddo da surar jikin ta, ta yaya zata sauya farat daya? Tunanin zucin da Mama ke yi kenan.

“Lafiyar ki kuwa Zahara?” Cewar Mama.

“Lafiya sumul nake Mama! Me yasa kika ce haka?”

“Naga kamar kin... Ban sani ba, amma yau kamar ba ke ba.” Mama ta fada cike da tsoron canjin yar tata.

“Ni din dai ce Mama.” Cewar Zahara tana dariya. “Ni ce dai Zahara, kawai yau ina ji na ne fiye da jiya. Jiya na yiwa kaina karatun ta nutsu sosai, kuma na yanke shawarar canza kaina daga sakaryar da ake kallo na! Ba murna ya kamata kiyi ba Mama?”

Mitsina kanta Mama tayi dan ganin ko mafarki take. Sai da ta dauki lokaci kafin ta fahimci meke faruwa. Lallai 'yarta ce ke mata magana, maganar ma mai tsawo kuma ba tare da ta sadda kai kasa ko kuma taji tsoron abinda take fada ba.

“Nidai Mama zan wuce wajen aiki idan ba haka ba zan yi latti. Duk kirkin ubangida na baya kaunar latti.”

Zahara fitowa tayi daga kitchen, ta baro Mama daskare a wajen cikin matukar mamaki.

Zahara kafin ta samu dan sahu, ta jawo kallo da yawa na yan unguwa, musamman maza. Dan ba wai kaya kawai ta canza ba, hatta tafiyar ta ta sauya. Duk da ba wani masifaffen kyau gareta ba, amma da yake duk inda mace zata yi shigar da zata fiddo da kirar ta haka zaka ga Maza na tuntube wajen kallonta, hatta mata ma yan uwanta.

Da tarfic da komai dan Sahu ya aje Zahara daidai bakin kofar kamfanin su cikin mintunan da basu wuce goma sha biyar ba. Gaishe da duk ma'aikacin da ta hadu dashi take. Kowannen su na mamakin sauyawar Zahara. Domin a kullum idan zata gaishe da mutum kanta kasa yake, yau kuwa sun ga abun a tsa-tsaye kuma ga wata shiga da basu taba tunanin ganinta da ita ba.

Yau ya zamana hira daya ake a kamfanin, hirar Zahara Usman sakatariyar Mr. Amar CEO. Mintuna talatin da zuwan Zahara, sai ga ubangidan ta Mr. Amar Yusuf yazo. Yanayin da yake bai sa ya lura da sauyin da sakatariyar sa ta samu ba, dalilin jiya matsalar da ya samu da mahaifiyar shi da ta tayar masa da hankali dan ya fada mata wacce yake son aure.

Gaishe shi Zahara tayi ya amsa ba tare da ya kalle ta ba yace “Please samo min coffee mai karfi.” Kafin ya shige ofishin sa.

“Toh shi kuma wannan meye matsalar shi?” Cewar Zahara tare da mikewa zuwa hado coffe.

Tana dawowa, konkwasa kofar tayi sau biyu kafin ta murda ta shiga. Tarar dashi tayi hankalin sa ga computer.

“Ga coffee din.” Ta fada tana ajewa saman table. Mr. CEO daukan coffee din yayi ya kai baki, yana kurbawa ya wani dame fuska tare da kiran Zahara dake kokarin fita.

“Wannan coffee ne? Me yasa baki sa suga ba? Kina son ki kashe ni ne ko me?” Ya fada har yanzu hankalin shi na kan computer.

“Sorry sir, amma ban taba jin coffee marar suga ya kashe mutum ba. Cewa fah kayi na hado maka coffee mai karfi.” Zahara ta fada da kusan kakkausar murya.

Dago kansa yayi cikin mamakin yanda Zahara tayi masa magana yace :

“Zahara da ni kike magana?” Ya fada da mamaki.

“Baka taba min magana da wannan sigar ba, shi yasa nima na baka amsa a hakan.” Zahara ta bashi amsa.

Amar tambayar kansa yake idan da gaske Zahara ce. Kallon Zahara yayi yaga irin shigar da tayi. Sauka idanunsa suka yi kan kirjin ta. Wata zuciyar ce ta gargade sa, Zahara kamar kanwa ce gareshi, da sauri ya sauke idanun sa.

“Toh yaya, na dauke coffee ne?”

“E..e..eh tafi dashi.” Ya fada murya na masa rawa.

“Ok, bari na hado maka wani.” Zahara ta fada kafin ta juya ta fita.

Kokawa Amar yake da tunanin sa marar kyau, da yake ingiza shi na son kallon mazaunan Zahara, amma ya kasa yin hakan. Dan daga idanun sa yayi da niyyar kallon ta, sai dai aka yi katari Zahara ta juyo suka hada ido. Signa tayi masa da ido kafin ta rufe kofar. Amar da sauri ya mike tare da bude maduban window, dan duk ac dake wurin amma zufa yake.

Meke faruwa kenan da Zahara? Tambayar da yake yiwa kansa Allah yasa ba wai maganar da suka yi bace, ta juyar mata da tunani ko kuwa da gangan ne take yi? Ba wanda za'a ce ya sauya farat daya idan ba munafuki ba ko mayaudari. Tsoro yake kar ya kasa rike kansa idan yarinyar nan tana a waje. Dan haka yafi kaunar Zahara ta da sau dubu akan wannan.

Tunani yake, ya kirkirar wa kansa abinda ba zai iya controlling ba. Sai dai ko da gaske shi ne silar wannan sauyi nata?

------------------------------------

Toh yaya fatan wannan chapter ta kayatar da ku? Idan haka ne ku nuna min a comment hakan zai kara min karfin gwiwa. Nagode 💓

AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 4


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo

*[📝I.W.A📝]*

Zahara ce tsaye a jikin madubin window tana kallon masoyan biyu dake wajen parking. Mr. Amar ne tare da budurwar sa wacce zai aura, ke ta shan firar soyayyar su. Zahara ba wai kishi bane take ji yayin kallon su, face wata murya dake ta maimaita mata a zuciya cewa wannan yarinyar ba finta kyau tayi ba. Dan haka ita ta cancanci wannan gurbi na auren Mr. Amar ba ita. Tunani take ta yanda zata yi ta bata wannan yarinya a idon Amar, amma ta kasa samun wata hanya domin bata santa ba kuma wannan karon ne ta fara ganin ta. Amma daga karshe yankewa tayi baka bukatar dalili kafin ka muzgunawa wani. Tabbatarwa kanta kuma tayi, ba wai wani abun zata yi mata ba, kawai zata yi yaki ne ganin ta maye gurbinta a wajen Amar.

“Lafiya kike ta faman murmushi?” Zahara taji an fada a bayanta.

Juyowa tayi taga Sarat ce da murmushinta na mugunta. Juyawa tayi ta cigaba da kallon masoyan da suka bar wajen parking din zuwa cafeteria. Sarat ganin sauyawar Zahara ta shiga dari-dari da ita, bama Sarat kadai ba duk wani ma'aikaci a kamfanin tsoron Zahara yake yanzu.

“Wai murmushin me kike haka?” Sarat ta sake tambayar Zahara tana mai matsowa ita ma tana leka window dan ganin me Zahara take kallo. Ganin Mr. Amar da budurwar sa dariyar keta ta kwace mata.

“Yanzu na gane dalilin kin kallo na da yake. Allah yasa na hakura da dadewa.”

“Yeah, gwara da kika yi hakan..” Cewar Zahara ba tare da ta kalli Sarat ba.

“Please ko zaki kama min na gyara library? Hajiya Rabi ce ta shiga, tana ta matsifa wai sai na gyara.”

“Ba zan iya ba, bana da ra'ayi.” Cewar Zahara har yanzu hankalin ta naga masoyan dake kokarin shiga Cafeteria.

“You are so strange kwanan nan, sai nake ji kamar ba ke ba.”

“Allah ko?” Cewar Zahara ba tare da ta fahimci me Sarat take fada ba.

“Eh, kamar an sauya ki da wata macen.”

“Kawai dan nace ba zan taya ki ba?” Zahara ta fada wannan karon ta juyo tana fuskantar Sarat.

“A'a, ina maganar sauyin da kika samu ne, domin a da ba haka kike ba...”

“Toh wa ya sani ko ni wata ce ba Zahara da kika sani ba?” Ta fada da alamun ta fara kosawa da Sarat din.

“Ha, ai hakan ba zai yiwu ba, yanzu dai kin taya ni ko a'a ba wani lokaci ba gare ni?” Cewar Sarat.

Zahara matsowa tayi kusa da Sarat ba tare da ta daina kallon ta ba. Tsoro ne ya kama Sarat ganin irin kallon da Zahara ke yi mata mai ban tsoro. Baya-baya ta shiga yi, amma Zahara ta sa hannu ta kamo kuncin ta, ta matse. Yar karar wahala Sarat ta saki tsabar zafi.

“Kin san wani abu Sarat? Ki bini a sannu. Bana son zama muguwa a kanki, kar ki tilasta ni na zama. Kina jina?”

Kokarin kwatar kanta Sarat take amma ta kasa sakamakon karfin Zahara kamar ba na mutum ba. Kuka kawai ta iya yi domin kumatun ta suna mata zafi sosai.

“Sarat kin ji ni ko baki ji ba?”

Da sauri Sarat ta gyada kan wahala. Ita kuwa Zahara murmushi ta sakar mata kamar komai bai faru ba. Sarat tsoro ne fal a ranta. Kallon Zahara take tana shafa kuncin ta. Takaici na cinta a rashin wani katabus akan Zahara da tayi. Ba wai iya karfin dantse Zahara ta nuna mata ba, har da na kwarjini domin Zahara ta cika mata idanu ta yanda zuciyar ta ke wani irin bugu wanda yasa da dafen bango ta bar wajen Zaharar.

A bangaren Mr. Amar Yusuf

Ya hadu da Salmah ne ta dalilin yayan shi Kamal. A wata rana ne, da Kamal yake dawowa daga wata tafiya ta tsawon wasu watanni da yayi. Amar ya shirya domin zuwa airport dauko shi. Da zuwan sa ya tarar da Kamal yana magana da wasu yan mata guda biyu, abinda ya bashi mamaki Kamal bai cika yawan magana ba, indai ba akan aiki bane, kuma a lokacin yana da tabbacin ba maganar aiki bane yake da yan matan. Matsawa Amar yayi kusa da su kuma ya tabbatar da yayan ne nashi.

Sallama yayi musu koda ya karasa wajen.

Bayan sun amsa sallamar Kamal yace :
“Har ka iso?”

Bai bi ta kan dan uwan nashi ba, ya gaisa da yan matan.

“Khadija, wannan dan uwana ne, sunan sa Amar.” Kamal ne ya gabatar da Amar.

Amar kallon wacce aka kira da Khadija yayi dake masa murmushi, suka sake gaisawa.

“Mu friends din dan uwan ka ne, wannan ita sunan ta Salmah.” Cewar Khadija.

“Nice to meet you Salmah..” Amar ya fada yana mata murmushi.

Daga baya ne, Kamal ke fada masa shi da Khadija sun hadu ne a Texas, ita kadai ce yar Nijar, shi yasa suka yi saurin sabo, kuma cikin ikon Allah suka fara soyayya, Khadija ita ce wacce Kamal ke iya yiwa magana ba tare da wata matsala ba.

Ita kuwa Salmah, Amar bata wani saurin birge shi ba, bai wuce sau uku bane suka hadu, shi ma idan Kamal da Khadija sun shirya haduwa ne. Amma da yake mutum ne shi mai yawan surutu da shiga rai, dandanan suka yi sabo shi da Salmah, ya karbi number ta suna waya da chatting a whatsapp kafin abin nasu ya juye zuwa soyayya mai karfi, sai dai koda ya yiwa mahaifiyar su zancen ta, ta buga kasa tace ba ita zai aura ba. Ta yiwa kawarta alkwarin zai auri 'yarta...

“Ko zuwa muke muyi mata bayani a tare? may be ta yarda da soyayyar mu? Nasan ta dan dauki zafi ne, idan ta sauko zata sa mana albarka.” Salmah ke fadawa Amar.

Shuru yayi domin yasan mahaifiyar su. Idan tana son abu, zata iya kona gari dan ta same shi.

“Please ci abincin nan kar yayi sanyi Saly.” Amar ya fada ganin ta ture plate din.

“Ni na koshi, ba zan ci ba. Ina son muyi magana akan yanda zamu bullowa mommyn ka ta yarda da auren mu.”

“Please calm down Salmah.” Ya fada tare da kama hannun ta domin rarrashin ta.

“Baka san yanda hankali na yake a tashe bane, ina tsoron ta raba ni da kai. Amar idan ka auri wata ba ni ba, zan mutu. Ba zaka iya kwatanta damuwar da nake ciki ba. Idan mahaifiyar ka bata yarda da auren mu ba, me zaka yi? Ba zamu iya aure ba albarkar ta ba.”

“Salmah ki saurare ni, koda Mahaifiyata bata son auren nan, duk da haka sai na aure ki. Kina jina? Mu kara mata lokaci, zan yi iya kokarina ganin na shawo kanta, idan kuma bata yarda ba, zamu yi auren mu domin nasan Kamal da Daddy zasu goya min baya ko mai zai faru.”

Salmah hankalin ta ya dan kwanta da abinda ya fada, duk da haka tana tsoron kar ya kasa shawo kan mahafiyar sa.

“Kici abincin Saly.”

“Bana jin yunwa. Bansan ko ka fahimci me nake son ganar da kai ba. Kayi tunani idan muka yi aure ba da yardar mahaifiyar ka ba, kuma tazo daga baya tayi duk yanda zata yi ganin ta raba mu.”
“Salmah kin dauka bansan kina diet bane?”

“Ni ba wani diet da nake yi, kawai ina traitement na wani vitamin ne kuma iya yau ne.” Ta bashi amsa tana mai kare kanta. “Kuma dan Allah ka daina canza mana magana.”

“Salmah tsayin ki 1m65 ne, nauyin ki kuma kilo 55. Ba kiba gare ki ba, kuma a hakan so kike ki kara ragewa?

“Please ka daina canza magana Amar... Haba dan Allah!”

Ranta ya fara baci, domin gani take kamar Amar bai wani damu ba sosai akan kin amincewar mahaifiyar sa. Mikewa tayi tare da daukan jakan ta zata bar wurin amma ya rike hannun ta, zata yi magana wata murya ta katse ta.

Ba kowa bace face Zahara da tana shigowa cikin cafeteria ta hangi budurwar Mr. Amar tsaye da alamar damuwa a fuskar ta. Murmushi tayi dan ta fahimci kamar fada ne suke. Matsawa tayi tare da yi musu sallama cikin wata murya mai kama da rada.

Kallon ta Salmah tayi da mamaki, ita kuwa Zahara ta jefa mata wani munafukin murmushin ta.

“How are you Sir? Daman Alhaji Bala ne yace zai yi dan lattin zuwa, nazo ne na fada maka domin nayi kokarin kiran ka ta wayar office amma baka dauka ba.”

“Eh hakane ban fito da waya bane shi yasa baki same ni ba. Zo ki zauna, me zaki ci a kawo miki?”

Kallon budurwar tashi Zahara tayi, da tuni ta koma ta zauna ta shiga cin abincin ta ba tare da ta kula su ba. Mr. Amar kallon ta yayi tare da yi mata murmushin keta kafin ya cewa Zahara ta zauna...

“A'a bana son na takura ku...” Zahara ta fada da alamar damuwa, alhali cen cikin ranta tikar rawar murna take.

“No babu takura. Zauna ki gayi me za'a kawo miki. Kinsan yana da kyau cin abinci domin lafiya, kar ki biye irin na wasu. Oh na manta, Zahara kinga Salmah, wacce zan aura, ita ce wacce na taba yi miki maganar ta.”

“Eeeh.. Anya Bamu taba maganar wata ba mai wannan sunan ba.” Cewar Zahara.

Sosai ta tuna da ranar da yayi mata maganar Salmah, amma da yake a dambe kowanne naushi halali ne, sai ta nuna masa bata taba jin sunan ba.

“Kwarai na taba yi miki maganar ta domin unguwar ku daya.” Cewar Mr. Amar

“Ta yiwu ba ni ba ce, domin ban tuna anyi hakan ba...”

“Ba damuwa idan bata tuna ba.” Cewar Salmah wannan karon, tana yiwa Zahara murmushin yake.

“Ita ce assistant dita, sunan ta Zahara. Kamar kanwa take a gare ni...”

Wani makirin murmushi Zahara tayi, a ranta tace ba kyau karya Mr. Amar. Ai bata san mutum zai iya sha'awar kanwar sa ba! Domin irin kallon da yake mata idan tana cikin office din sa, ba irin na kanwa bane.

“Eh, gaskiya kin yi dacen miji.” Zahara ta cewa Salmah.

“Humm nagode.”

“Toh me za'a kawo miki?” Cewar Amar.

“Nima ban sani ba, ban saba cin abinci anan ba. Yanzun ma saboda ku ne.”

Zahara ta fada da sigar tausayi, amma tana iya jiyo idanun Salmah a kan ta, alamar kishi.

“Toh shikenan, zaku iya kara sanin juna kafin na dawo. Ku dan bani minti biyu.”

Mikewa yayi tare da nufar kofar fita. Zahara kallon Salmah da tayi kamar hankalin ta yana ga plate din abincin ta alhali yana ga Zahara.

“Kina da kyau masha Allah.” Cewar Zahara. “Ban taba tunanin Mr. Amar yana da wacce zai aura ba. A gaskiya ban taba jin yayi maganar ki ba, amma nasan wata kila saboda wani dalili ne babba...”

“Eh..ta yiwu..”

“Mata da yawa na rubibi a kanshi, idan da bai fada musu yana da wacce zai aura ba, Allah kadai yasan me zai faru.. Kuma.. Ni bana son shiga abinda bai shafe ni ba amma ina tunanin wani lokacin yana biyewa zuciya, ya dan shakata...”

“Kinga Fatima kike ko Zahara, bansan ya ake kiran ki ba, amma nasan meye kike kokarin yi yanzu. Ni ba sakarya bace, irin wannan kinibibin ba yau aka fara yimin shi ba. Nasan saurayi na kuma nasan me zai iya aikatawa.”

“Gaskiya kin yi kuskure.” Zahara ta bata amsa. “Ina son kawai naga na ankarar dake ne, amma idan ba haka kika dauki abun ba, shikenan. Kiyi hankali kawata, karki yi sanya, domin idan ba haka ba zai subuce miki. Ni zan tafi na cigaba da aiki na.” Zahara ta fada tare da barin wurin.

Zahara na fita daga cafeteria cike da farin ciki ganin alamar maganganun ta sun yi tasiri a kunnen Salmah da tuni azababben kishi ya rufe ta. Bata yarda da zancen da Zahara ta fada mata ba, amma cen cikin ranta tana da shakku. A'a bai dace ta yarda da abinda Zahara ta fada ba, ai ita ba yarinya bace da zata bari irin maganganun nan suyi tasiri a kanta. Hakan take ta maimaitawa cikin kanta da tunanin samun nutsuwa domin har wani daukewa numfashin ta yake dan takaici.

Hango saurayin nata tayi ya taho da jakarta a hannun sa. Mikewa tayi ta nufe shi.

“Bani jaka ta, gida zan je.” Ta fada da dan fada fada.

“Ina Zahara, har taci abincin ne?”

“Meye damuwar ka Amar? Bani jakata nace!”

Amar jakar ta ya mika mata domin baya son ta tara masa mutane. Shuru-shuru ce ita wata kila amma idan ranta ya baci ba kyau.

“Muje na raka ki.”

“A'a, i zaman ka nan. Je ka gani idan Zaharaka taci abinci da kyau. Zan iya kai kaina gida, kuma kar ma ka gajiyar da kanka wajen biyo ni.”

Amar da tunanin ko maganar da suka yi dazu ce ta sanya Salmah ke wannan abun, ya yanke shawarar barinta ta tafi tare da bata dan lokaci har ta samu nutsuwa.

A gidan su Zahara kuwa, Mama ce hankalin ta a tashe na ganin sauyin Zahara, yasa ta nemi da malami kuma limamin unguwar da ya taimaka mata. Bayan yazo gidan, Mama ta bashi labarin abinda ke faruwa da 'yarta. Koda ta fara zayyana masa irin sabbin dabi'un da ta tsiro dasu, ya tabbatar da shafar aljanu ce kuma tana bukatar rukiya. Mama cike da farin ciki ta nemi da malamin ya fara rukiyar idan Zahara ta dawo. Malamin ya yarda da bukatar Mama, amma yace ta bashi awa daya zai je gida kafin Zahara ta dawo. Baya bukatar komai, kawai yana son ace Zahara tana nan.

Da fitar malam daga gidan ba'a fi rabin awa ba sai ga Zahara ta shigo gidan fuskar ta dauke da murmushi... Da saka kafar ta cikin gidan, taji wani zafi ya sauka jikin ta, fasa kara tayi tare da zubewa kasa a wurin. Mama ce ta kusan zubewa lokacin da ta tarar da Zahara kwance a kasa bata motsi.

“Zahara, Zahara” Mama ta shiga jijjigar ta domin ta tashi.

Sai da aka dau lokaci kafin Zahara ta farfado, amma tana jin duk jikin ta a mace, kuma wannan karon taji ta dawo a Zahara ta da. Kunyar Mama ce ta rufe ta ganin irin kayan dake jikin ta. Kanta kasa tacewa Mama :
“Zan hau sama.”

Taimaka mata Mama tayi ta mike tsaye amma bata barta ta tafi ba. Zahara kallon Mama tayi.

“Na dan gaji ne, nasan da na samu bacci zan warware.”

“Muje falo tukunna, daga baya kin kwanta ki huta.”

“Saboda me ?”

“Zamu yi bako ne.”

Zahara bata sake cewa komai ba, tabi bayan mahaifiyar ta. Falo suka zauna suka shiga jiran Malam.. Mintuna.. Awanni babu labarin Malam Liman, Zahara da ta gaji da jira ta bingire nan ta shiga bacci. Mama har zuwa goman dare tana jiran Malam Liman da tunanin wata kila wani abun ne ya rike shi. Dole ta hakura ta tashe da Zahara ta raka ta daki ta kwanta.

Washe gari da safe Zahara ta shirya zuwa wajen aiki, ta tarar da kusan duka gidan sun hadu cikin jimami. Tana son ta tambayi meke faruwa amma tana jin kunyar yin maganar a gaban yan gidan su. Ba tare da kowa ya lura da sauyin da ta samu yau ba, ganin kwana biyu sauyin da ta samu na saka matsatsu kaya, yin kwarkwasa da sauran su, amma yau ta dawo kamar da sanye da shigarta wadda take yi a baya kuma ta kasa daga murya tayi magana.

Ba wanda ya lura da ita, domin duka suna cikin alhinin mutuwar Malam Liman da tazo musu jiya.

Zahara sulalewa tayi ta fita zuwa wajen aikin ta. Da zuwan ta cen ta tarar da uban gidan ta. Shi da kullum take rigan shi zuwa, Zahara ta dauka tazo a latti ne, nan ta shiga ba Mr. Amar hakuri.

“Me yasa kike bani hakuri? Nazo da wuri ne yau, da yake akwai abinda zan karasa mai muhimmanci.”

Mr. Amar bai daina azawa kansa tambayoyi akan canzawar shigar sakatariyar sa ba da kuma dabi'unta. Bata iya magana sosai kamar jiya, kuma bata iya kallon sa cikin ido. Kansa ya daure! Tunani yake meke faruwa cikin wannan kankanin lokaci, wannan yarinyar akwai abin al'ajabi a tare da ita.

Zahara godiya ta yiwa uban gidan ta kafin ta nufi ofishin ta da tulin aiki ke cen yana jiran ta. Sai dai ta kasa maida hankali kan aikin domin ta kasa daina tunanin abinda ya faru kwanakin nan biyu da suka wuce. Kwarai, tana tune da komai, tasan duk abubuwan da ta aikata wanda bai dace ta aikata su ba tana cikin hayyacin ta, wani abu ya shiga jikin ta.

Tasan cewa ba kowa bace ta aikata mata hakan face Amriya kuma ko ba dade ko ba jima zata sake dawowa.

AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 5


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo

*[📝I.W.A📝]*

Kwanaki da yawa sun shude, Zahara bata sake jin wani motsin Amriya ba, babu wani sauyi da ta sake ji a kanta. Wannan shurun kuwa ba karamin tayar mata da hankali yake ba. Tana son tayi amfani da wannan shurun wajen cigaba da rayuwar ta kamar baya, amma duk lokacin da zata nufi wannan corridor sai taji kamar ana kallon ta. Sai dai ba ita kadai bace ke cikin rudu ba a wannan kamfanin. Uban gidan ta da sauran abokanan aikin ta hankalin su a tashe yake na ganin sauyin da ta samu. Sai dai ba wanda yayi gigin fadar wani abun dan kar su janyo fushin uban gidan su.

A yau, Mr. Amar Yusuf ya shirya wata yar walima a gidan su domin taya kamfani murna kan wata contact da ya samu daga kasar Korea. Mr. Amar ya nemi duk ma'aikatan su hadu a dakin meeting inda ya basu labarin nasarar da suka samu da kuma walimar da ya shirya tare da basu adreshin gidan su. Zahara da tuni ta yanke shawarar kirkiro wani abun da zai hana ta zuwa, taji Mr. Amar yace wajibi ne kowa sai ya halarta.
Bayan duk abinda ta aikata, duk abinda wannan Amriya ta aikata mata, bata jin zata iya zuwa wajen wannan walimar, amma gashi uban gidan ta yace wajibi ne sai kowane ma'aikaci yaje. Kuma ita ce sakatariyar

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment