Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ba kai ne silar damuwar ƴata ba. Kuma abu ne mai kyau da ka zo ku sasanta tsakaninku. Halin musulmin kirki ne, nayi murna sosai. Wata ƙila kai ka yi nasarar saka ta ta yi magana, hankalinmu a tashe yake.”

“Kar ki damu zan yi hakan Mama, tana ina yanzu?” Ammar ya tambaya.

“Tana ɗakinta, a sama ɗaki na ƙarshe. Kar ka biye mata idan ta gwada yin wani abun, kamar yanda na faɗa maka ba a hayyacinta take ba a halin yanzu.”

“Kar ki damu da ni Mama, nasan me zan yi."

Mahaifiyar Hafsat ta yi wa Ammar izini ya hau sama wajen Hafsat, tana addu'ar Allah yasa shi ya shawo kan ƴar tata.

Knocking yayi sau uku, sannan ya jira. Cikin ƙaramar murya Hafsat ta tambayi waye ke knocking.

“Ni ne." Ammar ya faɗa.

Cikin bacci-bacci Hafsat ta ɗauka mahaifinta ne ya yi magana. Bata yi tunanin Ammar zai yi gangancin zuwa gidansu har ƙofar ɗakinta ba, shi yasa da ta ji muryar namiji ta zata mahaifinta ne. Saidai lokacin da ta buɗe ƙofar ta yi ido huɗu da Ammar kusan faɗuwa ta yi. Ƙoƙarin rufe ƙofar ta yi amma Ammar ya yi saurin sa ƙafa ya tare ƙofar. Ƙarfi Ammar ya sa ya shigo sannan ya rufo ƙofar.

Cikin takaici, Hafsat ta juya ta koma bisa gadonta.

“Idan ka zo ne ka tsokane ni, Bismillah ga guri nan." Hafsat ta faɗa a hankali.

“Me yasa zan tsokane ki Hafsat? Kar ki ce min saboda haka ne kike gudu na?” Ammar ya tambaye ta.

“Eh ni sakarya ce, na je nayi sakarcin da bai dace ba a wurin da bai dace ba, ban ga dalilin da zai sa ba zaka tsokane ni ba? Ba abinda kullum kake min ba kenan?” Hafsat ta faɗa da shaƙaƙiyar murya.

A hankali Ammar ya ƙaraso inda take.

“Yi min wuri please, ina son muyi magana.”

Bayan dogon nazari da Hafsat ta yi, ta ƙara matsawa nesa da inda take zaune domin bashi guri ya zauna. Ammar bai yi mamaki ba da ganin hawaye cike da idanun Hafsat.

“Na taimake ki ne domin ba zai taɓa yiyuwa na ƙyale ki cikin wannan matsalar ba. Idan ina nan saboda na damu da halin da kike ciki ne, ba wai dan na yi miki izgilanci ba. Ba mutumin da kika sani a baya ba ne, stupid and dumbass. Ina son kawai na ga kin dawo daidai. Bana yin hakan domin samun wani abu daga gare ki, zan iya yin hakan ga kowace mace domin nasan adadin yanda hakan ke wargaza rayuwa.”

“Ban nemi taimako daga gare ka ba, kuma bana buƙatar tausayinka. Tambayar da nake wa kaina, yanda kasan duk wannan zancen, wa ya sani ma ko kana da hannu a ciki? Wa ya sani ko kai ne ka saka shi ya yi min barazana domin daga baya ka zo a matsayin jarumi a haka zai sa in sauko ta yanda zaka iya samu na cikin sauƙi.”

Mamakin jin abinda ta faɗa, sai da ya ɗauki lokaci kafin ya yi magana.

“Ban yi mamakin jin hakan daga gare ki ba, na ji haushin hakan sosai. Har abada tunanin yin hakan ba zai taɓa zuwa kaina ba. Na yi bincike a kanki ne saboda na damu sosai. Dole ne na fitar da ke daga nan domin kamar yanda na faɗa miki ba wanda kika sani ba ne a baya. Amma ina ga Afnan tana gaskiya, kin tsane ni kuma babu abinda zai canza hakan. Idan kin shiga wannan halin ne da tunanin zan tsokane ki kuma na sanarwa duniya abinda kika aikata, zaki iya cigaba da rayuwarki domin ni inada abubuwa mafi muhimmanci a gabana. Hankalin familynki ya tashi, dan haka kiyi wani abu domin kwantar musu da hankali.” Ya ƙarasa maganar tareda miƙewa tsaye.

“Ina mai baki haƙuri akan duk abinda nayi miki domin ina tunanin hakan ne ya sa kike tunanin zan iya komai domin na ƙuntata miki. Bugu da ƙari, ni ba wanda kika sani ba ne a baya amma hakan ina tunanin abinda ba zaki iya gwada ganewa ba ne. Na barki lafiya Hafsat. Ki kula da kanki.” Ya ƙara da hakan kafin ya bar ɗakin.

Hafsat bata san ma me zata yi tunani ba, wannan mutumin ya taimake ta da gaske amma ta kasa daina tambayar kanta dalili, ganin basu taɓa jituwa daidai da rana ɗaya ba. Tana tambayar kanta me yasa lokaci guda yake son shiga al'amuranta. Tana tunanin ta wuce iyaka na zarginsa da ta yi amma ta yi hakan ne kawai domin kare kanta daga tsokanar da zai yi mata. Bata son saurarar muryar da ke ta mata yawo cikin kai akan cewa wannan mutumin ya sauya. Bata son sauke makamai kuma ta sake faɗawa wani tarkon. Ta cutu iya haka, ya kamata ta yi nesa da maza a halin yanzu, har sai ta dawo hayyacinta.


To be continued....


AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story📖

By Malik al-Ashtar 🖋


CHAPTER 35

I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 35 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”

http://www.ashblogg.com.ng/2022/04/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-35.html



Zahara bata san ina take ba, bata san wace rana ba ce yau ko wane lokaci ne yanzu, abinda ta sani kawai tana wani guri ne...a cikin duniyar nan. A razane take sosai da yasa bata iya yin wani ƙwaƙwaran tunani. Tsawon kwanaki take nan, a cikin wannan ɗakin, bata cin komai, bata shan komai kuma abinda yafi bata mamaki shine bata jin yunwa. Bacci kawai take yi idan ta tashi da ƙyar take iya yin wani tunani. Tunanin tafiya gida ko kaɗan baya zuwa kanta.

Wannan ranar, wani abu ya sauya... Wannan ranar koda ta farka, ta ji alamun mutum kusa da ita saidai bata tsorata ba. Kamar ƙiftawar ido wata mata ta bayyana a gabanta. Ta gane Aisha ce, matashiyar matar nan da ta haɗu da ita bakin kogi ƴar ƙawar mahaifiyarta da aka ce ta rasu. Duk da kiɗemewar da take ciki, Zahara ta fahimci ko wa ke bayan duk wannan. Da sauri ta duba hannunta, nan ta ga babu laya ɗaure a hannunta. Komai ya dawo mata a bayyane yanzu.

“Kin tashi?” Amriya ta tambaye ta tana zaunawa kusa da ita.

Zahara so tayi ta tashi ta matsa daga inda Amriya take amma ta kasa. Murmushin Amriya ya tabbatar mata da ita ce silar sandarewarta.

“Me yasa kike son yin nesa da ni? Me yasa kike gudu na Zahara? Alhali inada kirki kuma babu abinda nake so face farin cikinki.”

Zahara bata ce komai ba sai ma ƙoƙarin karanto addu'o'i da ta yi domin kare kanta tunda babu abinda zata iya da ƙarfinta. Lokaci guda wani kuzari da bata san da shi ba ya ziyarci Zahara, ta tambaye ta :
“Me kike so da ni Amriya?”

Murmushi aljanar ta yi, kafin ta fara ɓaɓɓaka dariya.

“Wayyoh nii!” Amriya ta faɗa tana ƙoƙarin tsayar da dariyarta. “Kawai ina son na nuna miki ne, na nunawa sauran babu wanda ya isa ya ja da ni. Idan ina son abu, ina samun shi. Kawai ina son ki gane ba zaki iya guje min ba kuma ko ba daɗe ko ba jima zan zo na neme ki. Kin so ki guje min kuma ki halaka ni amma gashi na dawo da ƙarfi fiye da da.”

Shafa fuskar Zahara Amriya ta yi. Ita kuwa Zahara da sauri ta ja baya.

“Tsoro kike ji? Ki daina ! Ba zan cutar da ke ba, ban taɓa cutar da wanda yake tare da ni ba.”

“Kin yi kuskure, bana tare da ke kuma ba zan amince ki tsare ni nan kamar wata fursuna ba...”

Dariya Amriya ta yi, ita kuwa Zahara bata iya jurar ganin yanda Amriya ke nishaɗi.

“Na ga ko motsi baki iya yi, kamar ɓera haka kike cikin tarko. Ni kaɗai ce wacce nake iya fitar da ke daga nan. Saidai kin ga ni... bani da burin barin ki ki tafi.”

Miƙewa tsaye Amriya ta yi ta shiga zagayen ɗakin da babu komai cikinsa, sai baƙaƙen labulaye kuma Zahara ta kasa fahimtar me ya kawo wannan tarin labuyen alhali babu taga ko ɗaya.

“Ban san dalilin da yasa baku son na zauna cikin rayuwarku ba... Ni kawai ina son a so ni ne kamar yanda ya so ni...” Amriya ta faɗa tana kallon bango.

Zahara cikin shakku, tayi amfani da wannan damar domin ƙara sani game da wannan aljanar.

“Waye shi?” Zahara ta tambaye ta.

Amriya da ta faɗa duniyar tunani, tuna wasu abubuwa na wannan mutumin ya sa murmushi ya ƙwace mata.

“Kin san wani abu Zahara, mu aljanu muna da saurin manta abu amma ni yau tsawon ƙarnika da dama kenan amma na kasa mantawa. Na so shi, so ba kaɗan ba... amma suka raba ni da shi.”

Son jin labari irin na Zahara, yasa take son jin na Amriya.

“Zaki iya min bayani, wata ƙila na fahimci irin yanda kike ji.” Zahara ta faɗa.

Wani mugun kallo Amriya ta watsowa Zahara. “Ta yaya ke bil'adama zaki iya fahimtar abinda ni aljana nake ji. Duk haka kuke, munafukai kuma masu son kai ! Kasancewar ku halittun da Allah yafi so, ba shi ke baku damar ku cutar da mu ba.”

Zahara ji ta yi tana son ta faɗa mata a yanzun, ita ce ke cutar da ita ba wai ita Zahara ba. Saidai ta yi shuru ganin irin zafin da Amriya ta ɗauka, faɗar hakan zai ƙara harzuƙa ta ne.

“Ke kin ɗan banbanta... shi yasa nake nan tare da ke. Ina son mu zama ahali. Ina son kiyi taimako ni ma kuma na dinga biya miki duk wata buƙata da kike so..."

“Ni gida kawai nake so...” Zahara ta faɗa kasa da murya.

“Eh zaki koma gida my dear.” Amriya ta faɗa kare da ƙara matsowa kusa da Zahara. “Zaki koma gidanku amma ki sani...rayuwarki na hannuna. Zaki yi abinda kawai nake son ki yi kuma zaki faɗi abinda kawai nake son ki faɗa. Hakan bai fi ba tsakanin mu?"

“Me yasa sai ni?” Zahara ta tambaye ta ƙwalla sun ciko mata ido, ta ɗan zauna da Amriya kuma ta san abinda take iya aikatawa.

“Na faɗa miki Zahara, ki ƙara haƙurin jira. Ke daban kike da sauran, muna ganewa juna ni da ke. Na yafe miki duk wani abu da kika min baya, nasan mahaifiyarki ce ta so raba ni da ke amma kamar yanda na ce babu wanda yake iya tsayar da ni. Wannan tsohon ɗan tsubbu, ya naɗe ku ne kawai a baibai.”

Shuru Zahara ta yi, ta kasa motsi. Tana tunanin me ya faru da wannan tsohon da ya bata layar nan, shin ko Amriya ta kashe shi ne. Ba ma ta da ƙwarin gwiwar tunanin abinda Amriya ta aikata mishi.

Kamar ta karanta tunaninta, aljanar tace mata :

“Na tabbatar a halin da yake ciki yanzu yafi gwammace mutuwar ma. Ai sai da na gargaɗe shi amma bai saurare ni ba, nafi ƙarfin duka aljanun da yake tare da su. Ko mahaifina bai iya yin komai a kaina... Yana daga cikin maƙiyana amma sanadin alaƙar da ke tsakanina da shi a baya yasa ban yi masa komai ba!”

Amriya ta ƙara da cewa : “Yanzu mu daina tuna baya, mu saka gobe da ke jiran mu a gabanmu. Kamar yanda na ce ɗazu, zan bar ki ki tafi a madadin haka zaki zama baiwata.” Ta ce wa Zahara da murmushinta na mugunta da ya ƙara tsorata Zahara.

Bata san a me ta ƙara jefa kanta ba amma tasan wannan karon zai yi mata wahalar fita. Tana jin tsoro, tsoro sosai amma batada wani zaɓi da ya wuce amincewa ko bin umarnin Amriya dan gudun kar ta cutar da mutanen da take so.




ƁANGAREN KAMAL

Kamar koda yaushe tun bayan ɓatan Zahara, bayan ya yi wanka kuma ya yi sallah Kamal ya shirya fita cigaba da neman Zahara. Tsawon makonni kenan amma ya ƙi ya haƙura. Ya kan ce idan wata rana ya tashi bai nemi Zahara ba tamkar ya jefar da ita ne.

Hakan yasa, da farko baida lokacin kulawa da Khadija da har ya kai su ga yin faɗa. Khadija tana zarginsa da cigaba da maƙalewa Zahara alhali sun rabu. Amma gudun duk wani tashin hankali, Kamal ya tsara lokacin kula da budurwarsa da kuma neman Zahara ba tare da Khadija ta sani ba...

Koda ya saka ƙafa waje da niyyar zuwa wajen motarsa, ya ga mahaifiyarsa Hajiya Karima tsaye bakin ƙofarshi. Yayi mamaki sosai da ganin ta.

“Mom.. lafiya?” Ya tambaye ta.

Rungume ɗanta Hajiya Karima ta yi na tsayin wani lokaci.

“Dole sai na sa ƙarfi kafin na samu wannan rungumar?” Ta tambayi ɗan nata.

“Mu shiga daga ciki.”

Jagora Kamal ya yi wa mahaifiyar tashi cikin falo sannan ya zauna kusa da ita. Yanzu da yake gabanta, sai yake ta dana sanin barin ta. Matsalolin da yake da, yasa gaba ɗaya ya manta da shari'ar mahaifinsu da Afnan. Haka ya manta da rashin jituwar da ke tsakaninta da Ammar.

“Mahaifiyarku ce ni amma tsawon watanni kenan rabon da na ji ɗuriyarku. Mun samu saɓanin fahimta amma ban yi tunanin zaku nuna ko in kula ba a kaina har haka.”

Hajiya Karima ta yi alƙawarin ba zata yi kuka ba, amma faɗar wannan kalaman ya tuna mata adadin yanda abun ke cin ta a zuciya.

“Ni ai ina kiran ki lokaci zuwa lokaci. Kawai dai..”

“Kana tunanin hakan kaɗai ya isa?”

“Muna da matsaloli ne da dama a halin yanzu. Amma kina ranmu.”

“Ba wai juya min baya da kuka yi ba, zai sa matsalolinku su gyaru. Ammar yana tunanin yin nesa da ni zai sa ya fi jin daɗin rayuwa amma ni uwa ce kuma kowa ya san yanda uwa take da daraja. Yanzu a shirye nake na yi komai ganin na dawo da ƴaƴana kuma na yi rayuwa mai kwanciyar hankali."

“Akwai wuyar faɗa amma Mom kin san ba komai zai koma daidai ba bayan abinda Daddy ya aikata, ba zamu iya yin kamar komai bai faru ba !”

“Zaku iya yin..."

Katse ta Kamal ya yi : “Mom, jiya Ammar ya kira ni domin yi min maganar hujjojin da detective ɗinsa ya samo, Daddy ya yi ƙoƙarin kawar da komai amma da yake idan Allah ya so hukunta ka babu abinda kake iya yi domin gujewa hukuncinka. Muna respecting yanda kike kare Daddy amma wani lokacin yanada kyau buɗe ido kan wasu abubuwan kafin su jagule daga baya a zo ana nadama.”

“Wane irin hujjoji?” Hajiya Karima ta faɗa ƙasa da murya.

“Kiyi haƙuri amma babu abinda nake iya faɗa miki.”

Shuru Hajiya Karima ta yi, tana son ta faɗa masa abinda ta sani akan shari'a ta gaba, tana tsoron ƙarasa ruguje alaƙar mijinta da ƴaƴanta. Saidai a nan ta tuna, ta rufe ido akan abubuwa da dama a baya amma wannan idan tayi, zata yi nadama kamar yanda ɗan nata yace.

“Zan faɗa maka wani abu ɗana amma ka yi min alƙawarin zaka kalli maganar da hikima kamar yanda ka saba?”

“Kin san ni, bana yin abu farat ɗaya, ba kamar idan abun mai muhimmanci ne dan haka zaki iya faɗa min."

Ajiyar zuciya Hajiya Karima ta yi, tana shirin bayyana abinda ta sani. Abubuwa da dama zasu sauya bayan ta furta wannan maganar. Amma hakan shine mafita da a ce daga baya ta zo tana nadama.

“Mahaifinku zai bai wa alƙali cin hanci.”

“Kin tabbatar da abinda kike faɗa kuwa Mom?" Kamal ya tambayi mahaifiyar tashi.

“Na tabbatar, shi ya faɗa min. Har ya faɗa min sunan alƙalin Malam Yahaya.. bansan wannan Yahayan ba, amma abinda na fahimta abokanai ne su."

“It's very serious abinda kike faɗa min Mom, ya kamata mu yi magana da Ammar. Ya kamata mu yi wani abun domin dakatar da shi ! Ko kin shirya zuwa wajen Ammar ɗin yanzu?”

“Ban sani ba ko tunani ne mai kyau, na tabbatar har yanzu yana fushi da ni kuma bana son daɗewa waje idan ba haka ba Daddynku zai yi tunanin wani abu !”

“Kina da gaskiya, sai mun yi taka tsantsan. Kar ki damu Mom na tabbatar zai dawo da kanshi gare ki.”

“Ina fata Allah ya sa komai ya tafi daidai. Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu. Ni zan tafi yanzu." Ta faɗa tare da miƙewa.

“Bari na raka ki.” Cewar Kamal.

“A'a kar ka damu, zan iya zuwa ni kaɗai. Ka kula da kanka !"

Yanzu Kamal ya san me ya rage masa ya yi.


To be continued...
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels


4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment