Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗazu yake jira. Ɗaga kiran ya yi ba ɓata lokaci. Wanda ya kira shi yana ƙoƙarin gaishe shi Ammar yace
“Please Farouk mu ajiye gaishe-gaishen nan. Faɗa min komai ko hankalina zai kwanta.”

“Ok." Cewar wanda ya kira da Farouk. “Na samu bayanai da yawa cikin ƙanƙanin lokacin nan. Sai da ma nayi hacking duka wayoyinta. Na ɓata duka daren jiya ina karanta chatting ɗinta. Fatan dai ba zata ji haushina ba?”

“Ina jinka Faruk, ka faɗa min abinda nake son ji kawai.” Ammar ya faɗa tare da zaunawa dan kar ya faɗi.

“Ina tunanin abu ne da zamu iya saurin shawo kansa. Ta haɗu da wani saurayi ne a cikin gari... Suna magana amma kuma suna exchanging nude pics sosai. Saidai saurayin ya fara yi mata barazana lokacin da ya gano ƴar gidan mai Shakur Company ce. Da fari tana yin abinda suka ce, saidai a hankali ta fara yi musu tawaye, hakan kuwa ya sa abun ya juya kanta. Saurayin ya fara bibiyarta har zuwa ranar da ta zo gidan yayanka mutanen sun doke ta kuma sun mata barazanar zasu dawo idan ta faɗawa wani. Yanzu haka suna son ta same su a hotel ran asabar.”


“What? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Ammar ya faɗa cikin tashin hankali.

“Bana tunanin babu abinda mutanen nan zasu yi mata. Amma inada sunan saurayin da kuma adress ɗinsa. Zamu iya cafke shi da mutanensa.”

“Nagode sosai da wannan aikin naka Farouk. Ka turo min duk wani abu da ka samu, zan turo maka ladan aikinka zuwa gobe. Ni zan ji da sauran.”

“Game da mahaifinka kuwa, zan yi maka bayani zuwa gaba idan mun haɗu. Har yanzu ina kan abinda muka tattauna a baya.”

“Ok, nagode Farouk. Na yarda da kai. Sai mun haɗun."

Ya kasa yarda har yanzu ana yin irin wannan abun. Bai taɓa tunanin Hafsat zata aikata hakan ba. Ta iya turawa wani hotunan tsiraicinta har ya yi mata barazana da su. Dole shine zai gyara komai tun da har ya saka kansa tsundum a ciki.

Hafsat zata ƙara tsanar sa idan ta san ya shiga rayuwarta amma idan hakan shi zai yi ya ceto ta, a shirye yake ya sake maimaitawa.


ƁANGAREN KHADIJA

Gaban madubi take tana shiryawa rai a jagule. Da ƙyar take iya jiyo me aminiyarta take cewa. Tana tunanin yanda zata yi ta cire layar hannun Zahara. Bata san meye amfanin wannan layar ko abinda yasa Amriya take son ta cire ta ba. Abinda kawai ta sani, shi ne ba zata so ta shiga tsama da wannan aljanar ba.

“Idan na matsa miki, faɗa min ya kamata ki yi Khadija.”

Juyowa ta yi ta kalli Salmah.

“A'a wallahi..ina sauraron ki.. kawai na ɗan yi nisa cikin tunani ne.”

“Ina faɗa miki, Mansoor ya nemi da na yi tunani akan tayin da ya yi min. Yace min yana son mu tsayar da magana kafin ya koma USA. Ni yana burge ni, kuma na san idan muka yi aure zan kamu da son shi, guy ɗin ne ya haɗu sosai. Amma ina tunanin anya zan iya jiran sa har na shekara ɗaya... Yace min zai yi iya ƙoƙarinsa ganin na je cen nima. Amma bana tunanin son ƙara barin garin nan.”

Miƙewa Khadija ta yi wannan karon !

“I'm sorry Salmah.. amma inada abubuwa da dama cikin kaina... Ban san me zan yi ba. Yanzun ma fita nake son yi amma zan dawo ba da jimawa ba, na yi miki alƙawari."

“Ina zaki je? Me yasa baki faɗamin komai ba? Lafiya babyn yake? Kina saka ni cikin damuwa Khadija." Cewar Salmah tana saukowa daga bisa gado.

“Kar ki damu, zan ji da komai. Na yi alƙawarin da komai ya tafi daidai zan baki labarin komai.” Khadija ta faɗawa ƙawar tata ba tare da ta yi mata wani ƙarin bayani ba.

Fita ta yi ta bar Salmah zaune cikin damuwa da ruɗu.


ƁANGAREN ZAHARA

Zahara ce ta fito daga office. Yinin yau sam bai mata daɗi ba, sai ma da ta ga Khadija tsaye bakin motarta tana jiranta. Ta yanke yin kamar bata ganta ba saidai tuni ta makaro domin Khadija ce ta ƙaraso inda take da sauri.

“Cen saurayinki... yanzu kuma ke...gaba kuma waye zai zo?”

Khadija jin saurayinta yazo gurin yarinyar nan, ta ji kalaman tamkar sukar wuƙa. Sai da ta jajurce kafin ta iya controling fushinta gaban Zahara. Ta zo ne aiwatar da wani aiki, dan haka ba zata so yin abinda zai kawo mata cikas ba.

“Ban zo nan dan faɗa ba, na zo ne mu yi magana."

“Babu maganar da zamu yi, yanzu na fito daga aiki kamar yanda kike gani, a gajiye nake dan haka ki min afuwa, bana da lokacin yin magana yanzu.” Zahara ta faɗa kafin ta gifta ta gaban Khadija da niyyar wucewa. Saidai Khadija ta fizgo hannunta da sauri.

“Please ki bani mintuna goma, ba daɗi ba ragi.”

Numfashi Zahara ta ja na wasu ƴan daƙiƙu kafin duk da haka ta yanke tafiya. Ba zai yiwu ta tsaya saurarar wannan matar ta faɗa abinda ita kaɗai ta sani ba.

“Wata ƙila ki yi nadamar tafiya ba tare da kin ji me zan faɗamiki ba."

Tsayawa Zahara ta yi, ta juyo a fusace.

“Barazana kike min yanzu? Ki saurare ni da kyau, ba zan bari a taka ni ba, ko ki tafi kowa ya je gida lafiya, ko ki tsaya ki ga ɓacin rai iya ɓacin rai.” Zahara ta faɗa da yanayin da ita ma bata san shi da ita ba.

“Me kike yi nan Khadija?”

Suka ji wata murya ta faɗa a bayansu. Dukansu sun san me wannan muryar ba kowa ba ne face Ammar.

Ja baya Khadija ta yi tare da kallonsa ta yi murmushi wanda da ka gani ka san ƙirƙirar sa ta yi.

“Na zo ne na ga Zahara..”

“Ko na kira Kamal ne?” Ammar ya tambaye ta.

“A'a... Tafiya ma zan yi yanzu. Zamu haɗu an jima.” Khadija ta faɗa tare da juyawa.

Komai ya tafi da sauri da ya sa Zahara bata san Khadija ta fizge layar hannunta ba.

Ammar tambayar Zahara ya yi da kallo. Ya san duka me yake faruwa amma baya son saka baki ne.


“Ko na zo na ajiye ki gida ne?” Ammar ya ce wa Zahara.

“A'a.” Ta bashi amsa tare da nufar bakin titi inda zata tari mai adaidaita.


To be continued...

AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story📖

By Malik al-Ashtar ??


CHAPTER 33

I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 33 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”

http://www.ashblogg.com.ng/2022/03/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-33.html


“Ƴata, na roƙe ku, ku dawooo min da ƴata.” Abinda mahaifiyar Zahara ke ta nanatawa kenan.

“Dan Allah Mama ki kwantar da hankalinki, Zahara zata dawo...”

Maryam ce ke ƙoƙarin lallashin mahaifiyar ƙawar tata amma ko ita bata yarda da abinda take faɗa ba.

“A'a ba gaskiya ba ne. Tsawon kwanaki kenan da ɓatanta. Na tabbatar wani abu ya faru da ita. Ilhamar uwa ba zata min ƙarya ba.”

Ƙoƙarin kwantar da ita kan doguwar kujera Maryam ta yi amma Mama na ta kokowa da iya ƙarfinta da yasa mutanen da ke falon gane bata son a taɓa ta. Mahaifin Zahara bai iya jurar ganin matarsa cikin wannan yanayin kuma bai san me zai yi ba domin ya rarrashe ta. Ya yi nema ko'ina cikin gari : wajen aikinta, bakin kogi amma babu labarin Zahara. Tunani na ban tsoro iri-iri na ta ziyartar ƙwaƙwalwarsa : Kidnapping, kisa, fyaɗe. Tunanin ƴarsa cikin halin rashin kariya kaɗai na ɗaga masa hankali. Babu wanda ya fahimci abinda ya faru. Wata safiya, ta tashi daga bacci, ta cewa ƴan gidan zata fita ta ɗan sha iska kamar yanda ta saba idan bata jin daɗi. Babu wanda ya yi tunanin ba zata dawo ba. Ta saba irin wannan fitar amma bata taɓa wuce awa biyu zuwa uku ba.

Hankalin kowa ya tashi. A ɗaya ɓangaren kuwa, Kamal ne ke bin lungu da sako na garin Maradi neman Zahara. Bai yi bacci ba tun jiya ga gajiya kuma ta fara haye masa. Accident ya kusan yi, nan ya fahimci ya kamata ya tsaya ya huta kafin ya cigaba da neman ta. Ba amfanin komai gajiyar da kai idan ba zai iya tsayawa ya yi tunani mai kyau ba.

Haɗa sauran kuzarin da ya rage masa ya yi ya nufi gidansa. Lokacin da ya isa ƙofar gidansa, ya tarar da ɗan uwansa da shi ma yanzu ya fito daga motarsa. Gaisawa suka yi a tsaitsaye kafin ya shigewarsa cikin gidan ba tare da yace komai ba. Bin bayansa Ammar ya yi. Ya san adadin yanda Kamal yake cikin ruɗu a halin yanzu. Rufo ƙofar ya yi bayan ya shigo, ya zauna kan kujera a falo. Bayan kamar rabin awa sai ga Kamal ya fito da alamu wanka ya yi amma bai sauya kayan jikinsa ba kuma har yanzu akwai alamar gajiya a idanunsa.

“Ka dawo hayyacinka Kamal, na tabbatar za'a gan ta.” Cewar Ammar.

“Na fara fidda rai akan hakan. Na neme ta ko'ina. Ba wani wuri take zuwa ba sosai, ban ga me zai sa a kasa ganinta ba. Hankalin mahaifiyarta ya tashi sosai.”

“Akwai al'ajabi a wannan lamarin !”

Kallon sa Kamal ya yi bai ce komai ba. Da sauri ya duba wayarshi ya ga missed calls da dama na Khadija sai dai ba ta ita yake ba, ya yanke shawarar sake komawa neman Zahara.

“Ko zaka taya ni ne?” Ya tambayi Ammar.

“No.. akwai wani guri da zan je.” Ya bashi amsa.

Kamal ya ga ɗan uwansa ba yanda ya saba ganin sa ba amma sai bai yi masa magana ba kuma ma baida lokacin wani binciken daban. A ɓangaren Ammar, yana ƙoƙarin shi da wasu mutanen Farouk gyara lamarin Hafsat.

“Shikenan.. ni na tafi.”

“Ka kula da kanka Kamal, ka ci abinci sannan ka huta.” Ammar ya bashi shawara.

Gyaɗa masa kai Kamal ya yi sannan ya tafi. Ammar ya isa wajen meeting ɗin cikin ƙanƙanin lokaci inda Farouk yake jira shi da mutanensa huɗu. Suna kusa da Hotel ɗin da Hafsat zata zo. Suna jira a nutse hankali kwance.

Bayan kamar awa biyu, Ammar ya hango Hafsat ta nufo hanyar shiga hotel ɗin. Ya hango yanda Hafsat take shakkun shiga hotel ɗin. Ammar ya ce wa sauran su jira har ya musu alama kafin su taho. Fitowa ya yi daga cikin mota ya bi bayan Hafsat cikin sanɗa. Su biyun suka shiga hotel ɗin. Ammar ya tsaya daga nesa yana kallon yanda Hafsat take a mugun tsorace.

Godiya Hafsat ta yi wa ma'aikaciyar hotel kafin ta nufi lifter. Ya tabbatar idan ya bi ta cikin lifter ɗin zata gane shi. Wajen ma'aikaciyar hotel ɗin ya je domin sanin sauran bayanan ɗakin da Hafsat zata je.

Cigaba da bin ta Ammar ya yi, yana mamakin yanda sakarcin Hafsat har ya kai haka da wasu zasu yi mata irin wannan tarkon. Kuma me yasa bata nemi taimako ba? Ya tabbatar wannan mutanen ba zasu daina yi mata barazana ba... Yau sun bata rendezvous su da yawa, gobe Allah kaɗai yasan me zasu buƙaci ta yi.

Hawan lifter ya yi, ya je hawa na huɗu. Ya shiga duba corridor da mamaki ya ji ta shuru. Baƙin ƙofar ɗakin ya je, ya kara kunnensa ko ya ji abinda suke faɗa amma jin shuru babu motsi ya ƙara tsorata shi.

Knocking ya yi sau uku, sannan ya jira.

“Waye?” Wata murya daga ciki ta tambaya.

“Ƴan sanda ! ” Ya basu amsa.

Babban motsi ya ji daga ciki da sauri ya sa katin buɗe ƙofar, ya banka ƙofar ya shiga.

“Banza ƴan sanda kika zo mana da su...”

Ammar ya shiga daidai wani mutum damƙe da hannun Hafsat.

Wasu mutanen biyu zaune bisa kujera, da sauri suna tattara kayan da ke kan center table amma duk da haka sai da Ammar ya fahimci farin garin da ya gani cocaine ce. Komai ya tafi da sauri. Ammar ya fiddo wayarshi ya yiwa sauran sign, ya yi musu kwatancen komai cikin daƙiƙun da ba su wuce bakwai ba. Shiga ya yi tsakanin Hafsat da wannan mutumin.

Sauran da har yanzu suke cikin shock basu wani yunkuri ba amma ganin Ammar ya shiga tsakanin Hafsat da mutumin suka zaburo.

Ɗaya daga cikin su ne ya fiddo wuƙa daga cikin aljihunsa ya dumfaro Ammar. Kare kansa ya yi da ɗayan hannunsa, ɗayan kuma ya mayar da Hafsat bayanshi. Ita kuwa Hafsat a tsorace take sosai. Da ka gani ka san ba a hayyacinta take ba.

Sauran biyun ne su ma suka zo suka shiga dukan Ammar, duk da yana da ƙarfi amma ba zai iyawa har mutum uku ba. Bayan wani ɗan lokaci suna cikin dukan Ammar, ɗaya daga cikin su ya koma kan Hafsat, ya cakume ta yana ƙoƙarin kaita ɗayan ɗakin.

Daidai lokacin Allah ya ji addu'ar Ammar, sai ga Farouk da mutanensa sun faɗo ɗakin. Cikin ƙanƙanin lokaci, Ammar ya yi tunanin ta yaya su Farouk suka shigo ciki alhali basu da katin shiga sai dai zafin naushin da yake ji ya tuna masa da ba wannan ba ne a gabansa yanzu.

“Ku yi sauri tana cikin ɗaki.” Ammar ya faɗa.

Yayin da su Farouk suke ƙwatar Ammar, sauran kuma suka yi saurin shiga ɗakin domin ceto Hafsat.

Lokacin da suka shiga, sun tarar da Hafsat zaune gaban gado kuma abun mamakin bata kuka. Ta ƙurawa bango ido kamar babu rai a jikinta. Ɗaya daga cikin su ya taimaka mata ta miƙe tsaye. Bata yi gardama ba, ta bar mutumin yana jagorantar ta.

Bayan kamar rabin awa, su Ammar suka yi nasarar jiggita abokan faɗan nasu.

“Mr. Ammar ku je su Hamza za su raka ku gida, ko kuma na kira maka ambulance domin wannan raunukan naka ya kamata a yi treating ɗin su da sauri, ni zan ji da sauran matsalar.”

“Za muje gidana ne, Hamza zai iya raka mu. Raunuka kuma zan ji da su. Kuma dan Allah Farouk ka yi yanda ka san waɗannan mutanen ba zasu sake dawowa rayuwar Hafsat ba.”

“Kar ka damu. Ka yarda da ni." Cewar Farouk.

“Good.” Ammar ya faɗa yana ƙoƙarin tashi. Hamza, ɗaya daga cikin mutanen Farouk ne ya taimaka masa ya miƙe tsaye. Yana yin tsaye bisa ƙafafunsa ya matsa kusa da Hafsat yana tambayar ta lafiya take. Hafsat ko kallon sa bata yi ba. Ammar ya fahimci har yanzu tana cikin shock ne kuma ya yanke shawarar ƙyale ta har ta dawo daidai.

Lokacin da suka isa ƙofar gidansa, Ammar ya kira Afnan dan ta zo ta buɗe musu. Kusan faɗuwa ta yi lokacin da ta ga ɗan uwanta jina-jina wani mutum kuma ɗauke da Hafsat.

“Kar ki damu, ba komai ba ne.” Ammar ke ƙoƙarin kwantarwa da Afnan hankali amma ita ba zata iya ba.

Ammar nunawa Hamza ɗakin da zai kai Hafsat ya yi da tuni bacci mai nauyi ya ɗauke ta.

“Nagode Hamza, sai mun haɗu gobe ko jibi insha Allahu.”

Sallama Hamza ya yi musu kafin ya tafi.

“Wai me yake faruwa ne?” Afnan ta sake tambaya har yanzu cikin shock.

“Shuut, bacci take yi. Yi magana a hankali.”

“Hankalina ne a tashe yake, ko zaka iya faɗa min me yake faruwa? Me yasa Hafsat take nan? Kuma me yasa jikinka duk jini? Faɗa ka yi ne?”

Kama hannun Afnan Ammar ya yi, ya tilasta ta bin shi falo. Zaunawa suka yi bisa kujera, nan ya shiga bata labarin abinda ya faru ba tare da ya bayyana mata duka sirrin Hafsat ba.

“Yaushe kuka zama shaƙiƙai haka?” Afnan ta tambaye shi.

“Ba abokanai ba ne mu amma ba zan iya barin ta cikin wannan halin ba ita kaɗai.”

“Na gani, Allah ya sa komai ya daidaita daga yanzu. Zan je na ɗauki akwatin agaji. Bakada kyan gani haka.” Afnan ta ce da shi.

Kawo akwatin ta yi ta taimaka masa wajen treating ɗin raunukan. Bayan sun gama, ya yanke zuwa ya yi wanka.

“A ɗakin naka zaka yi wankan?” Afnan tambaye shi.

“Eh mana, wace irin tambaya ce wannan?"

“Amma Hafsat tana ɗakinka. Ba zaka iya yin wanka a cen ba.”

“Me zai hana? Kamar dai idan na je zata gan ni ne ba kaya ko me? Kuma ai ɗakina ne, ina da ƴancin yin abinda nake so.” Ya bata amsa.

“Haka ne, da ka kawo ta ɗakina ai ko kuma ka ce na gyara ɗakin baƙi.”

“Wai meye naki a ciki? Je ki kwanta Afnan ! "

“Eh, eh ai haka zaka ce.”

Ɗaya daga cikin pillow da ke kan kujera ya jefa mata.

“Haka zan ce me? Kina tunanin zan iya yi mata wani abun ne bayan abinda ya faru?"

“Ni fa ba haka nake nufi ba, amma idan ka yi kamar baka gane ba ni ma zan yi kamar na yarda da kai. Dan haka zan je in kwanta.” Afnan ta faɗa tana miƙewa tsaye.

“Kin ci sa'a inada raunuka Afnan kuma dan Allah zuwa gobe ki bi Hafsat a sannu. Ina son kawo ƙarshen yaƙina da ita. Na gaji da wannan faɗan marar kan gado.”

“Kar ka damu, bayan abinda ya faru da ita bana tunanin zan bari wata tsama ta shiga tsakaninmu.”

Godiya Ammar ya yi mata kafin ta wuce ɗakinta ta kwanta.


ƁANGAREN HAJIYA KARIMA

Zuciyarta ta mahaifiya ke zubar da jini. Ta fara gajiya da jurar wannan nisan tsakaninta da ƴaƴanta. Kamal yana kiranta ba sosai ba amma bata da labarin Ammar ko kaɗan. Bata san me zata ce ko me zata yi ba domin su dawo. Wannan rayuwar nesa da su, babu komai ciki sai tashin hankali. Tana cigaba da harkokinta yanda take iyawa amma babu abinda yake hana ta tunanin ƴaƴanta. Yanzu da ta rasa su... A hankali ta fara gane da ta yi wani abun a baya. Daga ƙarshe gashi ya ja mata rasa ƴaƴanta biyu. Bata taɓa son haka ta faru ba, tana son kare su ne kamar kowacce uwa da ke kare ƴaƴanta. Amma Hajiya Karima bata taɓa tunanin akwai ranar da zata bar su su ma su tashi da fukafukinsu ba. Ta barsu su bi zaɓinsu, ta barsu su yi nasara, su faɗi, su koya daga faɗuwarsu domin hakan shi ke bai wa yaro damar zama babba.

Bayan dogon nazari, ta yanke shawarar zuwa ganin ƴaƴanta : Kamal sannan Ammar kuma ta yi ƙoƙarin daidaita komai tare da dakatar da shari'ar nan da ke ƙoƙarin ƙara raba kan ahalinta fiye da yanda ta yi a baya. Sai dai ba wannan ba ne ra'ayin mijinta.

“Kike iya zuwa inda suke bayan duk abubuwan da suka aikata mana? Su fa suka guje mu amma ke kike son ki cigaba da bin bayansu?”

“Ba maƙiyanmu ba ne, na gaji da zama cikin wannan rashin fahimtar, na gaji ka ji ko? Ƴaƴana kawai nake son gani kuma mu sasanta tsakaninmu.”

“Wallahi Karima bakida hankali ! Duk irin abinda na yi miki da wannan zaki saka min?”

“Toh me kake son na yi? Kar ka manta zargin fyaɗe ake yi maka amma duk da haka na tsaya bayanka. Na juyawa ƴaƴana baya, amma yanzu na gaji da wannan lamarin. Zan je na gan su ko kana so ko baka so!”

“Baki jin kunya Karima. Kina yin kamar wata victim, alhali saboda ke ne ƴaƴan naki suka juya miki baya. Idan ni ne ke, zan jira sai an gama shari'a. Na tabbatar idan Alkali Malam Yahaya ya wanke ni, zasu zo har nan da kuka suna roƙo mu yafe musu.”

“Wane Malam Yahaya kake magana? Kar ka ce min zaka bashi kuɗi domin ya wanke ka? Daga yaushe files ɗinka suka koma hannunsa? Idan baka da laifi me yasa sai ka biya kafin ka samu ƴancinka?”

“Nasan ƴaƴanki, nasan zasu iya yin komai ganin sun durƙusar da ni duk da gaskiyata. Anan ko ba komai, nasan za'a wanke ni. Ba zan ɗauki risk marar amfani ba, Malam Yahaya zai yi abinda ya dace.

A hankali Hajiya Karima ta fara gane wanene asalin mijinta. Son da take masa ne ya rufe mata idanu amma ƴar hirar da suka yi yanzu kuwa ya nuna mata asalin mummunar fuskarsa.

To be continued...


AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story📖

By Malik al-Ashtar 🖋


CHAPTER 34

I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 34 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”

http://www.ashblogg.com.ng/2022/04/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-34.html




Yau Ammar da wuri ya tashi daga aiki. Zahara bata nan yanzu dan haka wahalar ji da ayyuka a kwanakin nan yake. Hakan ne yasa ya ɗauki tsohon sakataren mahaifinsa da ke aiki yanzu a wani kamfanin domin ya taya shi. Da yake sakataren yanada ƙwazo sai ya zamana Ammar ya samu isasshen lokacin ji da wasu matsalolinsa na in da cen.

Yanke shawarar zuwa gidansa ya yi domin yin magana da Hafsat da kuma ganin ko ta dawo hayyacinta. Saidai lokacin da ya je gidan ya yi mamakin ganin Afnan ita kaɗai. Bai yi wani mamaki sosai ba, shi yasa ya yi abinda ya yi domin hana ta tafiya a halin da take ciki.

Kasa ɓoye fushinsa Ammar ya yi, ya sa ran ko magana su yi kafin ta yi tafiyarta. Ya ji haushi sosai da yasa ya sauke kan kanwarsa Afnan.

“Ko ƙoƙarin tsayar da ita da kin yi ai..” Ya ce wa Afnan cikin ɗaga murya.

Afnan da ke saka takalmi domin komawa school ta yi saurin ɗagowa jin abinda ɗan uwanta ya ce. Da sauri ita ma ta ce :
“Ta yaya zan iya tsayar da ita idan kai ma ka kasa? Ba ƙaramar yarinya ba ce, na yi ƙoƙarin lallaɓa ta amma ko kula ni bata yi ba.”

“Ai da sai ki kira ni ki faɗa min. Abinda ya kamata ki yi Afnan ! Bansan me yake damun ki cikin kai ba.”

“Ni ce ko kuwa sauke fushinka kake a kaina? Ni zan tambayi me yake damun ka, matar nan bata son tsayawa nan, ina ga ya kamata ka yi tunani kuma ka shafa mata lafiya. Ka cece ta, toh me kuma kake so bayan wannan? Ta yi maka godiya? Idan baka fahimta ba, bari na sanar da kai, wannan yarinyar ta tsane ka. Ya kamata ka daina ƙoƙarin shi-shige mata.” Afnan ta faɗa masa.

Kalamanta sun shiga kunnuwan Ammar kuma sun ƙara haura fushinsa.

“Ki tafi daga nan kafin raina ya ƙara ɓaci.” Ammar ya ce wa Afnan ƙasa da murya.

“Eh ai haka zaka ce..” Cewar Afnan saidai duk da haka ta yanke tafiya ganin adadin yanda ta fusata yayan nata.

Rufe kansa Ammar ya yi cikin ɗakinsa. Rai a yamutse. Ya kasa fahimtar me yasa ransa ke ɓaci har haka. Ba ƙaunar juna suke ba tun asali amma me yasa ji daga bakin ƙanwarsa ya fusata shi haka? Yasan tsakanin shi da Hafsat ba wata ƙwaƙwarar soyayya ke akwai ba, kuma hakan bai dame shi ba. Saidai yau Ammar yana jin wani sauyi a cen cikin zuciyarsa.

“Na tabbatar tausayinta ne kawai..” Ya faɗa cikin ransa.

Bayan duk abinda ya faru da ita, tabbas ya ji tausayin ta. Wannan yasa yake ƙoƙarin ƙulla wata sabuwar alaƙa da ita.

“Ko ma dai meye Afnan tayi gaskiya. Na taimake ta, shikenan yanzu. Ya kamata in mayar da hankali ga rayuwata da kuma Shari'ar ƴar uwata. Wannan ne yafi muhimmanci.” Ya faɗa.

Bayan wasu kwanaki, Ammar ya kasa manta Hafsat. Yarinyar nan ta ƙi fita daga cikin kwanyarsa hakan kuma ya kusan mayar da shi mahaukaci. Kamar wanda aka yiwa sihiri, hargitsi ne cikin kansa. Kuma babban abun, har yau yana tunanin iya tausayinta ne kawai yake ji. Wata rana, ya yanke zuwa gidansu Hafsat domin ganin yanda take. Idan ya tabbatar tana nan lafiya wata ƙila ya ɗan samu sukuni cikin ransa. Da wannan tunanin Ammar ya tafi neman Hafsat.

Mahaifiyar Hafsat tayi mamaki saidai tayi murna da ganin Ammar. Ƴarta kusan bata cin komai kuma kullum rufe kanta take cikin ɗaki, bata fitowa kuma ta daina zuwa wajen aiki. Kowa damuwar halin da take ciki yake, amma ita bata yi komai da zata kwantar wa da dangin nata hankali ba.

“Shigo ɗana, ya kake?”

“Lafiya lau nake Mama, fatan kuma haka?” Cewar Ammar yayin da yake bin bayan mahaifiyar Hafsat zuwa falo.

“Lafiya lau Alhamdulillah, ya momynka?” Ta tambaye shi.

“Tana nan lafiya.”

Ammar ya bata amsa a gaggauce da gudun kar ya tuna memories masu ɗaci.

“Masha Allah. Na kawo maka abun sha ne?"

“A'a nagode Mama, ina son ganin Hafsat ne.”

Shuru mahaifiyar Hafsat tayi na wasu ƴan daƙiƙu kafin ta ce masa :

“Bana son shiga sha'aninku amma ina tunanin baku rabu ta daɗi ba haɗuwarku ta ƙarshe. Zan iya cewa ko kun sake haɗuwa kuma saboda kai ne take cikin wannan halin? Idan haka ne Ammar, ba zan..."

Katse ta Ammar ya yi.

“Kiyi haƙuri Mama, amma ba abinda kike tunani ba ne. Ban ma san bata jin daɗi ba, na zo ganin ta ne kawai domin sasanta tsakaninmu. Tun bayan abinda ya faru tsakaninmu, bana jin daɗi. Ina son samun sukuni da kaina. Ko wani abu yana damunta ne?”

Ammar ya tilasta kanshi yin ƙarya, domin abinda ya fahimta Hafsat bata faɗawa mahaifiyarta komai ba.

“Ah har naji daɗi ɗana,

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment