Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin fara'a take, yau a murtuke take. Tunanin abinda ya kawo su Zahara take.

Ruwa da lemu Mama ta kawowa bakin amma basu da alamar zasu taba wani abun. Da ganin haka Zahara tasan ko ma me ya kawo su yana da alaka da ita. Tun haduwar ta da Amriya babu wani abu dake tafiya daidai. Sosai take da nasanin kula Amriya. Dama hakuri kawai ta bata tayi tafiyar ta gida, da duk hakan bata faru ba.

“Zahara baki ji ana miki magana ne?” Cewar Mama.

Duka kallo ya koma ga Zahara. A daburce ta bayar da hakuri.

“Ba komai kawai ina son jin ko kina lafiya ne?” Cewar Mami.

Kai a kasa cikin sanyin murya Zahara ta amsa da
“Lafiya kalau.”

“Toh madallah, abinda yasa nazo tare da dan uwana Ali da kuma yar uwata Mariya, dan muyi magana ne akan abinda ya faru rannan a gida na.”

Koda tace hakan, Zahara taji idanun Mama a kanta.

“Tun ranar ban samu runtsawa ba Zahara. Zuwan ki ba karamin fama min tsohon ciwo na yayi ba. Nasan mahaifiyar ki kuma kema na sanki... ko kuma ince ina tunanin na sanki. Ke yarinya ce mai hankali da tarbiya, wadda bata dagawa ko yaro murya bare babba. Toh tun zuwan ki gidana nake dorawa kaina wannan tambayar. Me yasa kika min haka? Me yasa kika kirkiri wannan labarin Zahara?”

“Mami wai me yake faruwa ne, ku yimin bayani. Me Zahara tayi?

“Asiya ke kamar yar uwa kike gare ni, amma ba zan taba lamunta ba wani naki yazo yamin rashin kunya. Zahara tazo gidana dauke da gyalen da na yiwa marigayiya Aisha kyauta. Tace min taga Aisha ne bakin kogi, kuma ita ta bata gyalen. Kin san wani yanayi na shiga a lokacin? 'yata Aisha ta rasu da dadewa toh me zai sa Zahara tazo har gida na ta fada min haka?”

“Tsaya kina nufin ita Zahara din ce, taje har gida tace miki taga Aisha bakin kogi?” Cewar Mama.

Gyada kai Mami tayi.

“Nasan akwai wani abu da ba mu fahimta ba a wannan lamarin. Nasan 'yata kuma ina da tabbacin ba zata je tayi miki rashin kunya ba ta wannan sigar.”

“Zahara? Mama ta kira sunan ta. Yi mana bayanin abinda ya faru. Ko dai kin ga wata ce mai kama da ita?

“Ai ban ce tasan Aisha ba.” Cewar Mami. “Aisha tun tana karama take hannun mahaifin ta a USA, tana cikin shekara ta 17 ne tazo nan Nijar wajen hutun karatu. Dan haka da wuya su san juna.”

“Zasu iya sanin juna ba tare da mun sani ba.”

“Kai hakan zai yi wuya, kuma wannan ba shi ne zai sa tayi min abinda tayi min ba.” Cewar Mami.

“'Yata.” Cewar Mami da murya mai alamar kuka. “Har abada nasan ba zan sake ganin 'yata ba. Kuma har yau ina nadamar bari da nayi mahaifin ta ya tai da ita. Ban kawo zata tafi ta barni ba haka da wuri. Ta tafi da wani bari nawa, ke da kanki Asiya kinsan ba haka ba nake ba a da. Har abada ba zan manta da ciwon rashin ta da nake ji ba. Bamu wani zauna ba sosai a tare, amma soyayyar uwa akan danta bata jin wani nisa. A gaban idanuna ta mutu, ina cikin ambulance din da ta dauko ta. Mala'ikan mutuwa ya dauki ranta a gaban idanuna. Har abada ba zan manta da kallo na karshe da tayi min ba, kallon da yake dawo min kullum a cikin mafarkina. Asiya ke yar uwata ce, amma ba zan lamunci abinda 'yarki tayi min ba. Ba zan lamunci rashin kunya kiri-kiri akan margayiya ba.”

Zahara ta rasa ta yaya zata fada masu ita bata taba sanin wata Aisha ba. Ba ita taso su hadu da matar nan wacce tace mata sunan ta Amriya ba, kuma take kama da 'yar su da ta mutu da dadewa. Taji tausayin Mami sosai amma ita bata da laifi a ciki. Da gaske ita taga 'yarta bakin kogi dan haka me zai sa tayi karya. Yanke shawarar kawai ta baiwa Mami hakuri tunda babu wani kwakwaran bayani da zata yi masu su yarda da ita. Zata bata hakuri koda kuwa daga ranar ba zata sake yi mata irin kallon da take yi mata a baya ba.

“Zahara kina da abin cewa ne?”

“Mu kawai muna son ta gane cewa bama wasa da irin wannan abubuwan. Bansan me yasa tayi haka ba, amma ya zama shine na karshe.” Cewar dan uwan Mami.

Akwai ciwo a zarge ka akan abinda baka yi ba, amma Zahara ba yanda ta iya dan bata da wata hujjar kare kanta na cewa taga yarinyar jikin hoton nan kuma ma har ta fada cewa Mami ce mahaifiyar ta.

“Kina da abin fada ne? Yi min bayanin meke faruwa dake Zahara?” Cewar Mama.

Sunkuyar da kai Zahara tayi, tana rokon Allah ya kawo mata dauki na wannan yanayi da take ciki. Jin ta take tamkar barewa a tsakiyar kuraye.

“Dan..dan Allah kuyi hauri, insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba.” Zahara ta fada tana share hawayen da suka zubo mata.

Dago kanta tayi dan ta kalli Mami ta nuna mata da tsantsar gaskiyar ta tayi nadamar abinda suke tunanin tayi. Ganin idanun Mami cike da hawaye hakan ya kara karyar mata da zuciya.

“Kiyi hakuri Mami, nasan ba zan iya lallashin ki ba yanda ya dace amma insha Allahu Zahara ba zata sake zuwar miki da makamancin wannan zancen ba. Bansan gangancin me ya kaita yin hakan ba, amma nasan yanzun tayi nadama. Dan Adam ajizi ne, dan Allah ki yafe mata.”

“Shikenan na yafe mata Asiya, amma bana tunanin zan manta nan kusa.”

Har yanzu kan Zahara a kasa yake, jira kawai take su Mami su fita ko ta samu yin numfashi da kyau.

Suna tafiya Mama ta dawo kan Zahara akan dole sai ta fada abinda ya faru. Rokon mama tayi da ta barta ta samu bacci idan ta tashi sai tayi mata bayanin komai. Ba dan mama taso ba ta hakura ta barta taje ta kwanta. A babbar kujerar falon ta kwanta, domin tace babu tsautsayin da zai sake maida ta dakin ta. In har ba solution ta samu akan matsalarta ba.

Bayan kwana biyu, Zahara ta daina jin alamun komai, har ta dan fara sakewa. Har yau bata yiwa Mama bayanin komai ba. Duk lokacin da zata kawo zancen, sai Zahara tasan yanda tayi ta zame. Ba wai bata son fadawa mama bane, a'a tana tsoron kar ta saka rayuwar Mama a hatsari. Kuma ita ba zata juri hakan ba.

Zahara na tunanin abinda kwana biyu yasa bata sake jin wani motsi ba, saboda aikin dake gareta a office, yana mantar da ita wasu abubuwan. Office ba wani wuri bane da take so, amma tafi sakewa akan gida. Ba kamar idan Mr. Kamal yayi tafiya. Zahara tana mugun tsoron sa, ba ma Zahara kadai ba har ma da sauran ma'aikatan kamfanin. Bai cika zama ba a kamfanin amma idan yazo kowa shan jinin jikin sa yake, domin bayada wasa kuma kullum fuskar sa a murtuke take. Zahara kamfanin ma koma mata yake tamkar barikin soji. Tana shan wahala dalilin wannan matar Amriya amma Mr. Kamal yana daya daga cikin dodannin mafarkin ta, domin idan yana a wuri numfashi ma wahalar yi yake mata. Akwai kuma dan uwan shi, wanda ba halin su daya ba, kuma shine ogan su Zahara, wanda ita ce sakatariyar sa, Mr. Amar Yusuf sunan sa, amma suna kiran sa da Mr. CEO. Yana da kirki sosai, kuma kullum cikin fara'a yake, gashi da aji amma duk da wannan ba irin mai daukar raini bane idan abinda ya shafi aiki ne, amma a waje mutum ne shi mai girmama ma'aikatan sa, Ba kamar Mr. Kamal ba da fuska a daure kowanne lokaci. Wani lokacin Zahara har tambayar kanta take anya kuwa ma ya taba dariya.

Yau ma Zahara zaune take a office tana gyaren wasu takardu sai ga Mr. CEO ya shigo.

“Ina kwana Zahara, kin tashi lafiya?” Ya fada yana mata murmushi tare da ajiye jakar shi bisa desk din ta.

Cen cikin makoshi kamar koda yaushe Zahara ta amsa:
“Lafiya kalau...”

“Ba zaki tambayi ya nake ba?” Ya fada yana fiddo wasu files daga cikin jakar shi.

Murmushi kawai Zahara tayi tare da amsar files din da yake miko mata.

“Toh lafiya kalau nake, tunda ba zaki tambaye ni ba. Well, na duba wannan files din jiya sai dai basu cika ba. Zaki iya karanta su sai ki kara abinda babu. Zaki iya aje su wajen ki har zuwa gobe ma. Bana bukatar su yau.”

“Ok...” Amsar da ta bashi kenan.

“Dan Allah ko zaki hado min coffee, dan yau ban samu damar yin breakfast ba.”

“Ok, yanzu insha Allahu.”

“Thank you.” Yace kafin ya nufi office din sa.

Zahara ta mike da niyyar zuwa hado masa coffee, sai ga Sarat, intern ce a kamfanin, ta nufo ta da niki-nikin takardu a hannu.

“Ina kwana Zahara.” Ta fada tana sauke numfashi dakyar.

Amsawa Zahara tayi tana kallon ta.

“Dan Allah ko zaki mika min wannan takardun a dakin meeting? Wallahi yau a gajiye nake sosai.” Ta fada tare da zubawa Zahara su a hannu. Tsabar nauyin takardun kusan faduwa Zahara tayi, Allah yasa kujerar ta ta tare ta.

“Yauwa nagode Zahara, bari naje na dan huta.” Ta juya tana takun ta dai-dai har zuwa stairs. Zahara ta bita da kallo. Tana sanye da wani mini skirt baki kamar na kanwarta, sai kuma wata riga fara da ta fiddo da kusan rabin kirjin ta. Gashin kanta ya sauko har zuwa kafada, yasha gyara, gwanin sha'awa wanda yake ra'ayin shigar kamar irin Zahara, tana yawan rayawa a ranta da tana da kirji kamar na Sarat da ita ma zata dinga sa irin wannan rigunan.

Ba dan Zahara taso zuwa aiken Sarat ba, tayi hakan ne dan kar taga tayi mata ba daidai ba. Daman ta saba yi mata haka, aikin da ya kamata tayi sai ta baiwa Zahara shi, alhali itama tana da nata aikin ba kadan ba. Idan zata bata aikin, zata kirkiro wani abun tace ko kanta na ciwo ko kuma ta gaji. Zahara na son tace ba zata yi ba, amma tana tsoron Sarat ta sakata a layin makiyanta. Bare kuma daman Sarat mafadaciya ce, ita kuwa a halin da take ciki ba zata so ta kara da fadan Sarat ba.

Hanyar dakin meeting din ta nufa, in yaso bayan ta kai takardun sai taje ta hadawa Mr. CEO coffee shi. Tana cikin tafiya a tsanake zuwa dakin meeting, taji wata murya nace mata :
“Wawuya kawai, kin barta tana wani juya ki!”

Da sauri ta tsaya tare da waiwayawa ko zata ga mai maganar amma babu kowa. Kuma abun tashin hankalin zata iya rantsewa wannan muryar iri daya ce da ta Amriya da suka hadu bakin kogi. A ranta tace “Na tabbata kwalwa ta ce ke kitsa min wannan abin.” Haka tayi ta maimaitawa tare da cigaba da tafiyar ta. Bata sani ba ko tsoro ne yasa, amma tunda taji wannan muryar kalar yanayin corridor ta sauya. Corridor dake da haske ga kuma kwalliyar fulawowi da aka kayata ta da ita, amma ta sauya zuwa duhu, har da wata yanar gizo gizo kamar tsohon kangon da aka shekara dari ba'a shiga ba. Yanayin lungun ya komawa Zahara kamar a cikin horror film ko a makabarta... Sauri Zahara ta cigaba da yi, amma wannan karon har da kukan jemagu take ji. Gudu ta fara iya karfin ta, abinda kawai take so a wannan lokacin shine ta fita daga cikin corridor da taga batada niyyar karewa.

Nauyin takardun dake hannun ta suka fara gajiyar da ita. Cikin rashin sa'a, kafar ta daya ta bugi dayar ta fadi kasa tare da takardun. Kokarin tashi tayi amma taji hannu bisa kafadar ta, bata san lokacin da ta kurma uban ihun tsoro ba.

________________________________________

Karshen wannan chapter kenan, ku biyo ni domin jin yanda zata kaya.
AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 2


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo

*[📝I.W.A📝]*

Kowa a offishin yaji irin karar da ta fito daga corridor, hatta Mr. Kamal da shigowar sa kenan. Haka ma Mr. CEO duk da nisan dake akwai tsakanin offishin sa da corridor yaji wannan karar. Saving aikin da ya fara a computer yayi tare da fitowa da sauri domin ganin meke faruwa. Yana fitowa yayi kicibus da yayan shi Mr. Kamal da shi ma karar ce ta fito dashi.

“Karar meye wannan?” Mr. CEO ke tambayar dan uwan sa. Shi kuwa daga masa kafada kawai yayi a matsayin amsa.

Nufar inda suke tunanin karar ta fito suka yi. Tun daga nesa suka tsinkayi kamar alamar mutum a kwance. Sai da suka karasa Amar ya gane Zahara ce. Tambayar kansa yake abinda ya faru da har ta tsinci kanta a nan. Tsoro ne ya kama shi ganin ya tabata bata motsa ba. Durkusowa dan uwan nasa yayi tare da taba jijiyar hannunta kafin yace :
“Suma ne tayi.”

Ajiyar zuciya Amar yayi, cak ya dauke ta ya nufi office din sa da ita. Shi kuwa dan uwan sa ya tsaya tattare takardun da suka zube a kasa.

Aje sakatariyar tasa Amar Yusuf yayi kan doguwar kujerar da ke a offishin nasa. Kokarin tayar da ita ya shiga yi a hankali amma bata tashi ba. Dan uwan sa ne Kamal Yusuf ya shigo, ya ajiye takardun bisa desk din Amar kafin ya samu kujera ya zauna. Amar kokarin kiran likitan su yake domin yayi gaggawan duba Zahara, amma ya dakata sakamakon ganin ta fara motsi. Kokari take ta tashi zaune da sauri yazo ya taimaka mata ta zauna.

A bangaren Zahara kuwa, har yanzu hankalin ta bai dawo jikin ta ba, bata iya tuna komai ba. Razanar da tayi yasa ta manta a wajen aiki take.

Sunan Mama ta kira tana murza idanun ta. Tana kallon wanda ke a gaban ta, da har yanzu dishi-dishi take ganin sa. Sai dai lokacin da ta fara dawowa hayyacin ta, ta fahimci hannuwan da ta taba yanzun ba na Mama ba ne. Daga kanta tayi anan tayi arba da fuskar Amar wato ogan ta. Da sauri tayi baya tana mai tashi daga kujerar. Kamal da ya mayar da hankalin sa ga wasu takardu ya dan juyo ya kalle su.

“Dan..dan..dan..Allah..ku..kuyi hakuri, ban..bansan me nake..yi..ba anan.” Zahara ta shiga i'i'na tana bada hakuri ba tare da tsayawa ba.

“Suma kika yi, shi ne na kawo ki nan. Lafiyar ki kuwa?” Cewar Amar.

“Dan..Allah..kayi hakuri, ba da gangan...”

Wai hakuri take badawa da suman da tayi? Kamal ya fada a zuciyar sa tare da sake kallon su karo na biyu.

“Me yasa kike bani hakuri? Ba fa da gangan kika yi ba. Toh saboda me ma zaki yi karyar suma? Zauna ki huta, bari na kirawo doctor.” Amar ya fada da sigar umarni amma Zahara ta cigaba da bashi hakuri.

“Kayi hakuri, ban so in takura ka ba.”

Kamal da ba shiga lamuran mutane yake ba, yaji halin Zahara ya takura shi yace :

“Bayar da hakurin ya isa haka, ki jira ya kira doctor idan kuma ba zaki iya aikin ba ki tafi gida.” Ya fada da kakkausar murya da alamun an takura shi.

Wannan ne karon farko da ya fara yi mata magana tun zuwan ta kamfanin nan. Ya fada mata hakan ne yana kallon ta cikin ido. Hakan kuwa ya tsorata Zahara ba kadan ba. Allah yayi mata dabi'ar bada hakuri ba tare da ta tsaya taji ita ke da laifi ko kuwa. Bata son tashin hankali ko kadan shi yasa da abu ya hada ta da mutum take kokarin su rabu lafiya.

“Kina son na kira likita ne ya duba ki? Ko zaki tafi gida ki huta. Zan samu wani sai ya karasa aikin naki.” Cewar Ogan nata.

Juya Zahara tayi tana fuskantar shi tare da cewa zata iya cigaba da aikin nata.

“Bana son na kara tarar dake a kasa. Na yarje miki, zaki iya tafiya idan baki jin dadi.”

A cikin ranta, babu abinda take so kamar zuwa gida, amma bata son taje bayan takurawar da tayi masu. Gashi kuma tana da aiki da yawa, kuma tana son kammala documents din da ya bata dazun. Tunawa tayi da har takardu zata kai a dakin meeting. Amma bata sani ba ko tana da kuzarin da zata kara tunkarar wannan corridor ba. Har yanzu tana tuna abinda taji lokacin da hannun nan ya taba ta. Lokacin da ta juyo bata ga kowa ba. Alhali ita tasan hannu ya dafa ta.

Amar gani yayi sakatariyar sa tayi nisa cikin tunani kuma da ka ganta zaka san akwai abinda ke damun ta. Koda basu wani dade ba a kamfanin nan, yayi wa sakatariyar tasa farin sanin koda yayi mata tambayoyi ba amsa masa zata yi ba. Irin kullum cikin tunani take, ga wahalar fitar magana a bakin ta.. Kamar dan uwan shi. Ya fada a zuciya. Niyyar ya barta taje yake da, amma kafin nan yana son yaji me ya kaita cikin corridor nan.

“Fada mini Zahara, me ya kai ki wannan wurin? Idan ban manta ba cewa nayi ki hado min coffee.”

“Naje na kai wasu takardu ne a dakin meeting.” Zahara ta fada kanta kasa.

Kunya ce ta kamata da ta gayi hakan, domin taje aiken Sarat akan na oganta.

“Na dauka wannan aikin Sarat ce ya kamata ta yi shi?”

“Eh, amma tana wani aikin ne..”

Amar yasan sakatariyar sa karya take masa domin ba sau daya yana kama Sarat ta saka ta aiki ba. Yayi shuru ne da tunanin ko badin ba jima Zahara zata daina yarda Sarat na sata aiki sai dai ba haka abun yake ba. Canza maganar yayi domin baya son yayi ta gaban dan uwan sa da yasan halin sa. In yaso sun yi maganar daga baya.

“Zaki iya tafiya.” Ya fada.

Zahara ji tayi kamar tayi tsalle da jin abinda oganta yace. Zuwa tayi da niyyar daukan takardun amma ya hana, yace ta barsu nan. Fita daga offishin tayi bayan tayi masa godiya. Koda ta rufe kofar office din Amar yaji alamun shi yayan sa ke kallo.

“Wai da gaske wannan ce sakatariyar ka?” Cewar kamal.

Gyada masa kai Amar yayi yana kokarin kunna computer.

“Ban ga alamar iya aikin nan gare ta ba. Anya kuwa tana yin aikinta yanda ya kamata?”

“Tana da kwarewa sosai. Kawai tana da dan sanyin hali ne. Amma tana aikin ta da kyau.” Cewar Amar.

“Gwara ka sallameta idan ba zata iya ba. Domin kana dab da ci baya idan ka barta a matsayin sakatariyar ka.”

Kamal ya kasa gane me yasa dan uwan shi yake iya zama da ma'aikata masu sanyin hali kuma suke iya kallon sa cikin ido. Yasan dan uwan shi da tausayi, yana iya daukan mutum aiki dan ya dinga samun albashi mai kyau ba wai dan kwarewa ba. Bai san iya adadin lokacin da ya kori ma'aikata ba a madadin dan uwan shi saboda rashin kwarewa. Saboda halin dan uwan shi, yake zuwa duk bayan wata uku kamfanin dan bincikawa idan komai na tafiya daidai.

Kamal yana da tsanani idan akan aiki ne. Shi yasa Amar ke tsoron kar ya kori Zahara, domin shi yana tausayin ta sosai. Gashi yanzu saura yan watanni dan uwan nashi yazo duba aikin kamfanin, dan haka zai yi kokari yaga Zahara ta sake da mutane dan ganin dan uwan shi bai koreta ba. Abinda yasa yake son zama da Zahara saboda tana tuna mishi da dan uwan shi, kusan dabi'un su daya, na koda yaushe shuru-shuru da kadaice kansu daga mutane. Abin mamaki ne wata kila amma Kamal yanada karancin yarda da kanshi, amma da yake shi mutum ne very intelligent sai ya zamana yana iya controlling rashin yardar shi.

“Ka barni na tafiyar da ma'aikatana yanda nake so dan Allah, kai ma kaji da naka damuwowin.”

“Ni kai ne damuwa ta, nasan idan na kyale ka, shekara daya tayi yawa ka durkusar da kamfanin nan.”

“Daddy kai ya fara yiwa tayin zama CEO a kamfanin nan amma kace baka da bukata. So please kaji da naka matsolilin, ni nasan yanda nake tafiyar da kamfani na.”

“Zan kyale ka ne duk ranar da ka iya handle emotions din ka.” Cewar Kamal da ransa ya fara baci.

“Ba'a ce dole sai mutum ya zama robot kafin ya iya tafiyar da kamfani ba. Ni ba kamar ka bane Kamal. Ba mai fatan ya zama kamar ka. Ina son naji ni a raye, in yi kuka idan abun kuka ya sameni haka ma dariya idan ina cikin farin ciki. Bana da ra'ayin cire duka wannan kawai saboda aiki.”

Cewar Amar shi ma cikin bacin duk da yasan ya dan wuce gona da iri wajen fadawa yayan sa wannan kalaman. Kuma ya yiwa yayan nasa farin sanin da yasan irin wannan kalaman suna taba shi amma ba zai taba nunawa ba. Sai dai ya kamata ya fada masa gaskiyar abinda yake tunani game da halin yayan nashi.

“Ni ba munafuki bane. Ba zan yi karyar dariya ko kuka ba domin nunawa mutane akwai ni. Ina yin abinda nake ganin ya dace ne, bana bukatar sai mutane sun soni. Amma idan kana tunanin gaba kake da ni saboda kana kewaye da mutane masu sonka, toh congratulations.”

Kamal kayan shi ya shiga tattara yana kokarin barin office din. Shi kuwa Amar yaji bai kyauta ba, kuma ba zai juri fushin dan uwan sa ba.

“Bro, tsaya please... Kayi hakuri akan abinda na fada maka... Ba wai nayi bane dan...”

“Kana bani hakuri ne saboda da gaske kayi nadama ko kuwa dan ka nuna min kai mutum ne mai kawa zuci? Toh ka sani emotions ba zasu amfanin komai ba idan dai ba abinda kake ji bane da gaske.” Kamal ya fada kafin yayi tafiyar sa ya bar dan uwan nasa yana tunani.

A bangaren Zahara kuwa, tsoron da take ji ya sake nunkuwa. Domin motsi kadan sai ta tuna da hannun da ya dafa ta dazun. Ta kasa gano me yake damun ta. Amma yanzun ta fara tunanin ko aljanu ne ke bibiyar ta. Idan kuwa haka ne me aljanun nan suke nema da ita? Me tayi masu? Wata kila idan ta samu tattaunawa dasu zasu fada mata abinda tayi masu, daga nan ma ta nemi yafiyar su, su shafa mata lafiya.

Har wajen karfe sha biyun rana, Zahara na bisa internet tana neman yadda ake korar aljani, ko yanda mutum zai yi magana da aljani mai bibiyar sa. Gaba daya tabi ta karanta duk wani posting dake bayani game da shafar aljanu. A wasu shafukan shawara ta samu akan ta yawaita saka suratul Bakara duk safe da yamma domin korar aljanin. Wasu kuma wuridi suka bata da zata yi da dare domin yin magana da aljanin. Amma ita tafi ganewa saka Al-kurani mai girma.

Tana cikin binciken nata, sai ga Sarat ta shigo a kidime...

“Mr. CEO yana ciki? Yanzu ya kira ni, yace yana nema na.” Sarat ta tambayi Zahara.

“Eh yana ciki.” Zahara ta bata amsa.

Koda ta shiga Zahara ta tuna bata kai takardun da ta bata ba. Oga yace kar ta yi. Ta ma manta da takardun na meeting ne. Addu'a take har cikin ranta Allah yasa dai kar Sarat ta tsane ta. Cikin rashin sa'a kuwa Sarat na fitowa ta wurgo mata wani mugun kallo wanda yasa Zahara shan jinin jikin ta.

“Idan kin san ba zaki je ba, me yasa baki fada min ba da ki je ki kaiwa Mr. CEO su. Ba'a taba wulakanta ni ba irin na yau.” Sarat ta fada kafin tayi gaba.

Idan da ta tsaya da Zahara tayi mata bayani zata fahimci cewa ba laifin ta bane taso da gaske taje ta kai takardun... Amma, koda yake yanzun bata da lokacin wannan, domin matsalar Sarat auta ce a cikin matsalolin da take fuskanta yanzu. In yaso daga baya ta ma Sarat bayani.

Komawa tayi ta zauna ta cigaba da abinda take. Da ta gaji ta aje ta shiga tunanin da ta saba, kafin Mr. Amar ya katse ta, ta dan tsorata domin bata san lokacin da yazo ba.

“Oh sorry na tsorata ki?” Ya fada.

A lokacin ita ko ya kankanin motsi yake ma tsoro yake bata.

“Ah ba komai.” Ta fada tana gyara zaman ta.

“Kin karasa aikin ne?”

“A'a saura kadan dai na karasa.”

“Kadan ya rage? Ok, zaki iya zuwa dashi gida ki karasa. Muje na aje ki, yau kusan unguwar ku zan je..”

Tunani take daman yasan gidan su. Nan take kuma ta tuna wata rana

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment