Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni ne sosai."

Sarat ta shararo wannan karyar. Saidai ba banza Mami take mahaifiyar ta ba. Dandanan take gane karya take yi.

Fiddo wayarta mahaifiyar Sarat tayi, ta shiga latsawa cikin kankanin lokaci sai ga wayar Sarat na ringing.

“Waya biyu gare ni yanzu." Cewar Sarat.

Saidai mahaifiyar Sarat bata tsaya kula ta ba, ta tashi ta nufi dakin Sarat. Sarat bata yi kokarin hana ta ba, domin hakan zai kara kwadaitawa mahaifiyar ta son shiga dakin.

A lokacin babu irin addu'ar da Sarat bata karanto ba domin tasan yau kashinta ya bushe.



A BANGAREN ZAHARA



“Na tabbatar kece kike tunanin haka." Cewar Maryam.

“Ba mahaukaciya bace ni. Duk lokacin da zamu hadu sai ya fadi rashin lafiya kuma ina yin nesa da shi zai dawo cikin koshin lafiya. Ina ganin ni ce ke saka shi rashin lafiya."

“Na fada miki Zahara wannan tunanin ki ne kawai. Ta yaya zaki iya bayanin kece ke saka shi rashin lafiya duk lokacin da kuka hadu? Nasan yana sonki amma ba irin wanda zai sa ya fadi rashin lafiya da ya ganki ba.” Maryam ta fada da sigar wasa dan ta kwantarwa da yar uwarta kuma kawarta hankali, saidai hankalin Zahara nesa yake da kwanciya.

“Maryam ina ji a jikina wani mummunan abu ne ke faruwa."

“Subhanallahi Zahara, ki daina fadar haka. Kin cika tunani da yawa, shi yasa har kin fara irin wannan zancen. Kawai ki ce baida lafiya ne kuma insha Allahu zai samu sauki.”

“Hakan saukin fada gare shi, idan ba'a san abinda ke faruwa ba."

“A kan me kike magana?” Maryam ta tambaye ta tana ajiye kofin tea dinta a kan center table.

“Ban sani ba, idan fa.."

“A'a kar ma ki fara, kar ki min maganar sihiri dan ni ban yarda da irin wannan abubuwan ba."

“Aljana ta taba shiga jiki na Maryam."

“Ba zan ce karya kike yi ba ! Dan haka dan Allah kar ki sa in fada. Yanzu mu je ki raka ni kasuwa kafin mijina ya dawo. Karfe nawa zaki je ki ga Kamal din?"

“Ban sani ba.. bana son zuwa.. ko kuma ince ba zan iya ba."

Ajiyar zuciya Maryam tayi.

“Me kike son yi kenan?"

Kallon ta Zahara tayi.

“Komai.. bansan me zan yi ba, kuma hakan ba karamin damuna yake ba."

Zahara ta kasa daina tunanin Amriya, amma kuma tana ganin mawuyaci ne Amriya ta sake dawowa. Shafa layar dake hannun ta tayi tare da kallon Maryam da itama take kallon ta.

A ranta tace ina ma zata iya nemo wannan tsohon.

“Tunanin me kike yi?" Cewar Mayarm.

“Komai, tashi muje kasuwar."

Kasuwa suka je, bayan sun yi siyayya Zahara ta kama mata suka sanya kayan bayan mota kafin Maryam ta kaita gidan Kamal. Tana son ta ganshi domin ta yi masa bayanin abinda take tunani, ta tabbatar shima irin tunanin yake amma yaki ya fada mata dan kar ta tashi hankalin ta.

Knocking kofar gidan tayi, kafin ta ji sautin tafiya na zuwa, ta gane Khadija ce. Zahara a ranta tace tana amfani da rashin lafiyar Kamal domin kara samun kusanci da shi, tinda ita Zahara babu abinda zata iya.

Zahara na tunanin Kamal ya yiwa Khadija zancen domin tana bude kofa ta hau Zahara da balbalin bala'i.

“Kin zo ne ki karasa shi ko me? Me yasa kika zo bayan kinsan kina sanya shi rashin lafiya?"

Zahara bata tsaya sauraron ta ba, ta wuce kai tsaye cikin gidan. Dakin saurayin nata ta nufa ta tarar da shi zaune yana cin abinci. Da alamu yana cikin koshin lafiya.

Murmushi yayi mata koda ya ganta. Ita ma ta mayar masa da martani saidai ita nata kamar yake tayi.

“Yanzu nake shirin kiran ki." Yace da ita.

“Gani nazo amma zan iya dawowa wani lokacin idan kana so." Tace da shi.

Daidai lokacin Khadija ta shigo.

“Bar mu dan Allah muyi magana Khadija.”

“Amma.." Tayi kokarin musawa amma ta juya ta fita sakamakon wani kallo da Kamal ya watsa mata.

Koda Khadija ta fita, Kamal ya budewa Zahara hannuwan sa alamar tazo.

“Amma...ka..san.."

“I miss you so much.. I just want to..”

Bai kasara maganar da yake son fada ba, ya shiga yin tari kamar wanda aka shake. Zahara duk ta bi ta rikice, tana son taimaka masa amma bata san me zata yi ba. Tarin da Kamal yake yi ne ya janyo hankalin Khadija ta fado dakin da sauri tare da wata mata a bayan ta. Koda suka karaso Zahara ta gane Hajiya Karima ce mahaifiyar Kamal.

“Mommy kin ga abinda nake fada miki ko? Yarinyar nan mayya ce, duk lokacin da ta kusanci inda yake sai ya kwanta rashin lafiya. Lafiya lau fa, yake yanzu yake cewa zai dan fita yaga gari. Na fada miki muguwa ce." Cewar Khadija tana ture Zahara domin zuwa kusa da abokin ta.

Wani mugun kallo Mahaifiyar Kamal ta yiwa Zahara kafin ta fiddo wayarta. Hannuwan ta na rawa ta kira ambulance.

“Fice min daga nan yanzu, bana son kara ganin ki kusa da dana." Hajiya Karima ta cewa Zahara bayan ta gama wayar.

Cike da jin kunyar tsintar kanta a tsakanin mutanen nan, Zahara ta fita da gudu daga gidan. A ranta tana cewa suna da gaskiya, laifin ta ne idan baida lafiya.

Idan tayi nesa da shi, ba zai kara cutuwa ba.


BANGAREN SARAT DA AMMAR

“Me ya kai ka zuwa nan a wannan lokacin? Baku da gida ne ko me? Kana tunanin tarbiya ce mai kyau mace da namiji babu aure tsakanin su, su kadaice cikin daki daya?”

“Kiyi hakuri dan Allah Hajiya, insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba." Cewar Ammar.

“Idan har da gaske kana son 'yata kazo ka nemi aurenta mana."

Kallon Sarat Ammar yayi itama ta kalle shi. Tana kuka kasa-kasa tana rokon sa da idanu.

“Zan yi tunani insha Allahu Hajiya.”

“Na baka nan da gobe kayi tunani, idan ba zaka aure ta ba kar ka sake zuwa nan kana zubar mata da mutunci. Ka jini ko?"

“Naji Hajiya."

“Shikenan, zaka iya tafiya ina son yin magana da 'yata."

Yaso tsayawa domin dafawa Sarat amma mahaifiyar ta, cikin fushi take sosai ta yanda babu abinda zai iya yi.

“Ni ne da laifi, kiyi kokarin fahimtar ta dan Allah."

“Inyi kokarin fahimtar ta kamar yaya? Kana nufin ban baiwa 'yata tarbiya ba ko me? Kar ka shiga abinda babu ruwan ka.”

Hakuri ya kara bata kafin ya dauki jacket din sa ya bar gidan.

Ina ma zai iya auren Sarat din. Shi abinda yasa yazo gun Sarat gudun auren ne yayi kuma ba zai so ya sake fadawa wata chakwakiyar ba.

Bai bata lokaci ba yayi tsinke gidan sa, da shigar sa yaji kamshin soyayyun kaji ya bade masa hanci. Afnan ce yau ma ta sake hada girki mai dadi. Wanke hannu yayi da niyyar cin abinci.

Dakin da Afnan take ya leka dan yi mata godiya da girkin da tayi amma ya tarar tana bacci.

Shi ma yana bukatar hutun domin kwana biyu baya samun bacci sosai. Tun lokacin da Salmah ta fara yawo da sabon saurayin ta, ya daina samun sukuni. Yayi kokarin shima ya manta da ita amma hakan da ciwo ba zai iya ba.

Ganin ta tare da wani ba karamin kunci yake shiga ba. Ya yarda yayi amfani da Sarat dan ya sa Salmah kishi amma ya lura ita ko a jikin ta : hakan yasa ya fara tunanin dama cen bata taba son sa ba.


(....)


Washe gari, yayi sauko wajen aiki. Ya hadu da Sarat tace masa tana son yin magana da shi. Ya jira ta duka yinin ranar amma bata zo ba. Daga baya ne ta kira shi tace tana son suyi maganar ne wajen kamfani. Yana kokarin tafiya sai ga likitan Afnan Dr. Abdallah yazo.

Sam Ammar ya manta da likitan zai zo yau, kuma Zahara bata tuna masa ba. Ya lura kwana biyu bata yin aikin ta da kyau, yana son yayi magana da ita domin ba zai yiwu aiki ya cigaba a haka ba.

Bayan Dr. Abdallah ya shigo suka gaisa, Mr. Ammar yayi masa tayin wurin zama.

“Thanks. Sorry kan makarar da nayi. Ayyuka ne suka min yawa a hospital." Cewar D. Abdallah.

“Kar ka damu, nima ayyuka sun min yawa anan. Ko zaka sha wani abu ne?”

“A'a nagode, nazo ne ina son muyi wata magana mai muhimmanci."

“Ok ina sauraron ka."

“Magana ce akan kanwar ka. Kamar yanda na fada maka, ta yarda tayi min magana. Kuma nayi iya kokari wajen ganin na taimaka mata.”

Gyada kai Ammar yayi alamar gamsuwa.

“Abubuwan da nake tattaunawa da patients sirri ne da bana fitarwa, amma idan an aikata wani crime ya zama dole na fada domin a dauki mataki na gaggawa akan criminel din.”

“Ban fahimta ba. Me kake son fada? Wani crime aka aikata?” Ammar ya tambayi Doctor hankali a tashe.

“Abinda nake kokarin fada maka yanzu baida dadin ji amma ya zama dole ka sani.”

“Please Doctor ka fada ina sauraron ka."

“Mahaifinku shi ya yiwa kanwar ku fyade.. kuma ba sau daya ba. Idan baka dauki mataki ba ni zan je da kaina na kai karar sa wurin yan sanda kuma zan yi amfani da duk wani karfi na ganin na shawo kan Afnan ta bada shaida. Fatan zaka dauki mataki mai kyau da kanka.”

“Kace mahaifi na? Kar ka raina min hankali Doctor ! Kamar yaya fyade aka mata?”

“Ba zan yi gangancin bayyana abinda ba gaskiya ba, kanwar ka ta fada min komai kuma sai da na tabbatar ba karya take yi ba."

“Kace mahaifina shi ya yiwa kanwa ta fyade? Yar uwata Afnan? A'a ! Ba zai yiwu ba, wannan ba gaskiya bane domin mahaifina ko kuda ba zai iya cutarwa ba."

“Ka kwantar da hankalin ka sannan kayi tunani."

“Ta yaya zan kwantar da hankali na bayan abinda kazo ka fada min? Wannan ba karamar magana bace Doctor ina son yin magana da yar uwata."

“Zaka iya magana da yar uwarka, amma kar ka takura ta domin har yanzu rauni gareta. Ya kamata taji zata iya dogaro da kai, kar ka sa wannan kwarin gwiwar nata ya rushe."

“Ba zan maka alkawarin komai ba, ina son sanin idan da gaske ne ko a'a.."

Ya tabbatar kuskuren fahimta ne, ba zai taba zama gaskiya ba.. a'a.. ba dai mahaifin su ba.. Mommy ta fada masa wani saurayi ne ya yiwa Afnan ciki. Wata kila shi ne wanda yayi mata fyaden. Toh me yasa zata zargi mahaifin su...?


To be continued....
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels http://www.ashblogg.com.ng/search/label/Hausa%20Novels

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 25

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚




Watanni sun shude kuma abubuwa da dama sun faru.

Kamal har yanzu cikin bakin ciki yake tun lokacin da ɗan uwansa ya faɗa masa abinda mahaifinsu ya aikata. Kamal bai iya haɗa idanu da Afnan; babu wanda yake iya yin hakan duk da ƙoƙarin da suke yi wajen nuna kamar komai bai faru ba. Yayyun Afnan din sun yi mata alƙawarin cigaba da kallonta kamar a baya amma bata san kawai dauriya ce suke yi ba. Ba mai yiyuwa bane nuna kamar komai bai faru ba.

A ranar nan lokacin da Ammar ya kira family meeting kuma kowa yazo, har da Kamal da yake asibiti sai da ya nemi da a kawo shi gida. Ya gaji da zaman asibitin kuma wannan meeting din sai ya zamar masa wata dama, duk da ƙaguwar baro asibitin nasa ta ɓace lokacin da yaji gaskiyar dalilin kiran meeting din.

Ammar yazo da Afnan. Daddy kuwa sai muzurai yake, yana kallon Afnan cike da tsana. Yaso yayi wani wasan kwaikwayo a wurin kuma ya tari Afnan hannu biyu saidai hakan bai yiyu ba sakamakon tsanar da yake ji game da yarinyar. Abinda bai sani ba, Afnan ba zata bari yayi magana ba ko yin dramar da ya shiryo ba. Tana jin wani ƙwarin gwiwa a tattare da ita sakamakon kasancewar Ammar a gefenta. Ba zata ce bata jin tsoro ba, amma tana jinta cikin tsaro kuma a shirye take domin tunkarar wannan dodon.

Lokacin da Hajiya Karima ta dawo gida tareda ɗanta Kamal da kuma daya daga cikin nurses na asibitin, Mijinta da Afnan na zaune a falo babu yanayin alkhairi a yanda ta gane su, dandanan ta fahimci meke faruwa. Kuma ta fahimci lallai familynta bai gama rushewa ba.

Cikin yanayin ɓacin rai ta taimakawa Kamal ya zauna. Ta gaishe da mijinta bayan ta ba banza ajiyar Ammar da Afnan. Wuri ta samu ta zauna sannan ta fara magana
“Me ya kawo ku gidana?” Tace da Ammar da Afnan.

“Ki yarda naso kar na sake tako ƙafata cikin gidan nan.” Cewar Ammar.

Daddy da tun dazu yayi nisa cikin tunani yace
“Ɗanki ne ke zargi na da aikata wani abu marar dadin faɗa, har kunya nake ji na furta hakan.”

“Afnan, kin rantse sai kin wargaza min iyali ko? Bayan kin je kin yi karuwancin ki waje shine kike son ni ki zo bata min sunan ahali ko? Me na faɗa miki a baya?”

“Kin san da zancen kenan?” Cewar Ammar da mamaki. “Kuma shine baki ce komai ba?”

“Saboda ƙarya take, kawai tana son wanke kanta ne ta hanyar ɓata nawa gidan. Ba zan yarda da wannan ba!” Cewar Mommy.

“Wai meke faruwa ne?” Kamal ya tambaya da muryarsa ta marasa lafiya.

“Ba komai ɗana, bari na sa nurse ya kai ka tsohon ɗakinka domin ka huta.” Cewar mahaifiyar tasu.

“Ba komai? Wannan mutumin da muke kallo a mahaifinmu shi ya yiwa Afnan fyaɗe.”

Da farko Kamal bai fahimci komai ba, amma da maganar ta rasa illahirin ƙwalwarsa, waro idanu yayi ya kalli Daddy ya kalli Ammar.

“Rufe min baki.” Cewar Hajiya Karima. “Kar na sake jin ka ƙara faɗar irin wannan shirmen ƙanzon ƙuregen da bakinka."

Afnan ɓoye fuskarta tayi da tafin hannuwanta a bayan Ammar. Shi kuwa Daddy gefe yake kallo ba tareda ɗaya daga cikinsu ya canki abinda yake tunani ba.

“Tsaya Ammar. Wannan fa ba ƙaramar magana bace. Na kasa fahimta, kayi min bayanin abinda ya faru.” Cewar Kamal.

Ammar ya fara bashi labarin duk abinda ya sani da kuma yanda yayi ya gane gaskiya. Lokacin da ya ƙare, Kamal ya kalli Afnan yace
“Afnan, dagaske ne abinda ya faɗa?”

Afnan bata ce komai ba na tsawon wasu mintuna.

“Dagaske ne abinda ya faɗa?” Kamal ya ƙara tambayar ta wannan karon gyaɗa kai tayi alamar eh.

Kunya ce sosai ta lulluɓe Kamal ya rasa me zai yi. Wannan ne na farko da yaji kunya na kasancewar shi ɗan wannan mutumin. Ya tabbatar da gaskiyar Afnan da Ammar, yana jin ina ma ace mafarki yake.

“Barin wannan maciya amanar zaka yi su zubar maka da mutunci?” Hajiya Karima ta juya kan mijinta da yayi shuru bai ce komai ba.

“Shikenan a ɗauka da gaske ne abinda ta faɗa, ina son ganin hujjoji. Idan naga hujjojin cewar mijina ne ya yiwa yarinyar nan fyaɗe ni da kaina zan kai ƙararshi."

“Bama bukatar nuna miki hujjah idan baki yarda ba shikenan. Bana bukatar taimakonki wajen yin wani abu. Amma jin cewa kinsan da wannan zancen baki faɗa mana komai ba na gane kin wuce yanda nake tunani. Koda na fahimci kin ƙirƙiri wani labari kawai dan ki kare daddy naji ina son barin gidan nan, na ƙara yin nesa da shi. Kuma ina son ku saurari sammacin kotu."

“Shikenan...” Cewar Daddy da ya dawo hayyacinsa.

“Ban gane shikenan ba? ƙoƙarin wargaza mu fa yake kuma kasan kamfanoni zasu durƙushe.” Cewar Mommy.
Ta ƙara da cewa
“Ina guje maka ranar da zaka san ainihin wacece wannan yarinyar, ranar zaka yi baƙin ciki. Zaka yi nadamar yiwa mahaifinka sharri da kuma juya mana baya da kayi. Kayi nadamar yarda da maganar wannan makirar, rayuwarka ta zama babu komai sai wahala..”

“Wahala ce a rayuwata tun lokacin da na gane abinda iyayena ke iya aikatawa, bana tunanin akwai wani baƙin ciki da yafi wannan. Ina fata adalci yayi halinsa."

“Ina fatan haka nima.." Daddy ya faɗa cen ƙasan maƙoshi. “Zan yi iya ƙoƙarina wajen dawo da mutuncina da ka zubar na yimin wannan mummunan sharrin. Ke kuma Afnan bansan me nayi miki ba da zaki saka min ta wannan hanyar. Bansan cewa sakamakon da zan samu na zamar miki uba da nayi ba shine sharrin fyaɗe.” Ya fada da ƙaramar murya ba tareda ya kalli kowanne daga cikinsu ba.

“Babu abinda kayi, baka buƙatar sai ka faɗa my love. Na yarda da kai, na yarda ba zaka taɓa aikata hakan ba. Allah yana tare da mu.”

Tashi Ammar yayi sannan ya taimakawa Afnan ta tashi.

“Ina fata wannan ne na ƙarshe da zan ganku cikin wannan gidan." Cewar Hajiya Karima.

“Kar ki damu Hajiya koda yunwa zata kashe ni ba zan ƙara saka ƙafata a gidan nan ba." Cewar Ammar kafin ya juya ya cema Kamal sai sun haɗu gidansa.

Kamal bai bashi amsa ba, domin babu wannan kwarin gwiwar a tattare da shi.

Koda suka fita daga gidan Afnan ta fashe da kuka.

“Bana son ka rabu da su saboda ni.” Cewar Afnan.

“Ban rabu da su ba saboda ke. Ki daina faɗar haka bana so. Ki daina kuka please. Idan da gaske kina son ki taimakamin wajen taimaka miki ya kamata ki daina ganin laifinki. Babu laifinki a cikin duk wannan."

“Eh amma..”

“A'a, babu amma. Komai zai yi daidai. Na tabbatar Kamal a ɓarinmu yake. Ba zamu kasance mu kaɗai ba.”

Haka aka yi koda Kamal ya samu sauki, ya nunawa su Ammar da yana tare da su. Makonni sun shuɗe kuma sun shigar da Alhaji Yusuf ƙara kotu. Cikin sa'a suka samu Rakiya yar aikin gidan tace zata bada shaida domin tasan abubuwa da dama. Lauyen Afnan din yace mata lauyen Daddy zai iya tsorata ta akan me yasa bata faɗa ba tun farko amma ya samar mata hanyar da zata bi ta bashi amsa mai kyau ba tare da an zarge ta ba.

A yanzu haka suna cikin haɗa ƙwaƙwaran file ne na shari'ar da za'a yi nan da wata huɗu.



(.......)


Kamal ne ke fama da yin wani zane da zai yiwa wani balarabe da zai bawa matarsa a matsayin kyauta na birthday ɗinta. Kamal yana ɓata lokaci sosai akan zanen dan ganin ya ƙawatu da kyau.

Amma wannan ranar, wani abu na damun Kamal. Yanzu yake tunanin kusan wasu watanni kenan rabon da yaga Zahara ko jin labarinta kuma abun mamakin bayada bukatar ji. Duk lokacin da ya ɗauki waya da niyyar kiranta sai ya manta kuma ba zai sake tunawa ba. Kuma abinda yafi bashi mamaki, baya jin kewarta ko kaɗan. Irin abinda yake ji game da ita duk ya ɓace, kamar ma hakan bai taɓa faruwa ba. Hakan na damun sa sosai domin yayi imani da soyayyar da yake yi mata. Ya kasa fahimtar meke faruwa kuma baya son sanin meke faruwan.

Ya kan ji a duk lokacin da yaso ya nemi sanin me yasa yake sauyawa game da Zahara wani abu na hana shi kuma sai ya tilasta shi mayar da hankali ga wani abun daban.

A ɓangare ɗaya kuma rayuwa sai yiwa Khadija daɗi take. Kowace rana da zata wuce, tana jin ƙara samun kusanci da Kamal take. Bai iya kwana biyu ba tare da yaji labarinta ba, kullum ciki son ganinta yake da son jin muryarta. Har ya nemi da Khadija ta kwana a gidanshi, abinda bai taɓa yi ba a baya kuma yake nadamar aikata shi. Saidai ita Khadija hakan da ya nema bai wani dameta ba.

A wannan daren, sha'awa ta rufewa Kamal idanu. Ya nunawa Khadija adadin yanda take jan hankalinsa. Sun aikata a ko'ina, a falo, cikin kitchen, cikin ɗaki har cikin bathroom ma.

Washe gari, Khadija tayi sauko wajen aiki. Fuskarta cike da annuri kamar wacce aka yiwa albishir da gidan aljanna. Tana cikin murna domin burinta ya cika, Kamal ya kamu da sonta. Me kuma zata nema bayan wannan? Komai ya tafi da sauri ta yanda har yau ta kasa yarda. Abu ɗaya ya rage mata yanzu shine AURE !



(.....)


“Ba dai haka zaki zauna ba, har sai kin ƙarar da hawayenki akan wannan mutumin?" Cewar Maryam tare da dauke pillow din da ta jefawa Zahara.

Komawa Zahara tayi gefen gado tareda share Maryam dake ta faman masifa domin da alamu ta saba.

“Zahara! Wai kina saurare na kuwa? Ki daina wani abu kamar yarinyar ki tashi! Ba zaki ɓata watanni kina kuka akan mutumin da bai damu da ke ba. Ki tuna ajinki mana..”

Wani sabon baƙin ciki ne ya mamaye Zahara, taji kamar Maryam ta caka mata wuƙa amma kuma tasan gaskiya ta faɗa. Kamal bai damu da ita ba.

“Ya isa haka, yanzu ki tashi ki shirya ki je wajen aiki kamar yanda kike yi a baya kafin ki haɗu da shi. Kina tayar da hankalin kowa."

“Idan da kin san yanda nake ji.."

“Ki yarda da ni, nasan abinda kike ji fiye da kowa.” Maryam ta bata amsa cikin sanyin murya wannan karon. “Ba zaki cigaba da cutar da kanki ba alhali shi yana cen yana sheƙe ayarsa wa ya sani."

“Nasan wannan nisan da nayi da shi shine mafita. Nice silar duk wani hali da yake ciki. Wata kila hakan ne yafi. Amma ba zan iya hana kaina tunaninsa ba.. nayi kewarsa sosai har yasa ina jin zafi. Ina jin ciwo sosai Maryam.”

“Bansan me zan ce miki ba.” Cewar Maryam. “I'm really Sorry.. kinsan wani abu? Ni zan je in ganshi.” Maryam ta faɗa tare da saukowa da sauri daga bisa gadon.

“What? A'a!" Cewar Zahara. “Kar kiyi hakan."

“Saboda me? Kawai ina son gane dalilin da yasa yake miki...”

“A'a..a'a..a'a.." Zahara ta katse ta. “Bana son sanin komai.. please kar ki aikata hakan.”

“Toh ni dai ina son sanin meke faruwa kuma yanzu zan je. Ai nasan gidan nashi.”

Maryam ɗaukar gyalenta da takalminta tayi da sauri ta fice daga ɗakin kawar tata. Tashi Zahara tayi domin taro Maryam da tuni ta daɗe da fita daga gidan.

TO BE CONTINUED...


Readers na daina jin ra'ayoyinku gameda wannan labari. Ya kamata ku fito domin labari ya fara nisa nasan duk kuna nan kun yi likimo. 😇
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

CHAPTER 26


I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 26 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”

http://www.ashblogg.com.ng/2022/02/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-26.html


“Sai an wuce asibiti gidansa yake ko kuwa kafin a kai? Ina tunanin na ɗan manta takamaimai inda gidan yake.” Maryam ta cewa Zahara da sigar wasa.

Zahara gyara ɗakin da ta duk yamutse tayi, ita kuwa Maryam ta zauna bakin gado tana kallonta.

“Well, ina ga kinada gaskiya, ba shawara ce mai kyau ba zuwa gidan Kamal koda kuwa ina son zuwa. Bansan me zan ce masa ba, kuma nasan lamarin ne zan ƙara dagulewa maimakon inyi gyara.” Cewar Maryam.

“Naji daɗi da kika gane hakan, ban son yayi tunanin ni marar yawo ce da ba zan iya mantawa da komai ba, na cigaba da harkar gabana. Ina son cigaba da rayuwata kamar baya, wacce nake yi kafin in san shi.” Cewar Zahara.

“Ba rashin wayo bane gareki, ke mutum ce shi yasa. Wannan ce wahalar soyayyarki ta farko, kuma kinada ƴancin yin kuka. Amma kinada gaskiya, yanada kyau kiyi gaba, ki ƙara sanin wasu sabbin abubuwan rayuwa. Saidai ba zai yiwu na barki ki koma rayuwarki ta baya ba, a'a wannan ba yiyuwa bane. Zahara lokaci yayi da zaki zauna kiyi tunani akan ƙarancin yardarki. Ya kamata mu nemo wata hanyar canza hakan.”

“Ba abu bane da za'a iya zancawa, yau ko gobe." Cewar Zahara.

“Haka ne, amma ke babu wani ƙoƙari da kike yi. Zan kama miki amma kece zaki yi aikin mafi muhimmanci.”

“Eh na sani Maryam, ki yarda da ni, ina son na canza."

“Toh, yanzu mu ɗan fita. Mu je muci wani abun a waje."

“Ina?”

“Suprise ne!”

“Idan mijinki ya kira fa?"

“Bah what? Ni ba prisoner shi bace, ina zuwa inda nake so. Essential shine nasan inda nake saka ƙafata. Ya yarda da ni kuma yasan adadin yanda nake sonsa.” Maryam ta faɗa tana murmushi.

“Mtsw sannu Romeo da Juliet. Well.. ina son fita amma na gaji ba zan iya ba.” Zahara ta faɗa tareda komawa bisa gado tayi kwanciyarta.

Ba tareda ta shirya ba taji Maryam ta janyo ta daga bisa gadon, sai gata ta faɗo ƙasa.

“Wayyoo karya ni kike son yi ko me? Da fa na karya hannu.”

“Hannun naki ya karye ne?” Maryam ta tambaye ta.

“Ina tunanin bai karye ba amma...”

“Good, tashi kiyi wanka, ni zan fiddo miki kayan da zaki saka.”

“Hum ban yarda da ke ba, idan basu mini ba, ba zan saka ba."

“Ban damu da ra'ayinki ba, oya je kiyi wanka sai wari kike!”

“Nan fa ƙarya kike yarinya.” Zahara ta fada tareda tashi daga ƙasa.

“Ki je kiyi wanka ki daina wannan surutun dan Allah!” Cewar Maryam tareda jefawa Zahara pillow.

“Zan je dan Allah, daina ɗaga murya.” Zahara ta faɗa tareda shigewa bathroom kafin Maryam ta tashi gidan.


BANGAREN KHADIJA


Khadija na tunanin ciki ne da ita. Bata da wani ƙonƙonto akan hakan. Tun bayan wasu makonni, take jin alamar

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment