Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, me yasa kuke barin kowanne mutum yana shigowa ciki?”

Security ba tareda ya kara jiran ko minti daya ba, ya damki Ammar ya fitar da shi waje. Bai kuwa sha wahalar fitar da shi ba domin yanda yake da girma. Duk da kokowar da Ammar yake amma saida security'n ya fitar da shi ba tare da wata matsala ba.

“Zamu hade Salmah, na rantse miki zamu hadu.” Ya kwalla kwarai yanda zata jishi.

Ba tareda ya jira jin gargadin da security yake masa ba, ya shiga mota ya nufi gidan Kamal.


(....)


“Dariyar me kake yi? Na fada maka fa Salmah taci amana ta.” Ammar ya fada cike da takaicin yanda dan uwan nashi bai dauki maganar da muhimmanci ba.

“Ni kuma na fada ma ba cin amanar ka tayi ba, daman ta fada maka bata bukatar ka yanzu.”

“Eh amma tana cikin fushi ne, ba hakan bane a zuciyar ta.”

“Sosai haka ne a ranta." Cewar Kamal yana kokarin rike dariyar sa.

“Shikenan, ni zan wuce gida na."

“Ka kwana nan, I need your help dan ban karasa warkewa ba."

“Je ka ga Zaharar ka, ni gida zan je."

“Kar kayi haka, da gaske I need your help."

“Shikenan amma gobe tun da safe zan yi tafiya ta, domin zan je in ga Dr. Abdallah daga nan in wuce gidan su Salmah domin ban kare da ita ba."

“Yaya akwai wani cigaba game da lamarin Afnan?"

“Eh, a yanda Dr. Abdallah yayi min bayani ta amince zata yi magana da shi. Shi yasa ma yake son gani na."

“Toh Allah yasa komai yaje daidai. Me zai hana ka mayar da ita gidan ka?” Kamal ya tambaye shi.

“Nayi wannan tunanin nima. Amma nafi son ka dawo da ita nan wurin ka, ganin ni inada aiki sosai ina tunanin zata fi sakewa nan."

“Ni akwai tafiyar da zan yi cikin makon nan, akwai wasu ayyuka da nake son kammalawa kafin na bude workshop dina."

“Ah, daman baka watsar da wannan project din ba?"

“A'a, ni ban taba tunanin haka ba. A ina kaji wannan?”

“Nayi tunanin zaka cigaba da zuwa kana dafa min a kamfani."

“Boye murnar ka, nasan ka jima kana mafarkin jagorantar wannan kamfanin kai kadai. Kuma kasan bani da ra'ayin harkar kamfanin nan, daman ina zuwa ne domin baka shawarwari ganin kai sabo ne a jagorantar babban kamfani kuma naga kana kokari sosai dan haka nima zan karkata gun nawa mafarkan.”

“I will support you whatever happens.” Cewar Ammar.

“Thanks." Kamal ya fada. “Kuma idan na dawo ina son zuwa neman auren Zahara.”

“What? Amma wasa kake ko?”

“A'a ! "

“It Zaharan ta amince ne? Bai yi wuri ba yanzu? Kay ! Yarinya ce fa har yanzu."

“Mun yanke zamu yi aure wata mai zuwa.”

“Amma tilasta ta kayi ko?”

“Kamar yaya, me yasa zan tilasta ta?”

“Abin ne da mamaki, ni dai nasan kai da ba son rayuwa kake da mutane ba, har ma da mu, yanzu kuma kace min zaka yi aure? Na tabbatar ka sihirce Zahara dan ta amince. Ko kuma ita ce ta sihirce ka dan ka fara tunanin aure.”

“Ba yaro bane ni yanzu kuma ina ganin Zahara ita ce matar da ta dace da ni. Ba zan so in batawa kaina lokaci ba.”

“Ita kuma Khadija fa?" Ammar ya tambaye shi.

“Khadija me?”

“Tana da labari?”

“A'a zan yi mata maganar idan na dawo. Kuma ina son yi mata magana game da abinda take wa Zahara, bana jin dadin hakan. Domin Zahara a takure take kuma na fahimci hakan.”

“Ba dai sun hadu ba?” Ammar ya fada da mamaki yana mai kara matsawa inda Kamal yake kwance.

“Eh.. akwai zafi-zafi tsakanin su.”

“Rayuwar ka kamar shirin film bro, ya kamata ka dinga yimin update duk sati. Me kake jira, na fada maka irin son da Khadija take maka. Amma ka ki ka bude ido.”

“Ta fada min, ta fahimci mu biyu ba mai yiyuwa bane, ta fahimta amma ni ba haka yanayin ta ya nuna min ba.”

“Haka ta fada ma? Da mamaki amma ina baka shawara da ka bata lokaci zata dawo daidai.”

“Zan yi mata magana. Ina son ta fahimta a yita ta kare.”

“Allah ya bada sa'a. Amma har yanzu mamaki nake wai zaka yi aure kuma Zahara zaka aura. Zan so kuwa ganin yanda rayuwar ku zata kasance as a couple.”

“Kaji da Salmah da Hafsat shi yafi ma. Yaushe zaka je ka ga Mom?”

“Daina min wannan zancen ko nayi tafiya ta."

“Kasan dai ba zaka cigaba da share ta ba, ko mai ta aikata maka ba zaka taba canza sunanta ba na mahaifiyar ka. Ba karamin hatsari bane abinda kake yi. Kasan darajar da iyayen suke da ita."

“Kai ni kaga tafiya ta, Allah ya koro sauki.” Cewar Ammar yana mikewa tsaye.

“Ka yiwa kanka karatun ta nutsu dai.”

“Zan je wajen Sarat, domin ita kadai ke fahimta ta a halin yanzu.”

“Wacece kuma Sarat?”

“Bar zancen, na tafi.”



To be continued...
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels http://www.ashblogg.com.ng/search/label/Hausa%20Novels

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 24

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚


Ammar bai iya tuna ko ta yaya yazo gidansu ba, domin sam hankalinsa baya jikinsa sosai yake cikin shock. Tambayoyi ne a cunkushe cikin kansa. Da saurinsa yake tafe da son yaga ya karasa ƙuryar gidan amma gidan kamar kara tsayi yake. Ko mai gadi bai yi gangancin gaishe shi ba ganin yanayin da yake ciki. Yanada gaskiya domin Ammar baida lokaci da ƙarfin tsayawa amsar wata gaisuwa.

Shiga yayi cikin falon tattare da duk wani ƙunci da yake ji a zuciyarsa. Yana tafiya ne kamar wani saƙago mai aiki da remote, burinsa ya san gaskiya ko nauyin da yake ji a zuciyarsa zai ragu. Har Ammar yana ganin kawai saɓanin fahimta ne kuma zai fanshi kanshi ne yayin da yaji gaskiyar lamarin, domin a cen ƙasan zuciyarsa yasan ba gaskiya bane. Duk da maihaifinsu ba mazauni bane, amma ɗan zaman da yayi da shi ya isheshi yace mahaifinsa yana cikin mutanen kirki da ya sani.

Koma dai meye ya kamata ya ƙara tabbatarwa da kansa.

Hawan sama yayi zuwa hanyar ɗakin mahaifin nasu kamar yanda yasan hanyar tamkar yunwar cikinsa. Wannan ne na farko da jimawa sosai da yaji tsoron tunkarar shiga ɗakin. Wannan yanayin ya tuna masa da shekaru da dama baya, lokacin da idan yayi laifi dole yazo yayi bayani gaban iyayensa. Bambanci a wannan ranar shine za'a yiwa bayani. Kuma wannan karon yaji ina ma ace shine dai yaron nan da zai zo yayi bayanin laifin da ya aikata.

Daga ƙarshe ya iso bakin ƙofar, tafiyar da yaga tayi masa tsayi sosai. Knocking yayi sau biyu sannan ya jira.

Jiran da yayi na wasu sakanni yaji kamar yayi jira na awanni ne kafin mahaifinsa yazo ya buɗe.

“Ah kai ne. Daga asibiti kake?” Cewar Mahaifinsa.

Kallon sa Ammar yayi da alamar tambaya.

“Bakada labari ne? Ɗan uwanka baida lafiya. Mommynka na cen, nima yanzu nake ƙoƙarin tafiya."

Ammar a ransa yake tambaya idan tunani ne mai kyau ya yiwa maihaifinsa zancen yanzu. Wani tunanin ne ya kara zo masa : ba kowane irin zance bane wannan, ana maganar fyaɗe ne, gara suyi maganar yanzu a yita-ta-kare.

Wata tambayar ce ta sake zuwar masa wacce ke da wahalar amsawa : Ta ina zai fara yiwa mahaifinsa wannan zancen?

Alhaji Yusuf ganin yanayin da ɗansa yake ciki, ya fara jin zufa na karyo masa.

“Meke faruwa ne?" Cewar Daddy.

“Ina son muyi magana ne akan Afnan.” Ammar ya faɗa a wahalce.

Tsayuwa ce ta so ta gagari Daddy jin dansa ya ambaci sunan ƴar ƙanwar matarsa. Zuciyarsa ta shiga dukan uku-uku, yayi kokarin ya daidaita nutsuwarsa amma hakan yaci tura hakan yasa ɗansa ya fahimci akwai abinda mahaifin nasa ke ɓoyewa.

“Wani abu ya same ta ne?” Daddy ya tambaya.

“A'a lafiya lau ko kuma in ce ina tunanin lafiya take har lokacin da doctor ya faɗa min wasu abubuwa da na kasa fahimta."

“Ba an hanasu fitar da sirrin patients ba?” Cewar Daddy.

“Sai idan babu wani crime da ya auku.” Ammar ya bashi amsa.

Ta ƙare masa Daddy ya faɗa a ransa. Jiya ya kira, wani ɗan abokinsa wanda yake yi masa duk wani abu da yake so. Ya faɗa masa su shirya yin kidnapping ɗin Afnan su yi nesa da shi. Ya shirya kuɗaɗe masu yawa da zai bata da zata iya wata sabuwar rayuwa nesa da su. Ya cewa ɗan abokin nasa da ya bashi nan da sati ɗaya ya yi tunanin ƙasar da zasu kai Afnan.

«Da na kawar da ita, tun lokacin da na samu dama.» Daddy ya faɗa a zuciyarsa.

“Daddy, dagaske ka yiwa wannan yarinyar fyaɗe?" Ammar ya tambaye shi da tsananin ƙuna a zuciyarsa, yana jin wahalar ambatar sunan fyaɗe da kuma mahaifi a lokaci guda.

Shuru Daddy yayi, amma tashin hankali ne a cen cikinsa. Muryoyi biyu ne ke faɗa cikin kansa. Kuma wacce tafi naci tayi nasara, ba zai taɓa yiyuwa ya amsa wannan laifin ba. Kuma duk yanda aka yi ma babu shaida, maganarsa ce against maganar Afnan. Daddy yana tunanin tasirin da yake da ga Afnan yanada karfi sosai ta yanda zai iya juye laifin kaf a kanta.

Dole ma ya jajurce.

“Maganar me kake yi Ammar? Ta yaya ka iya tunanin daidai da rana daya zan iya aikata irin wannan abun? Afnan kamar ƴata take, na rene ta da duka iya soyayyar duniyar nan. Ta yaya zan iya aikata hakan? Ita ta faɗa maka haka?”

“A'a Doctor ne, kuma nasan..”

“Toh kuma shine zaka zargeni, ba tareda kayi magana da Afnan din ba? Kana son ka tozarta ni ne ba tareda ka samu wata ƙwaƙwarar hujja ba? Me kake nufi ne Ammar?"

“Wani buri Doctor zai cimma idan yayi min karya akan abu mai muhimmanci haka? Zai iya rasa komai idan ta tabbata abinda ya faɗa ba gaskiya bane. Bana tunanin mutum mai ilimi irin Dr. Abdallah zai iya yin hakan."

“Ai wannan ƙazafin zai iya taɓa mutuncina !” Cewar Daddy wannan karon da ɗaga murya. “Zan yi ƙarar wannan likitan.”

“Kafin hakan yayi nisa, zan yi magana da Afnan. Ita ce wacce abun yafi shafa, idan tace hakan ƙarya ne. Toh nan zamu iya shari'a da Dr. Abdallah."

“Yi sauri ka kirata. Amma ka sani ban ji daɗi ba ace ɗana bai yarda da ni ba.”

“Kai ka koya min sanin gaskiya kuma abinda nake ƙoƙarin yi ne yanzu a matsayina na mutum kuma babban yaya. Ko me zai faru ba zaka taɓa sauyawa daga matsayin mahaifina ba.” Cewar Ammar kafin ya fita ya bar mahaifinsa cikin zulumi.

Ammar bai ƙara jiran ko minti daya ba, ya wuce gidansa. Sai da yayi ta knocking sau ba adadi kafin Afnan ta zo ta buɗe masa.

“Zo ina son yin magana da ke.” Yace da ita.

Afnan ba tareda sanin abinda ke faruwa ba, taje ta samu ɗan uwanta.

“Fatan komai lafiya?” Ya tambaye ta dan kar ya rikita ta.


“Lafiya lau. Meke faruwa?" Ta tambaye shi domin hankalinta ya fara tashi. Zaunawa tayi saman kujerar da ke kusa da shi.

Juyowa Ammar yayi yana fuskantar ta a take yaji wani bakin ciki ya hayo masa zuciya. Bai taɓa kawowa a zahiri ko a tunani za'a ce mahaifinsa ya aikata makamancin hakan ba.

“Nayi tunanin idan wani abu ya same ki zaki iya faɗa min?" Ya faɗa ba tareda ya kalle ta ba.

Afnan ta fara tunanin akwai abinda ke faruwa, a take ta fara jin zufa kuma numfashi na kokarin ya gagare ta. A ranta tana tunanin ya aka yi ya sani.

“Eh.” Ta bashi amsa.

“Afnan, ko akwai abinda Daddy yayi miki?”

Daman tasan bai dace ta yarda da Doctor Abdallah ba, domin shi kaɗai ne zai faɗawa Ammar komai. Hajiya Karima da mijinta ba zasu taba yin hakan ba.

“Ki bani amsa Afnan!" Ya faɗa da yar tsawa.

Afnan bata ce komai ba, sai ma ƙasa da ta kurawa idanu. Tana tunanin me yasa ma zata bashi amsa. Tasan babu wanda zai yarda da abinda zata faɗa.

“Kalle ni Afnan."

Ammar ya tashi ya durkusa gabanta tareda dafa kafaɗunta.

“Ki faɗa min gaskiya. Kar kiji tsoron komai. Zan yi iya ƙoƙarina wajen kare ki, nayi miki alkawari. Amma dan na iya taimaka miki sai kin faɗa min komai. Kar ki barni cikin duhu."

Shuru Afnan taki magana.

“KIYI MAGANA AFNAN.” Ya faɗa da ƙarfi tareda girgizata har sai da ta fara kuka.

Ja baya yayi tareda komawa yayi zaune a ƙasa yana bata hakuri, amma Afnan sai ma ƙara sautin kukanta take. Nan ya fahimci lallai akwai abinda ya faru, yanayin da mahaifinsa ya shiga yanzu kuma ita. Babu wata tantama yanzu.

“Tashi muje.” Ya umurce ta bayan shima ya miƙe tsaye.

Kama hannun Afnan yayi ya nufi hanyar fita da ita.

“Yau za'a yita ta ƙare. Idan dagaske Daddy ne mai laifi, ina son ki fallasa shi. Kar kiji komai, ki fallasa shi. Nasan hakan ba sauki gareshi ba amma zan goyi bayanki ko me zai faru.”

“Babu abinda..ya faru..ka rabu da ni dan Allah.” Ta faɗa tana cigaba da kuka.

“Listen.." Ya faɗa yana fuskantar ta. “Ba zaki taɓa samun sukuni ba idan har baki ƙwaci ƴancinki ba ga wannan mutumin. Wata ƙila ki makaro ranar da zaki ji kin shirya fallasa shi. Kin san yadda ƙasar nan take kuma kin san yadda Daddy yake da ƙarfi. Ana dukan ƙarfe ne tun da zafinsa. Wannan jarabawa ce mai ciwo amma kowa zai goyi bayanki. Ba zan taɓa bari ki faɗi ƙasa ba. Kin ji koh?”

Gyaɗa kai Afnan tayi, shi kuwa Ammar ya rungumeta domin ƙara kwantar mata da hankali.

“Kawai ni zaman lafiya nake so.” Afnan ta faɗa kasa da murya.

“Zaki samu bayan zuwan wannan mutumin prison. Rufe shi ba zai maido miki da darajarki ba amma ko ba komai shari'a zata hau kansa. Zaki iya samun wannan kuma takun farko ne zuwa ga waraka.”

Ammar yana magana yana lallashin ƴar uwarsa amma har yanzu ya kasa yarda mahaifinsa ne ya yiwa Afnan fyaɗe. Yasan idan ya nuna rauninsa, Afnan zata ɗaga hankalinta fiye da yanda take a yanzu.”

Yana buƙatar zaunawa shi ɗaya yayi tunani amma kafin nan zai kira family meeting yanzu-yanzu domin sanar da kowa abinda ke faruwa.


Mommy da Khadija ne a ɗakin da aka kwantar da Kamal da ya kasa daina tambayar kansa me yasa Zahara bata zo ba.

Ya yanke shawarar share tunanin da ke ta yi masa yawo a ƙwalwa cewa budurwarsa ita ce silar wannan kai-komo din da yake asibiti.

Abinda yake ji game da Zahara ƙarfi gareshi sosai ta yanda baya fatan wani abu yazo ya raba shi da ita.

“Na ɗauko maka ko ayaba ka ci ne?” Mommy ta tambaye shi.

“A'a..bana jin yuwa." Ya bata amsa.

Khadija kallon inda mahaifiyar Kamal take tayi kafin ta juya tace
“Na kira Zahara amma bata ɗaga ba. Tace min zata dawo amma har yanzu shuru."

Kamal bai ce komai ba, yasan Khadija ba gaskiya ta faɗa ba amma gudun matsala yayi shuru.

“Kamal ina son muyi magana akan yarinyar nan." Cewar Mommy tana kallon ɗan nata ko yanayinsa zai sauya.

Cigaba tayi ganin Kamal bai ɓata rai ba.

“Ina ji a jikina ya kamata ka yi nesa da yarinyar nan...”

Kallon mahaifiyarsa Kamal yayi.

“Kar ki ce zaki rabani da ita ko ma me kike tunani a kanta.” Ya faɗa da sanyin murya.

Wannan maganar tashi ta sa ɗakin yayi shuru. Kallon Khadija Mommy tayi tareda daga kafada irin ai sai da na faɗa miki.

Lokacin da Khadija ta tarar da Mommy ta faɗa mata irin haɗarin da ke tattare da Zahara akan Kamal, Mommy tayi mata bayanin babu abinda zata iya yi. Kamal bai taɓa bari wani ya saka masa baki a cikin al'amuransa ba, kuma hakan tun yarinta yake.

Hajiya Karima ta damu lokacin da Khadija ta faɗa mata amma tasan babu abinda take iya sauyawa. Zata iya yiwa yarinyar da ake cewa Zahara magana, amma Kamal ba zai taɓa yin abinda zata sanya shi ba. Haka abun yake tun asali. Ta gargaɗi Khadija akan hakan amma sai da ta yiwa Kamal maganar.

“Ya kamata ka saurari mahaifiyarka.” Cewar Khadija cikin jin haushi.

“Babu ruwanki.” Cewar Kamal.

“Na gaji, ku barni na yi bacci." Ya sake faɗa.

Tashi Mommy tayi ta bar ɗakin.

“Gaskiya baka kyautawa abinda kake yiwa mahaifiyarka.” Cewar Khadija.

“Khadija... Nasan ke kika je kika faɗa mata wasu abubuwa game da Zahara. Wannan ne gargaɗina na ƙarshe da zan yi miki, a karo na gaba zan datse alakar da ke tsakaninmu. Ki shafawa Zahara lafiya. Ina son Zahara, dan haka ke ko wani ba zai canza hakan ba.”

“Ni zaka kora daga cikin rayuwarka akan wannan yarinyar?”

“Idan kina son ki cigaba da zama a matsayin friend dina, ki daina muzgunawa Zahara! Wannan ne na ƙarshe da zan faɗa miki hakan. Kuma wannan yarinyar da kike cewa ita zan aura dan haka ina son kiyi respecting ɗinta.” Ya faɗa babu alamar wasa yana kallonta cikin idanu.

“Kawai ina son..."

“Ni ina son ki fahimci wannan ne.” Ya katse ta.

Khadija taji kamar ta kama da wuta. Bata ce komai ba amma a cikin zuciyarta, tasan ba zata iya kallon mutanen nan biyu suyi aure ba. Amriya tayi mata alkawarin zata raba su kuma aiki ya fara kyau domin a yanzu Zahara bata iya shan inuwa daya da masoyinta Kamal.

“Kuma ai basu ga komai ba." Khadija ta faɗa a zuciyarta.

To be continued...
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels https://bit.ly/3Egdy1m

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 23

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚




A BANGAREN SARAT

Tasha aiki duk yinin ranar amma ganin sa a bakin kofar ta ya isa ya dauke mata duk wata gajiya da take ji. Da tayi shirin bacci, ko tsayawa diner bata yi ba tsabar baccin da take ji, saidai Ammar yanada baiwar tayar mata da kowanne sassa nata.

Bude masa kofa tayi tare da taya shi rage kayan jikin sa. kiss yayi mata da ya sanya ta yin murmushi Kafin ya wuce cikin dakin.

Bin bayan sa tayi da sauri.

“Jira wurin duk a hargitse yake, nayi shirin bacci ne. Zo ka zauna falo kafin na gyara cikin dakin dan ka samu sakewa.”

“Ba komai kar ki damu, ba bako bane ni.”

Hakan yasa ta dan ji sanyi da ya nuna bai damu ba amma ita kanta ba zata samu sakewa ba a yanda dakin yake a hargitse.

“Zaka ci wani abu?"

Ta tambaye shi. Mace ce ita da bata son yin girki, amma a kansa zata iya komai indai zai saka shi farin ciki. A gare ta, tasan shine zabinta duk da shi hankalin sa na wani gurin, bata san takamaimai wacece ita a wajen sa ba. Haka bata son yi masa wannan tambayar dan tsoron kar ya gudu ko ta rasa shi. Saidai tambayar taqi ta daina takura ta, ta kan cewa kanta ya kamata tayi rayuwa da abinda take da yanzu sannan ta bar gobe ta tsara kanta. Kuma tana ganin cigaba cikin alakar daga sex-friend zuwa sex-friend da kuma confident kuma tana fata nan kusa alakar ta fi haka. Ta zamo macen da tafi kowa farin ciki.

Gashi bata sani ba idan zata iya jurar yace mata alakar su ba zata wuce fiye da hakan ba.

Muryar sa ce ta dawo da ita daga duniyar tunani.

“Tunanin me kike?”

“Ah ba komai.”

“Kin tabbatar?” Ya tambaye ta.

“Eh kar ka damu. Maganar ma me muke yi ma?"

“Kin tambaye ni abinda nake son na ci ni kuwa nace miki bani jin yunwa.”

“Ah ban ji abinda ka fada ba."

“Ai na gani, akwai abinda ke damun ki ne? Me yasa naga hankalin ki na wani wurin daban?"

“Kawai na gaji ne, amma babu komai."

“Toh zo ki kwanta." Ya fada yana bude mata hannuwan sa yanda zata iya shiga. Hakan kuwa tayi babu musu.

Dariya yayi lokacin da tayi wani abu kamar mage yayin da taji dumin jikin sa da ya yi mata dadi.



Haka suka tsaya na tsayin wasu mintuna, har bacci ya fara daukan Sarat lokacin da muryar sa ta tashe ta.

“Ki shirya mu je Niamey, iya mu biyu kawai."

Cikin bacci taji maganar amma sai da taji kamar ta daka tsallen murna.

“Da gaske kake?" Ta fada tare da dago kanta tana kallon sa cikin ido.

“Eh sosai, ina son muje cen domin mu dan huta. Naga alamun gajiya a tattare da ke. Kuma nima ina son na dan sha iska da wannan abubuwan da suke faruwa da ni kwana biyun nan."

“Naji dadi sosai da wannan labari. Yanda baka zato.” Ta fada cike da nuna jin dadin ta a fili.

“Cool, toh ki shirya wannan weekend din."

Kwanaki na gaba, Sarat cikin farin ciki take sosai. Babu abinda yake iya bata mata rai. Gidan gyaren jiki taje, aka darje ta kamar wata amarya. Kusan suman farin ciki tayi lokacin da Ammar ya bata credit card din sa domin ta siyi duk abinda take so ai kuwa bata yi kasa a gwiwa ba. Ta siyo dogayen riguna, skirts, kayan bacci, takalma da sarkoki. Ta dinga jin ta tamkar wata princess.

Ranar juma'a suka hau jirgi cikin kankanin lokaci sai gasu babban birnin Niamey, suka sauka a wani kayataccen five star hotel. Hutawa suka yi har zuwa gobe da yamma da ya nemi da su fita zuwa restaurant. Dan haka Sarat ta cancara kwalliya kamar wata jarumar Hollywood. Bata tabbatar da hadewar ta ba sai da taga irin kallon da Ammar yake mata. Ba iya shi kadai ba, lokacin da suka zo restaurant, idanu suka yi ca a kanta hakan yasa ta kara jin ajinta ya karu.
Da fari komai na tafiya daidai, daya daga cikin ma'aikatan restaurant din yayi musu jagora zuwa table din da Ammar yayi reservation. Suna hira cikin nishadi kafin Sarat ta lura hankalin Ammar yana wani gu daban. Ya daina sauraron ta kuma bai daina kallon bayan ta ba. Dan ganin me ya daukar masa da hankali Sarat ta juya nan taga Salmah tsohuwar budurwar sa.

Salmah ce tare da wani saurayi kuma da alamu itama ta gansu. Kallon Sarat take ba tare da Sarat ta fahimci ma'anar kallon ba. Kafin ma Sarat ta kai ga gane meke faruwa, taji Ammar ya janyo ta tare da hade bakunan su na tsayin wasu mintuna. Irin kiss din da bai taba yi mata ba a baya.

Sarat ba sakarya bace domin tasan duk wannan abun da yayi dan ya ba tsohuwar budurwar sa haushi ne. Kuma ta tabbatar ba coincidence bane idan sun hadu duka nan.

Haushi ne ya kama Sarat amma tayi kamar ba komai. Ta qi barin duk wani emotion ya bayyana da Ammar zai gane ta harbo jirgin sa.

Ta gane hakan ne ya kawo shi Niamey lokacin da suka koma daki. Shuru yayi kuma yaki ya kalle ta duk da masifaffar rigar da saka. Ranar Sunday suka baro Niamey ba tare da sun yi komai ba, idan nace «Komai» ina nufin asalin komai. Ko fita ma basu yi ba, shi da yayi mata alkawarin dream weekend.

Taki ta yarda da hakan, amma cikin kanta hargitsi ne sosai, yanzu ta tabbatar Ammar yana tare da ita ne kawai dan rage lokaci, kafin ya dawo da tsohuwar budurwar sa.

Amma zata cigaba da biye masa a hakan, har lokacin da zata fahimtar da shi ba zata bari ya subuce mata ba.

Saidai cikin rashin sa'a, ranar lahadi da dare zuwa karfe goma, suna tsaka da action suka ji ana knocking kofa. Mamaki Sarat tayi domin babu wanda take tsumayin zuwan sa a wannan lokacin. Da sauri ta saka kayan ta, ta bar Ammar kwance tare da rufo kofar dakin sannan ta kauda duk wani abu da zai nuna akwai wani a gidan bayan ita.

Zuwa tayi ta bude kofar, nan tayi arba da mahaifiyar ta. Jiki ne ya shiga yi mata bari domin ba taba zaton mahaifiyar ta zata zo a daidai wannan lokacin ba. Sosai take cikin shocking ta yanda ta kasa furta ko kalma daya.

“Ni bani hanya in wuce, ko kuwa kara shanya ni zaki yi a nan?"

“Mami me kuma kike yi nan?”

Ture ta mahaifiyar tata tayi tare da kutsa kai cikin falon.

“Kamar ya me nake yi nan? Nazo ganin ki ne tunda ke ko ganin kiran wayar ki ma wahala yake."

“Amma kinsan aiki nake 24 hours. Ina cikin hutawa ne domin gobe sauko zan yi wajen aiki."

“Sai kuma me?" Cewar mahaifiyar ta. “Kora ta zaki yi ne saboda kawai a gajiye kike? Me yake damun ki ne? Ko kin canza uwa ne?"

“Wace irin tambaya ce wannan Mami? Ni ban ce ke ba mahaifiyata ba ce, kawai dai a gajiye nake."

“Koma dai meye sai na tsay...”

Wayar Ammar ce tayi ringing cikin daki da yasa kiris ran Sarat ya fita daga jikin ta.

“Meye wannan?” Mahaifiyarta ta tambaye ta.

“Oh..wayata ce. Na manta ban saka ta a silence ba." Sarat ta fada duk a rikice.

“Yaushe wayar ki ta fara irin wannan ringing? Sakarya kika dauke ni ko me?"

“Na canza ringtone ne, wannan yana burge

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment