Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da masu gaskiya. Ban yi komai ba ni, kare kaina kawai nayi.”

“Good.. ka fice min daga gida yanzu. Daga yanzu ban sanka ba." Cewar Mahaifiyar sa tareda barin falon.


“Good, daga yanzu ni maraya ne banda uwa.”

“Ya isa haka..” Cewar Kamal.

Mommy ta fice daga falon, Daddy ya rufa mata ba tareda ya sake kallon inda Ammar yake ba.

“Ka wuce gona da iri.” Cewar Kamal.

“Ina ruwana, su basa ganin adadin yanda nake cutuwa? Eh nine mugun cikin labarin.”

“Abinda ka aikata yanzu, ba komai kayi ba illa kara jagule lamarin. Kuma ina baka shawara da ka bata hakuri gobe ko jibi idan komai ya laba.”

“Ba wani hakuri da zan bayar... I just want to stay alone.”



SARAT

Karfe 12 na dare
A gajiye take sakamakon aiki da ta sha gaba daya yinin yau. Tana shirye-shiryen bacci taji wayarta na ringing. Tayi tunanin ko yayanta ne dake kasashen waje, domin shi kadai ke kiranta irin wannan lokacin. Baccin da take ji ne ya kaurace lokacin da tayi arba da sunan oganta a jikin wayar. Da saurinta ta daga kiran.

“Hello?”

“Bacci kike?” Ya tambaye ta.

“A'a, a'a kwance dai nake, kana lafiya?”

“Zo ki bude min kofa..”

Rudewa Sarat tayi, jin Mr. Ammar na bakin kofarta. Zuwa tayi bakin kofar, ta leka ta huda ta tabbatar da shine a tsaye. Har yanzu yana sanye da suit dinsa tun na safe, jacket din a kafadarsa, rabin mabbalan rigarshi kuwa a bude, ya bar kirjinsa waje.

Bata gama kare masa kallo ba, ya rungume ta. Bata sani ba ko farin ciki zata yi ba ko damuwar yanayin da ta ganshi ciki. Sai da suka dau lokaci a haka kafin ya sake ta su shiga ciki. Zaune yayi cikin kitchen yana kallonta tana hada masa coffee. Ganin sa take kamar wanda yayi dambe, bata yi gangancin tambayar sa meke faruwa ba.

“Sorry na zuwa da nayi a wannan lokacin.”

“Kar ka damu... da yake ba komai nake yi ba.” Ta bashi amsa.

Coffee yasha ba tareda ya sake cewa wani abu ba, ita kuwa Sarat kallonsa take yanda yake kai kofin coffee a nutse zuwa bakin sa. Ta kasa dauke idanunta daga kanshi, domin ko a wannan yanayin kyanshi take gani. Kasa tsayar da kanta tayi, taje inda yake tareda rabashi da jacket dinsa. Kissing dinsa tayi shima ya mayar mata da martani. Da son zuwa nesa, a hankali ta cire masa riga, ta shiga sumbatar ko'ina na jikinsa, shi kuwa ya tsayar da ita ta hanyar ture ta.

“Ba wannan bane..ya kawo..ni.. Ina son muyi magana ne.”

Kallon sa tayi ta kara tabbatar da yana cikin damuwa kuma ba kadan ba. Hannun sa ta kama ta jashi zuwa dakinta. Tagogi ta bude sannan ta cire masa takalmi. Kwance tayi bisa gado tareda gayyatarsa shima.

“Zo ka huta, komai zai dawo daidai.”

Sai da ya kalleta na wasu yan dakiku sannan ya gyada mata kai. Kwantawa yayi gefenta tareda dora kansa bisa kirjinta. Rufe su tayi da zani, a hankali ta fara shafa shi dan ya samu nutsuwa. Tana tunanin haka ne yake bukata a halin yanzu.. domin bayan wasu yan mintuna taji numfashinsa ya karu alamar yayi bacci.
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels https://bit.ly/3Egdy1m

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 20

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚


Kwanaki na shudewa babu abinda ya sauya gidan Alhaji Yusuf. Kamar yanda yace, Ammar ya bar gidan iyayen sa ya koma sabon gidan shi da babu nisa da kamfani. Yana ganin abinda ya faru ya gyarashi na wani bangaren, domin ya bashi damar yin tunani akan matsalar shi, ya kan zauna yayi nadamar laifin da ya aikatawa mahaifiyar sa. Amma idan ya tuna yanda mahaifiyar sa tayi masa, sai yaga ba laifin sa bane.

A bangaren Hajiya Karima kuwa, ta kasa gasgata abinda danta yayi mata. Tayi tunanin idan tace zata sallamashi zai ji tsoro yayi abinda take so, saidai tayi kuskure. Mamakinta kasa boyuwa yake, a takaice dai cikin zuciyarta tsoron rasa danta take, wanda shi kadai ne yake sauraronta kuma yake mata biyayya ba tareda wata matsala ba.

Tana jin kamar a dawo baya, ta hana bakinta fadar wadannan kalaman kuma ta shawo kan matsalar ta wata hanyar. Tayi ta kokowa da son kiran dan nata na tsawon makonni amma ji da kai ya hanata kuma zuciyarta na ce mata ai zai dawo gare ta. Jiran da take yi masa kenan a kullum.

Tsawon watanni kenan tana jira amma bata ga inuwar danta ba, babu kuma labarin shi. Hakan ba karamin tayar mata da hankali yayi ba, har ta fara fidda rai. Gashi kawarta na fushi da ita. Babu mai goya mata baya, har mijinta ya daina shiga al'amarin, alhali shine na farko da ya kamata ace ya saka lamarin.

Saidai Hajiya Karima bata san ba rabuwa da danta bane kadai tashin hankalin da zata fuskanta. A safiyar yau, kamar kowacce safiya tsayin wasu watanni, Afnan ta daina zuwa school. Hajiya Karima tayi ta mata tambayoyin dalilin barin zuwanta school, ita da ke da kokari sosai. Amsar da Afnan take bata na damunta : Kawai bana son zuwa ne.

Duk da fadan da Hajiya Karima ke mata, Afnan taki tayi mata bayanin me yake damunta. Hajiya Karima ta fara tsorata da canjin da 'yarta take samu. Ta daina cin abinci sosai, amma sai kiba take yi, batada aiki sai yawan bacci da cin gyada. Halin da har ya janyo hankalin Rakiya mai aikin su. Afnan ta kan yawan ce mata ta hada mata tea da mint domin duk safe zata ce bata jin dadi. Hajiya Karima ta lura da duk yanayin 'yar tata amma taki ta yarda da abinda take tunani.

Saidai yau da safen nan, taga Afnan ta sauko daga sama ta nufo inda take, lokaci guda kuma ta nufi toilet a guje rike da bakinta. Ganin yanayin 'yar tata, Hajiya Karima tabi bayanta ita ma. Tana saka kafarta cikin dakin, karnin amai ya bade mata hanci. Nan taga Afnan durkushe gefen masai tana amaye duk abinda taci jiya.

Yanzu ne ta gasgata abinda take tunani, komai gashi zahiri a idonta, amma taki yarda. 'Yarta juna biyu gareta. Duk da haka sai da ta yiwa Afnan tambayar kamar idan taji gaskiyar ga bakin 'yar tata wani abu zai canza.

“Ciki gare ki?”
Zabura Afnan tayi tareda faduwa kasa, muryar Mommy ta tsorata ta. Dama kwana biyun nan tsoron yin amai take gabanta, yau ma bata ankare bane har ta rutsa ta. Tasan ko ba dade ko ba jima Mommy zata gano gaskiya kuma abin mamaki murnar hakan take. Murna take saboda daga yau babu wata barazana da zata sake fuskanta. Fashewa da kuka tayi yayin da ita kuma Hajiya Karima ke addu'ar Allah yasa mafarki take.

“Mom..” Afnan ta fada cikin kuka tana mai tuna irin ciwon da taji ranar da ta gane tana da ciki. Saidai wannan ciwon ba komai bane akan ciwon sanin uban cikin da ba kowa bane face mjin wacce ta rike ta.

“Mom? Har kina da karfin gwiwar kirana Mommy? Idan da kina daukata a matsayin mahaifiyar ki da ba zaki janyo min wannan abun kunyar ba.”

Afnan kuka take kamar ranta zai fita.

“Please Mom..”

“Please what?” So kike in taya ki murna ko me? Me zan fadawa mahaifiyar ki wacce ta bani amanar ki? Me zan fadawa mutanen da zasu ce ban baki tarbiyar ba domin ba uwa ta gari bace ni? Ta yaya kike son na kalli idon duniya?”

Hawaye ne suka zubowa Hajiya Karima, ta rasa me ke mata dadi. Da abinda ya faru a baya, tayi tunanin koda kowa zai juya mata baya, Afnan ba zata taba bata kunya ba. Saidai ashe irin haka na tafe.

“Goge aman, maza ki same ni a falo!” Mommy ta daka mata tsawa.

Cikin kuka Afnan ta gyada mata kai sannan ta tashi dan cika umarnin mahaifiyar ta. Anyi wannan amma mai wahalar yana tafe. Me zata yi yanzu? Me zata fada? Wannan sune tambayoyin dake yiwa Afnan yawo cikin kai. Tsawon makonni kenan take shirya amsoshin da zata ba uwar rikonta. Ta shirya cewa wani saurayi gareta shedan ya rude su suka aikata abinda bai dace ba. Afnan tana ganin hakan zai zo da sauki kuma zai kareta daga sharrin wanda ake dauka a matsayin mahaifin ta. Saidai yau da ranar tazo, taji batada kwarin gwiwar yiwa Mommy karya domin tasan zata gane karya take mata. Ba yau take zaune a hannunta ba, dan haka ta santa ciki da banta.

Cikin wasu yan dakiku Afnan tayi wani tunani cewa uwar rikonta ta gane gaskiya kuma ta yanke zata yi shari'a da mijinta dan ta kwatowa 'yar 'yar uwarta hakkin ta, a cikin tunaninta taga Hajiya Karima na kareta duk da bakin cikin gano cin amanar da mijinta yayi mata.

Mai yiyuwa taso kanta da tayi irin wannan tunanin, amma Afnan tace itama ta cancanci farin ciki fiye da sauran ahalin gidan. Bari dai kar tasa rai da yawa, ba zata taba aikata makamancin haka ba. Ba zata taba tona asirin uban rikonta ba domin idan tayi haka zata wargaza farin cikin ahalin ne fiye da yanzu abun kunyar da ta janyo musu.

Addu'a tayi ta roki Allah yasa komai yaje daidai kan karyar da zata yi akan wanda yayi mata ciki. Tana tunanin wannan karyar da zata yi zata sa uban rikonta ya dena hayke mata.

Tana cikin wannan tunanin, Afnan ta goge aman da tayi, bayan ta gama sai da dan tsaya cikin dakinta domin tattara kuzarinta hannu biyu kafin taje. Tafiya tsakanin dakinta da falo ba karamin tsayi yayi mata ba amma duk da haka sai da ta karasa falon. Ta tarar da Mommy zaune bisa kujerarta, ta buga tagumi daga gani kasan cikin tashin hankali take.

Afnan a hankali ta karasa falon tareda zaunawa kasa nesa da Mommy. Shuru Mommy tayi, shurun da har ya fara bawa Afnan tsoro.

“Tun yaushe kika san kina da ciki?” Mommy ta tambayi Afnan ba tareda ta kalle ta ba.

“Sati uku da suka wuce..” Afnan ta fada cen kasan makoshi.

“Kuma bakida niyyar fada min ko? Tabbas me yasa ma hakan zai bani mamaki? Waye uban cikin, ina son ganin shi yau dinnan!”

“Ya koma kasar su.. a Korea yake.”

“Ko ma a Italy yake, ko a sama ko a cikin ruwa ba abinda ya dame ni, ina son ganin shi cikin kankanin lokaci."

Afnan duk ta shiryawa irin wannan tambayoyin na Mommy.

“Soja ne kuma yana cikin mission ne yanzu, ba za'a iya samun shi ba sai shekara mai zuwa.”

“Dan asalin wacce kasa ne?” Mommy ta tambaye ta.

“Mahaifiyar shi yar Nijar ce, mahaifin shi ne dan Korea.”

“Shine daga ganin shi kika fada mishi ba tareda wata kariya ba, ko tunanin me zai je ya dawo ko? Kina tunanin zaki haife wannan cikin har ki rene shi? Kina tunanin zaki iya kula da abinda zaki haifa alhali ke daliba ce? Da wani kudin kike tunanin kula da shi? Ba dai kina tunani ni zan iya rikon shege, na sai mashi sutura, takalmi da sanya shi a makaranta, na yi masa magani idan baida lafiya, na yi masa duk wani abu da yake so. Tunda kina ganin kin yi girman da zaki je kiyi abun manya, yanzu ai sai ki ji da abinda kika jangwamo. Mahaifin ku ba karamin Allah wadai zai yi miki ba.”

Tayi alkawarin yin karya domin kare mutuncin gidan, amma anya zata iya jure daidai da minti daya a dinga suffanta ta da irin wannan kalaman, alhali ba ita bace mai laifi. Kare mutuncin gidan wani abu ne daban haka tunkarar fushin mahaifiyarta ma wani abun ne daban. Zuciyar ta ba zata juri hakan ba.

Afnan babu abinda ta iya yi face sake fashewa da wani sabon kuka.

“Hajiya ina son fada miki wata magana..”

Rakiya ce mai aikin su ta shigo falon. Tunda take gidan bata taba katse magana mai muhimmanci ba irin wannan, shi yasa Hajiya Karima tayi mamaki domin tasan Rakiya tasan wannan maganar mai muhimmanci ce.

“Rakiya baki ga ina cikin magana da wannan yarinyar bane?”

“Nima maganar ce nake son yi miki.. Nasan ba hurumi na bane amma nasan idan ban fadi abinda na sani ba, ba zan taba yafewa kaina ba.”

Wani kallo Afnan tabi Rakiya da shi. Abinda Rakiya zata fada tasan zata iya rasa aikinta amma dole ta fada ko dan ta samu sukuni da zuciyar ta.

Afnan tambayar kanta take, me Rakiya zata fada da yafi wannan muhimmanci.

“Ok, ina sauraron ki. Zo ki zauna.” Cewar Mommy.

Rakiya bata zauna ba, ta fara magana
“Na kasa hana kaina daga jin maganar da kuke yi, Hajiya kar kice na miki rashin kunya amma kinyi kuskure na ganin laifin Afnan...”

Afnan ba zata iya barin Rakiya ta fadi abinda take son fada ba.

“RAKIYA WANNAN BA ABINDA YA SHAFE KI BANE!”

“Fyade aka mata.” Rakiya ta fada.

Da sauri Hajiya Karima ta mike tsaye.

“Me kika ce?”

“A nan gidan hakan ke faruwa, tsawon shekaru.”

“RAKIYA IDAN KIKA SAKE FADAR WATA KALMA .." Cewar Afnan cikin tashin hankali.

“RUFEWA MUTANE BAKI.” Hajiya Karima ta dakawa Afnan tsawa.

Wannan ne karon farko da Hajiya Karima ta daga mata murya. Saidai Afnan ko a jikinta, abinda take so shine ta hana Rakiya magana.

“Ke kuma ina jinki, me kike son cewa ne?" Cewar Hajiya Karima ga Rakiya.

“Da farko, na dauka su biyun suna cin amanar ki ne amma daga karshe na gane yana tursasa ta ne yin abinda bata so. Naji tsoron fadar gaskiya kuma itama naga alamun tana tsoron tona masa asiri amma yanzu tunda hakan ta kasance ba zan iya rike bakina ba.”

“Wanene? Ammar? In dai shi ne ban yi mamaki ba !"

“Rakiya.. ki yiwa girman Allah.. kar ki yi haka. Kada ki bata mana rayuwa.” Cewar Afnan amma Rakiya bata da alamun yin shuru.

“Alhaji ne mijin ki.”

Dariya Hajiya Karima ta fara.. sosai take dariya ta yanda ta kasa tsayar da kanta.

“Kenan, bayan kin je kin gamo karuwancin ki waje, shine zaki zo ki sharracin mijina akan fyade ko? Kuma babban abun shine har da saka Rakiya cikin makircin ki. Lallai yarinya, bansan irin wannan sakayyar zan samu ga rikon ki ba. Bayan duk abinda nayi miki, bayan duk abinda shi yayi miki ki samu karfin halin zuwa ki ce min mijina yayi miki fyade."

“Mommy ni ban ce miki haka ba, kuma bansan dalilin da yasa Rakiya tace haka ba amma wallahi karya take."

“Kina tunanin Rakiya zata zo tayi wannan karyar ne ba tareda kin ce tayi ba?"

“Please Mommy ki yarda da ni, ban ce Rakiya tayi wani abu ba. Laifi na ne, ni naje waje nayi iskanci na kuma ga sakamakon da na samu. Ki yafe mini Mommy.”

Afnan sai rusar kuka take durkushe rike da kafar Mommy. Bata yi tunanin lamarin zai kwabe haka ba, a tsorace take sosai. Abinda take gudu shi yake shirin faruwa.

“Ki fice min daga gida Afnan, daga yau ni ba mahaifiyar ki bace. INA SON DUKA KU BIYUN KU BAR MIN GIDA."

“Ke Afnan, yau zaki koma gun asalin mahaifiyar ki, wata kila ita zata iya renon shegen da kike dauke dashi. Bayan duk abinda nayi miki : na kula da ke, na soki kamar yar da na haifa a cikina.. ke kuma ki rasa da me zaki saka min, sai ki shiryo wannan bakin sharrin dan ki raba min ahali. Wane buri kike son cimma? Me kike so? A baki kudi dan kiyi shuru? Na kasa fahimta..."

“Kar ki guje ni Mommy.. wallahi duk wannan ba gaskiya bane."

Kafa Hajiya Karima tasa ta ingije Afnan ta fadi kasa kafin ta bar falon tareda bangaje Rakiya. Da gudu Rakiya ta nufi Afnan da niyyar taimaka mata amma Afnan ta hana ta taba ta.

“Na sani ba wanda zai yarda da ni, shi yasa na bar sirrin a zuciya ta domin kare mutuncin wannan gidan amma gashi ke kin zo kin wargaza komai. Kin bata min rayuwa. Rakiya, da kin kyale ni naji da lamarin da kaina, Mommy zata ji haushi na ne amma ba zata taba korata ba. Amma yanzu.. kowa zai tsane ni, yan uwana.. kin raba ni da sauran farincikin da ya rage min.”

“Yanzu ne zaki samu yancin ki Afnan, nasan ba hurumi na bane kuma nayi katsalandan amma bana nadamar yin hakan. Ba wanda ya cancanci irin rayuwar da kika yi, ba zan iya bari su bata miki suna akan laifin da ba kece sila ba. Ki bata lokaci zata fahimta ko ba dade ko ba jima, idan ta cigaba da rufe ido akan laifin mijinta to bata cancanci zama mahaifiyar ki bane."

“BA KECE ZAKI FADA MIN WACCE TA CANCANCI ZAMA MAHAIFIYA TA BA. BA KECE ZAKI FADA MIN ABINDA YAKE MAI KYAU DA MARAR KYAU BA GARE NI. NAGODE DA RUGUJE MIN RAYUWA DA KIKA YI RAKIYA. KI RABU DA NI YANZU.”

Ba tareda ta sake jin kalma daya ba ta Rakiya, Afnan ta tashi tayi shigewarta daki. Rakiya tayi kokarin zuwa ta ga Hajiya Karima dan ta kara yi mata bayani amma bata ganta ba. Dakin Afnan ta nufa domin sake yi mata magana da kuma kokarin kara shawo kanta akan ta tsaya ta kwato yancin ta.

Koda ta karaso kofar dakin Afnan, tayi ta knocking amma Afnan bata bude ba. Hankalin ta ne ya tashi, ta shiga kwala kiran sunan Afnan amma bata amsa ba. Da iya karfin ta ta shiga dukan kofar har daga karshe ta bude. Saidai abinda ta gani ya sanya ta mutuwar tsaye. Afnan ta gani kwance hannun ta cikin jini, ta yanka hannun ta da reza. Kuma bata motsi.


(....)


A wannan rana, Khadija ta gaji da shariyar da Kamal yake mata. Tana kiran shi, tana tura masa da texte amma baya amsa mata. Dan haka ta yanke shawarar zuwa ta ganshi. Wajen karfe hudu taje gidan sa, tayi ta knocking amma bai bude ba. Tayi alkawarin ba zata bar wurin ba in har bata ga Kamal ba. Bayan wasu mintuna, taji sawun tafiya. Kamal ne ya bude kofa nan ta fahimci dalilin da yasa bai daukar wayarta.

Da alamu baida lafiya sosai domin tsayuwa ma bai iya yi da kyau, labbansa sun yi fari kal kuma idanun sa kamar zasu fito daga gurbin su. Hankalin Khadija ne ya tashi...

“Subhanallahi ! Me yake damun ka?” Ta tambaye shi tana shigowa da sauri cikin gidan. Rufe kofar tayi sannan ta taimaka masa dan tsayuwa duk da girma da nauyin shi. Bai ce komai ba ya barta ta taimaka mashi. Daki Khadija ta kaishi ta taimaka masa ya kwanta. Jan bargo Kamal yayi, ya rufe jikin sa.

“Tun yaushe kake rashin lafiya? Me yasa baka fada min ba?"

Bata jira jin amsar shi ba, ta ajiye jakar ta ta shiga kitchen neman basin na ruwa. Daya daga cikin towels din sa ta dauka ta jika, ta dora masa a kai domin rage zafin zazzabin da ke gare shi.

Ba a dau lokaci ba, Kamal yayi bacci. Kusa da shi ta tsaya har lokacin da ya farka. Da alamu yaji dan sauki.

“Kana jin yunwa ne?” Ta tambaye shi.

Gyada mata kai yayi.

Porridge ta hada masa sannan ta taimaka masa ya ci. Koda taga da alamun yaji sauki, ta fara magana
“Me yasa baka kira ni ba?”

“Ba wani abu bane babba.” Ya bata amsa. “Kawai yar gajiya ce.”

“Eh amma da ka kira ni lokacin da ka fara jin ciwo, da nazo kuma na raka ka asibiti.”

“Gaki nan ai.. kuma yanzun ma taimako na kike. Gashi har naji sauki.”

“Eh amma me zai faru idan da ban zo ba? Nasan da ka kira ni idan da bamu samu matsala ba a baya, nazo ne na fada maka na amince da abinda ka yanke. Ina son ka kasance cikin farin ciki kai da Zahara, nasan matsayi na. Nasan mu biyu babu komai tsakanin mu bayan abota.. dan haka ina son komai ya dawo kamar baya. Ka min alkawari.."

“Nayi miki alkawari." Kamal ya bata amsa.

“Yauwa, yanzu ina son ka shirya zamu je asibiti."

“Mene? Na fada miki na samu sauki. Bana son zuwa asibitin nan."

“Ba ruwa na.” Cewar Khadija. “Duk da haka sai mun je domin kara tabbatarwa."

Yayin da Khadija ke kokarin shawo kan Kamal domin su je asibiti, a bangaren Zahara na tunanin me yasa Kamal ya daina kula ta. Tayi kewar shi sosai ta yanda ko aiki ta kasa yi da kyau. Dan haka ta yanke shawarar zuwa ganin shi idan ta tashi daga aiki domin ko a waya bata samun shi. Ba halin sa bane bacewa na tsawon makonni babu labari. Har saida ta fara tunanin idan ba yayi niyyar raina mata hankali bane. Kuma ya ki kiranta ne saboda ya gaji da ita. Saidai da sauri ta kawar da wannan tunanin daga zuciyar ta, domin kullum Kamal cikin tabbatar mata yake. Bai dace ta dinga bari irin wannan tunanin na zo mata ba.

Tana sauka daga aiki, ta tsayar da dan sahu domin zuwa ganin Kamal. Tana zuwa kofar gidan, tayi knocking. Murmushi take har kunne duk da damuwar da take ciki, da kaguwar son ganin sa.

Saidai a maimakon Kamal wata matashiyar mata ce ta bude mata.. kyakyawar mata. Zahara tambayar kanta take wacece wannan kuma me take yi nan.

“Ah Zahara, kina lafiya?”

Ya aka yi ta sanni? Cewar Zahara a zuciyar ta.

“Lafiya lau.” Duk da haka ta amsa mata cikin ladabi.

“Kamal kike nema? Yana ciki, zaki iya shigowa. Daman shirin tafiya nake, shi ne ya kira ni bai dan jin dadi jikin sa ne. Ayya na cika ki da surutu, ni sunana Khadija, ni best friend din sa ce.”

Zahara ji tayi kishi ya turnuke ta, tana cen tana ta damuwa, bai yi komai ba dan ganin yanda take, bai ko kirata ba dan ta taimaka masa amma yana da karfin jiki da lokacin da zai dauki waya ya kira wannan yarinyar.

Dogon numfashi ta ja kafin ta tuna wautar ta ta tsayawa kishi alhali Kamal baida lafiya.

“Ya jikin nasa?” Zahara ta tambaye ta.

“Da sauki, kar ki damu na kula da shi da kyau har ya samu sauki. Ba zaki shigo ba?”

Zahara nunawa tayi bata lura da murmushin munafuncin da matar ke mata ba. Bata ma san ina tasan sunan ta ba.

“Nasan Kamal yayi mata zance na, wata kila tare suke zaunawa suna min dariya." Wani bangare dake cunkushe da kishi na zuciyar ta ne ke rada mata hakan.

Iya kokari take ganin ta boye damuwar ta, amma ga banza domin duk wanda ya kalle ta zai gane tsantsar kishi shimfide a fuskar ta.

“Ba zaki shigo ba?” Khadija ta sake maimaitawa.

“A'a." Cewar Zahara. “Gida zan wuce.”

“Ok, zan fada masa kin biyo. Na tabbatar zai kira.."

Ba tareda ta jira jin sauran abinda Khadija zata fada ba, Zahara ta juya tayi tafiyar ta.


[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels https://bit.ly/3Egdy1m

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 21

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚


Komawa Khadija tayi ciki tana murmushi tare da tambayar Kamal ko zata kara tsayawa domin taya shi hira.

“Waye yazo?” Kamal ya tambaye ta.

“Zahara ce.”

Da mamaki Kamal ya kalle ta jin Zahara tazo har gida neman shi. Gashi daman ya jima rabon shi da ita sakamakon halin da gidan su yake ciki ga kuma zanen da wani kamfani na kasar Malaysia suka bashi da zai gama shi da gaggawa. Ga kuma rashin lafiyar da yake fama da ita kwana biyu. Yayi kewar ta sosai, yana da tunanin da ya samu sauki yaje gidan su. Sai gashi cikin sa'a tazo, ba karamin dadi yaji ba.

“Tana ina? Ce mata ta shigo."

“A'a tayi tafiyar ta."

“Kamar ya ta tafi?”

“Na fada mata kana nan kuma tana iya shigowa amma tace min wucewa zata yi. Nasan ko sauri take.”

“A'a, ba gaskiya bane abinda kike fada. Idan da tana sauri ne ba zata zo nan ba. Kuma koda tazo nan ba zata ki shigowa ba. Me kika ce mata?”

“A'a komai kawai nace mata baka da lafiya ne kuma ni ke kula da kai.”

“Me kake yi haka? Me yasa ka tashi?” Ta tambaye shi tana mai nufo shi da sauri shi kuwa yana kokarin sauka daga bisa gadon da kyar.

“Tambayar ka nake, ina zaka je?”

“Zan je na ganta ne, na tabbatar tayi wani tunani ne a kanmu.”.

“Kamar ya tayi wani tunani, bata yarda da kai bane ko me? Baka da karfin jikin da zaka fita yanzu, ka kira ta wani lokacin sai ka yi mata bayanin babu wani abu tsakanin mu. Ni zan iya zuwa na ganta saboda kai.”

“No, kar ki damu nafi son naje da kaina.”

Cikin wardrobe din sa ya bincika ya dauko bakin jeans da t-shirt ita ma baka. Duk da yana jin babu kwari jikin sa amma dole sai yaje

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment