Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mama.”
Tayi kokarin kare kanta amma dariya hakan yaba Mama.

“Ni dai nasan akwai wani abu tsakanin ku. Me ya fada miki kenan?”

“Please.. Mama ki daina. Bana son yin maganar da ke...” Zahara ta fada tana boye kanta bayan pillow.

“Toh ai baki da kawayen da zaki fadawa. Ni gani nan, zan iya baki shawara. Oya, yarinya ina sauraron ki."

Mama tana da gaskiya Zahara bata da wata kawa da zata iya hira da ita. A irin wannan yanayin ne take nadamar yanda take amma bata shirya irin wannan hirar da Mama ba.

“Zan fada miki komai Mama, i promise.”

“Shikenan, ina jira. Zan je in karasa girkin.”

Bayan Mama ta fita, Zahara ta koma ta kwanta bisa gado, ta shiga juye-juye kamar hakan zai taimaka mata wajen gyara hargitsin dake cikin kanta. A confusing take sosai. Yace yana son relation ta gaske, amma ita bata taba yin saurayi ba, tana da raunin experience a wannan fannin, ta yaya zata fara maganar aure? Shida bama ya cikin tsarin ta, aure da yake karshen list na objective din ta.

Kamal yana birge ta, wannan ko tantama bata da amma bata tunanin zata iya kasancewa matar da yake buri...


A BANGAREN KHADIJA

A yau ta karbi albashin ta, ta shirya zuwa gidan Kamal domin yi masa wata kyauta. Odan dinner tayi daga “Eden restaurant” inda ake soya lafiyayyu kaji. Tana sa ran da wannan kazar, yau ta samu kanshi domin tana tunanin kamar gudun ta yake. Ta sani aikin da yake dole ya kasance busy amma a da yana samun damar kiranta dan jin ya take.

Tayi kewar shi sosai, yana wahala rana ta wuce bata yi tunanin sa ba. Idan ta kira shi baya dagawa sai bayan wasu awanni yake sake kiranta, kuma shima dan yace mata yana wani aiki ne ya sake kiranta. Kiran da ba zai yi ba kenan. Bata san dalili ba, amma a da baya mata irin wannan halin. Dole akwai abinda ke faruwa wanda bata sani ba. Dan haka ta yanke shawarar yi masa bazata.

Salmah har yanzu tana gidan ta, bata jin dadin barin ta ita kadai a gida bare ma yanzu da take cikin wannan yanayin, amma kafin ta fito ta tabbatar mata da babu abinda ke damun ta, ita ma ta taimaka mata wajen zaben kayan da zata saka.

“Bakin abu na yi maki kyau.” Cewar Salmah tana mai ja mata zip din riga.

“Thanks my dear. Rigar tana da tsada, tayi min ne ba yanda na iya dole na siya.” Cewar Khadija.

“Zaki yi kwalliya ne?” Salmah ta tambaye ta.

“Eh amma ba da yawa ba, babu lokaci gaba na. Gashi odan da nayi yana hanya. Me zaki yi bayan tafiya ta?”

Sai da Salmah taja dogon numfashi kafin ta bata amsa.
“Da ina tunanin fita, amma ban sani ba.”

“Kizo muje tare gidan Kamal din. Hakan zai dan debe miki kewa.”

“Bana bukatar ganin ko daya daga cikin dangin Ammar kuma bana so na takura ku.”

“Ba fa wajen soyayya zan je ba.”

“Eh amma, zaki iya amfani da wannan damar ki fada masa abinda kike ji game da shi.”

“Bani da wannan kuzarin, yana dauka ta a matsayin best friend din sa ce.”

“Kece kike daukar kanki matsayin best friend. Idan da kin fada masa tun farko da tuni kuna ta shan soyayyar ku.”

“Idan yana sona, da tuni ya fada mini.”

“Ai kin fi kowa sanin shi, kinsan yanda yake da dan shan kai.”

“Banda lokacin da yasan yana san abu.” Khadija ta bata amsa.

“Eh, ai baida budurwa ko kuwa? Mai yiyuwa yana jira ki fara fada ne.”

“Baida budurwa, amma shi ba irin mai jiran nan bane, idan da gaske yana son na zama budurwa sa, da tuni ya sanar da ni. Daina bani fake hope Salmah.”

“Ba zaki samu duk abinda baki gwada neman shi ba, nidai na fada miki.”

“Kafin ki tura ni gun Kamal, ki fara gyara tsakanin ki da Ammar.”

“Daina yimin wannan zancen. Kema kin sani ta kare tsakanin ni da shi. Ba zan so na dawo baya ba. Ke kuwa kar ki yarda ki rasa damar ki.”

_“Tana da gaskiya, babban kuskure ne rasa namiji irin Kamal.”_

Juyawa Khadija tayi da sauri ganin wanda ya rada mata wannan maganar a kunne. Amma babu kowa daga ita sai Salmah.

“Kece kika fadi haka?” Ta tambayi Salmah.

“Na fadi me?”

“Kika ce « babban kuskure ne rasa namiji irin Kamal. »”

“A'a ban fadi haka ba, sai idan mafarki kike dai. Mai yiyuwa kin fadi hakan ne a zuciyar ki.”

A'a.. ita bata fadi hakan ba a zuciyar ta, da kyau taji wata muryar da ta gayi hakan. Ko kuma Salmah tana da gaskiya, mafarkin tsaye ne take.

Daidai lokacin da ta gama kwalliya aka danna kararrawar kofa. Turare ta fesa sannan ta dauki karamar jakarta.

Kazar da tayi oda ce, karba tayi ta biya kudin. Sannan ta nufi bakin hanya, tayi saurin samun dan sahu, ta fada masa inda zai kaita. Ba bata lokaci ya ajiye ta bakin kofar gidan Kamal. Konkwasa kofar tayi, wutar gidan a kunne take hakan ya tabbatar mata da yana nan.

Sautin tafiya taji yana tunkaro kofar. Kamal ne ya bude mata.

“Khadija..” Ya fada da mamaki.

“Ni da kaina.” Ta fada tana murmushi.

“Me kike a nan, daidai wannan lokacin?” Ya tambaye ta.

“Kamar ya me nake yi? Nayi kewar ka ne. Ko bani da 'yancin kawo maka ziyara ne?” Ta tambaye shi.

“A'a, amma ban yi tsamanin ganin ki bane. Ok, shigo.” Ya fada tare da kaucewa dan ta shiga, babu bata lokaci ta shige.

Tasan gidan sosai, dan haka kai tsaye ta wuce falo tayi dare-dare bisa kujera. Komai na falon a tsare yake, kamar yanda ta saba tarar da shi, TV a kunne amma tana tunani yana cikin yin zane ne.

“Na takura ka ko?” Ta tambaye shi lokacin da ya dawo cikin falon, yana sanye da T-shirt da ta fito da kirar shi.

“No, kar ki damu. Ina cikin yin zane ne.”

“Nasan ka tsani a takura maka lokacin da kake zane amma ba zan iya kara kwana daya ba tare da na ganka ba, nayi kewar ka sosai. Ban sani ba ko nice na sa a kaina, amma naga kamar da gaske gudu na kake.”

Da farko dan daure fuska yayi, amma bayan yan sakanni ya saki fuskar. Khadija ta dauka ko wani kwakwaran bayani zai yi mata amma sai yayi mata murmushi kawai kafin ya tambaye me ta kawo. Yayi hakan dan ya janye hirar.

“Soyayyar kaza ta Eden restaurant, nasan kana sonta.”

“Cool, daman ban kai ga cin abinci ba.” Ya fada. “Je ki wanke hannu, bari na dauko plates.”

“Ok, bari na fara ajiye ledar nan.”

Tashi yayi ya nufi kitchen. Itama ta mike ta nufi hanyar bathroom dan ta wanke hannuwan ta. Taje wucewa ta corridor, ta hangi dakin da yake yin zanukan shi a bude. An dau lokaci rabon da ta ga zanukan shi. Shiga tayi ta tarar da ya lullube zanen da yake cikin zanawa, a hankali ta kwaye dan ganin me ya zana domin itama Allah yayi mata jarabar son zane.

Sai da ta dau lokacin kafin ta gane fuskar wacce Kamal ke zanawa. Daidai lokacin Kamal ya shigo dakin da sauri ya koma ya lullube zanen. Ita kuwa Khadija kokarin fahimtar dalilin da yasa Kamal ke zana yarinyar nan, ta yaya suka san juna kume meye alakar shi da ita. Ita da shi sun san juna tsawon shekaru amma bai taba zana ta ba.

Khadija a ranta tace, bayan ruguza soyayyar Ammar da Salmah da tayi, har ta iya samun kuzarin tunkaro Kamal? Kamal din ta?

_“Ya ishe ta haka abinda tayi, ki hana ta kwace abinda yake mallakin ki.”_

Ta sake jin muryar da tayi mata rada dazu, ta fada.
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels https://bit.ly/3Egdy1m

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 17

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚


ZAHARA
Koda ta koma gida, wanka ta shiga tati. Biki yayi biki an kuma watse lafiya. An kai amarya Maryam gidan mijin ta amma kuma sai da su Zahara suka tsaya suka gyara gidan su Maryam din kafin su koma gidajen su.

Abinda ya faru a daren nan ba karamin tayar mata da hankali yayi ba, a ranar bikin kasa komai tayi illa tunani. Tana tsoron fada ne amma tasan aikin Amriya ne, duk da tsoho yace ba zata sake dawowa ba. Koma dai meye a yanda take, wata kila ma kawai imagination ne irin nata. Kuma layar da Mama ta bata, har yanzu tana daure a hannun ta. Abinda yasa daga baya ta dena tunanin Amriya, hankalin ta ne ya koma ga Kamal da duk yinin yau bai kira ta ba.

Bata daina duba wayar ta ba, kuma a duk lokacin ta duba bata ga sakon shi ba sai taji yar damuwa a ranta. Haka bata daina dubawa ko matsalar network ne ko na wayar. Domin bai taba tsallake rana bai turo mata texte ba dan jin ya take. Har sai da ta fara tunanin kiran sa jin me yake yi kuma me yasa bai kira ta ba, amma ta kasa samun kozarin yin hakan.

A kamfani kuwa Mr. Ammar aiki yake ba hutu, haka ma'aikatan ma bai barsu ba. Dukan su dole suyi aiki da irin salon yake so, Zahara dake tunanin yanayin sa zai dawo daidai, tana jin kamar kara tabarbarewa ma yayi. Duk safe, idan yazo tana lura yanayin yanda yake magana da yanayin al'amuran sa babu abinda ya sauya. Zaman kamfanin ya rage dadi ga Zahara. Daman lokacin da aka dauke ta aiki a kamfanin, ba dan tana so ba amma tuna kyan hali da raha na Mr. Ammar yana sa taji kwarin gwiwar cigaba da aikin. Hakan nasa taji son zuwa ta tunkari Salmah amma bata tunanin zai iya sauya wani abu kamar yanda Kamal ya fada mata.

Lokacin da ta fito daga bathroom, taga message din Farida, tana tambayar ta idan bata biyo da gyalen ta ba. Dubawa Zahara tayi cikin jakar ta bata ga gyalen ba. Ta kira ta domin sanar da ita.

“Ok, kar ki damu nasan ko gidan Maryam na baro shi. Gashi ina jin wahalar komawa.”

“Zan iya zuwa na dubo miki shi, idan kina so.”

“No, it's not urgent. Toh ya kike ya gajiyar biki kuma?”

“Lafiya lau, yanzu na fito daga wanka ma. Ina son na kwanta tun yanzu dan na tashi da wuri insha Allah.”

“Ok, bari na barki ki huta. Nace ko gobe kina da dama muje restaurant?” Cewar Farida.

“Bayan kin sauko daga aiki.” Ta kara da hakan. “Nasan zaki yi mamaki amma akwai abinda nake son fada miki.”

Eh da mamaki jin hakan daga bakin ta, amma Zahara ta amince ko dan jin me zata fada mata goben.

“Ok, zan I would be available zuwa karfe bakwai na yamma insha Allah.”

“Cool, zan kira ki kafin muje akwai inda nake son mu biya.”

“Ok, Allah ya kaimu.”

“Ameen, ok sai da safe.”

Koda Farida ta katse kiran. Zahara ta kwanta. Bata samun yin wani dogon tunani ba barci ya dauke ta. Washe gari, tayi shirin zuwa office. Yau sai da ta dan dauki lokaci tana shiryawa domin har yanzu barcin bai sake ta ba. Tana jin kamar barcin minti biyar kawai tayi, shi yasa tana zuwa ta tarar da Mr. Ammar har yazo. Kuma ta tarar da ya bar mata tulin aiki. Jakarta ta ajiye ta nufi office din sa domin gaishe shi.

“Kin zo? I hope kin samu bacci mai isar ki?” Mr. Ammar ya fada kuma ta gane akwai zolaya cikin maganar sa.

“I apologize for the delay..” Ta fada cike da jin kunya.

“Kar ki damu Zahara, amma ina son files din nan da ke bisa desk dinki su zama cikin shirin kafin yamma.”

Aikin yana da yawa kuma zai yi wuya ta karasa shi kafin yamma, amma wace ita tayi masa gardama a yanayin da yake ciki. Dan haka wucewa tayi ta hado masa coffee din shi sannan ta hau aiki.

Bayan wasu sa'o'i, Sarat tazo inda take.

“Shi kadai ne a ciki?” Sarat ta tambaye ta.

Zahara bata bukatar digiri domin fahimtar abinda Sarat take nufi.

“Ban sani ba.” Zahara ta bata amsa a takaice da dan zafi. Abinda yasa Sarat dariya kenan.

“Yana takura miki har hakan? Yanzu na fara gasgata kema sonshi kike. Kice in fara saka ki jerin abokan takara ta kenan? Ba fa zai yiwu ki rike waina sannan da kudin waina ba. Ba zaki iya game su duka biyu ba. Toh bari in fada miki, Mr. Ammar ya yaba da abinda ya gani a hotel. Kuma ya riga ya shigo tafin hannu na.”

Jin hakan daga bakin Sarat bai wani ba Zahara mamaki ba, amma jin wai Mr. Ammar ya fada tarkon Sarat ya girgiza ta. Kenan dai da gaske sunyi wani abun yayin da yaje neman ta a dakin hotel. Abinda take zargi gaskiya ne kenan.

“Ba wai mugunta bace ko wani abu, amma Mr. Ammar ba sonki yake ba kuma ba wai dan kin bashi kanki ta sauki zai haukace a kanki ba.”

Sarat tayi mamakin jin hakan daga bakin Zahara, ita kanta Zahara bata san ina ta samu wannan kwarin gwiwar ba. Ranta ne a bace, dan haka a shirye take ta fadawa Sarat duk abinda ke zuciyar ta.

“Stop please, ni ba sakarya bace, nasan babu abinda yake ji yanzu a kaina, amma babu abu na kwarai dake samuwa ta sauki, zan jajurce. Kuma a ranar da zamu fara soyayya mai karfi zaki fahimta. Kullum ina hankalce da ke, kuma na lura hassada ta kike da kuma ta farin cikina. Zan cigaba da saka miki ido, idan har naga kin kusanci inda yake da wata manufa, zan sa kafar wando daya da ke.” Sarat ta fada tare da yin kwaba kafin ta shige office din Mr. Ammar ba tare da tayi knocking ba.

Zahara a ranta tace, tana fata ranar da Sarat din zata gane Mr. Ammar ba sonta yake ba hakan ba zai mata ciwo sosai ba. Sarat ta makance sosai akan kudi da kyawun Mr. Ammar ta yanda bata ganin cewa shi mutum ne tsoka da jini kuma yana tare da ita ne kawai dan kauda damuwar sa da kuma kadaicin da yake ciki.

Zahara kokarin cigaba da aikin ta tayi, amma tunani ya hana ta. Har wasu sa'o'i suka wuce amma ta kasa aje hankali tayi aiki.

“Sannu da aiki.”
Dago idanu tayi ganin mai magana, taga Ibrahim ne.

“Yauwa sannu.” Ta bashi amsa.

“Kamar da gaske aikin kike yi, alhali tunani naga kina yi.” Ya fada da dan guntun murmushi.

“Ina kokarin ganin na karasa hada files din nan ne.”

“Ah shi yasa bamu ganki wajen break ba. Na gama aikin da zan yi, ko nazo na taya ki ne?” Ya tambaye ta.

“A'a kar ka gajiyar da kanka. Nima yanzu zan mayar da hankali.”

“A'a kar ki damu zan taya ki, ai babu haka tsakanin mu.”

Bai jira jin amsar ta ba, yaje ya dauko kujera ya zauna kusa da ita tare da tambayar ta abinda zai yi. Ba bata lokaci ta shiga kwatanta mishi taimakon da zai mata.

Zahara sai da ta fara danasanin barin shi ya taya ta aiki, duk da yasa yanayin ta ya sauya wajen saka ta dariya da yake yi.

“Ya isa haka..” Ta fada cikin dariyar wani labari da ya bata. “Ya kamata mu maida hankali in ba so kake Mr. CEO ya dauka ba aiki muke ba.”

“Ta ya zai yarda ya hana ki dariya, kin ga kuwa yanda dariya ke miki kyau kamar kar ki daina.”

Shuru Zahara tayi domin ta fahimci inda ya dosa. Dole ma tayi baya baya da shi kafin har ya kai ga furtawa wata rana. Shima Ibrahim ya lura da jikin ta yayi sanyi...

Kaste yanayin nasu aka yi da sallama. Nan take Zahara ta gane mai muryar domin zuciyar ta bata yi wata wata ba ta shiga dukan uku-uku. Karfin halin dagowa tayi ta kalle shi. Shi ne a gaban ta, da dan sabon sajen gemun sa da ya kewaye masa fuska. Yanayin fuskar sa ya tabbatar mata da bai ji dadin ganin Ibrahim kusa da ita ba. Shima Ibrahim din ya fahimci hakan, shi yasa ya nemi uzirin karya domin barin wurin. Zahara bata ma ji abinda Ibrahim din yace ba domin hankalin ta yana ga Kamal din.

Bayan Ibrahim ya tafi, Kamal bai bata lokaci ba ya karaso inda take.

“Ya kike?” Ya tambaye ta tare da wani murmushi wanda tasan bai kai ciki ba.

Tayi mamakin amsar da ta bashi
“lafiya.”

“Naso kiran ki amma wasu ayyuka suka rike ni.”

Bai wani yi mata cikakken bayani ba amma hakan ya dan yaye mata damuwar da ta shiga na rashin jin motsin sa tun jiya.

“Nima ban samu lokaci ba kwana biyun nan.”

“Na gani..” Ya fada a hankali amma ta gane yana nuni da ita da Ibrahim ne.

Tuni, tayi alkawarin gaisuwa kawai zata dinga hada ta da shi. Domin kar Kamal yayi tunanin akwai wani abu tsakanin su. Taga alamun kamar hakan na takura mishi.

“Yaushe zaki karasa aikin?” Ya tambaye ta tare da duba agogon hannun shi.

“Akwai files da yawa da zan gyara, ban sani ba ko zan kai karfe bakwai na yamma.”

“Idan kina so, zan iya taya ki. Kinga mu biyu zamu yi saurin gamawa.”

“Eh, amma ina tsoron Mr. CEO ya dauka da zafi.”

“Kenan wannan mutumin yanada damar tayaki ni kuma a'a?” Saida ta dau lokaci kafin ta gane Ibrahim yake nufi. A ranta tace, ashe yana kishin ta.

“Shikenan tinda baki son nawa taimakon..” Ya fada tare da kada kafada.

Ba wai bata son ya kama mata ba ne. Tayi shuru ne domin tunanin da take na me yasa yake kishi dan ya ganta tare da Ibrahim alhali babu abinda ke tsakanin ta da Ibrahim. Kenan yana cikin irin mazan nan masu masifaffen kishi?

“Brother na yana nan? Shi kadai ne ciki ?” Ya tambaye ta.

Sai da ta dau lokaci kafin ta bashi amsa, ganin yanda ya canza maganar tasu lokaci guda.

“Eh shi kadai ne.”

Nufar kofar office din yayi. Gyaren murya Zahara tayi kafin tace
“Zan karasa aikin kafin bakwai.”

Da tunanin ko bai ji bane, ta sake dan daga murya dan yaji da kyau. Juyowa yayi tare da yi mata murmushi, sannan yayi mata godiya da amincewa da tayi. Daga nan tace zata kira Farida ta bata hakuri kan haduwar da zasu yi.


(.....)

KHADIJA

Waige-waige take tana kallon inda take, idanun ta ne suka tsaya kan kayan adon dake gurin domin kara konkwance su. Bata taba ganin irin gurin nan ba, ga kyau, sanyi da kuma dan duhu. Yanda wurin yake da kyau, yayi kamar wata farfajiyar masarauta. Bata san me yasa babu haske ba, domin da akwai da wajen sai yafi kyau.

Cigaba tayi da tafiya, tana mai bawa idanun ta abinci. Kasan wurin gaba daya an bishi da kayataccen floor mai dadin takawa. Sautin da gidan ke fitarwa ya tabbatar mata da irin gidan nan ne na da. Sauri ta dan kara, nan taga matar da tayi mata iso lokacin da ta shigo gidan. Har yanzu bata san ta yaya ko yaushe ta shigo gidan ba. Abinda kawai ta sani ta ganta cikin gidan, kuma yayi matukar burgeta.

“Ya kika ga gidan?” Matashiyar matar ta tambaye ta.

Wannan karon, ta karewa macen kallo. Dazun hankalin ta ga kyawun gidan yake, shi yasa bata lura da kyawun da matar take da ba da yafi na gidan.

Kyakyawa sosai, fatar ta fara babu ko digon tambo. Kyakyawar farar abayar ta da gyalen ta da suka yi matching da jikin ta. Kallon Khadija ne ya sauka kan kafafun matar da babu takalma. Dan dago idanun ta tayi, nan taga dige-digen jini ya bayyana bisa cikin matar da kuma bisa gyalen ta. Take tsoro ya kankame Khadija.

“Kar kiji tsoro...” Matar ta fada tana mai karasowa inda Khadija take. Koda hannuwan ta suka taba na Khadija, taji gaba daya jikin ta ya saki kamar wacce tasha myorelaxant.

“Zo muje..” Matar ta fada tare da jan hannun Khadija.

Bin ta Khadija tayi kamar rakumi da akala suka shiga wani daki. Taimaka mata tayi, ta zaunar da ita bakin gado.

Zanin gadon, tsaftatacce ne sosai ga dadin tabawa yanda Khadija taji kamar tayi kwance tayi ta barci. Juyawa tayi da niyyar yiwa matar magana amma bata ganta ba. Tashi Khadija tayi, ta shiga dudubawa amma babu alamun matar. Komawa tayi ta zauna bisa gadon, nan sai ga matar ta bayyana kusa da ita. Tsalle Khadija tayi ta ja da baya, ganin yanda matar ta koma, wannan karon ba farar abaya bace gareta, baka ce mai shegen tsawo ta yanda ko kafafuwan macen bata gani. Gashin matar duk a hargitse kamar mahaukaciya...

“Kin gani.. kin gani abinda suka min? Kawai dan nace soyayya nake son yi..na fahimci halin da kike ciki Khadija. Akwai ciwo rasa wanda kake so.”

“Ban...ban..ban gane me kike nufi ba?” Khadija ta tambaye ta tana ja da baya domin ganin ta nesanta da matar.

“Baki cancanci abinda ya faru da ke ba. Kin jima tare da Kamal ... Baida 'yancin yi maki hakan. Ni zan taimaka miki..”

“Ta..ta yaya kika san da wannan labarin..? Ni ban sanki ba.”

“Ni na sanki, kuma yanda baki tunani.” Cewar Matar.

“Me yasa kike son taimako na? Ni bana bukatar wani taimakon ki.”

“Zan taimaka miki ne, domin nima an raba ni da masoyina. Ta dalilin wadannan mutanen, sun tilasta ni rayuwa babu shi. Sun wargaza min rayuwata.”

Tausayin matar ne ya kama Khadija, domin ta lura da bakin cikin da matar take ciki, kuma yaso yayi kama da halin da take ciki.

“Bani labarin abinda ya faru. Wata kila hakan zai yaye miki wani kuncin.”

Kallon Khadija matar tayi, sannan tayi mata dan murmushi.

“Wannan ne karon farko da wani ya damu da damuwa ta. Duk da tsoron da kike ji, amma kina son jin damuwa ta. Zan baki labari na wata rana, amma yanzu ina son ki yarda da taimakon da zan yi miki.”

“Na yarda...”

Kararrawar alarm na wayan Khadija ne ya kada. Sai da ta dau lokaci kafin ta gane duk abinda ya faru ashe mafarki ne tayi.

Tashi tayi da kyar, ta kashe alarm din. Ajiye wayar tayi bisa table dake kusan kan gado.

Zaunawa tayi bakin gadon ta dafe kai tana jira ta karasa wartsakewa daga baccin kafin ta tashi ta shirya zuwa wajen aiki amma wani abu ya dauki hankalinta, wanda yasa take tsoro ya shige ta.

A da idan tayi mafarki, da ta tashi bata iya tuna komai na cikin mafarkin, amma wannan karon da banbanci.

Gyale ta gani ajiye bisa table din bakin kan gado, kuma ba kowane irin gyale ba. Gyalen da matar nan ke dauke dashi ta cikin mafarkin ta.


--------------------------
Assalamu alaikum readers. Please ku cigaba da hakuri kan jimawa da nake ban yi update ba, da gaske na dawo kuma ina son ganin na ida wannan labari, amma yanzu lokacin sanyi ne dole za'a dinga samun jinkiri wajen posting domin typing wahala gare shi cikin sanyi. Ina fata za'a fahimta 🥰
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels https://bit.ly/3Egdy1m

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 18

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚



ZAHARA



Koda suka isa gidan Kamal, yayi mata nuni da ta zauna. Ajiye files din tayi bisa center table, ta fara aikin gyaren su kafin ya dawo. Dawowa yayi falon, ya sauyo kayan jikin sa, sannan yaje ya kawo mata abin sha duk da tace masa bata jin kishi. Bayan anyi haka, ya kama mata suka fara gyara documents din. Sai wajen karfe tara na dare sannan suka kare.

“Bari na hada wani abun da zamu ci.” Cewar Kamal. Ita kuwa Zahara gida take son zuwa ganin har dare ya fara yi.

“Nagode, amma gida zan je, bana son hankalin mama ya tashi. Domin ban fada mata zan kai warhaka ba.”

Mikewa yayi tare da ce mata ba zai dau lokaci ba, zai dafa wani abun marar nauyi ne. Ya fada ba tare da ya jira jin me zata ce ba, ya shiga kitchen.

Yanke shawarar kara yan mintuna tayi, da wannan damar tayi amfani ta shiga gyara wasu documents din.

Mintuna da dama suka zo suka wuce, amma Zahara bata ga Kamal ba, saidai motsi da take jiyowa daga kitchen, gajiya tayi da jira har ta kai ga tashi domin leka shi. Dariya ta kusan kwace mata lokacin da ta tarar dashi ya rike murfin tukunya da niyyar garkuwa da shi kar mai ya waltsar masa. Fiddo farfesun kaza yayi daga cikin freezer, yana kokarin soyawa.

“Kar ki karaso nan, dan zaki kone.” Cewar Kamal.

“Kawo, bari inyi..” Zahara tace tana mai kokarin karasawa.

“A'a.. kar ki matso dan zaki kone. Zan yi kar ki damu.”

“Ba lallai mu samun cin abun nan ba a yanda yake yi, bari ni zan yi ka yarda da ni.” Zahara ta

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment