Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai..”

Bayan wasu yan mintuna, Sarat tazo tana ta faman washe hakora.

“Sorry na bata muku lokaci. Kayan ne suna da yawa. Da naji maganar Zahara nazo da yan kadan.”

Zahara bata yi magana ba, bata san dalili ba amma tana ji a jikin ta akwai abinda ya faru tsakanin Sarat da Mr. Ammar. Bata gasgata hakan ba, sai da suna kan hanya, Sarat ke ce mata :

“Kina shanawar ki da yayan boss, nima wannan karon lokacin shanawa ta ne !!”

“Me kike nufi da hakan?”

“A'a komai, zan yi kamar ke. Nima sirri ne.”

No.. bayan duk maganar da suka yi jiya, Mr. Ammar ba zai fara wata alaka da Sarat ba, hakan baida wata ma'ana. Ta tabbatar Sarat, ta fada mata hakan ne domin tayi magana... Tana fata ace hakan ne.

Ta gasgata hakan da kyau.. bayan wasu kwanaki da dawowar su, ta fara lura da wasu abubuwa tsakanin Sarat da ogan su. A duk lokacin da suka hadu, tana ganin yanda suke kallon juna. A ranta tace wannan shi ne yake kira da fada akan masoyiyar sa? Dole tayi wani abu kafin ayi nisa. Duk wannan ta dalilin ta ne, zata taimaka masa ganin ya dawo kan hanyar daidai. Haka Sarat ya kamata ta fahimci Mr. Ammar yana cikin bakin cikin rabuwa da masoyiyar sa ne, shi yasa yake kula ta ba wai dan yana sonta ba.

A yayin da Zahara ke kokarin shawo kan Sarat amma taki ta saurare ta, a ranar bayan ta dawo gida daga aiki wajen shidda na yamma, cike da mamaki wa zata tarar in ba Kamal ba zaune a falon su.
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels https://bit.ly/3Egdy1m

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 16

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚


Rabon da Khadija taji irin wannan kuncin zuciyar, tun ranar da iyayen ta suka rabu. A lokacin tana da shekaru 15 dan haka tana fahimtar duk abinda ke faruwa. Kunci ba komai bane akan halin da ta shiga kwanakin da biyo bayan mutuwar auren iyayen ta. Yau gashi ta sake tsintar kanta cikin yanayin, kuma tsoro da fargaba ne suka dabaibaye ta na gudun abinda zai faru nan gaba..lokutan bakin ciki.. nadama da kuma wahala. Bata taba tunanin Kamal zai yi mata irin haka ba. Ta kawo tunani iri-iri na dalilin da yasa Kamal ke gudun ta, amma bata taba kawowa saboda Zahara bane.

Dafa bango tayi domin taimakawa kafafuwan ta da suka kasa daukan ta. Kamal shima bai ji dadin ganin zanen Zahara da tayi ba, bayan abinda Ammar ya fada masa. Ya kara tabbatar masa gaskiyar cewa Khadija tana son shi. Ba wani kwararre bane shi wajen gane irin haka. Amma yanzu da yasan gaskiya, lamarin ya ida cabewa. Ta yaya zai iya sanar da ita baya jin abinda take ji ba tare da ya cutar da ita ba? Kuma tashin hankalin yanzu, ta ga hoton Zahara dole zata so yayi mata cikakken bayani.

Kamal kokarin yanda zai yi ya tattara kalaman da zai yi amfani da su wajen yiwa Khadija bayani yake. Matsawa yayi kusa da ita, ita kuma tayi tsalle tayi baya tare da hadewa da bango.

“Kar ka matso kusa da ni, ta yaya ka iya yin haka? Me ke ga wannan yarinyar da kuke ta rawar kafa a kanta?”

“Maganar me kike?” Kamal ya tambaye ta. “Baki san me kike fada ba Khadija, bansan me aka fada miki ba, amma kin yi kuskure. Ba abinda kike tunani bane.”

“Nasan me nake fada, saboda yarinyar nan Ammar da Salmah suka rabu. Fada min ba soyayya kake da ita ba... Fada mini please.”

“Ba soyayya nake da ita ba, amma a shirye nake idan ta amince da ni. Babu wani bashi da kika biyo ni Khadija, rayuwa ta ce. Idan kina tunanin ta dalilin ta ne kawar ki da Ammar suka rabu good, ba zan tilasta ki ba ki karya ta kanki amma ba ke zaki fada min abinda zan yi ba.”

Khadija ji tayi tamkar an caka mata wuka a kirji. Taji numfashi na kokarin ya gagare ta. Dafe daidai zuciyar ta tayi tana tambayar kanta idan da gaske wanda ke gaban ta best friend dinta ne Kamal.

“Dan Allah ce da ni mummunan mafarki nake. Na tabbatar mafarki nake.. fada min please.”

Kamal yaji ba dadi na ganin halin da ta shiga. Amma bata da yancin shiga rayuwar shi. Ya tsani a dinga shiga sha'anin sa, kuma ba yau hakan zai canza ba. Ko mahaifiyar shi ta daina shiga harkokin sa.. domin bai bata dama ba.

“Listen Khadija, you are my best friend... kin fi kowa sanin ko ni waye. Kin san cewa ba zan bibiyi abinda bani da ra'ayi a kan...”

Katse shi tayi
“Ni ba best friend din ka bace, ban taba daukan kaina a wannan matsayin ba kuma kaima kasan da haka. Kasan cewa ina matukar sonka, kana tunanin zan zauna banda saurayi alhali ina da masu sona. Ban kula samari ne saboda ina hango kaina a matsayin matar ka.”

Kamal kara tunkarar inda take yayi, amma ta kara danganewa da bango da iya karfin ta.

“A'a.. bani bukatar wata tausayawar ka, kuma ka sani ba zan taba hakura da kai ba. Na rasa shekaru da dama na rayuwa ta ta 'ya mace saboda kai, bana tunanin zan yafe maka wannan. Ina son ka fada min komai game da yarinyar nan.”

Kamal yayi kamar bai gane me take nufi ba, sun dade tare amma bai taba ganin wannan dayan fuskar tata ba. Khadija ta kasance mai nutsuwa da tunani.

“Eh, ka jini da kyau Kamal. Na cancanci sanin ko iya wannan ne.”

“Baki biya ta bashin komai Khadija, i'm sorry amma ni ban taba yi miki wani alkawari ba. Ba lallai zan san abinda kike ji ba game da ni idan baki fada min ba yau. Ba laifi na bane kuma kinsan da hakan.”

“Nima ba laifi na bane idan sakarcin ka ya hana ka gane na haukace a kanka. Ina yin duk wani abinda kace nayi. Dan Allah Kamal...nasan tsakanin ka da ita pass attraction ne kawai...mun san juna tsawon shekaru...ba zaka ce baka jin sona ko kadan a zuciyar ka ba. Please kar ka min haka.”

Wannan karon Khadija hannun Kamal ta rike a hankali... domin fahimtar da shi adadin yanda take son shi, adadin yanda take tsoron rabuwa da shi.

“Hakan ba sauki ke gare shi ba gare ni nima, ban so hakan ta kasance ba tsakanin mu. Khadija ke mace ce mai kyau, mai hankali da ilimi you deserve wanda zai so ki ya kuma kula da ke. I feel something for her duk da bamu dade da sanin juna ba. I would never lie about my feelings, ba zan taba cewa ba ina son ki, dan na faranta miki. Wannan ba hali bane.”

Ba tare da ta saki hannun sa ba, ta durkushe kasa tare da fashewa da kuka. Kamal yayi kokarin dago ta amma taki.

“No..no..i can't accept it...i can't accept it..i can't...”

“Please Khadija be reasonable and kiyi kokarin fahimta ta. Kinga muje.. in maida ke gida.”

“A'a... ba zan taba fahimtar wannan zabin da ka yiwa kanka ba. Yarinya ce fa ita, bata san komai ba game da rayuwa, bata ma wani sanka ba. Da me ta fini? Me take da wanda bani da shi? Wannan zabin da kayi baka yi tunani ba, kuma ni zan ganar da kai. Wannan munafukar ta jefe ka ne kamar yanda ta yiwa Ammar, na tabbatar har da wasu mazan ma. Tana nuna ita saliha ce, ni kuma nasan ba haka bane.”

“Ya isa haka Khadija, wannan ba halin ki bane. Ba haka na sanki ba... Kuma saboda kyan halin ki ne nake son abotar mu.”

“Ba ruwa na, a yanzu nothing is going right.. Ko na birge ka ko kar na birge ka hakan bai dame ni ba! Kawai na fadi abinda nake tunani a kanta. Gara ka bude idanun ka ka gane wacece ita kafin ayi nisa.”

“Je ki dauki jakar ki, muje in kaiki gida.” Kamal ya fada a yayin da ita kuma ta mike tsaye tana kakkabe jikin ta.

“Ba sai ka kaini ba nasan hanya.”

Saidai Kamal bai kula ta ba, ya shiga dakin sa ya canzo kaya dan ya maida ta gida. Fitowa yayi da key din motar shi, ya taimaka mata ta saka takalmin ta ba tare da ta daina rusar kuka ba.


(....)

A BANGAREN HAJIYA KARIMA DA ELH YUSUF

“Alhaji ina tunanin sai ka sa baki cikin lamarin Afnan.”

Gaban alhajin ne ya fadi. Zufa ce ta fara kare masa, ya shiga kokarin boye tsoron da ya bayyana a fuskar sa dan kar matar shi ta gani. Dan gyaran murya yayi sannan yace
“Saboda me? Meke faruwa da Afnan din?”

“Ban sani ba, ina lura da ita yanzu bata son shiga mutane. Ina tunanin akwai abinda ke damun ta da taki ta fada min. Nayi iya kokarina jin meke damun ta amma sai tace ba komai, ni kuwa nasan karya take min."

“Ba yarinya bace ita, ki daina daga hankalin ki. Idan tace miki lafiya lau take, to lafiya take.”

“Ko kana ganin bata jin dadin zama da mu ne? Ka ganin na barta ta koma wajen iyayen ta?”

“Kina daga hankalin ki ne a banza, akwai matsalar da tafi wannan a yanzu wacce ya kamata mu warware, ta auren Ammar.”

Alhaji satar kallon matar sa yayi dan ganin ko zata manta da zancen Afnan kuma da alama yayi nasarar yin hakan. Yanayin matar sa ya sauya daga damuwar halin da Afnan ke ciki zuwa bacin rai.

“Yarinta har yanzu ke damun Ammar, da zai san dalilin da yasa muke yi masa duk wannan ba."

“Daina nuna karfi a kansa, ki sake kokarin yi ganar da shi. Nima zan yi masa magana.”

“Kana da gaskiya, zan sake yi masa magana in gani. Idan bai sauya ba dole zan yi ta karfin."

Alhaji ya daina jin me matar sa take fada, tunanin yanda zai fitar da Afnan kasar waje yake kafin ta sa matar shi ta fahimci wani abu. Yasan Hajiya Karima, bata taba karaya ba idan tana son sanin wani abu. Gara ta tafi kafin ta tona masa asiri.

Yasan abinda yake yi ba daidai bane, amma ba yanda za'a yi ya iya hana kanshi. Yarinyar nan tana tuna masa da matar sa lokacin da suna matasa. Matar shi a lokacin kyawawa ce ga diri mai daukar hankali, a lokacin maza rububin ta suke amma ita ta kyankyashe tace sai shi. Suka yi aure cike da son junan su, amma shekaru na shudewa sonta da sha'awar ta suka fara raguwar masa. Sai gashi yau a jikin Afnan yana ganin matar da ya fada soyayyar ta a baya. Yana bala'in sha'awar ta.. sosai ta yanda idan ya ganta sai yaji kamar ya yage kayan jikin sa yaje ya dauke ta.

Yasan Afnan ta tsane shi, hakan ne kuma ke kara sa yaji yana sonta... Shine na farko da ya fara sanin ta a 'ya mace, hakan yasa yake bata duk abinda yasan tana so. Yana siyo mata abubuwa masu tsada in har basu fi karfin arzikin sa ba. Amma ba zai bari wannan makauniyar sha'awar ta kaishi ga faduwa ba. Dole ya fidda ta kasar waje, zai yi mata maganar yau da yama idan kuwa taki amincewa. To fah zai yi abinda ba zai so aikatawa ba.


(.......)


Kwanaki na shudewa amma yanayin Khadija ya kasa daidaituwa, wutar tsanar Zahara na kara ruruwa a cikin zuciyar ta. Kamar mai shafar aljanu.

Hankalin Salmah ya tashi, ganin yanda kawar ta bakin ciki da damuwa na son suyi mata illa kuma babu abinda ta iya yi. Sai yanzu take fahimtar abinda Khadijar ta dinga ji lokacin da itama ta bata da Ammar.

Tana ganin yadda kullum kawar ta ke sauya... Har ta fara kasa gane ta.. bata cin komai sannan tafi son kulle kanta cikin daki. Ta daina zuwa wajen aiki kuma abinda yafi dagawa Salmah shine Khadija ta daina sallah.

Wata rana, ta shirya tayi kwalliya da har ta sa Salmah jin dadi da tunanin ko kawar tata ta fara dawowa daidai. Amma da tace mata zata je wajen Ammar ne tayi masa maganar Zahara, Salmah ta fahimci babu abinda ya rage na halin da Khadijar take ciki.

“Kada kiyi haka Khadija, zaki batawa Kamal rai ne kawai. Kuma ba lallai bane ta dalilin ta ne na rabu da Ammar. Ta dalilin mahaifiyar sa ne da shi kanshi.”

“Eh amma ita ta fara zuwar muku da matsala a soyayyar ku, zan yi magana da Ammar. Idan na fada masa komai wata kila ya iya budewa dan uwan sa idanu ya gane ko wacece Zahara.”

“Fushi ne zai ja kiyi abinda zaki jagula komai. Kuma nice zaki cutar idan kika yi hakan.”

“Kinsan babu abinda nake so da ya wuce farin ciki kawata. Amma ba zan iya barin yarinyar nan tana yin yanda taso ba.”

“Kiyi tunani ba wai dan kin bata ta ba, Kamal zai dawo gare ki. A'a, saidai ma su kara samun kusanci, dan haka kar ki ce komai, ki jira lokacin da ya dace. Idan nice ke, zan bi abun da nutsuwa. Kiyi kokarin kusantar shi, ki nuna masa kin amince ku cigaba da abotar ku.”

“A'a ba zan iya yin hakan ba. Amma nasan kina da gaskiya... Ya kamata in kara yin tunani kafin daukar wani mataki.”

“No, kiyi kokarin mantawa da komai nake nufi. Idan kika cigaba da saka abun a ranki zai iya zame miki wani ciwo.”

“Salmah matsalar ita ce bana bukatar in manta. Ba zan iya rungume hannuwana ba, ba tare da nayi wani abun ba.”


A BANGAREN ZAHARA

Wannan satin gaba daya, bata samu time din kanta ba, ga aikin office ga kuma shirye shiryen auren cousin dinta Maryam. Ba wani sanin juna suka yi da Maryam din ba. Kasar waje Maryam tayi karatun ta, ta girmi Zahara da shekara biyar. Ta dawo daga karatu a kasar Germany, tazo gaishe da Mama tare da sanar da su maganar auren ta. A nan ne Mama ta gabatar da ita ga Zahara.

Maryam mace ce mai saukin kai, tana hira da Zahara kamar sun dade da sanin juna. Sun karbi numbobin juna, suna waya akai-akai. Ta roki Zahara da ta taimaka mata wajen shirye-shiryen bikin auren. Zahara ba mai son shagulgula bace amma ba zata iya ce mata a'a ba. A daren ranar bikin, ta nemi Zahara taje gidan su ta kwana. Zahara taji dadin hakan, itama Mama tayi murna sosai da Zahara ta sanar da ita. Ko ba komai hakan zai fara sa Zahara ta fara kawaye.

Dan haka Zahara ta shirya yan kayan da zata je da su, taje gidan. Jajibirin biki ne amma gidan cike yake da yan uwa da abokan arziki. Lokacin da Zahara taje, Maryam ta gabatar da ita a wajen kawayen ta Hafsat da Farida. A nan suke fada Hafsat da Maryam a makaranta cen Germany suka hadu. Ita kuwa Farida kawa ce tun ta yarinta. Hafsat kamar Maryam take, akwai raha da sakewa da mutane. Ita kuwa Farida ciki ciki take, bata wani cika son yin magana ba. Sun iya kokarin su ganin Zahara ta sake da su. Har wani lokacin tana dan tsoma bakin ta idan suna hira...

Zuwa karfe sha daya na dare, cacaniyar gidan bata rage ba kuma har lokacin su Zahara basu ci komai ba. Yayin da sauran ke ta surutun su, Zahara da Farida suka yanke shawarar fita waje siyan abinda zasu ci da sauran.

“Ni zan biya kudin.” Cewar Farida tana fiddo kudi yan goma-goma daga cikin jakar ta. Sannan ta kara da cewa
“Zaku biya ni idan anje wajen party gobe.”

“Ai dama rowar ki ba zata bari mu ci mu sa miki Albarka ba.” Hafsat ta fada tare ce musu su biyo mata da ice cream.

Farida sai da taji abinda kowa yake bukata sannan ta cewa Zahara su je. Bakin titin yana da dan nisa da gidan, dan haka dole sai sun dan yi tafiya kafin su samu taxi. Bayan sun dan yo nisa da gidan, Farida tacewa Zahara ta manta id card dinta gida. Zahara tace to bari ta jira ta nan ta koma ta dauko.

Titin tsit yake, motoci daidaiku ne ke wucewa. Zahara bata tunanin ma zasu samu taxi ko dan sahu da wuri. Allah yasa ma akwai fitilun kan titi in ba haka Zahara zata ji tsoron tsayuwa ita kadai.

Tayi nisa cikin tunani, lokacin da ta fara jiyo kukan yaro. Da sauri ta juya ta hangi wani yaro cikin duhu inda fitilar hanya bata haska ba. Cikin dan tsoro tsoro Zahara ta wai-waiga ko zata ga wani babba da ke tare da yaron amma babu kowa. Dan haka ta karasa wajen yaron a hankali.

“Sannu..” Ta fada cikin tausashiyar murya dan kar yaron ya tsorata.

Yaron ya cigaba da kuka ba tare da ya kalle ta ba.

“Ina wanda kake tare da shi?” Ta tambaye shi, cikin sheshekar kuka yace
“Gi..gida..nake..son..naje...”

“Ina ne gidan naku yake? Kana tsoron zuwa gidan ne kai kadai?”

Gyada mata kai yaron yayi.

“Da kai da wa kazo nan?”
Bai bata amsa ba ya cigaba da kuka.

Tausayin yaron ne ya kama ta, a ranta tace bata san me yasa wasu iyayen basu da kula ba. Ta yaya zasu bar yaro ya fito a irin wannan lokacin?

“Kasan hanyar gidan naku? Ni zan raka ka kaji.” Ta fada da sigar rarrashi. Da jin haka yaron ya fara rage sautin kukan sa, har yayi shuru.

A daidai lokacin Zahara ta jiyo muryar Farida a bayan ta.

“Zahara? Me kike yi kuma a nan? Muje, sorry na dan jima ko."

“Ina zuwa Farida, bari in raka yaron nan gidan su. Yanzu na dawo ! ”

“Wane yaro kuma?” Farida ta tambaye ta cike da mamaki.

Juyowa Zahara tayi da niyyar nuna mata yaron amma babu yaro babu alamun sa a wurin. Ya bace bat.
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels https://bit.ly/3Egdy1m

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 15

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚



Zahara bata taba jin nauyi irin na yau ba. Karasowa tayi a sanyaye ta gaishe su da siririyar murya. Tambayoyi ne birjik a cikin kanta wanda ta gagara amsa su...

“Zo ki zauna 'yata, bari na kawo abin sha.”
Tashi Mama tayi ta nufi hanyar kitchen. Da kallo Zahara ta bita kafin ta yanke shawarar zaunawa domin jin me ke tafe dashi. Karasawa tayi a hankali ta zauna kusa da yayan ta da ta jima rabon ta da shi. Koda ta zauna, suka fara magana. Ji tayi suna maganar zane (art), suna fadar wasu abubuwa da bata taba jin su ba a rayuwar ta. A bakin Kamal, ba abin mamaki bane, domin ganin zanukan dake cikin falon sa, ta tabbatar shi mai son zane ne amma bata taba tunanin yayan ta yasan wani abu ba a harkar zane.

Mama ce ta dawo dauke da jus da ruwa, kama mata Zahara tayi wajen zubawa su Kamal. A yanda take a rikice, addu'a take kar ta barar da lemun. Bayan ta zuba musu lemun, Mama tayi shigewar ta daki. Yayan ta kuma baida niyyar tashi ya barta tare da Kamal. Duk da ba wasu makusanta bane sosai ita da yayan nata, amma kowa a gidan yasan yanda yake bata kariya. Bayan wasu mintuna, ya yanke shawarar basu wuri.

Kamal shan lemun sa yake cikin kwanciyar hankali, ita kuwa na ta kokarin ganin ta sarrafa tambayar da take son yi masa. Jira take har ya gama shan lemun, bai kuwa bata lokaci ba ya ajiye kofin.

“Ya kike?” Ya tambaye ta yana kallon ta.

“Lafiya lau...”

Tayi niyyar yi masa tambayoyin amma kamar an toshe mata baki. Sunkuyar da kanta tayi, domin bata iya jure kallon sa... bare kuma da yace yana son auren ta.

“Na sani, da na sanar da ke kafin nazo gidan ku amma kuma bana son ki ki karba ta. Nazo ne kawai na gabatar da kaina gidan ku, domin nuna da gaske nake ba da wasa ba. Abinda kika fada min rannan yasa nayi nazari sosai. Bai dace ki yarda da ni ba, alhali bamu wani san juna ba. Ba zan takura ki ba, domin ki aminta da ni. Nasan kina da tambayoyi da dama, ki sani zaki iya fada min komai. Zan kokarta ganin na amsa duk wasu tambayoyin ki.”

Shuru yayi kafin ya cigaba
“Kuma bana son kiyi tunanin zuwa gidan ku da nayi saboda wata manufa ce ta daban. Idan kina so, ba zan sake zuwa ba, har sai idan ke kika ce nazo.”

Sauraron shi take da kyau kuma ta kasa daina zuzuta kanta kan cewa yayi wannan tattakin ne saboda ita, domin tabbatar mata da gaske yake. Ba zata iya cewa ba ta yarda dashi, amma tasan ba yanda za'a yi ya dinga duk wannan kan abinda baida muhimmanci a wajen sa.

“Me yasa ni? Me yasa sai ni kake son aure?”

“Ba zan iya amsa wannan tambayar taki ba Zahara...”

Tana jin dadin yanda yake kiran sunan ta.. cike da yanga da dadin ji.

“Ba zan iya amsa tambayar ki ba, domin ni kaina bani da amsar ta. Ba zan ce ina miki mahaukacin son nan domin idan na fadi hakan nayi karya, amma kina daukar hankali na sosai. A da ina tunanin hakan a matsayin birgeni kawai kike, amma na gane yafi hakan. Ni ba yaro bane, ba wai dan kina daukar hankali na ba zan yi wata alaka da ke, mu rabu bayan na samu wacce nake so. Addini na yayi min hani da yin hakan. Kina daukar hankali na ne kawai, domin kamar yanda kika ce bamu wani san juna ba. Dan haka zan yi kamar yanda masu cewa soyayya wata aba ce dake ginuwa ta hanyar sanin masoyi, sanin halin sa har ma da kurakuran sa. Dan haka ina son sanin wacece ke kuma idan kema a lokacin kin ga wani abun da yayi miki game da ni. Ki sanar da ni zan zo na nemi auren ki.”

Shuru yayi domin barin ta taji da abinda ya koro mata.

“Of course, idan baki da ra'ayin yin hakan, zan fahimta. Zan ji ba dadi amma zan fahimta, zan yi kokari ganin ban dauki abun da nauyi ba. Ina son kiyi tunani sannan ki fada min abinda kika yanke. Waya ta a kunne take a koda yaushe, zaki iya kira na kowanne lokaci, a lokacin da kika so, zan kasance cikin kaguwar jin amsar ki da sa ran ki amince.” Ya fada da dan guntun murmushi.

A ranta tace, yana tunanin ba abinda zata yi da shi alhali a rikice ne take. Bata san amsar da zata bashi ba, dole ma ta samu nutsuwa tayi tunani.

“Ni zan tafi kafin dare yayi. Kar ki manta, zaki iya kira na a kowane lokaci. Zan zauna zaman jiran amsar ki.” Ya sake tunatar da ita kafin ya mike tsaye.

Mikewa tayi itama da sauri kamar wacce aka sawa remote, tana jiran ya tafi amma ya matso inda take tare da miko mata wani kwali. Hannun sa ta kalla, ta kalli kwalin sannan ta kalle shi.

“Chocolate ce, ban sani ba ko kina son irin wannan abubuwan. Ina son kawai yi miki kyauta ne.”

“Ba zan karba ba..” Ta fada murya cen kasa.

Hannun ta ya kama tare da dora mata kwalin.

“Zaki iya zubarwa, amma ina tabbatar miki chocolate akwai dadi. Ki karba, zan ji dadin haka.”

Karba tayi tare da yi masa godiya. Murmushi yayi sannan yayi hanyar fita daga falon. A daidai lokacin Mama ta fito daga kitchen.

“Ina zaka je? Girki ya kusan kaiwa.”

“Zan dawo wani lokacin Mama, inda nake ne akwai nisa.”

“Toh Allah ya tsare ka gaishe da mutan gidan.”

“Zasu ji Insha Allahu.” Ya fada tare da nufar hanyar fita. Zahara na biye da shi domin rufe kofa idan ya fita. Lokacin da ya fita, sai da ya juyo ya kalle ta tare da yi mata sai da safe.

“Allah ya kaimu and thanks for chocolate.”

Murmushi yayi mata kafin ya shiga mota. Tayar da motar yayi, har sai da yayi nisa sannan ta koma gida.

Da shigar ta gida, Mama ta shiga kallon tana mata murmushi. Kunya ce ta kama ta tace
“A'a Mama, babu abinda zaki ji...”

“Ban taba tunanin my little girl tana da saurayi ba, kuma kyakyawa dashi. Me yasa baki fada min zai zo yau ba? Da na gama girki da wuri.”

“Lahh Mama ba fa saurayi na bane, kuma bansan zai zo ba.” Zahara ta fada tare da hayewa sama da tunanin ko Mama ta bar zancen, amma Mama ta biyo ta har daki.

“Mama...”

“Ba fa zaki ce min kawai aboki ba ne. Naga yanda yake kallon ki kuma ke baki son kallon shi.”

“Ba wanda nake iya kallo cikin ido

4 Comments On AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
avatar
abdulyasar

2 years ago

Reply

Allah Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulyasar

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment