Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

╨╧рб▒с>■  |~■   klmnopqrstuvwxyz{                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                ье┴g Ё┐0╝bjbj┌к┌к .h╕└ob╕└obG       ╖ZZ╓╓╓╓╓    ъъъъD.< ъ┌FljjjjjE E E y2{2{2{2{2{2{2$FH╢№J`Я2ї╓E E E E E Я2╓╓jj█ФFE2E2E2E Ї╓j╓jy2E2E y2E2E2E2j    pйз&g┘    90▐E2e2кF0┌FE2\K2.\KE2\K╓E2 E E E2E E E E E Я2Я2E2E E E ┌FE E E E                                                                     \KE E E E E E E E E ZB Ь: An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels (Romance)


Writing By Amnah El Yaqoub


Dedicated to Aisha's Name

Like my Page On Facebook=╪G▄<╪√▀
https://www.facebook.com/amnahel



1&2

______

Chamo,Dutse Area (Jigawa State)

Wata tsohuwa ce me kimanin shekaru Sittin da Shida tashiga cikin wani madedecin gida na masu qaramin qarfi, Sai mita take tana sababi "Haba! Wannan aba da'ake ganin darajarta, ake saka mata d'an kamfai, asaka mata siket, sannan ad'aura zani akai,yau itace a wangale wannan Yara na Asbiti Sai leqawa suke"

Ta qarasa maganar tanajan kujera 'yar tsugunno tana zama, Ummah dake Gefe a zaune tana yanka albasa akan qanzo tace "Sannu da Zuwa Hajja, bade har yanzu bata haihu ba?"


Wadda aka kira da Hajja tace "bata haihu ba har yanzu,wannan yarinya tana ganin azaba, sunce fa tasamu yaga har waje hud'u"

Ummah ta zaro ido tace "Hud'u?"=╪3▐

Ta6e baki tayi tace "yaga Hudu Hadiza, wata yarinya tana nan Sai leqawa take, takasa tsinana mata abun Arziqi, nide nataho nabar jummai acan Sai dawurwuri take tana tsoro kar jikarta ta mutu"

"kode wata yarinya ce siririya, zaki ganta 'yar doguwa itace take kar6ar haihuwar?" cewar Ummah

Hajja tace "itace inajin, tana nan wata Mai kamar Sanda de"

Ummah tace "Hajja tokode Sandar cema?"

Wadda aka kira da Hajja tace "Fad'i kanki tsaye Sandar cema, wannan qirji ashafe, ga uban tsawo, tun dazu take cewa ga kainan yataho Amma shiru kakeji, nikam nataho, idan ta sauka saina koma"

Wata yarinya ce tafuto daga d'akin Hajja,bazata wuce shekara goma Sha takwas ba, fara ce tas Me matsagaicin tsawo, tana Sanye da Hijabi madedeci ajikinta, kasancewar hijabin ba dogo bane hakanne yabawa bajajjan hips dinta damar bayyana, kallon su tayi duka su biyun, ta zabgawa Hajja Harara, sannan ta d'auki buta ta wuce bandaki, cikin ranta tana tunani tabbas zama da mad'aukin kanwa.... Gashi yanzu itama Ummah ta biyewa Hajja suna zagin baiwar Allah, fisabillillah banda sharrin Hajja tayaya za'ayi a cewa mutum Sanda?>╪▌

Hajja databi Bayan yarinyar da kallo tasaki ajiyar zuciya tace "mesunan qawa da masifa take, tunda tafara qirgen dangi muka shiga uku da saka hijabi acikin gidannan, kullum tana cikin Hijabi kamar abun masifa, d'an girgen dangin ne bataso mugani, inba hakaba mutum yayi ta yawo da hijabi muba had'a dangi mukai da limamai ba, wannan jaraba har Ina, da wannan zafin duniyar mutum zaiji koda yawo da Hijabi "

Ummah tayi murmushi ba tace da'ita uffan ba, saide cikin ranta tace"kunfi kusa"

Adede lokacin yarinyar tafuto daga bandaki, har yanzu hararar Hajja take, tsugunna wa tayi tafara alwala, saida tazo wanke fuska sannan ta janye hijabin dake jikinta, lokaci d'aya tulun gashinta me santsi da tsawo ya bayyana, gashin har qyalli yake saboda yasha wanki, Hajja ta kalleta ta Ta6e baki sannan ta shige cikin dakinta inda yarinyar tafuto

Ummah ta kalleta tace "AISHA, idan kin idar da sallar ga qanzonku Nan keda Hajja"

Kafin ta amsa mata, Hajja tafuto daga cikin dakinta da robar Vanillah a hannunta tace "A a nikam bazan iyacin qanzon Nan ba, Jikar Jummai tana can a Asbiti rai a hannun Allah, Ina Naga tacin qanzo"


Wadda aka kira da Aisha, ta bude d'an qaramin bakinta Mai launin pink, cikin siririyar muryarta ta kalli Hajja tace "Amma ai gashinan hakan bai hanaki qulla Vanillah ba"

Kafin Hajja tabata amsa wani yaro yayi sallama yashigo yace "Hajja A'i, abani kunun Aya na Hamsin"

Kudin ta kar6a, tabashi kunun ayar tana fad'a masa "kadawo min da jarkar kaji"

Yaron yace "To" sannan yafice daga gidan

Aisha ta'idar da sallar, sannan tafuto tsakar gidan hannunta d'aukeda Radio tana kunna wa.

qanzon dake gaban Ummah ta d'auka, ta zauna akusa da Hajja, sannan ta ajiye Radion agefe, tayi Bismillah tafara cin qanzon,had'in qanzon yayi mata dad'i sosai, batasan lokacin data tamiqa hannunta taqara sautin Radion ba, Adede lokacin ne me karanta labarai take cewa"to masu sauraro kuci gaba
Sauraron Freedom Radio dake Nan jihar Jigawa domin samun rahotannin bidiyo da hotuna kan labarun Najeriya da Nijar da ma sauran sassan duniya baki daya,ayau ne Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kafa dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin yi wa Щaramar yarinya fyaWe, acikin birnin tarayya Abuja kuwa, Shahararran d'an kasuwa, Kuma matashin Shugaban E.F.C.C, Wanda akafi Sani da MAHMUD WAKILI, ya Bawa Yan qungiyar qwallon qafa ta Nigeria kyautar nera million talatin, sakamakon samun nasara dasukai har suka samu kyautar kofun zakarun nahiyar Africa, matashin de yaqware wajan aikin sa, inda yake aiki ka'in da na'in wajan ganin ya daqile cin hanci da rashawa acikin wannan qasar, MAHMUD WAKILI ya kasance..... "

Cikin sauri takashe radion,batare dataji qarshan labaran ba,qasa tayi da kanta ta zubawa qanzon dake gabanta ido

Batasan meyasa ba kawai taji mutumin bai wani birgeta ba, menene abun birgewa anan da har gidan Radio zasu dinga yayatawa? saboda Allah duk cikin Wanda ya Bawa kudin Nan tasan cewa sunada Hali, ga talakawa barkatai suna buqatar taimako Amma manyan qasar basayi musu, saide a qarawa me qarfi wani qarfin, mutum ne zaka ganshi da 'ya'ya samada guda shida, Amma bashida cin yau bare na gobe,yanzu Yan Ball za'a dauki kudi a basu har million talatin, jijjiga kanta tayi, cikin ranta tace "Allah yahad'ani dakai ko sau d'ayane arayuwa,a ranar zan manta cewa sunanka d'aya da mahaifina"

Hajja dake Gefe tace "masu abu da abunsu, yawanci zakiga masu suna Mahmud sunada kud'i, Amma ni nawa mahmud din Sai godiar Allah"

Daga Ummah har Aisha babu Wanda ya tanka mata, asalima Aisha ji tayi gaba daya ranta ya6aci Dajin labarin wannan mutumin, d'an qanzon datake ci taji yafita daga ranta, tashi tayi ta shige daki, tasauya hijabi domin shirin tafiya makaranta

Tana jiyo wayar Hajja tayi ringing, Hajjan ta d'auka tace "jummai ya'akayi? Me naqudar tasauka?"

Daga d'ayan bangaren jummai tace "tasauka Hajja, ansamu d'a namiji, yanzu ma gida nazo nadauka mata d'an kunun kanwa, nace ko za'a samu d'an sauran sikari (suger) awajanki zan zuba mata acikin kunun?"

Hajja tace "wallahi babu jummai, saide zuwa anjima zan siyo"

Jummai tace "to shikkenan" daga Nan takashe wayar


Aisha dake shirin futowa daga d'akin cikin ranta tace "Kai wannan mata da jarabar roqo take wallahi, jikar ki ta haihu Amma kikasa siyan sigan daza'a zuba mata acikin kunu Bayan ba kudin kika Rasa ba?>╪▌

Sallama tayi musu ta wuce makaranta, tanajin Hajja tana cewa"to me sunan qawa saikin dawo"


Tana fita tahangi qaninta jabir, kana ganinsa zakagano tsantsar kamar dasuke da juna, batace dashi uffan ba tawuceshi, shine yaga yanayinta kamar ranta a 6ace yace"me sunan qawar Hajja antafi ne?"

Share shi, cikin sauri ya qaraso wajanta ya fizge jakar littattafanta, cikin 6acin rai ta Kalleshi tace "JB Bani jakata Dan Allah, wallahi raina ne babu nishadi"

"keda Hajja ne?" yajefo mata wannan tambayar, ajiyar zuciya ta sauke tace "Wacce Hajja? Labari naji a Radio Wai shugaban EFCC MAHMUD WAKILI yabawa Yan qwallo kyautar kudi har million talatin jb, wallahi banason mutumin Nan, haka kawai naji bai kwanta minba"

Kwashewa da dariya jabir yayi yace "toke menene abun damuwa anan? Ke suna qoqari fa Yan Ball din, akwai su Big Brother manyan Yan ball ne,inde sunci ball menene aciki Dan anbasu kyautar kudi? Hakan zaisa su sake dagewa, muje na rakaki makarantar"

Ya qarasa maganar yana Jan hannunta, qwace hannunta tayi tace "yanzu Kai hakan be 6ata ma raiba? Nikam haushi yabani wallahi, Ina laifin ma yabawa talakawa kokuma nakasassu,har yanzu nema muke Asamu atara Maka kud'in registration katafi makaranta ko 'yar legal Ringim dinnan ne kaima kaje kayi,Amma Yan Ball fa jb, jinake da zan ganshi sainayi masa tatas wallahi, wannan ya wuce kashe kudi saide almubazzaranci"

Dariya jabir yasake yi akaro na biyu yace "Wai wa Zaki Gani? Shi Mahmud din? Ke irin wannan mutanan waye yafada miki suna zama a qasar? Mutumin daya shahara afannin kasuwanci, ga Kuma Babban muqami a Gwamnati shine kike tunanin Zaki Gani a wannan qauyen? To banqi ba in waya Zaki Ara kiyi search din photonsa a opera kigani, Amma inba hakaba Ina muke da hanyar ganinsa"

Cikin masifa tace "in ari waya inyi searching din photonsa me hakan zai tsinana min?"

Cikin murmushi jabir yace "Arziqi zai tsinana miki"

Cikin 6acin rai tace "saide tsiya wallahi"

Suna wannan musun suka qaraso islamiya inda take koyarwa, abakin get din makarantar tahadu da qawarta Walida wadda suke koyarwa tare a makarantar,Walida tace "Aysha Mahmud yaude munzo tare"


Cikin son kawarda 6acin ranta ta amsa mata, sannan suka shige cikin makarantar shikuma jabir yajuya zuwa gida

Wani yaro ne yashigo gidan yace "Hajja A'i abani ruwa na nera goma me Sanyi"

Cikin masifa tace "bazan bayarba, yankare masu shegen iyayi..., idan ruwa babu Sanyi kuce abaku me Sanyi, idan ruwa me Sanyi ne kuce abaku marar Sanyi, inada me sanyin bazan siyar ba, har a cinikin nera gomane mutum yakeda za6in kalar Wanda yakeso"(>╪-▌)

Yaron yajuya yatafi, Adede lokacin Jabir daya Raka Aisha makaranta yashigo gidan, Hajja na ganinsa tace "yauwa Jabir meqamin niqan Aya Dan Allah"

Kar6a yayi yajuya yatafi.


Sai karfe shida saura su Aisha suka tashi daga islamiya, suna tafiya ahankali itada Walida, ta Dubi Walida tace "Walida Dan Allah kinsan inda zanga shugaban EFCC?"

Walida ta zaro ido(=╪3▐)sannan tace''shugaban EFCC?"

Kai tsaye Aisha tace"Eh, shifa"

Cikin mamaki Walida ta kalleta tace "kinsan inda zakiga me kanfanin MTN?"

Aisha tace "Ina tambyarki kema kina tambayata, Ina zanga me kamfanin mtn Walida?"

Walida tace "to Alhamdulillah, Nima bansan inda Zakiga shugaban EFCC ba, nemansa abune me wahala,shiyasa nabaki misali dame kamfanin mtn, shugaban EFCC niko ganinsa ma bantaba yiba ko a photo,koke kintaba ganinsa?"

Tace "bantaba ganinsa ba, sonake de na ganshi azahiri...."
Kafin Walida tayi magana wata budurwa yar Gayu taqara so wajan su, daganinta kasan Gayu ya zauna, Kuma da alama ba'a qauyen take ba, budurwar ta kalli Aisha tace"qanwata Dan Allah a'ina kika siyo air lashes din idonki?"

Daga ita har walida murmushi sukayi, walida tace"ba air lashes bane, haka gashin idonta yake"

Murmushi budurwar tayi tareda yimusu godia ta wuce

Haka sukaci gaba da tafiya har sukazo inda zasu rabu kowa yatafi gidansu, Aisha tana komawa gida taga Hajja tana Dama kunun Aya, Jakarta kawai ta ajiye ta zauna tana tayata aikin

Sallama jummai tayi, Bayan sun gaisa suka sake yimata barka akan haihuwar jikarta, Hajja tace "Salaha Kuma ansauka, Allah sarki Allah yaraya, yaya yagar Tata Kuma?"

Jummai tace "ai infada miki Hajja A'i an dinketa tsaf, tana nan a kwance de"

Hajja tace "to Alhamdulillah Allah yaraya"

Jummai tace "Amin,Hajja A'i nace zan samu sauran sigan kuwa?" (>╪-▌)

Mamaki yakama Aisha da Ummah, tun kafin tatafi makaranta taji Ana zancen sigan Nan, har yanzu kenan Qin siya tayi tana jira Hajja tasiyo na kunun Aya Sai tazo ta kar6a, harta bude baki zatace babu, Sai taji Hajja tace" Wallahi jummai babu sigan, duka najuyeshi acikin kunun aya saide a tsamo miki aciki "(=╪▐)

Jummai tace" innalillahi wa inna ilaihirraji'un....Inkaji Ana haka Kuma ai masifar takai masifa, tayaya za'a tsamo min siga acikin kunun Aya, nabar ki lafiya Hajja A'i"

Daga Nan tatashi tayi gida, Hajja tace"inbanda masifa jikar ki ta haihu kikasa zare kudi ki mata abun Arziqi, me jummai zatai da kudi ne?"
tajuya tana tambayar Ummah, Ummah tayi murmushi tace"Sai haquri Hajja A'i"

LABARIN SU:

Aisha da Aisha qawaye ne, Wanda sukai karatu tare,tundaga js one, har candy a makarantar goron dutse dake jihar kano
Gaba d'ayansu Yan kano ne,Aysha Sulaiman Bompai, dakuma Aysha Yakubu Sagagi, sun shaqu mutuqar shaquwa, idan akazowa mutum daya visiting tare suke tafiya, haka dayar ma, babu Wanda yata6a jin kansu acikin makarantar, mutane dadama suna tunanin sudin yan'uwa ne, saide basuda wata alaqa illa qawance dakuma soyaiyar juna da Allah yasaka wa dukkaninsu, tun kafin suyi candy sukayi wa juna alqawari idan sukai aure daya ta haifi namiji, daya Kuma ta haifi mace to zasu hada yaransu aure, idan Kuma duka mata suka Haifa, zasu saka musu suna AISHA , ma'ana zasuci sunansu, idan Kuma kowacce namiji ta Haifa acikinsu, to zasu sakawa wadannan mazan suna MAHMUD, Alokacin dasuke wannan karatu ko uniform babu, atamfa suke sakawa a matsayin uniform, makaranta zata baki Riga da zani dakuma wani zanin spire, Sai suke yafa dayan zanin a matsayin mayafi, awanan lokacin babu waya, saide wasiqa idan kana buqatar tura saqo.

Aisha da Aisha suna tsaka da wannan qawance nasu lokacin candy yazo, sukayi candy cikeda kewar juna, Bayan kowa yakoma gida Aysha Sulaiman Bompai dayake iyayenta sunada Hali, tasa direban gidansu yakaita unguwar Sagagi ta kaiwa qawarta Aysha Yakubu Sagagi ziyara,Bayan wahala dasuka Sha kafin su samu gidan, saboda babu waya, Aysha Yakubu Sagagi taji dadin ziyarar qawar Tata, sun dade suna zantukansu na yanmata inda anan ma suka sake jaddada alqawarinsu na makaranta, Bayan sunyi aure idan daya tahaifi mace, daya ta haifi namiji, zasu hadasu aure, idan mata suka Haifa zasu saka musu suna AISHA, idan maza suka Haifa zasu saka musu suna MAHMUD, da tunanin wannan alqawari Aysha Sulaiman Bompai tadawo gida, rabuwar dasukai kenan, har yau, har gobe, babu Wanda yasake saka dayansu acikin idon juna, tsawon shekara sittin da shida kenan kowa yana neman dan'uwansa, Amma babu wani labari

Bayan ziyarar Aysha Sulaiman Bompai data kaiwa qawarta, Bayan wasu kwanaki aka maida mahaifin ta aiki Garin jigawa, Alokacin jigawa da kano ahad'e suke ba'a rababa, Aysha Yakubu Sagagi taji shiru tashirya taje ta nemi qawarta Aysha Sulaiman Bompai,saide tana zuwa mutanan unguwar suka sanar mata cewa ai sun saida gidan,sun koma Jigawa dazama,haka ta dinga zarya harta gaji.


Ahankali rayuwa ta dinga juyawa, kwanaki suka koma Satuka, Satuka suka koma watanni, watanni suka koma shekaru, Aysha Yakubu Sagagi ta auri wani Dan Nijar me kudi Wanda yazo kasuwanci Garin kano

Aysha Sulaiman Bompai kuwa agarin Jigawan Allah ya hadata da Miji tayi aure, ya aureta daga Garin Hadejia, yakaita wani qauye a dutse, mesuna Chamo, mahaifin ta Kuma daga baya yakoma kano da zama gaba daya, Bayan yayi retired, inda yasai wani gidan a unguwar yankaba

Aysha Sulaiman, haka tayi hakurin rashin mahaifin ta, ta rungumi mijinta, suna Zaman su lafiya, har Allah yabata ciki, Bayan doguwar naquda tahaifi danta Namiji, babu 6ata lokaci kuwa ta fadawa mijinta cewa tanaso ya sakawa Yaron suna MAHMUD, Haka akayi kuwa

Aka sakawa Yaron suna Mahmud, shine yafara kiranta da Hajja, daga baya Kuma sauran mutanan qauyen suke ce mata Hajja A'i, Bayan haihuwarsa bata sake haihuwa ba, har Mahmud yakai munzalin aure, ya samu mata Mai suna Hadiza, mafulatanar asali ya aura, Bayan aurensa da wata hudu, Allah yayiwa mijin Hajja rasuwa, anan taci gaba da Kula da Mahmud dinta, Wanda Yan qauyen suke kiransa da Mamuda, Mamuda bai dade da aure ba, matarsa Hadiza ta haifi 'ya mace Mai Kama da'ita sak kamar an tsaga kara,alokacin mamuda yace zaiyi wa Hajja takwara, Amma Hajja A'i wato Aysha Sulaiman bompai tayi tsalle ta dire tace wannan yarinya sunan qawarta Aysha za'a saka mata, shikuma Mamuda yadage sunanta zai sakawa yarsa, Amma ba sunan qawarta ba, haka Hajja ta dage tace inde sunan tane bata so, itade a sakawa yarinyar sunan qawarta wadda take burin su sake haduwa inda rabo, haka Mamuda ya sakawa yarsa suna Aisha, Bayan matarsa Hadiza ta tausheshi, tunda duka de sunan Nan iri dayane, saide ita Hajja har gobe tana fada bafa sunanta aka sakawa yarinya ba, sunan qawarta ne, wannan dalilin ne yasa take Kiran Jikar Tata da MESUNAN QAWA.

wato me sunan qawarta Aysha Yakubu Sagagi, Bayan haihuwar Aisha da shekara daya da rabi, Allah yabawa Ummah ciki, ta haifi Jabir, tsiransa da Aisha baida yawa, daga Nan bata sake haihuwa ba, Aisha taja qaninta Jabir ajiki, sun shaqu sosai, tunda tayi candy bataci gaba da karatu ba, saboda babu Hali, saide bata fitar da ran zuwa gaba zatayi karatun koda a Dakin mijinta ne, Jabir yana candy Shima ya zauna baici gaba da karatun ba, hakan yasa Hajja A'i tafara sana'ar kunun Aya, tana Tara kudinta, saboda karatun Jabir dakuma auren MESUNAN QAWA.

Suna Zaman su lafiya lafiya, saide wataran idan gigin tsufan Hajja yatashi, haka take tada hankalin kowa na gidan, mesunan qawarta ce kawai take taka mata birki azauna lafiya, Idan taso Kuma zakiga gidan kalau, idan Yan mulkin suka tashi kuwa Tofa Sai abunda tace.

Aisha tana zuwa wata makarantar islamiya, Ana biyanta nera dubu biyu a wata, wannan dubu biyun haka tatara na wata hudu tasiyo akuya take kiwonta, tana so Sai Jabir yasamu Addmissoin zata siyar da'ita ta siya masa kayan provisions dashi, batada yawan magana, Amma idan tafadi wata maganar saikinyi mamaki, kyakykyawa ce ajin qarshe, tanada dogon gashi irinna fulani me kyau da tsantsi, bakinta Dan qarami ne me launin pink, tanada dogon gashin ido, Wanda mutane dayawa suke tunanin sakawa take banata bane, tanada innocent face, zata aikata ma laifi Amma idan tayi kalar tausayi Kai ba zakace itace ta aikata ba, a'ido zakayi tunanin saliha ce,saide idan aka ta6ota Tofa babu haquri, masifaffiya ce, wannan Kuma bamu Sani ba halin Hajja ne tad'auko, wato Aysha Sulaiman bompai, kokuma Halin takwararta ta Dauko wato Aysha Yakubu Sagagi? Saimun nutsa cikin labari zamu tantance(=╪▐)


Back to story





Fan's ya Bayan kwana biyu? Ina fatan duk Wanda ya karanta wannan labari ya qayatar dashi


SHAHAAB littafin kudi ne, nera 300 ne babu yawa,kullum zaku dinga samun update, zaku turo nera 300 ta wannan account number=╪G▄<╪√▀

0164549488
Amina muhammad
GTbank


Zaku turo shedar biya ta wannan number 08033300034





Amnah El Yaqoub
'<╪√▀
[10/09, 22:14] +234 803 697 8511: <╪8▀SHAHAAB<╪8▀
(Romance)


Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name

Like my Page On Facebook=╪G▄<╪√▀
https://www.facebook.com/amnahel


3&4

ABUJA

mutane ne kusan guda biyar suke take masa baya, kowannensu yana Sanye da baqin glass a'idonsa,hakan bai Hana mutane rissinawa suna gaidashi ba.
cikin sauri yake tafiya kunnan sa guda d'aya manne da Bluetooth, daga yanda yake tafiya kadai zaisa kagane cewa matashi ne Mai jini ajika, ko kadan bayajin nauyin jikinsa, Sanye yake cikin suit launin ash, saide yacire jacket din Saman ya riqeta ahannunsa, hakan ne yabawa murdaddan dantsan hannun sa damar futowa, faffad'an qirjinsa yasamu yabaje yanda ya kamata acikin rigar, hannunsa daya, yana Sanye cikin aljihun wandon sa, fuskarsa a daure take, babu alamun fara'a kokadan, Amma hakan baisa kyawun fuskarsa damar bayyana ba, magana yake cikin aji, Amma dimple dinsa futowa suke duk da ba dariya yake ba, yanada hasken Fata yanda ya kamata, mutanen dake take masa baya basu barshi ba, saida suka kusan kaishi har gaban office dinsa, daga Nan ya daga musu hannu kawai batare Dayayi magana ba, yana shiga cikin office din Adede lokacin ne yake cewa "duk kayaiyayin mu dasuke kasuwa asake saukar musu da farashi yanda talakawa zasu iya siya, banaso sukai lokacin azumi" yana gama fadar haka yasaka Dan yatsansa ya danna agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa touch, Nan da Nan wayar ta katse

Wasu file yaduba, ko ten minutes baiyi ba, yad'auki wata takarda, yatashi yasaka suite dinsa,I'd card dinsa ya saqala agaban suite din nasa setin qirjinsa,anrubuta MAHMUD WAKILI, EFCC CHIRMAN.

Kai tsaye d'akin da zasuyi taro yanufa, dogon daki ne Wanda yaji kujeru masu mutuwar kyau tareda dogon table, an ajiyewa kowa gorar ruwa a gabansa, fuskar kowa d'aukeda face maks, office din yayi kyau sosai, gaba dayansu maza ne, Sai mata guda biyu, suna ganin shigowarsa cikeda ladabi suka miqe tsaye, saida ya zauna akan kujerar sa wadda take d'aukeda tambarin hukumar, dakuma manyan rubutu Wanda aka rubuta EFCC ajiki, sannan kowa ya zauna.

daga Bayan kujerar daya zauna sojoji ne guda biyu sun qame waje daya, Sai babbar tutar tambarin hukumar EFCC, dakuma wata babbar tuta ta qasar Nigeria, daga can sama Kuma Babban photonsa ne yayi kyau cikin suit yana murmushi, dakuma wani photon daban na shugaban qasa.


Basu bata lokaci ba suka fara tattaunawa akan abunda ya tarasu, zasu fitar da wani salon na yaqi dacin hanci da rashawa a Nigeria.

Saikuma maganar sunayen wadanda hukumar ta d'auka,a matsayin Wanda zasu bawa horo, zasu fitar da sunayen su zuwa wani watan ta manhajar hukumar, dakuma kafafen yad'a labarai.

Basu dauki lokaci Mai tsawoba suka tashi daga meeting din, daga Nan office dinsa yakoma yafara ganin mutane kowa da irin maganar dayake zuwa da'ita

Sai yamma yayi shirin tafiya gida, yana futowa kuwa mutanan nasa suka take masa baya har zuwa mota, mutum dayane yabude masa mota yashiga, Alokacin har anfara yayyafi kasancewar kudancin qasar sunfi arewacin Nigeria saurin samun ruwan sama, yana shiga motar ya Lumshe Idonsa, ga qamshin ruwan sama me dadi yana busowa cikin motar, yagaji sosai, zaiso ace yasamu anyi masa massage Ayanzu (>╪-▌)
Tafiya Mai Nisa sukayi, kafin su qarasa gida, Alokacin har ruwan yafara qarfi, sojoji ne awajan gidan, dakuma daidai kun Yan sanda, get man nabude musu get, driver ya danna hancin motar zuwa cikin gidan, gida ne babba gari guda, ba zakayi tunanin ma acikin qasar Nan gidan yake ba, acikin harabar gidan ma sojoji ne suke shawagi, motarsa tana tsayawa daga me gadi har sojojin wajansa suka nufa kowa yanayi masa sannu da zuwa, hannunsa yadaga musu kawai,kasancewar Ana Dan ruwa yasa yayi sauri Kai tsaye yawuce part din MAMA.

Yana shigowa falon yafara cire jacket dinsa, tareda necktie din wuyansa, duk da girman falon Nata, wani kafet ne Mai masifar laushi yake malale a falon, ga wata katuwar plasma tana aiki, daga fentin falon har kujerun da labulaye duka milk colour ne, wata tsohuwa ce mai kimanin shekaru sittin da shida a zaune, saikuma wata yarinya a tsugunne a gabanta, tana matsa mata qafafu

Cikin fad'a-fad'a tadubi yarinyar "ke! Kidena matsa min qafa da qarfi mana kamar kinsamu wani dutsi, nagaji dayin complain a kanki, Nan gaba kad'an zan'iya sallamar ki idan baki gyara halinki ba"

Cikin ladabi tace "kiyi hakuri Hajiya"

Cikin muryarsa Mai cikeda miskilanci yace "mama"

Kallan sa tayi tace "SHAHAAB kadawo?"

Bai bata amsa ba saida ya zauna yana fadin "wash! Allah na mama nagaji"

Yarinyar datake matsawa wadda aka kira

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

9 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment